You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uban ka zanci'' daga kai '' har wancen munafikin
abokin maka'' dannasan komeye kai kake zugashi'' shashashai kawai'' Momy kam gani
tai bala'in bazai kare ba hakan ne yasa''ta kalli munir tace'' munir tashi ka je
abokin naka yana sama'' Allah ya muku albarka'' ameen yace'' sannan ya mike ya nufi
saman benan'' dakin Habib ya shiga ,yayi sallama'' afalo'' ya sameshi a zaune'' ya
hada kai da gwywa sai huci yake'' sallamar ma ya gagara amsawa'' shiko munir
karasowa yayi kusa dashi ya zauna'' ya zuba masa ido'' daga bisani kuma yace''
bross meyake faruwa ne?" Naga gaba daya yanayin ka ya sauya ba yadda na saba ganin
kaba ?"Please waye ya taba min kai ?"hmm dan Allah munir ka keleni da abin da ya
dameni''wai har Ni mace zan na fada tana fada'' metstsssss yasa ki tsaki''ya daki
hannun kujerar sa da karfi'' yace oh my god'' munir Ni?" Am sorry bross kada wannan
abun ya dameka'' kaine haba daya bakason harkar wayewa'' danine tuni abinnan ya
huce'' a gurina''kaga abokina kwa kwantar da hankalin ka'' bari na kira wata baby
ta ''ta yaye maka da muwarka'' me kace'' mace''kuma Ni?"Ni ba dan iska bane'' kai
kasani kai ma da kakeyi kaji tsoran Allah'' uhm haba bross baza ka gane ba''kaganta
kuwa ta hadu komai nata''me kayau ne'' bari fa ka ganta'' hmm habib yayi kwafa ya
juyar da kai'' munir dai duk da haka be kyale Habib ba'' ya dakko wayarsa'' ya
bude'' yashiga neman hotunan Safiyya a wayar sa'' ko minti 蓷 aya ba ayiba sai gashi
ya nemo hoton safiyya'' nuna wa Habib yashiga yi amma Habib ya ki kallo yayi masa
banza'' da ya gajima,sai ya tun kudar da wayar ta fadi kasa'' ta tsage'' agigice''
Habib ya sa hannu ya dakko'' yana bawa munir hakuri'' sannan ya juyo da gaban wayar
nan take idonsa ya yi tozali da kekkewar fuskar safiyya''fuskar da bazai taba
mantawa da me ita a rayuwarsa ba''bakinsa har rawa yake yace'' munir kasan ta ne?"
Uhm nasanta mana baby na ce'' itace wadda nake cemaka zata kaudar maka da
damuwarka'' murya a sanyaye'' yace'' wannan din'' to idan baka sani ba wannan
yarinyar itace silar shiga ta wannan bacin ran'' kuma wallahi bazan gushe ba har
saina koya mata hankali'' ashe ma karuwa ce'' ''yar tasha'' shine zata kalli
tsabar idona tace min'' watakila ma kashin kare yafini'' daraja'' ashe ay gwarani
da ba zina nake aykatawa ba'' munir dan Allah inason ka hadani da wannan yarinyar
domin ina wulakanta rayuwar ta'' wallahi sai mahaukaci tafita kyaun gani a idon
duniya'' munir taya zan samu wannan damar''


