You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta komai ya
fito kamar bata saka kaya ba. Duk namiji mai lafiya in ya kalli Narma a wannan
shiga sai ya ji yanayin da bai shiryawa jin sa ba har ƙwaƙwalwarsa. Ɗauke idanu
daga kan Narma a wannan lokaci abu ne mai wahala, sai mai juriyar gaske ne zai
kawar da ita daga idanunsa.Ta tsaru a cikin rigar, ta kuma yi mata kyau kamar ka
ɗauke ta ka gudu.

Kallon Mum tayi da take zaune ta ce, "Mum zan je shoprite" ta faɗa tana gyara zaman
hular kanta. Mum bata kalle ta ba ta ce, "ki taho min da diet stick ɗina ya ƙare."
"Okay Mum" ta amsa tana fita.

A harabar gidan ta tsaya tana ƙarewa motar ta kallo, ta san ta ce a wanke mata amma
sai ta ga kamar ba a taɓa ba. Cikin ɗaga murya ta ce, "Ina Kashim!?." Kashim jin
maganar ta ya fito cikin sauri da rawar jiki ya ce, "ga ni Ma'am." Nuna masa motar
ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ya kalli motar ya kalle ta ya ce, "i'm sorry
ma'am, bani da lafiya ne shiyasa......" dakatar dashi ta yi ta ce, "in ka ƙarasa
wallahi sai na mare ka." Jin abinda ta ce sai ya kalle ta dan kuwa a shekaru ita ba
sa'ar sa ba ce, ko yayanta Nabil ya girma balle ita.

"Who do you think you are...? You won't wash my car, and now you're telling me
you're not feeling well?. Damn your sickness!" Ta faɗa cikin ɓacin rai tana kallon
sa.

"I'm sorry" ya furta a sanyaye yana kallon ta. Narma ta saka baƙin glasses ɗin
hannunta ta ce, "ko mutuwa ce a kan ka kar ka sake aikata wannan gangancin, in na
ce ayi kawai ayi in ba haka ba you must regret about it."

"In sha Allah, Sorry Ma'am."
"Zan ƙyaleka saboda wannan ne karo na farko da ka yi haka, kar ka sake maimaitawa"
ta faɗa tana barin wajan kafin ta ce, "And make sure you've washed it before i get
back" ta faɗa tana karɓar key ɗin motar Mum ta shiga. A guje gate man ya buɗe mata
gate ta fita a guje.

Sai bayan ya kulle gate ɗin ya kalli Kashim ya ce, "ka yi sauri ka ƙoƙarta ka wanke
kafin ta dawo, yarinyar nan bata da kirki, a iya watan nan masu aiki goma ta kora
ta kuma ɗauko guda goma. Ka yi haƙuri ka yi kar ta ci maka mutunci a banza." Kashim
ya ce, "wallahi bani da lafiya."
"Haka zaka yi haƙuri. Kuma wallahi ba a wanke musu mota a gidan nan car wash ake
zuwa, kawai saboda ta samu hanyar ciwa wani mutunci ne ya saka ta ce ka yi. Dan ita
tana so ta ga tana ciwa mutum mutunci. Ta waje guda take da kirki wani lokacin, in
ta ga mutum a kwance babu lafiya a nan zata ɗan tausaya masa. Amma sai ciwo ya kai
ciwo, bata ɗauki ƙaramin ciwo a komai ba." Kashim ya yi ajiyar zuciya ya wuce jiki
a sanyaye. Inda an sabo da wulaƙanci da cin fuska da ƙasƙantar da mutum da yanzu
sun saba a wajan Narma.

•••••••••••
*KADUNA STATE*
*ALHAJI ABDALLAH AHMAD RESIDENT.*


Alhaji Abdullahi sannen ɗan kasuwa ne mai ji da kuɗi da iko da kuma alfarma a faɗin
ƙasa nigeria. Yana da matuƙar kirki da daɗin mu'amala ga kowa, ko ma'aikatan gidan
sa ya ɗauke su kamar ƴan uwan sa baya wulaƙanta su ko tozarci ko yaushe cikin wasa
da dariya suke. Mutum ne wanda ya san ya kamata, bashi da wulaƙanci ko kaɗan kamar
ba mai kuɗi ba, in ka ga fushinsa akan abu tabbas ransa ne a ɓace.

