You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya zamo ina wuta
su Goggo su sakata cewa wai ta gama mallake
Mujeeb tunda har bai iya aiwatar da komai sai itace
mai aiwatar masa, baya shawara da kowa a
al'amuransa sai da ita to ba ita bace zata haihu, sai
ta bari tayi duk abin da taga dama a nata amma
wannan ta ja baya taba mai haifuwa fili ta yi yadda
take so lokacinta ne ita kuma sai ta jira nata lokacin
yazo.
Wadfannan maganganun sukansa Muneeba kuka, tunda ita tana yin komai domin Allah ne ba
don a sota ko a yabeta ba, amma sai gashi bita da kulli ne ke biyo baya ana zargin ta kuma tasan wani
55
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
abun in bata sa baki ba Mujeeb baya saya cewa
yake a bari ta haihu lafiya sai ya saya.
Kullum Mujeeb cikin lallashin Muneeba
yake yi akan ire-iren maganganun Goggonsa da
matarsa, don ma yana takawa Suwaiban birki a daki
yake wanketa da soso da sabulu batare da Goggo ta
san anyi ba tunda itace ke daure mata kugun yin
takama da duk iskancin dataga dama a cikin gidan
shi kuma a daki har bara zanar rabuwa da ita ya
keyi, a cewarsa don ya saketa ba wata tsiya bane,
ita kuma da taji Kalmar sakin sai ta shiga taitayinta
don a duniya babu abin da take so irin Mujeeb,
balle yanzu da take dauke da cikinsa, ita ta sanma
barazana yakeyi b zai taba iya sakinta ba, sai dai
wannan barazanar da ya ke yi tasa zata shaidawa
Hajiyarta a kansa tunda har yanzun basu mallaki
zuciyarsa irin yaddda suke so ba, ta na jin idan ta
haihu wani bokan zasu canza in har ba suga canji,
ba tunda suna so yaso jaririn da Suwaibar za ta
Haifa irin mahaukacin son nan da bai taba yiwa
kowa irinsa ba a duniya, shi yasa. duk inda zasu
sami asirin wannan soyayyar to za su je su bada
kudi komai yawansu ba su da matsalar kudi Mujeeb
na sakar masu bakin aljihu daidai gwargwado.
56
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
**** ***** *****
Cikin tsakiyar dare nakuda ta kama Suwaiba, Allah yasa Mujeeb a dakinta yake ihunta ya tashe shi ya farka a gigice ya ganta kwance a Rasa tana birgima
tana ihu ya diro daga gadon yana tambayarta
menene ta ce "Ciki na da marata da baya na ne suke
ciwo zan mutu ka taimakeni kả kaini asibiti wallahi
mutuwa zan yi ya zo ya riketa yana cewa "Ki dinga
yin Salati ne ba ihu za ki dinga yi ba bari in taso
Goggo ina jin haihuwa za ki yi sannu ki yi hakuri
yanzun za mu je asibiti." ya mike zai tafi kiran
Goggo, ta damko kafarsa ta rungume tana kuka
tana cewa "Ni mu tafi asibitin ba za ka fita ka barni
ba wayyoo Allah ka zo ka taimakeni" ya dawo ya
tsuguna gabanta ya ce ki yi hakuri ki daina ihun nan
sunan Allah kawai za ki kira shi ne zai taimakeki
sakeni in taso Goggon mu tafi "Da kyar ya banbare
kafarsa da ta danka ya fice da sauri ya je ya bugawa
Goggo kofa, jikinta na rawa ta tashi ta bude tana
tambayarsa abin da ya faru yace Suwaiba ce ba.
lafiya ina ganin haihuwa zata yi shine na ce bari in
gaya miki za a kaita asibiti.
Tace to! Abin ya zo? To Allah ya raba su
lafiya bari in je dakin sai ka yi maza ka fito da mota
ta wuce dakin Suwaiban shi kuma ya nufi dakin
Munceba tana zaune bisa Sallaya tana addu'o'i
bayan ta gama nafilar dare ne ta ji ana bugun
kofarta gabanta sai đa ya fadi a tsorace ta zo tana
57
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
tambayar "Wa ye? Ya ce nine Munceba bude tana
jin muryar mijinta ta yi sauri ta bude kofar tana
tambayarsa abin da ke faruwa ya gaya mata
Suwaiba ce za ta haihu nan da nan ta soma jero
addu'o'i ga 'yar uwar zamanta na Allah ya sauketa
lafiya koma daki ta yi ta dauko wayarta dama da
dogon hijabi a jikinta ta yi saurin rufo dakinta ta
biyo shi zuwa dakin Suwaiban ta iske su da Goggo
suna kokarin daukota don a fita da ita zuwa waje
cikin mota.