Pege 6

Nisan tawa munir yayi'' sannan yace hanya daya ce'' bross'amma gaskiya banjin zaka
iya ba'' fadamin munir koma mene zanyi Indai zanga rayuwar ta a wulakance'' uhm to
kawai ka auteta''takoma karkashin ikon ka ''dagan kuma saika yimata duk wani
hukuncin da zakai mata'' inyaso sai ka saketa''uhmm shawara me kyau'' da feyde''
nayi niyar na biya wani kudi yayi mata'' nasan zataji ciwo sosai an rabata da
budurcinta'' ashema ''yar kwaltace'' idan ma nayimata haka amemakon taji babu dadi
sai dai taji dadi'' shikkenan''yaushene zaka kaini gidan su?" Yauma idan a shirye
kake zan rakaka'' okay babu damuwa, kabari sai gobe ,yau zanyiwa abban mu magana,
gobe idan yaso sai aje a nemamin aurenta, sanan adaura auren a lokacin, dan har na
matsu na fara azaf tar da yarinyar, hhhh munir yayi dariya ya ce kai abokina,
wallahi duk wan da ya tsokano ka ya san me ya tsokano, Ni yanzu zan huce'' gida,
okay'' babu damuwa ka gay da su umma'' Tom zata ji ya mike har yaje bakin kofa
''sann ya juyo yace'' bross ya zakai da Anty Adama kasan dai Anisa tana sonka''
kuma sabi da kai ta dawo gidannan da zama '' wallahi da matsala fa sosai'' dan da
nashigo na iske anty Adama a falon'' kasa'' tana ta surfa masifa'' .

Metstsssss'' yayi tsaki yace dan Allah munir kabar wanan zancen'' nifa banason
Anisa'' na fadamata amma ta kasa ganewa'' kuma ina ruwana da masifar mahaifiyar
ta'' kaga munir wallah duk abin da nace zanyi sai nayishi hankalina zai kwanta''
sai dai duk abin da za,ai agidannan ayi . okay tom shikenan ni dai kaga tafiya ta
''kadaiyi tunani sosai ...yana fadar haka ya fice daga dakin..

Shima Habib sauka yayi ''kasa be ga kowa ba a falon'' da alama dai Anty Adama ta
tafi'' kai tsaye dakin momy ya nufa'' ya kwankwasa'' kofar ''daga ciki aka bashi
izinin shiga'' ya murda kofar,bakinsa dauke da sallama ya shiga'' cikin Muryar
Dattako Abba ya ce'' Wa, alaikumussalam'' ya amsa'' Habib shiga yayi'' ya samu
guri a kasan kafet ya zauna'' yayi shiru bece komai ba'' momy ce ta kallacrshi
tace'' Abee kashigo kuma kayi shiru'' meyake damun kane''kwanan nan'' uhm momy dama
''uhm dama nasamu matar aurene'' ya fada yana sosa kai'' wacece ita'' momy zan
kawota ku gysa'' abee Wai ba dai kacemin Ba Anisa bace'' eh momy ba ita bace'' what
to wacece''. Wallahi baka isaba'' abee ''sokake kasa adama'' ta zo tayimana hauka a
gidannan'' ''yar ta kafe ta ki aure tace sai kai shine zakace mana kai baka sonta''
ita waccan wadda ka keso'' 'lyar gidan uban wace'' a garinnan'' waye ubanta abee
har da zaka ki ''yar,uwarka akanta'' haba Fateema'' Meyasa kukeson yiwa yaronnan
dolene''yace baya son ita Anisa din'' ba''sai ku hakura ba'' yanzu ko mace an daina
yiwa auren dole, ballantana namiji'' shekara nawa muna son yayi aure amma ya ki
yayi'' saiyanzu Allah ya kawo kuma sai ki hana a,a''. abee yaushe kakeson muje
munema maka autenta'' Am abba gobe na keso'' sanan agiben nakeso a daura auren''to
gobe kuma abee ''to Allah ya kai mu Allah ya sa albarka aciki'' bari sai na kira
kawunka na masa magana '' a sawo goro da alewar daurin aure'' ke kuma fateema ki
tashi ki sanar wa hjy zee ta yo mana Odar kayan daga kasar waje ''sanan kice agobe
da safe muke bukata'' ita dai momy bata sake cewa komai ba sai Tom ......


Abba ne ya sake kallon Habib yace'' tashi katafi abee Allah ya maka albarka...