Mutum ne mai kyautatawa iyalan sa da matuƙar ƙaunar su, baya bari iyalan sa su yi
kukan babu ko ya ya abin yake. Haka kawai zasu kulle gidan a bar ƙasar kawai dan
jin daɗin ƴaƴan sa da walwalar su. Babu abinda iyalan sa suka nema suka rasa, kuɗi,
mota, fita ƙasashen waje da sauran kayan more rayuwa ya tanadar musu dashi. Shiyasa
suka kasance ƴan gata gaba da baya.

Matar sa ɗaya mai suna Zeenatu, uwar gidan sa mai suna Bilkisu Allah ya yi mata
rasuwa shekaru masu yawa da suka wuce. Yaran sa shida, biyar daga wajan Zeenatu
ɗaya tal daga uwar gidansa. Ahmad shine babba, Jawad, Jidda, Nayla, Jalila, Jalil.
Yara ne masu tarbiyya da sanin ya kamata, dukkan su sun tashi a turbar tarbiyya mai
kyau, ilimi, addini da kuma kyakykyawar rayuwa.

Kyakykyawar farar budurwa ce ƴar kiminin shekaru ashirin da huɗu zaune a
ƙasaitaccen falo mai kyau da girma tana danna waya. Falon yana da girma sosai ya
kuma tsaru matuƙa, kana ganin falon ka san na masu kuɗi ne ba na talakawa ba. Tana
da haske da kyawawan idanu da ƙaramin baki mai ɗaukar hankali, tana da ƴar ƙiba
kaɗan ba mai yawa ba, yanayin jikin ya dace da ita sosai dan komai ya yi daidai da
halittar ta.

Tana zaune tana danna waya fuskarta ɗauke da kyakykyawan murmushin da yake bayyanar
da dimples ɗinta, kana kallon ta ka san duk abinda take kallo a wayar yana bata
nishaɗi sosai. A yanayin ta zaka hangi tsantsar nutsuwa da kuma fara'ar da take da
ita. Hauwer Abdallah Ahmad kenan, wacce ake yiwa laƙabi da NAYLA.

"Nayla me ki ke kallo haka ki ke dariya?." Juyawa tayi ganin wacce tayi
mata magana sai tayi dariya cikin murya mai daɗin saurare ta ce, "Mama ina kallon
comady ɗin ƴan TikTok ne. Abiy ya fito?." Wacce ta kira da Mama ta zauna a kusa da
ita tace, "Yanzu zai fito."

"Gani na fito." Jin muryar mahaifin nata mafi soyuwa a gare ta sai ta miƙe tsaye
tana murmushi ta ce, "Abiy sannu da zuwa." Ya dafa ta ya ce, "Yauwa Mamana. Ya aka
yi ki ke nema na?." Zama yayi bayan ya zaunar da ita tana murmushi ta ce, "Ina so
daman zan je Kano cikin gari wajan Hajja na yi kwana biyu." Nan da nan annurin
fuskar sa ta gushe ya ɗago ya kalle ta ya ce, "Nayla!." Gabanta ya faɗi jin a yadda
ya faɗi sunan ta, kasancewar bai cika faɗa ba sai dai ya ce Mamana. Ta kalle shi ta
ce, "Na'am Abiy."

"Meyasa ki ke son zuwa Kano ko yaushe? Meyasa bakya son zaman gidan nan?." Nayla ta
kalle shi bayan ta rausayar da kai ta ce, "Ba haka bane ba Abiy, waya mu ka yi da
Hajja tace min yaushe zan zo shine nace mata sai na kammala nysc. Kuma yanzu Abiy
na gama services, tahfiz ɗin ma da na shiga na gama shiyasa nake naje" ta faɗa
cikin yanayi na shagwaɓa wanda zai tabbatar da ita ɗin ƴar gata ce.
"Amma kin san bana son zuwan ki Kano ko yaushe ko?."
"Na sani Abbiy, amma Hajja kakata ce tana so na je na dinga gaishe ta. Kuma duk
dangin Ummana a can suke, suna jin daɗi in naje na gaishe su."