Munecba ta ce, Ka fito da motar ne? Ya cе,
duk na rude wallahi na manta in fito da ita ga
makullin can kan (Side bed) dauka ki fito da motar
da dau makullin da sauri ta je ta fito da motar daga
inda take ta juyata ta fuskaci hanyar fita sannan ta
dawo suka kamata suka kaita bayan mota ta suka
kwantar da ita tana ta aikin ihu da kiran Mutuwa
Goggo na ta lallashinta da ta ji Mujeeb ya ce ta
daina ihu ta dinga Salati sai ta haushi da fada, Don
Allah ka kyale yarinyar nan in ma ta yi ihu ba laifi
bane saboda haihuwa tamkar zarar rai haka radadin
ya yake don dai baka san zafin bane, in ba za ka
lallasheta ba to ka kyaleta.
Muneeba na kokarin shiga gaban mota su
tafi sai Goggo ta ce A'a ba da ke za a ba, wannan
sabgar ta manya ce" Muneeba ta yi saurin ba
Goggo hanya ta shige motar Mujeeb ya matso
kunnenta yace "Yi hakuri bari mu tafi da Goggon
58
S
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ki tayamu addu'ah Allah ya sauketa lafiya, tunda kin tada hankalinki bana ma son ki je wata damuwar za ki karawa kanki" ya shafi kumatunta
ya zagaya ya shiga mota suka tafi.
Wasa farin girki, ashe ma nakudar somin
tabi ne wai maye ya ci jariri domin kuwa da a ka je
asibiti lokacin ne ma ta soma asalin nakudar wadda
ta kaita har wayewar gari bata haihu ba sai bakar
wahala da take sha tunda har ruwan nakudan an sa
mata amma ba ta haihuwa ba.
Muneeba tana gida hankalinta a tashe duk
da cewar suna waye Mujeeb na gaya mata duk halin
da ake ciki haihuwarta ta zo gadan-gadan har kan
bebin ya fara kunnowa amma sam babu hanyar da
zai fito Nosis din sun yi iya kokarinsu don ganin ta
haihu da kanta amma abin ya faskara hakan ne ya
sa suka yanke shawarar sai dai a yi mata operation
(C.S) a cire bebin domin kuwa ya wahala sosai za a
iya rasa ransa ko a rasa ran uwar tasa.
Hajiya Harira da ta iso da Goggo suna jin
maganar za a yi mata aiki sai suka hau kuka Mujeeb
sai ya kasance shine mai basu hakuri lokacin da ya
je ya sa hannu a yi mata aikin a ofishin likitan.
Tuni har an kammala shirye-shirye sun shiga da ita Mujeeb ya lalubo waya sa ya kira
Muneeba tana dauka cike da zumudi
Tace, "Hala ta haihu?" ya sauke ajiyar
zuciyar yace "Bata haihu ba yanzu haka ma (C.S)
59
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
suka ce zasu yi mata nasa hannu har an shiga da ita
sai ki taya ta addu'a Munceba ta dafe kirji ta сс C.S
ba za ta iya haihuwar bane za su yi mata C.S? Ya ce
yaron ya kunno kai amma babu kofar da zai fito sun
yi iya kokarinsu abin ya gagara, sunce za'a iya rasa
bebin ko ita shi ya sa ya zama dole ayi aikin" Ta ce
Innalillahi wa Inna Ilahiri Rajiun Haka Allah ya
tsara al'amarinsa sai dai mu yi addu'ar Allah yasa
ayi aikin cikin sa'a Allah ya basu lafiya ita da bebin
gaskiya ba zan iya zama a gida ba gani nan yanzu
zan zo asibitin.