Pege 7


____tun a rananr da munir ya bar gurin Habib ''ya huce'' kai tsaye inda suka saba
haduwa da Safiyya'' ba ,a fi ''yan mintina ba sai gata ta iso gurin'' tana zuwa ta
zauna a bakin gadon shima zama yayi''ya dan kwantar da Muryar sa yace'' safiya''
tambayar ki nakeso nayi ,ina so ki fadamin tsakanin ki da Allah'' insha Allah zan
fadamaka gaskiya koma meye'' muddum nasani'' okay ya fada tare da dakko wayar sa a
aljihu'' ya budeta''ya shiga hotuna'' ya dakko hoton Habib ''sanan yace'' kinsan
wanan?" Karbar wayar Safiyya tai tace'' gaskiya bansan shi ba Ni ban taba ganin
mekama da wanan mutumin ba ko a film''ay ina tunanin irin wadannan mutanen ganin su
sai ancike Form'' kokuma kaje kasashen waje'' munir kam tun da Safiyya ta fara
magana'' ya gane cewa tabbas ba ita ce ta yiwa Habib ''rashin kunya ba''to kenan
idan ba ita bace wace'' saliha ce'' dagowa yayi ya sake kallon Safiyya
yace''kincemin kanwarki tana da tsiwa sanan bata da kunya'' ko?"ehy'' anyi haka
tabbas saliha bata ragawa kowa'' uhmm yayi murmushi yace'' am Safiyya''bakece kuka
hadu da Habib ba''salihace'' yanzu zancen da nake miki Habib ya kamu da soyayyar
ta'' gashi ita kuma bata da kunya'' shi kuma bayason raini'' ko zaki taimaka mana
akan wanan lamarin'' tunanin tafada'' tashig nazarin maganar munir'' azuciyar ta
tana cewa''tabbas bazata bar damarnan ta huce ''yar,uwar taba'' dolema tayi wani
abu akai'' dontasan muddum salula taji maganar nan ba yarda zataima'' murmuushi
tayi daga bi sani kuma tace'' na'amince zan taimaka muku'' amma me kukeson na yi
akai'' anna take munir ya fadamata duk abin da zatayi'' sanan ya sanar mata yana
bukatar adaura auren agobe'' Da taso taki yarda amma daga bisani kuma sai ta amince
da maganar sa'' sukayi sallama ta huce gida''.


A lokacin da ta shiga gi da bata ga saliha ba'' hakan ya na nuna mata alamun''
tatafi islamiyya'' Umman su kuma tana daki'' daman bata ga fitar taba'' batasan
kalar kayan da tasaba'' wani mayaudarin murmushi tayi'' ta shiga dakin'' ta rike
kugu tace''umma ina Safiyya take?" Wallahi sai nama yarinyar nan rashin mutunci''
umma kema da kinsa dagama ta kafa kawai nake''sabi da tarigani sha 茩 ar iskar
duniya'' da sauri umma ta mike zaune tace''haba saliha ke dan Allah bake gajiya da
masifa ne''kidaina yi mata irin wanan bikiga yayar kice bane'' dan Allah kirage
wanan halin naki gidan wani zaki'' murmushi Safiyya tayi ''jin yadda mahaifiyar
su'' bata gane taba'' cikin salo irin na ''yan duniya tace'' uhm umma daman yanzu
nake shirin fada miki'' kinyi siriki'' baki umma ta rike tare dacewa to rasa
kunya'' wato har wani cemin kike kinyi saurayi ko''nasan da safiya ce bazata yi
haka ba'' cigaba ina jinki''uhm umma abin fa babbanne'' dan dangidan hamshakin me
kudine''wallahi umma mun warke da talauci'' wai yace aya asanar da magaba tana gobe
zasu zo da magaba tanshi'' za,a daura aure'' kai dan Allah dagaske cewar umma ta
zaro ido'' Tom kirawomin baffanku'' a waya'' jikin safiya harrawa yake tashiga''
kiran numbar baffanku'' bugu biyu ya daga'' umma ce ta karba'' tayi sallama ya amsa
suka gaisa'' sanan ta shiga sanar masa abin da Safiyya tace mata'' babu laifi yayi
murna sosai'' sanann yace insha Allah gobe da da safe zamu zo'' gidan domin a
daura auren'' daga haka sukayi sallama'' tashi safiya tayi ta futa'' daga dakin
tabar umma sai murna takeyi'' tana futa'' tashiga'' tsalle ganin cewa tayi nasarar
yiwa Ummansu basaja'' ban daki tashiga'' ta watsa ruwa ta dauro zani a kirji ta
shigo dakin'' jiki a sanyaye tace'' umma dazu naji''kunata murna da ke da saliha
lafiya kuwa me yafaru'' anan umma ta kwashe komai ta fadawa Safiyya'' bakin safiya
kamar ya tsare dan dariya'' daga bisani kuma tace'' umma yanzu ina salihar take?"
Yanzu tafito ina tunanin tayi gidan su hafsane'' ko tahuce makaranta'' okay
''tafada tare da hucewa ta zauna a gefenta'' ...