Abiy yayi shiru bai ce komai sai kallon ta da yake yi ganin haka sai ta sunkuyar da
kai tana addu'ar Allah ya sa ya barta ta. Abiy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "zan
bar ki ki je amma baza ki jima a can ba, sannan ban yarda da yawo ba." Nan take
tayi murmushi mai bayyanar da kyaun ta da ƙuruciya tace, "in sha Allah Abiy. Na
gode sosai." Ganin tana farin ciki shima sai ya yi murmushi sannan ya tashi ya yi
musu sallama ya fita.

Nayla ta kalli Mama da farin ciki ta ce, "Mama bara naje na fara shirin tafiya
Kano." Mama tayi murmushi ta ce, "to sai kin dawo. Sannan kar ki damu da yace kar
ki jima, in kika tafi ba sai ya gan ki ba?." Nayla tayi dariya ta ce, "Kuma fa haka
ne Mama, bara naje na dawo" ta faɗa tana tashi da sauri ta shiga ciki.

Da muguwar harara Mama ta bita bayan ta ja tsaki ta ce, "na rantse da girman Allah
sai kin bar gidan nan, yadda uwar ki ta barshi kema sai kin bari. Wannan soyayyar
da yake nuna miki sai ta koma ƙiyayya nan ba da jimawa ba. Sai na saka kin zama
abin ƙyama a idanun mahaifinki. Irin wahalar da uwarki ta bani a gidan nan sai kin
an ninka miki ita a gidan aurenki. Bazan taɓa bari samarin da suke tururuwar son
auren ki su aure ki ba, in suka aure ki ai ban yi riba ba, ɗiyar Bilkisu ta rayu a
cikin gidan aure mai ɗauke farin ciki bayan ni ta wahalar dani a nawa gidan auren?.
Hmmm ai duk wanda ya ci tuwo dani miya ya sha, wallahi sai kin gwammace ba a haifo
ki ba. Mu je zuwa Nayla!."

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Tsakanin Narma, Nayla da Omar waye zai amsa KIRAN RABO..?🤩

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t

Book 1
P 02

Omar ko da ya fita a ƙofar gida ya tarar da yaran sa su uku suna jiran
fitowarsa, suna ganin ya fito sa suka miƙe ya ƙaraso cikin su yana kallon su sannan
ya ce, "ehmm matan Alhaji Yusuf na wa?." Ɗaya daga cikin su ya ce, "Alhaji Yusuf
nan baya?." Ya ɗaga masa kai alamun eh ya sake cewa, "Matar shi ɗaya ce." Omar ya
girgiza kai bayan ya saka hannu a aljihu ya ce, "mu je gidan."

Tafiya suka fara yi yana tsakiyar su fuskar nan tashi a tamke matuƙa, babu alamun
fara'a a tare dashi gabaɗaya babu damar kawo wasa ko raini a kan fuskarsa. Duk inda
ya wuce kallon sa ake yi amma babu damar ayi masa magana saboda kwarjinin da yake
dashi.

"kai Ummaru!."

Aka faɗa daga bayansa ya tsaya cak tare da juyawa dan ya san kaf unguwar mace ɗaya
ce ke ɓata masa masa ta kira shi da Ummaru. A hankali ya juya kamar yadda ya yi
tunani kuwa ita ce ya sake haɗe fuska ya ƙarasa wajan ta yaran sa suka rufa masa
baya ya kalle ta ya ce, "Omar sunana, in baza ki faɗa ba ki ce Tiger."

Ta harare shi ta ce, "bazan faɗa ba, ko zaka saka ni na faɗa ne?. Na faɗa Ummaru."
Ɗan kawar da kai ya yi ya ɗan saki fuska kaɗan domin yana matuƙar girmama tsohuwar
da babu abinda zai hana bai yi mata warning ɗin da baza ta sake ganganci ce masa
Ummaru ba. Hajja ta kalle shi ta ce, "Kwana biyu baka shigowa mu gaisa ko?." Ya
kalle ta ya ce, "zan zo."
"Allah ya kawo ka, a daina rashin ji a san an girma dai. Ka gaishe da Aisha
mutuniyar kirki."