Ya ce "Yauwa gara ki taho, sai ki shiga
dakin Suwaiban ki hado kayan bebi da duk wani
abu da kika san za'a nema bayan an fiddo bebin sai
ki hado ki taho da su, ta danyi jim sannan ta ce,
'Kana ganin ba matsala idan na shiga dakin? Don
gaskiya ina gudun abinda zai je ya zo, ya ce ba wata
matsala tunda zuciyarki Fes za ki yi abinda na
umurce ki tace, shike nan, a ina makullin dakin ya
ke? Ya dan yi shiru yana tunanin inda ya saka
makullin lokacin da Goggo ta je ta rufo dakinta
mika masa makullin, sai ya laluba aljihunsa saboda
tunawa da ya yi kamar anan ya jeia shi ilai kuwa sai
ya ji makullin ya ja tsaki ya ce k n ga ma makullin
nan a aljihu na yanzun ya za'a y shi ya sani ba na
son ana wani rufe-rufen kofa ko ne za'a dauka ko
ayi mata a daki ban sani ba, g shi mun taho ba
kayan bebi yanzun idan sun fiddo shi sai dai uwarta
60
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ni
ta
ban
circ lullubin ta ta bayar a rufe mata jikan ta don san yadda zan yi ba" Abin dariya abin takaici
duba
Muneeba ta cc, yanzu ka yi sauri kawai kazo sai mu kayan idan muka dauka sai mu tafi tare" Ya ce shike nan gani nan zuwa".
Ya je shaidawa su Goggo zai je gida ya dauka kayan jariri Hajiya Harira tayi Karaf ta се, "Bari in zo mu je sai in duddubo tunda kai ba sanin abubuwan da za'a dauko ka yi ba" ya ce a a ku
zauna bari kawai in je ai Muneeba na nan sai ta taya ni mu duba". Goggo ta yi saurin cewa, Muneeban
ce za ka sa ta shiga ta yi mata bincike a daki,
wannan ai ba daidai bane in dai ba kai za ka dubo
ba to ba zai yiwu ita ta shiga ta duba ba ehe! Ta kare maganar a zafafe kuma cikin bashi umurni.
a
Ba da son ransu ba ya tafi ba tare da wata a
cikinsu ta bishi ba ya shiga gidan ya iske Muneeba
tsakar gida tana ta aikin mai kawo cikin damuwa
take sosai. Ta yi saurin ta zo ta rungume shi tace
har yanzun basu fito da ita ba? Ya ce basu fito da
ita ba amma muna sa ran za'a yi nasara ki kwantar
da hankalinki mu je mu dibo kayan".
Ya sa makullin ya bude dakin Suwaiban
falon tsaf tsaf suka wuce d'akin baccinta nan fa suka
iske fakin kaca-kaca tamkar me 'ya'ya goma sai
karni dakin ke yi a zuciyar Muneeba tace kila shi
yasa Mujeeb sam baya zuwa dakinta kwana sai dai
kullum ita ke binsa nasa dakin ita kuwa kusan koda
61
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
yaushe a dakinta yake kwana a cewarsa yafi sakewa
a dakinta a dalilin rashin dabi'ar da Suwaiban ke
gwada musu sai ta bari Muneeba na dakin ranar
girkinta kawai sai su ganta tsulum tayi sallama ta
shigo babu ruwanta da bin dokar Musulunci na
cewa sai an baka izini sai ta kutsa kai tace tazo
daukan abu kaza ne idan yayi mata magana sai ta ce
ita da dakin mijinta ba me kafa mata dokar idan
zata shiga sai ta nemi izini. Tun daga ranar
Muneeba ta kudiri niyyar sai ta shayar da ita
mamaki in dai takamarta rashin kunya da nuna isa
da Gadara aka kuwa yi sa'a wata rana ta kutso
musu har dakin baccinsa tayi kyakkyawan gani don
ba zancę mummuna ba dama motsin shigowarta tayi maza ta canza salon
wasannin da takeyiwa Mujeebun sai ta shagaltar
dashi cikin mafi soyuwa awasannnin da yake son
tayi masa indai suna tare tunda tasan nan da nan
yake birkicewa ya shiga zuba sambatu da kukan
nishadi don ya kayatar da haduwar tasu.