Suna zaune a dakin sai ga saliha nan ta shigo ''dauke da qur'ani a hannunta''
shiga dakin tai ta zauna ''tana yatsine fuska tace'' kash umma nagaji wallahi'' san
samu school dinan dana ke zuwa ace ina da motata wadda nake tafiya aciki'' uhm
saliha kenan kwana'' daga yaufa shikkenn'' sai dai mijinki yadinga kaiki a
motarsa'' ke da zama ki auri danmasu dash'' cewar umma'' what ''me umma ni nace
muku nashirya aure ne'' Ni da ko saurayi ma bana dashi'' bangane inda kuka dosaba''
idan ma wasa kuke'' Ni banason irin wannan wasan'' tafada tare da hade girar sama
da ta kasa'' afusace umma tace kajimu da shashashar yarinya nuzaki rainawa
hankali'' ki mai dani karamar mace'' wallahi''idan ma wani abun. Ne yashega kanki
tunwuri'' ki dawo hayyacinki ''dazunnan kigama cemin gobe za azo a daura aure''
yanzu Kuma ki nunamin baki san zancen ba''kull wallahi saliha kikiyayeni'' ko kinki
ko kinso sai an daura auren nan gobe'' dan da hannunki kika kira baffanku'' a
waya'' na sanar kasa'' Kuma kinsan baya magana biyu''


Pege 8

hannu saliha tasa aka ta tusa ihu ''ta fashe da kuka ta ajiye qur'anin ta watsa a
guje'' bata tsaya ko ina ba sai gidan su hafsa'' Hafsah tana zaune da ita da
mahaifiyar ta a tsakar gida'' kawai sukaga saliha ta shigo gidan tana rusa ihu''
gaba dayansu ta shi sukai suka rukota'' suna tambayar ta menene'' saliha lafiya
mene ya faru?"ko ummace bata da lafiya''ki fadamana meyafaru kin tadamana da
hankali?" cewar umman Hafsah'' kuka take kamar ranta zai fita tana koramusu bayani
tana cewa''dan Allah Hafsah kintaba ganina da saurayi a tsaye?"a,a meyafaru ?"wai
ummace tace gobe za,a daura mana aure da wani wan da Ni bansanshiba''what'' aure
kedawa kuma'' yaushe akai haka?"anan saliha tafada musu duk abin da ummanta tace
mata'' mamaki cike afuskar umman Hafsah''tace amma fa wannan abun da abin mamaki
yake'' anya kuwa'' ko dai Safiyya ce ta fadamata bakeba''wallahi umma zata iya
yiwuwa itace'' sabi da aduniya safiya ta tsaneni' bansan me naimataba'' amma kuma
ay ummanmu'' tana ganemu'' Meyasa takasa ganewa yanzu?"dan Allah kufadamin mezanyi
asan bani na kawo mijin aure ba'' uhm Hafsah tayi kwafa tace'' kije kisamu Safiyya
ki tambayata''kuyi maganar fahimta dake da ita ''idanma itace zata fada miki''
sannan kada kimata rashinkunya fa domin nasan hali'' uhm tom shikenanan na gode
tana gama fadar haka ta fice zuwa gida''