Bai ce komai ba ya juya suka cigaba da tafiya yana ɗan murmushi jin abinda Hajja ta
ce wai a daina rashin ji. Tafiya suke yi har ƙofar gidan Alhaji Yusuf kamar yadda
suka yi niya. Ɗaya daga cikin yaran sa ne yayi sallama a ƙofar gida aka amsa daga
ciki. Kafin ka ce kwabo mutane sun taru a wajan saboda mamakin ganin Omar a ƙofar
gidan a tsaye, wannan dalilin ya saka aka tsaya kallo dan a ga me zai faru.

Alhaji Yusuf ya fito ganin Omar shi kansa sai da gabansa ya yanke ya faɗi dan bai
san dame yazo ba. Ya dake bai nuna tsoro ba ya kalli wanda ya yi sallamar ya ce,
"Lafiya?." Omar jin maganar sa sai ya ƙaraso yana kallon sa ya ce, "Ka jawa matar
ka kunne, kar ta dake faɗar abinda ta faɗa in ba haka ba zata yi dana sani." Alhaji
Yusuf ya ce, "me tayi maka?."

"Har gwara ace ni ta taɓa da zata fi zama lafiya, in ka tambaye ta zata faɗa maka.
A dai ja mata kunne saboda gudun gamuwa ta gaba" abinda ya ce kenan ya tafi daga
wajan. Yaron sa mai suna Tk ya kalli Alhaji Yusuf ya ce, "a ja mata kunne, Tiger
gargaɗi ɗaya kawai yake yi. Tunda kaga yazo har nan tabbas Didi aka taɓa, ka
tambayi matar ka abinda ya haɗu su zaka fahimta" yana gama faɗa ya bar wajan aka
bar Alhaji Yusuf da sakaken baki yana bin su da kallo.

Kamar yadda ya faɗa cikin unguwar Yakasai suka shiga kasancewar magriba
gabato garin a cike yake da ƴan kasuwa da ake dawowa. Har inda ya san ƴan dabar
yakasai suna zama suka shiga, kai tsaye ya hango wanda yake nema ya ƙarasa wajan su
yana kallon su kamar yadda suke kallon sa. Zama yayi a cikin su yana bin su da
kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ya kalli babban su ya ce, "Meyasa akuyar ka ta shiga
gidana ta cinye min dusa?."

Kallon sa ya yi ya ce, "Tiger ban fahimce ka ba." Tk da yake tsaye a baya ya ce,
"Tiger yana magana akan yaron da aka kashe a nan bayan kun kwace wayarsa, ɗan arear
Tiger ne."

Kallon Omar ya yi ya ce, "Tiger afuwa ban mu san na ku bane da hakan bai faru ba.
Ka gan shi nan yanzu maganar ma mu ke yi" ya faɗa yana dukan kan yaron. Omar ya
kalli wanda aka nuna masa kafin ya dawo da kallon sa ga Jijiya ya ce, "Wanne mataki
aka ɗauka akan hakan?."
"Babu abinda mu ka yi a yanzu."
"Ya zama dole a hukunta shi! Bazai kashe banza ba, kai ka san bazan ƙyale ba."

Jijiya ya ce, "Haba Tiger duk an zama ɗaya fa, kuskure ne kuma baza a sake
maimaitawa ba." Ya sauke ajiyar zuciya ya sake kallon Jijiya ya ce, "ya san an zama
ɗayan ya kashe rai?."
"Tiger kana da abin mamaki, meye aibu a kashe rai kamar yau aka saba?."
"Ko ku bari hukuma tayi aikin ta ko mu mu yi aikin mu, wanne ku ka zaɓa?." Jijiya
ya kalli Tiger ya ce, "yadda ka ce haka za a yi." Omar ya miƙe ya ce, "ku tashi mu
je wajan ƴan sanda"

Wanda ya aikata laifin yayi tsiru-tsiru da ido jin ana zancen ƴan sanda ya kalli
Jijiya ya ce, "Haba Jijiya ai ba a yi min adalci ba." Jijiya ya kalle shi ya ce,
"Kenan na bar ka da Tiger ya hukunta ka?." Kai ya sunkuyar cikin rashin abin yi, ya
kalli Tiger da yake kallon wani wajan daban.

Ya tuna kwanaki da wani ya aikata irin abinda ya aikata yaƙi yarda ya kai kansa ga
ƴan sanda, aka bar shi da Omar yana da ƙafafunsa basa takuwa saboda sun tashi aiki.
Omar ba ya kisa, amma za a yi maka abinda zaka gwammace kashe ka aka yi.

Ajiyar zuciya yayi ya ce, "mu je ga hukumar." Omar ya koma gefe kamar ma bai san
ana yi ba, tare suka tafi police station aka gabatar da mai laifi kamar yadda
maganar ƙwace wayar ta zaga duniya saboda irin kisan da aka yiwa wanda aka ƙwacewa
wayar. Video aka yi masa aka yaɗa a duniya ana tabbatarwa da mutane wanda ya yi
kisan ya shiga hannu, kuma za a yi masa hukunci daidai da abinda ya aikata.

A nan suka yi sallar magriba gabaɗaya, DPO yana ta yabawa Omar akan abinda
ya yi, duk da an saba ire-iren wannan laifin ya kan kawo wanda ya aikata don a
hukunta shi. Shi kuwa ko maganar kirki samu daga gare shi ba burinsa a hukunta shi
in ba haka ba shi ya ɗauki mataki. Ya tsani yadda ake ƙwacewa mutane waya kuma a
cutar dasu, kai da abin ka a ƙwace maka kuma a cuce ka saboda tsabar zalinci. In da
iya ƙwacen ne ma da sauƙi, amma bayan a ƙwace sai an cutar da kai. Shiyasa baya
ɗagawa kowa ƙafa akan ƙwace, ko da kana daga cikin yaran ka aikata sunan da ake
kiran sa zai yi tasiri a kan ka. Damisa ƙi sabo!.

Suna idar da sallah suka koma unguwar su kamar yadda suka saba. Waɗanda suka kalli
video da aka yaɗa sai kallon Omar suke yi suna mamakin yadda wani lokacin yake yin
aiki irin na masu hankali wani lokacin kuma ya yi aiki irin na ƴan daba.

Tare suka shiga gidan da yaran sa su uku har shi na huɗu. A lokacin Didi tana zaune
akan sallaya a tsakar gidan tana sauraron abinda ake faɗa a video da aka yaɗa na
yaron da Tiger ya saka aka kama. Ganin shigowar su sai ta kalle shi ta ce, "ka
ɗauko mu ku abinci." Bai ce komai ba ya nemi waje ya zauna dan sun san bazai dauƙo
ba. Goje ne ya ɗauko abincin da kansa dan gidan ba baƙon su bane, babu inda basa
shiga dan sune kamar ƴan aiken ta. Abincin ya kawo kowa ya zuba abincin yana ci.

"Omar amma abinda ka yi ka kyauta sosai, ina nan ina fargabar kar ka ɗauko min
magana ashe gyara ka je kayi. Da haka ka ke yi da ba ayi maka wani kallo na daban
ba" Didi ta faɗa tana kallon sa.

Numfashi kawai ya sauke bai ce komai ba sai tayi murmushi bata damu da shirun na sa
ba ta ce, "Tukur meyasa bakwa yiwa mai gidan ku faɗa ne? Meyasa bakwa faɗa masa
gaskiya?." Tk ya kalli Didi yana murmushi dan itace kawai take ce masa tukur a
zauna lafiya, Tk shine sunansa ba Tukur ba. Ya ce, "Didi Tiger fa ba yadda ki ke
tunani ya ke ba, mutum ne mai son zaman lafiya in kinga an samu matsala dashi akasi
aka samu."

"Ba wani nan, kawai kana kare mai gidan ka ne, kuma bakwa faɗa masa
gaskiya" ta kalli sauran da suke cin abinci suna murmushi ta ce, "Sai murmushi ku
ke yi babu mai faɗa masa gaskiya a cikin ku, na tabbatar in Omar ya watsar da
makaman sa kuma za ku watsar, domin kuwa ya zamar kamar shi ne komai na ku, in ya
ce ayi kuna yi, In ya ce a bari kuna bari. Da tattara ku ya yi ku ka koma kasuwa
duk da hakan bai faru, da nima na huta da ɗauko min maganar da ku ke yi." Ƴar
dariya suka yi dukkan su dan in da sabo sun saba da wannna maganar ta Didi. Shi kam
ko motsin kirki bai yi ba balle yayi magana abinci kawai yake ci.
Da kansu suka kwashe mata kayan aka shiga dashi kitchen kafin su miƙe tsaye Goje ya
ce, "Tiger zamu wuce." Shima tashi yayi suka fita gabaɗaya ta bisu da kallo tana yi
musu fatan shiriya. Sallah i'sha tayi bayan ta idar ta kunna tv kasancewar suna da
wutar solar, rana tsaka ta ga Omar da masu haɗawa aka haɗa a gidan. Da ta takura
masa da tambayar inda samu kuɗi sai ya ce sadaka aka bashi. Ta kuma san gatse ya yi
mata, kawai bazai faɗa bane shiyasa ta haƙura.

Babu jimawa ya shigo da sallama ta amsa ya samu waje ya zauna ta kalle shi ganin
yayi shiru yana kallon hoton da yake kafe a falon. Hoton su ne shida ita da
mahaifiyar su a ranar da ya cika kwana bakwai a duniya. Ganin abinda ya ke kallo ya
saka ta kalle shi ta ce, "ko dan saboda ita nake so ka gyara rayuwarka ka koma
mutum kamar kowa saboda tayi alfahari da kai a ranar tashin qiyama. Ko dan saboda
Mama da Baba...." Kafin ta ƙarasa ya kalle ta ya ce, "iya Mmaan dai, ki cire na
ƙarshen."

Da mamaki take kallon sa ta ce, "wai tsaya! Omar Baba ba shine ya haife ka? Meyasa
baka so a dinga zancen sa kamar ba uban ka ba?."
"Bai cancanci na dinga tunawa dashi ba ko kaɗan."
"Mahaifin?."
"Shi fa" ya bata amsa kai tsaye.
"Me ya yi maka?."
"komai ma" ya bata amsa yana ɗora ƙafa kan ɗaya.

"Omar ko dan saboda ƙasa da ta rufe idanunsa ya kamata ka manta da abubuwa
da suka wuce a baya. Kuma abinda ka ke fushi a kai baka san an yi ba labari aka
baka, amma ka ara ka yafa." Ya sauke ajiyar zuciya bai yi magana ba, ganin hakan
sai ta canja batun ta ce, "Baba Adamu ya yi min waya ɗazu yana tambayarka na ce
baka nan."
"Waye haka?" Ya faɗa yana danna waya.

Ta sake kallon sa ta ce, "Baba Adamu fa nace maka." Ya kalle ta yana ɗaga
yalwatacciyar gashin girarsa ya ce, "Shine nace waye haka?."
"Yayan mahaifiyarka." Ya girgiza kai ya ce, "ban san shi ba." Banza tayi masa bata
sake magana ba dan in ta biye masa ranta ne zai zo ya ɓaci da irin waɗanan kalaman
na sa marasa control. Jin ta yi shiru sai ya girgiza kansa ya ce, "ba dan ba dan ba
ko....hmm." Jin abinda ya ce sai ta kalle shi suka haɗa ido ya ce, "bani da dangi a
kaf duniyata, ke kaɗai ce dangina a kaf rayuwata."

"Hmmm Omar kenan!." Ta faɗa kawai bata tanka masa ba, in ta biye masa taurin kansa
ɓacin rai zai jawo mata, shi kuma ko a jikinsa gaskiyar abinda yake zuciyarsa ya ke
faɗa. Tv take tana kallon a lokacin aka hasko fuskar wacce ta kunna tv domin ta a
daidai lokacin tana cewa, "Sunana Narma Sagir Sani wacce ku ka fi sani da Barr
Nass."

