Downloaded From https://tknovels.com.ng πŸ’–WAZAN ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bismillahir-rahmanirraheem Ya Allah kabani ikon kammala wannan littafin nawa lafiya, kamar yanda nagama da BURINAH lafiya, Ya Allah kabamu ikon yin amfani da abinda yake me kyau aciki 1 Wasu tsala-tsalan yanmata ne guda biyu agaban mirror suna shiryawa, dukanninsu komai yaji babu makusa, da alama akwai inda zasu "Haba YAYA IMAN, kindauki wannan, kindawo kin dauki wanda nace shi nakeso, gaba dayama Naga alama bakida alqibla" hannu tasa ta fizge laffayar me launin green ahannun Iman tafara nadata ajikinta, wadda aka Kira da Iman dince tajuyo takalli yar'uwartata da Dara-daran shanyaiyun idanunta masu kama dana mejin bacci, kadan yarage nayarda wayar hannu na, Jin wata irin zazzaqar murya tace "yaro de yaro ne" Itama dayar cikin sigar shagwaba tace "to yaya Iman hada ki riqe gaba daya kawai" Saida tayi mata gwalo ta gefen ido, yanda bazata ganta ba, sannan tasaki wani murmushi wanda yayi silar lobawar kumatunta (dimple) Sannan cikin sanyin muryarta tace haba DR.BILLY menene Kuma abin fishi anan? Bata jira amsar ta ba itama tafara nada Tata laffayar me launin baqi, wadda taji adon fararen stones, sosai laffayar tahau ajikinta, farar fatarta ta haska aciki, goshinta kadai zaka kalla kagane cewa Allah yayi baiwar gashi awajan Da alama ta hada jinsi da wani yaren daban Itama dayar Jin ankirata da Sunan datake mutuqar so, yasa tasaki ranta, Dan ita aduniya babu abinda takeso kamar taga tazama cikakkiyar doctor Shiyasa yar 'uwar Tata takeyi mata yanda takeso, dazaran taga ranta yabaci zata fara lallashin ta tana cewa haba dr. Billy, tofa shikkkenan zance yawuce HAJIYA datake tsaye abayansu tasaki murmushi ita kadai, Jin irin yanda yaran nata sukeyin abinda suka saba Akan abinda ake siya musu, ba komai suka tuno mata ba Sai lokacin dasuke gida itada yar'uwarta ZAINAB, Hawaye ne suka gangaro asaman fuskarta wanda batasan da zuwansu ba face duminsu daya ankarar da ita, Yatsun hannunta dasuka ji zobunan gold tasa tashare hawayen, sannan ta girgiza kanta ta wuce ta gefen su Iman wanda basu San da tsayuwar tabama. *** *** *** Ahanzarce yake shiryawa, yanayi yana kallan agogon dake manne abangon Dakin, bottir din gaban rigarsa yake rufewa, rigar takarbi jikinsa sosai me launin light blue, Parfums ne agabansa Kala Kala masu mutuqar tsada, dauka yayi yafara fesawa kamar wani sabon ango Wata yar qaramar kit yabude agaban mirror, agogo nagani aciki ajere iri-iri, yasa hannu yadauki wani baqi qirar Rolex yasaka Wajan takalmansa ya nufa yadauki wani baqi qirar Italy yasaka Brief case dinsa yadauka sannan yazo gaban mirror yadauki wayoyinsa, anan naqare masa kallo, dogo ne dede misali, yanada doguwar fuska, haka yanada dogon hanci, bakinsa dede misali,girarsa acike take da gashi, kalar fatarsa wankan tarwada ne, ba fari ne tass ba, hutu da Jin dadi dakuma Zaman waje daya yasa fatarsa tayi wani irin fresh kamar saurayin qasar Ethiopian Har yazo bakin kofar Dakin, sai Kuma yadawo yadauki jacket din suit din dake jikinsa Besakata ajikinsaba, kawai Lanqayata yayi ahannunsa,dayan hannun Kuma yana riqe da brief case din, yafuto yana wani irin taku tamkar wani yarima, wajan haduwa Kam wannan gayen yagama haduwa, babu macen dazata ganshi yagaza tafiya da imaninta Harabar gidan yafuto, anan na qarewa gidan kallo makeken gida ne, da alama mamallakin gidan yajiqu da nera Parking space nakalla motocine guda hudu manya Banda guda biyu dasuke gefe daya angama wanketa, dayar Kuma Sani yana kan gogeta Cikin sauri- sauri yaqaraso wajan motor da aka gama wanketa qirar Mercedes Benz yabude yasaka jakar hannunsa aciki, sannan Yarufe motor yanufi cikin gidan Cikin azama sani dayake goge Mota yaqaraso yace barka da futowa BARRISTER hannu kawai yakada masa yayi gaba Dan yau bayajin surutu, saboda yayi latti dayawa Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bismillahir-rahmanirraheem 2 Yana shiga falon Adede lokacin hajiya tana dining tana bubbude flaks din domin tagani babu de matsala kamar yanda tabada umarni ayi Direct wajanta ya nufa cikin murmushi kamar Koda yaushe tace "IMRAN har anfutone" Saida ya gaisheta sannan ya kalli agogon hannunsa yace" eh hajiya zan fita office duk da Naga nayi latti ma" tace "oya zauna kayi break fast saika fita" No hajiya kibarshi kawai Bata jira yatafi ba tayi sauri tahada masa tea dakanta, kujera ta nuna masa ya zauna Sannan takai masa cup din bakinsa domin tabashi tea din babu musu yafara Sha Farhan dake gefe yana daddanna waya, yatabe baki, Wai hajiya saitaita lallaba yaya Imran kamar wani sarki Cikin kamala da sanyin Hali tace ya za'ai kafita office bakaci komai ba imran Jin yayi shiru ne tanayi masa magana yasa Takai kallanta wajansa Gani tayi hankalin sa gaba daya ya tattara waje daya Tana duban wajan itama tasaki murmushi "hajiya mun futo zamu tafi" Ok harkun gama shiryawa? Billy ce tace eh hajiya Toku zauna kuyi break mana Iman ce taja kujera kusada imran ta zauna, tace ai hajiya anty tace ta ajiye mana hadaddan abinci, kawai ki barshi, idan mundawo mahadu Tace hmm to maji magani, in Kuma da rabon kundawo min da yunwa to Gaba dayansu sukasa dariya Qasa qasa yayi da muryarsa cikin rada ya matso da fuskarsa dab data Iman yace "MURADINA har zaku tafi " Tana wasa da Yatsun hannunta tace" eh yaya, kasan halin baba, idan bamujeba yaji munkoma school, zaiyi mana fada" Gaba daya ya tattara hankalin sa akanta, da alama yamanta akwai mutane awajan Hajiya datake riqe da cup din tea ahannunta tasaki murmushi tayi gaba Billy ma data lura dasu tace "morning yaya" Dagowa yayi yana ajiyar zuciya yace Bilkisu kunde dage saikun tafi Tana murmushi tace yaya ai kasan halin baba, yace hakane, to kutashi mufita Nima dama fita zanyi Dukansu suka tashi, hajiya tace nasa ankai muku Wasu kayaiyaki boot din motar saiku kaiwa antynku Gaba daya suka amsa da to hajiya Kai tsaye Iman tatafi wajan Farhan ta meqa masa hannu, Malam bani wayata Dago kansa yayi daga danne dannen dayake da wayar yace "danma kinsamu na ari wayarki, abinda inawa yaya magana zai aikomin da sabuwa" Tace "eh naji, ayi zuciya asiya " Anqi ayi zuciyar, wallahi Bazan Dena daukar wayarki ba,abinda Kema ba kudinki ne yasiyaba, samari ne suka baki, Tace edin, kaima kaje yanmatanka su siyama Imran da hajiya da Billy suka saki murmushi gaba dayansu, inda Sabo sun saba Sallama sukai da hajiya suka futo harabar gidan, gaba daya laffayar dasuka saka ajikinsu take wani irin walwali, Sunyi mugun kyau kamar asace su Sani ne yataho aguje yace hajiya angama wanke motor Saida ta yatsina fuska sannan tace, sani, sani saunawa zancema banason hajiyan nan Kiyi hakuri za'a kiyaye insha Allah Har gaban motar dazasu shiga ya rakasu, ya budewa Iman murfin motar, tace to yaya zamu tafi, saimun dawo Shima yace Wai kina nufin kece zakiyi driving da kanki? Tace emana yaya No banyarda ba, gaskiya driver yakaiku, bansan ki wahala Murmushi tasaki tace yaya karka damu Yace to saikinmin alqawari idan kika gaji, Zaki Bawa Dr.taqarasa daku Tace to yaya nayi ma alqawari Toki kula da kanki, saikun dawo, Nima zanje Court OK yaya bye Shiga motar tayi,yar qarama mai kyau qirar Acura, already Billy tana zaune aciki, saboda itakam bazata iya kallansu ba,key tayiwa motar, mai gadi yabude musu gate suka fita, sannan Barrister yabisu Abaya Shima *** *** *** KATSINA STATE da wuri suka Isa, aikuwa kamar hadin baki suna Zuwa kofar gidan baba yana Nan a zaune, shida maqocinsa, suna futowa wajansa suka qarasa har qasa suka tsugunna suka gaidasu, maqocinsa ne ya amsa musu faram faram Amma shi baba,babu wani sakin fuska da nuna Jan Naka ajiki, ya amsa musu, duk da cikin ransa yanaqin abinda yake musun, Amma Kuma babu yanda zaiyi ya boye bacin ransa idan yatuno da abubuwan dasuka faru Abaya Tashi sukai sukayi cikin gidan, Wasu yarane mace da namiji suka taho da gudu, suna oyoyo ga anty, saura kadan su yarda Billy aqasa, Iman tace owk, wato ni Baku ganni bako? Saikuma suka saki Billy itama suka rungume ta Anty ce tashimfida musu babbar tabarma atsakar gidan Suka baje, anan aka fara gaishe gaishe, suka Bata saqon da hajiya tabasu su kawo, less ne da atamfofi guda biyu Tace Kai hajiyan taku de Bata gajiya, Allah yasaka da alkhairi, suka amsa da ameen Saida suka huta, sukaci abinci, sannan anty tace zataje tadawo Tana fita Billy tasaki tsaki, Iman tace menene Kuma? Tace wallahi HAROON ne yayimin 3miss call, wayar nacikin hand bag dina, banjiba, shine nakirashi yanzu yaqi yin picking sai text yaturomin Wai yana busy ne To menene abin fishi Kuma Billy, Kema kitura masa text din mana Wallahi yaya Iman bazan tura masaba, Kenan ma nice na matsu dashi, yaje yayita aikin Ninagaji da wannan soyaiyar wallahi, kekam kinji dadinki yaya Imran yana sanki Iman tace Kema komai zaiyi daidai insha Allah, ki kwantar da hankalin ki kinji? Ajiyar zuciya tasauke tace to yaya Iman Saida yamma tayi, sannan suka fara haramar komawa gida, inda anty taitayi musu nasiha Akan karatu, shikuwa baba dama bawani jansu yake ajikiba, haka de ya qara yimusu fada suka tafi *** *** *** Sai yamma liss suka dawo gida, suna shiga falon wata yar qaramar yarinya bazata wuce 11 years ba tataho da guda ta rungume su Tace anty Billy shine kuka gudu Baku tsaya nadawo daga school ba, Kuma nace muku zanje Kumatunta Billy taja, tace sorry princess, tuba nake Turo bakinta tayi gaba tace a a sai kinsaimin alawa, tace to zan siyo, shikkenan? Daga mata Kai yarinyar tayi Hajiya ce tace ku kyale zeey kuci abinci kuyi wanka ku huta Jan zeey sukai dakinsu, saida suka huta, sannan sukaci abinci, suna falo gaba dayansu suna fira, Yashigo falon yahade cikin qananun Kaya, farin wando jeans sai baqar Riga me adon fari Sumar nan tasha gyara kamar ba gobe Iman ya duba yace kungama shiryawa ne mufita? Eh munshirya yaya, cewar Billy Iman de batace komai ba, saboda yanda ya wulla zuciyar ta cikin tunanin tafi sauran mata sa'ar masoyi Daki suka koma aka sake kwalliya, riguna ne ajikinsu ready made, har Gara Billy tasaka babban mayafi, Amma Iman wani Dan siriri ne tayi rolling dashi Suna futowa falon Farhan yace Dan Allah kar'agaji dani, wayar de Saida ta harareshi sannan tace haka de aka iya,da'an tabaka zaka fara cewa Ina magana yaya zai siyamin, gashinan kakasa Yace please sisi Wayar tabashi suka fita, wajan shopping suka je, suka zazzabo abinda zasu qara domin tafiyarsu school gobe, kowa yagansu saiya sake kallansu saboda yanda sukai bala' in haduwa, duk inda Iman tayi yana manne da ita, Billy ce tariqe hannun zeey sukayi wajan ice cream da sweet Ita kuwa Iman, banda uban kayan make up babu abinda Barrister yake jida, sai Diba yake kamar ba kudi ne zasu biyaba Agajiye suka dawo gida,kayan suka nunawa hajiya tace suje daki su fara shiryawa acikin jaka *** *** *** SWITZERLAND Sosai yayi kyau acikin kakin, wandon dark blue ne sosai, wanda zaka iya kiransa da ruwan shanshan bale, sai farar Riga wadda ta karbi kakkarfan jikinsa, dantsansa kadai zaka kalla kasan cewa mamallakin jikin kakkarfa ne Daga kafadun sa jikin rigar wani tambari akayi na sojoji, ba rank bane kawai adone ajiki da akayi da ruwan gold, Saikuma Akasa dark blue a gefe, kalar wandon jikinsa, Saikuma wani adon agaban aljihun rigar Baisaka hulaba, hakanne yabawa Sumar kansa damar baiyana, ta kwanta luf, tana sheqi, da alama Ana narkar mata da dukiya wajan gyarata Fari ne tass, jikinsa amurde yake, baida tsawon hanci, Dan dede ne, haka girarsa yar dede, bakinsa Dan qarami mai launin ja, Allah yabashi idanu Yan manya Yanada tsawo, ba siriri bane tsararren daki ne dayaji kayan alatu ta ko'ina, komai na Dakin fari ne da ratsin dark green, daga labule har furnitures din cikin Dakin Wasu hamshaqan kujeru ne ajere acikin Dakin farare, da qananun fillos a kansu masu launin dark green, a Kalle kallan danake ne, Naga wani babban photo Elergemant a ajiye agefe, shi dinne nede ajikin pic din Daga qasa Kuma Naga anrubuta "Chief of Air Staff" Amma abin da zai baka mamaki shine idan kakai kallanka kan hadaddan gadon Dakin, yayi kaca kaca, kamar anyi danbe akai Tsaki yake saki shi kadai, yakama bedsheet din yana kadewa, da niyyar gyarawa, idan ya bazashi Akan gadon, sai wani gefen ya nade, yaqi warewa gaba daya Haushi yasa yayi wulli da bedsheet din Daga bayansa yaji motsi, yana Juyawa yaganta atsaye a kofar Dakin, da alama ta jima da tsayawa awajan tana kallansa Kofar Dakin takama da niyyar fita tayi waje, Saikuma ta fasa sannan tace "ai duk wanda baishirya aure yanzu ba, to wahala Bata qare masaba, ai Yanzu kafara wulli da bedsheet HAIDAR, tukunnama" Kamar zaiyi mata kuka cikin shagwabar daya saba yace "Kai MAMY Dan Allah" Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 3 Ko kallansa Bata sakeyiba tarufe masa dakin tatafi Ajiyar zuciya yasauke idanunsa na Kan window din dake dakin, Aure de Aure de, kullum mamy zancenta Kenan, Bama wannan ne damuwar ba, HAIDAR haka Kai tsaye Ko babyn data saba fada masa yau babu Yanda yayi wulli da bedsheet din haka yabarshi awajan, yajuya Kan kujerun dake dakin yasaka hannu yadauki wasu manyan wayoyi guda uku, yafice Daga dakin Shima Yana Zuwa falon yakalleta yace mamy zanfita wajan meeting saina dawo Idanunta Akan wasu wasu pictures tace masa "OK to kafin kafita zokaga gani" Kamar de Yanda yazata hakanne kuwa yakasance photunan Yan matane Kala Kala, ahannunta Janyoshi tayi yazauna dab da ita, tamiqa masa pictures din tace "gashinan duba acikinsu Ko akwai wacce tayima" Dariyace taso kamashi, ganin Yanda tadage bil-haqqi Akan nema masa matar Aure Amma saiya danne dariyarsa, yakarbi pictures din yadubasu daya Bayan daya, sannan ya ajiyesu Hannayenta yakama duka biyun yace "mamy na kiyi hakuri, Amma ni duk cikinsu babu wacce tayimin,asalima mamy gaba dayansu babu wadda zan Iya zaba amatsayin uwar yayana, to banqi ba de Yan aiki haka, idan su ne Kam, nabaki dama ki zabamin guda dayama ta isa" Saida tagama sauraron kalamansa sannan tace cikin ranta Lalle Yaron Nan yagama renamin hankali Amma saita shareshi tace "baby toka auri Basma mana, yarinyar menene laifinta"? Kansa yadafe da hannunsa yace mamy Basma fa To'ai Har Gara wadannan yaran ma, yafadi haka yana nuna mata pictures din yanmatan data bashi Kallansa tayi sosai ido cikin ido, tana nazarinsa, Basma yarinyace wayaiya, wadda tatara ilmin boko, Bata rasa komai ba abangaren hallitar mace Shima kallanta yayi ganin Yanda tazuba masa ido batace dashi komai ba Adaidai lokacin Kuma mamy tace "baby Anya kuwa kanada lafiya?" Baisan lokacin daya sunkuyar da kansaba, saboda Yanda tambayar Tata tayi masa nauyi, gakuma kunya dayaji Mamy indatasan Yanda yake hakuri aida batayi masa wannan question dinba Lallausar sumar Kansa yashafa sannan yace mamy lafiya ta kalau,insha Allah, wataran zakiga Aure na, harma kiga jikokin ki " Murmushi tasaki, dataji yatabo mata inda takeso Tace" to Allah yasa, Amma kasamo da wuri gaskiya " Shima cikin fara'ah yace to mamy nah, ninafita Rigarsa ta janyo cikin sauri tace" Ina zakaje bakayi break ba, " Atika! Atika! Tafara kwalawa me aikinsu Kira Shikuwa mamaki ne yakamashi,Daga cewa zai Nemo matar Aure Har aka fara tarairayarsa haka Adede lokacin Atika ta iso, Har qasa ta tsugunna tace gani Hajiya Kallanta tayi tace kiyi sauri ki hadowa baby break fast Saida ta kalleshi ta gefen ido, sannan tace to Hajiya, tajuya tayi kitchen cikin ranta tana cewa Wai Hajiya batada aiki saidai ta dubi wannan qaton tace masa baby Cikin sauri tahada masa chips daflantain, sai tea Mai kauri Mamy agaba tasashi tana tayi masa fira, yanacin abincin, Shikuwa mamaki ne kawai yakamashi, tun farko inda yasan haka mamy takeso, aida tuni yasa ansamo masa wata yarinyar yakawo mata ita, idan mamyn taganta saiya sallami yarinyar Daga baya, shikkenan yahuta da rikicinta Saida yagama sannan ya kalleta tace "to Allah yadawomin dakai lafiya" Kafin yabata amsa daya Daga cikin wayoyinsa tadau qara, cikin Murmushinsa Mai tsada yadaga Kiran "Broth ya akayi?" Bansan meya fada masaba, nagade yaci gaba da Murmushi, yakadawa mamy hannu yafice cikin takunsa na kakkarfan soja *** *** *** ALIYU HAIDAR Kenan, da guda daya tak awajan Hajiya FATIMAH , wadda yake Kira da mamy, mahaifinsa SA'AD cikakken tsohon sojane, wanda yayiwa Nigeria hidima da karfinsa dakuma lokacinsa, Allah yayi masa rasuwa ne awajan fafatawarsa da maqiya afagen yaqi Tun kafin yarasu yafara Dora dansa Akan turba tasan yayi aikin soja, Kuma Hakan yayi Rana, tunda tun Bayan rasuwarsa Yayan Alhaji SA'AD Wato BILAL yaci gaba da daukan nauyin komai na Aliyu, Har Allah yatemakeshi dayake yanada manya asama Aliyu yasamu damar riqe babban maqami na sojan Sama, qwazonsa da jajircewarsa awajan aiki ne yasa President da Kansa yabashi mulkin shugaban sojin Sama na Nigeria Aliyu akwai aiki, yanada qoqari awajan aiki, haka ta bangaren yaqi, ba baya bane wajan fafatawa da maqiya, ya qware sosai wajan harbi, duk da becika yi da kansaba saide yabada umarni ayi Aliyu miskili ne naqarshe, bashida magana, mamy itace qawarsa, itace abokiyar shawararsa, idan yazauna yana yiwa mamy surutu bazakace Aliyu bane, baya shiga harkar yanmata, asalima Koda yayi niyyar cewa yanason yarinya saiya rasa ta inda zai fara fada mata, saboda Bai sababa Abokinsa qwaya dayane, daya Daga cikin matemakansa, wato Mustapha Shekarar Aliyu 34 duk tsawon wannan lokacin baiga wadda tayi masaba, Allah yazuba masa kishi, yanada kishi sosai Akan abinda yakeso, hakanne ma yasa duk inda zaije to kafarsa kafar mamynsa, yana zaune a danqareren gidansa a Abuja, shida mamy ne kawai suke rayuwarsu aciki, Saikuma atika me aikinsu data zama Kamar yar gida,yanzu haka sunje Seminar ne Switzerland Kuma zata daukeshi Zuwa Dan wani lokaci, shiyasa yadauki mamy Dame aikinsu atika suka tafi Mamy tanaso taga Aliyu yayi Aure, takawo masa yanmata dayawa ciki kuwa harda yayan qawayenta nanma abin beyuba, shiyasa takori duk wasu ma'aikata dasuke gyara masa part dinsa, tace yadinga yi da kansa Ko yayi zuciya yayi Aure, Shima yahuta Back to story (kuyi hakuri da Jina dakukai shiru kwana biyu, Hakan yafaru ne saboda matsala da wayata tasamu) Mrs Usman Ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 4 Washe gari suka hada yanasu yanasu suka futo tsaf dasu domin tafiya makaranta Bayan sunyi sallama dasu hajiya direct harabar gidan suka futo, Amma hajiya afalo tayi zamanta, Dan Bata qaunar abinda zai nisanta ta da yaran nata saide dole Billy ce tadubi Zeey baby tace "Autar hajiya maza jeki part din Yaya kice masa shi muke jira" Kafada ta dage alamar bazataba, tace um um anty banaso kisake guduwa ki barni, saide muje dake " Iman dake tsaye kusada Farhan tace" Bari inje inkirashi " Kallanta Farhan yayi yace" malama kawai de dama neman hanyar Zuwa kike, tojeki " Juyowa tayi tace eh zanje kaima kayi zuciya kaje wajan taka mana" Tana fadar haka tayi part din Barrister Falon yayi neat sosai Kamar babu mahaluqin dayake rayuwa aciki, komai tsaf dashi, Barrister akwai son gayu da daukar wanka, inde wajan tsafta ne da kwalliya kazo wajan Barrister toka Gama, shine yayi training din Iman tun kafin tasan kanta, yakoya mata ado da daukan wanka, basai nafadaba kowa yasan Yanda barristers suke da Daukan wanka, haka yake ma awajan Imran,shide burinsa kawai yaganta Tasha wanka na kece raini sufita yawonsu, bawai Dan baya Santa ba, a a kawai shi mutum ne maisan ace yau gashi da fitacciyar mace Mai kyau da aji Kamar Iman Daga kanta tayi ta kalli Saman falon, photonsu ne amanne shida ita, yazuba mata ido yana kallanta itama haka, babu wanda zaice basu birgeshi ba, indai yagansu Tana kallan pic din batasan yafutoba, Shima tsayawa yayi yana Kare mata kallo, tayi kyau cikin Riga da wando qirar fakistan, sai mayafin kayan tayi rolling dashi, "kona ciro Miki kitafi dashi " Maganarsa ce tasata Juyawa da sauri, babu kunya ta Zuba masa ido tana kallansa, gaskiya babu qarya Yaya Imran yahadu, ita kuwa wacce sa'a gareta dahar wannan gayen daya gaji dayin kyau yake kaunarta Qasa tayi da Idanunta, Bayan tagama kallan nasa, takowa yayi ahankali Saida Yazo dab da ita, Har sunajin hucin juna, ahankali yasa hannunsa yakama hannayenta, yayi Qasa da murya yace "kingama kallan nawa Ko Kuma na tsaya ki kalli abinki San ranki?" Bata Iya bashi amsa ba, domin kuwa gaba daya yakashe mata jiki da wannan maganar dayake mata me kama da rada Ahankali ta Bude bakinta tace am Yaya dama jiranka muke yi zamu tafi, Kar muyi missing flight Kamar wani gaula haka ya zubawa lips dinta ido wanda yakeji Kamar yakamasu ya tsotsa Dago Zara zaran gashin idonta tayi ta kalleshi, anan taga inda hankalinsa yafi karkata wato lips dinta Cikin sigar shagwabar da batasan tanada itaba tace "Yaya fa!" Sai asannan yadawo nutsuwarsa, hannayenta daya kama yariqe su ya murza ahankali, Kasa kallansa tayi saboda Yanda takejin wani irin baqon yanayi atare da ita, batasan Cewa yafita shiga cikin yanayin ba, ahankali yace "MURADINA please ki kulamin da kanki kinji, kada kibari wani da namiji ya rabeki dasunan soyaiya, idan Hakan yafaru bazan yafewa kainaba, please kada kibari Hakan yafaru kinji" Bata Iya bashi amsaba, wayarsa tadau qara, yana dagawa Hajiya tace Imran mekuke jirane? " cikin kunya yace Hajiya gamunan, tareda kashe wayar Kamo hannunta yayi suka futo harabar gidan, baisaki hannun nataba haka sukazo Har wajansu Billy da Zeey, sai Kuma Farhan, Mota suka shiga dukansu, inda Farhan yayi driving dinsu Zuwa AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT *** *** *** GHANAH Teemah kin zauna silent dake, Ko Har yanzu tunanin muradin naki kike? Ajiyar zuciya tasauke sannan tace "kede bari besty nasan yanzu yanacan yana missing dina Wlhy , fari tayi da Dara daran idanuwanta taci gaba da Cewa babu me kula dashi, Koda yake ai ga hajiyata Nan, nasan inde tana Nan banda wata damuwa" Billy ce ta yatsina fuska ta dubi wadda aka Kira da besty tace "kinjita Ko? Saiki rantse Akan irin wata muguwar kulawa take bashi, Bayan Ko Iya kallansa batayi, yana fara yimata magana zakiga kanta aqasa Kamar wani sirikinta" Tana gama maganar ta miqe tsaye zatabar wajan, harara Iman tasakar mata, tace "Ina Kuma zakije kibar wannan kayan, ki tsaya ki shirya mana su" Besty ce tace haba Teemah kofa hutawa bakuyi ba, duban Billy tayi tace Kinga jeki Billy, zan shirya komai Kallan Iman Billy tayi batace mata komai ba, kawai de ta girgiza kanta tashige toilet domin ta watsa ruwa Itama Iman miqewa tayi tafara cire kayan jikinta, wandone gajere ajikinta iyakarsa gwiwarta, sai best yar qarama, Riga da wandon Pakistan din data cire ta ajiyesu agefe, yusra ce ta Kalleta tace um lalle muradin wata zai huta dayawa, irin wannan abubuwa haka Sai a lokacin na qarewa hallitar jikinta kallo, cikinta ashafe yake, tanada manyan boobs tsayaiyu, hips dinta abaje yake, wanda idan tana tafiya saika rantse da niyya take kadasu, Kuma Ko daya bahaka bane, kawai hallitar ta ce haka Murmushi tasaki tace Allah sarki muradina Wlhy Besty Ina kaunar Yaya Imran, Har so nake muyi mugama school dinnan ayi mana aurenmu wallahi Teemah Kenan, yanzu fa Billy tagama Cewa bawani kulawa kike bashi ba, Kinga fa karkiyi Sanya, mazan yanzu kana basu kulawa ma Yaya aka qare, bare Kuma keda kika mallaki namiji Kamar barrister Wlhy yusy kinsan me, sainayi niyyar inyi masa wani Abu daya shafi soyaiya sainaji nakasa, kinsanni da karatun novel, to idan natuna abinda yake faruwa a novel shine zai faru tsakaninmu sainaji kunyarsa wallahi, yusy tace ai kuwa Gara ma kidena, Dan shikam Kinga wayaiyan mutum ne dayakesan wayaiyar mace Suna wannan firar Billy ta futo Daga wanka Daga ita sai towel, Itama Iman ta miqe tashige toilet din *** *** *** Azaune take afalo ita kadai, less ne ajikinta launin ja, sosai yayi Mata kyau, dinkin yakarbi jikinta Kamar ba wata me shekaru ba Daga ganta kasan cikakkiyar bafulatana ce basai anfadaba Wayar tace tadauki qara, tasa hannu tayi picking call din Cikeda fara'ah tace" Hajiya maimuna yagida ya mutanan Nigeria? " Itama Daga dayan bangaren tace" Hajiya Fatima wallahi lafiya kalau, ya Switzerland? " Mamy da fara'arta tace Alhmdlh, ya yata Basma, Hajiya maimuna Bata amsa mataba tace" Hajiya wallahi dama wani me maganin gargajiya ne naji yana tallar maganin jinnu, shine nace Bari nafada Miki Ko Zaki siya ku gwada Ko za'a dace," Cikeda mamaki mamy tace "to yanzu Hajiya maimuna nikuma meya hadani da maganin jinnu?" Cikeda izza tace, a a Wai Hajiya Fati kina nufin Dan wajan ki Aliyu ba aljana ce ta Aure Shiba? Mamy tace Hajiya wacce irin magana kikeyi haka? Aliyu na Kuma? Daga dayan bangaren Hajiya maimuna tace to Hajiya fati kekuwa idan ba aljana ce ta aureshi ba, wazaiga mace Kamar Basma yaqita, aisaide inba me cikakkiyar lafiya ba, " Sai yanzu mamy tagano bakin zaren, wato magana ce take fada mata saboda Aliyu yace bayasan yarta Basma Cikeda fishi Itama mamy tace" Hajiya aljana Bata auri Haidar dinaba, ai Aure lokaci ne, Shima wataran zaiyi " Hajiya maimuna batayi shiru ba tace a a Hajiya kide bincika, kinsan halin Dan yau Mamy batace komai ba takashe wayarta, dafe kanta tayi da hannunta, koma me aka fada mata Aliyu ne sila, wannan Yaron kode sadakarsa zata bayar ne Ahankali yake ja dabaya yana komawa cikin kitchen, bayaso mamy tajuyo taganshi bare ma tasancewa yaji wayar Daga gama (bincika son thanks dinnanba, kawai inkunason injidadi Kuma kuga posting Akan lokaci kazuba min sharhi nafijin dadinsa fiye da godia) Har yanzu muna Kan shinfida ne, bamu nutsa cikin labarin ba Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 5 Kamar kullum yauma uniform ne ajikinsa saide nayau kalar blue ne, sosai kayan yakarbi jikinsa, wata yar qaramar bindinga ce asoke ajikin aljihun wandonsa na baya Shiru yayi yana nazarin kitchen din Kamar wanda yake neman wani Abu daban Yanzu akansa Har abin yakai Ana Kiran mamynsa awaya Ana fada mata magana? Shikuwa wanne irin yarone? Ajiyar zuciya yasauke Mai karfin gaske, Daga bisani yafara magana shi kadai acikin ransa Insha Allah nasaka araina Cewa Daga yau zansa adubamin yarinyar data dace in aura, basai naganta ba, inde anganta Kuma halin ta yayi, to zan Aure ta domin mamy Yana gama maganar yafuto Daga kitchen din cikin fara'ah yayi wajan mamy wadda ta rafka tagumi tana tunanin halin da Aliyu yasata Ta Bayan kujerar da take Kai yazagaya, yadora kansa Akan kafadarta, tanajin qamshin turarensa ta share shi, Murmushi yasaki shi kadai Cikin Murmushin yace mamy nah kinsan wani Abu? Batayi masa maganaba kawai de ta girgiza kanta Wayarsa yadauko Daga aljihun sa, data yabude yashiga Google, Bansan meya bincikaba, naga yazagayo yazauna kusa da ita Wayar tashi yamiqa mata, yace "mamy Kinga wannan materials din Kamar zasuyiwa qawayenta kyau ranar dinner Ko?" Asheqe ta dubeshi tace "wa Kenan?" Shima Sarai yagane a kusa take, Yanda tayi kicin kicin da rai ne Daria taso kamashi Bai Iya boyewaba Saida ya murmusa Sannan yace "mamy matata mana, wadda nake San aura" Tanajin Hakan tasaki ranta, harda qara matsowa kusa dashi tana kallan material din, tace "Kai Amma yayi kyau gaskiya" Wani irin dadi yaji acikin ransa, ganin mamyn nasa tasaki ranta Wani less yanuna mata, yace wannan Kuma Kinga zaiyi muku kyau, keda mutananki Wannan Karon mamy karbe wayar tayi, tace wow, gaskiya baby ka Iya zaben Kaya, Kamar kashiga Raina, Amma de kungama dedetawa da yarinyar Ko? Hannunsa yadora akansa yana Sosa qeyarsa yace "a a mamy Wai idan Allah yakawo" Haidar tashi kafice kabani waje Mamy yanzu idan akai ordering dinsu tun yanzu ba shikkenan anhutaba idan bikin Yazo Saboda bacin rai Kasa yi masa magana tayi, kawai hanyar kofar fita Daga falon ta nuna masa Yana shafa Lallausar sumar kansa ta fulani, yace to mamy, ankirani meeting na gaggawa yanzu, saina dawo " Shiru tayi ta qyaleshi Beyi Shiru ba, yasake Cewa" kinji " Nanma Bata kulashiba " kinji mamy na tafi " Dan tausayi yabata Dan haka tace" naji Haidar Ala kaika lafiya " Daria yasaka sannan yafice Daga falon cikin takunsa na qasaita *** *** *** Shiru dakin nasu Kamar babu kowa aciki, kowa yariqe waya yana abin gabansa, Iman ce tasaki tsaki, yusy tadubeta " me akayiwa Besty nane? " Wlhy wata shegiyace Naga tasa pic din barrister a Instagram, wallahi na tsani yarinyar Nan" Besty tace "wacce yarinya Kuma?" Ke babba cefa ba yarinya ce irinmu ba, kullum batada aiki saide takirashi awaya, kiji tawani maqe murya, hello babban barrister ya gida " Cewar Billy Daria ce takama yusy Saida ta Dara sannan tace" Kuma Ke Iman kina gani kika qyaleta? " Iman tace Toya zanyi yusy, yanzun nasan inda tasamu pic dinsa, bashi yabata ba Billy tace a a Yaya Iman karkiyiwa Yaya sharri, dagake harshi takanas kuke Zuwa wajan photo ayi muku, kawai na dorawa a dp ne, Kinga kwa aikonice tunda Naga Ana sakawa dole nadauka, ni wallahi innice Itama Bayan nasa pic din saina rubuta my fiance to be Dallah malama kiyiwa mutane Shiru, Kamar antambayeki sai wani zuba kike Cewar Iman Yusra ce takatse musu zancen dacewa, Kai Kai Iman Billy kunga wani video danagani yanzu a net Wallahi wasu sojojine suke karya kafar kidnappers Suko Imani ma basu dashi ne Besty Tafadi maganar tana duban Iman Billy ce tace Kai Kai bani nagani yusy, tasa hannu ta karbe wayar Daga hannun yusy Cikin Jin Haushi da bacin rai Iman tace yusy, Dan Allah idan zakuyi haukanku kudena sani aciki Ke waye yafada Miki sojoji mutane ne? Billy tace to Yaya Iman sudin aljannu ne? "ni bance Miki aljannu bane, kawai de ni arayuwata Bana qaunar soja, kokadan basa birgeni " Yusy tace Toda Imran dinki soja ne Yaya zakiyi? Bana fatan haka Besty, wataran kana zaune acikin gida za'ayi sallama dakai amiqama takarda, kana budewa zakaga sunan mijinka yafada cikin wadanda suka mutu awajan yaqi" Yusy tace tab wallahi kuwa hakane Billy tace ni dama Haroon daba wani kulawa yake bani ba, inda ace soja ne ai nabani Ai wannan Haroon din naki sai aslow, Cewar yusy Wallahi ni na matsu ma exam dinnan ta qare nakoma gida kusa da anty na Wallahi nayi missing dinta, inji Billy Iman tace eh dole kiyi fada da Haroon, wato shi bakiyi missing dinsa ba, Billy tace share shi Yaya Iman "ai Nima sonake mugama aranar nakeso mugudu 9ja, tadubi yusy tace Besty ai Kema zakije Ko? Yusy tace Anya kuwa zani, one week nefa zamiyi mukoma wata semester kawai zan zauna, basai najeba " To Allah yakaimu Cewar Billy *** *** *** Dakin taron nasu ya tsaru matuqar tsaruwa, dukanninsu kaki ne ajikinsu , gaban kowa akwai lasifika wadda aka rubuta NTA ajikinta, da alama duk abinda suka tattauna awajan kai tsaye yana tafiya ne akafar sadarwa ta nta, daga saman aljihun rigar kowa naga anrubuta sunan kowa ajikin tasa rigar, shine kawai yake zaune akan babbar kujerar dake nuni dacewa shine shugaba awajan,shima gaban rigar sa ansa ALIYU SA'AD bayan qaddamar da bayanai dasuka gama , aka miqo masa wata takarda , umarni yabayar abude takardar akaranta Wanda yagama karantawa ne yayi bayani akan takardar , takarda ce qasar ghanah