Tana shiga gidan abin ka da me hali baya fasa halinsa'' ta rufe Safiyya da masifa
ta in da tashiga'' batanan take fitaba'' tana cewa'' safiyya Meyasa zaki min haka''
ashe har tsanar da kikaimin takai haka''to bari kiji tun wuri kisa asoke wannan bu
kowallahi na manta da girmanki a matsayin ki na yayata na miki duka a gidannan'' me
saliha nikike fadawa wadannan maganganu''hmm Nagode ''kuma kije wallahi Indai
rashin kunya ce'' jurar ki wataran sai ansamu wan da zai koya miki hankali'' ki
rike wannan a zuciyarki'' domin nasan komai daran dadewa zakituno da abin da na
fadamiki'' tana gama fada mata haka''ta shige dan kwangon dakinsu'' ta barta a
tsaye tana huci'' zama tayi a gurin ta saka kuka'' tana ta tunane tunane kamar
wadda zatai hauka''.... Atakaice dai saliha anan gurin ta kwana dan ko runtsawa
batayi ba sai dai bacci barawo idan ya dauketa''...


To washe gari su baffanta suka yo sammako suka taho daga kauye'' tun karfe 7suka
taho basu isoba sai misalin karfe 2na rana '' suna zuwa suka tarar da har magabatan
Habib su iso harma da Habib din'' yasha farar shadda'' sai washe baki yake da alama
dai akwai wata makarkashiya dayake kullawa' masha Allah yau take ranar juma'a inda
ake shaida daurin aurena Saliha Usman aliyu'' da angonta Habib Alhasan madaki''akan
newa dubu dari 2''lakadan ba ajalan ba''masha Allah.

pege 9

Lokacin da sanar War daurin hauren tazo kunnen saliha'' sai da ta gigice'' dajin
sunan habib ''hakama Hafsah wadda tasan komai a tsakaninsu'' innalillahi
wainnailaihirraju un'' Hafsah nashiga uku'' Habib ne ,nasan ya aureni ne domin ya
wulakanta rayuwata innalillahi wainnailaihirraju un... Tana tsaka da yin salatin
nan sai ga baffan ta yashigo'' yana zuwa yace'' Saliha ,tace na'am baffa'' maza
kije mijinki yana son magana dake'' jikin Saliha na rawa zuciyar ta na dukan
uku'uku ta mike jiki babu kwari'' tafuta kofar gida'' tana fita sukayi idon hudu''
dashi ya sakar mata wani mayau darin murmushi wan da ita kanta batasan me murmushi
yake nufiba'' ahaka dai ta daure ta kara sa inda yake''ta tsuguna zata gaisheshi
yayi saurin dakatar da ita yace'' au ashe daman kina da tarbiyya'' ay nazata iya
masu tarbiyya ne suke iya gaishe da wan da kashin kare ya fisu daraja'' walhi sai
na koya miki tarbiyyar da kika yi missing dinta a baya, sai na nuna miki Ni Habib
dan duniya ne nafiki duniyan ci'' kuma daga rana irin tayau kifara irga'' ranakun
mutuwar ki'' Ni bani zankasheki ba amma wahala zata kasheki'' yana gama fadar haka
yayi tsaki ya ce karuwa kawai me bin mata'' daganan kuma yasa hannu a aljihu ya
debo bandir din kudi ya mika mata ''dakamar bazata karba ba '' sai tajuya taka duk
idon mutane akansu yake'' hakan yasata sa hannu ta amsa'' ta juya zata tafi'' yace
kuma ki shirya anjima za,a zo adaukar mini ke amarsuna ,yayi murmushi ya kashe mata
ido daya ya bargurin''....

Tsayawa tai tabi bayansa da kallo''tana nazarin abin da Habib zai iya aikata
mata'' tabbas tun yanzu tafara gasgata maganar Safiyya''datace in dai rashin
mutuncine zata samu ubanta ''ay ko gashi tasamu tunkan taje ko ina.