Bai ma san a duniyar da yake ba a lokacin
data shigo Muneeba tayi tamkar bataji shigowarta
ba tana ganin yanayin da suke cikin abin ya kidima
ta ya kular da zuciyanta taja tsaki ta soma magana a
Kufule "Ribon dina nazo dauka ni banma san an
biyo miji ba, dadin abin dai abin da akewa mutum
nima ana mini, harma na fi mutum tunda ga zahiri
nan a jikina an gani" ta sake jan uban tsaki tasa
62
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
hannu ta dauki ribbon din nata dama ta aje shi ne Musamman don ta dawo dakin. Ta ficc Fuuuu ta bugo musu kofar fakin baccin gararam.
Duk Munceba na kallonta a fakaice shi
kuwa dan Gogan ya lula duniyar nishadin ma'aurata baimasan anyi ba shine fa tun daga ranar
ta kiyayi shiga dakin in bata da girki inma ta matsu
zata shiga to bata shiga haka kai tsaye ko tayi
sallama sai an bata izini take shiga.
ta
Muneeba ta dubi Mujeeb tace, Ka san inda
shuya kayan bebin ne? Ya girgiza kaim baisan
inda ta aje su ba amma ai ba zasu wuce cikin
Wardrob ko cikin akwati ba shi ya wuce gurin
wardrob ya soma dubawa ita kuma ta soma duba
akwatunan Suwaiban.
Wata babbar Leda ya dauko a cikin wardrob
din ya leka cikin Ledar sai ya hangi duk kulle-kulle
ne na magunguna kala-kala ya sa hannu ya soma
ciro su yana shinshinawa ya dubi Muneeba ransa a
басе уасе "Dubi wasu tarkacen magunguna ko na
mene ne? Oho in dai don a mallake ni ne to an yi
latti sai dai a mallake wani ba ni ba ya mikawa
Muneeba ledar yana fadin Dubi shirme don Allah.
Ta amshi ledar ta soma shinshina
magungunan sai taji sam ba su yi kama da
magungunan mata da ta sani ba tabbas Surkulle ne
da Kulumbotso irin na bokaye don da jin warin
magungunan sai kaji tsigar jikinka ta tashi.
63
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Amma sai ta kare Suwaiban da cewa Haba
dai abokin rayuwa ai ba zata yi abin da zai cutar da
kai ba, wadannan fa 'yan magungunan mune da
mata da ake sha na Karin ni'ima kudai maza kunji
dadinku komai fa za'ayi don kuji dadi ake muku
kun zama 'yan lelen mata. Ya ja tsarki yace, "Ni fa
banga amfanin shaye-shayen nan ba tunda babu
abinda ya amfana mata in don inji dadi takeyi to
batayi dace ba tunda har yau bata kamo kafarki ba.
Ita dai shiru ta yi saboda wasu daurin layu
dana gani a can kasar ledar, kawai sai ta yi saurin
daure bakin Ledar suka cigaba da dubo kayan
jaririn. Wani guru da aka zagaye da layu irin na
daurawa a kugu shi ya dago yake nuna mata tare da
wasu tarkacen magunguna da ya gani ransa ya sake
6aci yace Lallai yarinyar nan Mushirikace, dubi
uban layu da tarkacen magunguna na shirka yanzu
da zanyi magana sai Goggo tace sharri zanyi mata
to dai Allah yasa na gani zan san irin zaman da
zanyi da ita kema sai kiyi taka tsam-tsam da ita
tunda ba ni kadai zata yiwa ba har dake, ițama
Goggon nasan asirin sukayi mata suka mallekata
sam bata ganin laifin Suwaiban balle ta ga aibunta
mikomin wannan ledar duka haďasu zan yi in kona
zan ga uban da za ta tambaya idan ta nemi kayan
asirin nata bata gansu ba.
Ya amshi ledar ya zazzage kayan ciki sai
yaga layun da Muneeba ta boye dan kada ya gani ya
64
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
dubeta ya dubi layun yana girgiza kai yace "zama
na da yarinyar nan ina jin ya zo karshe don ba zan iya zama da mace mai asiri ba tunda ta riga ta halakar da kanta ni ma kada tasa in halaka.
Muneeba ta soma lallashinsa ka yi hakurі
fushin Fari ba naka banc, kabi komai a hankali
addu'a za ka yi mata Allah ya shirycta ya ganar da
ita hanyar gaskiya tasan cewa abin da takeyi ba
daidai bane kaga kun fara aje zuri'a dole kayi hakuri da ita".