taturo musu , suna gayyatarsu meeting na kwana daya akan dedeto dakuma zaman lafiya tsakanin Nigeria da Ghana Goshinsa ya dafe da hannunsa "Yazasu turo mana wannan takardar bayan sunsan bama qasar, yanzu haka muna wajan seminar ne?" Wanda ya karanta dinne de , yace"Sir ai 1week suka nema muyi da farko, bayan anyi musu bayani ne suka rage yakoma 1day saboda ansanar musu muna bakin aiki" "Ok toba damuwa " na gefensa yaduba sannan yace"jiragenmu sun zama ready ne?" Eh sir Toshikkenan, ashirya mana tafiya zuwa next week insha Allah" Dahaka meeting din nasu yaqare *** **** *** Azaune take afalo remote ne ahannunta , Atika ce azaune aqasanta tana matsa mata qafafu Hankalinta yana kan tv tace "kai Atika nagaji da zaman wannan qasa wallahi" Dariya atika tasa tace Tab ai mamy nikam bangaji ba wallahi , kofa sati biyu bamuyiba, ai banqi ace muyi zamanmu anan ba" Mamy tace lalle atika bakisan dadin gidaba, atika kowa yabar gida ai gida yabarshi" Banda ma jaraba irinta haidar ai da yabarmu agida Atika tace a a mamy wallahi gara da mukazo , ai ko yanzu nikam nahau jirgi Dariya tabawa mamy , danhaka tayi mata murmushi kawai Lemo ne ahannunsa na gwangwani , rigar jikinsa amless ce sai wando gajere iyakarsa gwiwarsa, sai yau naganshi cikin qananun kaya, kullum cikin kaki yake Farar fatarsa saita haska acikin kayan, kamar ba hausa fulani ba, yana zuwa ya ajiye lemon hannunsa aqasa ya kwanta akan kujerar tareda dora kansa akan cinyar mamy Atikace ta kalleshi ta qasan idonta Aranta tace shide wannan kullum kamar qaramin yaro, garama yayi aure ko mamy ta huta da wannan shagwabar Shafa kansa tayi tace baby ya akayi, kallanta yayi yana daga kwancen yace mamy tafiya takamamu zuwa ghana Murmushi tasaki tace kamar kasan kuwa yanzu nake cewa nagaji da zaman wannan qasar, kaga shikkenan daga nan saimu wuce nigeria Murmushi yasaki wanda yasa gefen kumatunsa suka lotsa (dimple) Yace mamy ai yanzu kuka fara zama kuwa, kwana dayafa zamuyi aghana mudawo , bawani daukan lokaci zamuyi ba" Kiyi hakuri mamy banasan abinda zaisa kiyi nesa danine shiyasa Aikuwa dole kayi nesa dani baby tunda zakayi aure, Kuma dan zanyi aure mamy shikkenan saina rabu dake Haba mamy aiko nayi aure ina tare dake Murmushi tayi tace to Allah yasa baby Amin mamy nah, amma mamy yunwa nakeji Tashi kaje kazuba da kanka kaci, Cikin shagwaba yace haba mamy , haba mamy To haidar idan kaji haushi kayi aure mana Baice mata komai ba, yadubi atika fuska babu alamun wasa yace"ke tashi kibamu waje" Tunma kafin yarufe bakinsa atika tabar wajan, saboda tasan shi da mugunta tsaf zai iya maketa *** *** *** Wow teemah gaskiya kinyi kyau ba qarya, rabonda ki tsatso wannan kyan kin dade Manyan idanuwanta ta juya tace "kekuwa yusy ba gara inyi kwalliyaba, zanje naga MURADINA Billy tace nikam gaskya katsina zan wuce , bazan shiga kanoba Iman tace ki gaida anty da baba , amma nikam sainaga Hajiya hankalina zai kwanta Yusy ce ta yafa mayafinta, tace kutashi mutafi Sunyi kyau gaba dayansu , billy abaya tasaka tayi rolling da dankwalin abayar Iman kuwa riga da wando tasaka , kayan sun amshi jikinta, hips dinnan suncika fam acikin wandon jeans din data saka, sai riga data saka fara me adon Dark blue agaban rigar, dukiyar fulanin masha Allah gasunan Sai doguwar riga data dora akai after dress me kalar dark blue itama, zare ne agefen rigar , hannun rigar kuma baza gareshi , sai stone da aka diga ajikin hannun rigar Zaren rigar takama tadaureshi acikinta, sai wani shegen takalmi data saka me tsini, batayi kitso ba, kawai kama dogon gashin kanta tayi tadaure, batayi rollinga kawai dankwalin after dress din ta yafa, jakarta takama tanaja suka fita daga hostel din nasu Suna fita mota suka tare direct takaisu Airport Suna shiga cikin Air port din suka gama abinda zasuyi , suka zauna awasu kujeru agefe sunata firarsu tareda yusra datace bazata tafi ba saitaga tashinsu Iman ce tatashi tsaye tace bari inje can insiyo ruwa nadawo Bata dade da tafiya ba tadawo hannunta dauke da ruwa da chesee Ruwan tabasu , itakuma tabude chesee din tafaraci tana daga tsayen Adede wannan lokacin shikuma yashigo cikin Airport din tareda rundinarsa Yayi masifar kyau cikin kakinsu na sojoji Yau harda hular yasaka akansa Already sunada jirginsu , so babu abinda zai jira kawai tafiya zasuyi sukoma Switzerland tunda sungama meeting din daya kawosu Wayarsa ce tayi qara, yatsaya yana magana cikeda aji Juyowar dazaiyi yahangeta atsaye tanacin chesee Daskarewa yayi atsaye , ga waya ahannunsa yana magana amma yayi shiru Danqaramin bakinta yake kalla yanda take juyashi Kamar wani abin arziqi take ci Yusy ce tace kai teemah kinga wasu sojoji can, inama zani gida kuma ace jirgi daya zamu hau, yasin dasai munyi selfie indora a Facebook yanzu zakiga anaban girma Hararar yusy tayi , tace kesuka dama, nikan basa gabana can dayawarsu Billy ce tadagakai ta hangesu , itama daga kallan farko bata sake yimusu na biyu ba Sir ga waya ana kira daga nigeria Sir! Sir!! sai alokacin ya kalli musty dayake bashi wata wayar Dayar wayar datake hannunsa yakatse batare daya gama maganar dayakeba Qasa qasa yayi da murya yace Musty katse wayar nan in nunama abinda nagani Kallansa mustapha yayi da mamaki, yace meke faruwa ne? Da hannunsa yanuna masa iman datake tsaye, yace"kai kaga wata sura" Masha Allah kawai mustapha yace, sannan yaci gaba dacewa Gaskya tayi, ba qarya tahadu, kuma abinda zaka duba shine komai yaji, musanman breast dinta, kana son mace maishi Cikin kishi ya dakatar da musty da fadin"kuma menene abin maimaitawa, sai wani zancen breast kake, matar dazan aura cefa insha Allah Dariyace takama musty , kawai daga ganin yarinya shikkenan harta zama matar dazai aura Dariyarsa ya gintse, gudun laifi awajan abokin nasa "Idanunsa yana kanta yace amma kuma musty meyasa zatasa wannan kayan tafuto waje, dubafa dan Allah mutane sai wani kallanta suke, aida saitasa hijab ko? shide musty dayake dariya qasa qasa yace inaga ba halinta bane hakan, yanzu ne kawai tasaka Qasa yasakeyi da muryarsa yace kafadawa daya daga cikin sojojin nigeria dasuke zaune anan ayimin bincike akan yarinyar nan, akawomin komai nata nanda jibi Cikin serious mustapha yace angama sir Ga wayar taka, yabawa Aliyu wayar , shikuma yajuya yana fadawa wani soja dayamusu rakiya zuwa Airport saqon Aliyu, tareda nuna musu su iman dasuke tsaye Murmushi yasaki, dayaga me kiran nasa daga nigeria, yana dagawa yace tuba nake bros , inadan wani uzuri ne shiyasa nayi rejecting call din naka, dakatawa yayi da magana yana sauraron dayan bangaren Bansan meyace masaba naji haidar yace a a karka damu ai ABIN BROS NA BROS NE Yana wayar yajuya yasake kallan iman da batasan dashiba, sannan yatafi sojoji suna take masa baya Suna tafiya, iman tajuya takalli inda yusy tace mata ga sojoji nan hankalinta ne yakai kansu, saide alokacin sunbasu baya sun riga dasun tafi, sai bayansu tagani Juyawa tayi taci gaba dacin chesee dinta (Tofa yanzu chakwakiyar tafara,😱 anya kuwa Haidar bai debo sama da zafi ba😱😱 ???? (Waima wacece iman ne?nasan mai karatu yanaso yaji wacece wannan iman din da ake magana akanta, to kubiyoni danjin wacece iman) Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 6 Lokaci Nacika sukai sallama da yusy suka tafi Zuciyar yusra daya tafita tatare taxi saide abinda Bata saniba shine akwai masu bibiyarta Abaya, Saida sukaga shigarta hostel din sannan suka tsaya wajan masu gadi *** *** *** Karfe biyu nadare flight dinsu yasauka, direct Daga Airport Mota ce ta daukesu tamaidasu masauqinsu Shima gida aka wuce dashi Yana shiga Shiru gidan kowa yayi bacci, baiyi gigin tashin mamy ba, dakinsa ya wuce yafada Kan gadonsa Saman dakin yazubawa ido yana kallo, saide azahiri idonsa ne awajan, ruhinsa da tunaninsa Suna gareta Gaskiya Allah yayi baiwar komai da komai awajan Ashe a wannan zamanin zaka samu mace haka, wata Zuciyar tace dashi Har fin hakama Ana samu Tokodan baya shiga sabgar yanmata ne shiyasa Bai hadu da irinta dinba Kozata Soni? Yake tambayar kansa Wani bangare na Zuciyar sane yarinjayeshi Akan Cewa ai bashida aibun dazata qishi Harya matsu lokacin daya Diba su cika domin yaje ya tunkareta gameda abinda yakeji acikin ransa "To Allah yasa de tasoni" yafadi Hakan afili cikeda Alhini Tashi yayi cikin nutsuwa yacire takalmin sa tareda kakin jikinsa yashiga wanka *** *** *** Zeey yakamata Musa Yaya yakaimu saloon Ko? Kanta yana kan cinyar Iman, tace "Eh anty Daga Nanma saiki kaini wajan wasa, ki siyamin Ice Cream, da sweet" "a a Zeey, abin Yamin yawa, bazan iyaba, Daga zancen saloon saiki ta jeromin wannan abubuwa haka " Fizge kanta tayi Daga hannun Iman tayi wajan Hajiya dake zaune tana kallansu " hajiya Kinga anty Wai bazata saikin sweet ba " Cikin fada Iman tace yes fadi da ihu yarinya bazan siyaba Itama cikin hawaye tace dama bakizo ba anty Bilkisu kawai tazo, kekwa ki zauna a school, dog ya cinyeki Ba Iman kadaiba hatta Hajiya ma Saida tayi Daria, ta janyo zainab jikinta tace Rabu da anty Iman, yanzun Nan zankira Miki Bilkisu awaya tataho Daga katsina takaiki duk inda kikeso Washe bakinta tayi, tayi cikin daki dagudu tana murna Falon yashigo yayi masifar kyau cikin qananun Kaya, agogon dake hannunsa, Yazo dab da ita yazauna Akan hannun kujerar datake Kai, Kasa yayi da murya yace "muradina zan fita Ko akwai abinda kikeso?" Hajiya tana kallansu ta gefen idonta, wannan rashin kunya tafara isarta, garama Iman tayi tagama school dinnan ayi musu Aure Ko sa huta Itama Ahankali tace masa Saloon suke San Zuwa itada Zeey Sai a lokacin yadago Daga sunkuyawar dayayi yanayi mata magana Daga murya yayi yakira Zeey, ai kuwa aguje tataho ta rungumeshi Yace yanmatana jeki futo muje wajan saloon keda anty Ko? Saida tayiwa Iman gwalo sannan tajuya ciki da gudu Tana futowa sukai wa Hajiya sallama data nuna Kamar Bata ganin su Suna fita tabisu da kallan birgewa, hannu ta Daga tace Allah ka qara hademin Kan yarana Amin *** *** *** A dinning suke zaune mamy nacin abinci taga sai juya abincin yake, kallansa tayi da mamaki tace Baby me yake damunka ne? Babu tunanin komai yace "mamy akwai aikin Dana bayar ne Bansan asamu matsala aciki" Spoon din hannunta ta ajiye tace "to menene abin damuwa, kayi hakuri insha Allah babu matsala kaji?" Cikin sakin fuska yace to mamy Yauwa baby nah ci abincin ka Nan take ya ware yana cin abincin, Amma cikin ransa adduah yake Allah yasa angama binciken da za'ayi Akan yarinyar Nan Suna gamawa yace mamy zanje nadan motsa jikina, yafice Daga falon Yana harabar gidan yana motsa jiki Amma tunani yahanashi yin abin kirki Towel din dake gefen sa yadauka ya share zuffar dake zubomasa Huci yayi, tare da firzar da iska Mai zafi Daga bakinsa, yajuya yadanna wayarsa Ko zaiga Kiran musty, nanma Shiru Haka ya hakura yayi dakinsa tareda shigewa wanka Har dare yakasa fita Ko Ina yana zaune a daki yana aikin tunani, Wai wannan wacce irin masifa cene? Dama haka masoya sukeji? To ai Har Gara masoya ma sunsan sun furtawa junansu so, to Amma shifa Ko yarinyar ma batasan yanayi ba Kasa hakuri yayi yadau wayar sa yakira Mustapha, bugun farko Mustapha yadauka yace sorry sir gani Nan a hanyar Zuwa gidan Batare dayace komai ba yakashe wayar, yafada Kan gadonsa tareda runtse idanunsa Ba'a dauki lokaci Mai tsawoba musty yashigo gidan, Saida suka gaisa da mamy sannan yayi dakin Aliyu Yana shiga qamshi hadeda sanyin esi suka bigeshi, qarasawa yayi Kan gadon yazauna yace" Sir gashi angama komai" Yanajin haka ya Bude idonsa yace "musty kadameni da wannan sir din wallahi, Dan Allah ya Isa haka, haba! Saida yagama mitar tasa sannan yace" bani" Takarda yamiqa masa yace Nima sai dazu suka turomin ta email Dina, to da zan turoma ta Email din saina fasa naje aka ciro ta yanzu Yana gama magana yamiqe Yace "to abokina saina dawo latter naji bayani, Dan yanzu aiki nake nataso" Batare daya kalleshi ba yace kaide kawai Kace guduwa zakayi babu wani aiki Da gaske nake, madam tayi kirana, zan dawo Zuwa gobe Kansa kawai yakada masa Batare daya yarda da maganar ta Mustapha ba, kawai de yasan Cewa yabashi dama ne yakaranta abinda yakawo masa Mustapha nafita ya gyara zamansa a Saman gadon yabude takardar tareda karantawa cikin ransa Wacece Iman? Sudin cikakkun shuwa Arab ne dasuka Tashi agarin maiduguri, mahaifiyarta da dangin mahaifiyarta dukkansu maiduguri ne tushan su Asalin Sunanta shine FATIMA SHU'AIB Amma Ana Kiran ta da (Iman) Tanada yar'uwa Bilkisu wadda ta kasan ce Shiru Shiru marar magana, komai nasu daya ake musu, kasancewar su Kamar wasu twince, tare suka fara makaranta tun Suna Yara, Bilkisu nayiwa yar'uwarta biyaiya,hakane yasanya take Kiran ta da Sunan YAYA IMAN, saide Iman akwai ta da tsiwa, Tanada San girma, akomai tanaso taga qanwarta Bilkisu tabata girma mahaifinsu cikakkan bahaushe ne Dan asalin jihar Katsina Garin Funtua Yanzu Iman tana matakin gama degree dinta na farko ne Aqasar Ghana itada yar'uwarta Bilkisu, saura Semester daya su kammalla karatun su Inda suke Karatun bangaren likitanci Ajami'ar KWAME NKRUMAH UNIVERSITY OF SCIENCE AND TECHNOLOGY saide abinda ba'a saniba shine Bilkisu tana hannun mahaifinsu ne a katsina, ita Kuma Iman tana hannun Mahaifiyarsu ne agarin kano Anyi musu hutun semester ne na one week shine suka shirya tafiya gida hutu ___________ Ajiyar zuciya yasauke daya gama karantawa, idanunsa yakai kasan takardar yaga number wayarta dakuma sunayen datake amfani dasu ashafukanta na yanar gizo Baiyi qasa agwiwaba ya adana komai nata acikin wayar ta hanyar saving Yana saving number ta yaga dashi take whatspp sannan ya tafi shafinta na Facebook da Instagram, anan yaga ruwan pictures dinta, domin kuwa Iman takanas barrister yake daukanta suje ayi musu pic, da Hakan take amfani wajan Dora Iya nata ayanar gizo Afili yace "wannan yarinyar me yake damunta ne take dorawa Dunia pictures dinta?" Dan qaramin tsaki yasaki yasake Cewa yanzu haka kowa yadauka " Saving din pictures din nata yayi dayawa, sannan yakashe datar sa Bama wannan ne damuwar ba, menene yasa sister nata take zaune ahannun babansu? Dole ne gobe yanemi Mustapha domin qarin haske Akan Hakan Photunan ta yaci gaba da kalla, dazaran yaga wannan zai koma Kan wani yayita kallah, Bai Tashi ganin lokaci ba sai gani yayi dare yayi sosai, Dan haka yayi adduah ya kwanta domin yanaso gobe da sassafe mamy taji daddadan labari *** *** *** Next day Yana Tashi Daga bacci yashiga wanka, Kamar kullum wando yasaka three quarter Sai rigar jikinsa wadda ta kasance marar hannu Shi kansa jinsa yake cikin nishadi, Kuma yasan Hakan baya rasa nasaba ne da wannan yarinyar Wai a hakama Bata fara bashi kulawa ba, to inaga sunyi Aure Kuma, Ko menene zai kasance? Kiran musty yayi awaya yana dagawa yace "kazo gida ka sameni, akwai sauran abinda ban ganeba game da yarinyar Nan" Daga dayan bangaren Mustapha yace eh dama Ina Kan hanya gani Nan Zuwa " Yana kashe wayar, cikin galary dinsa yashiga, yafara duba pictures dinta, fridge yanufa yadauki lemo yariqe ahannun sa Batare daya fara shaba yaci gaba da aikin kallan ta Anya kuwa dayasan yarinyar Nan bazaice ba kalau tabarshi ba? Daga ganin ta yashiga irin wannan yanayi? Yana wannan tunanin Mustapha yashigo dakin, yana zama Haidar yabashi labarin komai, yaci gaba da fadin Amma abinda bansaniba shine meyasa basa zama waje daya itada yar'uwarta? Mustapha yace ni aganina kawai ashare wannan maganar Daga baya idan kun dedeta zaka San komai "eh hakane Musty, Amma gaskiya inasan yarinyar Nan, banajin zan Iya rabuwa da ita, bantaba tunanin zanso wata yarinya Har hakaba Murmushi Mustapha yasaki yace ai kaima ba bayaba abokina, nasan insha Allah za'a dace "to shikkenan Musty, saimun sake waya, zan shiga wajan mamy, Dan Ko break fast banyiba Hannu musty ya miqa masa suka sake gaisawa sannan ya tafi Sai wani walwala yake shi kadai, yanata fara'ah, atika ce tafara ganinsa, a ranta tace to yau Kuma me akayi masa Kamar qaramin yaro yana Zuwa yazuba ajikin mamy, Kai Haidar narasa yaushe zaka girma, wannan ai saika karyani Atika dake gefe tace cikin ranta uhm yaushe zai girma kuwa kullum Ana ce masa baby Cikin farin ciki yace "mamy albishir" "goro fari Haidar " Yaune Karo na farko dayaji nauyin fada mata magana, kodan maganar Tanada alaqa da Zuciyar sane Qasa yayi da kansa yace" mamy yaude kinsamu in law" Baby idan wasan daka saba minne, please kadena " " mamy da gaske nake, inasonta, Kuma so na Aure, gaskiya mamy idan ban sametaba akwai matsala, meeting din danaje Ghana acan naganta, Amma Har yanzu banyi magana da itaba, sonake sai kinganta tayi Miki tukunnah " Wayarsa yadauko yashiga cikin pictures dinta, yabawa mamy wayar yaci gaba da fadin" mamy Kingantafa " Tana ganin photon gabanta yafadi, meyasa yarinyar take mata kama da ZAINAB? babu banbanci sak photo copy din zainab ce Amma saitayi tunanin may be kama ce kawai Haidar yanajinta tayi Shiru yace mamy yakika ganta, tayi Ko batayiba, idan Bata Miki ba asake wata Jijjiga kanta tafara sannan tace Gaskiya Baby wannan maqiyinka ne kawai zaice ma batayiba, but tanamin kama da wata mata , ita wannan yarinyar a'ina take? "mamy akano take wajan mahaifiyarta, " Jin wannan amsar da Aliyu yabata yasa Zuciyar ta yarda Cewa ba wadda take nufi bace" Daga murya mamy tayi tace atika zonan Atika nazuwa mamy ta nuna mata pictures din Iman tace Kinga budurwar baby, yaude gori yaqare " Atika nagani tace Kai masha Allah, wallahi mamy saikace balarabiya Dukansu Daria sukayi Yau Atika saboda anga waje, taganshi yana farin ciki, akace, Kuma ya sunanta? Kai tsaye yace sunan mamy nah gareta, Fatima, Amma Iman ake cemata Mamy tace masha Allah, gaskiya yarinyar tayimin, Allah ya tabbatar da alkhairi, kafada mata da Aure kakesanta bakasan abin yadau lokaci idan tana sanka Sunkuyar da kansa yayi yace to mamy Mamy am hungry Atika ta kallah da sauri tace maza atika kawowa baby abinci nabashi Shikuwa saboda farin ciki harda Dora kafa daya Kan daya, yau Mamy zata bashi abinci da kanta, yaushe rabo Dakanta taciyar dashi, yanaji yaqoshi yayi dakinsa domin Kiran Iman awaya (waishin wacece wannan zainab din? 😏😏 Anya kuwa Kuna ganin Iman zata amince da Haidar? πŸ™‰πŸ™‰πŸ™‰πŸ™‰ To kubiyoni de fatana ku nishadantu da wannan labari (Ayau Ina farin cikin sanar da fan's Dina Cewa zaku dinga Jina kullum, Kamar Yanda nasaba yi muku Abaya, dama nadan samu matsalar waya ne) Mrs Usman Ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 7 Tunda yakoma dakinsa yakasa zaune yakasa tsaye, saiya dauki wayarsa zai kirata saiya fasa, yayi Hakan yakai sau biyar, to idan yakirata me zai fada mata? Gyaran murya yayi, yafara gwadawa shi kadai agaban mirror yana kallan kansa Sunana Aliyu Sa'ad Bilal Ina sonki Girgiza kansa yayi, "no Hakan baiyi ba" Salamu alaikum, Am Sunana Aliyu Haidar, dama naganki ne a airport shine nake sanki Tokuma idan tace nikuma Bana sanka fa, girgiza kansa yayi, Allah ma yakiyaye Qara gyara tsayuwarsa yayi, harda gyara wuyan Rigarsa, sannan yace "Ni Sunana Haidar, ni soja ne, nadade Ina neman matar Aure bansamu ba, Saida naganki shine kawai Nima naji Ina sonki Wata Zuciyar ce tace dashi, wato kace mata kadade bakayi Aure ba, Daga Nan Kuma sai tace dama kwantai kayi shiyasa ni kazo wajena Dayawan mata ba'a cika birgesu ba idan kahadu da ita gani na farko ka baiyyana mata sirrin dake ranka, wasu matan sunfi son saikun fahinci Juna tukunna kafin ka baiyyana musu sonka atare dasu Ajiyar zuciya yasauke, yanemi waje yazauna Afili yace gaba dayama bazan fadi Ko dayaba, kawai zanbi shawarar mamy, datace nafada mata Cewa da Aure nake Santa May be Tunda Nabi shawarar mahaifiya saina dace Da wannan shawarar yayi amfani wajan dauko wayarsa yabude data, Kai tsaye whatspp yahau Yaduba number dinta, yatura mata da "hi" Kuma sai akai dace adede lokacin tana chatting ne da yusy Ganin sabuwar number taturo mata da hi, Kuma gashi batasan number dinba, hakanne yaja hankalinta wajan Bude saqon Yana ganin alamun an Bude saqon yazuba tagumi yace to Allah gamu gareka Kai tsaye tatura masa tambaya "waye?" "Sunana Aliyu Sa'ad " Afili ta furta Aliyu Sa'ad Kuma? Waye Hakan? Tambayarsa tayi Cewa" waye? Kuma wakake nema? Yace "ke nake nema" "kasan dawa kake magana kuwa? " Shima anasa bangaren yatura mata Cewa" da Yaya Iman " Mamaki ne yakamata, to wannan duk Yanda akai may be yasanta sosai, Tunda Har yasan ta da wannan sunan " me yake faruwa? Abinda tatura masa Kenan Shima yace "inasan nakiraki idan kin bani damar Hakan" "no, kafadamin menene, Bana buqatar Kira " Afili yafurta" tofa" Achat din saiya tura mata Cewa, "Sunana Ali Sa'ad Bilal, Kamar Yanda nafada Miki, Ina aiki ne tareda Rundunar sojan Sama ta Nigeria, naganki ne aghana, inason na Aure ki" Daria maganar ta Bata, Saida Tasha dariyarta, Afili tace wannan wanne irin mutum ne? Kuma ma Wai soja, Anya kuwa yasan Yanda ta tsani sojoji, kwata Kwata basa birgeta Amma acht saita ce masa 'thank you " Shikuma yarasa me zai fada mata, Kenan Bata sanshi ne kokuma tana sanshi, me wannan thank you take nufi Tambayarta yayi, Zaki Iya Aure na? Itama tatura masa Cewa bansankaba, bantaba ganinkaba, kawai Daga haduwa a cht sai in amince inyima alqawarin Aure? Kansa yashafa, zuciyarsa tafara daukar zafi, gabansa na faduwa yace mata, ga pic Dina Nan a dp, ki duba Abangaren Iman kuwa mamaki ne yake sake kasheta a zaune, wannan wanne irin mutum ne? Kana neman Abu a wajena Amma aji za'ace kokuma girman Kai yahanaka yin biyaiya Wato pic dinma bazai Iya turo mataba, saide ita tabude, inta matsu Shikuma anasa bangaren Bai fadi Hakan dawata manufa ba, shide na farko Bai saba hulda da yanmata ba, bare yasan abinda suke so Ko abinda basa so, sannan shi aganinsa atsaya Ana wani kece farin cikina, kace kaza Dina, duk ba abin birgewa bane, shi yafi San idan kana San Abu, toka nuna abaiyane Kuma agaban kowa Abinda yasani shine Allah yadasa masa soyaiyarta acikin Zuciyar sa Yanda baya zato Iman batayi qasa agwiwaba tabude pic din Naka Photo ne dayayi shi acikin jirgi, yana gefen window, da farin kaki ajikinsa na sojan Sama Saving pic din tayi a wayarta, sannan tace masa Amma Kai fulani ne Ko? Sai a sannan yayi dariya harda gyara zama ganin tafara kulashi, yace no, babu wani fulani, ni bahaushene dan'uwanki Itama tatura masa Cewa ai ni ba bahaushiya bace Yace sorry namanta, ashe fa ke Shuwah ce Afili tace Wai wannan mutumin ya akai yasan abubuwana dayawa ne? Bata bashi amsaba yace nabaki dama kiyi bincike akaina, Kuma kiyi tunani idan Zaki Iya Aure nah, Ki gaida Bilkisu Bye Yana gama tura mata yasauka online Gaba dayama tarasa tunanin mezatayi, wakuma zata fara tunkara da wannan magana? Billy batanan tana katsina, Amma ga yusra Nan ai Suna chatting Bari tabata labari Ta chat din takira yusy tace Besty akwai labari, yusy tace Kai Teemah saboda tsabar gulma Akan ki turomin saikin kirani Iman tace inaa ai babban labari ne yafi karfin chat Yusy tace to qawata bani Nasha Iman ta kwashe komai tafada mata, harda pic dinsa ma duk tatura mata Yusy tace 'Besty Anya kuwa ba qarya yake Miki ba? Ba irin samarin unguwa bane Yan renin sense? "Nima abinda nayi tunani dafarko Kenan Besty, but abinda zai baki mamaki shine harfa Bilkisu yasani, Wai harda Cewa Yaya Iman, sannan Wai ni Shuwah ce Yusy tace to yanzu yaza'ayi? Nikam yusra ai ban Isa in saurari waniba, Bayan ga Yaya Imran, Kinga wannan pic din nasama Ina turo Miki nagogeshi a wayata, gudun matsala, Wai harda Cewa aghana yaganni, inba qaryar mazaba aghana a'ina? Muda ba yawo mukeba Yusy tace a a karkice komai, Tunda yafadi Hakan nasan ba zaiyi qaryaba, Tunda naganshi babba ne, yanzu abinda za'ayi shine Tunda yace kiyi bincike akansa, kiyi din mugani waye shi Nifa ba zanyi wani bincikeba yusy, kawai zan bashi hakuri in fada masa inada wanda zan aura Yusy tace karkiyi haka Iman, bahaushene fa yace so Mai sonka, ke zakiji dadi idan Allah yadora Miki son wani daban, ki tunkareshi kifada masa Amma aqarshe irin wannan amsar tabiyo baya? Ki lallabashi ku Rabu lafiya, ni aganina hakanne mafita, Kinga kun Rabu lafiya, Shima beji haushinki yaje ya dirka Miki wani asirin ba Tanajin zancen asiri tace na shiga ukuna Yusy tace a a bafa Cewa nayi zaiyi Miki asiri ba, kawai de nafada Miki abubuwan dasuke faruwa ne gameda wasu samarin idan kace Baka kaunarsu Cikin sanyin jiki Iman tace to yanzu Yaya zanyi? Yusy tace menene sunansa? Kai tsaye Iman tace yacemin sunansa Aliyu Sa'ad, Kuma shidin sojan samane na Nigeria Yauwa Kinga saimu bincike mugani inma qarya yake ai zamu gani, inji yusy Iman tace to tayaya zamu bincika? Yusy tace kadaa ki kashe wayar Bari naduba sunayen sojojin Sama a Google nagani, inma babushi ai zamu gani Iman tace toyi sauri Ina jiranki Yusy batafi minti biyar ba tasaki ihu ta cikin wayar Iman tace Besty karki kashen kunne, yusy tace Iman wallahi Ina searching sunansa naganshi, shine shugaban sojojin Sama na Nigeria baki daya Sunansa kawai nasaka, Amma anturomin harda pic dinsa, Kuma shine de wannan wanda kika turomin ajikin pic din Shikkenan Besty keda bakyason soja, gashinan kin kwaso shugaban su Ajiyar zuciya Iman tayi, sannan tace zan fada masa gaskiya Besty, bazan boye masa komai ba, karma yaga narabu dashi yayi zatan na yaudareshi (Yaya kuke ganin Aliyu zaiji idan Iman tafada masa gaskiya?) Duk wanda yaga banturo masa WAZAN ZABA a group dinsaba, to banga sharhi bane Idan anjini Shiru, tokada anemeni, Nima najika Shiru ne Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA? πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 8 Da wannan shawarar ta yusy Iman tayi amfani, wajan kawar da maganar Aliyu Daga cikin ranta, tama manta dashi taci gaba da sabgogin gabanta *** *** *** Tunda sukai wannan mgnr da Iman acht ya tsinci kansa cikin farin ciki, shida kansa yasan yasauya, komai yanayinsa cikin walwala, hatta da abokan aikinsa sun fahinci Hakan, saide musty ne kawai yasan sirrin Mamy kanta tana lura da yanayinsa, saide tayi Murmushi taqara godewa Allah, daya karkato mata da hankalin danta izuwa abinda takeso Kamar Koda yaushe yauma break sukeyi shida mamy, atika tana goge kayan falon, Bayan tagama mopping Ruwan tea yakesha Amma wayarsa tana hannunsa yana danne danne, wanda azahiri pic din Iman yake kalla, mamy data kula hankalin sa baya Kan abincin Tayi Murmushi tace" baby mekake kalla ne bakasan cin abinci? " Kamar wani marar gaskiya haka yadauko wayarsa yanuna mata screen din wayar, Pic din Iman tagani, tace to yanzu Haidar aida kabari kagama saikaje kayi ta kallanta Ko" Babu kunya Aliyu yace "mamy ai idan Ina ganin photon zanfi cin abincin?" Girgiza kanta mamy tayi, tace um duniya Ina Zaki damu? Wai yau Kaine me kallana kace in kana ganin girl friend dinka zakafi cin abinci Sai a lokacin ya lura da katobarar dayayi, ashefa mamy ce Dan haka kawai saiyayi Shiru yana sosa kansa, wayar ya ajiye asaman dining din sannan yamaida hankalin sa Kan tea din dayakesha Mamy data zuba masa ido tana kallansa cikin ranta tace damafa hakane, duk wanda zakaga baya kule kulen yanmata, Ko Kuma yanmatan Suna sonsa baya saurarensu qarshe sai kaga soyaiyar wata daban tana wahalar dasu Farfesun datasa atika tayi, tadauko flet tazuba masa, spoon tasa tadiba ta nufi bakinsa dashi, tace "dauki wayarka kayi kallanka, saina baka abincin, Shima baiyi musuba yadauki wayar, yana kallan pictures din Iman mamy Kuma na bashi abinci Saida ta tabbatar ya qoshi sannan ta qyaleshi Tissue yadauka yana goge bakinsa, yace" mamy ai dole ne inkira Bros awaya in bashi labarin yarinyar Nan, " To ai daka Bari idan muka koma gida saika fada masa, Nima sainayiwa Yaya magana, kaga sai manya su shiga cikin maganar " to shikkenan mamy nah yanzu Bari inji muryarsa kawai, ni kada ma yayi fishi, kullum saide yakirani bancika nemansa ba Ringing biyu wayar tayi, akayi picking Daga dayan bangaren "Bros ya akayi? Aliyu yace "normal ya gida ya harkoki, dafatan mutanan gida kowa lafiya Lafiyarmu kalau Bros, kasan akwai wasu zafafan motoci Ahmad muhd marzuq yakawosu Daga Cairo, inaso saika dawo Nigeria saimuje mu siyosu, but yaushe zaka dawo ne,? Saina tura masa da kudin da wuri Murmushi Aliyu yayi, yace no, wannan Karon bakaine zaka siya manaba, nine zan siya mana Shima yace no Bros Aliyu ma yace karka damu, ai ABIN BROS NA BROS NE Daria sukasa gaba dayansu, sannan sukai sallama Mamy tace wato Aliyu bazaku Dena wannan sarar taku bako? Yana Daria yace mamy ai wasa ne kawai *** *** *** Tundaga wannan lokacin Iman Bata sake magana da Aliyu ba, Har tsawon kwana biyar, adede wannan lokacin Har hutunsu yaqare sunkoma school, sai yau yayanke shawarar kiranta awaya, domin yasan Cewa Zuwa wannan lokacin ai ta Riga data gama yanke shawara Tana zaune adakinsu ita kadai, su Billy sun fita itada yusy, taji wayarta na ringing Zuciyar ta daya tadauka, cikin Isa da taqama irin tasa yayi Mata sallama Bata Gane wayeba, kawai de abinda tasani shine taga number wata qasar tana kiranta, amsawa tayi tareda Cewa waye Agajarce yace Ali Sa'ad Lokaci guda ta ganeshi, tace OK yakake Kai tsaye yace Alhmdlh, Dama nakirane inji Yaya kike, sannan Kuma me kika yanke game da maganar da mukayi Handout din dake hannunta ta ajiye tace kasan abinda ake nufi da Trailer irin babbar motar Nan? Da mamaki yace nasani mana, To Kamar haka samari na suke, inada samari dayawa, akwai wanda nakeso, da Kuma wanda banaso Cikin yarda da Kai da Kuma ji dakai irin nasa yace "zanso shiga daya Daga cikin wannan motocin, harma nazama nine nake Jan motar watarana Taqamarsa ce tasata Daria, tace bazaka iyaba, domin sudin ba qananun qwari bane Kamar Yanda kake tunani " kidena hadani da irin wannan samarin, nasan kaina, ni ba irin su bane, Zaki Gane hakanne idan kika bani dama guda daya tak, damar kuwa itace ki amince da soyaiya ta, zakiga Yanda zanyi fatali da gwamnatin kowa, tawa gwamnatin ce kawai zata mulki birnin Zuciyar Ki Aranta tace waishi irin jiji da kannan zai nuna min, nikuwa zan nuna masa yayi kadan, zanga karshan qaryar tasa Domin ta qureshi tace shikkenan nabaka dama Wani sanyi yaji acikin ransa, Murmushin Nan take ya wanzu a fuskarsa yace godia nake MATAR ALIYU yakashe wayarsa *** *** *** Wayar ta riqe a hannunta cike da mamaki, afili tace waishi ji yake irin babban qwaron nanne a soyaiya Karatun ta taci gaba dayi, tana cikin karatun su yusy suka dawo Suna zama ta dubi yusy tace Besty wannan gayen fa yakirani yanzu, Nan tabata labarin komai Yusra tace ai kuwa zamu qureshi, muga karshan cika bakin nasa Bilkisu tana jinsu tatabe baki tayi Shiru, to basu sata acikiba, yanzu tana magana Yaya Iman zata hauta da bala'i *** *** *** Tundaga wannan lokaci Aliyu yafara shigar da kansa awajan Iman, Kiran safe daban, na Rana daban na dare wannan daban ne Wataran tayi picking wataran Kuma ta share shi Duk lokacin da taqi dagawa yusra ce maiyi mata fada Akan ta saurareshi ai Suna so su qureshi ne Ahankali take kulashi, harya kasan ce kullum sai sunyi chatting Kamar kullum yauma Suna chatting taje tasaka pictures dinta a status masu zafi Bata dauki lokaci dasakawa ba, kiransa yashigo cikin wayarta Tana dagawa, yace "kije kicire pictures din dakika saka yanzu, " meyasa zan cire? " Damafa Ina sakawa Zuciyar sa na quna yace nasani, nikwa nasan kina sakawa, Amma abinda nakeso kisani shine, Ina sonki, Qasa yayi da muryarsa cikin Shagwaba yace" Ina kishinki Iman, bazan Iya ganin pictures dinki wasu mazan Suna kallah ba "batasan meyasaba haka kawai ta tsinci kanta da Cewa to shikkenan Bari nacire Tana cire pictures din, tarufe datar Tama gaba daya Duniyar tunani tafada, shi wannan yana sonta, yana kishinta bayasan wasu mazan suga pictures dinta Haqiqa kowacce mace tanaso asota, Kuma nuna kishi shine alamun soyaiya, Aliyu halinsa daya yar'uwar ta Bilkisu, inama ita yanema da farko, da halaiyarsu ta dace da Juna, Bilkisu tana saka Kaya na kirki na mutunci, Bata da rigima, Kuma Bata da magana, Haka Kuma saka pictures dinta a yanar gizo Bai dametaba Shikuma wannan yasonta, yana Bata kowacce irin kulawa, Amma Kuma shine yake kaita wajan photo da kansa tadauka, harma tasa a Internet Amma Bai taba hanataba It means yana sonta, bayasan ganin laifinta, yana Bata dama tayi duk abinda takeso Runtse Idanunta tayi, kanta fa yafara daukar zafi Jaruman maza guda biyu, ma banbanta awajan Halaiya Yusra na bacci, Sai Billy dake zaune a gefe duk tana kallan duk wani motsi na yar'uwar Tata Duban ta tayi tare da Cewa Yaya Iman ya akayi ne? Meyake damunki? Wayarta ta ajiye a gefe daya, sannan takamo hannun yar'uwar Tata, Bilkisu cike da mamakin yayar Tata tace Yaya Iman, keda waye kike waya yanzu? Bata amsa mata tambayar tataba tace "Bilkisu idan mutum yana kishinka me Hakan yake nufi? Manyan idanuwanta ta juya tace Yaya Iman Hakan yana nufin yana sonki ne mana Jijjiga kanta tayi, sannan tasake jefo mata wata tambayar " Tokuma yanzu misali kece mutum biyu suke sonki, daya yana kishinki, daya Kuma yana nuna Miki soyaiya Amma Bai cika nuna Miki kishi ba, kullum zakici kwalliya ki fita babu ruwansa da wanda zai ganki da wanda bazai ganki ba Abu daya kawai yasani shine kece Muradinsa Shin wazaki zaba acikinsu? Murmushi Bilkisu tayi Kamar ba yar'uwarta ce take cikin damuwa ba Tace "Yaya Iman, idan na fahinceki kina magana ne Akan Yaya Imran da Kuma wannan sabon boyfriend din naki dakika yi, Yaya Iman ki godewa Allah, Yaya Imran yana sonki, yana qaunarki,, kowa dayake familynmu ya shaida Hakan, bance Miki wannan sabon saurayin naki baya sonki ba, a a Amma abinda Zaki duba shine, Yaya Imran dashi muka tashi, yasanki, kinsan shi, yana sonki, kina sonshi To meyasa ma Zaki tantama a kansa? Ki godewa Allah da baba yabaki dama kika saurari Imran, kinsan halin mahaifin mu Yaya Iman Kina gani de, Ina zaune yakawo Haroon yace shine mijina, shine wanda zan aura, baya sona, Bana sonsa, Amma ahaka nayi hakuri nayi masa biyaiya Yaya Iman ni kadai ma na isheki ishara, dazatasa kici gaba dason Yaya Imran Ni yanzu na Isa na saurari wani namiji Bayan Haroon? Ban isaba, Tunda umarnin babane Hakan Maganar dakikemin ta innice wazan zaba Kuma, shine idan nice adduah zanyi, Allah yaciremin son sabon saurayin araina Shikkenan an zauna lafiya Iman tace "nagode da shawarar Ki Bilkisu, insha Allah zanyi Yanda kika ce Itama Billy cikin Murmushi tace yauwa Yaya Iman Rungume Juna sukayi cike da kaunar juna *** *** *** Agajiye yadawo Daga wajan aiki Hajiya dake sake gwadawa Zeey auta home work, ta dubeshi tace sannu Imran Kaine bakasan zama, kullum cikin yawo kake Cike da Shagwaba yace to hajiya ai hujjoji nake nema, Kuma yanzu ai shari'ar ma taqare, nine nayi winning Murmushi tasaki tace to Dana, Allah yaqara temakawa Duban zainab tayi tace auta riqe littafinki nabaka Yaya abinci Ko? Kyabe fuska yarinyar tayi alamun kuka Imran na ganin haka yace Hajiya zauna, Naga alama Yan gidannan gaba dayansu kishi suke Dani Ai Gara Zeey Akan Farhan ma Kusha Zaman ku Bari inje inyi Sarving din kaina Yana gama fadar haka yatashi yayi dinning Bayan yagama yadawo wajan hajiya, lokacin zainab tatashi, kansa yashafa yana kallanta Murmushi tayi tace Imran Dina, Kamar akwai abinda yake damunka Ko? Sosa kansa yayi sannan yace Hajiya dama inaso ne kifadawa Alhaji idan su Iman sun qare semester dinsu sun dawo, Dan Allah dasun dawo atsaida ranar bikinmu Yana gama fadar Hakan, yatashi yayi part dinsa kansa aqasa Ha'ba hajiya takama, oh yaran yanzu zai Ahankali, Imran Ko kunya babu? To dama Yanda ake wannan rashin kunyar agabanta shida Iman, ai yaran nata Suna gamawa za'a tsaida lokacin biki ayi kowama yahuta *** *** *** Kuka take sosai, Idanunta sunyi jajir, yusy ce me rarrashinta Best ki fadamin mana me yake damunki ne Wai? Ko akwai abinda yake faruwa a gida? Girgiza kanta tayi alamun a a Yusy tace nashiga uku, Kinga Bari nakira Barrister nafada masa Dasauri tariqe hannunta, cikin kuka tace yusy.... Pls.. Karki kirashi, nashiga ukuna Besty Yaya zanyi? Nifa Iman kin dauremin Kai, Dan Allah ki sanar Dani me yake faruwa Kasancewarta fara yasa kukan datasha yasa Kan hancinta yayi jajir Cikin kukan tadago da kanta ta kalli Yusra tace "Besty nashiga ukuna wallahi Ina sonsa" Adede wannan lokacin Billy tashigo cikin dakin, wannan maganar ce tasauka akunnanta Iman taci gaba da Cewa "Bansan yaushe Hakan tafaru ba, bilkisu tabani shawara, Kuma nayi Amfani da ita, duk addu'oin danakeyi abinma qaruwa naji yanayi Halayensa, kulawarsa agareni, ajinsa da komai Nasa sunja hankalina, wallahi idan ban sameshi ba ayanda nakeji cikin zuciya ta Besty akwai matsala Nashiga ukuna, shikkenan nazama butulu ni Iman " Cikin zafin rai Billy dake gefe aqame, tace" Butulu kuwa ta gaske Yaya Iman " Dukansu Juyawa sukai suka kalleta, domin kuwa ba Susan da zuwanta ba Cikin hawaye Iman tace Dr. Daga mata hannu Billy tayi tace, babu wani Dr. Ayau Yaya Iman, wallahi kin bani mamaki, Har yaushe Zaki Bari Zuciyar Ki takamu dason wani bare, bakisanshi ba, besankiba, haduwar network, Har yaushe Zaki soshi Akan Yaya Imran? Ina shawarar Dana baki Yaya Iman? Tsautsayin dayasa kika amince dashi shi zaisa kije kirabu dashi Wani lokacin kina bani mamaki Yaya Iman, Wai kokin manta da wacece Hajiya awajanmu ne? Halaccin Hajiya agaremu Dani, dake, da baba, kadai ya Isa yasa kiso Yaya Imran Yusy dake gefe ta dafe kanta da hannunta duka biyu, tace ni duk kun dauremin Kai wallahi Please ku fadamin wacece HAJIYA? Kuma Yaya kuke da BARRISTER IMRAN? (tonima de inaso naji wacece hajiya,πŸ€”) (Anya kuwa Hatsaniyar da Iman ta debo me bullewace 😱😱? Ba anan Hatsaniyar ta qare ba, fatana kuci gaba da hakurin bibiyata Share Comments Sharhi Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 9 Alhaji Abubakar, shine cikakken sunan Mai gidan, gogaggen Dan kasuwa ne, daya Shahara aharkar Saida yari Yanada shaguna dayawa akano duk na Saida yari ne, mugun me kudi ne dayasan mutane dayawa manyan Yan kasuwa dakuma manyan Yan gwamnati Matarsa daya Hajiya Maryam, wadda ake Kira da Hajiya, tana business dinta a gida, tana Saida kayan mata irin su less da shadda da atamfofi, idan mutum yatashi Aure kawai waya za'a yi mata tahada kayan lefe saidai kawai katura mata da kudin ta account Yawan sanyin halin ta da haba haba datake da jama'ah yasa mutane dayawa suka Santa Kowa kataba Hajiya Maryam hajiya Maryam Sai Maryam din tabuya, kowa yake kiranta da Hajiya Hatta da yaran gidan Hajiya suke kiranta, Alhaji Abubakar da kansa Shima Hajiya yake Cewa Ita Ana kiranta da Hajiya, shikuma suke kiransa da Alhaji, wani lokacin suce Alhaji wataran Kuma suce Abba, Amma alhajin yafi yawa Yanada zafi, musanman Akan iyalansa, shi mutum ne Mai magana daya, idan yayita tota zauna agidansa, zaiyi wahala yayi Maka magana biyu Kowa na gidan shakkarsa yake, more especially yayansa Lokaci dadama saide yaran suyiwa Hajiya magana Akan su tunkareshi da magana, saide suce Hajiya kifadawa Alhaji Abu kaza Taurin Kai Gare shi Kamar mutanan farko Mutum ne Mai aqida daya Dansa na farko shine Imran, cikakken saura yi Mai aji dakuma qwalisa Baida Yawan magana sosai, idan kaga yana zuba surutu tofa saide da Yan gidansu ne Yana 33 years yanzu,yayi karatunsa na bangaren lauya degree da masters yanzu yana aiki A hight court dake Garin kano Sai Farhan dayake 23 year's Yagama degree na farko ajami'ar ghanah Saikuma yar auta wato zainab Hajiya Maryam tanada yar'uwa guda daya, wadda suka tashi tare Kamar wasu Yan biyu sunanta ZAINAB hawaye bilkisu dake bada labari ta share, sannan taci gaba dacewa,wannan ZAINAB din itace mahaifiyarmu Nida Yaya Iman, agarin katsina aka haifemu, Bayan mun girma munyi wayo, Allah yahada mahaifiyarmu da cutar asma, Bata dauki tsawon lokaci ba, tana Fama da wannan jinyar Allah yayi Mata rasuwa Awajan mahaifinmu mukaci gaba da zama, dagamu saishi a gida, yau muci me dadi gobe muci akasin haka, kasancewarsa talaka Ganin dagamu saishi a gida ne yasa mutane suka fara surutu Akan ya ajiye mu a gida shibai nemi mace ya aura ba,da wannan damar Hajiya tayi amfani wajan nunawa baba tanason riqonmu yadawo hannunta Bamusan dalili ba haka baba yaqi yarda, agabanmu Hajiya take zarya tsakanin kano da katsina, Akan baba yabata mu Amma yaqi, daqyar ya yarda yabata Yaya Iman, nikuma na zauna ahannunsa, Kuma Har gobe Bamusan dalilin dayasa baba baya Shiri da yan'gidan Hajiya ba, kwata Kwata bayaso yaga mun rabi Hajiya, gashi Kuma itace kadai muka sani wadda zamu Kallah amatsayin mahaifiyarmu Zamana da baba mu biyu a gida ne yasa baba ya auri wata yarinya Mai hankali nuriyya, muna kiranta da anty Yanzu haka yaranta biyu tareda baba, mace da namiji Riqon Yaya Iman yana dawowa hannun Hajiya komai yasauya Sai abinda Iman takeso akeyi agidan, ke Hatta abinci sai wanda Yaya Iman takeso akeyi agidan Tasamu kulawa sosai, Baga Alhaji ba, Baga Hajiya ba Saikuma Barrister daya dauki son Dunia yadora mata Tunda tazo gidan, ya wayar mata dakai, kasancewarsa mutum wayaiye, duk wani abin gayu na qawata mace budurwa Imran yayiwa Yaya Iman shi Shine yakoya mata Yanda zata soshi tun Bamusan kanmu ba, Haka Hajiya Bata taba nuna mana wani banbanci ba tsakaninmu da yaranta Idan ta nuna ma to mu taso Akan yaranta Kuma Har gobe idan kikaje gidan Hajiya idan ba fada Miki akayiba, bazakice ba itace ta haifemu ba Umma kawai haifarmu tayi da renonmu nadan wani lokaci, Amma Hajiya itace komai namu Duk zafin Alhaji, shi da kansa yana son Yaya Iman, domin kuwa da kansa yasai mata Mota, wadda muke yawanmu aciki, muje duk inda ranmu keso Yusy ta duba sannan tace Kuma ahakan idan ban Kira Yaya Iman da butulu ba, da wannne Suna kikeso na kirata saboda tana nema taqi jinin Hajiya? Sake duban Iman tayi sannan tace da kinqi da kinso Yaya Imran jinin Hajiya ne Kuma shi muka sani bawani bare ba, Dan haka shi Zaki aura Cikin fada tace wallahi bilkisu idan bakimin Shiru ba zan sabar Miki anan wajan Itama cikin Haushi tace a a to Yaya Iman saboda me bazan fadi gaskyaba Dakeda yusy Yanda kukaje kuka qullah haka zakuje ku warware Baqin ciki ne yakama Iman, cikin kuka tace to Wai Dan Allah Nina dorawa kaina sonsa ne? Nimafa haka naji, shikkenan Zaki zauna kinamin rashin kunya, Wai harda Cewa haduwar network Shiru bilkisu tayi tana kallan yar'uwar Tata da karfin Hali Tace ikon Allah, to Yaya Iman ba haduwar network din bane? Qarya nayi? Itama cikin kuka tace Ko haduwar iska ne ahakan Yamin, Kuma inasonsa, bazan Dena sonsa ba, inyaso Haushi yakashe ki Abin natama saiya Bawa Billy Daria, Dan haka batace mata komai ba, tayi Daria kawai ta kwanta, tareda juya musu baya Sai asannan yusra tasaki nannauyar Ajiyar zuciya, tace Gaskiya Teemah al'amarin Nan ba Dan qarami bane, ni inda nasan tun farko haka kuke da barrister gaskiya da bazan baki damar kallan namiji Bama bare ince ki saurareshi Kanta ta Jijjiga cikeda gamsuwa sannan taci gaba da Cewa Barrister mutum ne Teemah Dole ki Rabu da Ali Sa'ad Cikeda masifa ta Daga Kai ta kalli yusra tace dallah malama Niki kyaleni, duk ba kece kika sani kulashiba, Kuma yanzu zakice narabu dashi, anqi arabu dashi din, banzaye kawai Tatashi fuuuuuu tayi waje Billy najinsu tana ta Daria qasa qasa, ita kadai *** *** *** Kinsan me? Teddyn dake gefen gadon ta taja ta rungume sannan tace "um um saika fada" Inaso ne kibani dama nazo Ghana naganki, but da sharadin saina gama da wannan seminar din Cikin shauqi da Jin dadi tace kabari saina koma Nigeria saikazo, saboda yanzu semester dinmu yayi Nisa Shima cikin wani irin shauqi yace kin amince Bayan kin koma Nigeria nataho Nida mamy nah duka muzo gidanku? Batare da tantamaba tace why not (nikwa nace jama'ah a wanne gidan πŸ€”πŸ€”)?? Zara zaran gashin idanunsa ya Lumshe cikin Jin dadin Yanda yasamu karbuwa awajan ta, yasan Cewa Zuwa wannan lokacin idan baiyi fatali da kowanne namiji acikin ranta ba Toya kusa Domin tabbatar da Hakan saiyace Ina samari? Zuwa wannan lokacin babu kowanne irin tsoro acikin Zuciyar Iman, Yanda take jinsa acikin ranta gani take bazata Iya boye masa komai daya shafeta ba Dan haka tace, samari Suna Nan kalau Cikin taqaicaccan Murmushi yace, wato ban koresu ba Kenan duk Suna Nan Kamar da Wannan karfin halin nasa yana birgeta, yanada iko Kamar wata Matarsa Tace, kayi nasarar korar kowa but banda mutum daya Cikin mamaki yace waye Hakan? Kai tsaye tace MURADINA mamaki ne yakamashi yace shikuma hakane sunansa? Idanunta alumshe tace bahaka sunansa ba, kawai de munhana Juna fadar sunanmu ne, saide wannan sunan Cikin dakiya yace Zanso kituromin pic din wannan muradin naki naganshi Kai tsaye tace OK, tareda kashe wayar Zuwa tayi tatura masa ta whatspp, already yana online Dan haka Nan take ta tura masa pic din Barrister Imran Akwance yake agado, Amma Baisan lokacin daya tashi zaune ba, gabansa ne yake wata irin faduwa, hannunsa ma kansa rawa yake Kamar bazai Iya riqe wayar ba Komawa yayi yakirata, Zuciyar ta daya tadaga tace kaganshi? "naganshi, Amma kin tabbatar wannan gayen dakika turomin pic dinsa shine Saurayinki? Babu tunanin komai tace "yes shine MURADINA" Idanunsa ne suka kada sukai jajir lokaci daya, Bai nuna mata komai ba yace mata to shikkenan zan Dan kwanta sai anjima Wayar ta takallah afili tace to lafiya irin wannan sallamar? Kafada ta Daga taci gaba da sabgar gabanta Wayar hannunsa ya wullar gefe daya, kadan yarage wayar ta Fado Daga Kan gadon dayake Kai Lallausar sumar kansa ya hargitsa, Nan take yafara maimaita kalmar innalillahi wa inna ilaihirraji'un Adede wannan lokacin mamy tashigo dakin nasa, ganin yau tajishi Shiru Bai shigo wajantaba Hankalinta atashe taqarasa wajansa tace baby me yake damunka? Be Iya Bata amsaba, saide wayarsa daya nuna mata Wayar ta dauka taduba, photon data gani a screen din wayar Bai tsoratata ba, tasake dubansa tace menene Wai Kansa ya dafe da hannunsa duka biyu, idanunsa jajir yace Mamy....Shine....shine saurayin Iman Da tsananin mamaki tace Iman Kuma? Waye yafada ma Hakan? Hawaye ne suka cika idanunsa, yace Mamy yanzu take fadamin Imran saurayinta ne Yana gama fada mata hawaye suka sauko a idanunsa Sai yau Mamy ta tabbatar dacewa ba qaramin so Haidar yake yiwa yarinyar nanba, kuka! Yau Haidar dinta ne da kuka Akan mace Ajiyar zuciya tasauke, Amma abin yabata mamaki, gudun kada yagane halin datake ciki, saita dake tace ALIYU dausari yadago manyan idanunsa ya kalleta, yau ba baby, ba Haidar, Kai tsaye Aliyu Be Iya Bata amsaba, saide kallanta dayake Tace Aliyu amatsayina na mahaifiyarka, Ina baka umarnin karabu da yarinyar Nan " (tofa wata sabuwa, Nima nace Ko meyasa? 😏😏) Sharhi Sharhi Sharhi please Mrs Usman Ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 10 Saida ya goge hawayen idonsa sannan yace but mamy... Cikin sauri ta dakatar dashi, "dakata Aliyu, sokake nabaka goyon baya Akan Kaci gaba da neman yarinyar da Imran yake so? Kafi kowa sanin Yanda nakeso kayi Aure, Amma Hakan bazaisa na amince kaso abinda Imran yake soba, kayi Hakuri, Allah ya musanya ma da mafi alkhairi Cikin dakiya yace "to shikkenan mamy," "yauwa Allah yayi Maka albarka "Tana gama fadar haka tatashi tabar dakin Shima miqewa yayi Ahankali yashige toilet *** *** *** Computer ce agabansa yana aikin wasu takardu, sau biyu yanayin mistek awaje daban daban Tsaki yasaki yature computer Daga gabansa, meyasa komai zaiyi saiya tunata? Dole ne yabi umarnin mahaifiyarsa kodan yagama da Dunia lafiya, yayi kokarin Raba kansa da tunaninta Amma yakasa jurewa Idan ya kwanta bacci yayi mafarkinta, ido Bude yayita aikin tunaninta Yarasa Yaya zaiyi da ransa, saboda ya nisanta kansa agareta yasa yau kusan 1week Kenan Bai sake neman ta ba, Amma abin yaqi dadi Yana wannan tunanin musty yashigo gidan, afalo yasameshi, Bayan sun gaisa yace banga su mamy ba kobasa Nan ne? Ahankali Kamar wani marar lafiya yace "sun fita sunje shopping" Computer yaturawa musty, ka qarasa wannan aikin, bazan iyaba Da mamaki Mustapha ya kalleshi yace meyasa? Meyake damunkane? Batare daya kalleshi ba yace "Fatima, girlfriend din Barrister Imran ce" Arazane Mustapha ya dubeshi yace tayaya? Kasan me kake fada kuwa? Kansa ya girgiza yace itace ta sanar Dani Hakan da kanta, nafadawa mamy komai tace tabani umarnin narabu da ita Jikin musty yayi sanyi Kafin yayi magana Aliyu yace Bama wannan ne damuwar ba, Yanda na dauketa nasata araina shine damuwar, yanzu haka nakasa Dena tunaninta, wannan aikin tun safe nake Abu daya, Amma nakasa qarasawa sai mistek nake, Kuma tunaninta ne ya haifar min da Hakan Ajiyar zuciya yasauke yace, kayi hakuri abokina, maganar mamy itace ta gaskiya, bazai iyu ba Hakan, Allah yasa hakane yafi alkhairi, Amma kayi kokarin rage tunanin kada Hakan yataba lafiyarka Insha Allah zan kiyaye musty *** *** *** Next day Tun Daga wannan lokacin Aliyu yahana Kansa neman Iman, duk da yanasan Hakan, wannan satin dayan dayayi Batare daya nemetaba jiyake Kamar Akan qaya yake, yasha gwada kiranta Amma saiya katse, idan yatuna da umarnin mamy Yanzu ma yana harabar gidan yana motsa jiki abinda yazame masa qa'ida duk safiya kokuma da yamma sai yayi Tunanin ta yake, wannan jaraba ta isheshi Dan haka ya yanke wa kansa hukuncin kiranta Yana Kira cikin sauri ta Daga, atare sukai Ajiyar zuciya, "yanmatana ya kike? " Cikin shagwaba tace" Bayan ka manta Dani, Baka kirana, gaba daya kazubani a kondon sharah Waneni na manta dake, ai Har abada bazan Iya mantawa dakeba Taji dadin wannan maganar tasa Tace "to meyasa Baka kirana? Qanwata kawai ayyukane sukamin yawa, kinsan mu Bama zama, yau mune can gobe mune can Qanwata? Ta maimaita kalmar acikin ranta, yau Aliyu ne yake kiranta da Qanwata? Tunanin ta baikai wani wajenba tace to shikkenan Allah ya temaka Toki kulamin da kanki, saimun sake magana latter, Dahaka sukai sallama *** *** *** Yaya Iman, yakamata ki rage wannan tunanin fa, kema kinsan semester mu tayi Nisa, Gara muyi karatu, Amma wannan tunanin babu inda zai kaiki "Nima ai bani nadorawa kaina tunanin ba, kema kanki kinsan da inada damar careshi araina da tuninayi, Amma yariga daya shiga Raina, dole Hakan zan barshi "to Yaya Iman, kibarshi aranki, Tunda Kinga Zaki iyada iyayenmu ai shikkenan, Tunda haka kika zabawa kanki " Itama Iman cikin dakiya tace" haka nazaba, Kuma haka zanci gaba, sannan Kuma kitashi kibarmin wajan Nan kafin naci Miki mutunci "a a Yaya Iman, abin baikai nanba, Billy tasa hannu tadauki handout dinta, tadubi yar'uwar tace Toni nayi library "Daga Nan Bayan kin gama karatun ki hada harda takardar ki cinye " Cewar Iman Daria ce takesan qwacewa Billy Saida danne tareda ficewa Daga dakin Tana ganin fitar Billy, tayi wulli da fillos din dake Kan gadon nata, wannan jaraba Dame tayi kama? Iman meya kaiki kula wannan bawan Allah? Yanzu gashinan saboda Bai nemekiba kina Fama da tunaninsa Haka taita magana ita kadai Kamar marar lafiya Batasan Cewa Shima awajansa hakane ba, kawai yana daurewa ne domin yin biyaiya ga mamynsa *** *** *** Nifa abokina banga amfanin boye matan dakake ba, kawai kafuto fili kafada mata gaskiya, rashin baiyana gaskiyarka agareta hakanma matsala zai janyo, Tunda kaika fadamin da kanka Cewa tafara qaunarka yarinyar Nan Hakane musty, wallahi idan zan fada mata maganar mamy agareta jinake nakasa, Har yanzu gani nake Kamar zan Aure ta Murmushi musty yayi, yace hakane Matar mutum kabarinsa, Amma inaso a duk lokacin daka tuna da ita, toka tunada barrister Imran Hakane musty insha Allah zan fada mata, muyi hakuri, Dan ba ita kadai ce zatayi hakuri ba, dukanmu ne Daria Mustapha yayi sannan yace yauwa kokaifa,yanzu zanje inci gaba da aikin daka bani, yayi masa sallama yatafi Musty na tafiya, yadauko wayarsa yakirata, a lokacin tana zaune ita kadai adaki, computer ce agefenta tana kallo Yusy da Billy sun fita kasuwa domin yi musu cefane Tana kallan Kiran nasa taqi dagawa Wai irin Jan ajinnan, afili tace wato sai yau kayi niyyar kira Tana gama yin mitar Tata, tadaga Kiran nasa saura kadan Kiran ya katse Abinda tafara Cewa shine, haba Sojana kasan Yanda nake jiran kiranka kuwa? Bakasan ahalin danake cikiba adalilin rashin kiranka Ko? Pls kadena, zuciya ta bazata Iya jurar hakanba Banasan na dameka da kira saboda nasan Cewa kana wajan seminar, Amma badan hakaba saika gaji da ganin kirana Idanunsa ne sukai jajir, akwai matsala Kenan, inde Itama tanajin irin abinda yakeji, Bayan Kuma dole su Rabu kodan barrister Imran To yanzu shida yakirata domin yayi Mata zancen rabuwa, Yaya zaiyi yasanar mata? Wata Zuciyar ce tace Aliyu kadaure, kadaure Aliyu Haka cikin sanyin jiki yace da ita "kiyi hakuri, akwai dalilin dayasa Bana nemanki, Abaya nasa araina Cewa zan Aure ki, Amma yanzu babu Hakan araina, nayi kokari nacire soyaiyarki Daga cikin zuciya ta, kema Ina fatan Hakan Daga gareki Iman, wannan gayen dakika nunamin amatsayin saurayinki, inasonsa fiye da kaina, Ina sonsa fiye da ke, bazan Iya qwace masa abinda yake soba, kiyi hakuri idan nabaka Miki rai ataraiyyata dake Tun kafin yagama magana hawaye ya wanke mata fuska, cikin kuka tace Amma Ina sonka Aliyu Kirjinsa ya danne dayakejin Kamar Ana zuba masa barkono aciki, cikin dauriya yace kiyi Hakuri Fatima, sannan yakashe wayar Yana Kashe wayar, ya zauna awajan, zazzafan zazzabi yana neman rufeshi Wayar dake hannunta tasaki, Nan take wayar tafadi qasa Har screen guard dinta yafashe, kanta tadora Akan gwiwarta tasaki wani irin kuka Wallahi Yanda take jinsa aranta, Ko Yaya Imran batajin Hakan akansa, to waye shidin? Meya hadashi da Yaya Imran da zaice yafi sonsa akanta? Tana wannan kukan suka shigo cikin dakin kowacce da Kaya ahannunta niqi niqi Gabon Billy ne yafadi, Don tayi zatan kowanine ya mutu a gida Ledar hannunta ta zubar taqarasa wajanta da gudu tace Yaya Iman lafiya? Menene yake faruwa a gida? Banza tayi mata, Ko dago kanta batayiba Yusy ce tazauna jikinta asanyaye tace, Besty Meyake faruwa Dan Allah? Sai a sannan tadago da kanta idanunta jajir da kuka tace, Baya sona, Wai baya sona, bazai Iya Aure naba, Aliyu baya sona " Ajiyar zuciya Billy tasauke tace alhamdulillah, wallahi ni jinake ma wanine ya mutu a gida Cikin kuka Iman tace Yanda nake jinsa araina, Har Gara wani Abu yasameni Akan narasashi Me Billy zatayi inba Daria ba, wayyo Allah Yaya Iman, yanzu duk wannan haqilon dakike akansa, da wannan gayu irin naki, shine yace baya sonki? Wayyo Allah cikina, Kai wannan Abu Yamin dadi wallahi, soja soja, Yaya Iman ta sojanta Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 11 Batare da tacewa yar'uwar Tata komai ba Akan dariyar datake mata tajuya baya tareda kwanciya Ba'a dauki tsawon lokaci ba zazzabi Yarufeta Yusy ta kalli bilkisu tace dr. Kinga muna ta neman mafitar Yanda zamu Rabu da wannan gayen gashinan shida kansa ma yabamu hakuri "hmm damafa rikici ne irin na Yaya Iman, inba hakaba mutimin Nan baki sanshi ba, ba ganinsa kikai azahiri ba, kawai magana ta chatting shikkenan Har kije kidorawa kanki damuwa akansa? Cewar Billy Yusy tace aikinsan Zuciyar mata daban take data maza, inda munsan za'a yi hakanma Ina ita Ina sauraron shi Hakane Kam, to Allah yaqara kiyayewa de Amin "inji yusy Tashi sukai suka tafi kitchen domin yin girki Iman kuwa Daga wannan kwanciyar batama San inda kanta yakeba, zazzabi yayi Mata mugun kamu Saida suka gama hada komai, zasuci abincin yusy tace Teemah taso muci abinci, taji Shiru Besty na, kohar yanzu fishin ake damu ne? Nanma taji Shiru, Dan haka tatashi taje takama hannunta zata jata" Jitayi jikinta zafi rau, tace subhanallah, da karfi tace Besty!! Billy tataso dasauri tace Yaya Iman menene? Tana tambayar tana tattaba jikin Iman din Innalillahi Yaya Iman ai zazzabi ne yakamaki, Daga nanfa jikin Billy yayi sanyi Lalle wannan al'amarin na Yaya Iman ba qarami bane, ita wannan Aliyun Allah yasa de ba aljani bane yar'uwar ta tayi Gamo dashi Yanzu gashi memakon su qureshi Kamar Yanda suka fada su ya quresu Kamata sukai, suka tafi clinic, abincin da basu ciba Kenan *** *** *** Awajan daya ke motsa jikin anan ya zauna, dafe kansa yayi dayake ji Kamar zai Rabe gida biyu Ya tsani kukan mace, Kuma dagaji yasan Cewa kuka take yakashe wayar Nan, yau Wai shine fatimansa take kuka bashida damar dazai rarrasheta Dan qaramin towel yaja yagoge face dinsa, sannan yajuya yanufi dakinsa Ruwa ya watsa yafuto, Daga shi sai singlet da gajeren wando yafada Kan gado ya kwanta, kansa nayi masa mugun ciwo *** *** *** Tun Daga wannan Rana Iman tashiga damuwa, tun Billy najin Haushi harta dawo tana tausayin yayar Tata Sonsa yana Nan daram acikin ranta, Har Zuwa yanzu dayace baya Santa bataji kaunarsa taragu ba acikin ranta Sunata shirin rubuta exam dinsu na qarshe, haka Billy da yusy suka dage Akan Iman wajan Bata shawarwari masu kyau, to shine ma ta kwantar da hankalinta take karatun exam din Yauma Suna dakin Dukansu Suna fira, wayarta ce ahannunta, ba komai take ganiba sai pictures dinsa Bilkisu ta kalleta tace Yaya Iman kirage tunanin nanfa, Itama kallan bilkinsun tayi sannan tace keba tunani bakeba, kawai pic din Aliyu nake gani Hannu Billy ta miqa mata tace muga pic din Aliyun naki yau de Yaya Iman Babu musu tamiqa mata wayar, Billy na karba tace wow yayi kyau gaskiya Dadi yakama Iman, sosai, Har Billy ta lura da Hakan, Dan ta qara kwantarwa da yar'uwar ta hankali saitace gayen yahadu sosai, baida makusa, sai waje daya tak Da mamaki Iman ta kalleta tace Ina Kenan? Billy tace makusarsa daya awajena shine dayace yadena son Yaya Iman dina Dukansu sukasa Daria, Iman tace emana, waishi banza, ai yaban Haushi wallahi, Wayar ta karba awajan Billy ta kalli pic din Nasa sannan taci gaba da Cewa Kaiko hmm saina Rama abinda Kamin wallahi Dukansu kallanta suke Kamar wata me aljannu inba aljannu ba Ina zata ganshi ma bare Har aje ga ramuwa Ammafa Yaya Imran yafishi doguwan fuska, Kuma Daga gani ma Yaya Imran dinmu zai fishi fara'ah Ko a photo Zaki Gane haka Cewar Billy Iman tace ni Bilkisu Ko Imran dinnan zan barmiki ne? Kinwani dameni Yaya Imran Yaya Imran ha'a Sakare Bilkisu tayi tana kallanta tace ke kanki kinsan da ace banda Haroon babu abinda zai hanani Aurensa Tunda ke gudunsa kike Ni inada halacci bazan Iya Qin jinin Hajiya ba Cikin masifa ta hayaiyaqo tace to saiki fadamin waye yake Qin jinin hajiyan? Gashi kuwa kinason wani bare, kinqi dan'uwanki Inji Bilkisu Daga kwanciyar datake tatashi zaune, tace to Wai in tambayeki Bilkisu, jinake da din ninace Ina Sonsa, Kuma na dawo nace banaso Cikin Daria Bilkisu tace ai bazaki birgeniba Yaya Iman saikin kalli idan Yaya Imran kince Bana sanka Imran Cikin bacin rai tace Wallahi zan Iya Bata Miki rai yanzu Bilkisu, kinfa rainani, kin kaini bango Kunnanta takama tace sorry Yaya Iman, Ala barmana ke Kude Allah ya shiryeku wallahi, adinga maimaita magana dayade, Tunda yanzu komai ya wuce ba shikkenan sai ayi hakuri ba Iman tace ai ita Naga farin ciki take da rabuwar Tamu, namutu konai rai babu ruwanta Jin furucin Iman yasa jikin Billy yayi sanyi, tace kiyi Hakuri Yaya Iman, insha Allah ma bazaki mutu ki barni ba *** *** *** One week later Waya take da qawarta Daga Nigeria, tana lura da yanayinsa, Tunda yazauna yake juya tea din dake gabansa Tagama lura dashima kwata Kwata tunaninsa baya wajan Miqawa yayi, yayi cikin dakinsa, atika dake zaune tana kallo tabishi da kallo, a ranta tace yau Kuma waya taba babyn mamy Yana Zuwa daki, yafada Kan gado tareda jawo blanket Yarufe duka jikinsa dashi Zazzabi yakeji da ciwon Kai sosai, Kuma bayasan ya kwanta mamy tagane, Gara yadawo daki may be idan yahuta zaiji normal Tana gama wayar datake ta miqe, Bata zarce ko'inaba sai dakinsa Dasauri ta qarasa Kan gadon, bargon daya rufa dashi ta janye, wani irin zafi ne ya bigeta Tace subhanallah baby, zazzabi ne ajikinka Amma bazaka Iya fadamin Akira doctor ba Narasa Gane wanne irin miskilin mutum ne Kai wani lokacin wallahi Cikin runtse ido, yadafe kansa dake masa ciwo yace mamy..... Kaina... Ciwo mamy Janyoshi tayi jikinta tana Jijjiga jikinsa tace sannu baby, yi hakuri Bari nakira Mustapha Yazo da likita ya dubaka Wayarsa ta dauka tanemi musty, tana shiga tasanar dashi halin da ake ciki Tareda doctor suka dawo, doctor na ganin situation din dayake ciki, yace dole suje asbiti domin ayi masa Dan gwaje gwaje Mustapha ne yakamashi, suka fita, sai sojoji guda uku dasuke take musu baya, Suna Zuwa asbiti aka bashi gado, likita yayi gwaje gwajensa yadawo Ya samu mamy da Mustapha yace Hajiya gaskiya yakama ta adinga kula dashi sosai, saboda yasa damuwa aransa, tunani yayi masa yawa Gashi yanzu Hakan harda haifar masa da Hawan jini Mamy da Mustapha ne suka hada baki wajan fadin Hawan jini doctor (kuyi hakuri da wannan nayi busy ne,πŸ˜’) (Daga yau nadena posting WAZAN ZABA a Facebook, duk me buqata Iya mata, ta turomin number dinta zan sakata a group na whatspp, wannan group din saboda sharhi na budeshi, please idan kinsan bazakiyi magana a karki turomin phone number naki, Iya mata plsπŸ™πŸ™ Mrs Usman Ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 12 Sosai makuwa hajiya, hawan jini yayi masa mugun kamu, yakamata adena barinsa shi kadai, yana kebewa bare Har Hakan ya haifar masa da damuwa Duk wata kulawa zan dinga Zuwa Har gida Ina bashi, idan time din shan maganinsa yayi zanzo nabashi, ki kwantar da hankalinki insha Allah inde kunyi amfani da shawarar Dana Baku, zai warware Kamar da Cikeda damuwa mamy tace to shikkenan likita mungode Tashi tayi takoma dakin da Aliyu yake, bacci yake, harma ruwan da aka daura masa yakusa qarewa Agefen gadon dayake ta zauna, tazuba uban tagumi tana kallansa Cikin sanyin jiki Mustapha yashigo dakin, yana kallan mamy yaji duk tabashi tausayi, gaba daya hankalinta atashe yake, Ahankali yaqaraso cikin dakin, yazauna akujera ya fuskanci mamy sannan yace mamy kiyi hakuri, ki kwantar da hankalinki insha Allah zai samu sauqi Kamar zatayi kuka tace ta Yaya zan kwantar da hankalina Mustapha, Aliyu shi kadai gareni, shi nake kalla inji dadi, yau gashi akwance asanadin soyaiya, ni DANA SANI ban matsa masa Akan yasamo yarinyar dazai auraba, da duk haka Bata faruba A a mamy kidena fadar haka, Aure ai dole zaiyi Aure dama, Kuma dakin yi masa magana da bakiyiba dole Tunda Allah yatsara Hakan, to dole zai gamu da abin Wannan Karon mamy hawaye ne suka zubo mata, tasa hannu ta share, tace Mustapha idan ban Hana Aliyu yadena kula yarinyar nanba, nan gaba idan magana tayi Nisa kunya zamuji Kai kanka kasan komai Jijjiga kansa yayi Cikeda gamsuwa yace hakane mamy, Allah de yabashi lafiya Bata Iya Cewa komai ba, sai sharar hawaye datake *** *** *** Kwanansa daya suka sallameshi yakoma gida, saide doctor yana Zuwa gida yana duba shi akai akai, Kamar Yanda yace Mamy tayi masa fada sosai Akan rashin lafiyar sa, sannan taqara da nasiha da Kuma lallashin yadena tunanin Iman, ya hakura yacireta aransa Tundaga wannan lokacin, tadena barinsa yazauna shi kadai, bare ma yayi tunani Saide abinda mamy takasa sani shine, yana nuna mata ne ya hakura da Iman, Amma acikin Zuciyar sa, kaunarta sake nunkuwa take, inda ace akwai inda zaije acire masa soyaiyar ta, da tuni yaje, Kodan Imran *** *** *** Wallahi zazzabi nakeji Bilkisu Billy ta kalleta Cikeda da tausayi tace Yaya Iman kisawa Zuciyar Ki salama Akan wannan bawan Allanfa Ke kanki kinsan abinda kika dauko, bamai dorewa bane Ko awajan iyayenmu Sannan Kinga Koda yaushe kina Fama da zazzabi, Ina tsoron Kar wani Abu yasameki Yaya Iman, Hajiya ni zatayiwa fada Cewa ba kula dakeba, Kamar Yanda Kema idan nice Hakan tafaru Dani fada zakisha Kina nan kinata Haqilo akansa, Bama lalle shi yanayi Miki irin wannan soyaiyar ba Cikin yatsina fuska alamar tanajin zazzabin tace Bilkisu yana sona wallahi Kawai de Bansan meyasa yace bazai Iya Aure naba, Kuma Bansan alaqar datake tsakaninsu da Yaya Imran Ba, Amma Ina komawa gida zan tambayeshi naji Karma kifara Hakan Yaya Iman, Kema kinsan dole Yaya Imran zai tambayeki Ina kika hadu dashi,? Kuma kinsan Cewa de Bai baki damar kula kowaba, tun kafin mukai yanzu Toshikkenan na hakura da tambayar nashi, Amma gaskiya inason Aliyu, bazan Iya mantawa dashiba Yayar tata tabata tausayi, Dan haka tace to Yaya Iman Allah yayi mana zabi mafi alkhairi, Tashi Kisha magani, mutafi, kibazaki Iya rubuta exam dinba? Cikin dauria tace zan Iya, muje Tashi sukai, suka tafi, already yusy tatafi, dayake Suna zana exam dinsu na qarshe ne *** *** *** Yana kwance Akan kujera, yadora kansa Akan cinyar mamy Lallausar sumar kansa tasha tace, baby Kamar jikinka akwai zazzabi, Ko de asbitin nan zamu koma ne? Cikin shagwaba yace mamy Allah nawarke fa, kinjifa Yafadi Hakan yanajan hannunta yadora awuyansa Murmushi tayi tace Aliyu Kenan, tasan Cewa kawai yafadane, Amma yanajin jiki, yade boye mata ne gudun kada tashiga damuwa Waya tadauka takira doctor tasanar dashi yanayin jikin na Aliyu, babu dadewa Yazo Har gidan Yana gama aunashi yadago kansa Cikeda damuwa yace Hajiya, Har yanzu fa BP yana nan Yanda yake, dole saikin sake dagewa Akan rashin lafiyar Yaron ki Mamy Kasa magana tayi, haka doctor yayi masa allurai yatafi Aliyu naji mamy tayi Shiru, yadago da kansa yace mamy ki kwantar da hankalinki..... Bai qarasa magana ba ta dakatar dashi, Zuciyar ta karyewa tayi Saida tafashe da kuka tace dakata Aliyu, sai yaushe ne zaku Dena cemin in kwantar da hankali na? Saika mutu kaima narasaka Kamar daddynka Ko? Tafadi Hakan idanunta jajir Jikinsa ne yayi sanyi, yama Kasa yimata magana, yasan Cewa tabbas yasa mamynsa a damuwa, dole zai San matakin dazai dauka Akan haka Mamy Bata sake ce masa komai ba, tadauki waya takira yayan mijinta Bugu daya aka Daga wayar tata Cikin kuka tace Yaya Ina wuni? "lafiya Fatima, meyake faruwa ne naji kina kuka? Wallahi Yaya Aliyu ne bashi da lafiya, tsawon sati biyu Kenan kullum Bama cikin kwanciyar hankali, yanzu ahalin da ake ciki likita yace yanada hawan jini, dole yarage damuwa Amma Aliyu yaqi Jina, shine nace zan fadama, Saika fada masa da kanka, kozaifi Jin maganar taka Akan tawa Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un yanzu Fatima dannawa ne yake kwance a gadon asbiti babu lafiya, kikasa sanar Dani inzo Inga halin dakuke ciki? Hawaye ta share tace bahaka bane Yaya..... Ya'isa Fatima, waikoke kadai kike da iko Akan Aliyu ne? Cikin girmamawa tace a a Yaya To inbaso kike ki nunamin iko Akan Aliyu ba, nabaku kwana daya ku tattaro yanaku yanaku kudawo gida, Kuma ba Abuja zaku sauka ba anan gida zaku zauna Har sai jikin yarona yayi kyau, yazaki barmin yaro ya lalace da jinya Fatima Mamy tace kayi Hakuri Yaya Cikin fada yace kinji abinda nafada Miki de, yakashe wayar Mamy tagoge hawayen idonta tace basai na maimaita maba, ai kaji abinda yace, Itama tatashi tayi cikin daki Tana tafiya yadafe goshinsa cikeda damuwa, shikkenan Kuma komai ya lalace ai Tunda mamy tafadawa wannan masifaffan, ai dolensa yakoma *** *** *** Yusy kide cika alqawarin dakika dauka, Dan Allah kidaure watarana kizomin katsina, Kinga Yaya Iman kullum Kuna tare akano Karki damu doctor Billy insha Allah zan shigo Miki Farhan dayazo Airport daukarsu yace Dan Allah malamai kushigo mutafi, haba a dinga fira de Iman tace to jarababbe ai Kuma mun dawo saita Allah Yusy ce tayi musu sallama tatafi, yayinda suma suka shiga Mota Farhan yajasu sai gida Suna Zuwa gida Zeey tataho da gudu ta taryesu, Billy tace iyeee mamana fa yanmata take zama Iman tace Kuma tana qara fitsarewa ba Buga kafafunta tafara yi aqasa tace anty Bilkisu kinji ta Ko Kama hannunta Billy tayi tace Rabu da Yaya Iman mamana, nan sukai ciki gaba daya Hajiya bakinta Kamar gonar auduga, yau taga yayanta Saida sukai wanka, sannan suka Suka nufi dinning dukansu domin cin abinci Hajiya tace Bilkisu yaude babu inda Zaki tafi, kibari idan kika huta gobe saiki wuce katsina, kikira babanku kifada masa sai gobe Zaki tafi To Hajiya, zan sanar dashi, inji Bilkisu, cikin ranta tana adduah, Allah yasa Kar yayi Mata fadan daya saba Iman ce ta kalli ko'ina Bata ganshi ba, tajuya de taga babu wanda yake da niyyar yi mata zancensa Ta dubi Farhan zatai magana ya katseta Muradin ki kike nema, baya nan yatafi Abuja, sai gobe zai dawo Gaba dayansu sukasa Daria harda Hajiya da kanta *** *** *** Suna idar da sallar asuba Hajiya taje dakin nasu tace toyau babu komawa bacci, munada baqi, atashi ashiga kitchen Dukansu suka hadu a kitchen din, Iman tafi kowa dagewa wajan girki, Jin Hajiya tace Yaya Imran yana hanya Bilkisu aranta tace oh Yaya Iman Kamar ba itace take Cewa Bata sonsa ba Abinci suka hada Mai rai da lafiya, aka jera komai a dinning Hajiya suka Bari suka koma daki, Bilkisu tafada Kan gado tace Kai wallahi saina huta zan shiga wanka, nagaji Iman ma tace ai in kika ce hutu dayama Kenan, Itama zama tayi tana daddana waya, fira suke gwanin sha'awa abinsu Iman wata yar qaramar Riga ce ajikinta, takama jikinta rigar, na shanun nan gasu nan atsaye, sai sket din jeans Bilkisu Kuma doguwar Riga ce ajikin ta, Amma roba ce rigar, hips dinnan ya baiyyana muraran Hon sukaji anyi da karfi,atare suka ce Kai waye wannan Billy tace Bari muga Ko Yaya Imran ne, Tafadi haka tana Daga labulen window Abinda taganine yasata Cewa la'ila sojoji Yaya Iman Da mamaki Iman tace mun shiga uku mezai hadamu da sojoji, lokaci daya jiniyar motocin suka cika unguwa Billy ce tayi karfin Hali tace zomuje falon, Tafadi Hakan tana Jan hannun Iman Adede lokacin dasu Iman suka futo falon, suma alokacin suka sako kansu cikin falon, mamy ce Akan gaba, sai Aliyu da Imran abayanta Daskarewa Iman tayi atsaye Shima anasa bangaren gabansa ne yayi muguwar faduwa, meya kawo wannan yarinyar gidansu BROS? Billy tana ganinsa taganeshi, ita kanta ta razana da ganinsa Cikin farin ciki hajiya ta karbi handbag Din hannun mamy, tana Cewa Hajiya fati sannunku da Zuwa Tajuya ta kalli su Iman dasukai mutuwar tsaye tace Bilkisu bakwa ganin baqi ne Wai kun tsaya Kuna kallansu kun barsu da Kaya ahannu Billy ce tayi diri diri Tama rasa Yaya zatayi,Daga qarshe de takarbi jakar hannun hajiya Hajiya ta dubi mamy sannan tace Hajiya Fatima wannan fa yaran Zainab ne yar'uwata Mamy tana Kai idonta Kan Iman kallo daya tayi mata taganeta, cikin ranta tace akwai babbar matsala Kenan Amma afili saita saki Murmushi tace masha Allah, waisu ne suka girma haka? Hajiya tace eh wallahi " Sannan ta kalli Iman data tsaya Kamar gunki ta dalla mata harara tace cikin fada, Iman me yake damunki ne kin tsaya Akan mutane kina aikin kallansu Nuna mamy tayi da hannunta tace wannan Matar qanin Alhaji ce daya rasu, wannan na Abujan danake Baku labari Alhaji Sa'ad Sannan ta nuna Aliyu dayayi mutuwar tsaye tace wannan Kuma Haidar ne danta,BROS din Imran Kenan Ahankali Bilkisu tace tab lalle Yaya Iman kina cikin DalalaπŸ€”πŸ€” (tonima de nace Iman tana cikin dalala, kuyi hakuri jiya kinjini shiru wallahi naje unguwa ne, bansamu zama ba,) Wannan page din kukadai naturawa a Facebook saboda qorafin da kukaimin na rashin babbar waya @Maman mamaaa Team din Aliyu Team din barrister Tofa saikunyi hakuri dukanku πŸ˜’πŸ˜’domin kuwa abubuwa da dama zasu faru a wannan Zaman na gida daya Sharhi pls πŸ™πŸ» Mrs Usman ce ✍🏻✍🏻WAZAN ✍🏻✍🏻 ZABA?πŸ’–βœπŸ»βœπŸ» Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 13 Kallan su Aliyun tayi, tasaki yar qaramar dariyar yaqe Ahankali cikin siririyar muryarta tace Sannan ku dazuwa, Kai tsaye Imran ta tunkara zata karbi jakar hannunsa, kashe mata ido daya yayi, sannan cikin kulawa yace no barshi, karbi ta hannun Bros, shine baida lafiya, yana fadar haka yayi ciki Shikuwa gogan nan take yahade rai Kamar an aiko masa da mutuwa, yakoma sojansa, Yanda yayi Kamar arayuwarsa Bai taba sanin wata Iman ba Ahankali takai hannunta zata karbi jakar, baiyi mata musu ba yabata,Garin karbar jakar hannunsu yagogi na juna Gaba dayansu wani irin shork ya ziyarcesu, atare suka kalli junansu, saide Yanda taga ya tamke fuska Kamar wani kumurci hakanne yasa cikin sauri tajuya da jakar tayi cikin daki Itama Dukansu Suka baje a luntsuma luntsuman kujerun falon Mamy tacire mayafinta tace Kai tafiya yankin azaba Wallahi nagaji Hajiya tace ai dole ku gaji hajiya Fatima, tundaga Abuja amota, meyasa Baku biyo jirgi bane? Nuna Aliyu tayi tace rigimar danki mana, Wai akwai mutanan dazai gani a Abuja domin ya turasu Switzerland su wakilceshi, Akan qarasa seminar dayaje Tokuma daya gama memakon mu biyo jirgin shine yace mutafi amota, yaga gari Hajiya tace ashe sun gama qulla abin su shiyasa jiya Imran yacemin shikam yatafi Abuja, bazai Iya jira harku zoba, shi Tunda aka fada masa rashin lafiyar Aliyu shikkenan yadaga hankalinsa da gashi Har Alhaji Duban Aliyun hajiya tayi sannan taci gaba da Cewa Aliyu yajikin Naka? Saida yashafa sumar kansa sannan yace cikin Murmushi Dasauqi hajiya, dafatan mun sameku lafiya Cikin farin ciki tace Lafiya kalau Aliyu Iman Da Billy kuwa Suna cikin daki Yanda kasan munafukai sunqi futowa falon Alhaji ne yashigo gidan, mutum Mai dattako da riqaqqen Hali, fuskarsa babu alamar wasa yaqaraso cikin falon Mamy cikin girmamawa tace Yaya sannu da Zuwa, ya gida? Adake yace "lafiya Fatima, yame jikin Kuma?" Kanta aqasa batare data kalleshi ba cikin ban girma tace Jiki da sauqi Yaya Yana zama acikin kujerun ya amsa mata da Allah yaqara afwa Zamansa Akan kujerar yayi daidai da saukar Imran da Aliyu qasa Atare suka ce Alhaji Ina wuni? Bai amsa musu gaisuwar ba, saima tambaya daya jefowa Aliyu yasauqin jikin Naka? Kansa aqasa Cikeda girmamawa yace Alhmdlh Alhaji, jiki yayi sauqi Shima cikin iko yace, ban gamsu da wannan sauqin nakaba, nayi magana da likita zai dinga Zuwa dubaka duk Bayan kwana biyu, idan kagama warwarewa saika koma bakin aikinka Cikin ransa yace Innalillahi.... Ai kuwa zamana acikin gidan nan babu abinda zai sauya saima qaruwa da rashin lafiyar tawa zatayi Amma afili sai yace To Alhaji Kallan Imran yayi, yace kadena barinsa yana shiga tunani shi kadai, gaba dayanku Bana San abinda zai haifar muku da damuwa Shima Imran din cikin nutsuwa da girmamawa yace to Alhaji, insha Allah Anan qasan sukaci gaba da zama, hajiya tace aida Zuwa mukai kukaci abinci saikuje kuhuta, Ko kuwa Hajiya fati? Taqarasa zancen da Kallan mamy Mamy tace to hajiya, sannan tayi hanyar dining din Hajiya tabita Abaya Alhaji ne ya kalli su Imran da Aliyu yace Kai kutashi muje kuci abinci Suma sukabi Bayan Alhaji, suka dunguma Zuwa dinning din Alhaji ne yawaiga baiga kowaba yajuya ya kalli hajiya yace Ina yaran nan ne? ''autata tana school, Farhan yafice yawonsa, saide su Iman Suna cikin daki Babu wasa a fuskarsa yace Tome suke jira su bazasu futo suci abinci ba? Murya ta Daga tace Bilkisu kuzo nan Daga nesan Billy tace to hajiya Miqewa tayi zata fice Iman ta riqeta, da mamaki Billy tace menene Yaya Iman? Ni wallahi tsoron fita nake, Dan Allah karmu fita, ni wallahi tsoron sa nake, ni da nasan haka yake tun farko wallahi daban kulashiba, Kinga Yanda ya hade rai Kamar zai rufeni da duka? Daria ce takama Billy tace to yanzu Yaya Iman, Kiran hajiyan zamu qi Zuwa? Keda masoyinki? Kamar zatai kuka tace wallahi tsoron sa nake, Wai dama haka yake afili? Yamin kwarjini Billy, Jikinta ta kalla sannan tace, Toni mema yagani awajena dahar Nakai matsayin da wannan zai furtamin kalmar so? Wallahi ba inda zamu, Kema bazaki fita ba, kibari idan suka gama saimu fita Kafin Billy tayi magana, Suka juyo muryar hajiya tana Cewa Wai me kuke jirane? Ai aguje suka futo falon, Ahanya Billy ta kunce dankwalin kanta tayafa Dan tana kunyar futowa haka, Amma abinda Bata saniba shine, Bai gama rufe mata gashin kantaba, hakade tayo gaba Iman kuwa ahaka tatafi abinta, to waye banqonta aciki? Aliyun Ko Imran? Directly Suma dining din suka nufa, tun kafin su qaraso Imran ya kafe Iman Da kallo Shikuwa gogan Ko dago kansa baiyi ba, bare yasan da halittarsu Kujera sukaja Suma suka zauna, Hajiya ta kalli Iman tace toko nice zanyi sarving dinsu? Batacewa hajiyan komai ba, Ahankali tatashi tsaye tafara zubawa Alhaji tatura masa gabansa, Bai jira komai ba yafara ci Sannan tafara zubawa mamy, Mamy kallanta take, sosai ta Yaba da yarinyar, komai tanayinsa ne anutse, batada makusa Ko kadan Yanzu ZAINAB harta haifi ya Kamar wannan? Kenan de tarihi ne yakeson maimaita kansa (nikwa nace to wanne tarihi Kuma πŸ€”) Tana zuba mata sannan tasawa Hajiya, Bata kalli gwarazan samarin nataba, takai hannu tadau flet din gaban Imran zata saka masa Dasauri ya katseta yace no zubawa Bros tukun, " Miqewa tayi Daga Dan sunkuyawar datayi tana Zuba abincin, Ahankali takai kallanta wajansa Shikuwa Aliyu baima dago kansa ya kalleta ba, yace " no" Shima Imran din yace no Bros tazuba ma tukun Batare dayace komai ba ya girgiza kansa, still Bai dago ya kalleta ba Kafada Imran yadaga yace to shikkenan ai ni dashi duk dayane, abin Bros aina Bros ne, yadubi Iman yace zubamin Alhaji yana jinsu baice musu komai ba, inda Sabo ai yasaba da irin wannan shirman nasu, Wai ai abin wane na wane ne Itama Iman cikin ranta tace Yan renin hankali gaba dayanku, sannan tafara zuba masa Shima Aliyun ta zuba masa, sannan tasaka musu itada Billy Bakajin motsin kowa, sai qaran spoon dakakeji yana tashi Aliyu cikin ransa yace watode wannan gidan Har yanzu Suna nan da dabi'arsu ta idan Alhaji yana wajan cin abinci babu wanda ya Isa yayi magana To yaukam saide ayi hakuri, domin kuwa bazaiqi fadar gaskiya ba Gyaran murya yayi sannan yace Ahankali,"Hajiya girkin ki yayi dadi sosai " Cikin Jin dadi hajiya tace ashe yayima dadi Aliyu, aiba nice nayi ba, ga gwanayen girkin nan, ta nuna masa su Iman Sannan taci gaba da Cewa musanman stew din, Iman Hana kowa tabawa tayi, tace Dakanta zatayi yau Sai a lokacin yadago da manyan idanunsa Zuwa gareta, Idanunsa Basu sauka ako'inaba sai Akan nashanunta Dasauri yajanye idanunsa yakalli qwayar Idonta Adede lokacin Itama ta dago karaf idanunsu suka sarqe Dana Juna Lokaci daya ya tamke fuskarsa, Itama sunkuyar da kanta tayi, taci gaba da cin abincin Billy ce take kallansu, Daria tana kamata Amma Kuma babu damar yi, a ranta tace tab lalle wannan miskili ne dayawa Iman kawai wasa tayi da abincin bawani cin kirki tayiba, tatashi tayi cikin daki, domin kuwa Zaman wajan gaba dayanta gani take kowa yasan abinda yake faruwa Billy na bin Bayan yar'uwar ta tayi, Suna shiga daki, Iman ta zuba tagumi, Billy tadubi Iman tana cire kayanta domin yin wanka, tace ya'akayi ne Yaya Iman? Cikin damuwa tace ya tsaneni Bilkisu Billy tace Hakan shine mafita Yaya Iman, tana fadar Hakan tashige toilet, Saida ta futo sannan Iman ma tashiga tayi wanka Laffaya Bilkisu ta nada, Iman Kuma tasaka doguwar Riga ta atamfa dinkin fitet gown, sai shafaffan cikin ta ya buya aciki, yayinta hips dinta suka cika rigar, dinkin ya karbi Jikinta yayi Mata Dass Wayar Billy ce tayi qara, tana dubawa afili tace babane Iman tace Daga muji menene Billy tana dagawa Bayan sun gaisa, naji tace to baba yanzu kuwa insha Allah, sallama sukai, tajuyo tacewa Iman, baba yace natafi yanzu Cikin damuwa Iman tace wayyo Bilkisu yanzu tafiya zakiyi kibarni cikin wannan rikicin? Cikin tausayawa Billy tace Toya zanyi Yaya Iman kawai sai Iman tasaka kuka, Bilkisu cikin tashin hankali tace Yaya Iman me aka Miki Daga maganar tafiya sai kuka? Cikin kuka Iman tace wallahi bazaki tafi ki Barni dasuba, Billy tace suwa din? Cikin hawaye tace su su Aliyun, Allah ba inda Zaki Suna wannan halin Hajiya tashigo cikin dakin tana Cewa biyoku nayi Naga yaude me kuke yi a daki Kamar wasu baqi... Maganar ta ce ta tsaya ganin Iman na kuka, tace ita Kuma me aka mata take kuka? Billy tace Wai Dan baba Yamin waya yace natafi yanzu, shine take kuka Wai kada natafi Kuka hajiya Nima banasan tafiya wallahi, kawai de danya zama dole ne Jikin hajiya yayi sanyi, gaba daya tausayinsu ya kamata, kafin tace musu komai Iman cikin kuka tace hajiya Dan Allah yau ki fada mana, meyasa baba bayasan mu rabeki? Cikin sanyin jiki hajiya tanemi waje tazauna agefen gadon, Suma binta sukai suka zauna Cikin damuwa hajiya tace Haqiqa yau zan fada muku dalilin dayasa babanku bayasan zamanku ahannuna Nida yar'uwata zainab, mun kasance kyawawa a lokacin damuke yanmata kamarku, basai nafada muku ba kunsan halin duk wani qabilar shuwah basason Auren talakan mutum, to hakane yafaru awjanmu Nida zainab Munzo kano wajan biki nahadu da Alhaji Abubakar mahaifinsu Imran, ban Bata lokaci ba nakulashi, saboda Ina kaunarsa, yan'uwanmu damukazo biki dasu kowa dayaji shiyake sona zai bani goyon baya a kansa saboda shidin mutum ne Mai mugun kudi Soyaiyar mu tayi Nisa harta kaimu gayin Aure, watarana zainab tazo hutu kano gidana, anan qanin Alhaji wato mahaifin Aliyu yanuna yana sonta Yayansa Alhaji wato mijina yatsaya masa yanayin abinda yaso da kudi, gakuma aikin soja dayake, nanma yana samu kasancewarsa babban soja, haka duk yabi yan'uwanmu na maiduguri yake Raba musu kudade, bawai danya siyesuba a a yayi hakanne kawai domin zainab Aikwa nan yan'uwanmu suka ce basusan kowa ba inba Sa'ad ba, shi zata aura, Amma abinda basu saniba shine zainab Bata qaunar ganin Sa'ad, kwata Kwata Bata sonsa Akwai wanda takeso a katsina shu'aib wato mahaifinku Haka akayi akayi zainab ta auri Sa'ad taqi yarda, Daga qarshe mahaifin Aliyu daya gaji da bibiyarta saiya hakura, wataran yaje yola daurin Auren abokinsu yahadu da wata bafulatanar yola ya aura, wato hajiya Fatima, Aliyu yana kiranta da mamy Aurensu shekara daya ta haifi Aliyu, beyo Kamar Alhaji Sa'ad ba, saiyayi Kamar mahaifiyarsa Shekarar Aliyu daya aduniya nahaifi Imran, Imran baiyo kamataba saiyayi kamar Alhaji Yan'uwanmu ganin Alhaji Sa'ad yahakura da zainab harma tahaihu yasa suka tsaneta, komai tayi sai an hantareta, nice na tsaya mata tareda Alhaji iyayenmu suka yarda ta auri mahaifin ku, Saida tadau tsawon lokaci Allah Bai Bata haihuwa ba, saidaga bayane Tahaifi Iman, sannan Bilkisu Haka rayuwa taci gaba da tafiya, Sa'ad yana rayuwa da Matarsa a Abuja, mukuma muna kano, yayinda zainab take katsina Ina qaunar naganku awajena tun Bayan rasuwar zainab, idan na kalleku tunamin kuke da rayuwar da mukai nida ita, Hakan ne yasa Bayan ta rasu, nanemi abani ku kudawo hannu na, da farko mahaifinku yaqi yarda saboda yana ganin Cewa zamanku awajena zaisa kukoyi Hali irinna yan'uwanmu kuqi talaka Kamar Yanda danginmu suka nuna qarara basa kaunarsa da zainab Hajiya ta dubi Bilkisu tace Kuma nasan yahadaki da Haroon ne saboda kada kihadu dawani me kudi anan gidan idan kinzo, shiyasa yayi Miki katanga da duk wani namiji dazai soki a gidan nan Yayarda da soyaiyar Imran da Iman ne saboda Alhaji ne yagoya masa baya Dari bisa Dari Har ya samu auren zainab a lokacin dayake nemanta Wannan alkunyar dayakewa Alhaji ce tasa Itama Iman, baiyi mata miji talakaba Tadubesu sannan tace to kunji Yanda abin yake Billy tasaki Ajiyar zuciya aranta tace Kenan Aliyun ma sun hada dangantaka dashi, hartakewa Yaya Iman tsiya tana San bare bataso dan'uwantaba Iman ce ta iyayin magana tace yanzu hajiya Kenan ahaka za'aci gaba da zama? Shi bazai sauyaba? Hajiya tace kuyiwa mahaifinku Addu'ah wataran zai sauya Miqewa tayi tace Bilkisu Bari nadauko Miki saqo kikai musu, tafice tabarsu a dakin Tana fita, Bilkisu tace tab Yaya Iman kice soyaiyar ki da Aliyu akwai matsala, Kuma kinji dazu hajiya tana Cewa mahaifiyarsa mune yayan zainab, Kenan itama tasan mama Ajiyar zuciya Iman tasaki tace dama dole tasan mama mana, Tunda mijinta yaso maman, ni Bama wannan ba, tsoron haduwa nake dashi wallahi, da'ace kina nan zan danji sanyi Kiyi hakuri Yaya Iman insha Allah zan lallaba baba nadawo, Iman tace kinyi Alqawari? Billy tace nayi Miki Yaya Iman Hajiya ce tashigo da Leda a hannunta tace to gashi Bilkisu kikai musu Kuma kice Ina gaishe su Atare suka futo Daga dakin Dukansu,babu kowa afalon, hajiya Takoma ciki wajan mamy, Iman Kuma tarako Billy harabar gidan Zaratan mazan guda biyu ne kawai atsaye aharabar gidan, Barrister yana waya yajuya bayansa, yayinda Aliyu yake fuskantar kofar shiga falon Dan haka Suna futowa yagansu, a gefe suka tsaya itada Billy, driver ne Yazo da sauri yakarbi babbar ledar hannun Billy Iman tariqeta tana share hawaye tace Billy Dan Allah kidawo da wuri, wallahi ni yanzu shi kansa Yaya Imran dinma kwarjini yakemin bare Kuma wannan miskilin Kafeta yayi da idonsa, fuskarsa atamke cikin ransa yake tambayar kansa meyasa take kuka? Anya kuwa tasan Yanda kukanta yake taba Zuciyar sa!? Abin tausayi Billy ce ta share mata hawayen Kamar itace babbaπŸ˜ƒ Tace karki damu Yaya Iman insha Allah zan dawo Iman nagoge hawaye tayi cikin falon su da gudu Bilkisu najuyawa tafara tafiya wajan driver Taji ance mata "jimana" Juyawar dazatai taganshi atsaye, gaban tane yafadi, kaki ne ajikinsa tunna safe dasukazo, itafa batasan harkar sojojin nan, bare Kuma shi fuska atamke Sharhi please,πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»shike qaramin qaimi wajan sanbado muku typing Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 14 Kasa yi masa magana tayi, gaba daya ta rikice, koshi saida ya lura da Hakan, domin ya kawar da wannan tsoron dayake gani a fuskarta yasa yasaki wani irin tsadaddan Murmushi sannan yace "Ina zakije?" Cikin ranta tace tab, ashe yana Murmushi Ahankali cikin nutsuwa kanta aqasa takasa duban qwayar idonsa tace "zantafi gida ne katsina" Har zai sake tambayar ta meyasa ita bazata zauna anan ba, kawai Kuma sai wani tunani Yazo masa yashare Jijjiga kansa yayi Cikeda gamsuwa yace "ok you can go... Ai tun kafin yaqarasa tajuya tayi gaba, dama tarasa dalilin tambayar Bayanta yabi da kallo, masha Allah dukansu haka suke da baiwa, Amma meyasa yakasa tambayar ta abinda yataso dashi Daga inda yake? Meyasa yakasa tambayar dalilin kukan dayar? Dafashi yaji anyi, yana Juyawa yaga Imran ne, "Bros mekake tunani anan? Kaga muje ciki, domin kuwa kasan bazan yafewa kainaba muddin naganka cikin tunani Shima yace no ba tunani nakeba Bros, kawai de na tambayi wancan yarinyar ne Ina zataje? Sai a lokacin hankalin Imran yakai wajan da motor su Billy tafara tafiya, ta glass din motor yaganta, kawai yadaga mata hannu yana Murmushi, Itama haka Kallan Aliyu yayi yace OK Wai Dr. Billy, may be zata tafi gida ne Cikin zaquwa dason sanin dalili Aliyu yace but meyasa zata tafi? Murmushi Imran yayi yace ai baban su akwai tsauri dayawa, anan yabashi labarin komai, game dasu Aliyu yace to Amma aida anyi masa magana Zaro ido Imran yayi, yace wa? Bros bakasan halin wannan mutumin bane, wallahi gwaska ne Kafada Aliyu yadaga yace ai shikkenan, muje ciki na watsa ruwa na kwanta Part din Imran suka nufa dukansu, Amma Aliyu cikin ransa tunani yake Yanda zaiyi Bilkisu tadawo gidan dazama, Amma yaza'ai tatafi ita Kuma wannan tadinga kuka, ai kawai tayi zamanta, Dan gaskiya bazai juri ganinta tana wannan koke kokenba, yanzu waya sanima Ko Hakan ya haifar mata da ciwon Kai *** *** *** Suna shiga part din yacire kayansa yashige wanka, ya futo daure da towel aqugunsa yayi gaban mirror yana goge jikinsa da wani Dan qaramin towel din Shima Imran wankan yashiga, lokacin daya futo Har Aliyu ya shirya cikin wata farar jallabiya Kallan Imran yayi wanda yafara wanka da turare spray yace bro Bari indan rintsa kadan kona 30mnts ne Imran yace to Bros atashi lafiya, sannan shikuma yasaka qananun Kaya yadauki computer yajuyo yadubi Aliyu dahar ya kwanta yace Bros Ina falo zan danyi wani aiki Idanunsa a lumshe yace to Barrister na fita, Yaji yakasa yin baccin, meyasa yakejin farin ciki? Wata Zuciyar ce tabashi amsa da fadin saboda Iman ne Juyi yasakeyi idonsa arufe, Iman ta Bros ce bazai taba samun taba, Gara yasawa Zuciyar sa salama tun kafin soyaiyar ta tayi masa illah Sumar kansa ya hargitsa, afili yace ya Allah kakareni da aikata abinda zaisa Yan gidannan Susan abinda yafaru tsakaninmu da yarinyar Nan Fillo din dake gefe yadauka ya rungume sannan yafara samun bacci, jiyake Kamar itace atare dashi Yana falo yana nazari acikin computer, Saida yagama sannan Yarufe yabarta anan ya shiga dakin domin duba brother dinsa Yana shiga dakin yaganshi yana bacci rungume da Fillo, Murmushi yasaki afili yace Bros kawai kafuto fili kace mamy Aure kakeso Be tasheshiba Yarufe masa dakin yayi part dinsu Hajiya Yana shiga yaga Farhan da Iman Suna kallo, kallo daya tayi masa cikin sanyin murya tace Yaya sannu da Zuwa Beji kunyar qaninsa dayake wajan ba yace saunawa zan sanar dake Bansan Jin wannan sunan Murmushi tayi batace masa komai ba, ganin Farhan na nan Yaya sannunku da dawowa, inji Farhan Yauwa Farhan, sannu Farhan yace Yaya ya banga yaya Ali ba, Koya fita? Barrister yace no, yana daki Miqewa yayi yace a a Bari natafi, Bana rasa abin samu ba idan naje Dasauri Imran ya tareshi yace to sarkin son kudi, yana bacci saura Kuma Naga kaje katadashi Kallan Iman yayi yace muradina Ina hajiya ne? Cikin ladabi tace masa tana cikin daki Tashi yayi yashige dakin hajiya, Farhan naganin tashinsa yacewa Iman yarinya dama nafada Miki inawa Yaya magana zai siyamin waya, yanzu gashi Yazo Har gida, Kinga kuwa nahuta da renin hankalinki Murmushi Iman tayi tace au Wai dama shi kake nufi zai siyama wayar? To inka Isa jeka fada masa, yanzu zakaci duka, wannan me fuska Kamar an aiko masa da mutuwa din tab Farhan yace emana soja Kenan yarinya, Nima shi zankoma ai, Ina zama soja zan hadaku gaba dayanku indinga jibga, Billy kawai zan ragawa Itama dannaga saliha ce shiyasa Tabe baki Iman tayi tace a a kadaki wasu de, Farhan yace aishi Yaya Ali daban yake, yanada kirki, kawai de kema Dan Baku saba bane, Amma ai zaku saba ne kafin su koma Abuja Suna zaune Suna kallo tareda musun dasuka saba, Har barrister yafuto, yana Zuwa yadubi Farhan yace Kai Tashi kafita da Allah Sosa Kai Farhan yayi, yace to Yaya Amma babu abinda zan samu ne? Kallansa yayi yace Wai Farhan mekake da kudi ne, ba rannan nayi ma transfer 50k ba? Kafin Farhan yabashi amsa Iman tace yanmata Harara Farhan ya aika mata sannan yace Yaya wallahi bawasu yanmata, Imran yace naji jeka, zan turo ma Saida yasake dalla mata harara sannan yabar cikin falon Yana fita, barrister yamaida hankalinsa kanta, yace muradina, nayiwa hajiya maganar bikinmu Batasan dalili ba, kawai de nan take faduwar gaba ta ziyarceta Kenan Hakan fa yana nufin shikkenan tarasa Aliyu? Ni Iman na shiga uku karfa nayi Aure da soyaiyar wani daban acikin zuciya ta Maganar sace tadawo da ita Daga tunanin datake yace kinyi Shiru, kobakya maraba da angon naki Ahankali tace I nayi yaya Matso da fuskarsa yayi dab da Tata cikin muryar sa maisa jiki yamutu yace na matsu Naga na aureki muradina, na matsu Aure kawai nakeso Kuma dake Suna wannan halin yasako kansa cikin falon, Baisan dalili ba nan take yaji gefen inda Zuciyar sa take yayi zafi Zuba masa ido tayi tana kallansa, saiyau tataba ganinsa da qananun Kaya, sosai kayan yayi masa mugun kyau, Kodan baicika sakawa bane oho Barrister Jin Iman tayi Shiru yasa ya kalli inda take kalla Nan take fara'ah ta wanzu a fuskarsa, yace Bros shigo mana, Cikin danne kishin sa yashigo falon ya zauna Ahankali cikin zazzakar muryar ta tace masa Ina yini? Fuska ahade yace lafiya Imran yace Bros wannan itace muradina, matar danakeson aura Kamar Bai santaba yasaki Murmushi yace to Bros Allah yakaimu musha biki Tashi yayi tsaye yace Bari Naga mamy, batare daya jira amsar dan'uwan nasaba yayi gaba, wanda azahiri yana kishin ganinta da Ko wanne da namiji ne, hakanne yasa yagudu yabar wajan, kome yake fada mata suka wani hade Kai Kamar zaiyi kissing dinta, mutsw yasaki tsaki shi kadai Aliyu na tafiya, barrister yace kiyi hakuri fa, Bai Miki maganaba Daga gaisuwa, haka yake, baida Yawan magana, pls kada Hakan yabata Miki rai Cikin ranta tace ah iskanci de ba rashin magana ba Amma afili saitace babu komai muradina, Hakan tada fada saiya sanyayawa barrister zuciya *** *** *** Yana shiga cikin dakin yaganta tana shirya Kayanta cikin wardrobe Mamy Wai yaushe zamu koma gidane, Naga Har kayanki kike shiryawa Kamar wanda zamu Dade Zama Zamu yi Har lokacin daka sauwaqewa kanka kadena tunani kawarke ras Kamar Yanda Yaya yace Nikam ai inabin umarnin sane Kamar zaiyi kuka cikin shagwabar daya saba mata yace Amma mamy Taya zanji sauqi Bayan yarinyar Nan tana cikin gidan nan, yanzu fa mamy kinganta can fa afalo tana tare dashi Yaqarasa maganar Kamar zaiyi kuka Zuba masa ido mamy tayi ganin karfin Hali irinnasa Tace to menene danna zauna tare dashi, batare ka gansu ba? Dama can ai tare suke Amma mamy kamarfa zaiyi mata ki..... Tunawa yayi tare yake d mamy hakanne yahanashi qarasa maganar tasa Murmushi tayi, Sarai tagane abinda yake nufi, Dan haka tace baby, banasan fitina kaji Ko, tun wuri ma kasawa Zuciyar ka salama Akan sha'anin yarinyar Nan, kayi hakuri Kamar Yanda mahaifinka yayi, kukuma haka Allah yadoramuku Cikin mamaki yace mamy menene yafaru da daddy din? Tana shirya kayan nata tace daya nemi mahaifiyarta yarasa, ya hakura yanemeni Kuma yasamu, gashi Har mun sameka, to kaima inaso ka hakura kaji baby Mamy Nikam aina Dade da hakura, haba mamy Kamar wanda banajin maganarki Daria tayi, tasan Sarai yafada ne, domin hankalinta ya kwanta, Amma so Kam yana nan, itade fatanta daya, Allah yakare mata shi Daga wata rashin lafiyar Mamy Ina wannan yarinyar ne, kike aiki da kanki? Mamy tace Wai atika? Yace yes Nace tatafi gida tahuta, idan zamu koma Abuja saita dawo Wandonsa na jeans yafara nadewa Daga qasa Kamar wanda zai tsallaka wuta yace to mamy Bari na shirya Miki Batayi musu ba tasakar masa *** *** *** Washe gari da Rana dukansu Suna zaune Suna cin abinci, Farhan, hajiya, Imran, Aliyu, Iman, mamy Mamy tayi Shiru tana wani tunani ita kadai, saida tagama yanke shawara ita kadai sannan ta dubi Hajiya tace Hajiya nikam yaushe Bilkisu zata dawo ne? Cikin ransa yace Alhmdlh mamy Kamar tasan inda yakemin qaiqayi Hajiya tace Bilkisu may be muganta da wuri, tace zata lallaba baban su tadawo Jijjiga Kai mamy tayi tace Yarinyar babu ruwanta, nayaba da hankalinta Kamar Fatima, idan ba'a yi maganar auranta ba inayiwa Baby Ali sha'awar Auranta Lokaci daya Iman ta qware da abincin datake ci Shikuwa gogan Gabansa ne yayi muguwar faduwa Sharhi please πŸ™πŸ» Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 15 Dasauri Imran yatashi yazuba ruwa a cup yabata, Har bakinta yakai mata cup din tamkar zai Bata ruwan da kansa, qirjinta ne yariqe, daqyar take shan numfashi, haka ta karbi ruwan Tasha Dan kadan, hannunta dafe da kirjinta Atake mamy tagane Cewa dalilin fadar wannan maganar tatane yasa Iman wannan qwarewar, Kenan Hakan yana nufin Itama tanasan Aliyu Har yanzu Hajiya ce tace sannu Iman, nahanaki magana idan anacin abinci Amma bakyaji, yanzu haka nasan may be magana zakiyi Tunda kinji anyi zancen Bilkisu, Bayan Kuma abinci kikeci Mamy tace sannu Fatima Iman Bata Iya cemusu komai ba, Idanunta jajir alamar Taji ajikinta dalilin tarin datayi, ta daga Kai ta kalli Aliyu, sannan tatashi tsaye tace Hajiya banajin dadi zazzabi nakeji, zanje na kwanta Miqewa Imran yayi yanufeta tareda kama hannunta daya, dayan hannun nasa Kuma yazagayo dashi ta kafadarta, yace mata muje dakin Babu musu tajuya sukayi dakinta Jikinsa ne yayi sanyi, ya tabbatar dalilin maganar mamy ne yasa yarinyar Nan shiga damuwa lokaci daya, bayansu yabi da kallo, babu abinda yataba Zuciyar sa irin Yanda Barrister yariqe kafadarta Nan take ransa yabaci idanunsa suka kada sukai jajir Spoon din hannunsa ya Ajiye Shima yatashi yafice batare da yakalli Hajiya Ko mamy ba Hajiya tace ikon Allah Kinga duk sun watse, sai a lokacin Farhan yayi magana yace saini ba Mamy ce taimasa Daria kawai, domin kuwa tasan dalilin dayasa Aliyu yatashi Hajiya tace Hajiya fati naji maganarki, ni kaina zanso ace acikin gidannan Bilkisu tayi Aure kokuma cikin dangi, Amma mahaifinsu yabada ita ga wani yaro daya Daga cikin danginsa Batare da damuwa ba mamy tace to ai shikkenan Acan daki kuwa Suna Zuwa tazube agado, kirjinta zafi yake mata sosai, dasauri yafita saigashi yadawo da magani ahannunsa, daqyar tatashi Tasha maganin, yaja mata blanket yafita Daga dakin Tun Rana Har dare Iman Bata sake futowa falon ba, tana cikin dakinta akwance, Daga cikin bargo take goge hawayen dake tsiyaya afuskarta, Yaya zatayi dason Aliyu? Ta tabbatar Zuwa yanzu Kam yadena kaunarta, Tunda yafuto fili Kai tsaye yace yafison Yaya Imran fiye da ita, gashi yanzu mahaifiyarsa tana sha'awar ya auri Bilkisu, Kuma bataga ya nuna wani Abu dazai nuna baya kaunar hadin ba, Kenan ita kadai take haukanta banda shi, tun tana kukan hawaye harta dawo yi afili Da daddare Suna zaune a falo gaba dayansu,wayarsa yake dannawa Amma gaba daya hankalinsa ba'a wajan yakeba, yajita Shiru Kamar Bata gidan, ya matsu yaji awanne Hali take ciki Mamy Kamar tasan abinda yake tunani tace Nikam Hajiya banga takwarata ta futo ba Tashi Hajiya tayi tace um yanzu haka Taji relief ne tana aikin kallo a computer, Bari inje ingani kar'azo anamin fishi Hajiya natafiya dakin Iman, yasaki wata yar qaramar Ajiyar zuciya Tana shiga ta hangeta ta tuqunqune akarshan gado, sai riskar kuka take ita kadai Dasauri Hajiya ta karasa tace subhanallah Iman!! Tafadi haka tana yaye bargon da Iman din ta rufa Idanunta jajir taci kuka Kamar ba gobe, Hajiya tace nashiga uku Tashi, Tashi muje akaiki asbiti Dan qaramin mayafi tadauka mata tareda yafa matashi akanta Gaba daya tasaki jiki ajikin Hajiya, Suna tafiya Iman tana kuka wiwi Suna Zuwa falon gaba dayansu suka kalleta, Hajiya tace yau Naga takaina Iman kincika raki wallahi, haba Daga zazzabi saiki kama kuka Kamar wanda akai mutuwa Jikin mamy ne yayi sanyi, tasan itace silar komai datasan haka dabatayi maganar agabanta ba Cikin sanyin jiki mamy tace haba Hajiya kidena yi mata fada mana, kika sani Ko akwai abinda yake damunta Bayan haka Juyawa tayi ta kalli Iman dake kuka, tace Fatima zazzabin ne Har yanzu? Cikin kuka ta girgiza Kanta tace mamy qirjinane yakemin ciwo, idan zanyi numfashi sainaji ciwo Mamy takalli Hajiya tace to ai kinji, Bata lura da Aliyu da Imran dasuke zaune ba tasake Kallan Iman din tace, Ko kina kwana brezia ajikinki? Tambayar tabata kunya, danhaka kanta aqasa tace a a mamy Quri yayi yana kallanta, jiyake dama ciwon yadawo jikinsa ita tahuta Cikin damuwa Imran yatashi yace Bari muje asbiti Hajiya, yakama hannun Iman suka fara tafiya, juyowa yayi yace Bros taso muje Babu musu yatashi yabisu domin kuwa hankalinsa zaifi kwanciya Akan ayi mata komai agabansa Akan yazauna agida Barrister kwarara gudu yake, tana kwance Abaya, shida Aliyu agaba, nan da nan suka Isa Juwairiyya clinic and maternity Yana parking Aliyu yafuto, Shima Barrister yabude mata motor, Saida yatemaka mata sannan ta futo, hannunta cikin nasa suka qarasa cikin asbitin Sun yanki Kati da komai aka turasu wajan wata doctor, mace ce, Suna zama a office din barrister yayi Mata bayanin abinda yake damun Iman Tashi tayi tadubata da kanta, sannan sannan tarubuta mata magunguna tabashi tace zanyi mata allura yanzu insha Allah zataji dadin allurar musanman wajan yin numfashin, yanzu kaje office din gaba zasu baka sauran magungunan kakawomin Cikin kulawa yace OK doctor Amma kiyi mata Ahankali Dan Allah banaso Taji zafi kokadan Murmushi matar tayi tace wow da alama de mijinta ne Ko? Naga kana Bata kulawa Yanda yadace Sosai yaji dadin maganar Tata yace no, matar dazan aura cede insha Allah, tace masha Allah, gaskiya kun dace, Kuma kun birgeni, Allah yabada Zaman lafiya Yace amin, tareda fita Shikuwa yana zaune Akan kujera yayi Shiru, wato shine baya sonta Tunda baya Bata kulawa, it means haukan banza yake akanta Ransa abace, yasake hade girar Sama data qasa Allura doctor tahada tadubi Iman data Dora kanta Akan cinyarta tace to madam juyo nayi Miki allurar Ai Iman naji zancen allura tafara yarfe hannu, cikin hawaye tace nide wallahi banason allura Doctor tadubi Aliyu dayake zaune tace Amma Kai yayantane Ko? Agajarce yace "eh" Tace aikam naga alama gashinan Kuna kama sosai, Naga alama Kamar tanajin maganarka, kayi mata magana tayi hakuri ayi mata allurar Cikin Jin Haushin maganar doctor tunta dazu yadubi Iman yace "kitsaya ayi Miki, kina Bata mana lokaci" Doctor cikin ranta tace ah wannan bawasa, saikace wani soja, wannan ai dole Taji maganar sa Tana yarfe hannu tamiqe tsaye tareda Juyawa doctor baya, alamar tayi mata allurar Kenan Sunkuyawa doctor tayi tafara yimata allurar, Iman najin shigar allurar tasaki qara tana sake yarfe hannu, doctor tace kidena motsi fa, karkisa naji Miki ciwo, kisaki jikinki Iman Kamar bada ita akeba tana yarfe hannu ga hawaye shabe shabe tace ni wallahi banaso Tashi yayi Daga inda yake yanufesu, baiyi wata wataba yajata jikinsa ya rungume ta tsam afaffadan qirjinsa Yadubi doctor yace "yimata" Tace to tareda Sunkuyawa tanayi mata Allurar Jinta akirjinsa yasa tayi luf tana shakar qamshin dake Tashi ajikinsa, Shima anasa bangaren hakane,tudun dayaji akirjinsa na dukiyar fulaninta shine ya sanyashi shiga cikin wani irin yanayi, nan da nan idanunsa sukai jajir Basusan tagama allurar ba Saida ta dubesu tace nagama, sannan ya janyeta Daga jikinsa yazauna akujera cikeda mutuwar jiki Itama Iman kwanciya tayi Akan kujerar, tana shaqar qamshin sa dayayi saura ajikinta Suna zaune Shiru, doctor na rubuce rubuce Barrister yakawo magungunan, Saida aka daura mata ruwa Leda daya yaqare sannan suka tafi gida, ba laifi Taji karfin jikinta dalilin qarin ruwan da aka mata, dakanta tataka Har Zuwa gaban Mota Suna Zuwa gida taci abinci Tasha magani sannan tajedaki ta kwanta, Hajiya da mamy Har dakin suka rakata sannan suka dawo falo Suna fira *** *** *** Shabiyu nadare Suna zaune adaki shida barrister, takardu ne agabansa yana cikewa, fira suke jefi jefi Hankalin Aliyu Kam baya tare dashi, tunani yake Ko yanzu Taji sauqi? Yasan de Zuwa yanzu insha Allah zataji relief Tunda sun Dade da dawowa Daga asbiti Tashi yayi yakalli barrister yace Bros Bari naje wajan mamy nadawo, Barrister yace OK Futowa yayi yanufi part dinsu Hajiya, babu kowa a falon, tsayawa yayi yana nazari shin yashiga dakin yagani tadanji sauqi kokuma kawai yajuya? Karfa yashiga yaje ba ita kadai bace adakin mezece idan yashiga? Yana wannan tunanin mamy tafuto falo dauke da jug ahannunta zatakai kitchen Da tsananin mamaki afuskarta tace Baby me kakeyi anan? Arazane ya juyo, baiyi zatan ganin mamy ba a yanzu Cikin damuwa yace mamy... Kama hannunsa tayi taduba gabas da yamma babu kowa sannan tajashi cikin dakinta Tace mekakeyi a wannan lokacin bakai bacci ba? Kamar zaiyi kuka yace mamy Iman batada lafiya, nakasa baccin mamy...... Yaqarasa maganar muryarsa na rawa, nan take hawaye suka zubo acikin idanunsa Cikin ranta tace yau nashiga uku, wanne irin so Yarannan sukema junansu? Afili tace to menene abin kuka Kuma Dan batada lafiya? Ai zataji sauqi Kansa yadora acinyarta yace to mamy naje Naga halin datake ciki? Dan Allah mamy karki hanani kibarni, Wlhy tun dazu zuciyata zafi takemin, mamy Ina sonta.... Inasonta mamy bazan Iya cireta araina ba... Innalillahi.. Mamy take maimaitawa acikin ranta, tofa wannan al'amarin yafara daure mata Kai, ta saddaqar kawai tabarwa Allah komai dangane da wannan Yara, zata musu Addu'ah kawai shine mafita Afili tace nasan kana sonta Aliyu, ka kwantar da hankalinka, insha Allah zataji sauqi, Amma karma kaje dakinta, Aliyu idan kaje dakinta Garin futowa wani a gidannan yaganka mezamuce dasu? Kayi hakuri kaji baby insha Allah zata warke Ajiyar zuciya yasauke yace to mamy Dan Allah kijanye maganar dakikai tsakanina da Bilkisu, mamy bazan Iya auranta ba, idan kuwa na Aure ta to zan Aure tane dason yayarta acikin zuciyata, mamy kada na zalinceta, nayi Miki alqawarin zan Kwantar da hankalina Allah yayayemin yakwomin wata matar Shiru mamy tayi, itakam Zuwa yanzu ai babu abinda zata Iya Cewa game da wannan al'amari Tace to Aliyu Allah yayima albarka, jeka kwanta Tashi yayi jiki asanyaye yakoma part dinsu *** *** *** Next day Dasafe Suna zaune a falo, game suke bugawa a TV kowa ya nutsu yanaso yaga yaci, Daga Aliyun Har Imran wando ne ajikinsu three quarter Na Imran fari sai farar Riga marar hannu Na Aliyu Kuma Daga wandonsa Har rigar duk kalar kakin soja ne, Farhan yana zaune agefe anci manyan Kaya farare hardasu agogo Yana kallansu, Aliyu yace Bros yakamata muje wajefa mudan buga qwallo kadan, Shima Imran din hankalinsa yana kan game din dasuke bugawa yace Ok Bros Dan Murmushi Farhan yayi harda Sosa qeya yace Yaya Ina tuni de Murmushi Aliyu yayi yace Farhan karka damu wayarka tana hanya Jijjiga Kai Imran yayi yace wannan Yaron zaka siyawa waya? Sau uku Ina siya masa Yana Bawa yanmata, yanzu haka nan daka ganshi da manyan Kaya wajan yanmata zaije Murmushi Aliyu yayi kafin yayi magana Alhaji yashigo cikin falon, basuji shigowar saba, saboda game din daya dauke musu hankali, Imran Cewa yake yess nine first Aliyu yace inaaa Bros nine zancinye Hajiya da mamy Suna Daga can gefe Hajiya tace Alhaji sannu da Zuwa, mamy ma tace Sannu da Zuwa yaya Lokaci daya suka kalli kofa, Alhaji suka gani atsaye, kowa kansa ya sunkuyar Kamar marasa gaskiya Baqin ciki yakama Alhaji, dubesu Dan Allah azaune da wannan kayan, sun girma harsun gaji Amma babu me maganar Aure acikinsu, Ko ajikinsu Suna zaune sunyi biris da maganar Aure Aliyu ne yace sannu da Zuwa Alhaji, Imran ma yace sannu da Zuwa Be amsa musu sannun tasuba yace wato ku ba'a Isa dakuba, anyi muku maganar Aure kunyi Shiru, yanzu ku duba kuga kayan dayake jikinku Baku da maraba da arna Da hannu yanuna musu Farhan yace kuduba kuga qaninku yayi shigar mutunci Amma ku kokunya bakwaji Dasauri Imran yace Alhaji wallahi Shima Farhan din wajan.... Bai qarasa maganar ba Alhaji yace kowa nabashi nanda wata daya acikinku yakawomin matar Aure Imran yasosa kansa ya kalli hajiya, nan take tagane nufinsa tace Alhaji ai Imran yadade dayimin magana, nice de namanta banyima zancenba, Wai Tunda su Iman sungama school yanaso Asa ranar bikinsu Adede lokacin Iman tafuto Daga daki, da wata doguwar rigar bacci ajikinta medan kauri, wannan maganar ta Hajiya ce tasauka adodon kunanta Ahankali tajuya Takoma cikin dakinta gabanta na mugun faduwa A falo kuwa Alhaji Murmushi yayi sannan ya kalli Aliyu yace to kaima Aliyu kakawomin yarinyar dakakeso sai ahada gaba daya Asa muku ranar Jikinsa asanyaye yace to Alhaji insha Allah Alhaji yayi ciki, Adede lokacin wayar Aliyu tayi qara, abin mamaki yana duba me Kiran nasa yaga number Iman ce Kirjinsa ne yake masa zafi, yadubi barrister yace Bros Bari na amsa waya, yayi waje Yana fita harabar gida yafara Tari, jiyake abin nasa naqare ne, yasa hannu zai Daga Kiran nata yaji Tari yaqi qarewa, haka Kiran nata yakatse Bai dagaba Direct part dinsu yanufa dasauri yanaso yasha ruwa kozai daina tarin Yana Zuwa yanufi fridge yasha ruwa kadan, Amma still tarin yakeyi, amai yafara ji, dasauri yanufi toilet, yana shiga yaji amai yataho masa, danhaka yanufi sink yayi aciki Abinda yaganine yabashi mamaki matuqa Ahankali ya tambayi kansa "jini"? Sharhi please πŸ™πŸ» Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 16 Shiru yayi yana maida numfashi, yana gama Aman jinin sai tarin yatsaya, wanke bakinsa yayi sannan yayi brush yafuto Daga toilet din Agefen gado yazauna, yadafe kansa da hannunsa, yanzu Yaya zaiyi yasamu yarinya cikin 1month? Shiyasa yafadawa mamy tun farko zamansa agidannan wata matsalar zata haifar masa Ya tabbatar wannan Aman jinin yanada nasaba da Zuciyar sa Afili yace Innalillahi... Tunawa yayi da Kiran ta, cikin sauri yadauki wayar yakirata, ringing biyu wayar tayi Iman ta dauka Kukanta ne yadaki dodon kunnansa, rintse idanunsa yayi yanajin kukan nata nataba masa zuciya Daqyar yace "meyasa kike kuka?" Shiru tayi takasa magana sai shashshekar kuka datake Ahankali cikin rada yace Fatima banasan kukan nan, me akayi Miki Wai? Cikin kuka tace "kanajin abinda Alhaji yacefa, Wai zaisa min Rana da Yaya Imran, Allah banasan sa, ni Kai nakeso" "meyasa zakice bakya sonsa? Kenan bakyason Bros Dina nikuma kice kinasona nayarda, me Imran din yayi Miki? Yanasonki Fatima, "OK haka zakace? " " mekikeso nace Miki? Kisoni kiqi dan'uwana? Cikin takaici tace Masa shikkenan, tareda kashe wayar Wayar yabi da kallo, yanzu banda yanasan yarinyar Nan Yama za'ai takashe masa waya afuska? Yaya takeso yayi ne? Gaba daya jiyake yatsani kansa dakuma wannan rayuwar Wayar doctor din dake dubashi yakira yace masa basai yazoba yau, babu abinda yakeji na rashin lafiya atare dashi Yana kashe wayar, yayi wulli da ita agadon hadi da tagumi hannu bibbiyu *** *** *** Acan cikin gida kuwa Iman kuka take sosai Kamar ranta zai fita, hannu tasa ta share hawayen idonta, p.o.p din dakin tazubawa ido tana nemawa kanta mafita Iman Kinga wannan mutumin baya kaunarki, bayason mu'amularsa dake, qarara yadade da baiyana Miki abinda yake cikin Zuciyar sa, naci da jaraba irin taki ne yasa kika liqe masa, kin zubar da qima da darajarki ta ya mace kin nuna masa so, Amma shi yana Miki maganar Imran, wato da gaske Kenan yafison Yaya Imran akaina Juyi tayi Akan gadon sannan taci gaba da zancen zuci ita kadai Iman Barrister yana sonki, yana baki duk wata kulawar data dace, bazaki Iya cire son Aliyu acikin ranki ba, Amma haka zakiyi hakuri kici gaba da sauraron muradinki Saida tagama zancen zucinta sannan afili tace "insha Allah Nima nadena wahalar dakaina abanza, nadena wahalar da kaina Akan mutumin dabaisan darajar soba, bayace Ina sonsa naqi dan'uwansa ba? To yanzu zanso dan'uwan nasa Tunda haka yakeso Daga nan tatashi tashiga wanka, tana futowa ta zauna ta tsara kwalliya, atamfa ta saka Mai launin green dinkin Riga da sket, sosai kayan yayi Mata kyau, tafuto falo Hajiya da mamy Suna zaune a falo, sai Imran dayake jiran Aliyu suyi ball, tana futowa mamy cikin ranta tace masha Allah, dole Aliyu na ya rikice Aqasan kujera ta zauna, tana gaida su, gaba dayansu suka hada baki wajan amsawa, banda barrister daya Kafeta da ido Ahankali tatashi tayi wajansa, tace Yaya Dan Allah anjima muje shopping kaji, Wlhy kayan make up Dina duk sun qare Yana kallanta yace to shikkenan karki damu, Dama ai munjima bamu je yawoba, da yamma saimu tafi, Cikin murna tace to Yaya ngd Sannan ta maida hankalinta Kan Kallan dasu hajiya sukeyi Kusan minti talatin da zamanta, saiga Aliyu yashigo cikin falon,kallo daya tayi masa tadauke kanta, Shima anasa bangaren fuskarsa ahade yadauke kansa Barrister na ganinsa yace dama Kai nake jira, muje Dasauri ta tsaida shi, domin Aliyu yaji Haushi tace Muradina Dan Allah tsaya kasha Ko ruwane sai kuje Bata jira amsarsa ba, tajuya tayi kitchen da sauri, saigata da gorar ruwa da cup Tsabar iyayi irin nata data zuba masa ruwan Saida ta rissina sannan tace gashi kasha kaji sanyi aranka Dadi sosai barrister yaji, yasa hannu yakarbi ruwan da niyya yahada da hannunta yariqe Ahankali ta janye hannunta Duk abinda suke Akan idonsa, dasauri yakawar da kansa Harabar gidan suka fita, Daga can bakin gate sojoji ne wanda suka zo tareda Aliyu Dan haka sukai baya, suka fara buga ball dinsu *** *** *** Da yamma wani wankan tasakeyi, doguwar Riga tasaka baqa, sai fulawa ajikinta fara, rolling tayi da dankwalin rigar, sai zuba qamshi take Falo tafuto, Hajiya tace Ina zakije? Hajiya da Yaya zamu fita Hajiya tace Adawo lafiya, tayi kitchen Zama tayi a falo tana selfie a wayarta, ahaka yashigo yasameta, yayi kyau sosai cikin suit baqa Tana ganinsa tasaki Murmushi tace Yaya kayi kyau sosai Shima Murmushi yayi yace ai kinfini kyau Muradina Kofa ya nuna mata yace muje Ko? Babu musu tatashi suka futo Kowa yagansu saisun birgeshi, Yanda sukai kyau babu qarya Suna Zuwa wajan Mota yabude mata, Bata shiga ba Saida ta juyo tace Yaya Bari inyi mata pic Matsowa yayi dab da ita tayi musu selfie sannan tashige cikin motor, shikuma Yarufe yazagaya yajasu suka fice Daga gidan Suna fita yasaki labulen window din dakinsu, Ina zasuje haka? Kuma yanzu ahaka zasu fice maza suyita kallanta? Meyasa ma becewa Bros baida lafiya ba Dan su fasa fita? Harda yimusu photo, shi kuwa Tunda yake da ita Bata taba tunanin yin pic dashiba, may be bekai matsayin dazatayi dashi dinbane Da wannan tunanin danake garama natafi wajan mamy kozan danji sauqi, yana gama magana da Zuciyar sa yayi cikin gidan *** *** *** Suna tafiya ahanya yace Bansan meyake damun Bros dinaba, nace masa yashirya muje unguwa yaqi yarda, Amma inaga Dan yaga dake zamu fitane, kinsan shi bayason raini, yanzu sai yace mun dauki yarinya muna Abu agabanta, karta rainamu, abinda yasa ban matsa masa mutaho tareda kinsan shi idan zai fita dole Saida wannan sojojin, ranar da muka kaiki asbiti ma saboda darene shiyasa yataho shi kadai, Amma badan haka ba bazasu barshi yafita shi kadai ba, shiyasa yanzun ma na qyaleshi, banason tafiya da wannan jiniyar wallahi Murmushi tayi tace nikam Yaya in tambayeka Inajinki Muradina Naga kunason junanku sosai kaidashi, yanzu misali wani Abu yasameni, Shima Kuma wani Abu yasameshi, wazaka fara temakawa acikinmu? Daria yayi yace Kai Muradina, kincika rigima, mekuma yakawo wannan maganar Cikin shagwaba tace Dan Allah Yaya ka amsa min Hankalinsa yana kan driving din dayake yace, Fatima inason Aliyu fiye da Yanda nakeson kaina, zan iyayi masa komai danjin dadinsa, Kinga yanzu da Alhaji yasa masa wannan dokar ta fidda matar da zai aura cikin wata daya? To wallahi jinake araina dazan Iya cireki araina Dana cire nahakura nabashi Ke, nikuma nadau hukuncin da Alhaji zaiyi masa Dannasan bazai samu mace cikin wata dayaba, to matsalar shine inasonki Aliyu yana sona, tun bamusan kanmu ba ansha siya masa Abu yace ya hakura yabani, Mota tare muke bada order su idan zamu siya, Ke hatta waya yanzu ne muka daina siya tare , zan iyayi Masa komai Fatima, Kamar Yanda Shima na tabbatar zai iyamin fiye da haka Tanajin karshan maganar tasa tashareshi ta kalli window tana ganin gefen titi Wato kowannensu zai iyayin komai Akan dan'uwansa, kowa yanason dan'uwansa fiye Dani, ai sai kuje kuyi tayi, Naga Yan biyu ma, Kuma ta tabbatar da gaske yake, Tunda Har Taji yakirata da Fatima abinda saita Dade rabon dataji yakirata Da wannan sunan sai Abu me muhinmanci Jintayi Shiru ne yasa yace dafatan ban Bata ranki ba? Ahankali tace a a Yaya Shopping din sukayi, duk inda sukayi sai ankallesu, Daga nan suka wuce yawonsu *** *** *** Agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yaduba, Ina suka tsaya basu dawo gidaba Har yanzu Karfe Tara da kwata? Harabar gidan yake zagayewa Wayarsa yadauko Har zai Kira Bros, kawai saiya fasa yakira Mustapha Yanayin wayar yana duba Agogon hannunsa Har suka gama wayar baiga sun dawoba, lokacin Tara da rabi na dare Cikin gidan yashiga, yana shiga sai Hajiya da Zeey a falo, yace Hajiya mamy nafa? Daria tayi tace to Dan mamy gatacan a kitchen Daria yayi yana sosa kansa yayi kitchen din Mamy mekikeyi a kitchen da kanki? Batare data kalleshi ba tace baby tea nake hadawa Yauwa mamy hada Dani, zansha Nima Tace to baby Yana zaune yana Kallan Yanda take hada tea din, Amma tunanin sa yana can wata duniyar, kome suke basu dawoba? Wata yar qaramar wuqa ce a ajiye agefe yadauka yana wasa da ita, yana tunanin irin wulaqancin dazai yiwa yarinyar Nan Tunda Har tafice Daga gida, ta zauna awaje Har tsawon wannan lokacin (jama'ah kunji karfin haliπŸ€”) Mamy na juyowa da karfi tace Aliyu!!! Arazane ya kalleta Cikin fada tace Wai yaushe zaka Dena wannan tunanin Naka marar bullewa? Sau uku Ina kiranka kayimin banza, yanzu duba Yanda kajiwa kanka ciwo da wuqa Sai a lokacin ya kalli hannun nasa, jini ne yake disa awajan, shi bemasan yaji ciwonba, Ahankali yace mamy Bansan naji ciwonba Harara tazuba masa, cikin tashin hankali tace muje muje mutafi asbiti ayi treatment din wajan Kamar qaramin yaro haka tajawoshi suka futo falo Adede lokacin su Iman suka dawo da ledoji a hannunta Imran ne yasaki tasa ledar yayi wajan sa yace Bros, meyasami hannunka? Subhanallah ai ciwo kaji Hajiya ma tace Toya kuka tsaya asaka masa tissue awajan mana Haushi ne yakama Iman, ganin duk sun wani rikice saikace wanda akace wani mummunan hatsari yasamu Mamy tace Imran gashinan kawai ku wuce asbiti Imran yace no mamy , ai Iman tana nan Bari ta wanke masa wajan zata Iya Sai a lokacin suka Kai kallansu gareta tana tsaye awaje daya Shima gogan kallanta yayi cikeda takaici, shibama ciwon hannunsa ne yadameshi ba, sai Yanda taje ta zauna awaje da wannan yar iskar shigar Hajiya tace kinaji Ana Miki magana Amma kin zubawa mutane ido Cikin ranta tace Hajiya Kenan bakisan halin wannan me baqar Zuciyar ba Ahankali taqaraso falon tace Bari nadauko kayan, tayi cikin dakinta da sauri Saida tahado komai sannan ta futo falon, Hajiya na zaune agefe da Zeey, sai Imran da Aliyu dasuke can gefe Suma, wajan su ta nufa ta zauna aqasa, su Kuma Suna Kan kujera, Imran yace please muradina kiyi masa Ahankali kinji Ahankali tace to muradina Tadubi Aliyu datakejin Haushin abinda yayi Mata da safe tace kawo hannun Shima fuska atamke yakawar dakai tare d miqo mata hannun Saida ta kalli hannun nasa fari tas Kamar nata, gashi kwance abayan hannun, sannan tariqe tafara wanke masa wajan Da niyya take dannawa da karfi, duk Dan yaji zafi, Amma Ko a fuska bataga ya nuna yanajin zafin ba Shima yanajinta, yasan Sarai da niyya take masa Hakan, kawai yana tunanin irin hukuncin dazai mata ne Mamy ce takawo musu tea harda Imran din tana ajiye musu tace ga tea nan kusha, ta kalli Iman tace sannu takwarata kinji, anhadaki da aiki, ashe dama kin Iya Imran ne yace A'i medicine sukayi Daga ita Har Bilkisu Masha Allah, to Allah yatemaka, cikin Murmushi Iman tace amin mamy Mamy na tafiya wajan Hajiya Imran yace sannu Bros, aide bakajin zafi Ko? Kafada yadaga yace no babu zafi kokadan Bros Imran yace OK, yadauki tea dinsa zaisha Dasauri tace muradina Dan Allah karka wahalar da kanka kabari naqarasa saina baka Cikin mamakinta Imran yace iyee babyn nan Kin dagefa da bani kulawa, Naga alama kinaso ayi akaiki gidan barrister Tace sosaima yaya Murmushi yayi yace ai kuwa a ranar dakikazo gidana zakiga Yanda zan baki kulawa Nima, da kanki Zaki bani dama inyi bake-bake acikin Zuciyar Ki Murmushi tayi batace komai ba Duban ta yayi cikin bacin rai yace Wai baki gama bane? Dagoda kanta tayi ta kalleshi cikin bacin rai Itama tace nakusa Sai a lokacin ta maida hankali tadaure masa hannun, dama ta nayi Ahankali ne Dan tayi fira da Imran agabansa yaji Haushi, Kuma yajin Tana gamawa ta tattara abin gabanta tayi cikin daki Akan gado ta zauna tace nasan kaji Haushi, ai tukunnama, Dani kake zancen Bata sake futowa falonba, haka Suma su Imran suka tafi part dinsu, Allah Allah Aliyu yake yagamu da yarinyar Nan, zata sani ne *** *** *** Next day Da yamma Suna zaune itada Farhan a harabar gidan Akan kujerun roba Ice Cream ne ahannunta, gakuma wani agabansu, tace Farhan kadau ice cream din mana, Ajiyar zuciya yasauke yace Bari sister yaubata ice cream nakeba Wallahi wata yarinya nahadu da ita me zafi, Kuma da alama konayi mata magana ba za'a daceba, Dan Naga alama ustaziya ce Daria yabawa Iman, tace haba Farhan, kaida kake da yanmata, karka bani kunya mana Akan mutum daya, yarinya guda daya tak Kansa yashafa da hannunsa yace wallahi inason yarinyar Nan sosai Dazaki shirya Dana kaiki unguwarsu kinganta yau, Zaki ganta da hijabin ta, Amma saide kiganta Daga nesa saimu dawo gida mu tattauna akanta, idan tayi saina koma gobe Tace to shikkenan Farhan, Allah yakaimu yamman saimuje Daga bayansu sukaji ance yauba fada Kenan Ana fira Juyawa sukai sukaga Barrister da Aliyu da alama zasu shiga cikin part din Hajiya ne Murmushi tayi gamida miqewa tsaye tace Yaya sannun ku da futowa Cikin kulawa yace Yauwa muradina Kan Aliyu na qasa yana duba wayar hannunsa Ice Cream din hannunta tabashi tace Yaya ga ice cream, jiya damuka dawo dashi Naga baka shaba No muradina, Kisha abinki, bazan Iya shaba Bros Dina bayajin dadi saboda hannunsa Batare data nuna damuwarta Akan maganar saba tace a a muradina dansha kaji akwai dadi Ta debo a spoon tatura masa bakinsa, babu Yanda ya Iya haka ya shanye Haushi, takaici, kishi, duk suka taso acikin Zuciyar Aliyu, ya kalli barrister yace muje Bros Hannu Imran ya kadawa Iman sukayi cikin gidan Itama wajan Farhan Takoma sukaci gaba da tsara Yanda zasu fita anjima da yamma *** *** *** Dayamma tashirya cikin atamfa dinkin Riga da sket, Dan qaramin mayafi tayafa Iya kafadarta daya, tariqo fos dinta ahannunta sai wayarta Already Farhan na jiranta amota, tana futowa tashige motar suka tafi Basket ball su Aliyu da Imran suke bugawa, Dan haka Akan idonsu suka fita, Imran Bai kawo komai aransa ba, yasan Cewa yanzu haka yawonsu zasu fita Shikuwa Aliyu ransa abace yake, yagaji da wannan renin hankalin da yarinyar Nan take masa, zai jira harta dawo ayita taqare Har dare wajan isha'i su Iman su basu dawoba, Suna dakinsu ya kalli barrister yagashi Ko ajikinsa ma aiki yake a computer, bai dacewa yarinyar Nan tadawo Ko batada dawoba Ahankali yatashi yadubi Imran din yace Ina Zuwa Bros Kawai Daga masa Kai yayi batare daya kalleshi ba Aliyu na fita, yaje bakin gate Daga gefe inda hankalin mutane bazai kawo kansa ba yanemi waje yazauna Be Dade da zamaba suka shigo Itace tafara futowa Daga motar, sai Farhan, kwalin fizza ne ahannunsa yayi ciki, Itama ta biyoshi Abaya tana chtting da yusy tana Bata labarin Yanda abubuwa suke wakana Bamata Kallan gabanta kanta aqasa Taji anfizge wayar Anja hannunta, ihu zatayi yayi saurin saka tafin hannunsa Yarufe mata baki Tsoro ne yakamata lokaci daya, idanunta suka furfuto waje, kallansa take babu damar magana saboda yayi Mata mugun ruqo Inda yazauna dazu nan yakoma yatsaya sannan yacire hannunsa abakinta yace "dama jira nake kidawo, Wai in tambayeki, mekike taqama dashi ne? Mekikeji dashi dakikemin barazana da rayuwata? Kallansa take, Yanda Yarufe ido yana yi mata fada, yayi Mata kwarjini, Amma haka ta dake, murya na rawa alamar kuka tace," Kaine kakemin barazana da rayuwata, bantaba kwanciya jinya ba sai akanka, kanaso kakasheni kanamin maganar inama barazana da rayuwa..... Dakata Dan Allah, Aliyu yayi saurin katseta Karki sake cemin akaina kin kwanta jinya, aidama Sansa kike shiyasa kike biyeshi Kuna Zuwa yawon banza, sannan kizo kina kukan munafurci kice kina sona Wannan Karon Kam Iman Bata Iya tsaida hawayen idonta ba, cikin kuka tace edin Ina sonsa, koma menene ai Kaine kajawo, jinake Cewa kayi kafi sonsa akaina, tonima nasoshi, Kuma wallahi yanzu nafara nuna masa so Gefen da Zuciyar sa take yadafe, yace saboda Ke, saboda soyaiyar danake Miki nakamu da hawan jini, still kina fadamin kina sonsa, Idanunsa jajir, cikin Daga murya yace waike wacce irin marar Imani cene? Agabana kina Cewa Zaki Bawa wani qato tea, Agabana kindau ice cream kin bashi yasha, wato inmutu konai rai bakida asara.... Ke.. Ke... Nunata yake da hannu Amma yakasa qarasa maganar da zaiyi dalilin kukan dayazo masa Tashin hankali ne qarara ya baiyyana afuskarta, namiji babba baitaba kuka agabanta ba inde ba mutuwa ba, sai yau Ita kanta hawayen datake yaqi tsayawa, cikin kuka tace nakiraka awaya nayima magana akansa Jace zansoka inqishi, Wai Yaya kukeso nayi ne? Hauka kukesan sakani? Dago kansa yayi yana kallanta Adede wannan lokacin Alhaji daya dawo Daga sallar ishsha'i yagansu Da mamaki afuskarsa yace wannan yaran me yake faruwa suka tsaya anan? Sake kallansu yayi to ai wannan Fatima ce da Aliyu Bama Imran ba Tsayawa yayi yaqare musu kallo, nan take yagane Cewa kuka suke gaba dayansu biyun Su kuwa masifa ta rufe musu ido basusan dashi Bama (tofa team din Aliyu yau ruwa yaqarewa Dan kada πŸ€”πŸ€”kawai kuyi tagumi Dan Baku da ta Cewa) Sharhi please πŸ™πŸ» Mrs Usman Ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 17 Lalle akwai matsala, dole yaran nan akwai abinda yake faruwa atsakaninsu, lalle yakamata Zuwa wannan lokacin yasaka ido Akan iyalansa, Kuma yazama dole ya bincika yaji menene yake faruwa Alhaji nagama maganar zucinsa yajuyo yasake kallansu gamida girgiza Kai yayi cikin gidan Yana shiga falon nasu yaga babu kowa, sai Farhan dayasa fizza agaba yanaci Alhaji ya kalleshi yace turomin Hajiya, sannan yayi cikin dakinsa, dasauri Farhan yayi dakin Hajiya domin bin umarnin Alhaji *** *** *** Kallanta yake da idanunsa jajir, yace bazamu saki hauka ba, Amma aike kina neman sakamu hauka a kanki, a dalilin soyaiyar ki, kinsa inajin kishin dan'uwana Cikin kuka tace ni ban zama silar da zaisa kuyi kishi da junnanku akainaba, bazaku nunamin Kuna son junnanku ba, saikun Rabu Dani gaba dayanku OK haka kikace? Still cikin kukan tace eh haka nace, nace kurabu Dani gaba dayanku Yana huci yace za'a Rabu dake kuwa Itama cikin bacin rai tace fine, tayi gaba, Shima rai babu dadi yayi hanyar part dinsu Yana Zuwa part dinsu, ya janyo qaramar trolly yafara zuba kayansa aciki, aransa yanata masifa, zan nunawa yarinyar Nan qarshan zuciya, bade tace murabu da itaba, zantafi Saudia inyi Addu'ah Allah yayayemin wannan masifar Saida yagama shirya komai, sannan yaje wajan barrister yace Bros gobe zan wuce Abuja, akwai aikin danake so nayi acan Kallansa yayi jiki asanyaye yace Amma Bros idan likitanka yazofa, kana ganin Alhaji zai barka katafi kuwa? Kafadarsa yadafa yace karka damu, bazan wuce 1week ba zan dawo insha Allah, idan nayi masa bayani insha Allah zai barni Amma Bros tafiya haka Rana daya babu shiri, Aliyu yace yanzu suka kirani ne, akwai sababbin sojojin da aka dauka ake basu horo, inaso Nakai musu ziyara Jin haka yasa barrister yace to shikkenan Allah yakaimu Dahaka haka Aliyu yasamu ya lallaba dan'uwan nasa *** *** *** Tana shigowa falon, Farhan yaganta ido jajir alamar Tasha kuka Da mamaki afuskarsa yace sister lafiya kuwa? Tace abune yafadamin cikin idona, shiyasa Cikin alhini yace sorry Kawai Daga Masa Kai tayi ta wuce cikin dakinta, tana Zuwa wanka tayi, tayi sallah, sannan ta kwanta, hawaye yana tsiyaya ta gefen idonta, Zuciyar ta banda quna babu abinda take, banda ma renin wayo Kace in Rabu dakai, Kace zan soka inqi dan'uwanka, sannan kazo kanamin fada Akan nasoshi, koma menene ai banda laifi anan,Tunda Kaine kabani dama naci gaba da kulashi, shi na tambayeshi wayafiso tsakaninmu yace badan yana sonaba zai Iya sadaukar Maka Dani, Kai kacemin kana sonsa fiye Dani Sai garani kuke saikace wata qwallo Juyi tayi Akan gadon afili tace garama ku Rabu Dani gaba dayanku, Nima nahuta, Bata gama tunanin ba zazzafan zazzabi yarufeta *** *** *** Yana Kwance Akan gadonsa Hajiya tashigo dakin tareda sallama Akusa dashi ta zauna tace Alhaji sannu da Zuwa, ai Bansan gashigo ba, sai yanzu Farhan yake cemin kana nemana Tashi yayi zaune yace Hajiya dama nakiraki ne Akan maganar yaran nan Wanne Yara Alhaji? Ina nufin babu abinda kika fuskanta wanda yake faruwa tsakanin Aliyu da Imran da Fatima? "a a Alhaji, gaskiya ban fahinci komai ba, shi Aliyu kasan baya shiga Harkar Yara bare nace Ko tayi masa wani Abu ne Shikuma Imran kaga ni Tunda nake dashi banga abinda yataba shiga tsakaninsu ba, Amma Alhaji meyasa kayimin wannan tambayar? Girgiza kansa yayi yace "a a babu komai Hajiya, kawai de Ina tsoron ace zamansu da Fatima waje daya yasa kusanci a tsakanin su Har suji wani Abu aransu, kinsan zuciya hajiya Daria tayi tace Alhaji Wai soyaiya? Daga mata Kai yayi alamar eh Haba Alhaji, aisu ba qananun Yara bane da zasuso Abu daya, gaskiya Bana tunanin haka Alhaji Ajiyar zuciya yasauke, badan zuciyarsa ta gamsu da bayanin nataba, yace to shikkenan, Zaki Iya tafiya, idan Zaki dawo ki shigomin da coffee Tace to Alhaji, sannan tafice Bayanta yabi da kallo, aransa yace lalle su Hajiya ma basusan abinda yake faruwa ba, shi Dan yau kawai kazuba masa ido kaganshi kawai, Amma karma kafara shaida akansa, dole ne yatashi tsaye Akan sanin dalilin kukan su, yasan Aliyu da juriya Akan Abu, zai wahala kaga kukansa, dole akwai abinda yake faruwa *** *** *** Washe gari Aliyu baisha wahala ba wajan tsara Alhaji da mamy, babu Bata lokaci suka yarda yatafi Abuja Yana Zuwa Abuja yasa akayi Masa duk abinda yakamata da yamma ya wuce Saudia Iman kuwa tana daki, kasancewar tana Fama da zazzabi Babu wanda tafadawa, haka tawuni a daki, sai wajan azahar ta futo Harabar gidan ta leqa ta window bataga soja Ko dayaba Abakin zeey auta takejin labarin Cewa ya Aliyu yatafi Abuja Tabe baki tayi, cikin ranta tace kafi ruwa gudu Al'amarin Yan Saudia kuwa shida yaje domin yayi Addu'ah Allah yayaye masa son wannan marar kunyar, sai gashi ya bige da Addu'ah Akan Allah yakawo musu mafita Yagama komai Amma haka yaqi dawowa gida, yayi zamansa acan, Ko mamy batasan Cewa baya qasar ba, Tunda da Sim card dinsa yake amfani Wasa wasa tun Iman tana sharewa harde tazo tana zancen zuci Akan yaushe wannan mutumin zai dawo, tafiya kusan 1week Shiru babu labarinsa *** *** *** Suna zaune a falo Dukansu, zainab tana warware mata kalbar dake kanta Hajiya tace yanzu Iman banda lalaci irin naki yaushe Zaki bawa auta kanki ta nayi Miki tsifa,? Ta kalli zainab tace auta bakida homework ne? Allah Ina dashi Hajiya, Saida nace ba zanyi ba tace sainayi kotamin duka Dasauri Hajiya tace tashi tashi, kiyi ai kinki, tamaida kallanta ga Iman tace ki qarasa da kanki, kizo Kuma girki yana jiranki, Dan yau kece zakiyi bamasu aiki ba Iman Kamar zatai kuka tafara tsefe kalbarta da kanta, mamy dake gefe tayi Daria tace haba Hajiya, duk ita kadai, munada yawa a gidan fa Hajiya tace ai Hajiya fati idan bayi takeba Saida sangarce, kina ganifa babu abinda take a gidan nan sai de in anzo cin abinci tazubawa kowa, in Kinga Iman tayi girki to tabbatar baqi Zamu yi, ai Gara tafara tun yanzu, Tunda gidan Aure zata tafi Cikin shagwaba tace Allah Hajiya ba inda zani, Hajiya tace aikwa saikin tafi, bazansaku agaba ina kallo ba, Daga Ke Har Imran din nayafe Mamy tayi Murmushi tace Fatima taso na tsefe Miki kinji, babu musu Iman tatafi Mamy tafara warware mata kalbar gwanin sha'awa Hajiya tace andaiji kunya wallahi Suna zaune Imran yashigo yace Hajiya zanje court To Allah yadawo dakai lafiya, Yadubi iman yayi qasa da murya yace akwai bikin abokina da akeyi, anjima Zamu shopping musiyo kayan dazamu saka ranar dinner Ahankali tace to Yaya Mamy nagama mata tsifar, tashige kitchen tahada abinci me rai da lafiya, jallof din kuskus dataji Nama d kayan lambu, sai dambun shinkafa dayaji su carrots, sai zobo tahada dashi Yamma nayi suka shirya suka tafi wajan shopping, Kaya yasiya musu latest masu kyau, shi suit yasiya ja me shegen kyau, sai rigar cikin fara Ita Kuma yasiya mata wata doguwar Riga ja, Mai sirkin fari ajiki, da mayafin rigar nayin rolling Shima ja Kowa yaga kayan yasan ankone akayi, sosai yakashe mata kudi, suka taho Karfe biyar da rabi suka dawo gida, Suna shiga gidan sukayi tozali da sojoji a harabar gidan Gabantane yafadi, wannan mutumin yadawo Kenan, ai kuwa Suna qarasawa cikin falon taganshi a zaune akafet yanacin abinci, girkin datayi Kamar danshi, Yanda yazauna yanaci Kamar ba gobe hakanne zaisa kagane yadade rabon dayaci irinshi Hannu Imran yabashi suka tafa, ita kuwa Ko kallansa batayi ba tanufi wajan Hajiya ta nuna Mata kayan dasuka siyo Hajiya tana hankalce dasu Tunda Alhaji yayi Mata magana akansu Tana lura da ita Ko gaida Aliyu batayi ba, anan tasan Cewa lalle akwai abinda yake wakana Zama Imran yayi awajan sukaci gaba dacin abincin, Suna gamawa Hajiya tace Iman tashi ki kwashe abubuwan da yayanki yaci abinci kikai kitchen Tsam tatashi tanufi wajan nasu, tana Zuwa fuska atamke tafara hada kwanukan sai kwala flet din take da junansu daniyya Fuska tamke yace Kinga barshi, Bari Nakai dakaina Imran yace haba Bros yaza'ai Kaje kitchen, kabarta taje wannan ai aikin mutane Batace musu komai ba, tagama qwala flet din tadauka fuuuu tayi kitchen Duk Akan idon Hajiya Dawowa tayi ta zauna a falon, wayarta tadauki qara, tana dauka tace yusy yakike? Bayan sungaisa yusra tace mata ansa bikin wata qawarsu, harma anfidda anko, taduba whatspp zataga pictures din ankon tatura mata Kai wallahi yusy naji dadi, namata murna, Allah yabasu Zaman lafiya, kice dole mushiga kasuwa muyi siyaiyar kayan biki Yusy tace to amara Bawani amara, kede Bari saima Billy tashigo wani abun Dahaka sukai sallama, ta kalli hajiya tace Hajiya Wai kinji za'ai bikin wata qawarmu, Dan Allah Hajiya kiyi mana ankon nida Bilkisu kinji Hajiya Ke qyaleni da wannan ankon naku, ku bikinku baya qarewa, da biki yatashi zaku Daga hankalinku, ni wallahi kekika koyawa Bilkisu ma, nasan da bahaka takeba, anemi takalmi anemi jaka, anemi wacece Iman tace Kai Hajiya, Dan Allah mude kiyi mana, tana fadar haka tadau jakar kayan dasuka zo dashi tayi cikin daki Mezai faru,? Tana shiga cikin daki ta kwanta agado danta huta Taji qaran shigowan text wayarta, tana dubawa taga anyi mata transfer na kudi Har dubu Dari biyu , dasauri tatashi zaune tace Kai wannan mistek akayi, wannan kudin ai saide wani, ni Iman inani Ina wannan kudin, qasan text din taduba anan taga sunan wanda ya turo kudin Aliyu Sa'ad Bilal Kai!!! Wannan Ina yasamu account number na? Innalillahi kawai dagajin zancen anko saiya turomin kudi? Ina zan samu account number dinsa namaida masa abinsa? Tana wannan tunanin Taji wani massage din yashigo, tana dubawa taga shine ya turo mata text "kuyi amfani dashi wajan bikin," Cikin Jin Haushi tayi jifa da wayar Akan gado, gayen nan yagama Dani wallahi, komai nawa yasani Kamar aljani, Ko waye yabashi number account Dina?(nikwa nace tambayeshi😏) *** *** *** Next day Zaune take agaban mirror tana shiryawa,Karfe takwas da rabi na dare, kwalliya take ta kece raini Tunda Yaya Imran yace mata za'aje dinner dinnan take tunanin Yanda zatai wanka na kece raini Dan bakasan wazaka hadu dashiba Wayarta ce tayi qara, tana dubawa taga shine me Kiran, tana dagawa yace muradina nagama shiryawa kifuto mu wuce, Ina compound Janbaki ta zizara alips dinta sannan tace to Yaya gani nan, tareda kashe wayar Tana futowa Daga dakin ta, taganshi cikin qananun Kaya yana waya zai shiga dakin mamy, cak yaqame awajan da waya ahannunsa, yazuba mata ido yana kallanta, tsarki ya tabbata ga ubangijin daya qera wannan halitta, Ahankali yace Mustapha kajirani gani nan Zuwa, insha Allah komin dare zanzo, yana fadar haka yakashe wayar Yatunkareta, jatafarayi da baya da baya, Allah Yarufa asiri babu kowa awajan, Kallan tuhuma take binsa dashi Ahankali tace lafiya? Kallanta yasakeyi Daga Sama Har qasa, yace "Ina Zaki fita ahaka? Wato kinyi wanka zakije ki nunawa maza awaje Ko? Cikin bacin rai tace bangane in nunawa mazaba, nida muradina zamu fita, Dan Allah matsa kaban hanya Babu inda zan matsa, Kuma kema babu inda zakije Malam kaifa ba mijina bane dazaka hanani shigar danayi niyya, Kuma bakada damar dazaka hanani fita Tana fadar haka ta matsa Daga inda yatare mata hanya zata wuce Dasauri yariqo hannunta, yasake matsowa dab da ita, Har tanajin hucin numfashinsa, Ahankali Kuma cikin rada yace please Fatima, Dan Allah kirufamin asiri karki fita ahaka, naroqeki karki fita ahaka wasu mazan su kalleki, Fatima zuciya ta zafi takemin, inasonki Fatima, Dan Allah kisoni Ko Rabin son danake mikine kohakan zaisa kiji tausayi nah Wallahi kika fita ahaka kikaje wasu suka kalleki na tabbatar sainayi zazzabi Bata kulashiba tafara kokarin qwace hannunta, murya na rawa tace karabu dani, kaida baka sona, baka kaunata, kafison dan'uwanka akaina Sake riqe mata hannun yayi yace kiyi hakuri mana, naji nayi laifi kiyafemin Hawaye ne masu dumi suka zubo mata, ita kanta tarasa na menene, na farin ciki Ko akasin haka Ganin hawaye a idonta yasa hankalinsa tashi, Ahankali yasa hannunsa ya share mata hawayen, fuskarsa dab da Tata yace kin hakura? Ahankali ta Daga masa kanta alamar eh tahakura Baiyi wata wataba yahade bakinsu waje daya,cikin nutsuwa yake kissing Dan qaramin lips dinta Zaro ido Iman tayi, domin kuwa batayi tunanin abinda zaiyi mata Kenan ba Agogon hannunsa yaduba yaga lokaci yaja, Har yanzu Bata futoba, Dan haka yabiyo bayanta domin yaga meya tsada ta Yana Zuwa hanyar dakinta yagansu awannan halin, Gabansa ne yayi muguwar faduwa, nan take yaji jiri yana neman dibarsa (tab da alama gidan Alhaji zai kama da wuta, yasin na fece ) Sharhi please πŸ™πŸ» Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 18 Idanunsa ne suka ciko da qwallah, daqyar ya motsa Fatar bakinsa Ahankali yafurta kalmar Bros.... Babu Bata lokaci hawaye yasakko a idanunsa, dan'uwansa dayake so fiye da komai, shine yake kissing matar dayake mutuqar so ya aura Yana kallansu awannan halin ya juya yashige dakin Hajiya, domin kuwa ayanda yakejin qafafunsa Suna rawa, bayajin zasu Iya daukarsa Yana shiga dakin yacire suit din jikinsa yayi jifa da ita, Zuwa wannan lokacin kuka yake wiwi Duk abinda yadauka adakin Hajiya jifa yake dashi, gaba daya ya haukata mata daki, kuka yake sosai banda wani irin daci da yakeji a maqogwaronsa Dakarfi yace Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, bros... Why bros... Menayima dazaka min haka bros.... Awajan ya tsugunna yahada Kai da gwiwa yana sheshshekar kuka *** *** *** Ganin bashida niyyar daina abinda yake ne yasa Ahankali tazare bakinta Daga cikin nasa Wai dama haka yake? Gaba daya yayi Mata kwarjini, takasa hada ido dashi, Koda yake ai dama yataba fada mata Cewa shi idan yanason Abu to zai nunama ne abaiyane Idanu yazuba mata yanajin wani irin yanayi atare dashi, wannan ne Karo nafarko daya taba hada jikinsa Dana wata yarinya harma yayi wani Abu waishi kiss Ahankali ta Bude baki tace Naga kudi nagode, Amma Kuma ai sunyi yawa... Bata qarasa maganar datake yi ba ya katseta Baiyi yawaba, kisai muku ankon dashi, idan Bai isaba kawai ki sanar Dani Kanta aqasa tace mungode Babu godia tsakaninmu, kidauka Cewa wannan shine gift na farko Dana taba Bawa wata mace arayuwata, da sunan Ina sonta Zanje wajan Mustapha abokina yashigo kano, akwai aikin danakeso muyi dashi, may be saikinyi bacci zan dawo To saika dawo OK kikulamin da kanki, yana fadar haka yajuya ya fita harabar gidan, yana Zuwa yashiga Mota shida sojoji mutum biyu suka fita Itama Iman daki Takoma, tana shiga tafada Kan gado tasaki Murmushi, lips dinta ta shafa da hannunta, ashe haka akeji? Dasauri tatashi data tuna da barrister yana jiranta, wani janbakin tasake shafawa sannan ta futo harabar gidan, gani tayi bayanan Bayan Kuma yace mata yana wajan yana jiranta Wayarta ta dauko cikin fos din hannunta, takirashi Amma Bai dagaba, tasake Kira still Bai dagaba, Bai fiya shiga dakin Hajiya ba Saida dalili, danhaka Bata kawo Cewa yana canba Part dinsu taje, taduba ko'ina baya nan, haka tagama dubanta Bata ganshi ba, harda qwanqwasa toilet Ko yana ciki Afili tace to Yaya lafiya? Kafada ta Daga sannan tafice Daga part din nasu, cikin gidan Takoma, ganin babu kowa yau a falon yasa ta wuce dakinta ta zauna Agefen gado, afili tace may be Yaya yafita ne, Bari najirashi Ko Zuwa anjima zai dawo , Amma Kuma Saida nagama shiryawa zai fita? Girgiza kanta tayi tare da kwanciya *** *** *** Next day Haka Iman tagama jiran Imran Har bacci ya dauketa, Amma babu Imran babu alamar kiransa Da asuba ma haka taita gwada kiransa Amma yaqi dauka, hankalinta duk yatashi, haka taita zarya a falo Ko Hajiya zata futo Daga dakin Alhaji tasanar da ita halin da ake ciki, Amma Shiru Hajiyanma yau Bata futo da wuri ba Hakade Takoma dakinta Amma duk hankalinta atashe Al'amarin Imran kuwa yana gama kuka anan zazzabi Mai mutuqar zafi yarufeshi, Kuma Har Zuwa lokacin kansa yana kan gwiwarsa yaqi dago da kansa, Shiru babu magana, daya rufe idonsa su yake gani ahalin daya gansu jiya Sai wajan Karfe Tara Hajiya tafuto Daga dakin Alhaji, tasan Cewa Iman Da mamy Suna nan zasu gudanar da abinda yakamata ayi break fast dashi Dining ta kalla taga komai yana nan anshirya, Amma Kuma babu kowa, cikin ranta tace to lafiya? Kai tsaye tayi cikin dakinta, tuntube tafara yi da kayan da Imran ya hargitsa mata, da mamaki ta sake Kallan dakin nata Komai a hargitse, idontane yakai kansa, atsugunne taganshi, dasauri ta qarasa wajansa tafara tattabashi, tace Imran lafiya? Shiru yayi babu magana Gabanta na faduwa tasake Cewa Imran nashiga uku me yake damunka, nanma Shiru Imran babu magana To itade tasan Cewa Imran bashida aljannu, Amma gashi yau yanayin Abu Kamar na masu aljannu Daqyar tadago masa kansa tace Imran me yake damunka? Fadamin menene yasameka? Duk ta rude tanata tambayarsa Ahankali yace Hajiya zuciya ta zafi takemin, inajin kaina Yana barazanar tarwatsewa Batace dashi komai ba, tafice dasauri tayi dakin Alhaji, domin tasanar dashi halin da ake ciki Tare suka dawo dakin itada Alhaji, Alhaji yana kallansa yasan Cewa babu lafiya, fuska babu alamar wasa yace Kai taso kazo nan, yafadi haka tareda Juyawa Ahankali yatashi yana dafe da kansa dake masa ciwo yabi Bayan Hajiya d Alhaji suka futo falo Adede lokacin mamy ma tafuto, tashin hankali qarara ya baiyyana a fuskarta tace subhanallah Hajiya meyasa meshi? Hajiya tace wallahi Hajiya fati Nima bansaniba, kin ganshi nande Zama sukai gaba dayansu a falon, Kan Imran aqasa, idonsa jajir alamar yaci kuka yagaji Alhaji ya debeshi yace Imran Ahankali yadago da kansa ya kalli Alhaji, nan take hawaye suka zubo Masa, saboda yasan Cewa dole zasu so Jin dalilin dayasashi kuka Alhaji yasake Cewa menene yake faruwa Imran? Fadamin menene yasaka kuka? Batare daya goge hawayen idonsa ba yace bros ne.... Ya.. Ya... Alhaji bros.. Ne, kuka ne yaci karfinsa, kuka wiwi Kamar mace yakasa qarasa maganar dayake son fada Mamy najin ance bros ne gabanta yafadi, yau tashiga uku me baby yajawo musu a gidan nan? Alhaji yace me bros din yayi? Adede lokacin Bilkisu tayi sallama tashigo cikin falon tana janye da trolley dinta Gaba dayansu suka zuba mata ido, Hajiya ce tace Bilkisu sannu da Zuwa, Ahankali taqaraso cikin falon jikinta asanyaye ganin duk sun zubawa Yaya Imran ido Aqasa ta tsugunna ta gaida su, miqewa tayi zatayi ciki Alhaji ya dakatar da ita da hannu Yasake Kallan Imran yace inajinka me dan'uwan Naka yayi? Hawaye ya share yayi Shiru baice komai ba, ai abinma da nauyin fada Alhaji ya Jijjiga kansa yace owk yayi ma kyau, sannan yadubi Bilkisu yace Bilkisu Gara da Allah yakawoki Adede wannan lokacin, dama Koda bakizo yauba, inada niyyar nemanki, inaso inyi Miki tambaya ta farko Kuma ta qarshe, inaso ki sanar Dani gaskiya Idontane ya fur futo alamar tsoro, itakam dama batazoba Alhaji yana ganin yanayinta yasan Cewa akwai wani abun aqasa, yace Bilkisu menene yake faruwa tsakanin Aliyu da Imran da yayarki Fatima? Tare kuke da ita, kinsan komai nata tasan komai naki, danhaka Ina so kisanar Dani abinda kika sani dangane dasu Daqyar tadago idonta, ta kallesu Yaya Iman tajawo mata masifa yau, cikin in-ina tace Alhaji... Alhaji gaskiya akwai abinda yake faruwa wanda Baku saniba Sunkuyar dakai mamy tayi, domin kuwa abinda take kokarin boyewa yau yagama tonuwa, Bilkisu taci gaba da Cewa, Yaya Iman Da yayi Aliyu Suna soyaiya tun muna Ghana, maganar gaskiya itace yayi Aliyu Baisan Cewa budurwar Yaya Imran bace,...... Tas takwshe komai tasanar dasu Tana gamawa Alhaji yasaki nannauyar Ajiyar zuciya Hawaye suka sake tsinkewa afuskar Imran Alhaji yacewa Bilkisu jeki kiramin yar'uwarki, Bilkisu na tafiya, Alhaji yadau waya yakira Aliyu Kana inane? Alhaji Ina tareda abokan aikina ne To kazo gida kasameni yanzu yanzu Aliyu Bai kawo komai aransa ba yace to Alhaji gani nan Iman najin bayanin Bilkisu ta Dora hannunta akanta tace nashiga uku Haka suka futo gaba dayansu Zuwa falo, kansu aqasa suka nemi waje suka zauna Shiru falon yayi, kowa yana jiran yaji hukuncin da Alhaji zai yanke Bai wuce minti ashirin ba Aliyu yashigo falon, da mamy yafara hada ido Ta wurga Masa harara Akusa da Imran yazauna, Ahankali yace Alhaji gani Shiru Alhaji yayi yazuba musu ido yana kallansu, Hajiya tasaki Ajiyar zuciya tace Alhaji kayi Shiru bakace komai ba Alhaji yace to hajiya me zance musu? Ai abin nasu abaiyane yake, AI ABIN BROS NA BROS NE ( πŸ˜‚πŸ˜‚) Yadubesu yace bahaka kuke fadaba? Barrister yayi Shiru tareda goge hawaye Aliyu najin haka aransa yace shikkenan Mai faruwa tafaru, nasan Bros yasan komai yanzu Ganin duk sunyi Shiru ne ya Alhaji yadubi Iman tace Fatima Ahankali tadago da kanta tace na'am Alhaji yace Fatima kifadamin wa kike so tsakanin Aliyu da Imran? Sai lokacin takai kallanta garesu, kowa yana zaune kansa aqasa babu me kallanta acikin su, zancen zuci tafara, Yaya Imran me sona me kaunata, me bani dama inyi duk abinda nakeso, Dan Hajiya, matar data riqeni tasomu fiye da yayan cikin ta Aliyu me sona Mai kishi na, wanda a dalilin soyaiyar dayakemin yakamu da cuta, yazabi yayi jinya Akan dan'uwansa yasan Cewa yana sona Innalillahi ni Iman WAZAN ZABA??? (fan's Iman tana neman amsa, nide nace... um Bari nayi shiru🀭🀭de) Kuyi hakuri da wannan bayawa, da ba zanyi typing din Bama to nasan dole wasu jirani shiyasa nayi wannan, fatana ku kasan ce Dani, Ina yinki sosai my fansπŸ’ƒπŸ’ƒ Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 19 (Agurguje pls wlh nagaji da typing dinnanπŸ˜”πŸ˜”πŸ˜”) Dukansu su biyun ne suka dago kansu kowa yazuba mata ido yanaso yaji wazata zaba acikinsu Tashin hankali ne qarara Akan fuskarta, yaufa ake yinta, Ayau Kan tayi DANA SANI (my first novel) Akan Yin soyaiya ma baki dayanta Cikin kuka tatashi tayi cikin dakinta aguje Kowa ido yazuba mata, babu wanda yayi yunqurin kiranta, mamy ce tace Ai Yaya daka janye wannan tambayar ma, rikici ne kawai irinna Aliyu, domin kuwa tun farko muna Switzerland dayazomin da maganar Naja masa kunne, Kuma nayi masa gargadi akanta, kallanta takai Kan Aliyu taci gaba da Cewa yaro ne kahaifeshi Amma baka haifi halinsa ba Hajiya tace ai Hajiya ni duk banga laifinsu ba, gaba daya laifin yanakan Iman, meyasa tasan da haka tun farko bazata futo tayi bayaniba bare asan ta inda za'a warware matsalar Billy da kanta yake qasa Ahankali tace wallahi Hajiya Yaya Iman batasan sunada alaqa ba, kawai gwadash... Rufemin baki, aiduk bakinku daya, Hajiya tatare mata zancen kafin taqarasa fadar abinda yake faruwa Alhaji yace komai de ya lalace Hajiya tadubi su Aliyu tace toku yanzu sai daya yahakura yabarwa daya, Tunda bazaku Iya auranta ku biyu ba Alhaji yace babu wanda zai hakura acikinsu, ita fatiman data kulasu duka su biyun ai dole cikin ranta akwai wanda takeso, danhaka dole itace zata fidda kanta Daga wannan sarqaqiyar , ba kukaba kome zatayi saide tayi" Ya kalli Bilkisu yace tashi kibita dakin kutaho tare Ahankali Bilkisu ta miqe tayi cikin dakin na Iman, ita kanta yau ta tausayawa yar'uwar Tata, wannan masifa Dame tayi kama Tana Zuwa dakin taganta Akan gado ta kifa kanta Akan Fillo Ahankali ta qarasa kusa da ita tace Yaya Iman, al'amarin nanfa yayi tsamari, Alhaji yace kitashi muje Shiru Taji Tasake Cewa Yaya Iman fa, kinajina kinyi Shiru Still shirun Tasake ji Dasauri Takai hannunta jikin Iman tafara kokarin dagota Yanda ta dagota haka Iman ta koma Kan gadon ta zube yaraf Jijjigata tafara yi tana fadin Yaya Iman! Yaya Iman!! Amma Shiru Iman babu alamar numfashi atare da ita Gaban Bilkisu yabada dam Ido ta zazzaro tayi falo aguje tace Hajiya! Hajiya!! Hajiya!!! Yaya Iman ta mutu Wallahi Bata motsi Gaba daya ta rikice Kamar ma Bata cikin haiyyacinta, kawai dakin take nunawa da hannunta Ai sunajin haka gaba dayansu sukai cikin dakin harda Alhaji Hajiya da mamy duk sun rikice, Bilkisu kuwa kuka take wiwi Qirjin sane yake masa ciwo, nan take Tari yake shirin Zuwa masa, yasan Cewa idan yabari yayi tarin abinda zai biyo Bayan tarin zai sake sakasu cikin wani halin, danhaka ya danne yaqi yarda yayi Barrister kuwa kawai kallanta yake, tabbas idan ya rasata to ya tabbatar yarasa farin ciki Har abada Alhaji ne ya tsugunna dede inda take kwance ya duddubata yace kubani ruwa Suma tayi Dasauri Billy ta Bude fridge din dake cikin dakin nata ta dauko gorar ruwa faro, tabashi Ahannunsa ya zuba ruwan sannan yashafa mata afuska, Amma Shiru kakeji Ko motsi batayi ba Haka Hajiya da mamy ma suka Matso kowa yayi Yan dabarunsa Amma Bata farfadoba Bilkisu na ganin haka Tasake fashewa da kuka tace nashiga uku shikkenan Yaya Iman Hajiya da gabanta yake faduwa tajuyo cikin tashin hankali tace Wai Bilkisu Zaki mana Shiru Ko saina dokeki Hannu tasa abakin ta, Amma hawaye ne yake tsiyaya a idonta Alhaji kansa yashiga tashin hankali, Amma Bai nuna ba, gudun sake shiga tashin hankalinsu Duban zaratan samarin nasa yayi yace ku dauko ta muje asbiti Ai Kamar jira suke atare suka Kai hannu zasu dauketa Hannunsu ne ya bigi na juna, nan take ran Barrister yabaci ganin karfin Hali irinna Bros dinsa Shima Aliyun Haushi yaji, Yama za'ai yarinyar yakesan auranta, yake kishinta fiye da komai Amma Bros yataba jikinta Kowa fuska atamke, Kuma sunqi Kallan junansu Hajiya tace Alhaji da daukarta kayi muka tafi, su idan sun gama quncin sa biyo mu Daga baya Duk halin da ake ciki Bai Hana Alhaji murmusawa ba, ganin kishi qarara a idan 'ya'yan nasa Jin haka yasa Aliyu matsawa gefe sai kumburi yake Shima barrister cikin bacin rai ya dauketa suka tafi asbitin Motoci biyu sukayi, daya Hajiya da Bilkisu Abaya, sai Alhaji dakuma Aliyu dayakejan motar Dayar Kuma mamy ce Abaya ta Dora Kan Iman Akan cinyarta, sai barrister dayake driving Kai tsaye suka nufi private hospital na khadija memorial Suna faka motar, Imran ya dauketa, gaba dayansu suka shiga cikin asbitin, kowa yagansu yasan Cewa lalle wannan marar lafiyar tanada mutuqar muhinmanci awajan su Likitoci na karbarta aka kaita shiga da ita wani daki, mamy tace doctor bazamu Iya shiga ba? Kuyi hakuri Hajiya kubamu Minti ashirin, insha Allah zata samu lafiya, ku kwantar da hankalinku Zama Bilkisu tayi ta rafka uban tagumi, Aliyu kuwa zagayawa yake awajan, gaba daya hankalinsa atashe yake Imran ma zama yayi Daga can gefen Bilkisu, yariqe kansa dake yi Masa masifar ciwo da tafin hannunsa Suna zaune babu me Cewa dan'uwansa uffan, likita ya futo yace zaku Iya shiga ku ganta, zanje office na dawo Zuwa wannan lokacin hakurin Aliyu yagama qarewa, yamatsu yaga halin datake ciki Danhaka doctor na wannan maganar yasa kansa cikin dakin Suma sauran suka rufa masa baya Oxygen ne amanne ahancinta, shine yake temaka mata wajan janyo mata numfashi Dede kanta Aliyu yatsaya, yazaba mata ido, Wai fatimansa ce wannan halin, yarinyar da Ko zazzabi take baya samun isasshen bacci Bacci take tana numfashi Ahankali, gashin idonta dasuka hadu sai sukai kyau, fuskarta tayi fayau lokaci daya Ahankali Alhaji yace Allah Yarufa asiri Dukansu suka ce amin Turo dakin doctor yayi, yashigo da file Ahannunsa ya kalli Alhaji yace Alhaji Kaine mahaifin yarinyar Nan? Eh nine, inji Alhaji Glass din idonsa yacire yace haba Alhaji, Yaya zakuyi sakaci da rayuwar yarinyar ku, kun Barta tana Yawan tunani Gashi yanzu Har Hakan yataba Zuciyar ta Gaba dayansu suka razana dajin furucin doctor, atare suka ce zuciya likita!!!!! Jijjiga kansa yayi yace qwarai ma kuwa, Zuciyar ta ta kumbura, Kuma idan bakuyi gaggawar nema mata magani ba gaskiya zaku Iya rasata Hawaye ne suka wankewa Bilkisu fuska, sai yau taqara tabbatar wa tana son yar'uwar ta, Allah yasa karta tafi Kamar Yanda umma tatafi tabarsu Ahankali Aliyu ya Dora hannunsa Akan Zuciyar sa, wani irin radadi yakeji awajan Idanun barrister jajir alamar tashin hankali atare dashi Gumi Alhaji ya share yace yanzu doctor Yaya za'a yi? Konawane zan Iya kashewa inde yarinyar Nan zata samu lafiya Doctor yace Alhaji abinda zan Iya fadama shine a fita da ita qasar waje, India sunada qwararrun likitoci, inde ankaita insha Allah za'a samu abinda akeso Tunani Alhaji yafara, yana Kallan dakin, afili yace India India, alhmdlh ai kuwa akwai wani babban doctor dayake aiki a India Dan Bauchi state, inaga kawai Gara aturata wajansa Doctor yace to Alhmdlh, Allah yasawaqe, duk Yanda kukai dashi kusanar Dani Ina office, yajuya yafita Alhaji ya dubi Aliyu yace kiramin tsohon gwamnan bauchi daddy (BURINAH my second novel) Kafada masa ya turo ma number abokinsa jabir zamu tura masa da Fatima Wayarsa yadauka ya kirashi, Saida Kiran ya kusa katsewa sannan aka Daga, Daga dayan bangaren Aka Daga, the chief of air staff katafi Switzerland kazauna, Kuma Daga dawo Nigeria dinma kabuya Ahankali Aliyu yace daddy share wannan mgnr, yanzu de muna buqatar number jabir, zamu tura Masa da marar lafiya ne asbitin su OK Bari naturoma Aliyu na kashe wayar, daddy ya turo masa da number, Kiran jb sukayi nan da nan yafada musu Yanda zasuyi tsare tsaren tafiyar Zama sukai Dukansu a dakin kowa yayi Shiru yana Kallan Iman datake kwance Na'urar datake kusa da gadon Iman ce tayi qara, nan da nan numfashinta yafara Sama Sama Gaba daya hankalinsu yasake tashi, dasauri Aliyu yayi waje yana Kiran doctor... Doctor.... Kan Imran yasara, ganin halin datake ciki, kansa yariqe yana ganin dakin yana juya masa, bayasan yarasa Iman, jiri ne yadebeshi nan take yazube awajan Salati su Hajiya suka fara , Dukansu sukayi kansa, ga Iman datake wani irin numfashi Alokacin Aliyu yashigo tareda doctor, Gabansa ne yafadi, ya kalli Iman yaga abinda take, ya kalli Bros dinsa akwance aqasa Ko motsi bayayi Tashin hankali ya ziyarceshi na nan take, yayi dibi dibi Yama rasa wajan wa zaije Kawai saiyayi wajan Imran yafara Jijjiga shi, bros... Pls katashi, zata warke please bros.... Katashi... Yana Jijjiga shi yafara Tari, Alhaji ya janye shi, yana buga masa bayansa, yace Aliyu jeka Sha ruwa kadena wannan tarin Kafin yatashi yasha ruwan yafara Aman jini Tashin hankali,Zuwa wannan lokacin Alhaji da kansa jikinsa yafara sanyi dangane da al'amarin yaran Nasa Yana Tari jini yana fita Daga bakinsa, yadanne kirjinsa da hannunsa guda daya, Kuma still Jijjiga Imran yake da dayan hannun nasa, Bai damu da halin dashi kansa yake cikiba Mamy kuka, Hajiya kuka, Bilkisu kuka Dakin duk ya kaure da kuka Kamar wanda akai musu mutuwa Likitan dayaje Kan Iman ne yakira wasu doctor's din akai Kai Aliyu da Imran wani dakin Haka yazauna yana basu baki Akan suyi hakuri, Tunda anyi sa'ah abin nasu yafaru ne Suna asbiti Haka su mamy suka wuni a asbitin nan jugum jugum Farhan ma Yazo yakawo musu abinci Amma babu wanda yakula abincin Har dare *** *** *** Washe gari Hajiya ce awajan Aliyu tareda Farhan, mamy Kuma tatafi dakinda Imran yake itada Bilkisu Alhaji ne kawai yake zirga zirga domin tura Iman India Dayake abin nasune na manya a ranar aka turata babban asbitin India APOLLO HOSPITAL Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 20 Alhaji Saida yayi waya da jabir, jabir din ya tabbatar masa Cewa zasuje airport sujira Zuwan su Iman sannan sannan hankalinsa ya kwanta yace su kula da ita dakyau, ayi mata duk abinda ya Kamata inde kudi ne babu damuwa, Suma zasu taho Daga baya, saboda yanzun hankalin gida ba'a kwance yakeba Asbitin yakoma domin yaga halin dasuke ciki Dakin da aka kwantar da Aliyu yashiga, yana kwance yana bacci Amma Leda ce ajikinsa anayi masa qarin jini Hajiya idanu sunyi fari fat saboda kuka, tariqe carbi ahannunta tace Alhaji sannu da dawowa Waje yanema yazauna sannan yace Yauwa Hajiya, Yaya jikin nasu? Jiki dasauqi, ai Aliyu ma Naga yana daurewa, saboda yana cikin hankalinsa Likitan yadaura masa jinin, yace idan kadawo ma musameshi a office To Alhmdlh, Allah yaqara afwa, Itama Fatima sun tafi, angama komai insha Allah za'a dace, Daga baya saimu bita idan wadannan din sukaji sauqi, Hajiya Kinga abinda nake fada Miki Ko? Shiyasa nake Cewa kisa ido sosai Akan yaran nan, yanzu Kinga bamusan me yake faruwa atsakaninsu ba inda Allah yayi abin Yazo da qarar kwana haka duk zamu rasasu Hakane Kam Alhaji, ai abin nasu da mutuqar daure Kai yake, bazaka taba Cewa akwai wani Abu atsakaninsu ba Miqewa yayi yace muje muga jikin Imran din Daga nan saimu qarasa wajan doctor din Binsa tayi Abaya suka fita, akabar Farhan da Aliyu a dakin Dakinsu Imran sukaje, anan suka tarar da mamy da Bilkisu, Alhaji yace yajikin dannaki Fatima Cikin jimami tace jiki da sauqi Yaya, yanzu doctor dinma yagama dubashi, yace dazaran yafarka ayi saurin bashi abinci da wannan magungunan, sannan Kuma kada abarshi yayi tunani To Allah de yabasu lafiya, Amin Yaya Yakamata muje muga Likitan nan To Yaya Bilkisu suka Bari a dakin su Kuma suka tafi wajan doctor Suna Zuwa office din yabasu waje suka zauna, sannan yadago da kansa yace wato Alhaji abinda yake bani mamaki dakuma daure min Kai dangane da yaranka shine Dukansu cuta dayace take damunsu Shi Imran Abubakar Bilal shine me hawan jini, but Aliyu Sa'ad Bilal am sorry to say yanada daukeda ciwon zuciya Gaban mamy ne yafadi, nan take kuka Yazo mata, dama tasan dole za'a Rina, tun farko Saida baby yace mata tayaya zai samu lafiya Bayan yarinyar dayake rashin lafiya akanta tana zaune a gidan? A lokacin batayi tunanin cuta zata kama mata dannata qwaya daya tal a duniya ba, da Washe gari zasu hada nasu yanasu su tafi Abuja Hajiya ma hawaye take sharewa tace Innalillahi mukan munga ta kanmu, Allah kabamu ikon cinye wannan qaddara Likitan yace Hajiya ba kuka zakuyi ba, Addu'ah suke buqata, ni kaina nayi mamakin abin, ita yarinyar tana gab da kamuwa da ciwon zuciya, shi wannan hawan jini, shikuma dayan already yanada rashin lafiyar, saboda abinciken danayi Nagano ciwon yadade ajikinsa, Tunda Har abin nasa yakai limit din dayake tarin jini Amma insha Allah zamuyi Iya bakin kokarinmu muga sun samu lafiya Yadubi Alhaji yaci gaba da Cewa Alhaji ka kwantar da hankalinka yaranka duka zasu samu lafiya, saide shawarar dazan Baku zatasa lafiyar su tayi saurin samuwa idan kunbi Gumi Alhaji ya share, yana ganin yatura Iman India, matsalar sa zata Ragu, ashe ba'a Rabu d bukar ba anhaifi Abubakar Yace likita Ina jinka menene shawarar taka? Yauwa shi Imran adena barinsa yana tunani, kome zai faru kada abarshi shi kadai yana tunani, shi Yawan tunani shine tushe na hawan jini Sannan akula da bashi magungunan sa Shikuma Aliyu already yanada ciwon zuciya, dole za'a kiyaye abinda zai Bata Masa rai, a dinga yi masa abinda yakeso, insha Allah za'a dace, muma Kuma zamuyi bakin kokarinmu, sannan Kuma zaku Iya barin mutum daidai awajan su ku koma gida, zamu basu sauran kulawar data dace dasu Daga mamy Har Hajiya babu me Bawa dan'uwansa hakuri, to kowa share hawaye yake, haka suka futo Daga office din Alhaji yace Wai Hajiya Dame kukeso naji ne? Kunsani agaba kunamin kuka, yanzu fisabilillahi idan sauran yaran suka ganku su Kuma saisu fara hauka Kenan? Haba , fuuuuu yakada babbar Riga yayi dakin da Imran yake Ganin Alhaji yayi musu fada ne yasa suka daina kukan, suka bishi dakin Suma Alhaji yana Zuwa dakin Yadubi Bilkisu yace kikula dashi, zamuje gida muyi wanka Ahankali tace to Alhaji Allah yakiyaye Dakinda Aliyu yake suka koma, nanma suka ce Farhan yakula dashi, zasuje gida su shirya Haka suka futo Daga asbitin sukayi gida, wannan Karon Kam, Alhaji ne da kansa yajasu amotar *** *** *** Yaya kakejin jikin Naka? Jiki da sauqi doctor, nifa banajin komai, saide kawai inajin Tari yanadan tasomin kadan Eh gaskiya ne soja, wato nanma de sai an nuna jarumtar, to kadaure karkayi tarin Koda kanaji din, sannan karkayi wasa dashan maganinka Cikin Murmushinsa Mai tsada yace babu damuwa doctor, Bayan tarin babu abinda nakeji , zan Iya Zuwa Naga jikin Bros Dina? Farhan dake gefe yayi sauri yace haba Yaya Dan Allah kabari kasake Jin sauqi saikaje Murmushi doctor yayi yace eh gsky de Hakan zaifi sannan yafita Doctor na fita me aikin su Hajiya tazo driver yakawo ta, takawo musu abinci da abubuwan buqata *** *** *** Tana zaune akujerar dakin tafada duniyar tunanin yar'uwar ta, Ko tana wanne Hali yanzu oho Allah de yabasu lafiya baki dayansu Tana wannan tunanin taga yabude idonsa, Ahankali dasauri taqarasa bakin gadon nasa tace sannu Yaya, mekake buqata yanzu? Babu inda yakema ciwo? Haka taita jero Masa wannan tambayoyin Kansa yadafe da hannunsa cikin rintse ido yace kaina kemin ciwo sosai To Bari nakira likita, tafice da gudu Daga dakin Tare tadawo da doctor yaduba shi yace a bashi abinci yaci da magungunan sa, zai dawo yayi masa allurai Doctor na fita, dakin yasake yin Shiru, ita Bilkisu ba gwanar rawar Kai bace irin Iman, sannan ita bawani sabawa tayi dashi ba Kamar Yanda Iman tasaba dashi duk taga yayi kwarjini, tarasa me zata Masa, wayyo Allah itakam meyasa Alhaji yace ta zauna da Yaya yau, Allah yadawo dasu gaskiya Suna Zuwa zan koma gida Tunawa tayi da maganar doctor, Ahankali tatashi tazuba masa abincin, jallop din taliya ce da tsokar Nama aciki manya, sai turiri abincin yake, tazuba acikin flet tasa spoon Agefen sa ta zauna tace Yaya ga abincin Kaci, kaji doctor yace zai dawo yayima allura Ahankali yadauki spoon yafara cin abincin, cokali biyu yayi yace naqoshi Haba Yaya, Dan Allah kaqara Ko kadan ne Kansa yakawar gefe fuska babu alamar fara'ah yace naqoshi nace Kallan abincin tayi, Yama za'ai yace yaqoshi, kawai de damuwa ce tasa Baisan cin abincin Diba tayi cikin nutsuwa tanufi bakinsa d abincin Kallan ta yayi, yaushe yafara wasa d Bilkisu dazatai kokarin bashi abinci abaki? Kota manta Cewa shi ganin qanwarsa yake mata? Koda yaushe gani yake batada banbanci da Farhan da zainab auta Shiyasa ma Bai wani saki jikinsa da itaba bare harta Raina shi Kawar da kansa yayi, Jikinta ne yayi sanyi Ahankali tace please Yaya Haka yadaure take bashi abincin, sai wani Bata fuska yake Kamar tana bashi magani , Saida ta tabbatar ya qoshi sannan tadau tissue ta goge masa bakinsa, tafice Daga dakin Shide Binta yake da kallo kawai, yana aikin Bata fuska *** *** *** Washe gari Bilkisu tahada yanata yanata tatafi gida, itakam bazata Iya wannan Zaman jinyar ba, duk mutum atakure, shikkenan saide ta zauna tayi dunkum itaba kurma ba, Bayan ance yadena tunani, Amma bazai yimata magana ba saide ya shareta yana aikin tunani, wallahi Gara Hajiya Ko mamy sudawo su zauna dashi, bazata iyaba Ko Farhan dayake kula da Aliyu batayiwa sallama ba tayi gida Shi kuwa Farhan kalau suke fira da Aliyu, Kamar ma ba marar lafiya ba, sosai yake Daurewa Akan komai Duban Farhan yayi yace jeka ganomin jikin Bros kaji Farhan Zuciya daya Farhan yatafi dakin Imran, yatarar dashi Ana qara masa ruwa Amma bacci yake Danhaka yajuya dakin dasuke, yana Zuwa yaga wayam babu Aliyu babu labarinsa Hankalinsa ne yatashi, nan take yadinga nemansa daki daki, yafuto harabar hospital din nanma babu Aliyu babu labarinsa, kusan minti talatin yana dube dube Wata dabara ce tafado masa nan take yadauko wayarsa ya kirashi, bugun farko yadaga, cikin tashin hankali Farhan yace, Yaya Aliyu kana Ina ne sai nemanka nake? Murmushi yasaki Mai aji yace Farhan natafi India, idan kahada kayanmu kakoma gida kasanar dasu Alhaji Cewa Nina wuce India Sharhi please πŸ™πŸ» Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 21 Daria ce takama Farhan, yace to Yaya, tareda kashe wayar Dakinda suke yakoma yahada komai, yaje Har office din doctor yace to likita nizan wuce gida, mun sallami kanmu Doctor yace ban ganeba, kamarya kun sallami kanku? To likita majinyacin ya wuce India wajan budurwar sa Murmushi doctor yayi, Zuwa yanzu Kam yagama Gane Cewa duk saboda soyaiya ne suka shiga wannan halin Toshikkenan, idan kaje kagaida Alhajin Farhan nafita ya wuce dakin da Imran yake, yana Zuwa yaganshi yana bacci, Amma Kuma dakin babu kowa, tunani yayi Cewa may be Bilkisu tana toilet, danhaka yaja dakin Yarufe tareda fita *** *** *** Hajiya na zaune a dakinta tayi Nisa cikin tunani, yanzu saboda soyaiya yaransu Har uku Suna kwance a asbiti, saboda soyaiyar mutum daya Babban danta datake ji dashi, yaro me kazar kazar, marassa damuwa Arai, shine kwance a asbiti harda su hawan jini, Bata fatan ace Ko zazzabi ne yasamu Imran dinta, Amma yau gashi akwance asanadin soyaiya Shiru tayi tana neman mafita Wani tunani ne yafado mata, idan Dukansu maza biyun Akan mutum daya ne suke wannan jinyar, Tome zai Hana tasamowa wannan family nasu mafita ta wata hanyar? Bilkisu yar'uwar Iman ce, tare suka tashi, tanada nutsuwa da hankali, babu abinda Iman zata fadawa Bilkisu ta fannin diri na hallita kokuma sura Inda halinsu ya banbanta kawai waje dayane, Iman akwai daukar wanka, tana saka kayaiyaki na kece raini, sannan ta kasan ce mutum ce mai nuna kyanta afili, wanda Hakan yasamo asali ne ta wajan Imran daya dorata Akan wannan turbar Sabanin Bilkisu datake shiga ta mutunci, gakuma sanyin Hali, kwata Kwata batasan damuwa shiyasa ma Bata cika shiga sabgar Yan gidan ba, itade Barta da zeey auta Bilkisu tayi ta Ko wanne fanni, saide Kuma Kash Shu'aibu yayi musu katanga da ita, saboda wani dalilin sa can marar tushe Tashi tayi tana zagaye dakin, afili tace wannan Karon Kam Shu'aibu saide kayi hakuri, inaji Ina gani bazan rasa yarona ba, domin kuwa idan aka biya ta Alhaji dasunan Wai Iman saita zabi daya acikinsu, tofa Iman batada niyyar zaba, saide Daga qarshe Alhaji yace kowa ya hakura d ita Da wannan tunanin ta futo falo, turus ta tsaya ganin Bilkisu kwance akujera tana danna waya Tace a a yaushe kika shigo gidan bansaniba? Dago kanta tayi tareda ajiye wayar tace Hajiya wallahi na Dade da Zuwa, gajiya nayi da Zaman Shiru haka ba dadi A a kamarya gajiya kikai? Cikin shagwaba tace Hajiya Allah nikam nagaji, Wani yaje kawai Sallamar Farhan ce ta tsaida musu maganar dasuke Hajiya tace a a, kaikuma yanaganka da Kaya ahannu? Wai meyake damun kune? Duk kun baro marasa lafiya a asbiti kun iyo gida Zama yayi Akan kujera yace Hajiya ai ni mun sallami kanmu, yayi ya fece India wajan Iman, to dawa zan zauna? Shiyasa Nima nayo gida, Kuma yace afada muku shiya wuce India Murmushi Hajiya tasaki, ta kwalawa mamy Kira, futowa tayi tana daura dankwali tace Hajiya ya akayi? Wai Daga kwanciya bacci ya daukeni, kinsan jiya bamu rintsa ba Hajiya tace kinji Wai Aliyu yatafi India, shine Farhan yadawo gida da kayansu, Wai afada mana shiya tafi, ita Kuma wannan tagaji ne shine saboda tsabar sakarci tabarshi a asbitin ita Kuma tayo gida Tafa hannu mamy tafara tana Cewa, la'ilaha illallahu, yanzu shi Haidar dinne yakama hanya yatafi, wato Bai duba rashin lafiyar dayake ba Hajiya tace to yaza'amusu, ai sai hakuri Farhan ne yace nikam nagaji, Bari inje daki nakwanta na huta, ya kalli Bilkisu yace ainaje dakin naku bangankiba, sai Yaya ne kawai yake bacci, jinakema kina toilet ashe kina nan Wallahi gajiya nayi nataho gida, inji Billy Mamy tace to yanzu waye zai zauna da Imran din Bilkisu? Dasauri Hajiya tace nice zanje mana Hajiya fati, Tunda ita bazata Iya zamanba aini saina dauki mayafina inje in zauna dashi Murmushi mamy tayi data Gane gatse ne Hajiya takama Bilkisu Tana zama akujera Itama, tace a a Hajiya, zata Koma itama, duban Billy tayi tace Bilkisu yata tashi ki shirya, kikoma kinji, karya tashi Kuma yanemi wani Abu gashi bakya nan, Bari insa Mai aiki tayi muku abinci, saiki tafi muku dashi Kamar zatai kuka tace to mamy, tareda tashi tayi dakin Iman, domin shiryawa *** *** *** Kai tsaye Abuja ya wuce, Saida yagama abinda zaiyi sannan yatafi India Baisha wahala ba wajan Zuwa asbitin, Kai tsaye wajan jabir yanufa, Saida suka sake gaisawa sannan suka nufi Dakinda take ciki Tana kwance tana bacci, qarin ruwane ajikinta, Zuwa yanzu babu oxygen Din ancire mata shi, saide tana numfashi ne Ahankali, fuskarta fayau Dakin babba ne, da kujera 2seater sai qaramin fridge, da gadon datake kwance, komai na dakin kalar light blue ne Har kujerar, sai wata qaramar kofa agefe da alama toilet ne Har gaban gadon sukaje, ya sunkuya ya zuba mata ido, Kamar wanda yakeson gano wani Abu Sannan yadago ya dubi jabir yace, Zuwa yaushe ne zata farka ne? Aita farka dazu, Bayan ankaita tayi wanka ne, akayi mata allurar bacci, sai nanda awa shida zata tashi, insha Allah OK to shikkenan babu damuwa, Nima yakama ta muje Naga likita, ayimin abinda yadace inyaso saina dawo latter OK ba damuwa muje Fita sukai Daga dakin nikuma na iyo Nigeria *** *** *** Tsaf ta shirya laffaya, ta futo falon zata tafi asbiti Hajiya ta kalleta tace yanzu keda zakiyi Zaman jinya, yaushe Zaki saka Kaya masu nauyi, maza koma daki ki sake shiryawa Kamar zata fashe haka Takoma dakin, tana cire kayan tana mita, Tunda nadawo Daga katsina ban zaunaba, Daga wannan matsalar sai wannan, haka tasaka doguwar Riga ta atamfa, Daga Sama dinkin yakama kirjinta, Daga qasa Kuma abude take Dan qaramin mayafi tadauka tayafa, tana Kallan kanta amadubi tace Tunda nasaka babban Kaya ance incire, yanzu Kuma nasaka qarami nasan Shima Hajiya dawo Dani zatayi tace Ina tafe tsirara Kamar Yaya Iman Hakade ta futo falon, tadauki kwandon abincin tace Hajiya natafi ga mamakinta saitaga Hajiya tayi mata Shiru, batayi mata fada Akan shigar datayi ba, Tunda tasan bahaka tasaba fitaba, Dade Iman ce Saima Cewa datayi, Wai miye kike ta Bata raine? Ko asbitin ne bakya son Zuwa? Kamar tasan Bilkisu Dama jiran qiris take, nan take tace to hajiya shi yayan ne saiyayi banza ya qyaleni, dazu da safe abincin Dana bashi ma daqyar yaci, sai hararata yake, ni wallahi Hajiya dande kince saina koma ne Murmushi Hajiya tayi tace, haba Bilkisu, keda dan'uwanki? Lallabashi zakiyi, idan yaqi ci saiki lallasheshi kibashi, idan Kuma kin gwada lallashin yaqi saiki zare masa ido ki Bata fuska, idan bazai ciba, saiki qyaleshi Cikin Zaro ido tace Hajiya yayan zan zarewa ido? Um Hajiya sai anjima Tadauki kwandon tayi gaba, cikin ranta tana mita ita kadai taga alama Hajiya sotake taja mata fada awajan Yaya Imran, inba hakaba harda Cewa in lallabashi, in rarrasheshi, saikace wani jariri Hajiya kuwa Daria ce takamata, da niyya tabarta tafita da wannan kayan, saboda Hakan yana daya Daga cikin abinda Imran yakeso, wato daukar wanka, afili tace kuje de can ku qarata *** *** *** Ga magungunan Naka, Amma inaga da kazo munje gida gobe da safe idan Allah yakaimu saimu dawo kafin lokacin ma tafarka Cikin Murmushi yace no doctor jabir karka damu, zanjira harta tashin insha Allah, zan taho gidan Daga baya ok to saimun yi waya, inji jabir tareda fita Daga dakin Ajiyar zuciya yasauke Bayan fitar jabir, ya ajiye magungunan sa, sannan yanufi fridge din dakin yabude, acike yaganshi da kayan marmari da ruwa sai lemuka, yasan wannan duka aikin doctor jabir ne Lemon kwali yadauko guda daya, yadau cup yakoma Kan kujerar dakin yazauna, idonsa akanta yafara ballar maganin sa yanasha Saida yagama Sha sannan yatashi yakoma Kan gadon datake yazauna Agefen gadon, idanu yazuba mata yana jiran tafarka Haka yayita zama Shiru shi kadai, da lokacin sallah yayi yatashi yayi sallah yakoma, yana zaune harya fara gyangyadi, Amma Bata farka ba, kansa yadan Dora danyaji dadin gyangyadin, nan kuwa bacci ya daukeshi Can cikin dare tafarka, Ahankali take Bude idonta harta Bude gaba daya, kansa dayake dab danata hakanne yasa numfashinsu haduwa, da tsananin mamaki take kallansa, yaushe Yazo? Kode gizo yake mata? Anya kuwa soyaiyar Aliyu Batasa yafara yi mata gizo ba? Domin ta tabbatar da ba mafarki takeba yasa Ahankali takai hannunta Kan Lallausar sumar kansa tashafa Jin Ana shafa kansa ne yasa yabude lumsassun idonsa dake cike da bacci, yazuba mata ido Itanma kallansa take domin ganin Cewa tabbas shine ba mafarki takeba (um jiyakam kunjini Shiru sakamakon wani babban uzuri daya riqeni, 😱nasan mutane dayawa sun jirani, Amma inaso kuyi hakuri please πŸ™πŸ»πŸ™πŸ») Mrs Usman Ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 22 Hannunta dake kansa yadauke, ya damqe hannun nata cikin nasa yace "kin tashi?" Daga masa Kai tayi alamar eh, itade duk mamaki yacikata Tashi yayi Ahankali yasa hannu yadauketa cak, yanufi toilet da ita Duk da batada kuzari Saida tayi kokarin sauka Ahankali tace zan Iya tafiya, kasaukeni Kallanta yayi baice mata komai ba, Saida yakaita cikin toilet din, yabata brush da toothpaste, sannan ya fita tareda rufe mata kofar Yana fita ta jingina da bangon toilet din, sai Murmushi take ita kadai Shikuwa fridge din yanufa yahada mata fruit yakai mata gaban gadon, yahada mata magungunan ta Bude kofar toilet din tayi Dan kadan tace Yaya hijabina Dube dube yafara shine baiga wani hijab ba, sai wani mayafi, danhaka yadauki mayafin yameqa mata Kallan mayafin tayi, sai yau tayi Dana sanin rashin yawo da hijab Towel din jikin ta ta kalla Dan qarami, da kadan ya wuce Rabin cinyarta, haka tayafa mayafin Har kanta, ta futo Daga toilet din tana Jan towel din qasa Yana ganin futowarta yakalleta, cak ya qame a zaune yana Kallan ta Ganin taqi miqewa ne yasa yagane Cewa atakure take Shiyasa ya miqe yace Bari nafadawa doctor kin tashi, kiyi sauri ki shirya, yafice daka dakin Yana fita tasaki Ajiyar zuciya, dasauri kuwa ta zira kayanta, tatada kabbarar sallah *** *** *** Ahankali ta turo kofar Dakin tashiga tareda sallama, yana kwance idonsa biyu, Amma yadafe kansa da hannunsa guda daya,dasauri ta qarasa wajansa tazauna dab dashi, tace sannu Yaya, yajikin Naka? Bece mata komai ba sai rintse idonsa dayake danyi kadan kadan Hannunta tasa tajanye hannunsa Daga Kan goshin, sannan tadora hannunta awajan Dasauri ta dauke hannunta Jin zafi sosai Tashi tayi tace Bari nakira doctor Yaya, Ahankali yace Yazo yanzu yafita, yace zai dawo nanda 30minutes Dawowa tayi tazauna, tace to Yaya tashi Kaci abinci kafin yadawo Ahankali yatashi zaune, still hannunsa na dafe da goshinsa Zuba masa abincin tayi, tadawo kusa dashi tazauna Dakanta take bashi abincin, duk ta damu, tadebo a spoon takai bakinsa Babu musu yafara ci, goshinsa tasake tabawa tace sannu Yaya Zuba mata ido yayi yana Kallan ta, ganin da gaske take komai duk ta damu Lumshe idanunsa yayi alamar amsaba Abincin taci gaba da bashi, wayarta tadau qara, Kallan wayar tayi Amma Bata daukaba, Saida ta tabbatar ya qoshi sannan ta qyaleshi Dan qaramin handkerchief ta dauko a handbag dinta, taje toilet din dakin tajiqashi da ruwan sanyi, sannan tadawo tace kwanta Yaya, babu musu kuwa ya kwanta, shi Har yanzu mamakinta yake, Kamar ba Bilkisun daya saniba Yana kwanciya ta linka handkerchief din gida biyu, ta Dora masa Akan goshinsa, sannan ta dubeshi tace Hakan zai taimakama wajan rage Jin zafin Yaya Ahankali yace thanks Kujerar dake gefen gadon taja ta zauna, sannan tadau wayarta takira number data kirata dazu Hello ya Haroon kakirani Ina busy shiyasa ban samu dama nayi picking ba Shima Daga nasa bangaren yace wanne irin aiki ne wannan dazai Hana kidauki wayata? Yayanmu ne baida lafiya, aika ganeshima Yaya Imran, shine nake kula dashi Cikin bacin rai da nuna kishin sa afili yace, OK kina kula dashi shiyasa ni kika qyaleni, to menene amfanin Iman, aida saita zauna dashi To yanzu ya Haroon idan Yaya Iman din tana nan harna zauna anan? Batada lafiya Itama, an fitar da ita India ma Cikin nuna ko'in kula yace ok, sai anjima, yakashe wayarsa Wayar Tata tabi da kallo, ikon Allah, wato shi kawai maslahar kansa yasani, nafada masa yar'uwata batada lafiya Amma Ko Allah yasawaqe baiyi mataba Tsaki tasaki ita kadai, Imran dake kwance Baisan Sanda yayi Murmushi ba, Ahankali yace keda saurayinki Bilkisu, menene abin fishi Cikin shagwabar da batama San tayiba tace haba Yaya kanajin fa abinda Yamin, shine ya kashe min waya Murmushi yayi baice mata komai ba, Baisan dalili ba kawai de yaji aransa Yanda tayi shagwabar ta birgeshi Harma baiso ta daina ba, domin tasakeyi yace bani labari Kallansa tayi qasa qasa, tace labari Yaya Shima yace eh To wanne irin labari zan baka? Na samarinki Yaya ni banda samari sai Haroon, saide nabaka labarinsa No banaso To ai Kai kace na samari na, Tona fasa kibani wani labarin daban Toshikkenan Yaya Bari nabaka labarin soyaiya Babu Bata lokaci Billy tafara bashi labarai na soyaiya, tun yanaji yana gyada Kai harya dawo yana Daria, kawai aikin kallanta yake, Dan qaramin bakinta dake motsawa shiya zubawa ido yana kalla, yana ta mamaki aransa dama Bilkisu tana da surutu haka? Meyasa da baisaniba? Ita kuwa batasan ma yanayi ba, Zuciyar ta daya, kawai labari take bashi, Bata tunanin komai *** *** *** Yanzu saboda wannan yar allurar kike kuka? Dazai Gane dayadan matsa Daga kusa da ita, kusancin nasu yayi kusa da yawa, gashi yanayi mata magana qasa qasa Kamar Baisan wani yaji shi Wajan allurar da doctor yayi Mata yanzu yafita tashafa tace Allah Yaya akwai zafi Shikkenan naji, zauna nabaki fruit Babu musu ta zauna, dakansa yake Bata tanasha, tace inasu Hajiya? Ya akai suka yarda kataho? Waye yafadamiki sun sanma nataho? Basu saniba, nadai fadawa Farhan yasanar dasu Cewa natafi India Zaro ido tayi tace yanzu fa sunsan wajena kataho Kafadarsa yadaga yace so what, inasanki ne, bazan Iya ganin kinyimin nisaba, Bayan nasaba kullum saina ganki a gida Kuma kawai yanzu saisu dauke minke in zauna? Dadi takeji acikin ranta Wai yau Aliyu ne yake fada mata wannan maganganun Ahankali tace nagode da nuna soyaiyar ku agareni Um kekuma kin Kasa nuna manaba Da mamaki ta kalleshi tace kamarya? Bangane ba Emana gashinan Alhaji yace ki zabi daya acikinmu kin Kasa, kawai Daga yar wannan tambayar kin kwanta jinya Cikin shagwaba tace Kai Yaya Aliyu Dan Allah, Niba wata jinya Kawai kifito fili kice Alhaji Aliyu nakeso Kinga Daga lokacin Alhaji zaisan Cewa idan daddy yayi loosing ummanku ninayi winning Akan yarta Hararar wasa tayi masa tace dasu umman kake? Shima cikin Murmushi yace emana ai gaskiya nafada To nide idan Alhaji yaji kataho wajena Allah babu ruwana Aikuwa sonake yajima, Dan yasan Cewa mun matsu yayi mana Aure Fillo tadauka ta rufe idonta dashi *** *** *** Meyasa Zaki tafi? Da mamaki ta kalleshi tace ai dare yayi Yaya, Kuma akwai masu kula dakai, insha Allah gobe da wuri zanzo Badan yasoba, murya ciki ciki yace shikkenan Murmushi tayi tareda ficewa Tana fita ya runtse idonsa, meyake damun sane kwana biyun nan? Meyasa yakeji aransa bayaso tatafi gida tabarshi? Tana Zuwa gida Hajiya tace Bilkisu Shiru Har dare yayi bamu ganki ba sai yanzu? Agogon hannunta me kyau ta kalla tace laa Hajiya Karfe Tara nefa yanzu, shine Daren yayi? Hajiya ta girgiza kanta Cikeda mamaki tace um um dare beyiba Batareda talura da yanayin hajiyaba tayi cikin daki abinta Washe gari Tunda sassafe tashirya, abaya tasaka tayi rolling da dankwalin, Kamar wata balarabiya haka tazama Su Hajiya Suna futowa domin yin break suka ganta sai zagaya falon take, Itama tana ganin su tagaidasu tace Hajiya natafi, nasan Yaya yanacan shi kadai Shiru, saina dawo Gaba dayansu sukabi bayanta da kallo, mamy tace Bilkisu fa andage, Yanda take magana serious dinnan irin itace Likitan datake dubashi Hajiya tace um ai Hajiya fati tun jiya nake ganin iyayi iri iri, Wai jiya nace mata Bata dawo da wuri ba, Amma yarinyar Nan sai cemin tayi ai darenma baiyi ba Mamy tace gsky ne Bilkisu fira tayi dadi, ni wancan Tunda yatafi ma Ko nemana baiyi ba, yasan zanyi masa tas shiyasa Hajiya na Daria tace, anjima de maje musake gano jikin Imran din, sukuma Yan India idan sun gama rashin kunyar magani Ko zasu nememu, Nima Iman Ko Kira, Bayan Alhaji yayi waya da doctor jabir yace tafarka jiki yafara kyau *** *** *** Tunda ta zauna yaketa aikin kallanta, sai yanzu yake Ganin tsananin kyanda take dashi, wanda Abaya soyaiyar Iman tasa Bai Gane hskanba, Ahankali yace kinsan me? Girgiza kanta tayi tace um um Yaya saika fada Kinyi kyau sosai Gabanta ne yafadi, Yaya Imran dayake son yar'uwar ta, meyasa zai dinga yimata Abu haka? Murmushi tasaki tace ngd Yaya, Bari in shiga toilet, tashi tayi tashige toilet Yana ganin shigarta toilet yadauki wani memo dake gefen gadon dayake yayi Dan rubutu aciki yasaka acikin handbag dinta Tana futowa suka ci gaba da firar su Bilkisu tace Yaya yanzu Kam kaji sauqi, likita zai Iya sallamarmu Kwana kusa nasan Yatsina fuska yayi yace no, Har yanzu Ina danjin ciwon Kai gaskiya, yafadi hakanne Dan Baisan kulawar dayake samu awajanta taqare Ita kuwa zuciya daya tace to Allah yabaka lafiya Yaya Yace amin, yau bazaki bani labarin naki ba? Murmushi tasaki sannan tafara bashi labari, Shikuwa gaba daya ya tattara nutsuwarsa akanta, bawai labarin yake jiba, a a kawai kallanta yake San ransa Suna wannan halin su Hajiya suka shigo dakin, da mamy dakuma Alhaji Saida suka sake yimasa sannu sannan Alhaji yace su zasu koma gida Bilkisu tana zaune babu alamar zata tashi tayi musu rakiya tace to hajiya Allah yakiyaye Mamaki yagama kashe Alhaji, harsunje kofar fita Daga dakin Alhaji yadawo yace dama akwai maganar danakeso muyi dakai Ahankali yace to Alhaji Alhaji yace akwai wata yarinyar abokina danakeso idan ansallameku Daga asbiti kaje ka ganta Ko zatayima, inyaso ita Fatima saika barma dan'uwanka ita (wata sabuwa πŸ€”, Ko Imran zai yarda? Kome yasakawa Bilkisu acikin jaka? To nide fatana aci gaba da bibiyata) Sharhi please πŸ™πŸ» Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 23 Lokaci daya yayi Kicin Kicin da fuska Kuma de Tunda ance yarabu da fatiman menene sai an liqa masa wata Kansa aqasa yace a a Alhaji ai babu damuwa kawai abar wannan maganar Allah yakawo mafita Alhaji yace to shikkenan Allah yakawo mafitar Suka fita gaba dayansu, Suna cikin Mota Alhaji shi kadai yana Murmushi dama ya gwadashi ne yaga Yaya zaiyi Acan asbiti kuwa Bayan tafiyar su Alhaji barrister yayi Shiru sai bacin rai yake shi kadai Bilkisu ta kalleshi nan take yabata tausayi, yana kwance a gadon asbiti ma Amma ba'a qyaleshi ba, Ahankali tace kayi hakuri Yaya,kayiwa Alhaji biyaiya shine zakaga daidai Hannu kawai yadaga mata alamar tayi Shiru, Bata barshi d abinda yakejiba shine zata qara masa wata damuwar Awannan Rana haka suka wuni Shiru, shi yana tunanin mafita, ita kuwa tana tausaya masa ne, awani bangaren na Zuciyar ta Kuma tana Cewa Wai meyasa ma su Alhajin nan suka zone? Tasamu Suna Dan Zaman su rimi rimi Amma yanzu sunzo sun lalata komai Har dare haka takasa Gane kansa, domin kuwa shi yana tunanin Kamar zasu kawo masa wata yarinyar ne Haka Billy Takoma gida sukuku da ita *** *** *** Washe gari da wuri tazo asbitin Kamar Yanda tasaba, fruit yakesha Suna firarsu Sama Sama, yaude taga yadan ware ba Kamar jiyaba, jakar hannunta ya kalla yace Ina handbag din dakikazo da ita jiya? Tace tana gida mana Yaya, meya faru? No babu komai kawai de jakar ta nayi miki kyaune Murmushi tayi tace Allah Ko Yaya? Sosai makuwa jakar tanada kyau, Amma bakiga wani Abu aciki ba? Girgiza kanta tayi tace a a banga komai ba Yaya Jikinsa ne yayi sanyi, karfa tarasa wannan takardar Kuma azo asamu matsala Yanayinsa kadai ta Kallah tagane akwai wani Abu daban dayake boye mata Dan haka tasa aranta Cewa tana Zuwa gida zata duba jakar taga menene aciki Kafin tayi magana doctor Yazo yadubashi, yana Murmushi yace gaske jiki yayi kyau, yauma zaku Iya komawa gida, Cikin murna Billy tace yeee, alhmdlh Kallanta Imran yayi, wato murna take zata koma gida, shikuma baya murna asalima jiyake aransa dama su tabbata ahaka Dakanta tayi driving dinsu Zuwa gida, ahanya sai fira take masa Shikuwa yayi Shiru, Suna Zuwa gida suka zube a falo, anhadu a falo kowa sai murna yake, saboda dawowarsu gida Jikinsa a sanyaye yatashi yace Hajiya zanje part dinmu zan Dan kwanta na huta kadan Hajiya tace to Imran Yana Zuwa part dinsa ya kwanta, yazubawa Saman dakin ido, karfa ace yarinyar Nan tarasa wannan takarda, runtse idonsa yayi afili yace oh ya Allah, nikam inaga banida sa'ah Akan komai Bilkisu kuwa tana ganin yanayinsa ayanda yatashi yayi part dinsa tasan tabbas yana cikin damuwa, lokaci daya jikinta yayi sanyi, tashi tayi Ahankali tashige dakinsu, Hajiya na lura dasu gaba dayansu Tana shiga dakinsu tafada duniyar tunani, meyasa Yaya Imran ya sauya mata? Toma menene abin damuwa danya sauya matan? Ba saurayin yayarta neba? Maganar jakar dayayi mata dazu ne yafado mata Arai Dasauri tatashi tanufi inda suke ajiye handbags dinsu, wadda tasaka jiya tadauko ta zauna Akan gadon ta zazzageta bataga komai ba Hannu tasa ta laluba cikin nanma bataga komaiba, ziff din jakar ta zuge Aikuwa saiga yar qaramar takarda tafado Ahankali take Bude takardar harta warware ta dukanta, abinda da taganine acikin takardar yasa gabanta faduwa Hannunta tadora Akan kirjinta dayake wani irin lugude Ahankali ta sake karanta abinda yake rubuce a takardar da manyan baqi (BILKISU DO YOU MARRY ME?) Innalillahi... Yaya Imran nefa, saurayin yayarta, a duniya Bata taba kawowa aranta Cewa Wai zata Iya soyaiya dashiba, bare aje ga rayuwar Aure Kuma ai yasan Ina tare da Haroon , but meyasa zaimin wannan maganar? Lalle maza basuda kunya, inba hakaba Yanda take tsananin bashi girma meyasa zaiyi mata makamanciyar wannan maganar ma? Har dare Billy tana daki taqi futowa falon, zeey auta ce tashigo da gudu tace anty Bilkisu kizo muyi dinner inji Hajiya Tashi tayi zaune, takama hannun zeey tace Yaya yana nan? Zeey tace Yaya Farhan? No Yaya Imran Eh yana nan yana danna waya, kowa Yazo Ke ake jira Ahankali tace to gani nan Zuwa Zainab na fita tace ni yanzu da wanne ido zan kalleshi ma? Haka de ta futo falon, tun kafin ta zauna ya kafeta da ido yana kallanta, shi sai yanzu nema yake Ganin kyau da sura irinna Bilkisu Kujera taja ta zauna, Kuma sai akai sa'ah tana facing dinsa, Bata yarda tadago idonta taganshi ba, Shikuwa duk abincin dazaikai bakinsa idonsa akanta Hajiya na kallansu, aranta tace oh Imran babu kunya, Ko yar Kara ma babu Tace Bilkisu yanaga bakya cin abincinne sosai? Dago kanta tayi tace Hajiya inaci Dan satar kallansa tayi, ai kuwa karaf idonsu yahadu, dasauri ta maida kanta qasa Murmushi yasaki, aransa yace da alama taga komai Bayan sun gama cin abincin falon suka koma suka fara fira, Ana kallo, tashi tayi zata tafi daki Hajiya tace Ina zakije ki zauna Ke kadai? Salan kije kina tunani, zauna anan Haka de Billy ta zauna, Amma duk atakure take, Shikuwa Imran waya yake dannawa Amma hankalinsa yana kanta Har wajan Karfe goma na dare kowa ya watse yatafi dakinsa, Bilkisu dadi Taji dama tagaji da wannan Zaman Shima Imran yana futowa harabar gidan yayi dialing number ta, harta katse Bata daukaba Saida yasake Kira sannan ta Daga daqyar, Kisameni a falo yanzu Abinda yace mata Kenan, ya kashe wayar Gabanta yana faduwa ta futo falon, babu kowa, sai shi dayake zaune Kanta aqasa tatako tazo Har inda yake, aqasa ta zauna, shikuma yana kan kujera Yace taso ki zauna anan Bilkisu, ya nuna mata waje akusa dashi Zama tayi, Amma kanta aqasa tana murza zoben hannunta Qasa qasa yayi da murya, ita kanta badan tayi kusanci dashiba bazataji abinda yake