Gajiya tai datsaiwa a gurin don idan tacigaba da tsayuwa hawaye zai iya zubomata
abin da yafi sauki ta koma gida tanemi shawarar hafsa''

Shiga tai gidan'' ta samu hafsa'' a zaune ta yi tagumi''karasawa tayi ta kamo
hannunta suka fito waje'' tafiya suka shigayi har sai da suka isa wani lungu inda
babu kowa sannan saliha tace'' Hafsah nashiga uku'' bana fadamiki ba''Habib bazai
aureni ba sai da wata munifar'' dan Allah ki bani shawara'' yazanyi ne'' hafsa''
kodai na gudune?" Me ki gudu idan kika gudu ina zaki'' haba saliha kidai sake
tunani'' uhm,to ya kikeso nayi dan Allah Hafsah ki taimaka kifadamin yazanyi'' idan
kuma bazaki iya taimakona ba gwara na gudo'' don wallahi Habib bazai barni ba
kasheni kawai zai'' hmm saliha ,naam hafsa'' tayi magana cikin kaguwa'' inason ki
saurareni kiji mezan fada miki'' wannan fa abu da kika ga ya faru ''daman can Allah
ya tsara haka saita faru arayuwarki ''allah ya tsara dole sai kin zama matar Habib
''karki wani saka damuwa a zuciyarki kawata'' inason ki dake kamar yadda nasanki
baki da tsoro to inason idan Habib ''ya cemiki (A)kicemasa (Z)don billahillaxi da
alamun Habib akwai abin da yatama''kada kiji wani tsoro'' wuya bata kisa'' ko da
kin mutu'' a dakin mujinki kika mutu ba adakin wani katon ba''yanzu idan kikace
zaki gudu'' bafata nake miki'' ba ,ki hadu da wasu mugayen suyimiki fayde ko su
illata ki'' inga ya sun cuceki'' to ko kinga da wannan gwra zaman gidan Habib'' ko
banza zakici ki sha'' kimore'' habama sai na koyamiki abin da zakiyi sai kace ba
kike islamiyya ba ''kinga mukoma gida kada azo ana nemanki'' .uhm saliha tayi
ajiyar zuciya ta goge hawayen ta'' suka koma gida,...


*Anisa Anisa, meyasameki haka'' fadamin kukan mekikeyi'' yanaganki da jakar
kaya niki__niki kodai fateeman ce ta koroni?" Anisa a guje tasaki jakar ta fada kan
kirjin Hajiya Adama ta rungumeta'' tasaki kuka me sauti''zuciyarta na tukuki''
hankalin adamane ya tashi sosai'' tarasama mezatai'' bakinta har rawa yake daker
ta iya buda baki tace'' wai Anisa lafiya me akai miki'' kifadamin kinkasa magana''
ko wani abunne ya samu Habib''...?
Mami'' sun cuceni'' sai da suka bari nayi nisa akan soyayyar shi'' Meyasa
za,ayimin haka ''mami menarasa na ''ya mace''mene bani dashi?" Dallah Malama ki
fahimtar dani meyake faruwa ban gane ba'' suwaye'' suka cuceki'' zaki fadamin ko
saina ci ubanki a gidannan'' mami yau aka daura auren yaya Habib da wata, what
''hajiya Adama ta zazzaro ido tace'' kan kutumar uban can'' ammafa za a maimaita
yakin Badar '' me aurefa wai dagaske kike ko dai fada kikayi Anisa ,anya kuwa kinji
daidai'' za,ayi auren Habib dinne bansani ba''wallahi Allah mami da gaske nake
miki'' tarkashi ayko yau '' za ayi yakin duniya a gidan Alhassan'' Ni za aywa
tijara '' Ni Adama '' toni ba,a taboni bama hawa nake ballantana an tabani'' jar
uba'' Anisa'' huce'' muje gidan wallahi basu isa su wulakanta min zuri aba'' nafisu
dabbanta wallahi marabar mu da tinkiya wajan hauka'' Ni mutumce'' ita dabba, mota
suka shiga ''suka figa'' har cikin gidan su Habib'' ko motar bata tsaya ta gama
parking ba ''tafigi hannun Anisa tayi cikin gidan tana kwallawa Fateema'' kira''
kina ina bakar munafuka'' Fateema'' kufito ayita ta kare'' don wallahi yau
''mutuncin ma bansan shiba'' Fateema''munafuka ki fito ko na shigo ciki na koya
miki hankali...