Yace, "Don mun fara samun zuri'ah sai in
kyaleta ta cuci rayuwata? Ai ko duniyan nan ta
Haifa min ba zata yi kima a idona ba, tunda ta
kauce hanyar Allah, ke da baki haifamin kowa ba
kin fiye min ita sau miliyan tunda nasan halinki ciki
da waje ba zaki taba aikata abinda ta aikata ba, ba
zaki aikata abinda zai cutar dani ba ita kuwa cutar
dani za ta yi tunda kila asirin in karkata gareta ne ke
in juya miki baya kinga kuwa ai zata halakar dani in
dandana azabar wutar Allah. Shi yasa ma maganin
kada ayi to kada a soma.
Munceba dai hakuri take ta bashi. A wani
karamin Trolcy suka ga kayan da ta shirya na zuwa
asibitin suka dauko da sauri suka kulle ko ina suka
baro gidan saboda kiransa da Goggo tayi a waya
cewa ana nemansa a asibitin.
Isarsu asibitin kenan wata Nos ta leko tace a
bada kayan bebi cikin zumudi Goggo ta dau kayan
65
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ta mika mata tare da tambayarta har an ciro yaron
ne? Nos din ba tace mata komai ba kawai ta amshi
kayan ta shige dakin.
Za'ayi minti talatin sai gata ta sake fitowa
dauke da jariri cikin Shawul ta nufo su tana
murmushi tana cewa" Ga jaririn da aka ciro da
namiji ne anyi aikin lafiya idan an gama za'a fito da
ita." Goggo da Muneeba da Haj. Harira suka miko
hannuwa kowa shi yake son a soma ba dan Nos din
ta murmusa tace wannan yaro dan gata ne tunda
naga ana rububin daukarsa, bari ingani wazan fara
ba", ta dubesu tana nazarin kowanensu sannan tace
gadai matansa har guda biyu na gani sannan ga
uwarsa, to bari inba uwa shi don ita ke fara rikon da
a duniya kafın ya girma rikonsa da kularsa su koma
hannun matarsa”, ta mikawa Muneeba shi ta ce "Na
lura kece babbar uwarsa gara in baki sai ki raba
gardama tsakanin matansa ki fara ba uwargida don
ni a cikinsu bansan wacece amarya ba wacece
uwatigda kada suyi fushi suce sun fasa aurensa
daga zuwansa duniya ya fara walagigi".
Dukansu dariyan barkwanci wannan nos din
sukayi tayi Munceba data amshi dan tayi masa
addu'a ta tofa masa tace "Masha Allah, wannan da
namu da girma yake ga kyau duk me so sai ta bamu
sadaki" Ta mikawa Goggo yaron ta amsheshi
fuskarta cike da fara'a yau Mujeeb dinta ya haifi
dan kansa ta ce wannan ai kaine hoton Mujeebun
66
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
sak haka na haifoshi kato farin Sol, duba ki gani Hajiya Harira mijin namu son kowa kin wanda bai
samu ba? Muneeba na jin haka tasan da ita Goggo take amma sai ta saki baki tana fara'a an yabi dansu tunda tasan Allah dai shine mai badawa yadda yaba kowa tana fatan ya bata 'ya'ya masu albarka. Mujeeb ya iso gurinsun cike da murnarsa
tun kafin ya yi magana Goggo ta mika masa yaron
tana cewa "Ga yaro an ciro shi lafiya sai fatan Allah yaba uwarsa lafiya, gashi nan kamar kayi kaki ka tofar kamar kwabo da kwabo kai dashi, ka sami magajinka tun baka mutu ba.
Ya amshi yaron ya kura masa idanu yaron
kato kuma fari kamarsa sai dai shi baiga wata kama
da suka yi da yaron ba yadda Goggo ke kodawa illa dai yaron ya debo wasu abubuwa nasa kamar fari
da jajayen la66a sai dinful da yake dashi amma
idan ka debe wadannan yaron kama yake sosai da Suwaiba, sai dai kila nan gaba ya rikide ya zama
kamarsa tunda ance jarirai suna rikida su canza kamanni, amma yanzun suwaiba ya debo sai dai
babu wanda ya isa ya yi musun basa kama da
Mujeeb tunda Goggo ta fur'a dole a tafi akan yaro
ya yi kama da Mujeeb.