fada ba Cikin rada yace Bilkisu Yanda yafadi sunan kadai ya Isa ya birgeka Ahankali tace na'am Kinga Yanda Allah yake hukuncinsa Ko? Bilkisu Arayuwa ban taba tunanin zan Iya auran wata yarinya Bayan Iman ba, sai gashi Daga baya abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa harda hakuri danayi da ita nabarwa dan'uwa na, yanzu haka Ina fishi dashi ne Akan meyasa tun farko Bai sanar Dani gaskiya ba, yabar abin acikin ransa Har Hakan ya haifar Masa d mugun ciwo, a yanzu banida zabin daya wuce nasoki, azamana dake a asbiti nayaba da kyawawan halayen ki Bilkisu, please Ina neman alfarma awajanki ki daure ki aureni Kodan Hajiya (πŸ˜ƒπŸ˜ƒ) Kanta na qasa Ahankali tace Amma Yaya kasan Haroon... Haroon Haroon, kede kullum maganarki Haroon, Bilkisu Haroon Bai sonki, kema bakya sonshi Meyasa bazamu hada kanmu ba, muyi Addu'ah Allah yakawo mafita? Shiru tayi masa takasa bashi amsa, sake matsowa yayi dab da ita, yakama hannayenta duka biyun ya riqe, wani irin taushi yaji hannun nata nayi Innalillahi take maimaitawa aranta, banda wani irin yanayi daya ziyarceta lokaci daya, ita Tunda take wani babban namiji Bai taba riqe hannunta ba sai yau, Kuma Wai yau dinma Yaya Imran, wanda take ganinsa Kamar yayansu dasuke ciki daya Adede wannan lokacin Hajiya ta futo Daga dakin Alhaji domin tahada masa coffee Cak taja tatsaya batare data qaraso cikin falon ba, Ahankali ta juya cikin dakin, tace Alhaji zo kaga abinda idona yagani Alhaji na tasowa Hajiya takama hannunsa tajashi Har setin indasu Imran suke Shima ganinsu yayi, yasaki Murmushi Dukansu suka juya cikin dakin suka fasa futowa falon, Alhaji yace lalle Imran da rigima yake, yanzu Hajiya Yaya yake so muyi da shu'aibu?domin kuwa Zaman da yaran nan sukai kadai zai tabbatar mana da Cewa akwai wani Abu a tsakaninsu, Kinsan de yarinyar Nan akwai maganar wani akanta Hajiya tace hakane Alhaji, Amma gaskiya Nima Ina Bayan Dana, gaskiya Alhaji asan Yanda za'a shawo Kan matsalar nan Murmushinsu na manya yayi, yadauki wayarsa yakira doctor jabir Bayan sun gaisa yake tambayar sa Yaya yanayin jikin Fatima? Jabir yace jiki da sauqi sosai, anasa ran sallamarta ma nanda sati daya Godia Alhaji yayi masa ya kashe wayar Hajiya tace to ai Gara tadawo domin mufara shirin biki Cikin Daria Alhaji yace mata Kenan, Ana maganar mahaifin yaran kina maganar biki Afalo kuwa, Imran ya tsara Bilkisu da magiya Akan ta amince Hannunta dake cikin nasa take kokarin qwacewa Amma Kuma yaqi Bata damar Hakan Ahankali yasake Cewa please Bilkisu (Nima nace please Billy πŸ™πŸ») Sharhi please πŸ™πŸ» Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 24 Batace masa komai ba yasake Cewa "kin amince?" Ahankali ta Daga masa kanta, tareda qwace hannunta tashige dakinsu da gudu Bayanta yabi da kallo yanayin wani irin Murmushi, Ahankali yace Alhmdlh, sannan Shima yatashi yayi part dinsa *** *** *** Next day Hajiya na zaune asallaya tana lazimi, Bilkisu tashigo da sallamarta ta zauna agefe Hajiya na kallanta tasan Cewa akwai magana abakin ta, Amma Sai tayi Shiru batace mata komai ba tana jira taga gudun ruwanta Kanta aqasa tana wasa da yatsun hannunta tace Hajiya Na'am Bilkisu, inji hajiya Am Hajiya dama... Dama Yaya ne jiya.. Saita Kasa qarasawa Hajiya tasaki Murmushi tace meyake faruwa Bilkisu? Me yayan naku yayi? Hajiya shine jiya yace Wai yana sona, Kuma ni Hajiya Ina tsoron baba yaji Hajiya na Murmushin tace toke Kuma me kika cemasa? Ko bakya sonsa? Kunya ce takama Billy, yau ne Rana ta farko data tabajin kunyar Hajiya Cikin kunya tace wayyo Hajiya To Bilkisu me kikeso nafara tambayar ki? Kinsan de duk da Nina haifi Imran bazanso nayi muku auran dole ba, dole sai Kuna da ra'ayin juna Hajiya ni dama Ina tsoron baba ne To karki damu kinji Bilkisu, inde wannan ne ai akwai Allah, babu abinda yafi karfin Addu'ah, kuje kuyita Addu'ah Allah yashige gaba Ahankali tace amin Hajiya Tundaga wannan lokacin soyaiya Mai karfi tashiga tashiga tsakanin Bilkisu da Imran Ayanzu Kam yariga daya koya mata Yanda zata soshi, abin Har mamaki yake bata, Bata cikakken minti talatin batare datayi tunaninsa ba Bata fatan wani Abu yashiga tsakanin su bare Har aje ga zancen rabuwa, Abu daya take tunani da fargaba shin Yaya zata Iya Zaman Aure dashi? Tana ganin girmansa sosai, Kuma tasan Cewa dole akwai ranar dazatazo ta kauda wannan kunyar atsakanin su Abinda take fargaba Kenan *** *** *** Kowa na zaune a dining Suna cin abinci cikin walwala, Alhaji ya kalli family din nasa cikin ransa wani irin dadi yakeji, saide Aliyu da Iman ne kadai babu awajan Kwanan wata yasake dubawa ya jinjina kansa yasan Zuwa yanzu ansallami Fatima ya Kamata ace sun dawo gida haka Yaga alama yaran nan idan ba sune suka nemesuba tofa saisu shekara ahaka Danhaka yadauki waya yakira Aliyu saide harta gama ringing dinta Bai dagaba, haka Alhaji yasa wayarsa a aljihun sa yace Allah ya kyauta *** *** *** Suna zaune Afalo cikin luntsima luntsiman kujerun dasuka kewaye falon launin farare, firarsu suke cikin Jin dadi, basa tuna kowa sai kansu, Cikeda so da kauna ya dube ta yace Matar Aliyu Cikin nishadi da Jin dadi tace hmm Kamar gaske Wai matar Aliyu, Bayan kagama ban wahala Ji yarinyar Nan, kebance kin bani wahala ba, agabana fa kika Bawa bros ice cream, gefenda Zuciyar sa take yasa hannunsa awajan, yaci gaba da Cewa a lokacin dakinsan Yanda naji araina dabakiyi ba Fatima Ina Miki wani irin so Mai wuyar fassaruwa, bantaba soyaiya ba, Amma ansha kawo min mata Kala Kala na Aure su, Amma nace Ina Nifa Sam sai diyar Hajiya Murmushi tayi tace Aikuwa nabashi ne dannaga da gaske kake kadena sona baka kishina kokuma Har yanzu kana sona Hararar wasa yayi Mata yace um wato dama da niyya kikeson kashe Dan bawan Allah, duk abinda kike Ina gani ai, nasan da niyya kikeyi Wayarsa ce tayi qara, cikin nutsuwa yadaga Daga wajan aikinsu ne, Ahankali yake Bata order Kamar yana wajan, Saida yagama dasu sannan hankalinsa yakai Kan Kiran da Alhaji yayi masa Zaro ido yayi yace Innalillahi Tace lafiya Yaya? Meyake faruwa? Saida yashafa kansa yace wallahi Alhaji ne yakirani, kinsan sai yanzu natuna banma Kira mamy ba tsawon wannan lokacin? Kuma duk laifinki ne ai Cikin tashin hankali tace nashiga uku, wallahi Nima ban Kira Hajiya ba, wayyo Allah da wanne ido zan kalleta? Da wanne ido Zaki kalleta Koda wanne ido zan kalli mamy da bros? Ga Yan gida agefe da basu San nataho wajan ki ba sai saqo na bayar afada musu Yanzu Yaya Zamu yi Yaya? Cikin dakiya yace karki damu tsaya nakirashi nasashi a hands free kiji Yanda zamuyi Haka akayi kuwa, yana Kiran Alhaji ya ajiye wayar atsakanin su Cikin ladabi ya gaida Alhaji yace Alhaji wallahi wayar Bata tare danine lokacin daka Kira Alhaji yace eh ai Tunda Fatima tana tare dakai aiba saika nemi kowaba Hada ido sukai da Iman Kamar wasu munafukai Yace a a Alhaji wallahi bahaka.... Kafin yaqara sa maganar da zaiyi Alhaji yace nasan kun gama komai yanzu to inaso kukamo hanya kudawo gida, in Kuma Kuna nan din za'a daura auren to Cikin kuskurin kunya yace to Alhaji insha Allah, tareda kashe wayar Duban Iman yayi yace Kinga abinda kika janyo mana Ko? Tace kaji Yaya zaka doramin laifi, kajanyo mana de, ba Kaine ka biyoniba Yace naji, yanzu de tashi tashi muhada yanamu yanamu wallahi tun kafin su biyo sawunmu, mutafi gobe mubasu hakuri Haka suka tashi suka fara shiri *** *** *** Tsaye suke a filin jirgin Malam aminu Yayi kyau sosai acikin suit dinsa ruwan toka, yayinda ita Kuma tasa atamfarta Riga da sket dinkin yahau jikinta yazauna Kamar Dan ita akai Basufi minti talatin da tsayawa ba jirgin su yasauka, Suna futowa kuwa sukagansu, da gudu Bilkisu taje ta rungume yar'uwar Tata Oyoyo Yaya Iman Cikin murna Itama tace Bilkisu nayi missing dinki, inasu Hajiya? Uhm Hajiya tana gida, tun safe tahana kowa sukuni a gidan nan tana ta murna Zaki dawo, Ke baba mafa Yazo Cikin mamaki Iman tace baban? Yaushe Yazo? Wlhy tun sassafe Yazo, bakiga Yanda hankalinsa yatashi ba dayaji bakida lafiya, Aikuwa yau Alhaji yana masa waya yace zakizo, saiga baba da kansa akano Jinjina Kai Iman tayi tace um lalle baba yafara saukowa Cikin Mota suka shiga sunata firarsu sunma manta da Aliyu da Imran Shikuwa Aliyu cikin kunya ya Bawa Imran hannu da nufin su gaisa, gaba daya kunyar bros din nasa yake Shima Imran din anasa bangaren fishi yake da dan'uwan nasa Yana ta shan qamshi batare daya kalleshi ba yamiqa masa hannun suka gaisa Sama Sama Amota ma Iman Da Bilkisu Suna baya, Aliyu na zaune adaya gefen, yayinda Imran yake driving Hankalinsa yana kan driving din dayake yace "yajikin naki?" Iman tanajin tambayar tasan da ita yake, dole tasan dama zaiyi fishi, to Amma Yaya zatayi Ahankali tace jiki da sauqi, yasu Hajiya? Agajarce yace mata lafiya Har sukaje gida babu wanda yasake magana acikinsu, shi Imran yana fishi, shikuma Aliyu kunyar sa yakeji, gani yake Kamar yayi wa dan'uwan nasa qwace ne Yanayin parking su Bilkisu suka shiga cikin gidan, Imran ma Yarufe motor zai shiga Daga ciki, ba tareda daya sake Kallan Aliyu ba Abin nasa ne yafara damun Aliyu, Bai sababa, sannan Kuma basu sabarwa kansu da hakanba, cikin sauri yariqe hannunsa Ahankali yace bros... Imran ya kalleshi baice komai ba Yasake Cewa bros... Kayi hakuri Cikin fishi Imran yace kaga Dan Allah Malam kasakeni,zan shiga ciki ne Bazan sakekaba,saikayimin hukunci daidai da laifin Dana aikatama Cikin Jin Haushi yace haba! Haba!! Haba bros, mezaka fadamin Dan Allah? Yanzu ashe Har akwai abinda zaka boyemin azamana dakai? Kai wanne irin mutum ne bros? Saboda kanasan Fatima Ina Santa ka gwammata kakashe kanka Akan kafuto fili kasanar Dani gaskiya? Yanzu Bayan rashin lafiyar daka kamu dashi dakasa mun rasaka wakayiwa asara Sama dani? Aliyu yace kayi hakuri bros insha Allah bazan sakeba, hade hannayensa yayi waje daya yasake Cewa tuba nake bros Imran yace shikkenan na hakura, but karka sake kokarin gwada wani Abu makamancin wannan nan gaba Insha Allah bros, inji Aliyu Haka suka shiga cikin gidan Kamar babu abinda yataba shiga tsakanin su Dukansu sun hadu Afalo Bayan anci abinci, Alhaji ya dubi shu'aibu mahaifinsu Iman yace Malam shu'aibu kaga Kuma al'amarin dannaka yajuye yakoma Kan wani dannaka Cikin mamaki yace kamarya ya? Ban fahinceka ba Alhaji Abubakar Murmushi Alhaji yayi yace Ina nufin Fatima Allah da ikonsa ubangiji ya sauya al'amarin Aure tsakanin ta da Imran zata auri wani Yaron nawa Dan wajan Sa'ad Cikin mamaki yace ikon Allah, Sa'ad, Sa'ad de Dana sani? Shikuwa, gashinan ma a zaune, Alhaji ya nuna Aliyu da kansa yake qasa Shu'aibu ya kallesu duka yace wato gaskiya sai yau nasake yarda da qaddarar aurena da zainab Ya kalli Aliyu yace wato Kai da babanka ya rasa shine kaikuma ka dage Saida kasameta Ko? Duka falon sukasa Daria Yaci gaba da Cewa, wato Alhaji dama can akwai abinda Allah ya tsara shiyasa zainab taqi mahaifinsa, domin kuwa data Aure shi, tofa babu Yanda za'ai wannan yaro yaso Fatima, Tunda tariga data zama yar uwarsa ta ciki daya Amma Kuma sai gashi, yanzu Allah zai tabbatar da wannan al'amari Akan yayanmu, Naso ace zainab tana Raye domin taga wannan Rana, haka Naso ace Sa'ad yana Raye, nasan Cewa zaifi kowa farin ciki Yana fadar wannan magana duk sai jikinsu yayi sanyi, Alhaji ne kawai yace Allah yayi musu rahma, duka falon akace amin Shu'aibu yace to Alhaji Allah yakaimu lokacin bikin, ubangiji Allah yasa ayi damu, shikuma Imran din Shima Allah yakawo masa wata tagari Kamar almara zainab auta tace kawu shu'aibu ai anty Bilkisu yakeso, jiyama Saida nagansu Suna fira, Har abinci sukeci tare Imran najin wannan baran barama da zainab tayi masa tuni yasunkuyar da kansa qasa, jiyake Kamar qasa ta tsage yashige Dan kunya Ita kuwa Bilkisu da gudu tayi cikin dakinsu Murmushi shu'aibu yayi ya kalli Alhaji yace haba Alhaji? Yazakamin haka? Kuma yanzu fisabilillahi kasan da wannan maganar atsakanin yaran nan shine zakayi Shiru? Alhaji yace haba Malam shu'aibu, ai nasan kayiwa Bilkisu Miji Kuma nasan kanada kyakykyawar hujjarka tayin Hakan, shiyasa ma banyi maka maganar ba Shu'aibu yace haba Alhaji, a a ni banji dadiba, halaccin dakukamin Abaya Alhaji ai ya wuce nan, inde Bilkisu ce nabashi, shikuma Haroon zan samu dan'uwana wato mahaifinsa nayi masa bayani, insha Allah za'a warware komai, nide dama fatana kada Yara suyi koyi da Hali maras kyau, Kuma Alhmdlh, Yanda kakula da tarbiyarsu koni nan sai haka nagode sosai da sosai Su Kuma Yara Allah yabasu lafiya Duka falon suka ce amin Alhaji yace to Tunda abin Yazo da haka, Bari nakira maqotana Kawai atsaida lokacin bikin, kafin katafi Aikuwa haka akayi, anan take Alhaji yadau waya yakira maqotansa, agabansu akai komai, nan take aka tsaida lokacin biki nan da wata daya Sharhi pls πŸ™πŸ» Mrs Usman ce WAZAN ✍🏻 ZABA?πŸ’– Writing by Amnah El Yaqoub Bissmillahir-rahmanirraheem 25 Alhaji ne da kansa yarako Malam shu'aibu Har Mota da kayan sa ranar ahannun sa Kamar Yanda al'ada ta tanada, yasa sani driver yakai shi Har gida Sannan yajuya ciki Hajiya tasa Iman agaba Kamar za'a qwace mata ita, mamy tace Hajiya da yarta, Har an huce Kenan Hajiya tace ai dole na huce Hajiya fati, Tunda naji zancen saka Rana, saina kaita dakin Miji ma tukunna Kamar qaramar yarinya haka Iman tafara buga kafafunta aqasa cikin shagwaba tace Kai Hajiya Wai kullum saikina Cewa zaki kaini zaki kaini, nide ba inda zani, tana wannan shagwabar tashige dakinsu tabi Bayan Billy Hajiya ta dubi mamy tace kingafa irin tabarar yar Taki, ai dole nace nayafe Mamy tayi Murmushi tace Aikuwa bazamuyi jayaiyaba Mungo de Aliyu ne yatashi yayi wajan mamy Kamar zaiyi mata kuka yace mamy kiyi hakuri nayi laifi Tace a a baby, aini yanzu kunfi karfina, kuje can qurata, da shagwabar ka zanji Koda ta Matarka? Hajiya na Daria tace Gaskiya Kam, ta dubi Imran tace Dan Allah kuje ku huta muma kubarmu muhuta Aliyu Saida yasake Kallan dakin da Iman tashiga sannan yabi Bayan Imran Mamy na kallansa, aranta tace oh Aliyu Kam inajin idan anyi auran ma babu inda zaina fita Suna ficewa Hajiya tace yanzu Hajiya fati Yaya za'a yi? Mamy tace Hajiya ai saide kawai a fara Shiri tun yanzu, Tunda Kinga ansa bikin a qurarran lokaci, lefe de wannan damuwa Tunda gaki nan, Yara basu da matsalar wajan zama, kowa yana dashi, saide gyaran amare kawai wannan Kuma na dauki nauyin komai, duk abinda aka kashe zan Bawa masu gyaran, sai Kuma abinda baza'a rasaba Hajiya tace eh hakane Kam, to kawai Bari nakira waya gida a turo mana Mai gyaran jikin Daga can, Tunda sun Iya sosai Mamy tace eh yafi sauqi ma Hajiya ta dauki waya takira Yan uwansu na maiduguri tafada musu zancen bikin, sannan Kuma takira cousin sister dinta tayi mata bayani komai, nan take kuwa tace Washe gari zata aiko musu da me gyaran jiki, kafin Suma suzo bikin Washe gari kuwa tazo da yamma, Hajiya ta nuna mata amaren, a lokacin aka fara gyara su Kamar ba gobe *** *** *** Washe gari Aliyu yakoma Abuja bakin aikinsa, bisa umarnin Alhaji, Shima barrister bawani Zaman gidan yake ba Tunda Bros din nasa yatafi, Shima sai yafi maida hankalinsa Akan aikin yanzu Bayan sati daya Aliyu ya turowa mamy kudi taqarawa Hajiya Akan hado kayan lefen shida Bros Godia mamy tayi masa sosai Wannan Karon Kam Hajiya da kanta ta shirya tatafi dubai tayowa yaran nata siyaiya ta kece raini Kwananta hudu a dubai tadawo gida, akaci gaba da shirye shiryen biki *** *** *** Hajiya da mamy na zaune Afalo mamy tatura zeey takira mata su Iman Zainab na tafiya mamy ta dubi Hajiya tace Hajiya Wai wannan naman kazar ne Dana dafa musu nakeso su cinye shi yanzu Daria Hajiya tayi tace Hajiya fati kina shagwaba yaran nan naki, aida kin kyale Suma Yanda Naga mazan Suna rawar kafa ai abin nasu sai hamdala Mamy tace a a Hajiya Gara mu gyara su suje tsaf dasu Hajiya tace to shikkenan Aikuwa kyayi jinya, Tunda agabanki zasu zauna, Gara ni Suna can nasu waje Ina nawa Kafin mamy tayi magana kuwa suka zo, mamy tace Yauwa kuzo nan, gashinan kudauka ku cinye, kaji ne kowa yaci guda daya, babu musu suka zauna awajan daqyar suka cinye kazar, Shima Dan agaban mamy ne babu damar yin musu Dakinsu suka koma Bayan sun gama ci Da daddare Suna kwance Suna fira Sama Sama, Iman nabawa Billy labarin India, duk da bawani yawo tayi ba Mamy ce ta turo kofar Dakin tashigo da cups a hannunta, tabasu tace to kutashi kusha wannan, karba sukayi suka fara Sha, Iman tace mamy wallahi ba dadi Bilkisu ma tace nikam ya isheni mamy, ga sauran nan, Tafadi haka tareda miqa mata cup din Mamy tace shirman banza, wannan din ai shine gatan, kushanye maza Kuban cups Babu Yanda suka Iya haka suka shanye, mamy na fita Billy tace nikam abubuwan nan da mamy take bamu yafara damuna, mu Kenan kullum cikin shan magunguna, banda gyaran jiki Iman tace wallahi Nima haka, ni tsoron haduwa nake da Aliyu ma, idan muna fira Yanda kisan ya hadiyeni, Kuma yanzu tana bamu wannan abun Hmm ai Gara Ke Yaya Iman, ni wallahi kunyar Yaya Imran nakeji, abin da nauyi, Har yanzu nakasa Sawa Raina zan Iya yin wani Abu na Aure dashi Toya zakiyi dole hakuri zakiyi, kede kawai kiyi masa biyaiya Haka suke ta firarrakinsu Har sukai bacci *** *** *** Akace Rana Bata karya, Ayau ne dubban mutane suka shaida daurin auran Aliyu Sa'ad Bilal da amaryarsa Fatima shu'aib Yaqoub Dana Imran Abubakar Bilal Dana amaryarsa Bilkisu shu'aib Yaqoub Akan sadaki nera dubu Dari Dari lakadan ba ajalan ba Angwaye sunyi kyau acikin farin yadi da babbar Rigarsa, kasancewar basaka manyan kayan sukeba, sai yayi musu kyau sosai, photuna ake ta Ko Ina, bakinsu Kamar gonar audiga Cikin gida ma haka duk gida ya rikice da hayaniyar biki, yan'uwan mamy da qawayenta duk sunzo nakusa Dana nesa kowa yaji ance akano za'a yi bikin saiyazo, kasancewar Kanon tafi musu kusa Akan Abuja Iyaye sunyi angon atamfa da less Ranar yini sukasa atamfa, ranar da akai mother's day Kuma sukasa less Amare sunyi kyau Har sun gaji, komai na al'adar shuwah sukai, harsu kudin turare da komai haka su Aliyu suka bayar, komai anayinsa a wadace Ranar dinner yusy ce ta fadawa Yan school dinsu, Aikuwa sunzo, ankon materials sukayi, Amare Kuma sukasa dark blue, qawayensu Kuma milk color Ana dawowa Daga wajan dinner aka fara shirin Kai amarya Bilkisu gidanta, ita Kuma Iman sai gobe dasafe zasu wuce Bilkisu kuka take Kamar me, Iman ma nakuka, Hajiya kuwa kawai daurewa take, Amma maganar gaskiya batasan abinda zai nisan ta ta da yaran, hannun Iman na cikin na Bilkisu amotar da za'a kaita Saida tarakata Har gidanta, sannan suka dawo, acikin Mota ma a hanyar su ta dawowa Iman kuka Kamar ranta zai fita, sosai tabawa yan'uwansu tausayi haka suketa Bata hakuri Tana dawowa gida kuwa zazzabi ya rufe ta, Washe gari da safe suka fara shirin tafiya Abuja, Alhaji Saida yaqara yi musu nasiha Mai ratsa jiki sannan suka futo, Hajiya a daki ta kulle kanta tana kuka, bazata Iya ganin tafiyar Iman ba, mamy kanta Saida jikinta yayi sanyi, ta tabbatar ba qaramin so Hajiya takewa yaranba Ahanya mamy ce ta janyo Iman jikinta tana aikin rarrashi, Har sukaje Abuja Dawasu hamshaqan motoci nafara tozali a gidan, manya manya guda hudu Gidan Kamar ba'a cikin Nigeria kakeba, part din Aliyu da aka maida shi Zuwa na Iman, nan akai kaita, komai ya tsaru, falon kadai zaka Iya kiransa d aljannar duniya Da yamma mamy ta turo me kwalliya ta tsara mata kwalliya tagani tafada, acikin kwali ta dauko wata gown fara me kyau, rigar Kana tafiya tanajan qasa, dole sai an riqe maka ita Daga baya Sosai gown din tayi mata kyau, Mota ce tazo Har gidan ta dauketa, yana harde a gidan baya, Shima yayi kyau sosai acikin kakinsa , batayi musu ba wajan Bawa idonta haqqinsa domin kuwa babu qarya yayi kyau Tana zama wani irin qamshi yadaki hancinsa, Ahankali yakama hannunta yana murzawa, kansa ya turo daidai wuyanta yana shaqar qamshin datake cikin rada yace kinyi kyau Itakam al'amarin Aliyu yafara Bata tsoron, rabon data ganshi tun kafin bikinsu tasan kuwa idan yaganta dole sai Hakan tafaru, to Amma Kuma ai basu kadai bane amotar, akwai driver Janye jikinta tayi Ahankali tace nagode Wani hall aka Kai su, Suna futowa sojoji suka fara Sara masa, hannunsa yasaka cikin nata Suna tafiya Ahankali, Har suka shiga ciki, sojoji ne maqil aciki, wajan Zaman su sukaje suka zauna, Bayan sallama da sauran jawabi aka basu dama su yanka kek Dogon kek ne Mai Hawa Hawa, tana manne ajikinsa yayanko yasaka mata abakin ta, Itama haka tasaka masa, kawai ruwan photuna kakeji awajan baga wayaba baga camera ba Saida sukayi wasanninsu na sojoji parade Kala Kala sannan aka tashi da daddare Direct wajan mamy suka nufa, Iman de duk atakure take, mamy na lura da ita, danhaka ta dinga janta da fira harta Dan saki jikinta Sai wajan goma da rabi mamy tace Iman muje na rakaku, bacci nakeji, Ahankali tace many ki barni anan, saina kwana awajanki Dasauri yadago kansa ya kalleta, shikuma to dawa zai kwana? (kuji samu 😏da dawa kake kwana?) Mamy tace a a takwara, kuje kuyi baccin ku Nima nagaji, wataran ai Zaki kwana anan din Haka suka futo, Iman sai tura baki take gaba, ita Ala dole anhanata kwana anan Saida takai su Har falon, sannan tace to Saida safenku, taja musu kofar Mamy na tafiya ya kalleta yace wato tabarki ki kwana acan, nikuma nataho ni kadai Ko? Kanta aqasa tace a a bahaka nake nufi ba Shima kansa ya lura atakure take, Dan ta ware yasa yace shikkenan, Zaki Iya tafiya dakinki kiyi wanka kuhuta, Nima zanje na watsa ruwa Ahankali ta Daga kanta tace to, tayi ciki *** *** *** Rigar bacci ce ajikin ta fara qal da ita,duk namiji Mai cikakkiyar lafiya idan yayi tozali d ita dole yabada Kai, domin kuwa Ana ganin komai abaiyane, tana zaune Agefen gado tana sharar hawaye, tun jiya take wannan kuka, takasa sabawa dashi, su biyu kadai a gida, gashi babu wanda ya leqo musu Daga gida, tasan Kuma Hajiya ce tahana, wannan wacce irin rayuwa ce Daga shi sai gajeren wando da vest ajikinsa yashigo cikin dakin nata, dab da ita ya zauna, Har jikinsa ya gugar nata Cikin sigar rarrashi yace Yanzu saboda hajiyan kike wannan kukan? Cikin hawaye ta Daga masa kanta alamar eh Yace to kiyi hakuri gobe zan kaiki kinji? Kinga shikkenan ma saimu cigaba da zama acan Kamar da Goge hawayen idonta tayi tace da gaske kake Yaya? Cikin mamaki da Kuma qara tabbatar wa lalle Bilkisu yarinyace yace eh da gaske nake, ki kwanta kiyi baccin ki, Nima yanzu zanyi wani aiki ne idan nagama zanzo na kwanta Dasauri ta kwanta, harda kashe wutar dakin, ganin jiya sun kwana tare baiyi mata komai ba, shiyasa yau ma tagama sakankancewa Akan babu abinda zai mata, dama tasan Yaya Imran ai bazai Iya mata komai ba, Yanda take ganinsa Kamar yayansu, tasan Cewa Shima haka yake Ganin ta Danhaka tayi Addu'ah tajuya tafara baccin ta cikin kwanciyar hankali Cikin baccin ta Taji mutum abayanta, aranta tace may be Yaya Imran baisaniba, danhaka saita matsa gaba kadan, Shima yasake matsowa jikinta, sake matsawa tayi gaba, sai abin natama yabashi Daria, ganin Yanda take gudunsa, yau Kam bayajin zai Iya hakura, jiyanma ya kyaletane saboda tadan saki jikinta dashi Ahankali ya matsa jikinta, sosai yashige jikinta Kamar wanda yakeson komawa cikin ta Rungumota yayi jikinsa, cikin rada rada yace Bilkisuuuuu....yanda yaja sunan nata ne yasa tsikar jikinta tashi Gabanta yana faduwa cikin rawar murya tace na.. Na'a...na'am... Kansa ya cusa awuyanta yana shaqar qamshin dake fita Daga jikinta, yace ki kwantar da hankalinki babu abinda zanyi Miki kinji? Wanna Karan Kam Bata Iya bashi amsaba, sai Daga Kai datayi, yanzu banda rashin kunya Yaya Imran ne zaiyi mata haka? Yaya Imran fa, yayansu na gida Hawaye ne suka fara silalowa Daga idonta nan take tafara shashshekar kuka Cikin sauri ya juyo da ita tana fuskantarsa Fuskarta yakama da hannunsa duka biyun, Ahankali yafara matso da fuskarsa dab da Tata fuskar, harshansa yasa yana lashe duka hawayen nata,cikin rada yace kiyi hakuri, kiyi Shiru kinji? Tana kuka ta Daga masa Kai Gaba daya yabi Fuskarta yana lasa Kamar maye, Bilkisu kuka yaqaru ganin yanayi mata Abu Kamar ba Yaya Imran dinsu ba Domin yahanata kukan yahade bakinsu waje daya, Daga nan labari yasha banban Yayinta Imran ya nemi hanyarsa yashiga da qyar a lokacin Bilkisu taqara volume din kukanta, cikin kuka tace Yaya kayi hakuri, Yaya Dan Allah kabari Amma inaaa Imran Kan Baisan inda kansa yakeba, kawai aiki yake, shi kansa hawayen dadi yake, yakasa rarrashinta tana kuka tana Yaya natuba, Dan Allah kabari, Yaya zan mutu.... Shima Ahankali cikin kukan yake Cewa Hajiya... Hajiya nagode (πŸ˜‚πŸ˜‚) Bilkisu ganin baya hayyacinsa yasa tafara dukansa Amma haka tayi harta gaji ta Dena, ganin Kamar tana dukan gunki ne *** *** *** Cikin sanyin jiki tayi wankan tasaka rigar bacci ruwan siminti,Addu'ah tayi ta kwanta, Bata jima da kwanciya ba yashigo dakin da jallabiya ajikinsa Ahankali yace Fatima Shiru tayi masa, Kuma Sarai tajishi Fatima ki daure kitashi muyi sallah Ko Nanma Shiru tayi masa Murmushi yasaki yatashi yadauketa cimak yasauko d ita qasa Shagwaba tafara yi masa tana Cewa haba Yaya Dan Allah nifa nafara bacci Cikin lallama yace nasani, ki daure nace Nima Haka tasaka doguwar Riga Akan rigarta tasaka hijab, ya kalleta yace alwalafa? Murya ciki ciki tace masa inada alwala Murmushi yayi yatada kabbarar sallah, dama yasan tana jinsa ba bacci takeba Suna idarwa yayi Mata duk tambayoyin dasuka dace, kanta yakama yayi Addu'ah sannan yace kije kiyi baccinki Babu musu tatashi tahau gadon ta kwanta, Saida yakashe musu wutar dakin, sannan ya cire jallabiyar dake jikinsa yahau gadon ya kwanta Cikin tsananin farin ciki yace amarya Tana jinsa tayi Shiru Tsam yatashi yadawo gabanta, gashin kanta yafara shafawa, yace inason gashin nan Duk tana jinsa tayi Masa Shiru Girarta yashafa yace inasan wannan girar ma Sannan yadawo Kan idonta yana shafawa kafin yayi magana ta Bude idonta, cikin shagwaba tace Yaya Allah bacci nakeji, Dan Allah kabarni nayi Taya zan barki kiyi bacci Bayan baki tsaya munyi fira ba, Kuma baki bani abunaba Cikin mamaki tace wanne irin Abu Kuma? Bakinsa ya turo gaba yana yi mata nuni da nashanunta Aida sauri tarufe idonta, gaba daya kunyarsa ta Kamata Hannayenta ya janye data rufe idonta dasu, cikin kasala yace bakya son nabarki kiyi baccin? Gabanta na faduwa tace inaso Cikin tsananin sha'awarta da buqatuwa yace toki bani Ko Dan kadan ne saina barki kiyi baccin kinji? Shiru tayi masa Ahankali yace inyi? Cikin kunya ta Daga masa kanta Bakinsa ya Dora awuyanta yafara kissing dinta in gentle Shiru tayi tana jinsa, Amma gabanta banda faduwa babu abinda yake Yana kissing wuyanta ahaka harya saukko Kan abinda yake mutuwar so, Ahankali yaja rigarta ya cire ta Gaba daya, yanayin tozali dasu yayi musu kyakykyawan kamu Bakinsa ya Dora akai yanasha, saiga Iman tayi Shiru tanajin wani irin dadi Idanunsa jajir yadago kansa ya kalleta yace kinajin zafi? Dasauri ta girgiza kanta, kunnanta yaje yarada mata Cewa akwai dadi? Ahankali cikin kunya tadaga masa Kai alamar eh Kansa ya maida yaci gaba da abinda yake, can Taji Abu yanayi mata zafi, rintse idonta tafara, tana yarfe hannu Cikin azaba tace Yaya akwai zafi Shikuwa baima jitaba, kawai qara qaimi yake Akan abinda yake, kuka tafara tana Cewa Yaya Aliyu akwai zafi wallahi, zafi sukemin Bakinsa ya cire Daga kansu yahade bakinsu waje daya, cikin rashin nutsuwa yake kissing dinta, gaba daya yafice a hayyacinsa, laushin fatarta dakuma Yanda take masa shagwaba ne yasa yaqarajin tsananin buqatarta Da zafi zafi yake neman hanyar shiga harya samu, ananfa Iman ido yaraina Fata, kuka take sosai, Hajiya Yaya zai kasheni, mamy, Farhan, zainab, babu wanda Iman Bata kiraba, Amma tahadu da soja, kunnuwansa duk arufe suke babu abinda yakeji awannan lokacin *** *** *** Washe gari Cikin kuka tace Allah bazan zauna dakai ba, nide kawai kamaidani wajan Hajiya Murmushi yasaki, ganin Yanda ta hauka ce masa lokaci daya, yace yanzu Bilkisu haka kikeso muje wajan hajiyan? Kingafa tafiyarki ma Bata daidai ta ba, kibari Zuwa gobe saimu hada yanamu yanamu mutafi wajan hajiyan, Eh naji, Allah Ko baka kaini ba, saide kadawo kaga Bana nan, wallahi bazan zauna ka kashe Niba Awannan lokacin Kam Saida yadara yace naji, nayarda Amma yanzu de Kisha tea dinnan, ga maganin ki Kisha, insha Allah gobe sai wajan hajiya Tea din takarba tana Sha Ahankali, sai shagwaba take masa, Shikuwa sai biye mata yake *** *** *** Kunnansa daya takama ta murde, da karfi yace Auch mamy! Cikin fishi tace yanzu baby abinda kayi ka kyauta Kenan? Zakaje ka kashe yar mutane Ko? Kunya ce takama shi, tuni ya sunkuyar da kansa, yace mamy kiyi hakuri Tace a a bani zaka Bawa hakuri ba, idan tatashi a baccin akwai abinci da paracetamol kabata tasha, Amma nafadama karka sake irin wannan gangancin Kansa aqasa yace to mamy Tana tafiya yashiga cikin dakin na Iman, tana bacci, Idanunta sun kumbura, alamar tasha kuka, yasan Cewa tabbas yabata wahala, Amma Yaya zaiyi? Shima ba'ason ransa Hakan ya kasan ce ba Zuba mata ido yayi yanashi mata albarka cikin ransa Yana zaune harta farka, dasauri yatashi yace matar Aliyu me kikeso? Saida ta yatsima fuska tace Yaya ciwo nakeji Har yanzu awajan Cikin tausayawa yace kiyi hakuri insha Allah zai daina Ahankali kinji? Daga masa Kai tayi Key ne yabata yace gashi Fatima Kallansa tayi tace key ne fa Yaya na menene? Sabuwar motor Dana sake Miki ce, Itama Bilkisu nasa antura mata Tata kano dazu Cikin murna tasakar masa kiss akumatu tace wayyo Yaya Mungo de sosai No nine d godia ai, abinda kika bani Daren jiya yafimin komai, Allah yayi Miki albarka Cikin kunya tace amin Yaya Muje kiga motor Ko? Gatanan a waje dingisa kafarta tafara zasu fita, yace nahutar dake, yasa hannu ya dauketa cimak suka futo taga motor sannan suka dawo ciki *** *** *** After 4 year's Momy yaushe zamu tafi gidan su Haidar? Iman t kalli yar Tata yar shekara hudu tace Bilkisu gobe zamu tafi dukanmu harda mamy ma Cikin murna tace yeeee tafice da gudu Aliyu dake aiki a computer yadago kansa yace Suma dazu dazu suka kirani Wai yaushe zamuje nace musu gobe de muna nan Kan hanya insha Allah, nafadawa Bros ma kowa yazama cikin Shiri da munzo next week zamu wuce Saudia gaba dayanmu Kanta ta Dora akafadarsa tace to mijin Fatima, Allah yakaimu, Mungo de Allah yaqara budi, kissing dinta yayi yace amin matar Aliyu Gidan Aliyu Kenan, inda suke gudanar da rayuwar su shida mamy da Iman, sai babbar yarsu yar shekara hudu Mai sunan Bilkisu, da Kuma qanin ta Mai sunan Imran Suna kiransa da Lil Imran Suma akano haka abin yake, Bilkisu nada Yara biyu maza, daya sunan Aliyu anace masa Haidar, sai qanin sa Kuma maisunan mahaifin Aliyu Sa'ad Ana kiransa da boy Haka rayuwar su take gudana cikin kwanciyar hankali da kaunar juna Tammat bi hamdullah Anan nakawo karshan wannan littafin nawa Dan karami Mai Dan Karan dadiπŸ˜‚πŸ˜ƒπŸ˜‚ Mutara asabon novel Dina Mai Zuwa insha Allah, Allah kabamu ikon yin amfani da abinda yake Mai kyau acikinsa, kuskuren danayi aciki, Allah kayafeminπŸ™πŸ» Taku Har kullum Mrs Usman ce ✍🏻 Downloaded From https://tknovels.com.ng