Pege 10

Dasauri Hajiya fateema ta fito ''tana bata hakuri dan tasan za,a tuna''dan Allah
kiyi hakuri Adama abi abun asannu'' bazan bi asannun ba'' anki abi adun asannu'' Ni
zaku raina wa hankali'' walhi daidai nake da kugun ku daga ke har dannaki''
''yartawa zaku wulakan ta'' to wallahi ko yasaki'' waccan ''yar matsiyatan ya auri
Anisa,ko kuma yanzu na nunamuku Anisa na da gata'' aykin banza sai da kuka bari ta
gama zama ta wahalar da kanta taki kowa tace saishi''sanan kawai rana daya ku aurar
da danku ga wata.....

Dan Allah Adama kiyi hakuri''komai kikaga yafaru akwai sila''daman Allah ya ruga
ya tsara Anisa ba matar Habib bace'' dallacan tafi can''kirifemin baki''ay komai
daman yafaru akwai sila Kuma kece'' idan da kince ''yar,uwarsa zai aura ai da bazai
kiba'' sabo da tsabar bakin hali irin naku na ''yayan talakawa'' ay tun da yaya ya
auro diyar talaka munta samun talakawa a zuri'ar mu'' ke adama !!!ya daka mata
tsawa ya hade rai'' tare da karasowa gurin yace'' Adama matar tawa kike fadawa
wadannan maganganun?" Ashe dama baki da hankali'' haba yaya ni baka ga abin da
tamin ba'' sabo da tsabar rashin adalci tasan Anisa nason Habib amma takasa hanashi
auren waccan ''yar talakawan''Ni ban ma yadda da wanan matar takaba idan aka bibiya
ma ''yar uwasu ce'' dan nasan kaf danginsu babu masu ku 蓷 i bal...... Aykafin ta
karasa maganar ta taji saukar wani gigitaccen mari a kuncinta'' hagu da dama'' Waye
Abba ne'' afusace adama ta daga ido tana kallonta, dan tun da take da dan,uwanta
betaba sa hannu ya mareta ba sai yau'' jiki asanyaye'' tace yaya Ni kamara''?" Akan
na fadi gaskiya'' namareki Adama kiyi duk abin da zakiyi''akai badai akan Habibu
bane ''yace bayason Anisa ''gawadda yakeso sai na hanashi abin da yakeso ''to bari
kiji ko mace an daina yimata auren dole ballakuma namiji'' namijin ma dana '' idan
yazama dole sai jinina zata aura''tajira dawowar juneid muddum ya nuna yana sonta''
nikuma na amince zan auramata dana juneid''

A gigice Fateema''ta kalli Abba tace'' alhj juneid fa kace'' habibu ma be aure
Anisa ba sai juneid da ya shiga gari ya zagaye kasashen ketare yaga ''yanmata kala
da ban da ban'' banjin zai amince da auren Anisa''

Hajiya Adama kam bata karacewa komai ba''taja hannun Anisa'' suka fuce daga gidan''

Tun da suka koma gida Adama ke kaiwa da kawowa'' tana tafa hannu, Anisa na zaune
agefe tana bin ta da kallo'' jiki babu kwari Anisa tace dan Allah mami kiyi
hakuri''nasan duk wannan abin Ni naja miki ''har Abba ya mareki''idan akan yaya
Habib ne na hakura, no Anisa'' badai ance za ajira dawowar juneid ba '' mujira ya
dawo dan wallahi bazakiyi dakon banzaba'' A,a mami bana tunanin ya juneid zai
soni'' tun da Habib besoni ba juneid bazai taba sonaba , saboda yafi Habib komai na
rayuwa ''hatta kyau da duri da tsarin halitta Habib mummuna za,a kira shi agaban
juneid ''kuma wasa kukeyi''kawai ku bari na hakura'' walhi bazai yuwuba '' don
yanzu aka fara wasan'' dole sai Habib ko juneid ya soki...