Murmushi Didi tayi ta ce, "haka kawai Allah ya ɗora min soyayyar yarinyar nan a
zuciyata. Bana kallon shirin nan amma saboda a shafin ta na instagram na ga ta ce
yau za a saka interview ɗin da aka yi da ita ya saka na zauna." Kallon wacce take
kallo yayi yana mamakin ko meye abin so a yarinyar nan da Yayarsa take son ta oho.
Kallon sa tayi ta ce, "yarinyar nan bata burge ka?. Tana ƙoƙari wajan karɓar cases
na ƙananun yara, sannan an ce bata taɓa yin rashin nasara ba a duk case ɗin da zata
yi." Kallon tv ya yi ya kalli Didi ya ce, "Tunda ke tayi miki shikenan ai."

Dariya tayi ta dafa kafaɗar sa ta ce, "ɗazu da safe da baka nan Oga Mansur ya sake
zuwa gidan nan. Don Allah Omar ka daure ka koma harkar aikin kayan nan, aikin ya
karɓe ka kana da nasibi sosai akai meyasa baza ka dogara da kanka ba?."

"Bayan Allah akwai wanda na dogara dashi ne?" Ya tambaya ba tare da ya kalle ta ba.
Ta girgiza kai ta ce, "Babu, amma in da sana'ar aikin yin takalman nan ka ke yi sai
an fi ganin girmanka da martabarka, saboda kowa ya san harkar sa'anarka ka ke yi
babu mai yi maka wata magana ta banza. Aikin ya karɓe ka, ka iya fiye da tunanin
mai tunani, meyasa ba zaka riƙe iyawar ka ba?."

"Ni da ba sarki ko gwamna ba martaba da girman me zan nema? Tunda ina girmama kaina
hakan ya ishe ni. Kuma ko a yanzu babu wanda ya isa ya yi min maganar banza, ai na
wuce a kalli idona a yi min maganar da bata kwanta min ba. Ai ko kura ta rame ta
wuce rainin karnuka, kuma duk lalacewar giwa ai tafi ƙarfin suya, balle giwar da
lafiyar ta babu abinda ya same ta." Zata sake magana ya ce, "Didi zaki ɓata bakin
ki ne kawai, na wuce zama a ƙarƙashin wani, in zan yi sai dai nawa na kaina."

Ta girgiza kai ta ce, "Tunda kai ba kowa bane zama a ƙasan wani ya zamar maka dole,
kuma waɗanda ka ke so ka bawa haushi a rayuwa baza ka taɓa ɓata musu rai da ɗaukar
wuƙa ko adda da zaman prison ba. Murna ma zasu yi in suna ganin har yanzu kana
cikin wannan ƙasƙantacciyar rayuwar. Amma in ka gyara rayuwarka ka koma makaranta,
Allah ya ɗaukaka duk mai son ganin ka wulanƙanta a wannan gaɓar ne zai ji haushi."
Kallon idanun ta yayi na wani lokaci sai kuma yayi murmushi wanda fararen haƙoransa
da suke a jere reras suka bayyana ya ce, "Didi baza ki gane ba."

Kallon sa take yi ta ce,"Kar na gane Omar, Sai aukin iya karin magana kamar goyan
Kaka." Murmushi ya sake yi ta sake kallon sa ta ce, "Murmushi yana sake fito da
asalin kyaun ka Omar, Meyasa baka son yin murmushi sai wa ni kawai?."
"Ba kowa ya cancanci ya gani ba."
"Sai ni sai matarka?." Kallon ta ya yi jin kalmar mata da ta saka, ya ɗan sosa
walwatacciyar girar sa kamar yadda ta zama al'adar sa na ɗora yatsu biyu akan
goshin sa ya ɗan murza kaɗan amma bai ce komai ba.

Didi ta ce, "Hmm! Zan ga matar da zaka aura dai Omar."
"Au za a samu wacce zata aure ni?." Ta wara ido da mamakin kalaman sa ta ce,
"Meyasa ka ce haka?."
"Haka nan" ya bata amsa a taƙaice.

"Za a samu mana Omar. Shiyasa nake so ka ajjiye wannan ɗabi'ar ta ka, in kana a
haka ba ko wanne uba ne zai baka auren ƴar sa ba." Ya taɓe baki ya ce, "nima ba a
wajan ko wanne uba zan nemi aure ba." Murmushi ta sake yi jin abinda ya ce dan kuwa
ba a kayar

Please Login or Register in order to submit comment