Muneeba ta leka fuskar yaron dake beun
Mujceb ta ce "Kaga kyautar da Allah yayinana
ko? In banda Allah waya isa yayi wa metam
wannan baiwar ta samun da? sai ka godewa Allah
67
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Yana can gurin Likita aka fito da Suwaiba,
su Goggo suka bi bayan keken da aka gungurota
har zuwa dakin da za'a ajeta. Nos din su suka dora
ta a gado daya dake fakin suka gyara mata kwanciya suka gyara karin rowan da aka fito tiyata
daure a hannunta sannan suka fita a dakin, bayan
sun yiwa su Goggo duk wani bayani da ya danganci
yadda za'a kula da ita da jaririnta.
Sai a lokacin ne Muneeba ta tuna da kayan
abin ci da abubuwan sha da suka taho dasu, amma
duk sun barsu a mota shine da Mujeeb ya shigo take
tuna masa sukaje motar suka kwaso a lokacin ne
Goggom da Hajiya Harira suka fita don gabatar da
sallar Azahar da La'asar da suka subuce masu.
Jama'ar Dukku haka suka dinga yo motamota zuwa Gombe don yin barka tare da duba jikin
Maijego kwananta biyar a asibitin ta warke sumul
kuma a ranar da safe likita yazo ya bata sallama,
suka tarkato suka koma gida aka cigaba da shiryeshiryen bikin suna.
Duk wasu shirye-shirye Muneeba ce ke
gudanar dasu tun ma kafin a sallamota tunda suna
da tabbaci daga gun likita cewa zai sallameta idan
ta kwana biyar muddin dai jikinta yayi garau.
Taron sunan ya kayatar kwa:ai, saboda
Muneeba tasa Mujeeb ya kashe kudi sosai, kuma ta
tsaya tsayin daka wajen ganin anyi komai
wadatacce kuma yadda zai kawatar da sunan yaron
69
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
yaci sunan baban Suwaiba wato Adamu kuma
sunan Baba Adamu Baffan Mujeeb wato yayan
Goggo sai aka yi wa yaron lakabi da Baffa.
Duk wannan namijin kokari da jajircewa da
Muneeba tayi ta hana kanta zaune sai da taga kowa
ya wadata da duk wani abu da aka rabama 'yan
sunan amma sai da Goggo tayi korafin cewa bata
ba wasu cikin jama'arta jakunkuna da agogon
bango da akayi mai dauke da hoton jaririn ba, wai
duk ta rabarwa da 'yan uwanta, inda Allah ya
taimaketa ma ko su Khausar 'Ya'yan Mama Amina
da jama'arta da su ka zo su Murjama duk da yamma
suka zo saboda sunan ya hadu biyu can a dangin
innarsu ana wani sunan.
'Yan uwanta da take nufi sune 'yan gidansu,
su haule da sauran 'yan gidan zuwa iyayensu.
Kuma ana kawo kayayyakin tun ana gobe suna ta
dibarwa Goggon nata isasshe tace mai jegon ta debi
iya wanda zai isheta sai su bata sauran kuma duk a
dakin Goggo aka yi amma sai ran suna tace wai
kadan aka bata, shine fa Muneeba ta debo raguwar
na dakinıta tazo har dakin Goggo ta kawo mata tace
"Ki yi hakuri Goggo ni bansan wasu a gurinki basu
samu ba ni dama ta bangare na basu sami zuwa ba,
sai da yamma saboda sunan da akeyi a can gidansu
Dildi wadanda ma na rabarma duk 'yan cikin
gidanmu na ba, ga wadannan sai ki ba wadarda
a samu ba
74
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Ta ja tsaki ta ce "Kyale munafukai daga su har iyayensu mata sai naci mutuncin munafuncin
su. Au yanzu ne suka san ke tasu ce tunda anga mijinki na da abin duniya shi ya sa ma da suka zo gaishe ni kawai sukayi suka tare acan bangaren ki
suna kinibibi da gulma, kice su kika dumbuzawa kayan, indai don suga kirkin kine wallahi kin
makara ba zasu taba sonki ba, sai daí suyi miki
soyayyar munafunci tunda yanzun kina kyautata
masu kina masu alheri kina basu kwancen sutura
shegu marasa zuciya duk zan hadu dasu ai zan koma Dukkun".
Ta ce ba za ta amshi kayan da Muneeba ta
kawo ba. Goggonsu Hinde ta dubi Muneeba ranta a
бace tace "Ta fi da kiba 'yan uwanki da zasu zo anjima anan dinma duk wanda yace bai samu ba
wallahi karya yakeyi ya fada ne don ya haddasa
husuma tunda ni da hannu na raba abubuwan me
yasa ni ba'a zo ance mini ba'a samu ba sai ke yaya
Rahin za'a zagaya a gaya miki karya alhali ba
muneeba bace ta raba ta hana su, ko kuwa so suke bayan wanda ni na basu ita dole sai ta basu? Kai!
Jama'a aji dai tsoron Allah duk mai haddasa
husuma tsakanin al'umma wata ran shi zai
haddasowa kansa gobarar fitinar da zata cinye shi tas".
Diuk wadanda suka hada wutar fitinar suna
dakin harda Addan Mujeeb Zuwaira dama ita ba
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
shiri suke da Muneeba ba shi yasa da ta shiga falon
Muneeba tana fitowa ta je ta radawa Goggo wai ta
shiga Munceba na rabon abin suna tayi tamkar bata
ganta ba ta hana ta shine fa Musababbin fadan na
Goggo, dama Goggo Hinde na lura da takun
Zuwairan na rashin mutunci shi yasa tayi fadan da
tayi mai kama da jirwaye.
In banda neman su hada Goggo da Muneeba
mai yasa da suka je dakin Suwaiba da bata basu
komai ba basu gayawa Goggonba ita mai haihuwar
kenan balle Muneeba da ba ita ta haihu ba Goggo
Hinde ce take dada Karayin sababi Adda Fadima na
tausarta, har sai da adda Fadiman taje dakin
Muneeba ta bata hakuri cikin ikon Allah taron suna
ya tashi lafiya shi kanshi Mujeeb ya yabawa
Muneeba kan namijin kokarinta.
**** **** ****
Suwaiba haihuwar Adam (Baffa) kawai tayi
amma duk wata dawainiyya da kulawarsa tana
hannun Munceba, sabowa wani irin son yaron da
Aliah ya zuba mata wadda ko kukansa ta ji a dakin
suwaiba zata bar duk abinda take yi ta nufi dakinta
ta dauko shi ta goya shi, duk da tana lura da
Suwaiban ba haka take so ba, don ita a tunaninta
irin son da Mujeeb ke nunawa yaron zai sa
Muneeba taji haushin yaron batasan zuciyar
72
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Munceba ba haka takc ba, jin yaron take tamkar daga tsatsonta ya fito.
Ranar wata Talata tana hanyarta ta dawowa daga makaranta sai ta karkata akalar motarta zuwa
wani gurin sayar da kayan yara ko wane iri. Tа
sayowa Baffa Keken koyon zama saboda a lokacin
ya shiga wata na hudu, ta sayo masa Pampers
wanda takan ajiye a dakinta musamman don tayi
masa amfani dashi da sauran tarkacen kayan wasa
har da kwallo yaron da ko rarrafe bai fara ba yanzu
ne zai koyi zama amma har ana saya masa kwallo
har (baby Carryer) ta sayo saboda goyonsa aka
zubo kayan a bayan motarta ta taho gida.
Jume ta iske a harabar gidan yana yin
wankin mai gidan ya taso da saurinsa ya tarbeta
yana mata sannu da dawowa ta amsa fuskarta a
sake ta ce "A'a Jume yau baka zo da wuri ba ne, sai
yanzun kake wankin? Ya ce, nazo da wuri
amaryace ta aike ni Dukku na amso mata sako, ban
dade da dawowa ba, ta ce Ok, to sannu da kokari
don Allah ga kaya nan cikin mota a baya ka shigar
min dasu".
Ta mika masa makullin motar ta wuce cikin
gida kai tsaye dakin Suwaiba ta wuce wannan
fabi'arta ce idan ta dawo nan take fara shiga-kafin
ta wụce

Please Login or Register in order to submit comment