INDIA

Zaune yake akan wata blue din kujera ''yar madaidai ciya, me masifar laushi''
hannunsa douke da jarida karama'' ya kuramata manyan idanuwan sa masu kama da na
mage'' zama nayi na karemasa kallo tun daga kansa har 茩 afarsa , farine tass kana
ganinsa kaga balarabe sannan kuma bature'' yana da dogon hanci'' tamkar biro'' don
tsayi da tsini'' labbn sa ko''in da kasan sweet sabo da laushi'' gasu jajur'' kanan
yana yin zanan love'' masu kyau ''gawani gashin baki da gemu da ya karawa fuskar sa
kyau da kwarjini'' 茩 wayar idonsa ba baka bace'' blue color ce'' me dan rashin
farifari acikinta'' gashin kansa yana da tsaya'' baki me laushin gaske sai sheki
yakeyi'' yasha gyara '' dogone sosai ,mutum me kyau da kwarjini ga haiba''suffar
jikinsa me kyau ce'' sana. Duk gabansa a murde suke, kirjinsa ma kadai abin
kallone'' wow masha Allah ya hadu'' komai nashi me kyau ne inda kasan shiyayi
kansa'' ayadda na fasalta mukushi kenan amma a zahiri yafi hala kyau'' dan narasa
tayadda zan kwatan tamuku kyaun da Allah ya masa.



Pege 11

Hello , my name is isha'' duk maganar da take shi dai juneid idon sa na kan
jari da be dago'' ya kalleta ba'' har sai da taga ji da magana ,azafafe ta fisge
jaridar tace'' juneid'' magana fa nake maka'' kansa ya dago a hankula ya zuramata
wadannan manyan idanuwan nasa mekama da na aljanu'' ya watsamata harara''jiki na
rawa ta mika masa jari dar tace Am sorry '' banza ya mata bece komai ba ya karbi
jaridar sa ya mike ya bar gurin'' bayansa tanufa da kallo'' tare da runtse
idonta'' tace wow'' Juneid is very very beautiful'' atake a gurin ta hadiyi wani
azababben yawu jikake kukukut'' ta sharce gurin da ya tsatstsafo mata tace Juneid
sai na samu abin da nakeso '' kajira dawowata'' tana gama fadar haka ta bargurin...


Shiko juneid'' gurin Parking ya nufa'' zai shiga motarsa'' da sauri aka budemasa
kofar tare dacewa'' ranka ya dade ''allah ya karamaka lafiya danisan kwana'' ameen
kawai yace'' yashiga motar'' shima wan da ya bude din wata motar ya bude ya shiga''
sanna ragowar masu gadin juneid suma suka shiga tasu motar'' suka sakashi a tsakiya
suka bar gurin'' tafiya sukeyi sosai'' ba su tsaya a ko ina ba'' sai bakin wani
katafaren gida'' wan da Ni kaina nayi tunanin gabaki daya garin ne a gida Daya''
ashe gidan mutum dayane wato Juneid'' me gadine ya wangale musu get suka shiga''
masha ALLAH'' iya kacin gurin ajiye motocin ma abin kallone'' harabar gurin na
dauke da fulawoyi masu kyau da daukar hankali'' musamman ma gefan da ruwa yake sama
da kasa ''yana gudana a tsakiyar gurin'' bakaramin kyau yayiba ruwan na da launi
kala biyu'' launin farko farine na biyu kuma blue'' dasauri daya daga cikin masu
tsaronsa ''ya fito ya bude masa murfin motar ya fito'' yana tafiya kamar bazai
yitaba sabo da tsananin isa da kasaita'' har ya isa bakin kofar falon'' gidan'' tun
kan ya karasa kofar ta bude'' kofarma kadai abin kalloce''domin juyi takeyi tana
haske tana walwali'' kamar dai wadda aka sa mata wayarin a ciki'' shiga yayi ''ya
dan tsaya kadan ''sai ga wani basamu dan mutum nan ya karaso'' in da yake ya zame
rigar dake sanye a jikinsa'' yana cire masa ya tsaya cak'' tare da cewa'' Barka da
isowa yallabai'' daga kai kawai Juneid yayi ya huce'' wow masha Allah'' tarkashi
idan kaji ana cewa aljannar duniya to ga ta a cikin gidan Juneid'' falon'' gidan na
dauke

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment