Downloaded From https://tknovels.com.ng KULSUM 3 Littafin SUMAYYAHABDULKADIR takorikabara@gmail.com SADAUKARWA Ga dukkan matan da ke fama da lalurar 'nocturnal enuresis'(fitsarin kwance) a gidan aure. GODIYA Godiya ta musamman ga Nura Sada Nasimat sabida jimirinsa na bin rubutuna kafin bugawa da bada shawarwari. Allah ya raya mana zuri’a rayuwa mai albarka. JINJINA Ga daukacin mambobin TAKORI'S ONLINE FORUM, littafin Kulsum ya jinjina muku, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. You are my source of inspiration. GARGADI Banyar da a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba ba tare da iznina ba, tun daga radio, facebook, whatsappp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne, kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'I Wali. KULSUM-3 Har tana tuntube, saura kadan ta fadi… ta samu ta rike marikin kofar ofishin ta yunkura ta fice da mugun sauri. Ba ta tsaya a ko’ina ba sai a jikin motar Taufeeq. Babu inda ba ya rawa a jikin ta, ta tabbata Turaki ne ta gani ba mai kama da shi ba. Fatan ta a lokacin kawai shi ne ta hango fitowar Taufeeq su bar asibitin gabadaya, amma har aka shafe mintuna goma babu Taufeeq ba mai kama da shi. Sai can ta hango su su biyu suna tahowa a tare, da shi da Turakin, sai waige-waige suke yi. Rasa inda za ta sa kanta ta yi, sai kawai ta daddage ta taka da gudu ta boye a bayan wasu shuke-shuke. Daga inda ta ke tana iya hango su har cikin motar Taufeeq suke dubawa, daga baya Turaki ya juya cikin tafiyar nan tasa ta ‘ya’yan saraki ya koma cikin asibitin, Taufeeq kuma ya dauko motar sa ya tuko a hankali yana bin gefen hanya da idanunsa, tana iya hango tashin hankalin da ke shimfide baro-baro a kan fuskar sa. Sai da ta ga ficewar sa daga get din asibitin, sannan ta fito daga bayan shuke- shuken ta zo bakin get domin ta fice ta tari taxi zuwa Victoria Island gidan Sakeenah. Tana zuwa get masu gadin suka taso suka kulle get, suka koma gefe suka fuske, suna kiraye-kirayen waya. Wani mugun takaici ya kama Kulsum, ko kallon arziki ba su yi mata ba, amma sun kulle kofa sun hana ta ficewa. Ba'a jima ba ta ga mota kirar Acura na fitowa daga cikin asibitin zuwa inda suke. Tun daga nesa ta gane mai tukin nan cikin tsananin nutsuwa kamar bai son taka kasa. TURAKI ne. A wannan lokacin ba gilashi a idon sa, wannan ya ba ta damar gane shi sosai. Da gane irin canjawar da ya yi. Juyawa ta yi ta karasa gaban masu gadin ta soma rokon su su bude mata kofa. Ko daga ido su kalle ta ba su yi ba, har motar Turaki ta iso ta yi parking a gaban ta kamar za ta take mata ‘yan yatsun kafar ta. Zama ya yi cikin motar yana kare mata kallo. Ga wani makalallen murmushi a gefen bakin sa. Ya bude motar ya fito gaba-gadi, rataye da falmaran din bakaken suit din jikin shi a kafadun sa. Gaban ta ya zo ya tsaya suna fuskantar juna. Kallon ta kawai yake da idanun nan nasa da ke zuwa mata kullum cikin mafarki, ko a ido biyu. Yayin da ta yi kicin-kicin da fuska, za ka rantse da Allah bata taba sanin fuskar da ke tsaye gaban ta ba a tsayin rayuwar ta. “Malam lafiya?” Kulsum ta yi tambayar, muryar ta na rawa, tana mai dojewa kallon tsakiyar lumsassun idanun sa. “Na zo fita ka sa an tare ni, na ci bashin ku ban biya ba ne?” Ba ta yi aune ba ta ji hannun ta cikin na Turaki, shidewa ta kusan yi na wucin gadi, kafin ta tantance me ke faruwa, ya ja ta tana tirjewa ya bude motar shi ya sanya ta, tare da rufe kofar da key din hannun sa. Ya zagaya ya shiga mazaunin sa ya tashi motar. Masu gadin suka wangale masa kofa ya fice, suna daga masa hannu cikin girmamawa. Tafiya kawai yake bisa shimfidaddun titunan garin Lagos ba tare da Kulsum ta san inda aka nufa da ita ba. “Malam sace ni za ka yi? Malam ina ruwan ka da ni ne? A ina ka sanni? Malam ni matar aure ce ko ba ka gan ni tare da miji na bane?”. Tambayoyin Kulsum kenan ga Turaki, cikin rawar muryar da ke gab da rushewa da kuka. Idan stiyarin motar ya ba ta amsa, to mai tukin motar ma ya ba ta, inda ta ke wannan bai kalla ba, sai sharara gudu yake, amma makalallen murmushin da ke kan tattausar fatar bakin sa ya kasa bacewa. Kulsum ta soma bugun gilashin motar da duka hannayen ta, fatan ta gilashin ya fashe ko da zai yanke ta ne, ta yi ihun da mutane za su ji su kawo mata dauki. Amma ta lura gilashin motar ko sound ba ya badawa kuma ko za ta shekara tana bugunsa ba zai fashe ba. Kawai sai ta fashe da kuka tana kiran Goggon ta da Baffan ta. Abin da ya yi matukar bai wa Turaki dariya. Ya dube ta da lallausar murmushi ta gefen lumsassun idanun sa, cikin rada ya ce, “Saura Batulu da Umma!”. Idanun ta cike da kuka, amma hararar shi ta ke, daidai lokacin da suka kawo wani check-point na ‘yan sanda. Daga murya ta yi sosai tana kwarara ihu ba ta san cewa murya ba ta fita daga gilashin ba. Sai ta daga hannuwa tana yi wa ‘yan sanda alamar da ta sa daya daga cikin su ya zo jikin motar tare da kwankwasa gilassan, Turaki ya sauke glass a hankali ya kuma nuna masa katin shaida (I.D card) na shaidar aikin sa, nan da nan dan sandan ya yi baya yana daga masa hannu, ya yi sama da gilassan motar da sauri ya sake shan round ya shiga unguwar Ikoyi. Kulsumu ba ta bar kuka ba, don ta gane in ma sata ce Turaki ya gama sace ta. Sun wuce kyawawan gidaje kamar guda biyar kafin su shiga wani kyakkyawan lodge mai hawa daya. Maigadi ya zo ya bude, Turaki ta zura hancin motar sa cikin gidan. Ya yi parking a rumfar adana motoci wadda ke dauke da wasu motocin guda biyu, ya kashe motar tare da sakin ajiyar zuciya. Ya dubi Kulsumu wadda ta ki dagowa daga cinyoyin ta balle ta san inda ya kawo ta. Sautin kukan ta kadai ka ke ji a motar, kamar wadda aka gaya wa sakon mutuwar iyayen ta. Kirjin sa ne kawai yake dagawa yana sauka da sauri-da-sauri. Wani lokacin excitement zai iya haifar da bugun zuciya. Mutum ya fadi ya mutu farat daya. To hakan ce ta faru ga Turaki, wanda ke ganin komai da ke faruwa da shi yau kamar a mafarki… wai shi ne da Kulsumu a gabansa! Idan mafarki yake yana rokon Allah kada ya farkar da shi daga wannan mafarkin, har sai ya ga karshen sa, har sai ya gan shi tare da Kulsum matsayin ma’aurata a karo na biyu. Ashe duk mahaukacin neman nan da yake wa Kulsumu tana cikin kasar Nigeria, a garin da yake yawan rayuwa? Allah shi ne shaida kan babu abinda ya wahalar da shi a duniya irin neman da yai wa Kulsumu, shekaru dai-dai har guda hudu. Shi Allah da yake Gafurur-Raheem ne, yau ga shi ya tankado keyar Kulsumu ya kawo mishi ita har cikin ofishin sa. Shin shi wane irin wawa ne da zai yi saken da za ta sake kufce masa??? “If you are done with the cry (idan kin gama kukan) ki wuce mu karasa ciki”. A matukar fusace Kulsum ta dago ta dube shi, idanun ta a rufe sabida bacin rai, ta ce, “Da wacce hujja zan bi ka inda ban sani ba? Me ye hadin ka da ni? A ina ka san ni, ko na yi maka kama da ‘yammatan da ake daukowa bisa titi a garin Legas a kawo su guest house ne?” Kyabe baki ya yi, ya ce, “Ni ma ban san me ye hadin nawa da ke ba, kuma ba ki yi kama da ‘yammatan bisa titi ba, sannan nan ba guest house ba ne, gidan mutane ne, hujja ta ta cewa ki bi ni ciki mu zauna mu yi magana ta nutsuwa ita ce; kin yi min kama da matata ne, matar da ban saki ba har gobe, amma na neme ta na rasa”. Ya karasa maganar da kasalallen murmushin sa na gefen baki. “Ina so in tabbatar ne, I just want to confirm ko Kulsumu na ce wannan....I just want to confirm idan matata UmmuKulsum da na rasa nake nema ce… I just want to confirm idan reaction dinta saboda gani na a inda ba ta yi tsammani ba, yana nufin itama ta gane ni ne take pretending....ko kuwa wani abin ne daban ya firgita ta ta ke gudu tana neman mafaka…”. Kafin ya rufe baki Kulsumu ta amsa, “ni ban gane ka ba, babu wani sani da na yi maka. Ban sanka ba, ban taba ganin ka ba, sannan ni matar aure ce, kuma tare da mijina ka gan ni, amma ka sa aka rufe min kofa saboda tozarci, saboda ka sato ni ka kawo ni guest house. To tsakani na da kai Li’ilafi dubu”. Turaki ya yi wani murmushi, wani tattausan murmushi da rabonsa da yin emotional murmushi irin sa ba zai iya tunawa ba. He salute her courage! Yau ji yake babu wanda ya kai shi sa’a a duniya, babu wanda ya kai shi samun cikar buri. Ashe zai ga Kulsumu komai daren dadewa! Sai dai kuma watakila ganin nata ya zo at a wrong time, idan har abin da ta ke fadi gaskiya ne na cewa (wanda suke tare mijin ta ne). Idan har wannan ikirarin nata gaskiya ne, shi ya ya zai yi da rayuwar sa? Saboda ita ne har yau bai kara aure ba. Saboda ita ne har yau babu diya macen da ke burge shi. Saboda ita ne yake jin zai iya kare rayuwar sa single idan har bai same ta ba. Ashe ita tuni ta manta shi, she have move on tare da wanin sa. A zahiri bai kamata ya ga laifin ta ba, amma sai ya ji gabadaya duniyar na juya masa. Idan har da gaske matar auren ce, ya san hatta wannan kebewar da ya yi da ita a cikin motar sa haramun ne, sai dai ji yake in wannan shi ne haramun din da zai halaka shi… ba zai bari ta sake kubuce masa ba. “Look Ummukulsum, duka cikin mu nan ba yaro karami, ki yi ta pretending din ki ba zan hana ki ba, amma in kin ga na barki kin bar gidan nan, to kin fito mun shiga ciki ne, mun zauna mun yi magana, na fahimce ki kin fahimce ni". Kulsumu cikin shesshekar kuka, ta ce, “Ta ya ya zan yarda in bi ka ba ni da masaniyar ko za ka cutar da ni? Ta ya ya ka ke tunanin zan yarda in shiga inda daga ni sai kai babu muharrami a tsakanin mu, alhalin na kasance matar aure?” Turaki ya lumshe idon sa na sakan biyu ba tare da ya bude ba, kalmar auren nan tata da take ambata ta kasa yi masa dadi, ta kasa zauna masa a rai, haka ta kasa daina gasa zuciyar sa, sannan ya kasa yarda da ita, ya ce, “ki sa a ranki cewa, kina cikin amana ta, ke da auren naki. Amanar da idan na ci ta sai Allah ya saka miki. Ki yarda komai lalacewar duniya har gobe akwai sauran masu amana da kokarin cika alkawari”. Kulsumu ta ce, “babu ruwana da amanar ka, ko me za ka gaya min ka gaya min yanzu ka sallame ni in tafi, ni dai na san ban san ka ba, ban taba ganin ka ba ko a hanya. Kawai ka ga matar mutane a titi ka sako ta a mota ta karfi ka dauko ta, wannan ai cin mutuncin aure da keta haddin dan Adam ne”. Ba ta rufe baki ba Turaki ya bude motar ya fito, cikin zafin nama ya zagayo ya bude tata kofar, kama duka hannayen ta yayi ya dunkule a cikin nasa. Sannan ya janyo ta ta karfi daga motar. “Ni ma ban ce ki ce kin san ni ba, mu je a ba ki san nin ba, ni ma ai ban sanki ba Kulsum, amma dole mu yi magana ni da ke”. A haka suka shiga falon gidan, falo ne tsararre english parlour, bata ankara ba ta ga ya sa mukulli ya rufe kofar ya jefa mukullin cikin aljihun trouser din sa. A tsaye Kulsumu ta tsaya ta ki zama, Turaki ya tako har gaban ta ya tsaya hannayen sa duka biyu zube cikin aljihu kamar yadda yake a al'adar sa. Ya yi kokarin kallon tsakiyar idanun ta ya sakar mata signal. Ta dauke kai, amma hatta hantar cikin ta kadawa ta ke yi. Yana da wani irin effect (tasiri) a kan ta tun zamanin kuruciyar ta. Ta yadda idan ya kasance a gaban ta, ko ya gifta ta gaban ta hatta hantar cikin ta rawa take yi. Yau da ya kasance a gaban ta cikin wani sabon yanayi da bata taba tsammata daga gare shi ba, babu inda ba ya rawrawa a jikin ta, including tsokar zuciyar ta. "Ummukulsum yaya rayuwa? Yaya bayan saduwa? What is special a bayan rabuwar mu?" Bata bashi amsa ba, illa sunkuyar da kan ta da ta yi. Kamshin one man show ya cika hancin ta. Turaki ya kara takowa zuwa gaban ta, space din dake tsakanin su bai fi taku biyu ba. Ya ce. "Aka ce ba kya kasar? Aka yi ta wahalar da ni? Ashe kina cikin kasar nan Kulsumu? Kin samu rayuwa yadda kike son ta kin manta da ni ko, ni ina can ina ta wahalar neman ki lungu da sako, , Kulsum tell me about you ko dan yaya ne. I'm extremely intrigued! Me ya kawo ki Lagos?" Wannan karon ne ta dago kai ta dube shi cikin ido. Kai tsaye ta gatsine fuska ta ce "AURE! Aure ne ya kawo ni, ba zan gaji da gaya maka cewa ni matar aure ba ce. Ka mayar da ni inda ka dauko ni, tun kafin miji na yayi karar ka". Zuba mata ido ya yi kamar ya hadiye ta. Hannayen ta duka biyu Turaki ya kama kafin ayi haka ya rungume ta da wata irin azama, wata irin kyakkyawar runguma wadda ta hade bugun zuciyar su wuri guda, yana sauke numfashi da sauri, yana barin dukkan excitement din zuciyar sa ya na fita ta cikin numfashin sa. "Ko waye ya aure ki yayi aure kan aure UmmuKulsumu, ni da baki na ban taba sakin ki ba..... kuma har abada bazan yi ba! Kuma na rantse sai kin dawo gidan ki da yardar Ubangijin sammai da kassai. I don't mind your pretendings.... ki cigaba da yi, shekaru takwas da nayi ina dakon wahalar soyayya baza su tashi a banza ba..... this is a promise (wannan alkawari ne)". Kokari take ta zame daga jikin Turaki amma ya ki bata damar hakan. Kawai sai ta saka masa wani gigitaccen kuka da yasa dolensa ya sake ta, amma bai saki hannun ta ba, sunkuyawa yayi ya sumbaci goshin ta, karan hancin ta da saman bakin ta, abinda ya kara gigita Kulsumu, ta fizge daga rikon sa da karfi ta ja da baya tana hararar sa, tamkar idanun sa fado, murmushi ya yi, ya bude kofar falon suka fita. Bai sake ce mata komai ba. Shi da kan sa ya bude mata kofar motar ta shiga, shima ya zaga mazaunin sa ya zauna, sai da ya kara bata lokaci yana kallon ta da murmushin da bata taba ganin sa da shi ba. Gabadaya ta canza masa, ta koma masa sabuwar Kulsumu, ba 'yar ficikar yarinyar da ya aura a kauye ya gudu ya bar ta ba, tana ta sharar hawayen dake gudu a fuskar ta da gefen mayafin ta. Alamu ne dake nuna zuciyar ta na tono old memeories masu daci a kan sa da ta dade da binnewa lokaci mai tsaho. Ya kunna motar ya taka totur din ta, reverse ya yi ya fita daga ma’adanar motocin ya doshi get cike da kuzari. Maigadi ya bude musu kofa ya hau bisa kwalta yana jan motar tamkar tayoyin ta sun yi faci, sabida rashin gudun ta. “Wace unguwa zan kai ki Ma’am?” “Ka kai ni bus stop zan samu taxi zuwa gida”. “Wannan ne kuma ba ki isa ba, sai na damka ki hannun solobiyon mijin ki, kamar yadda na yi masa alkawari”. Wayar sa ya dauko ya kira lamba ya sa a kunnen sa, tare da saka wayar a handsfree, tarrr ta ji muryar Taufeeq yana fadin, “Doctor kun gan ta? Ga mu nan duk hankali a tashe”. Turaki ya ce, “security sun ganta, muna kan hanya yanzu haka. Fada min address din naku”. Tana ji Taufeeq na fadin lambar gidan Aunty Sakeenah da sunan unguwar Victoria Island. A ranta ta ce, “Shi ke nan tawa ta kare!". Amma a fili ban da kukan bakin cikin Turaki, ba abin da ta ke da rinannun idanun ta. Suna sanyo motar cikin get din gidan Aunty Sakeenah gabadaya jama'ar gidan suka nufo su har Engnr. Farouq. Shi ya bude side din da Kulsumu ke zaune, yayin da Taufeeq ya bude wa Turaki. Tana fitowa Nasmah da Aunty Sakeenah suka yi kanta suna kiran sunanta don tabbatar da lafiyar ta. Ba ta tsaya ba, wuce su ta yi dukkan su ta yi cikin gida da gudu, Aunty Sakeenah ta bi bayanta hankali a tashe. Taufeeq na bude masa kofar ya fito, inda Taufeeq din ya ba shi hannu, sannan suka yi musabaha, Taufeeq na ta yi masa godiya, ya ce, “Amma anya Doctor do you think she is okey?” Murmushi Turaki ya yi, wanda ya fi kama da na rainin hankali, ya ce, “Lafiyar ta kalau, na fi kyautata zaton akwai abinda ta gani ne wanda ya hargitsa ta. Amma tunda kai mijin ta ne ai za ta gaya maka”. Da haka suka yi sallama, Engnr. Farouq ma na ta yi masa godiya. Gabadaya suka rufu zuwa cikin gidan, Mujaheed ya ja Nasmah gefe suna magana. Tsayawa suka yi bakidaya a kanta, kowa da tambayar da yake jefo mata. “Kulsumu lafiyar ki kalau?” Sakeenah ta fada. “Ya ya za ki yi min haka Kulsumu? In kai ki asibiti mu shiga ofishin likita, kawai sai in juyo in neme ki in rasa? Kin daga min hankali yadda ba kya zato, kadan ya rage jini na ya hau, to ina ki ka shiga cikin asibitin da muka neme ki muka rasa?” In ji Taufeeq. “Ku yi mata a hankali, ba kwa ganin kuka ta ke ne? Duk mu kyale ta zuwa ta samu nutsuwa, please, na tabbata ko mene ne za ta gaya muku”. Cewar Engnr. Farouq. Da wannan duk suka watse suka bar ta da Taufeeq, ya zauna kusa da ita, ya kira sunan ta a tausashe, “Kulsum”. Ba ta amsa ba, kamar yadda ba ta dago ta kalle shi ba. Ya dora hannun sa bisa nata, ai da mugun sauri ta janye hannun ta. Abubuwan sun mata yawa, har suna son fin karfin kwakwalwar ta. “Wai me ke damunki ne? Are you okey?” Maimakon ta ba shi amsa, sai ta mike ta nufi toilet, ta shige tare da rufe kofar da mukulli, ba tare da ta ce da shi komai ba. Ya dade a zaune inda ta bar shi cikin matsananciyar damuwar da ya kasa gano ta inda zai bullo mata. “Ko dai Kulsum ta yi gamo da aljannu ne?” Wani bangare na zuciyar sa ya tambaya, a karshe ya ga shawarar Engnr. ita ce abar bi, wato su ba ta lokaci ko zuwa gobe ne. Yana so ya kira Hajiya Nasara ya gaya mata, amma bai san me zai ce mata ba, tunda bai san abin da ke damun Kulsum din ba. Don haka ya tashi jikin sa a sanyaye ya bar dakin zuwa falo, suka hadu dukkan su suna ta tattaunawa a kan al’amarin, kowa da abin da yake fadi. Sakeenah ta dubi Nasmah kamar ta mare ta, ta ce, “Tun farko da izinin wa ki ka dauke ta ku ka fita? Ba ki san amarya taka tsan- tsan ake da ita lokacin auren ta ba? Yanzu in gamo ta yi me ki ke so na gaya wa Mum? Da ma ba da son ranta ta yarda ta barta ta zo ba, ta fi so ko mene ne a yi shi a can Abuja da Gaya”. Nasmah ta yi narai-narai da ido, “Wallahi Aunty Sakeenah ba ni da laifi, kin gansu nan, su ne suka kira mu”. Ta fada tana nuna Taufeeq da Mujaheed. Taufeeq ya dalla mata harara, ya tashi ya bar wurin. Sakeenah ta ci gaba da yi wa Nasmah fada, ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba, kan don me za ta biye musu? Tunda ta san gyaran jiki ake mata kuma ba a barin ango ya ga amarya har sai bayan daurin aure. Nasmah dai ta karbi laifin ta, Mujaheed shi ne mai bada hakuri, don ya ce shi Taufeeq tausayi ya ba shi, ya damu ya gan ta sosai, amma su kwantar da hankalin su insha Allahu babu aljannu a tare da ita, kamar dai yadda likitan da ya kawo ta ya ce ne, wani abin ta gani ya hargitsa ta. Cikin dare Nasmah na barci, Kulsum ta tashi ta zauna dungurgur! Ya zama dole ta nema wa kanta mafita. Mafita daga auren mashayi wanda ba za ta iya ba, ko ita ta fi kowa halarci a duniya, da kuma kubucewa daga inda Turaki zai sake samun ta. Turaki daga dukkan alamu bai zo gidan su don ya kawo ta kawai ba, sai don ya ga inda ta ke. A yayin da ita kuma ba ta ga dalilin hakan ba. Duniyar sa ta riga ta kare a tata duniyar, ba ta fatan wata mu’amala ta sake hada su ko da ta gaisuwa ce. Ya riga ya gama playing duk wani game din sa cikin rayuwar ta. Ba ta jin a yanzu za ta iya sake daukar wani komai kankantar sa. Allah da ya hada Ya riga ya raba, don hakan ya zama alkhairi a gare ta. Alkhairin da ta ke zaton Taufeeq ne, ashe shi ma nashi kalubalen har ya fi na Turaki. Shawara ta karshe da ta yanke wa zuciyar ta shi ne, ta yi nisa da dukkan su, ta tanadi kalaman da Hajiya Nasara za ta fahimce ta ranar da duk Allah ya sake hada su. Mikewa ta yi ta dauko handbag din ta, ta duba return ticket din ta ta tabbatar yana nan. Tana da kudi wajen dubu ashirin a jakar ta, ta tabbata za su ishe ta har ma su yi canji. Allah-Allah ta ke a kira sallar asubahi, daidai lokacin da ta san maigadin gidan Sakeenah na tafiya zuwa masallacin kusa da su. Yadda Kulsum ta ga rana yau haka ta ga dare. A kan idonta da kunnen ta aka tada sallar asubahi, ko kayan ta ba ta dauka ba ban da handbag, waya da hijabin sallarta dogo har kasa. Sadaf! Sadaf! Ta fice daga dakin ta bar Nasmah na ta kirba minshari. A zuciyar ta tana fadin, “Sai watarana Nasmah! Zan yi kewar ki ba ‘yar kadan ba”. Ta kai bayan hannunta ta shafe hawayen idanun ta ta fice daga dakin. Kofar falon wadda za ta fidda kai waje jam-lock aka saka mata ta ciki. A hakali ta bude ta fice ta rufo kofar silently. Kanta tsaye ta doshi get inda cikin sa’a ta tadda maigadi ya shiga masallaci kamar yadda ya saba. Sakatar kofar wucewar mutum daya ta zare ta fice a hankali tare da rufo kofar. Sauri ta ke ta yi kamar za ta tashi sama, sai da ta kai bakin titi ba ta ga mota ko babur ba. Ta dan jima tsaye a titi tana waigen bayanta ko an biyo ta. Cikin ikon Allah sai ga wani okada-rider ya zo zai gifta gabanta. Da saurin ta ta tare shi, ta ce da shi cikin harshen Turanci ya kai ta airport na garin Lagos ko nawa yake so za ta ba shi. Mai okada har cikin airport ya shiga da ita, naira dubu biyu ya ce ta ba shi. Ba musu ta kirgo ta ba shi, sannan ta karasa. Ba yau ta fara hawa jirgi daga Abuja zuwa Lagos ba, don haka ba ta sha wahalar samun jirgin Abuja ba, amma sai karfe takwas na safe zai tashi, lokacin bakwai ta kusa. Don haka ta soma neman inda za ta buya, ta yadda ko su Taufeeq sun biyo bayan ta ba za su ganta ba. Cikin fasinjoji ta kutsa ta shige, masu jiran lokacin tashin jirgi, ta ja hijabin ta ta rufe fuskar ta. Karfe bakwai jirginsu ya tashi daga Lagos zuwa Abuja. Tana sauka a Abuja ta nemi taxi ta ce a kai ta Jabi Motor Park. Tana zuwa ta tambayi inda ake lodin Kano, aka nuna mata. Ta biya kudin mota, cikin sa’a motar saura mutum daya ta cika, tana shiga direban ya tada mota suka durfafi Kanon Dabo. Sai wannan lokacin Kulsumu ta samu ta sauke ajiyar zuciya, at least she escaped daga Taufeeq har Turaki. Ta san Baffa da Goggo za su fahimce ta, sannan ba za su taba bari rayuwar ta ta tozarta da auren mashayin giya ba. Kamar yadda ba za su kara bari azzalumi, mugu, mai son kansa, makiyin ta Turaki ya sake dawowa cikin rayuwar ta ba. Ta sa a ranta ta gama zaman Abuja, ta gama zaman gidan Hajiya Nasara, ta dawo gaban kakannin ta kenan har abada! Da ma karatu ta je yi, kuma cikin yardar Allah ta yi ta gama. Za ta koma mahaifar ta ta gina sabuwar rayuwa, ba za ta yarda ta wargaza rayuwar ta da sunan halarci ba don ko Ubangiji bai yarda da wannan ba. Haka ba za ta yarda a karo na biyu Turaki ya sake zamowa barrier ga farin cikin rayuwar ta ba. Tafiyar awanni biyar ta kawo su Kanon-Dabo, inda daga nan ta hawo bus mai zuwa garin GAYA. Bakin ta dauke da addu’o’i masu yawa na Allah ya sa Goggo da Baffa su fahimce ta, su fahimci ta yi hakan ne ba don butulci ga Hajiya Nasara ba, sai don ta gina wa kanta kyakkyawan future. Ba ta ji dadin auren kuruciya ba, ba ta fatan ya kasance shi ma auren da ta yi cikin cikakken hankalin ta ya zo ya samu nakasu, tunda kuwa zuciyar ta ba za ta iya juriyar zama da mashayin barasa ba. *** *** *** Baffa Jibo na gyare-gyare cikin dakin da yake jibge amfanin gonar sa, kafin ya kai su kasuwa. Ya jiyo wata siririyar sallama kamar ta Kulsumu. Kwana biyu ke nan da tafiyar Goggo Abuja, shi kadai ne a gidan, shi bai je ba don nan Gaya za a taho daurin aure ranar asabar. Duk wanda ya kamata su gayyata sun gayyata, mutanen 'Yalleman gobe za su wuce Abuja, inda za su kwana biyu daga can za su taho bakidaya ranar juma’a zuwa Gaya tare da Hajiya Nasara da jama’arsu, a yi daurin aure asabar, su juya da amarya ranar lahadi. To sai ga wata makalalliyar sallama yana ji kamar muryar Kulsumun. A cikin muryar akwai jigata da alamun gajiya. Da sauri Baffa ya fito, ya kalle ta sanye da zumbulelen hijabin ta har kasa idanuwan ta duk sun fada, ta yi zuru-zuru saboda wahala da yunwa. Baffa ya bude baki ya ce, “Kulsumu, ke ce? Ko kuwa mai kama da ke ce?” Ai tana ganin Baffa, hawaye ya kece mata. Ta karasa da azama ta rike shi cikin kuka, ta ce, “Ni ce Baffa”. “Lafiya na gan ki yanzu? Ke da waye?” “Ni kadai ce, tun daga Lagos na taho”. Baffa ya yi salati, ya sallamewa Ubangiji, amma sai ya kama hannun ta suka shiga dakin Goggo, sai da ya tabbatar ta kwanta a gadon Goggo ya juya yana fadin, “Jira ni ina zuwa”. Baffa bai fi minti goma sha biyar ba ya dawo rike da bakar leda guda biyu, gasasshen balangu ne mai yawa da damammiyar fura a ciki, ya samu har zuwa lokacin kuka ta ke yi kasa-kasa. Babban tashin hankalin ta shi ne, kada Baffa da Goggo su kasa fahimtar ta sabida kunyar Hajiya Nasara. Ba ta da nufin tozarta Hajiya Nasara ko shi Taufeeq din kansa, amma wannan aure ba za ta yi shi ba, domin ba ta son ta kara yin aure ta sake fitowa, auren mashayi kuwa babu kwanciyar hankali a cikin sa, sannan ‘ya’yan da za ta haifa watarana sai sun tuhume ta da zaba musu uba mashayin giya tunda dai Allah da ya nufe ta da gani gabanin auren, ya nufe ta ne da rahamar sa. Ko da ma can ita ba damuwa ta yi da ta yi aure ba, sannan Taufeeq ba wai tana masa mugun so ba ne, abubuwa ne da yawa suka taru suka yi dalilin amincewar ta da auren sa. Muhimmi shi ne, mahaifiyar sa da ‘yan uwan sa, sai kuma takurawar su Goggo a kan ta yi auren. Amma ita tun daga kan auren Turaki ba ta kara marmarin aure a rayuwar ta ba. Har yanzu ba ta daina tsoron maza ba. Ba ta daina tunanin dukkansu halin su daya ne ba. Halin selfishness da heartlessness irin na TURAKI. Wadanda ba su dauki mace a bakin komai ba. Baffa ya ce, “Tashi maza ki ci wannan, ko kin samu karfin yin sallah”. A halin da ta ke ciki ta manta da wani abu wai shi abinci. Duk wani kyakkyawan tunanin ta ya ta’allaka ne a kan yadda za ta samar wa kanta mafita daga auren Taufeeq, auren da sauran kwanaki uku a daura shi. Amma ta san in ba ta ci abincin nan ba, ba za ta samu nutsuwar yi wa Baffa bayanin da zai fahimce ta ba. Don haka ta sauko kafafun ta daga gadon karfen Goggo, ta karbi ledojin da Baffa ke mika mata. Ya juya ya fita yana fadin, “Ki ci ki yi wanka da sallah, sannan mu zauna in ji me ya faru kin ji Kulsumu? Ki kwantar da hankalin ki, da raina da lafiya ta babu abin da zan kasa yi miki”. Wadannan kalaman na Baffa su suka sanyaya mata zuciya. Har ta samu karfin gwiwar cin naman sosai. Da ma tsakanin ta da balangu akwai kyakkyawan aminci. Ta shanye furar gabadaya wadda ba'a cika mata sukari ba, sannan ta tashi ta je ta yi wanka ta dauro alwala. Sai da ta rama duka sallolin da ke kanta, sannan ta ji nutsuwa ta soma shigar ta. Sai da Baffa ya dawo sallar isha sannan ya kira Kulsumu a dakin sa. Ta shigo sanye da hijabi ta zauna ta rakube abin tausayi. Baffa ya ce, “Kulsumu?” Ta ce, “Na’am Baffa”. “Ina so ba tare da kin boye min komai ba, ki gaya min duk abin da ya faru. Mene ne dalilin tahowar ki daga wajen marikan ki kwanaki uku kafin daurin auren ki ke kadai tun daga Lagos?” Kulsumu ta share hawaye, ta ce, “Baffa auren ne na fasa”. Baffa ya hadiye fushin sa da razanar sa, ya ce, “A wane dalili, ko ko don ki wulakanta dattakon mu, ki saka hairan da sharran?” Hawaye suka zubo wa Kulsumu, ta ce, “ko daya Baffa, sai don in tserar da kaina daga sake zawarci a shekarun girmana, bayan wanda na yi a shekarun kuruciya ta, in zaba wa ‘ya’yana uba na gari, in kuma yi jihadin ceton tarbiyyar ‘ya’ya na a can gaba”. Baffa ya kasa fahimtar ta, sai ya ce, “kai tsaye ki gaya min, me ya faru?” Kulsumu ta sunkuyar da kai. “Baffa zan fi so a ce yana zaune zan fada, don kada ya samu damar cewa na yi masa sharri. Sannan Hajiya da Daddy kada su zarge ni da munafuntar su”. Baffa bai ce komai ba, sai ya yi shiru yana nazarin kalaman ta, amma hankalin sa ya tashi sosai, don ya kasa cankar inda zancen ta ya sa gaba. Kira ne ya shigo wayar Baffa a lokacin. Yana dagawa ya ce, “ga Nasaran nan ma”. Ya amsa suka gaisa a mutunce yadda suka saba, sai dai ya ji muryar ta ba yadda ya saba jin ta ba. Ta ce, “Baffa, Kulsumu Gaya ta taho?” Baffa ya dubi Kulsumu, sannan ya ce, “ga ta nan a gabana”. Wata irin ajiyar zuciya Hajiya Nasara ta saki a fili, ta jero alhamdulillahi sau uku. Ta juya ta ce da su Goggo, “Kun ji Kulsumu na Gaya”. Goggo ta yi salati ta sanar da Ubangiji, ta ce, “Idona idon Kulsumu… wannan yarinya ta dauki alhakin mu, ni Taufeeq na fi tausayawa, dubi yadda ya fita hayyacin sa sabida neman ta, wannan sakarci da me ya yi kama? Ki kamo hanya tun daga Legas ba tare da sanin kowa ba?” Hajiya ta nisa, ta ce “Ku daina fadan nan Goggo, ni na tabbata Kulsum cikin hankalin ta ta ke, akwai muhimmin abin da ke damun ta da ya sa ta aikata hakan. Da ma gobe za mu tafi Gaya dukkan mu ko mene ne za mu hadu a yi maganin sa, Daddy sai ranar daurin aure ya yi niyyar tafiya, amma gobe zan sa shi a gaba mu tafi tare gabadaya har Taufeeq din”. Hajiya Nasara ta kira Malam Hadi ta ce da shi, mutanen ‘Yalleman kada su zo Abuja, su zarce Gaya su ma gobe can za su tafi, an fasa yin kamu da wunin a Abuja. Taufeeq na shigowa ta gaya masa Kulsum na Gaya,. Zama ya yi jabar! A kan kujera ya rasa abin da ke masa dadi. Me ke damun yarinyar nan ne tamkar mai motsuwar kwakwalwa? Hajiya Nasara ta dube shi ta kasan idanu kafin ta yi magana cikin bacin rai. “In ma wani abun ne ka yi mata wanda har ta zabi ta koma wajen iyayen ta, kada ka yi tunanin za ka yi amfani da ni ka cuce ta, ita din marainiya ce kuma amana a hannuna. Zan yi adalci ne na gaskiya a tsakanin ku”. A jigace Taufeeq ya dago ya dube ta, he is looking helpless tun tafiyar Kulsum, tun jiya yake cikin tashin hankali da wahalar da Kulsum ta sabbaba masa. Shi kuwa me zai yi wa Kulsum da har za ta zabi barin su? Babu komai cikin zuciyar sa a kanta sai tsananin so da kaunar ta. Iyakar tunanin sa ya san bai yi mata komai ba. Ko dai Kulsum ta fasa auren sa ne shi ya sa ta ke tsiro da wadannan bakin halayen? Wani abu da shi kuma ba zai taba lamunta ba, ya yi saken da Kulsum za ta kubuce masa. Shi kadai ya san wahalar da ya sha kafin ya samu kanta, ko me ta ke so zai yi mata… amma ban da fasa aure! Washegari tun asubah suka kamo hanyar Kano a cikin babbar (Land Cruiser) din Daddy, Taufeeq ke jan motar, Daddy na gefensa, Hajiya Nasara da Goggo suna baya, Nasmah ba ta biyo su ba sabida ba za ta iya jure tafiyar mota ba, za ta jira su har su dawo tare da amarya in an dauro aure. Mujaheed sai goben zai bi su ya samu daurin aure. Karfe goma sha daya na safe suna cikin Kano, daga nan suka dauki hanyar Gaya. Wajen karfe daya na rana Taufeeq ya kashe mota a kofar gidan Malam Jibo. (Daga can nesa da su, wani gajeren saurayi ya fiddo waya jikin sa har rawa yake, ya lalubo lamba ya kara a kunnen sa). *** *** *** Daga inda ta ke kwance a kan gadon karfen Goggo tana jiyo sallamar su daya bayan daya. A hankali ta runtse ido tare da kiran sunan Allah. Goggo ce ta fara shigowa dakin ta haska ta da tocilan kasancewar dakin ba haske. Kwafa ta yi tare da cewa, “Kin kyauta abin da ki ka yi. Shin Kulsumu ke karamar yarinya ce, ko ko goyon ki ake yi? Kin bi kin daga wa bayin Allah hankali babu gaira babu sabar. Yanzu ga shi kin taso su bagatatan, wai kina cikin hankalin ki kuwa?” Kulsumu ta gyara kwanciyar ta ba ta ce wa Goggo komai ba. Ta yi bambamin fadan ta har ta gaji, Kulsumu ba ta tanka mata ba. Hajiya Nasara ce ta shigo ta bude tagogin dakin da Kulsumu ta rurrufe, haske ya wadaci dakin. Ta ce, “Fadan nan ya isa haka Goggo, ki bari su Daddy su dawo sallah sai mu zauna da ita mu ji damuwar ta. Na san Kulsumu ba za ta yi abubuwan da ta ke yi haka kawai ba”. Sannan ne Kulsumu ta samu lafiya daga sababin Goggo, ta sauko ta yi wa Hajiya Nasara barka da zuwa, tare da tambayar Nasmah. Hajiya Nasara kallon ta kawai ta ke tana mamakin yadda ta zabge cikin kwana biyu kacal. Ta ce, “Nasmahn da ki ka kusa sa wa nakuda lokacin ta bai yi ba. Ki ka jefa su a tashin hankali, ai ba ki da guts na tambayar ta. Amma Kulsum ko ma mene ne ki tsallake ni ki taho tun daga Lagos har Gaya ke kadai? Gaskiya ban ji dadi ba. Na dauka ni ce mutum ta farko da za ki fara dosa da kowacce damuwar ki?” Kulsum ta yi kasa da kai, ta ce, “Ki yi hakuri, ba zan sake ba Mum”. Iya abin da ta fada ke nan. Don bata da kalaman kare kan ta. Bayan kowa ya yi sallah mazan sun dawo daga masallaci, Baffa ya yi musu shimfida a falon sa. Tunda suka shigo Taufeeq ke raba idon ganin Kulsumu amma ko inuwar ta bai gani ba. Har sai da Baffa ya yi wa Goggo umarnin a kirawo Kulsumu. Daddy na zaune kusa da Baffa, Taufeeq a kusa da shi, sai Hajiya da Goggo daga kusa da kofar dakin. Kulsumu ta yi sallama ta shigo kanta a kasa, ta ja mayafi ta rufe fuskar ta. Daga kusa da Hajiya ta zauna ta ki yarda ta kalli bangaren da Taufeeq yake, wanda ke cikin dukkan damuwar duniyar nan, ya rasa abin da ke damun ta. Ya bi ta da kallo har ta nemi wuri ta zauna. Baffa ne ya bude taron da addu’a, sannan ya ce, “Na ji dadi da ku ka zo bakidayan ku, domin na yi-na yi da Kulsumu ta fada min abin da ya taso da ita haka afujajan tun daga Lagos har Gaya ita kadai, ta ki gaya min. Ta ce sai Taufeeq yana zaune”. Ya gaya musu a halin da ta zo masa jiya na jigata da fita hayyaci, sannan ya dube ta, ya ce, “To Kulsumu, ga Taufeeq ga iyayen sa, ga kuma mu kakannin ki wadanda ba ki da wanda ya fi su, muna so ki gaya mana abin da ke damun ki, ko hankalin wadannan bayin Allah ya kwanta a ci gaba da shirin daurin aure”. Kulsumu ta muskuta, ta ga cewa wannan ita ce damar ta ta karshe, idan ta yi shiru Baffa ya fusata da ita, ko ta zo daga baya ta fada ba zai saurare ta ba. A cikin ranta kuma sai ta ji tausayin Taufeeq ya darsu mata, don ita ta san irin masifaffen son da yake mata. Amma dole ta fadi abubuwan da idanun ta suka gane mata, ko da a ce zai musanta hakan. In ba haka ba hankalin ta ba zai taba kwanciya da shi ba. “Ke muke saurare Kulsumu, duka wajen nan babu bare, kamar yadda babu abokin wasan ki, idan ba ki da damuwa ki fada mana mu kama abubuwan da ke gaban mu”. In ji Goggo. A hankali muryar Kulsumu ta fito, ta ratsa kunnuwan su. “Baffa, na fasa auren Taufeeq, ku yi hakuri”. Goggo ta yi shiru tana mamakin karfin halin Kulsumu, shi kuwa Taufeeq dagowa ya yi a firgice ya dube ta. Duk da bai yi sa’ar ganin fuskar ta ba. Daddy ya hadiyi miyau da kyar, Hajiya Nasara kuwa a ranta cewa ta yi, ta san za a rina, don tuntuni ta yi zargin Taufeeq shi ne matsalar Kulsumu. Baffa ya ce, “Ko za ki fadi dalilin ki, tunda Allah ya hana hukuncin da babu hujja?” Kulsumu ta yi shiru, Daddy ya ce, “Kulsumu feel free to talk, we are all here for you. Idan mun amince da hujjojin ki ba za a daura auren nan ba”. Tausayin iyayen Taufeeq ya kama Kulsumu, amma haka ta rufe ido ta fadi abubuwan da ta gani a cikin firij din sa. Ta kare da cewa, “Ina tsoron auren ko da mashayin wiwi ne, balle giya. Ina tsoron halin da zan fada a gaba, da kuma ranar da ‘ya’yanmu za su gane dabi'ar mahaifin su, su zarge ni da zaba musu mai wannan dabi’a. Amma in Yaya Taufeeq ya ce na yi masa karya, yana iya rantsewa ba haka ba ne”. Tsit! Ka ke ji a falon, yayin da Taufeeq ya sunkuyar da kai yana hada zufa. Bai taba tozarta a rayuwar sa irin yau ba. Bai taba zato watarana asirin sa zai tonu ga iyayen sa ba, bai taba zaton abin da Kulsumu ta gani kenan ba ya hargitsa ta haka. Tun farko shi me ya kai shi kiran ta zuwa gidansa ya kasa hakurin a daura musu aure? Yau ga abin da ya janyo wa kansa. Hajiya da Daddy ne suka tsura masa ido, Daddy ya yi karfin halin cewa. “Da gaske ne Taufeeq?” Ya kara yin kasa da kansa kamar ya roki kasar ta tsage ya shige. Hajiya Nasara ta ce, “Da gaske ta ke ko sharri ta yi maka?” Cikin tsananin nadama Taufeeq ya ce, “Ba ta yi min sharri ba. Tabbas ta gani din. Amma Mum don Allah ku yi min afuwa, wallahi ban dade da fara sha ba… a komawa ta Lagos ne don in samu in rage tunanin ta, a lokacin da ki ka ce sai na jira ta for some years… na ga cewa ba zan iya jiran ba, shi ne na nemi abin da zai yi assisting dina, amma wallahi daga yau Mum na bari, na bari har abada, ba zan sake ba. Tsautsayi ne”. Goggo ta kawar da kai, jin hawaye na son zubo mata. Tausayin Nasara ya yi bala’in kama ta ganin halin tashin hankalin da ta fada lokaci daya. Daddyn Taufeeq kuwa kada ka so ka ga fuskar sa a lokacin sabida tsananin fushin da ke cikin ta. Ya ce, “Taufeeq, sabida mace ka zabi ka sha GIYA, ka saba wa Ubangijin ka? Duk tarbiyyar da uwarka ta yi maka? Ba ka sha giya a Turai ba sai a Nigeria Muhammad Taufeeq?” Hawaye Taufeeq ya soma, ya ce, “Daddy na yi kuskure, na yi nadama, zan yi istigfari, amma don Allah kada ku hana ni auren Kulsum, wallahi daga yau na bar giya har abada!”. Hajiya Nasara ta mike hawaye fal idon ta, ta ce, “Maganar aure tsakanin ka da Kulsumu babu ita, na soke ta har abada. This is your punishment, ka je ka yi karatun-ta-nutsu. Don mai shan giya bai iya rikon aure sai dukan mata. Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi”. Goggo ta ce, “Ku yi masa afuwa mana, don Allah ke Kulsumu ba kya afuwa? Da Allah ba ya afuwa gare mu da tuni bai kifar da duniyar ba? Dukkan mu masu kuskure ne, sai ake so in muka gane kuskuren mu a karbi hanzarin mu. Ki yi hakuri tunda ya ce ya bari”. Kulsumu ta girgiza kai tana hawaye. “Ba zan iya ba Goggo, tunda Hajiya ta ce a yi hakuri, to a yi. Zan taya Yaya Taufeeq addu’a Allah ya ba shi wadda ta fi ni”. Daddy ya ce, “Goggo a bar maganar nan, Taufeeq has to be punished don gobe ya gane ba duk abin da ka ke so sai ka same shi dole ba, a kuma lokacin da kake so. Ya je ya yi karatun-ta-nutsu, ranar da ya tabbatar ya zama mutumin kirki ya dawo ya auri Kulsumu, amma aure gobe babu shi”. Ya mike shi ma ya fice. Hawayen idon Taufeeq suka gangaro, ya ce, “Don Allah Baffa ku ba su hakuri, ina son Kulsum ba zan iya hakura da rashin ta ba…” Baffa ya ce, "Taufeeq yanzu sun dauki zafi, ka bari su huce. Ba za su saurare mu ba. Ku tashi ku je, Allah ya yi muku albarka”. Duk yadda Taufeeq ya yi don ya kebe da Kulsumu ya samu ya lallashe ta ta ki fitowa daga dakin Goggo, har Daddy ya yi kiransa domin su tafi cikin Kano su kama hotel su kwana, gobe su biyo su dauki Hajiya Nasara su wuce, don lokacin magriba ta kusa ba za su iya kama hanya ba. Haka Taufeeq ya bi bayan Daddy, yana mai jin karshen duniyar sa ya zo. Yana mai hasaso yadda rayuwa za ta koma masa babu Kulsumu. Ya yi nadama sau ba adadi, nadamar da ya tabbatar iyayen sa ba za su karbe ta a wannan lokacin da suke cikin tsananin fushi da shi ba. Sun idar da sallar isha, Hajiya Nasara na kwance a dakin Goggo, zazzabi ya rufe ta, Goggon sai ba ta baki ta ke, tana cewa, ta dauki abin nan da sauki kada ciwon zamani ya shige ta, yaran yanzu ai kowanne da matsalar sa, kuma Taufeeq ya yi nadama tana da tabbacin in ya auri Kulsumu ba zai sake ba. Daga kwancen da ta ke Hajiya Nasara ta ce, “Allah ya kiyaye in hada Kulsumu da mai shan giya, kuma tunda sai ya samu Kulsumu ne zai bari ya je ya yi ta sha, Kulsumu ta riga ta tsere masa’. Sallamar yaro suka jiyo daga tsakar gida, Goggo ce ta fito tana amsawa. Ya ce, “Wai ana sallama da Baffa”. Goggo ta ce, “Tunda ya tafi sallah bai dawo ba…”. Ba ta rufe bakin ta ba sai ga Baffan na shigowa, fadi yake, “Kai din bako ne da za ka tsaya a waje kana sallama? Da can haka ka ke yi ba sallama ka ke yi kan ka tsaye ka shigo ba?” Ya shigo, bakon na biye bayan sa. Hasken farin wata ya haska wa Goggo fuskar Yarima Turaki, gabadaya tsakar gidan su ya dauki kamshin sassanyan turaren sa, a idanun Goggo har tsayi da girma ya kara, fatar sa sai sheki ta ke a cikin hasken farin wata, ga wata shadda mai maiko da ya zuba sai walainiya ta ke (Excelcior), ya dora hula wadda ta dace da shaddar jikin sa ruwan toka, hannayen sa biyu zube cikin aljihu kamar yadda ya saba. Sai faman sunkuyar da kai yake, yana murmushin da da ka gani ka san na rashin nutsuwa ne. Dazun nan da safe yaron nan Sadi makwabcin su Kulsumu da ya sa ya dinga yi masa dakon zuwan ta Gaya ya fada masa ta zo har da marikan nata, kuma ya ji kishin- kishin gobe ne za a daura auren ta. Duk abubuwan da ke gabansa haka ya zubar da su ya taho Gaya, bai samu jirgi da wuri ba shi ya sa isowar sa Gaya ke nan ko gidan su bai shiga ba ya zarto nan, don ya ga ko da abin da zuwan sa zai amfana masa. Har gobe jikin shi yana ba shi zai samu Kulsum, zai dawo da ita cikin rayuwar sa komai daren dadewa. Ganin ta da ya yi a Lagos ya kara tabbatar masa Ubangiji na nufin wani babban al’amari a tsakanin su. Goggo ta ce, “A’ah! Turaki ne tafe?” Yayin da Baffa ya shimfida masa darduma ya zauna, Goggo ta shigo ta zauna a gefe suna gaisawa. Baffa ya dube shi ya yi murmushi, ya ce, “To alhamdulillahi, da ma yanzun nan da ka gan ni na dawo, gidan ku za ni wajen Maimartaba, in gaya masa in har yanzu kana bisa ra’ayinka na neman komen Kulsumu, gobe ka kawo sadaki a mayar maka da matar ka”. Turaki ji ya yi tamkar zuciyar sa ta yi tsalle ta fito daga kirjin sa, sannan ta kuma yin wani tsallen ta koma muhallin ta. Ya ji shi tamkar yana yawo a kan gajimare, duk da haka bai gaskata kunnuwan sa ba, domin wani abu ne da ya zo masa bagatatan tamkar saukar aradu, ya bugi zuciya da kwakwalwarsa a lokaci daya. “Na’am Baffa… me ka ce?” Ya tambayi Baffa don dai ya samu wannan karon zuciyar sa ta karbi tabbacin maganar. Baffa ya sake maimaita masa, ya ce, “A da, gobe za a daura auren ta da dan uwanta, to amma an samu matsalar da ta sa aka fasa, sabida haka in har yanzu kana kan ra’ayin komen, ni a gobe zan yi wa Kulsumu aure, da ko ma waye, jama’ar da na tara ba ni da bakin sallamar su”. Baffa bai yi aune ba sai ganin Turaki ya yi ya fuskanci gabas ya yi sujjadah. Murmushi Baffa ya yi don ya fi kowa sanin wahalar da yaron ke yi a kan neman komen Kulsumu, ko sati daya ba a yi ba ya zo, amma bai gaya masa ta kusa aure ba, don ba ya so ya karya masa zuciya. Ya yi musu hidima mai yawa ta kayan abinci kamar yadda ya saba, Allah ya sani! Tun farko ya fi so Kulsumu ta koma wa Turaki, kunyar Hajiya Nasara ce ta sa ya amince da zancen Taufeeq. Bayan ya dago daga sujjadar Baffa gani ya yi hatta kyawun fuskarsa ya karu. Ya ce, “Baffa "na gode" ta yi kadan ta bayyana godiya ta. Na gode Baffa, Allah ya yi muku duk abin da ku ke so a duniya da lahira. Ya jikan mahaifa, ya ja kwanan ku. Yanzun nan zan je na fada wa Maimartaba da Umma, kuma a daren nan ba sai gobe ba za a kawo sadaki”. Mikewa ya yi zai fita, jikinsa har rawa yake. Baffa ya ce, “Bari a kirawo Kulsumun mana ko gaisawa ne ku yi”. Turaki ya juyo daga bakin kofa gaban sa na faduwa, ya ce, “A’ah Baffa, kyale ta za mu gaisa gobe. Yanzu dare ya yi”. A zuciyarsa kuwa ya fadi hakan ne gudun rigimar Kulsumu kada ta ruguje wannan maganar, amma kwarai zai so ya sake ganin ta. Bayan ganin da ya yi mata a Lagos, wanda ya hana shi ko da runtsawa tsayin kwanaki biyun nan gabadaya. A hankali yake tukin motar hawaye na sauka a kan kundukukin sa. Hawayen farin ciki irin wanda bai taba tsintar kansa a ciki ba. Kai tsaye cikin gida ya wuce da sassarfa, bangaren Umma ya nufa. Har dakin barcin ta ya duba ba ta nan, sai ga Laraba za ta gifta ya tambaye ta Umma, ta ce tana turakar Maimartaba, ita ce mai girki. Bai tsaya ya gama jin me ta ke cewa ba ya wuce bangaren mahaifin nasa. Sallama ya yi cikin kokarin daidaita nutsuwar sa, duk suka amsa mishi, Umma na serving Maimartaba abinci. Murmushi ya yi lokacin da Turaki ya gurfana a gaban sa yana gaisuwa. Ya amsa, sannan ya ce, “Yanzu da ma na ce Umman ka ta kira min kai a waya, kwana biyu idanun nan nawa sun matsa min da kaikayi, ga wani hawaye da ke yawan fitowa”. Turaki ya yi kasa da kansa, ya ce, “Allah ya kara ma yawan rai, zan kawo maganin da za a dinga digawa”. Sannan ba tare da ya jira amsar Maimartaba ba ya dora abin da ke cin sa a zucci. “Baffan Kulsumu ne ya aiko ni Allah ya kara maka lafiya, ya ce, in har yanzu ina son komen Kulsumu in aika sadaki gobe a mayar da auren ta da zaa daura a kaina”. Umma ta saki cokalin da ke hannun ta, ta ce, “Kai Turaki bana son hauka, ko dai soyayya ta sa ka fara kuncewa ne? Ya ya za su daura wa ‘yar su aure da dan uwanta ka ce wai wani an ce da kai za a daura?” Murmushi ya yi, ya ce, “Wallahi Umma babu shirme cikin magana ta, na je ne in gaishe su kamar yadda na saba, sai yake cewa an samu matsala da wancan an fasa, in zo a daura da ni”. Maimartaba ya ce, “to ban da abinki rabon kwado yana hawa sama ne?” Umma ta yi hamdala a fili, ta ce, “Ina ruwan Allah, abinda nake gaya maka kullum ke nan Turaki, cewa ka fauwala wa Allah komai, idan da rabon sauran zama a tsakanin ku Allah zai ba ka wannan damar”. Sai ga hawaye a idon ta. Ta kai hannu ta goge ta sake cewa, “Allah na gode maKa da Ka nufi Kulsumu da dawowa gare mu”. Maimartaba kuwa cewa ya yi, ya kirawo masa Galadima a waya. Nan da nan ya kira ya hada su. Yana ji Maimartaba na bada umarnin a hada dukiyar aure da sadaki na alfarma su je shi da Chiroma su karba wa Turaki auren matar sa ta baya. Tuni Umma ta fice zuwa dakin ta. Batulu ta fara kira, sannan Yaya Hadiza da Ramla ta ce, su yi kokari dukkan su su zo gobe, amma ba ta gaya musu makasudin kiran nasu ba. Nan kuma ta hada barorin ta da masu girkin bangaren ta ta soma bada umarnin girke-girken da za a yi gobe, da abubuwan da ta ke so a tanada, Laraba kawai ta gaya wa ko me ke nan, sai ga tsohuwar tana rawa tana juyawa. A waya Baffa ya kira Daddyn Taufeeq wanda ke cikin Kano tare da Taufeeq din, ya gaya masa hukuncin da ya yanke na maida Kulsumu ga mijinta don ba zai iya kyale ta ta sake kwana a gabansa babu aure ba. Duk da Daddy ya ji ba dadi, don shi ya yi hukuncin ne don in an kwana biyu Taufeeq ya sake nutsuwa a dawo da maganar auren. Amma sai ya kasa fadin kudurin zuciyar tasa kada Baffa ya ga ya yi son kai, ya bi bayan nasa. Ya sa albarka tare da cewa, insha Allahu da su za a daura auren Kulsumu gobe kafin su wuce. Bai gaya wa Taufeeq ba, don a lokacin ma yana gaban sa yana masa magiya da hawaye, da zai amsa wayar Baffa sai ya kauce daga gaban sa don bai san me wayar karfe goma na dare ta kunsa ba. Karfe goma sha dayan dare Galadiman Gaya kanin Maimartaba da Chiroma da limamin masallacin fadar Maimartaba Sarkin Gaya suka iso gidan Malam Jibo. Babu wanda za su aika don haka Chiroma ne ya yi sallama da kansa. Baffa da ke yi wa Goggo da Hajiya bayanin hukuncin da ya yanke a lokacin, ya fito don ganin masu sallama. Nan ya ga manyan bakin dake tafe cikin dare daga fadar maimartaba Sarki. Komawa ya yi ya sanar da su Goggo suka koma dakin Goggo ita da Hajiya Nasara, suna ta kakabin al’amarin a zukatan su. Hajiya Nasara ba ta yi mamaki can-can ba, don ta san su Baffa har gobe suna son Turaki. Baffa ya shigo da bakin sa har dakinsa, nan aka yi magana ta gemu-da-gemu. Ya ce, sadakin da suka kawo ya yi yawa, don Kulsumu ba yau za ta fara zuwa gidan su ba, Galadima ya ce ai ba su da hurumin maida ko sisi ga maimartaba. Nan aka sa lokacin daurin aure karfe goma sha daya na safe. Kuma a daren ranar duk wanda ya kamata ya san zancen auren Turaki a masarautar Gaya sai da ya sani. Mata ne kawai ba su da labari, su ma zuwa wayewar gari duk Laraba ta gama fesawa kowa labarin dawowar uwardakin ta UmmuKulsumu. Nan aka fara hidimar girki wanda za a raba wa jama’a bayan daurin aure. Daga nan kuma mata za su zarce da biki ne. Kulsumu na kwance uwardakin Goggo a daren ranar, ba ta san wainar da ake toyawa ba. Haka kawai ta ke fama da guilty conscience? Ta ke tuhumar kanta, anya hukuncin da ta yanke a kan Taufeeq ta yi daidai? Me ya sa ba ta yi hakuri ta aure shi haka ba? Ko don albarkacin iyayensa da ‘yan uwan sa, ta san son da Taufeeq ke mata idan ta ce ya bar abu komai tsaurin sa za bari, in har za ta yi farin ciki. Yanzu ga shi ta jefa iyayen sa cikin damuwa, ta hada su da dan su, anya hukuncin ta bai yi tsauri ba, kuma bai yi kama da butulci ba? Da wannan guilty conscience din ta kwana, tana jin kamar ta je ta samu Baffa ta gaya masa ta janye hukuncinta. Amma lokacin karfe biyu ne na dare, Hajiya na falon Goggo tana sallah, ta san shiriya ta ke roka wa Taufeeq a wurin Ubangiji. Ta san halin Hajiya Nasara, duk wata matsala idan ta tunkaro ta, to ta daina barci ke nan har sai ta ga karshen ta da karfin addu’a. Ta kara jin nadama ta lullube ta, ta sa a ranta gobe in Allah ya tashe su lafiya the first thing in the morning (abu na farko da zata yi da safe) shi ne gaya wa Baffa, Hajiya da Goggo ta janye hukuncin ta, za ta auri dan uwanta Taufeeq cikin kowanne hali, ta taimaka masa ya yi yaki da kowanne irin sabon Allah. Da safe bayan sun idar da sallar asubahi duk su ukun ba ta tashi a wajen ba sai da ta bude baki ta gaya wa Hajiya da Goggo ta janye hukuncin ta, a ci gaba da shirin daurin aure. Ba su ce mata komai ba sai ido da suka bi ta da shi suna tunanin ko dai ta samu depression ne? Baffa na shigowa daga masallaci, shi ma ta je ta gaya masa. Murmushi ya yi ya janyo wata jaka ya tura mata gaban ta. “Dauki wannan, sadakin ki ne. Amma ba da Taufeeq ba, da wanda Allah ya tsaga da rabon sa”. Kulsumu ta bi Baffa da kallo kamar za ta yi kuka. “Baffa, sadakata ka bayar?” Wani murmushin ya sake yi, ya ce, “Wace irin sadaka bayan ga sadaki irin wanda duk garin nan babu ‘yar wanda ta taba samun rabin sa? Ni ba sadakar ki na bayar ba, aure ne na na-gani-ina-so. Ba ki kara kwana daya gaba na sai da igiyar aure a kanki, domin kin gama zaman Abuja”. Hankali tashe Kulsumu ta bar gaban Baffa ta koma daki ta soma rusa kuka. Daga Goggo har Hajiya babu wanda ya rarrashe ta. Gari na wayewa suka shiga hidimar da ke gaban su kada jama’ar da suka gayyata su fara isowa ba su shirya komai ba. Karfe goma sha daya na safe, dumbin jama’ar garin Gaya da wajenta suka sake shaida daurin auren UMMUKULSUM ABDULHADI ‘YALLEMAN da YARIMA ABUBAKAR TURAKI ABDULLAHI a kan sadaki lakadan ba ajalan ba. ‘Yan ‘Yalleman sai ana gab da daurin aure suka iso. Daga nan ne kowanne bangare (gidan su amarya da gidan su ango) ya zarce da wunin biki. Turaki dai ko ganin sa ba a yi saboda yawan jama’a, kai ka ce an yi sati guda ana gayyatar su. Kodayake su su Goggo sun yi gayyatar haka duk wadanda su Hajiya Nasara suka gayyato daga Abuja domin halartar auren dan su, sune suka halarci daurin auren Kulsumu da Turaki a karo na biyu. Cikin mahalarta daurin auren har da TAUFEEQ MUHAMMAD BELLO (tears). Boye kansa ya yi bayan daurin aure a cikin sassan shi da ke cikin gidan, ya gabatar da alwala ya sallaci walha (dhuha), sannan ya dora da sallar nafila raka’a biyu ya yi godiya ga Allah da Ya cika masa buri na karshe a rayuwar sa. Duk wasu burikansa Ubangiji ya cika masa su daya bayan daya, wanda yake gani a matsayin mafi wahala (wato samun Kulsumu), yau ga shi Ubangiji ya cika mishi ba tare da kokari, dabara ko iyawar sa ba. Lallai ne shi Allah fa’a’alun lima yuridu ne (wato mai aikata abin da ya so) a kuma lokacin da Ya ga dama. Wayar sa ya lalubo daga cajin da ya sanyata tun jiya, mutum na farko da ya kira shi ne, Dr. Abdul’Ahad Aminu Maikano, ya ce, "Aboki, kana ina?” Ya ce, “Ina Manchester, amma gobe insha Allah zan koma Reading”. Ya ce, “To kunnen ka nawa?” Murmushi ya yi mai sauti ta cikin wayar, ya san albishir din ba zai wuce a kan Kulsumu ba, the only obstacle of Turaki. To ko dai ya samo ta ne? Ya ce, “Kunne na goma sha biyu, plus na Turaki in an hada da nawa sun zama sha hudu kenan”. Dariya ya yi, ya ce, “To kai komai sai ka sa wasa a ciki? I called to inform you yau na zama angon UmmuKulsum for the very second time, cikin yardar Ubangiji da amincewar sa”. Dr. Abdul’Ahad ya ce, “Idan wasa ka ke min, to bana so mu yi magana ta gaskiya”. Turaki ya ce, “Na taba yi maka irin wannan wasan? Well, ba ni da lokacin ka yanzu. Zan so ka zo Gaya, akwai hawan angonci na musamman da zan shirya next week wanda ba a taba irinsa a Gaya ba. It''s a promise da na yi da dadewa cewa duk ranar da zan yi auren soyayyah zan yi hawan angonci. Your Horse is reserved for you (an ajiye maka Dokin ka)." Zuwa yanzu Abdul’Ahad ya yarda Turaki da gaske yake. At last ya samu Kulsumu, kowa zai samu lafiya. Ya ce cikin murmushi, “Dole ne ma in zo, ko don in ga Kulsum, in ga shin me ta taka haka da ta sukurkuta min aboki shekara da shekarusaura kadan yayi asarar likatancin sa a kanta?”. Murmushi Turaki ya yi, ya kashe wayar sa ba tare da ya ba shi amsa ba. Shi kansa in za'a tsare shi ba zai iya fadar abu guda daya da yake son Kulsumu sabida shi ba, ita din bakidayan ta yake so, the whole her. (Dukkanta). *** *** *** Umma ta aiko an gaya wa Goggo gobe lahadi da yamma za su dauki amarya, don haka duk wani shirye-shiryen su daga yau zuwa gobe gare su. Hajiya Nasara ta sa Sakeenah ta hado duka kayan dakin Kulsum da suka tanada ta taho da su Gaya a gobe-goben nan. Ba ta gaya mata ko me ke nan ba, ta dai ce ta yi kokari ta zo tare da kayan, kuma kada ta gaya wa Nasmah komai kada ta dage sai ta biyo ta ta zo tana haihuwa a kan hanya. Washegarin ranar Sakeenah ta iso da motocin kaya, Baffa ya bude dakin da ya ajiye wadanda Maimartaba ya aiko wa Kulsumu tun ma kafin auren ya juye kan dansa. Aka hada da wadanda su Hajiya Nasara suka yi wa Kulsum aka wuce da su gidan Sarkin Gaya inda za a yi wa Kulsumu kafi. Amma sai Maimartaba ya ce, Turaki ba zai zauna cikin gidan ba wannan karon, sassan ya yi musu kadan kuma ya tsufa, ya mallaka masa sabon gidan sa da ya gama ginawa a bayan gari, don haka can aka wuce da kayan, aka kuma yi wa su Hajiya Nasara da za su yi kafi jagora zuwa can. Lokacin da su Batulu suka iso, Umma ta gaya musu kome ke nan. Batulu hawaye ta dinga yi, farin ciki ya kai mata ya kawo. Ta ce a lokacin za ta tafi gidan su Kulsumu, Ummah ta ce ba ta yarda ta je ta cikata da dumi ba, ta bari sai gobe su je su dauko ta gabadaya. Dr. Sakeenah ta ji abin da ya faru, ta yi bakin ciki sosai a kan Taufeeq, ta yi fatan Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi, Ya yi wa Taufeeq sauyin alheri. Sun je sun yi kafi, suka dawo suna ta yaba tsaruwar gidan, Lami matar Malam Hadi ta rangada wa Kulsumu guda aka ta ce, “Allah ya sa kannen ki a damshin ki Kulsumu, gida kam na duniya kin yi shi, Allah ya sa na lahira ya fi shi”. Kulsumu wadda tun wayewar garin yau ta ke risgar kuka, damuwar ta shi ne, wannan aure da Baffa ya yi mata mai kama da auren sadaka da mijin da ba ta san ko waye ba. Duk maganganun da mutane ke yi a kan gidan wanda suka je kafi suka dawo ko daya bai burge ta ba. za ta fi so a ce Baffa ya yi hakuri ya kara mata lokaci ta kawo masa wani mijin, tunda ba su karbi nadamar ta a kan Taufeeq ba. To shi wannan din an san nasa halin? Kada dai ta yi gudun gara ta tadda zago. Kada garin neman gira ta rasa ido. Allah ya sa dai Baffa ba kudi ya gani ba, tunda yana ikirarin sadakin ta duk Gaya ba ‘yar wanda ta samu kamar sa. Su kuma ga su sun zo suna santin gida. Amma da ta tuna ko wane ne Baffan nata, ta san hakan ba za ta taba faruwa da shi ba. Ba ta samu kebewa da Babanta Malam Hadi ba sai da ya zo tafiya bayan daurin aure, kasancewar shi ba zai kwana ba, amma su Lami duk suna nan sai sun raka Kulsumu dakin ta. A zauren farko suka tsaya sabida yadda gidan ke cike da jama’a. Ya dubi Kulsumu wadda idon ta ya yi kozai-kozai don kuka, babu wata kwalliya ta amare a tare da ita. Haushin kowa ta ke ji, musamman Baffa. Ko da Aunty Sakeenah ta yi mata magana kan ta canza kayan jikin ta ko hoda ce ta shafa kuka ta fasa mata. Kukan da ya sa dole ta kyale ta, don ita Sakeenah ba ta son kuka a rayuwar ta. Malam Hadi ya ce, “Kulsumu komai ki ka ga ya faru da bawa, da ma rubutacce ne a lauhul mahfuz, wani ba ya auren matar wani kamar yadda wata ba ta auren mijin wata. Ki sa a ranki duk mijin da Allah ya zaba miki shi ne alherin ki. Na ji an fasa aure da shi wannan yaron dan wajen marikiyar ki sabida wasu matsaloli da suka taso. To dama ni tun farko na amsa ne sabida karamcin iyayen sa gare ki, amma Kulsumu na fi so ki koma gidan tsohon mijin ki. Hausawa suka ce da sabon gini gwanda yabe, su kam ai sun sanki ciki-da-bai din ki, babu wani abu naki da zai zame musu sabo, ke ma kuma in kin nutsu kin kwantar da hankalin ki sai kin fi jin dadin gidan Sarkin Gaya. A hankali Kulsumu ke daga kumburarrun idanun ta tana bude su a kan Baban ta. Wai me yake nufi ne da wannan zancen nasa? Ita ko alifun ba ta fahimta ba, ban da sunan gidan SARKIN GAYA. Har ya yi mata sallama ya sanya mata albarka tare da yi mata addu’o’I masu yawa ya tafi, Kulsumu ba ta koma daidai daga razanar da ya sanya ta a ciki ba. Maganar gidan Sarkin Gaya da ba ta fahimci musabbabin ta ba. Ga shi har ya wuce ya tafi ba ta nemi karin bayani daga gare shi ba. Harshen ta kamar an daure mata shi, haka ta ja jiki ta koma cikin gida kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Gadon Goggo ta hau ta kwanta, ta lumshe idanun ta tana sauke ajiyar zuciya. Cikin dare ta kasa barci sai juyi a kan gadon karfen Goggo, ta tabbata ita din yanzu matar aure ce, matar wanda ba ta sani ba, ta yi sallama da Taufeeq daga cikin rayuwarta. Kwata-kwata kwakwalwar Kulsumu ta ki yarda ta karbi zancen gidan Sarkin Gaya da malam Hadi ya yi mata, sabida tsabar ba ta kawo hakan a ranta ba. Ta fi sa wa a ranta ya fada mata ra’ayin sa ne kawai na gidan da ya fi so ta yi zaman aure. Ko mecece kaddarar ta tunda ita ta ki karbar Taufeeq ita ta ja wa kanta, dole ta karbe ta da hannu bibbiyu. Amma ba ta taba lissafo wa da Turaki cikin kaddarorin da ka iya samunta ba. Duk da haduwar su a Lagos ya bankado shafuka da yawa daga karkashin zuciyar ta da ta dade da binnewa na ciwon abin da ya yi mata. Wai "matarsa da ya rasa bai sake ta ba". Ta tuna statement din sa. Ita ta san wannan ba Turaki ba ne, Turakin gaske bai taba son ta ba! Turakin da ta sani daban yake da wanda ta gani, tunda ta aure shi har Allah ya raba su ba ta taba ganin murmushi a fatar bakin sa ba. Amma haduwar su a Lagos Turaki har rungumar ta ya yi, ya sumbace ta passionately, duk da ce masa da ta yi tana da aure, sannan ta ga murmushin sa ya kai sau nawa, wanda ya kusa tafiya da sauran numfashin ta. Tana wannan tunanin har aka yi kiran assalatu a kan kunnen ta. Har aka tada sallah ta kasa motsawa, sai da Goggo ta bubbuge ta. Ko da ta yi sallah kasa komawa barci ta yi, idon ta ya soye, zuciyar ta ma ta soye kamar soyayyar gyada marau- marau, da tunanin yau ne rana ta biyu da za ta sake barin gaban iyayen ta zuwa gidan aure. Akwai fargaba mai yawa a tattare da ita, wadda ta cika ruhin ta sakamakon tunanin shi kuma wannan auren me za ta je ta tarar a cikin sa? Idan lalurarta ta dawo fa? Tunda har gobe likita bai ba ta tabbacin warkewa gabadaya ba? Babban abin da ya sa ta ke gudun aure ke nan, ba ta so ta kuma yinsa a sake sako ta. Sannan ba ta son terere da bankada a kan lalurar da Allah ya dora mata. Duk da jikin ta yana ba ta ta gama warkewa, Dr. Sakeenah ma na da tabbacin hakan. A haka barci mai nauyi ya dauke ta, a karshe ta bingire a kan sallayar tana yin sa bilhakki, babu wanda ya tashe ta don sun lura kwanan ido biyu ta yi. Washegari gidan aka tashi da hidimar tafiya kai amarya wanda za'ayi da yamma, Dr. sakeenah ta ja hannunta suka shige dakin Baffa kasancewar ba ya nan ya fita. Wani fulas ta jawo ta aje mata a gaban ta ta ce, ta cinye kazar ciki tas! Ta ba ta kasusuwan, sannan ta ba ta wasu kwayoyin magani ta ce in ta gama ta hadiye su. Ta dube ta cikin ido, ta ce, “Na san Kulsumu ba za ki ki bin umarni na ba, na san kina girmama ni!”. Bayan fitar Sakeenah ta dade kafin ta fara ci. Kasancewar da yunwa ta kwana, sai naman ya yi mata dadi ta bude ciki ta ci sosai, ta hada mata kasusuwan kamar yadda ta umarce ta. Ta kuma hadiye magungunan da ba ta san na mene ne ba. Karfe biyar na yamma ‘yan daukar amarya suka zo, Dr. Sakeenah ta zabo mata wani sabon lace din ta don Kulsumu ba ta zo da kaya ba, sannan ba wasu kayan aure da aka kawo mata, Baffa ya sa an maida sauran ya ce, sadaki kawai zai karba kamar wancan karon. Wadanda suka zo daukan amaryar dattijai ne su uku, cikin wata kosasshiyar mota ta Maimartaba. Daya kanwarsa ce Goggo Hanna, daya yayar Umma ce da ta zo daga Gombe, dayar kuwa matar Galadiman Gaya ce Hajiya Rabi. A karo na biyu yau ma sai da Lami ta goya Kulsumu sannan suka iya tafiya da ita. Ko nasiha Goggo ba ta samu ta yi mata ba sabida tsananin tausayin da Kulsumun ta ba ta, ga ta cikin matsanancin kuka kamar na fitar rai. Abubuwa da yawa ne suka damu Kulsumu, zuwa yanzu ba ta damu da sai ta san ko wane ne mijin da iyayen ta suka zaba mata ba, domin ta sa a ranta wannan auren za ta je bautar Allah ne kawai albarkacin ba za ta iya tozarta Baffa ba. Ba ruwan ta da ko waye mijin. Tausayin Nasara da ‘ya’yanta shi ne babban abin da ya fi damun ta. Ta yi nadamar kin Taufeeq da ta yi, domin an ce ko a lahira wani kan ci albarkacin wani, amma ba ta duba hakan ba ta yi abin da zuciyar ta ta fi kwanciya da shi, ga shi sakamakon hakan ya jawo mata auren wanda ba ta sani ba, ba ta san shi kuma mene ne nashi nakasun ba. Kugin da motar ta yi na karshe a kofar gidan Dr. Turaki ne, kyakkyawan gidan da duk garin Gaya babu mai kyau da tsarin sa. Asali Maimartaba ya gina gidan ne don hutawar sa ba da sunan Turaki ba, amma da ya ji kowa Turaki zai aura, ya tabbatar Turaki da gaske yake ya karbi zabin da suka yi masa da hannu bibbiyu, kuma ya yi damarar zaman aure ne yanzu da Kulsum, sannan kaunar sa ga yarinya UmmuKulsum wadda ba ya wa Turaki sha’awar kowacce mace sai ita, sabida sun zauna da ita, sun san halayen ta. Sannan sun amince da dattakon iyayen ta, da soyayyar da ta ke yi wa Turaki. Da wannan zazzafan darasin da iyayenta suka koyar da shi, su suka hadu suka faranta ransa har ya yi wa Turaki kyautar wannan dankareren gida. Abin da ya janyo kishi karara daga sauran matan sa, amma ba su da ta cewa tunda ba su da Da namijin da zai kara da Turaki, duk ‘ya’yan su mata ne a gidan aure. Su Batulu ai tun safe ana gidan amarya, da ita aka yi jere/kafi da komai. Ba ta damu da ta ga Kulsumu ba tana cikin sabga sosai. Yaya Hadiza ce ta taro su lokacin da suka iso, ta yi musu jagora zuwa dakin Kulsumun, wadda ke rufe ruf cikin yalwataccen mayafin da Dr. Sakeenah ta lullube ta da shi. Hajiya Nasara ce rike da ita, a kofar dakin ta gaya mata ta shiga da kafar dama, sannan da addu’ar da za ta karanta. Batulu ba ta gidan, Umma ta kira ta don ta je su hada kayan sallamar masu kafi da kawo amarya. Daga Yaya Hadiza sai Aunty Ramla da sauran sisters din Turaki da suke uba daya. Ko da wasa Kulsumu ba ta bude lullubin ta ba wai don ta ga inda aka kawo ta. Kukanta ta ke bilhakki duk ta jika mayafin ta da hawaye. Lokacin da ta ji su Hajiya Nasara na haramar tafiya sai ta rirrike ta, cikin kuka ta ce. “Mum ki yafe mini, kin yi min komai a rayuwa, amma ni na ki Yaya Taufeeq a kan ajizancin da babu wanda ya wuce shi. Mum daga baya na so in gyara kuskurena baffa bai ba ni dama ba, wallahi Mum da wannan damuwar zan rayu har karshen rayuwa ta…”. Ta fada jikin ta tana kuka mai nuna nadamarta. Hajiya Nasara ta riko ta sosai a jikin ta, ta ce, “Kulsum kada in kara jin wannan maganar a bakin ki, ke ‘yata ce kamar yadda Taufeeq yake dana. Ba Taufeeq ne ya hada mu ba zumuncin Allah ne wanda Ubangiji ya yi mana umarni dole mu yi shi. Da kin auri da na da ba ki aure shi ba, matsayin ki na ‘ya a gare ni ba zai taba canzawa ba. Ba ki da wadda ta fi ni ke da Goggo, kamar yadda ba ni wadanda suka fi ku. Ki sa a ranki Allah ne bai kaddara aure tsakaninki da Yayanki Taufeeq ba, ki taya ni addu’a Allah ya yaye masa halin da ya jefa kansa ya samu mata nutsattsiya kamar ki ya aura”. Kulsum ta kara rungume Hajiya Nasara tana sakin wani sabon kukan, ta ce, “Na gode, na gode Mum”. Ta ce, “Ba kin gode ba, be happy with your marriage, ki yi wa mijin ki biyayyah, shi din mai son ki ne. Ina da tabbacin wannan karon sai kin fi kowa farin ciki da zaman aure. Daina kukan nan in mun tafi ki dauro alwalla ki yi nafila raka’a hudu ki roki Ubangiji Ya dorar da farin ciki a rayuwar auren ki”. Tana ji tana gani duk suka shige motoci suka tafi babu wanda ya rage a gidan. Hatta masu aiki Umma ta ce sai bayan kwana bakwai za a kai mata. Ta yi kukanta ma’ishi, a karshe ta yanke bin shawarar Hajiya Nasara, wato ta yi sallahr nafila. Mikewa ta yi ta warware mayafin da ke jikinta ta ajiye, idanun ta suka hango mata kyakkyawan dakin nata, wanda ya ji rantsattsun furnitures tafiyayyu tun daga China. Ta san wannan aikin Hajiya Nasara ne, ta yi mata tanadin rayuwa da danta, amma a karshe gidan wani suka shigo. Ta girgiza kai a hankali, ta doshi kofar da ta tabbatar toilet ne. Tana murda kofar toilet don fitowa, Turaki na turo kofar dakin don shigowa. Sanye yake da wani irin tattausan yadin filtex fari sol, dinkin tazarce. Kansa babu hula, sumar nan baka wuluk da ya tara a U.K ta kwanta luf a kansa, sai sheki ta ke yi, hade da lallausar sajen fuskar sa wanda a lokacin samartakar sa bashi da shi. A hankali ta daga idanu ta dube shi. It was a sudden shock irin wanda zai iya haifar da bugun zuciya a lokaci guda. Fuskar ta kuma ba ta boye halin shock na ba- zata da ta shiga ba, sai ta tsaya standstill rike da hannun kofa. Ta rasa mafarki ta ke yi ko idonta biyu? Ya fi kama da mafarki, wanda kusan kullum ba ta rabo da yin irin sa,. Seeing Turaki a matsayin mijin ta!!! Wani tattausan murmushi ya yi, wanda ya nuna fahimtar sa ga halin firgicin da ta samu kan ta, ya kuma gane ba ta san kan shi Baffa ya maida auren ba. Wannan abu ya kara yi masa dadi ba kadan ba. Takowa ya yi a hankali zuwa gaban ta. Ya mika hannu da nufin ya kamo hannunta. Da wani mugun zafin nama ta ja da baya, sannan ta daddage ta fasa wani firgitaccen kuka tare da durkushewa a kasa tana ta gunza shi kamar za ta fasa dakin. Wannan abu ya matukar bai wa Turaki dariya, waje ya samu gefen gadon ta ya zauna, ya zuba mata ido, daga baya sai ya kishingide ya dauko wayar shi ya shiga danne-danne, ba da sanin ta ba vedio yake yi mata. Cikin gunjin kuka ta ke fadin, “Na shiga uku na lalace ni Kulsum, abin da Baffa ya yi min ke nan???” Wannan karon dariyar Turaki ta kasa boyuwa. Ya ce, “Ummukulsumun Turaki, this is the best decision ever, ki gode wa Baffa saboda ya taimake ki. Ya dawo da ke inda kike so ake son ki. Ina amfanin badi ba rai? Ina amfanin ki je gidan Taufeeq alhalin kina da mijin ki a gefe? To ki je ki kai masa me? Bayan Turaki ya kwashe komai tun Kulsum na kwailar ta? Ai da muguwar rawa gwanda kin tashi”. Ya karasa da wani mischievous smile (murmushin keta) a siririyar fatar bakin sa. Kulsum ta yi sak! Daga kukan fitar ran da ta ke yi tana nazarin kalaman sa, kafin wani dan lokaci ta gane me yake nufi. Wata zuciyar na cewa ta rufe shi da duka ko ta ji dadi, wata na cewa ta fice ta bar masa dakin. Ta je ta yi jinyar abin da ya same ta ita kadai. Kamar Turaki ya san tunanin da ta ke yi, ya mike kamar zai fita, kawai sai ya murza wa dakin key, ya tako ya iso har gaban ta ya durkusa. For the first time a rayuwar sa da ya samu kansa durkushe gaban mace, sannan da niyyar lallashin ta. Kulsumu ta yi wuf za ta mike, ya riko ta da kyakkyawan rikon da ba za ta iya kubucewa ba. Sannan a hankali ya mike shi ma suka fuskanci juna, kirjin ta na heaving faster and faster tamkar mai ciwon asthma, yayin da zuciyar Turaki ke wani irin circulating tana haifar masa da abubuwan da bai taba ji a rayuwar sa ba akan diya mace. Kulsum ba ta gama tantance halin da ta ke ciki ba ta ji Turaki ya rungume ta da wata irin kyakkyawar runguma (tight hug) yadda jikin sa ya ratsa ko'ina na jikin ta. Bugun zuciyar ta ya karu, kamar yadda nasa ke yi, suka koma bugawa a tare, kamar zuciyar su za ta ballo allon kirazan su ta fito. Kokari yake ya lalubo bakin ta, amma Kulsum ta ki ba shi damar hakan. Sai faman cusa kai yake a masangalin wuyan ta yana sunsunar ta yana kissing iya abinda zai iya samu. Zamewa ta yi ta kasan hannayen sa ta koma toilet da gudu ta banko kofa ta murza key. Ta koma ta jingina da kofar bandakin tana sauke ajiyar zuciya. Gara ta kwana a toilet da ta kwana tana ganin Turaki a gaban ta, kuma wai a matsayin mijin ta na sunna a karo na biyu. Tana jin shi yana mata magana a daidai kofar bandakin, “It’s okey, ni ba bakon zafi ba ne. Na bar miki dakin ki, ki kwana cikin aminci UmmuKulsumun Turaki. And dreamt of our twin babies masu zuwa nan da watanni tara”. Ya yi murmushin da har ta ji tashin sautin sa, ya sake cewa “Allah na tuba wane dare ne jemage bai gani ba? Ai sai daren mutuwar sa. Mutumin da ya yi hakurin shekara takwas ai ba zai gaza yin na dare daya ba”. Ita dai ba ta ce komai ba. Ya sake cewa, “Na barki lafiya Princess”. Tana jin fitar sa da rufo kofar sa, amma ba ta fito ba sai da ta tabbatar ya fita din. Tana fitowa ta murza wa dakin makulli. Kasa tada sallar ta yi, sai ta zauna a bakin gado tana tunanin rayuwar ta mai abun mamaki. Turaki as her husband for the second time, tare da wasu mabambanta halaye da suka barranta da nasa. Ba ta da zuciyar da za ta kara yarda da Turaki, kamar yadda ba ta taba shirya wa ranta sake rayuwa da shi ba. Zai sha mamaki kuwa, idan har yana zaton wannan karon ma zai ci galaba a kan ta, kamar yadda ya ci a baya, idan zaton sa karamar yarinya Kulsumun da, ita ce a cikin gidan sa yanzu. Sai yanzu ta gane maganganun da Baban ta Malam Hadi ke yi a kan gidan Sarkin Gaya, ashe-ashe nufin sa can za ta sake komawa. To me ya sa Baffa ya boye mata? Ba shakka don ya san ba za ta amince ba ne. Hawaye suka zubo mata, how could she forget his wickedness (ta ya ya za ta manta muguntar sa?) Shi ne yanzu ya zo yana ‘yar murya don ta tashi daga Kulsumu ‘yar kauye, mai fitsarin kwance? Ta koma yadda yake son ganin mace? Ko ta rasa miji me za ta dawo ta dauka a gidan Turaki? Gara masa ya maida ita inda ya dauko ta ko ya shirya zama cikin bakin ciki da tashin hankali, ba za ta taba zaman lafiya da shi ba har karshen rayuwar ta. A wannan daren, duk iya sata irin na barci da kyar ya iya sace UmmuKulsumu, tana kitsawa tana warwarewa, amma ta kasa gano hanyar da za ta bi ta tserar da kanta daga auren Turaki. Bakin alkalami ya riga ya bushe. Ta yi kuka, ta yi kuka har ta gode Allah. A rayuwa Baffa bai taba bakanta mata irin wannan lokacin ba, shin ko sun manta wane ne Turaki ne? Turakin da ya bula musu kasa a ido, ta koma sunan karamar Bazawara a dalilin sa, har ta yi zaman gidan sa ta kare ba ta taba ganin murmushin sa ba, kalma ta arziki bata taba hada su ba, bai taba daga ido ya kalle ta ba, sabida a baya bai dauke ta mutum ba, yanzu ne ta ke mutum, sabida ba ta fitsarin kwance, kuma ta yi ilmi ta goge? Zai sha mamaki kuwa, don ba don shi ta dage ta canza rayuwar ta ba. Ta canza ne don amfanin kan ta. Tabbas za ta aro rigar rashin mutunci wanda ba halin ta ba ne ta saka a zama da Turaki, sai ya maida ita inda ya dauko ta yana so ko ba ya so. Da wannan tunanin barci ya samu nasarar sace ta goshin asubahi. Turaki a nasa dakin bayan ya rage kayan jikin sa zuwa na barci, komawa ya yi falo ya yi waya da Abdul’Ahad, yana bukatar raba farin cikin da yake ciki tare da aminin nasa. Ya ce, “Aboki, ga ni ga Kulsum a cikin gida na, matsayin matata for the second time, wace irin godiya ya kamata na yi wa Ubangiji?” Abdul’Ahad ya ce, “ka yi sadaka ga mabukata, ka ziyarci marassa lafiya a asibiti, ka yi musu ihsani. Sannan ka yi damarar rike matar ka tsakani da Allah, don ba dabararmu ce ta sa Ubangiji ya dube mu Ya yaye mana damuwar mu ba. Rahamarsa ce da Gafarar sa gare mu”. Turaki ya gamsu da maganganun Abdul’Ahad, ya yi niyyar bin duk abin da ya ce da zuciya daya. Nan ya ce, “Amma wani hanzari ba gudu ba, Kulsum matukar fushi ta ke da ni Aboki, don ba ta ma san da ni aka daura mata aure ba. Fushin da ban san yadda zan yi in rarrashe ta ba”. Murmushi Abdul’Ahad ya yi, ya ce, “Turaki kada ka bada maza mana, ai kawai rikidewa za ka yi daga likitan ido ka koma Romeo, ka yi hakuri da duk abin da za ta yi, za ta gaji ta bari ne tunda bakin alkalami ya bushe”. Turaki ya kyabe baki, ya ce, “ni fa ba zan yi abin da zai jawo min raini ba Malam, idan ta kawo ni bango dauke ta zan yi mu bar garin, mu tafi inda ba mu da kowa, in yaso ta tsire ni ta huta”. Dariya Abdul’Ahad ya yi, ya ce, “Sanda za ka zama Romeo din ai ba gaya min za ka yi ba. Ina nan isowa jibi insha Allahu, da ni za a yi kilisa”. A yau ya san ya yi barci irin wanda tsawon shekaru takwas da doriya rabon sa da yin irin sa. Duk wani tension ya kau. Duk wani migraine ya tabbata daga yau babu shi; Kulsum cikin gidan sa, matsayin matar sa ta sunnah! Babu wani kwanciyar hankali da contentment din da ya fi wannan a gare shi. Da asubahi ya so ya je ya buga mata kofa, sai kuma ya yi tunanin ya kyale ta, a sanin da ya yi mata sallar asubah ba ta wuce ta ba tare da wani ya tashe ta ba. Domin lokacin ne ta ke aikin wankin kayan fitsarin ta. Ta dade da tashi kuwa kamar yadda ya yi hasashe, ta yi wanka, amma babu kayan da za ta canza. Tana cikin gyaran gado ta ga wata jakar bacco a gefe, da ta bude sai ta tarar da kayan sawa ne na Dr. Sakeenah, ta santa da kayan a jikin ta, ta gane ajiye mata ta yi don ta yi amfani da su kafin a tattaro kayan ta daga Abuja a kawo mata. Kaunar Sakeenah da ganin girman ta suka kara cika ranta. Ta zabi wata shudiyar super holland riga da zani da dankwalin su ta sanya, ta lullube jikin ta da mayafin kayan kamar mai shirin fita unguwa, lotion kawai ta shafa, ko hoda ta ki shafawa kada Turaki ya dauka kwalliya ta yi masa. Tunanin sa kawai ya janyo mata wani irin bacin rai. Daidai lokacin da ta ji ana buga kofar ta. Dole ta je ta bude don rana har ta soma fitowa. Wa za ta gani? Batulu! Wani irin rungume juna suka yi, Batulu na fadin, “Kulsumu na, ashe zan sake ganin ki?” Ta ce, “Batulu kudurar Allah ai ta fi gaban haka”. Tare suka wuce zuwa tangamemen falon wanda ya sha tsari da tsadaddun kaya kamar a Turai. Batulu ta ce, “In na ce wa Yaya Turaki ya kwantar da hankalin sa, idan Kulsumu matar sa ce babu makawa sai ya same ta, sai ya ga kamar na fada masa karya, yau Allah cikin hikimar sa ga Kulsumun mu ta dawo mana cikin yardar Ubangiji”. Nan suka fara labarin bayan rabo, Kulsum ta ce, ina yaran ta? Ta ce suna wajen Ummah. Suna zaune kamar sa hadiye juna don kauna da aminci, kowacce na labarta wa ‘yar uwarta yadda rayuwa ta kasance mata bayan rabuwar su, Batulu na ba ta labarin irin bilinbituwar da suka sha ita da Turaki wajen neman komen auren ta. A cikin ran ta ta yi mamaki sosai, mamaki ba dan kadan ba, in ta ce mamaki tana nufin mamaki, sai dai wannan bai ishe ta ta yarda yanzu Turaki na matukar son ta ba ne, yana dai da hujjar sa, watakila don ya samu cikar wani burin nasa ne. Sai dai ba ta ce da Batulu komai ba, ganin yadda ta ke jaddada mata kaunar Yayan ta gare ta. To da ma ita soyayyar kan shiga farat daya ne bayan kiyayyah? Don dai ita a gabadaya sanin da ta yi wa Turaki kiyayya yake mata ba soyayya ba, don haka ba za ta yarda da wannan campaign din na Batulu ba, a dai yi sha’ani kawai wai kaza ta so tsegumi. Gyaran muryar Turaki ya sa Batulu ta nutsu, ya shigo dakin cikin shirin fita, kamshin sassanyan turaren sa one man show ya mamaye su. Ya dubi Batulu ya ce, “Ke kuma haka ake zuwa gidan mutane da sassafe? Mutanen ma amare sabon aure?” Dariya ta yi, ta ce, “wadannan ai tsofaffin amare ne. Yaya Turaki na kasa hakurin yamma ta yi ban ga Kulsumu ba. Ka san tun tafiyar ta ba mu sake haduwa ba”. “I can relate”. In ji Turaki. Ya maida duban sa ga Kulsum, “Ummukulsum zan fita, ko kina da sako wajen su Baffa?” Dauke kanta ta yi gefe ba ta amsa ba. Sai da Turaki ya yi da na sanin kula ta, ga shi ta dizga shi a gaban kanwar sa da ke matukar ganin girman sa. Yana fita Batulu ta ce, “Wai fushi ki ke da Yaya Turaki Kulsumu? Ki yi wa Allah ki yi wa Yaya Turaki adalci mana, ya sha wahala a kan ki, ya sha matukar wuya kafin ya same ki. Ya yi nadama!”. Murmushi kawai ta yi, ai Yayan ta ne da ta ke so, uwar su daya uban su daya, ba abin da ba za ta ce ba don kafa gwamnatin sa. Ita kuma ta sha wahalar soyayya idan shi wahalar neman ta ya sha, shekara da shekaru tana dawainiya da soyayyar sa, wadda ba ta ga ranar da ta yi mata ba. Batulu ta bar zancen don ta san ba hurumin ta ba ne. Ta ce su je su zagaya ta ga gidan nata sosai. Ba inda ba su shiga ba, har ran ta ta yaba da gidan, sai dai farin cikin ta ragagge ne duk da kasancewar ta mallakin sa, tunda da Turaki za ta yi rayuwa a cikin sa, wanda ba shi da gurbi ko kankani a zuciyar ta yanzu. Ko son ganin sa ba ta yi. Umma ta aiko musu da abincin karin kumallo a manyan warmers, suka zauna suka ci ita da Batulu. A lokacin ne baki suka soma zuwa ‘yan ganin daki da ‘yan ganin kwaf! ‘Yan uwan Turaki da ‘ya’yan zuri’ar su duk sun zo. Wadanda ta saba da su a baya, da wadanda sai yanzu ta san su. Har dare suna hidimar baki ita da Batulu, sai da aka zo daukan Yayar su Magajiya ‘yar wajen Hajiya Saratu, sannan Batulu ta bi su suka tafi da alkawarin gobe kafin ta koma Kaduna za ta biyo su yi sallama, ta kawo mata Nurain da Zunnurain ‘ya’yanta ta gan su. *** *** *** Turaki bai shigo gidan ba sai karfe tara na dare. A matukar gajiye yake, a kan dining ya samu abinci cikin warmers, ya debi wanda zai iya ci, ya koma kujerar tsakiyar falo ya yi zaman sa, ya kunna talabijin ya kamo tashar da yake so, wato CNN, ya koma cikin kujera yana cin abinci yana sauraron labarai. Bai damu da ya je inda ta ke ba, amma zuciyar sa da idanun sa so suke su gan ta, ko da kuwa rikici za su yi, ba zai iya kwana bai san halin da ta ke ciki ba. Mikewa ya yi zuwa dakin nata. Ya murda kofar ya ji ta a rufe. A hankali ya ce, “Ummukulsum, bude min kofa”. Banza ta yi da shi ta ci gaba da shimfidar gadon da ta ke yi. A ran ta ta ce, “Yadda ka aure ni ba da sani da amincewa ta ba, haka za ka gaji da ni ka maida ni inda ka dauko ni". Ya sake tausasa murya, “Kulsum kada ki yi abin da zai fusata ni, idan na shigo dakin nan...…”. Sauri ta yi ta je ta maida mukullin jikin kofar, yadda ko ya zira nasa ba zai budu ba, wato ya doke ta sannan ya hana ta kuka saboda zalunci? A lokacin da ta ke neman jin kan sa, kulawar sa da soyayyar sa bata samu ba sai yanzu da ta daina bukata? Hakan kuwa ya yi, domin dakin sa ya koma ya dauko bunch of keys na gidan gabadaya, ya zo ya yi ta gwadawa, amma ya ki shiga. Nan ya gane makullin ta bari a jiki. Ya yi kwafa. Ya ce. “Ni da gidana a ke rufe min kofa? Ki yi kina sani, ranar da zan rama tana nan zuwa”. Kulsum ta yi murmushi ta san ta shaka masa. A zuciyar ta ta ce, "da na ce gidana ne? Dadin abin ba daga bola ka tsinto ni ba”. Turaki kwana ya yi da wannan bacin ran, washegari ba ta fito ba sai da Batulu ta zo yi mata sallama tare da yaran ta. Suka yi sallama cike da begen juna. Kuma a ranar ne Malam Yusha’u ya kawo mata dukkan kayan ta na sawa da na amfani, da takardun makaranta daga Abuja. A daren ranar Turaki bai neme ta ba, ya sa a ran sa ya fita sabgar ta, don shi duk wata hanya da za ta kawo raini tsakanin sa da kowa bai son ta. Balle iyalin sa. Duk da hudubar da Abdul’Ahad ke ta yi masa na cewar, kwantar da kai zai yi, girman kai ba nasa ba ne a halin yanzu, ya aje sarautar sa da mulkin sa a gefe ya lallashi Kulsum, laifi har ba iyaka ya san ya yi mata, amma ya san shi ba zai iya ba, yana tattalin girman sa sosai. A tunanin sa in har zai samu su kebe cikin nutsuwa ya san ta duk hanyar da zai bi ya wanke laifin sa a aikace, amma ba ta irin hanyar da Abdul’Ahad ke so ba. Shi Ba-sarake ne, wanda ya gaji sarauta gaba-da-baya ba haye ya yi ba. Kulsum ta je ta yi ta yi, ranar da ta gaji za ta bari ne. Domin wannan karon auren su na har gaban abada ne, don haka tun ranar bai kara zuwa ya buga mata kofa ba, ita kuma ba ta fasa shigewa tun yamma ta kulle kan ta ba. Da ma ita in ta ci abinci karfe shida na yamma shi ke nan kuma ba ta kara ci sai breakfast din washegari. A haka suka zauna ba mai shiga harkar dan uwan sa har tsayin kwana biyar, ya kama washegari ne hawan angoncin da Turaki ya shirya da abokan sa da ‘yan uwansa maza. Kuma a ranar ne Abdul’Ahad ya iso, abin mamaki tare da Sajeedah. Bai gaya masa ba don ta ce surprise ta ke son yi musu. Ba za ta iya hakuri ta zauna ba ta zo ta ga Kulsum din Dr. Abubakar ba. Ta zama kawar ta ta farko daga bangaren matan abokan su. Turaki da kansa ya raka su wajen Umma da wajen Maimartaba suka kwashi gaisuwa, Umma ta dade tana jin labarin Abdul’Ahad a wajen Turaki. Ba karamar tarba tasa aka yi musu ba, aka kai su guest house din Maimartaba, amma sai Sajeedah ta ce ita Allahnbur wajen Kulsum za ta sauka. Abdul’Ahad ya harare ta, ya ce, “kin taba jin inda aka yi masauki a dakin amaryar da ko sati ba ta rufa ba?” Ta ce, “Dear, ni ba zan hana su amarci ba, akwai sakonnin da zan bata ne. And I want to be her first friend from Reading”. Turaki ya ce da Abdul’Ahad ya kyale ta, in sun yi wanka sun huta zai zo ya dauke ta zuwa wajen Kulsum din, amma a can karkashin zuciyar sa cike yake da zullumi da taraddadin tarbar da za ta samu daga Kulsum din, shi kansa a me yake gare ta balle wani nasa? Gabadaya ta canza daga Kulsum din da ya santa, saliha mai sanyin hali, ta rikide zuwa wata halittar daban. Kamar ba ta san girman hakkin aure a kan ta ba. Laifi ya san ya yi mata, amma ta ba shi da ma mana ya wanke kansa?, Ya ba ta hakuri kamar yadda Abdul’Ahad ya ce, su fahimci juna su manta baya? Babu dan Adam din da ba ya kuskure a rayuwar sa. Sai dai shi zaman nan da yake tare da Kulsum cikin gidan sa, duk da babu wata alaka mai dadi a tsakanin su, ya fiye masa gabadaya lokutan rayuwar sa a Reading dadi, sanin cewa ita din mallakin sa ce, kuma tana cikin dakin auren sa, shi ne babban kwanciyar hankalin sa. Bai aure ta don biyan bukatar gangar jiki ba, sai don ita din bakidayan ta yake so. Fatan sa Allah ya nuna masa ranar da zai sake mallakar Kulsum a shimfidar sa, ya wanke gabadaya laifukan sa na baya ta hanyar da shi kadai ya san ta, ta hanyar da shi kansa ya san unexpressable ce. Shi ne kuma kadai maganin taurin kan Kulsum. Da wannan tunanin ya iso gida, ya adana motar a inda ya saba adana ta. Cikin rashin karsashi ya nufi dakin Kulsum. Cikin sa’a ba ta kai ga rufewa ba kamar yadda ta saba, don a lokacin ta ke sallar la’asar ma. Yana shiga ya rufe dakin da makullin da ke jiki ya zare shi, ya rufe toilet shi ma ya zare. Ya hada su duka ya zuba a aljihun rigar sa. Kulsum na sallah tana jin duk abin da yake yi. Gaban ta ya yi mummunar faduwa da ba ta san dalili ba. Turaki ya kishingida a gefen gadon ta yana kallonta with lingering emotion a zuciya da idanun sa. Rabon da ya sanya ta a idanun sa yau kwana hudu ke nan. Haka kawai ta hana musu morar amarcin su da kuruciyar su, sabida wani fushin ta wanda bai karewa. Kin sallamewa ta yi, in ta sallame sai ta tada wata, bayan kuma ya san bayan la’asar ne ba lokacin nafila ba ne. Wato dai wadannan sallolin don shi aka kirkire su, ba don Allah ba. Murmushi ya yi ya mike ya saki labulayen dakin gabadaya, ya kashe kwan lantar ki ya kunna A.C. Dakin ya bada wani irin dim, sanyi mai dadi ya fara ratsawa a jikkunan su. Rigar voile din da ke jikin sa ya cire ya saura daga shi sai singileti da wandon jikin sa, ya yi kwanciyar sa a gadon Kulsum, yana fadin, “Yau daga ni sai ke, sai Ubangijin da ya sanya min soyayyar ki. Ki kashe ni ki huta Kulsum, ya fiye min wannan silent killer punishment din naki”. Ya dau filo ya rungume, ya yi kwanciyar sa. Kulsum ta rasa inda za ta sa kanta, ta yi sallolin har kafafun ta sun gaza daukar ta, sallolin da ta tabbatar babu lada a cikin su. Ba ta yi aune ba ta dan zauna tana hutawa, sai jin ta ta yi a hannun Abubakar-Turaki. Gabadayan ta ya sure ta ya haye gadon da ita, ya ja duvet mai laushi ya lullube su, bayan ya rungume ta tsam-tsam a cikin kowacce kusurwa ta jikin sa yadda bazata iya kwacewa ba. Kafin ya soma kissing din ta wholeheartedly ma'ana da dukkan zuciyar sa. Ya ja tunga da lips dinsa cikin nata, amma duk da ta soma ficewa a hayyacin ta a dalilin deep kisses din Turaki, ba ta fasa kokarin kwatar kanta ba. Ba abin da ta tuno a lokacin sai ranar su ta farko, ranar da Turaki bai taba tausayin ta ba… ranar da ya tabbatar mata ba ya son ta, ya tara da ita ne a bisa tilas. Nan da nan ta fara protest, wasu hawaye masu zafi na bin gefen fuskar ta. Turaki ya ji dumin su a kan fuskar sa, ya sassauta daga tsattsauran rikon da ya yi mata, ya sake kissing din tausasan labbanta softly. Wadanda a lokacin suka koma kalar light pink. A hankali ya kira sunan ta, ba ta amsa ba sai hawayen ta da suke kara gudu, sassanyan kamshin jikin sa na sanya ta cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa, ta daina kokawar da ta ke yi da shi duk jikin ta ya saki. Abin da yake so ke nan, ta nutsu ta saurare shi. Ya ce, “Ummu Kulsum ko mene ne a tsakanin mu, komai girman laifi na, ina rokon ki darajar iyayen ki ba don ni ba, ki jingine shi a gefe zuwa kwanaki uku, ki karbi bakuncin babban amini na da matar sa, wadanda suka taso takanas tun daga U.K, saboda su taya mu murnar aure”. Kulsum ta kwace jikinta daga nasa, ta juya masa baya. Har wata murna za a taya a wannan auren na rashin adalci? Turaki ya kwantar da kai a bayan ta, ya shiga magiya da rokon ta yayin da hannayensa ke shafa kwantaccen gashin kanta, abin da bai taba tunanin zai iya ba a rayuwar sa. Amma Abdul’Ahad na da babban matsayi a wurin sa, duk da ya san komai ba ya so ya tozarta a idanun Sajeedah kamar yadda ya tozarta a gaban Batulu, domin ya lura da gaske ta ke son Kulsumun, dole ya nemi hadin kanta kafin ya kawo ta. Kulsumu sai ta sa masa kuka, ta ce, “Ni ina ruwana da abokin ka balle matar sa? Ce musu ka yi auren soyayya ka yi da zan nuna musu ina son auren ka? Ai gara ma ka fada musu gaskiya cewa, yaudara ta ka yi ka dawo da ni gidan ka”. Ajiyar zuciya ya yi, ya ce, “Duk na amince, atleast forget everything sai sun tafi, sai ki ci gaba da gasa ni yadda ki ke so, in ci arzikin su. Ko a lahira wani kan ci albarkacin wani. Kada ki manta bakon ka Annabin ka”. Ba ta ce komai ba, amma reaction din ta ya nuna sassauci, ya mike daga gadon ya kunna fitila jin ana ta kiraye-kirayen sallar magriba. Ta ja quilt din ta rufe har kanta. Ya yi kwafa, ya ce, “Lokacin ki ne, ki ci gaba da wulakanta ni son ran ki, ni na jawo da na saka miki ido har zuwa yau. Da na bambanta miki da da yanzu, da ba ki raina ni har haka ba”. Kyabe baki ta yi a cikin quilt din, kamar yana ganin ta. Ya ce, “Zan dauko su idan na yi sallah, Umma za ta aiko da duk abin da za su ci. Don Allah Kulsum ki taimake ni, irin dan murmushin nan na mata da miji da caring din da mace ke nuna wa mijin ta. Ni kuma na yi alkawarin in sun tafi duk abin da ki ke so zan yi miki”. Da sauri ta ce, “Ba abin da nake so illa ka daina shigo min daki. Ba za ka taba samun yadda ka ke so a tare da ni ba. Me ya hana lokacin da ni ma nake bukatar kulawar ka a baya ka kula da ni ka tausaya mun? Ka kaunace ni? Amma sai ka tsallake ka bar ni? Sai yanzu don na zama mutum? Wallahi ba zan taba mantawa da ko wane ne Turaki ba. The vicious… the selfish… the rapist…”. (Mugu, mai son kai, mai fyade). Runtse idanun sa ya yi, ya ce, “Ummu Kulsum, ki san abin da ki ke fada min, I’m your husband no matter what, ki tuna mala’iku suna tare da ke. Ashe da ma akwai rape a cikin aure? Idan na ce miki nima a lokacin ban san yaya ake auratayyar bafa? Abin da zan ce shi ne, ki yi hakuri ki hadiye komai just for three days, ......please". Ya fada cikin roko. Shiru ta yi tana kara boye kanta cikin quilt, ba ta son kallon wadannan idanun na Turaki, wadanda ke zuwa mata kullum cikin mafarki, ko a ido biyu. Yau ga Turaki ta samu, amma zuciyar ta ta kasa karbar sa. “In je in taho da su Kulsum kin amince? Please Kulsum just for three days…”. Ta gaji da magiyar sa, kamar ba Turaki ba, wannan Prince din mai ji da kan sa, ciki-ciki ta ce, “na amince”. Sosai fuskarsa ta washe ba tare da sanin sa ba, ya yi murmushin nan nasa na gefen baki. “Inyaso in sun tafi sai a cigaba da gasa ni, ko a yi gunduwa-gunduwa da ni, Allah Sarki ni Abubakar”. Ya fice yana cewa, “Ki tashi ki shirya yanzu za mu shigo”. Ko amsa ba ta ba shi ba, ya bude mata toilet da kofa da ya rufe ya fice har wata irin sassarfa yake don farin cikin ya fara samun kanta. Masaukin su Abdul’Ahad ya koma ya samu duk sun kimtsa, shi suke jira. Sajeedah ta dauko ‘yar trolly din da ta zuba kayanta suka tafi. Tun fitar sa Kulsum ta mike daga gadon, wanka ta sake yi, ta fito ta shirya sosai. Wata shadda Ghanilla ta saka mai babban dinki senegalese ruwan goro, ta sha aiki daga sama har kasa. Ta kawo mayafin da ya dace da kayan ta yafa. Tana fitowa falo ta tarar Umma ta aiko ‘yan aikin ta sun kawo abincin da bakin za su ci. Ta jera komai a dining ta kunna turaren oud a burner, gidan gabadaya ya dau sanyin kamshi. Tana kokarin kunna talabijin ta ji sallamar su. Turaki ne a gaba, Abdul’Ahad ya biyo bayan sa. Sai wata kyakkyawar mace son kowa, wadda kallo daya ta yi mata ta gane zubinta ba na matan Nigeria ba ne. Ta amsa sallamar su, tare da karasawa ta karbi jakar hannun Sajeedah. Murmushi suka yi wa juna ta yi musu jagora zuwa cikin falon, amma ta kasa hada ido da Turaki, balle ta yi masa abin da yake so, don ita ba ta iya pretending a komai ba. Yanzu-yanzu idanun ta zasu bada ita. Sai dai ta sa a ranta ba za ta yi abin da zai bata ran shi ba, don ta lura kwarai yake ji da bakin nan nasa. Sosai Sajeedah ta ke kallon Kulsum, ta yaba da nutsuwa da kamalar ta. Kyau kam akwai shi, amma ba na tada hankali ba. Irin dai na fulanin Gaya. Farat daya ta ji Kulsum ta shiga ran ta. Duk yadda Turaki ke son su hada ido ta ki yarda. Ta kai kayan Sajeedah har bedroom din ta, ta dawo ta zauna a kusa da ita, sannan ta yi musu tayin cin abinci. Gabadayan su suka hau tebir ta yi serving kowa, making sure ta fara serving Turaki first. Wannan abu ya yi masa dadi, har ya samu karfin gwiwar yi mata magana. “Sajeedah ta ce a wajen ki za ta sauka”. Ta yi fara’a sosai tana duban Sajeedah, “You are most welcome Aunty Sajeedah, na gode sosai da wannan karramawa”. Ta fada da harshen Turanci, kasancewar ta gane Sajeedah ba ta jin hausa. Sajeedah ta ce, “Da fatan ba zan takura wa amarya da ango ba. ina so mu saba ne, mu fahimci juna. Wannan ne karona na farko na zuwa kasar Nigeria. I’m Eritrean”. Dr. Abdul’Ahad ya ce, “To fadi ba a tambaye ki ba”. Kulsum ta yi ‘yar dariya, tana son mutane irin Sajeedah, haka suke open minded, sannan ba sa bakunta a duk inda suka samu kan su. Mazan suka koma tsakiyar falo suna hirar da ta shafe su. Ta ja Sajeedah suka yi dakin ta. Sajeedah ta ce, “Ni fa na sanki ba tun yau ba, labarin ki iri-iri babu wanda ban sani ba”. Mamaki ya kama Kulsum, ta ce, “ke kuwa a ina ki ka san labari na?” Duk cikin harshen turanci suke magana. Sajeedah ta ce, “Duk wanda ya san Dr. Abubakar farin sani ya san ki Kulsum, ki gode wa Allah ba karamin so mijin ki ke miki ba. Har ya yi rayuwar dalibtaka zuwa ta aiki a jami’ar Reading Dr. Abubakar ba shi da budurwa. You are his only love tun daga sanda ya rabu da ke har zuwa yau da ya kara samun ki. Na san za ki yi mamakin dalilin da ya sa na nace sai na sauka a wurin ki. To babban dalilin shi ne, don in labarta miki yadda Turaki ya kwashe shekara da shekaru a cikin soyayyar ki, da neman inda zai gan ki. Babban burin kowace diya mace shi ne ta auri mijin da ke son ta, fiye da son da ta ke yi masa. In haka ne kuwa ke kam Kulsum kin dace, sai in ce ki kara rike mijin ki da daraja, soyayya da kauna don ki kara nesanta zuciyar sa daga sauran mata". Idanun Kulsumu suka cicciko da kwallah, ta ce, “Sajeedah, Turaki ya yi min laifi da yawa, laifin da zuciya ta ta kasa yafe masa….”. Ta labarta mata komai, na rayuwar su ta farko, amma ban da zancen fitsarin kwancen ta. Da haduwar su a Lagos, da yadda ta gan shi a matsayin mijin ta na biyu. Ta share hawayen ta, ta ce, “In ke ce za ki yarda yanzun da gaske yake son ki? A lokacin da na so ya so ni, zuciya ta ta ke matukar son sa duk bai so ni ba, sai lokacin da na yi yaki da ita na fidda shi da komai nasa a rai na?” Sajeedah ta dafa kafadun ta biyu, ta ce, “Na fahimta Kulsum, shi da ma aure na hadin iyaye ai haka yake, soyayya ba ta zuwa farat daya, tana zuwa ne gradually along the way a cikin rayuwar aure. So ki bude zuciyar ki ki karbi soyayyar mijin ki a wannan karon, ku mori rayuwar ku tare. Ki manta da duk abin da ya faru a baya, tabbas Turaki bai kyauta ba, amma ki dauki hakan as a system of understanding one another ke da Turaki. Ki daina waiwayen abin da ya riga ya faru, just the present. Ubangijin da ya halicce mu ma yana mana afuwa a bisa kurakuran mu in mun yi nadama, mun yi alkawarin ba za mu sake aikata wannan laifin ba”. Kulsum ta turo baki cikin shagwaba irin tata ta ce, “Aunty Sajeedah, Turaki ba ya lallashi na, komai cikin gadara da sarautar sa yake yin shi…”. Dariya Sajeedah ta yi, ta ce, “Ke kuma so ki ke ya kwantar da kai ya lallashe ki ko?” Kulsum ta kai hannu ta rufe fuskar ta kunyar duniya ta lullube ta. Sajeedah ta yi dariya, ta ce, “To ai wannan aikin ki ne Kulsum, shi naturally haka yake ko magana wahala ta ke masa. Amma a matsayin ki na mace za ki iya shaping behaviour din sa zuwa duk irin yadda ki ke so ya koma. Don Allah ki manta da komai Kulsum, Turaki needs your love, ki rungume mijin ki, ya sha wahala a kan ki yadda ba kya zato, yanzu ne lokacin da ya dace ya samu hutu da farin ciki a rayuwar sa”. Kulsumu ba ta ce komai ba, amma tabbas maganganun Sajeedah sun yi tasiri sosai a gare ta, ta yadda za ta fara gina kyakkyawar mu’amala tsakanin ta da Turaki ne ba ta sani ba. Akwai kunya sosai ta sauko da wuri haka. Sajeedah ba ta kyale ta ba ta ci gaba da tausar zuciyar ta, da kalamai masu dadi da karfafa gwiwa, sannan ta ce, “na zo miki da abin da zai kara mallaka miki Turaki, sirrin mu ne na matan Eritrea”. Ta dauko jakar ta ta dinga fiddo mata su, ta kuma takura mata ta sha a gaban ta. Sai wajen goma na dare Abdul’Ahad ya koma masaukin sa bayan sun yi sallama shi da Sajeedah. Ta yi shirin bacci ta ga Kulsum na gyara daya barin ita ma za ta kwanta. Ta ce, “A’ah Kulsum ya ya haka? Duk abubuwan da na fada miki ba ki dauki ko daya ba ke nan? Ai sai Turaki ya gan ni Yayar banza, na zo na makale masa mata a daki. Maza dauki duk abin da za ki dauka ki tafi turakar mijin ki”. Kulsum ta rasa inda za ta sa kanta da wannan umarni na Aunty Sajeedah. Ta kai kan ta turakar Turaki? To ta ce masa me? Me ya kawo ta? Girgiza kai ta yi, za ta yi magana Sajeedah ta tare ta, “Kulsum, mazan da ki ka sani a da, ba daya suke da na yanzu ba. Dole ki mike ki nemo aljannar ki, ba ruwan Allah da fushin da ki ke da Turaki, auren Turaki da ke wuyan ki shi ne abin da Ubangiji zai yi la’akari da shi ranar gobe kiyama. Don haka ki sa a ranki kin yafe wa Turaki dukkan laifukan sa, kin yi damarar kyakkyawan zama da shi daga daren yau, ki roki Ubangiji ya ba ki karfin gwiwa don na lura kina da riko’. Murmushi ta yi, sai dai ga dukkan alamu maganganun Sajeedah sun shige ta. Hatta ruwan da za ta yi wanka Sajeedah ce ta hada mata, ta zuba turaren su na mutanen Eritrea a cikin ruwan wankan. Ko da ta fito ita ta zabar mata rigar barcin da za ta saka. Ta ce, “Na fasa kwana a gidan nan, masaukin mu zan koma, har na kira Turaki na fada masa, yanzun nan zai maida ni”. Ta dafa kafadun Kulsum da idanunta suka yi rau-rau. “Enjoy the blessings of your marriage my dear. Sai da safen mu”. A nan ta bar jakarta, sai handbag dinta kawai ta dauka. Bayan fitar ta Kulsum kasa bin shawarar ta ta yi, ta yi kwanciyar ta a dakin ta, a ranta tana fadin, “Mu Hausa/Fulani ne Sajeedah, ba kabilar mu daya ba, da kunya da kamun kai aka haife mu”. Tana jin dawowar Turaki daga maida Sajeedah wajen mijin ta, ya kashe fitilun falo da kayan wuta ya wuce dakin sa. Mikewa ta yi ta kashe wutar dakin. Ta yi addu’a ta kwanta. Rana ta farko da ba ta sanya key a kofar ba. Amma har barci ya dauke ta babu Turaki babu ko inuwar sa. Wai kuma sai ta ji duk ta damu, ko dai shawarar Sajeedah za ta bi ne? Yau ta yarda ba ta taba daina son Turaki ba, daidai da dakika daya, fushi da bacin ran abin da ya yi mata a zaman su na baya shi ne ya danne soyayyar. A yanzu sai bankado kanta ta ke tana bude sababbin rassa tana zuba sabuwar yabanya. Musamman da ta ji labarin nan daga bakin Sajeedah na yadda Turaki ya sha wahalar dawainiyar soyayyar ta. Sai dai duk kokarin ta na ta iya kai kanta turakar Turaki ta kasa. Haka ta kwana tana juyi a gado, ga ciwon mara sabida magungunan da Sajeedah ta dankara mata masu karfi ne. Amma ta daure komai don tsira da jan ajin ta. A dakin Turaki kuma yana bisa na’ura mai kwakwalwa ne yana yin wani research a kan wani aikin ido da zai yi wa Sarkin Gombe mai fama da lalurar glaucoma sati mai zuwa. Aikin da ya kai shi har karfe biyu na dare. Da ya gama ya yi shirin kwanciya bai leka Kulsum ba, ba ya son ya yi abin da zai tunzurata ta fasa kula masa da bakin sa. Saidai kwarai yake son ganin ta ko dan fadan ne su yi kafin ya kwanta. Amma ya taushi zuciyar sa ya kyale ta, sai dai fa tun dazu da ya yi kissing Kulsum komai ya kwance masa, cikin karfin hali yake komai, amma al’amarin ya tado masa da tunanin can baya. Watarana guda daya da ba zai taba mantawa ba tsakanin sa da Kulsum, ranar da ta canza rayuwar sa da zuciyar sa akan ta, ranar da Kulsum ta shige sukuf cikin ransa. Washegari ba su hadu ba sai wajen karfe goma na safe, ita ta fito tana kara kintsa falon kamin isowar bakin su, shi kuma ya fito cikin shirin fita. Yadin filtex ne ruwan makuba mai shara-shara a jikinsa. Ta lura Turaki na son yadikan filtex marassa nauyi, masu taushi haka. Ba ta juyo daga abin da ta ke yi ba, wato karkade center table da duster duk da babu wata kura a jikin sa. Turaki ya iso gare ta, ta bayanta ya rungume ta ya sanya kansa a masangalin wuyan ta yana sunsunar ta, wani irin qamshi ya ji da ya gigita shi (turaren Sajeedah). Ya juyo da ita bakidayanta suka fuskanci juna, da azama ya kara rungume ta ya soma kissing idanun ta, hancin ta da bakinta very softly. Ta yi kokarin janyewa, amma bai ba ta damar hakan ba. Bugun da ake yi wa kofar shigowa ya sa dole ya janye daga gare ta ya je ya bude kofar. Abincin karin kumallon su ne da na bakin su Umma ta aiko a kawo. Hanya ya bai wa matan suka wuce zuwa ciki, shi kuma ya koma inda ya baro Kulsum, ta gagara ci gaba da aikin da ta ke yi ta zauna a cikin kujera tana regaining consciousness din ta. Ya ce, “Good morning Ma'am, za mu je gaida Baffa ni da Abdul’Ahad, ko kina da sako wajen Goggo? Sajeedah za'a rako ta yanzu, ba za ku gan mu ba sai dare, don yau ne za mu yi kilisa”. Ciki-ciki ta amsa, “Ba ni da sako, a gaida Goggo da Baffa". Amma har cikin ranta ta ji dadi, tana son mijin auren ta ya zamo mai yawan gaida iyayen ta, ko da ba zai ba su komai ba. Laraba ce ta rako Sajeedah tare da faggon kayan ta tare da wata yarinya budurwa, in kun tuna Laraba tsohuwar mai aikin Kulsum, Umma ta cika alkawari da ma ta ce sai bayan sati daya za ta turo wa Kulsum masu aiki, don daga yau an daina aiko musu da abinci daga can gida. Kulsum ta rungume Sajeedah tana mata barka da zuwa. Da kyar ta gane Laraba sabida ta kara tsufa. Zo ki ga murna wajen Kulsum ta rungume tsohuwar wadda ta ke hawayen farin cikin dawowar Kulsum. Sun yi zama na kauna da amana. Laraba ta gaya mata yarinyar jikar ta ce, sunanta Ladidi, su za su dinga yi mata duk wasu aikace-aikace, in tana da aike wajen Umma ta aika Ladidi. Kulsum ta raka su dakin da za su zauna, sannan ita da Sajeedah suka wuce nata. Wuni guda Sajeedah tana kara wayarwa da Kulsum kai a kan yadda za ta zauna da Turaki ta mallake zuciyar sa ita kadai, don ta fahimci Kulsum din har yau tana da raunin wayewar kai. Tare suka yi girkin rana da na dare suka adana na su Turaki wadanda ke can suna hawan angonci. Ba su shigo gidan ba sai bayan isha, Sajeedah ta dubi mijin ta cikin kayan sarauta abin ya yi matukar burge ta, Kulsum kuwa makalewa ta yi daga bayan labule tana leken Turaki cikin Royal Attire din sa, kayan da ba ta taba ganin shi da su ba. Ya yi mata kyau da kwarjini har yadda ba za ta iya kwatantawa ba. Ya fidda tuntumemen rawanin kansa ya dubi Sajeedah da ta rungume Abdul’Ahad a gaban sa, ya ce, “Ina Ummu Kulsum?” Sajeedah ta hau waige-waige, don dai ita dai ta san tare suke a falon, ba ta san yaushe ta shige ba. “Ai kuwa muna tare, ban san ina ta yi ba”. Turaki ne ya ga motsi a bayan labule, ya tafi kansa tsaye ya janyo ta suka shige daki. “Sai kin gaya min dalilin leke na, na yi kama da wannan raggon saurayin naki dan Abuja ne?” Kulsum ta yi kicin-kicin da fuska, ita a dole ba shi ta ke leke ba, hadi da zumburo baki. Bakin da ta zumburo ya sa yatsansa ibham ya dalle shi da karfi. Ta kai hannu ta dafe bakin ta hawaye suka ciko idon ta don zafi. Sai kuma ta ba shi tausayi, ya tarairayo ta ya rungume yana shafa bayanta a hankali cikin lallashi. “Kulsum ko wane irin laifi na yi miki ya kamata a ce zuwa yanzu kin hakura kin yafe min, tunda na kawo kaina a matsayin mai neman afuwa. No one is above mistake, Kulsum don Allah ki yafe mini mu shimfida rayuwar mu haka. Ko me ki ke so zan miki in dai za ki daina fushin nan da ni. Amma don Allah kada ki ce za ki sake bari na a karo na biyu…”. Saura kalaman suka makale a makoshin sa sakamakon jin hannayen Kulsum sun zagayo ta bayan sa sun rungume shi. Wani abu da bai taba zata ba a wannan lokacin, don haka fadin halin da Turaki ya samu kansa unimaginable ne. It was kind of gentle romance da biro na ba zai iya rubutawa ba. Yayin da Kulsum duk da ba ta cikin hayyacin ta sabida yadda Turaki ke gigitata da nau'ikan soyayyar sa ba ta manta da bakin su da ke falo ba. A hankali ta zame da kyar ta tura Turaki baya, ya fada bisa gado da baya da baya, dariya ta bashi ganin yadda duk ta sukurkuce, just daga kissing, ficewa ta yi tana cewa, “Kai da Abdul’Ahad babu ruwana”. Sanda ta fito Abdul’Ahad din da Sajeedah suna bisa dining suna cin abinci. Sajeedah ta jefo mata kallon ko ke fa? Kulsum ta yi murmushi, ta ja kujerar kusa da Turaki ta zauna, shi ta fara serving sanan ta zuba wa kanta. Shi da Abdul’Ahad suke maganganun da suka shafe su. A ranar suka yi sallama da su don gobe za su wuce Abuja su kwana, su bi British Airzuwa U.K. Sosai Kulsum ta ke kewar Sajeedah, tunda Turaki ya fita tare da su bai dawo ba sai sha dayan dare. Kulsum ta yi wanka ta fito tana shafa mai a kan stool gaban madubin ta, Turaki ya murda kofar dakin ya shigo sanye da fararen Pajamas. Tunda Kulsum ta kalle shi sau daya ta dukar da kai, ba ta kara iya hada ido da shi ba. Turaki ya kara kunna fitila mai haske a dakin yana ta kallon Kulsum sosai, ganin komai yake tamkar a mafarki. Tamkar idan ya rufe ido kafin ya bude za ta sake kufce masa. Rayuwa ta koya masa darussa sosai. Ya kara fahimtar ka rike abin da ka ke da shi da daraja, ranar da ya kubuce daga hannun ka za ka sha wuya kafin ka same shi, idan ma ka yi sa'a ka same shin ke nan! Sannan ya fahimci soyayya ta gaskiya ba ta faruwa a lokaci daya… ita wata irin aba ce da ba ruwan ta da lokaci, ko lafiya da dangogin su. Abu ce wadda ke faruwa a duk sanda ta so, ta gudanar da Tunani ta sarrafa gangar jiki (ALHERI-TAKORI). In haka ne, ke nan shi a ra’ayinsa bai yarda da abin da bature ya kira love at first sight ba, wannan infatuation ne. Ya karaso a hankali gaban Kulsum wadda ko shafa man da ta ke yi ta kasa ci gaba sakamakon idanun nan na Turaki masu kama da magnetism da hasken fitila da ya wadaci dakin. Gaban ta ya iso tamkar mai counting steps dinsa (kirga takun sawun sa). A hankali ya tsugunna a gaban ta ya dora hannun damansa a kan tafin kafar ta, ya jima tsugunne kanshi bisa cinyoyin ta, kafin ya dauke ta gaba daya su fice dakin zuwa turakar sa. Komai ya faru ne ba yadda ta zata ba, komai ya faru ne cikin kauna da soyayyah. Gently, softly, romantically, emotionally. Dare ne da al’amuran da suka faru cikin sa suka shige cikin kundin tarihin rayuwar Ummu Kulsumu. Ta amince da soyayyar mijin ta Turaki, ta yarda shi din ba wanda ta sani a baya ba ne, wani sabon Turaki ne wannan. Loving and romantic. Sannan fassarori da yawa da ta yi masa abin ba haka yake ba, shi dai bai shirya aure ba a wancan lokacin aka aura masa ita, amma ba kinta yake ba. Bai taba kinta ba. Ta amshi soyayyar sa da hannu bibbiyu, ta maida martani iyakar iyawar ta, suka dunkule suka zama abu daya a wannan dare mai dumbin tarihi a cikin rayuwar su. Ba su suka samu suka runtsa ba sai misalin karfe uku na sulusin dare. Goshin asubahi, a lokacin masallatai sun fara kiran sallah, Prince Turaki, ya muskuta manne da Kulsum a jikin sa, amma sai ya ji wani sururun sanyi na shigar sa ta kasan sa. Ya sake gyara kwanciya har zuwa yanzu bai raba Kulsum da barin jikin sa ba don kada ya tashe ta daga barcin hutun da ta samu. Jin sa ya yi male-male a cikin damshi, tun daga samansa har kasan sa a jike yake yarab! Daga shi har Kulsumun. Cikin tsananin tu’ajjibi da mamaki har ma da tsoro ya raba Kulsum da jikin sa ya mike zaune. Wannan ruwa daga ina haka? Motsin sa ne ya tada Kulsum, juyawar ta da zaman ta suka ankarar da ita abin da ke faruwa. “Ta yi fitsarin kwance!” “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Kulsum ta ambata cikin tsananin tashin hankali. Kafin ta sunkuya ta fashe da kuka, gigitaccen kuka mai nuna zurfin tashin hankalin da ta samu kan ta. Ta dauka ya tafi, ta dauka sun yi sallama, ashe jira yake ta yi aure ya dawo ya sake raba ta da farin ciki a rayuwar ta??? Shi dai Turaki har zuwa lokacin ya kasa gane komai. Kukan ta ne ya kidima shi, ya kamata, ta yi sauri ta janye jiki a hankali daga gare shi, ta koma can karshen gado ta ci gaba da kukan ta. Ta san rabuwarta da Turaki ta zo, a lokacin da ta gama samun duk wani contentment na rayuwa. Babu wani namijin da zai jure rayuwar aure da mai lalurar fitsarin kwance, balle babban likita mai matsayin consultant, kuma dan Sarki kwaya daya tal irin TURAKI. Kukan ta ya tsananta, ya kara gigita Turaki, gabadaya ya rasa gane me ke faruwa? Sai a lokacin kwakwalwar sa ta ankarar da shi. Shekarun baya ya tuna da hirar da ya ji tsakanin ta da Laraba, ashe ba ta warke ba din har zuwa yanzu, har tsayin zaman ta a hannun marikan ta? Fuskar sa expressionless (bata nuna komai ba) ya bar dakin jagab da pajamas din shi sai yarari yake. A toilet din dakin sa ya cire kayan, ya sakar wa kanshi shower. Ruwan na sauka a jikin sa yana tunanin ta yadda zai taimaki matar sa Kulsum. Tausayin ta ya bi ko’ina na jikin sa, ko kadan bai ji kyama ba, sai ma wata sabuwar soyayya da ta kara manne masa a zuci da ruhi, wadda tausayi ke assassawa. Yana iya hasaso how embarrasing ta ke jin kanta, shi ya sa ta ke wannan kukan tamkar na fitar rai. Ya sa a ran sa da taimakon Allah sai ya zama silar da Kulsum za ta samu lafiya, idan kuma wannan ita ce kaddarar ta, wato dauwama cikin lalurar fitsarin kwance, zai ci gaba da zama da ita cikin so da kauna, hakan ba zai raunata komai na daga soyayyar da yake yi mata ba. Zai saya musuwater mattress, washing machine da zannuwan gado masu yawa, zai taimaka mata ta dinga tsaftace kanta, a duk lokacin da lalurar ta same ta. Kulsum bayan ta ci kukan ta ta koshi, ta yi tunanin kiran Dr. Sakeenah don ta sanar da ita, ita ma ta san da laifin ta, likita bai ce ta daina shan magungunan ta ba ta daina, tunda ta ga cewa ta samu lafiya. Ba za ta iya tuna lokaci na karshe da ta sha maganin ba, sai dai kuma ta baro wayar ta ne a Lagos tun gigicewar ganin Turaki. Ta je ta yi wanka, hawaye na bulbula, fitowar ta ke da wuya ta sa mukulli ta kulle kanta, ba za ta iya kara hada ido da Turaki ba. What an embarassment (wannan abun kunya har ina). Sai daga baya ta yi tunanin to wa zai gyara masa gadon idan ba ta je ba? Gara dai ta boye kanta ta ji da gundumemiyar kunyar ta da tozartar ta. (Wannan ne halin da mata masu lalurar Enuresis ke fuskanta tsakanin su da mazajen su, ga wasu mazajen wannan shi ne dalilin wulakanci a gare su. Ya jama’a mu sani cewa, babu wanda yake sama da lalura duk matsayin sa duk ilmin sa, masu lalura soyayya da tausayi suke bukata, musamman daga mazajen su, domin kaddara ba ta wuce kan kowa ba. Allah ka kara mana lafiya da zama lafiya, amin- Takori). Turaki da kansa ya yaye zanin gadon, ya je ya sa shi a famfo ya zuba Ariel da hypo ya wanke. Ya rasa yadda zai yi da katifar dakin sa, sai ya kada omo a bokiti ya zo ya sa tawul ya dinga gogewa. Da ya tabbatar ya fita, sai ya daga ta ya shimfide a tsakar dakin ya sakar mata fanka da A.C. A gurguje ya shirya don Maimartaba yana jiran sa, ya fito zuwa dakin Kulsum. Murdawa ya yi ya ji ta rufe da mukulli, ya kira sunan ta a tausashe, “Ummu Kulsum bude min kofa”. Yana jiyo shesshekar kukan ta da ke tashi a hankali. Zuciyar sa ta kara raunana, ya ce, “Kulsum… please…..”. Cikin kuka ta ce, “I cannot face you…”. Murmushi ya yi ya ce, “Na ji to, zan rufe idona yadda ba zan gan ki ba”. Ta ce, “Ka yi alkawari?” Ya ce, “It’s a promise…”. Ta zo ta bude kofar tana rakubewa a bayan kofar. Ya janyo ta ya hada da jikin sa, “Duk wannan kukan na fitsarin ne? Idan ya sanya miki zazzabi fa? Haka kawai ina cikin amarci na a cuce ni?” Duk halin da ta ke ciki sai da ta yi murmushi, murya abin tausayi ta ce, “Wane amarci ga mai fitsarin kwance?” Ya kara matse ta a jikin sa sosai, sassanyan kamshin jikin sa na ratsa ta, yana haifar mata da wata irin nutsuwa da kwanciyar hankalin da ta rasa. Ya ce, “Kulsum ki sa a ranki, ba fitsarin kwance ba, ko yoyon fitsari ki ke yi, I’m at the extent of loving you, intending to stay with you, and vowing to help you… we will fight this problem together (ina kan kololuwar sonki, dauke da aniyar ci gaba da zama da ke, da kuma alkawarin taimaka miki. Za mu yaki wannan matsalar tare) insha Allahu. Just relax and pray. Yanzu zan je in ga Maimartaba akwai inda za mu je sai dare zan dawo. Me ki ke so in taho miki da shi?" Hawayen farin ciki suka zubo daga idanun Ummu Kulsum. Ba ta taba tsammanin martanin da za ta samu daga Turaki ke nan ba. Ta kara gamsuwa da cewa....this is not the previous Turaki… wannan wani sabon Turaki ne, mai dauke da kauna ta ban mamaki a gare ta. "Ba abin da nake so sai kai Prince dina”. Ta fada tana kwantar da kai a kirjin sa. Kaso tamanin cikin dari na tashin hankalin ta ya kau. Ya dan bubbugi bayan ta, ya ce, “In dai Turaki ne kin samu, I’m only yours. Zan kawo miki waya sabida su Goggo, amma ban yafe ba in ki ka yi magana da Taufeeq”. Ta lumshe ido tana murmushi, ta ce, “Ko ka yafe ba zan yi ba. Bana neman komai daga sauran maza, you are more than enough to me. Allah ya bar mu tare cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi”. Sosai Turaki yake kissing din kowacce halitta ta fuskar Kulsumu, ido, hanci, goshi, da baki sai da suka karbi rabon su na sassanyar passionate kiss daga Yarima Abubakar Turaki. Sannan da kyar ya janye ya gyara zaman hular sa ya fice da gudu- gudu sauri-sauri ganin sunan Maimartaba a kan fuskar wayar sa. Kulsum ta bi shi da lallausar murmushi. Ji ta ke kamar su dauwama cikin wannan yanayin da ba ta taba samun kanta a mai dadi da sanya nutsuwar sa ba. Ko da ya dawo a ranar kin zuwa dakin sa ta yi, har yanzu kunyar ba ta sake ta ba. Ta yi shirin kwanciya ke nan sai ga shi ya shigo, tun daga bakin kofa ya jefa mata harara. “Me ki ke nufi da ni ne matar nan? Ina ta jiran ki ki zo mu cike wasu takardu, kin barni ni kadai? Shirin kwanciya ma ki ke yi abun ki alhalin ga turakar mijin ki?” Kulsum ta langabar da kai abin tausayi, ta ce kasa-kasa. “Ina tsoron kada ya kara zuwa ne”. Ya sa hannu ya dago habar ta, murmushi ya sakar mata wanda ya ratsa har cikin ruhin ta. Sannan ya sumbaci bakin ta ya ce, “To sai me? Har na sayo mana injin wanki da katon din hypo da na omo (Ariel). In mun yi sai mu wanke. Watarana sai labari…..!”. Da karfi Kulsum ta kankame shi tana wani irin kuka. Gabadaya ya daga ta suka fice daga dakin. Cike takardu bai yiwu ba a wannan dare, domin ya kasance daren rahma ga ma’auratan, sun raya shi har yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba. Amma a karshe Kulsum ta ki yarda barci ya dauke ta, tana kallon Turaki yana barcin sa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali irin wanda miji ke samu idan ya samu kyakkyawar gamsuwa daga matar sa. Sai zarya ta ke daga gadon zuwa toilet tana kakalo fitsari. Ba ita ta kwanta ba sai da suka yi sallar asubahi, Turaki ya dube ta tana lazimi idanun ta sun yi luhu- luhu. Ya daure fuska sosai ya ce, “Look, hau gado ki kwanta sai karfe goma na yarda ki tashi daga barci. Wannan daura wa kai wahala har ina? Ina ce katifa dai tawa ce ko? Zanin gadon ma nawa ne ba naki ba?” Ta sunkuyar da kai tana murmushin maganar sa, soyayyarsa na karuwa a zuciyar ta. “Oya! Hau ki kwanta tun ban canza manufa ta ba”. Ta gane me yake nufi, don haka ta ja jiki zuwa gadon ta kwanta a dofane, ya jaquilt ya rufe ta da kansa. Tare da sunkuyawa ya sumbaci goshin ta. Ta yi barci kuwa sosai, domin kuwa shi ba'a cin bashin sa. Sai dai kuma ta tashi ne again cikin yanayin da ya fi na jiya. Turaki yana dining yana karyawa da abincin da Laraba ta tanadar musu. Sai da ya gama ya dawo dakin, ya shiga toilet ya yi wanka ya fito yana zaben kayan da zai sa ba tare da ya san halin da Kulsum ke ciki ba. Ta sanya kanta karkashin filo tana kuka, wanda da hawaye kawai ta ke yin sa babu sauti. Ba ta so yau ma ya yi aikin fitsari shi ya sa ta sa hannu ta toshe bakin ta. Sai da ya gama tsaf! Ya fesa turarensa one man show, sannan ya iso gabanta don ya duba ko ta tashi. Filon da ta danne kanta da shi ya dauke, “Kina so ki danne numfashin ki ne?” Gani ya yi wajen ya jike sharkab da hawaye. Nan ya gane halin da ta ke ciki. Fuskar sa ta nuna damuwa ya ce, “For God’s sake Kulsum, wannan kukan ne zai yi maganin lalurar? Duk abin da na gaya miki bai shiga kunnen ki ba. In dai a kaina ne ki ke shiga wannan halin ni kam kina zaluntata! Damuwar ki da fitar hawayen ki sune manyan damuwa ta ba fitsari ba. Idan ‘depression’ ya kama ki ba zan yafe miki ba”. Da kyar ta mike cikin tsananin jin kunya, ya taimaka mata ta hanyar kama hannun ta ta mike ta shige toilet. Ya yaye zanin gadon, amma wannan katifar in ba ta sha rana ba yau akwai matsala, domin ko an goge da omo sai ta yi warin damshi. Tana fitowa ta same shi ya balle links din hannun rigar shi ya kwance botir din wuyansa ya zage yana goge katifar. Kifa kai ta yi a jikin bango tana hawaye. Turaki ya yi kwafa ya ce, “Ki yi abin da ki ke ganin shi zai fishsshe ki”. Duk runtsi ba zai fidda katifar nan waje ba sabida ‘yan aikin su, balle Laraba da yake da masaniyar ta san Kulsum na da lalurar. Ya rasa yadda za su yi da katifar, ya dai sakar mata fanka ta sama da ta kasa. Ya canza kayan jikin sa ya je ya shigowa da Kulsum abin da za ta ci. Da kyar ya samu ta iya cusa dankali biyu a bakin ta. A ran ta ta yanke ba za ta kara kwana dakin Turaki ba duk abinda zai ce mata gara ta je ta yi ta kazantar ta ita kadai a dakin ta. “Tea din nan sai kin shanye shi, in har kina son zaman lafiya Kulsum". “Ka yi hakuri Prince, ba ni da appetite, wallahi na tsani kaina!”. Turaki ya tsura mata ido, kalaman rarrashi sun kare masa. A irin wannan stage din ne mata da yawa ke haduwa da depression wanda zai iya yin sanadin suicidal thought. Ya ajiye kofin shayin ya matsa gare ta ya rungume ta. Ta kwantar da kai a kan kirjinsa tana ta sharbar kuka. Ya ce, “Is o.k Kulsum, na san abin da ki ke ji. Amma don Allah ki kwantar da hankalin ki, wannan lalura ba kanki farau ba, mata da yawa suna fama da ita, wani lokacin ma har maza. Tun jiya na yi magana da kwararren nephrologist din da zai duba ki Dr. Ibraheem Mansur Takai (Rayuwar Rayhana). Za mu hadu da shi a U.K, zai zo asibitin da nake daga Illinoise (Chicago) kan wani aiki da za mu yi tare. So relax please, stop these waste of tears, ni ko ba ki warke ba ina sonki haka! Zan kuma ci gaba da zama da ke cikin kowanne hali, to the very end”. Kulsum ta shafe hawayen idanun ta, har yanzu kanta na bisa kirjin Turaki, ta ce, “Watarana za ka gaza… watarana za ka auro wata… in ta gane zan wulakanta… zan tozarta…”. Hannu ya sa ya toshe mata baki. “Ban yi miki alkawarin har abada ba zan kara aure ba, tunda Ba-sarake ne ni. Amma Kulsum ko aure ya kama ni sai na tabbata kin warke. Ba dai in yi aure saboda lalurar ki ba, don Allah ki kwantar da hankalin ki”. Kara shigewa jikin sa ta yi tana jin kanta tamkar a kan gajimare. Turaki ya gama yi mata komai a rayuwa, Allah ya sa ya tabbata a hakan. “Now, gaya min treatments din da ki ka taba karba a asibiti, in cike a wadannan takardun zan tura wa Dr. Ibraheem…”. Tiryan-tiryan ta soma gaya masa tun zuwanta Lagos gidan Aunty Sakeenah, treatments din da ta karba; pharmacological and non-pharmacological. Result din da treatments din suka bayar. Kwayoyin maganin da aka dora ta a kai, wato tricyclic antidepressants, tofranil (imipremine) da kuma (desmopressin acetate) da ta jima tana sha. Ta kuma daina sha ba tare da likita ya dakatar da ita ba, sai don a tsammanin ta ya tafi ke nan. Duka Turaki ya shigar da bayanan, sannan ya tura wa Dr. Ibrahim ta email din sa. Ba jimawa response din sa ya shigo, inda ya ce ya amince zai ga Kulsum a U.K sati uku masu zuwa. Turaki yake gaya mata da ma hutun da ya dauka na aure na wata daya ne, don haka za su koma a daidai lokacin da Dr. Takai ya diba musu. A nan ta ke ji ya zo Lagos ne ziyarar aiki ba'a can yake ba dindindin. Yana aiki ne da asibitin koyarwa na jami’ar Reading wato Royal Berkshire Hospital wanda reshe ne na NHS Foundation. A nan ne ta san abubuwa da yawa game da Turaki wadanda a baya ba ta sani ba. Har haduwar su a jami’ar Reading shi da Abdul’Ahad da irin abotar da ke tsakanin su, da rawar da ya taka wajen taimaka mishi ya same ta. Ya dube ta ya yi murmushi, “Shi ya sa na dame ki sosai kan ki karbi bakuncin su, they are your real supporters”. Yana kwance rigingine da laptop a kan kirjinsa yayin da kansa ke bisa cinyoyin ta suke hirar, a lokaci guda yana processing visa dinta ta shiga U.K as his spouse. In ka gan su sai sun ba ka sha’awa, yatsun ta cikin sumar kansa wai kitso ta ke mishi cikin tarin kwantacciyar sumar sa duk ta duddunkule mishi gashi, ko kofar gida yau bai fita ba, duk don kada ya fita Kulsum ta koma cikin damuwar ta. Da magriba ne ya je ya yi sallah ya dawo, ya ce ta shirya su je ta gaida Umma da sauran mutanen gida. Sosai ta yi shiga ta alfarma sai kamshi suke daga ita har shi. Tsakanin gidan su da masarautar Gaya ba tafiya ce mai yawa ba, a kafa ma za a iya zuwa. Amma mota suka hau, lokacin da suka isa Umma fada ta hau yi kan don me zai fiddo Kulsum ko wata guda ba ta rufa ba, in gaisuwa ce ai tana aiko mata kullum. Shi dai hakuri yake ba ta, bai gaya mata ba ya so ya fito ya baro Kulsum cikin damuwa ba ne. Umma ta tambaye ta, “In ce ko babu matsala Kulsum?” Kanta a kasa ta ce, “Babu Umma, muna godiya da dukkan dawainiyar ku. Allah ya kara girma, Allah ya kara yawan rai”. Umma ta ce, “Ko kina bukatar karin ma’aikata? An ce gidan naku da girma sosai”. Kulsum ta ce, “Umma har sun yi yawa, Baba Laraba akwai zafin nama kamar ba tsohuwa ba". Umma ta yi murmushi, ta ce, “Ga iya girki kuma. Sannan tana son ki sosai”. Kulsum ta ce, “Yaya labarin mutanen kaduna? Tun bayan biki babu labarin su”. “To ke din ce ai babu waya, Turaki ya ya batun wayar Kulsum ne?” Shi dai yana gefe kan shi a kan wayarsa ba sauraron su yake ba, sai da Umma ta kira sunan shi ya dago, ta sake maimaitawa, ya ce, “Ina sane, ban samu shiga Kano ba ne sai wajen jibi”. Duka dakin matan gidan sai da Kulsum ta je ta gaishe su, inda ta tarar Fulani wato kakar su Turaki tana kwance babu lafiya, likita ne ma a kanta ya daura mata ruwa. Tsohuwar tana jin jikin ta, amma albarka ta ke sa wa Kulsumu, tana rokon ta ta rike Turaki da amana, domin shi dan albarka ne, wanda duk gidan ba wanda ta ke so irin sa. Ba su koma gida ba sai wajen sha dayan dare. Kulsum ta sa a ranta sai dai Turaki ya yi fushi da ita, amma ba za ta sake kwana daki daya da shi ba, hakan cutarwa ne a gare shi, duk son da yake ikirarin yana yi mata in aka ci gaba da tafiya a haka tana sharkaba masa fitsari a gado, watarana na zuwa da za ya tsane ta, in ma bai hada da duka ba. Don haka ta lallaba ta shige dakin ta ta murza key, ta jingina da kofar tana sakin ajiyar zuciyar tausayin kan ta. Bugun duniya Turaki ya yi, kiran duniya da lallashin duniya amma Kulsum ta ki budewa, don bacin rai kasa kwana a daki ya yi shikadai ya dawo falo ya sa filo a kasa ya kwanta. Washegari sabida farin cikin ba ta yi fitsari ba don ta bi system din nan na non-pharmacological treatment, da kanta ta hada wa Turaki abin karin kumallo. Ta koma dakin ta ta yi wanka ta zuba kwalliya mai sanyaya zuciyar maigida. Ta feshe jikin ta da turaren fahrenheit ta doshi dakin Turaki. Da sallama ta shiga, yana kwance daga shi sai kayan barcin jikin sa yayi filo da hannayen sa yana fuskantar ceiling. Bai amsa sallamar ta a fili ba, amma ya amsa a zuciyar sa. Bai kalle ta ba, balle kwalliyar da aka yi domin shi. Tana iya karanto kwantaccen bacin rai a kan kyakkyawar fuskar sa. Ta karasa a hankali ta zauna a daidai saitin kansa. “Barka da safiya Prince”. Shiru ya yi mata, ta rasa abin da yake mata dadi. “Na shirya abinci, don Allah ka fito ka ci”. A lokacin ne ya juyo gaba daya ya fuskance ta. “Kulsum, yaushe raini ya gifta a tsakanin mu, da har za ki kulle min kofa? Ina miki magana ki ka yi banza da ni kamar ba ki san ina yi ba?" Hawaye suka zubo daga idon Kulsum, ta ce, "Ban yi don raini ba Prince, na yi ne don gudun cutar da kai. Yau da gobe duk hakurin ka da kaunar ka gare ni, wallahi sai ka tsane ni Prince”. “Abin da ki ka yi min shi ne babbar cutarwa a gare ni. Kin sani ba ni da wata matar bayan ke. Ni idan zan same ki a kullum ba ni da matsala da fitsarin ki. Don dai barin garin za mu yi ne, amma tuni na yi mana odar water mattress har guda biyu daga Amazon za su kai min gida na na Reading. In wadannan sun mutu babu damuwa”. Kulsum couldn’t help it ban da ta fada jikin sa ta fashe da kuka, wani irin kuka mai kara soyayyar da ta ke yi wa Turaki. Ta ce, “Na gode Prince, don Allah ka yafe min bacin ran da na sa ka jiya”. Ya ce yana mai tuje daurin da aka bata lokaci ana kalmasawa. “Ai hakuri daya ne, ki biya ni bashina na jiyan". Daga haka ya canza akalar hirar zuwa irin wadda ya fi so su yi. Tun daga ranar Kulsum ba ta kara rufe wa Turaki kofa ba, ta yarda shi din mai son ta ne, mai yawan kaunar ta da tausayin ta ne. Sai dai kuma ta daina barci, kullum cikin non-pharmacological exercise, wato ta daina shan abu mai ruwa-ruwa da shi ruwan kansa daga karfe shidda na yamma, sannan kafin ta kwanta sai ta tabbatar ta yi fitsari, bayan saduwarta da mijin ta abu na farko da ta ke yi shi ne fitsari, sannan ta saita alarm ta aje a saitin kanta tana tashi sau biyu cikin dare at interval ta je ta yi, daga lokacin da suka yi sallar asubah sai ta koma dakin ta, a can ta ke ramuwar barcin ta ta yi fitsarin ta son ranta, sai dai ta yi wata dabara, spreedsheet na kan dining table wanda leda ce ta dauke ta shimfida a saman katifar ta, ta lulluba zanin gado mara kauri a kai. Turaki ya kara sayo su da yawa ya jibge mata, tana tashi za ta yaye su har ledar ta wanke ta shanya a bandakinta, ba ta taba fitowa waje ta yi shanya ba. Turaki ba karamin tausaya mata yake ba, sabida irin yadda ta ke wahala wajen tsaftace kan ta da muhallin ta. Aikin da da hali da ba zai barta ta yi shi da kanta ba, tunda suna da wadatar masu aiki, shi ya sa sau tari yake zuwa ya wanke zannuwan gadon da kansa, idan ta jika su a omo ta shiga wata sabgar. Ta yi ta yi ya bari ya ki, cewa yake. “We are together in this difficulty (muna tare a cikin wannan wahalar)”. A gefe kuma yana ta shirye-shiryen tafiyar su U.K. Ya cika alkawari ya kawo mata dalleliyar waya, sai damuwar ta ta ragu. Kullum in ba ya nan tana tare da ‘yan uwan ta a waya, sannan duk inda ya je Allah-Allah yake ya dawo da wuri don kada kadaici ya jefa ta a damuwa. Ba ya son abin da ta ke yawan fadi na cewa, ta tsani kanta. Ji yake me ya sa ma tun farko bai zama kidney and bladder specialist ko Nephrologist ba? Da tuni ya bai wa Kulsum duk treatment din da ya kamata ba wanda ya ji ba wanda ya gani.. Ganin kwanakin da Dr. Ibrahim ya deba musu yake kamar shekaru uku. Ya je Gombe ya kwana biyu don gudanar da wani private aiki na Sarkin Gombe, wanda cikin ikon Allah aka yi nasara idanun Sarkin suka washe. A lokacin da ya samu lafiya ne ya kira Turaki, wai ya zo ga ‘yar shi Siyama ya ba shi kyautar ta ko a mata ta hudu ne, bayan iyayen kudin da ya tura masa wadanda sun ninninka kudin da suka yi za'a biya shi. Turaki ya yi dariya, ya ce da Maimartaba Sarkin Gombe, ya gode, amma ba zai karba ba, sabida ko wata bai yi da yin aure ba. Wannan labari Turaki ya zo yana bai wa Kulsum, bayan dawowar sa daga Gombe. Kulsum ta lumshe idanun ta ta ce, “Ai da ka karba Prince, ka ga ni babu tabbas din zan warke gabadaya, ko ba zan warke ba. A baya ne nake tsoron ka yi aure, amma yanzu na yarda da kai dari bisa dari, na amince babu macen da za ta sa ka juya min baya. Roko na gare ka shi ne, kada ka taba bari matar ka ta san ina da lalurar urinary incontinence (bed -wetting)”. Turaki ya harare ta son ran sa, ya ce, “Wato Kulsum ba kya kishi na ko?” Ta ce, “Kishi ba zai sa in kware ka ba, soyayyar da nake maka ita ce ta sanya nake son ka samu cikakken farin ciki kamar kowanne namiji. Ina farin ciki da jin dadi ga auren mai jika gado? Ai sai dai maneji, manejin ma sai irin miji na (Turaki) masu babbar zuciya ta tausayi da jin kai”. Fushi sosai Turaki ya yi, wai ta gasa magana kuma ba ta kishin sa. Wuni guda ya ki dawowa gidan, da ya dawo din kuma ya ki yi mata magana. Ya zauna a falo yana kallon football. Kulsum ta fito cikin kasaitacciyar kwalliya, ta zagaya ta bayan kujerar da yake zaune ta zagaya hannayen ta a wuyan sa suka sauka a kirjin sa. Ta sanya fuskar ta a masangalin wuyansa ta sumbace shi son ranta, sumba sosai, mai tsayi da zurfi. “Ina bada hakuri my Prince, ka je ka karata da mai fitsarin kwancen ka, ba zan kara cewa ka yi aure ba”. Duk halin fushin da yake ciki sai da ta ba shi dariya. Ya mika hannu ya zagayo da ita gaban shi ya zaunar ta bisa laps din shi. Bakin ta da ya sha wet-lips ya hau tsotsewa sannan ya dalle mata shi da karfi, sai da ta yi ‘yar kara. “Matar tawa ki ke cewa mai fitsarin kwance?” Don zafi sai da hawaye ya tsattsafo mata. “Ka yi hakuri, na bi Allah na bi ka”. Ya rungume ta sosai yana jin bugun zuciyar ta a kirjin sa. Sun dade a haka yana gaya mata babban abin da ba ya so shi ne ta ce ya yi aure, sabida lalurar ta. Kulsum ta ce a ran ta, tabbas da ta rasa Turaki, kamar yadda ta so yin wannan babbar wauta, hakika da ta yi asara irin wacce ba a mayarwa! Zancen zuci ta ke, ba ta san cewa ya fito fili ya shiga kunnen sa ba. “What are you saying?” Turaki ya tambaya, don bai ji sosai ba. “I said I love you”. “And I love you more”. “I can’t do without you”. “I can’t be happy without you too”. “Na gode Prince, once again, I love you with all my heart…”. Ita ce ta ke fadin soyayyar tata in theory, yayin da shi practically ya soma bayyana mata tasa. Ta gane cewa, tata soyayyar is underestimated. Ga masu soyayya in practice, wadanda ba sa bata yawun bakin su wajen bayyana ta. *** *** *** Kwanakin da Turaki zai yi a Gaya suka cika, wato wata daya. Ya kama gobe za su tashi zuwa U.K, visa din Kulsum wadda za ta je a matsayin matar aure ga ma'aikaci ta kammala, don haka yau da yamma suka shiga cikin gida don yi wa Umma da Maimartaba sallama, daga can kuma za su biya gidan su Kulsum. Maryam ‘yar Yaya Hadiza da ta dawo hannun Umma tun bayan auren Batulu ce ta sanar da su Umma na wurin Maimartaba, bayan sun gaida kowa sun gaida Fulani da jiki sun yi mata sallama tana mai sa musu albarka, suka karasa bangaren Maimartaba din. Kulsum da Turaki suka zube suka kwashi gaisuwa. Maimartaba sarkin Gaya kallonsu yake cike da murmushi, shi dai haka nan yake son yarinya Kulsumu kamar ‘yar cikin sa. Ya ce, “Ummu Kulsum, ina fatan babu matsala, kina nan kina ta hakuri da mijin ki?” Murmushi ta yi, ta ce, “Ai shi ma yana hakuri da ni’. Haka ya yi ta jan ta da hira kamar ba surukar sa ba. Ya ce, “Za a tafi kasar Turawa a bar mu ko? Ni dai aikin nan na Turai bana son sa Turaki, ba zan gaji da maimaita maka ba, kasar mu na bukatar likitoci irin ka, sau biyu ke nan kana min alkawarin dawowa gida gabadaya, amma sai ka kalallame ni ka kara komawa. Yanzu kuma Kulsumun ma za ka dauke ta, mu da ganin ku sai Baba-ta gani”. Turaki ya muskuta ya kara dukar da kan sa, ya ce, "Insha Allahu wannan karon zan cika alkawari, shekaru uku za mu yi mu tattaro komai mu dawo gida. Allah ya kara maka yawan rai, na yi alkawarin ni da iyali na ko birnin Kano ba za mu je ba, a nan Gaya za mu kafa rayuwar mu har mutuwa. Ina da burin bude asibiti idan na dawo, ga UmmuKulsum ma ma’aikaciyar jinya ce za ta taya ni kula da komai. Fatan mu dai a bi mu da addu’a”. Ran Maimartaba Sarkin Gaya ya yi fari tas! Ya ce, “Albarkar mu na tare da ku, albarkar uwa da uba, ba za ku taba tabewa ba”. Umma ma da ke gefe tana ta kallon su sun mata kyau a fuska, sun dace da juna. Turaki ya yi aure wanda ta ke so, kuma hankalin ta ya kwanta da shi, don haka ba ta da sauran damuwa a yanzu. “Umma, ke ma ki sa mana albarka”. In ji Kulsum. Umma ta yi murmushi, “Ai Maimartaba ya hada har da tawa, kada albarkar tamu ta yi muku yawa”. Kowa sai da ya murmusa. Ta ce, “ku tashi ku je gidan su Kulsumu ku yi musu sallama kada dare ya yi sosai”. Suka mike a tare suna godiya. “Goggo tana nan? Jibo na kiran ta a zaure”. Kulsum ta make murya ta fada daga tsakar gida. Goggo na lazimi ta jiyo ta, ta yi dariya da murmushi duka a tare. Baffa Jibo ne ya fara fitowa daga dakin sa. Ya nunata da dan yatsa. “Wannan Jibon dai ya fi karfin ki, in ma zawarcin sa ki ka zo”. Ta ce, “Haba! Kayyasa! Wane mutum! Ina da sardidin likita na a gefe, me zan ci da tsoho baki duk goro?” Turaki ya sunkuyar da kai yana dariyar su. Goggo ta fito ta shimfida musu tabarma, farin ciki ya cika ta, yau Kulsum ce tare da Turaki suna masu farin ciki da juna. Ya Allah ya kara mata tsawon rai, ta dauki jikokin su. Addu’ar da ta ke yi a zuciyar ta ke nan. Ko da Kulsumu suka shiga daki da goggo, ba ta gaya mata fitsarin ta ya dawo ba. A wannan gabar ta rayuwar su ta amince suna bukatar kwanciyar hankali. Ta kuma kwana da sanin babban tashin hankalin su a rayuwa fitsarin kwancen ta ne. Duk wani support da encouragement (karfin gwiwa) ta gama samun shi a mijin ta abin kaunsr ta (Turaki). Ba abinda fada musun zai haifar sai tashin hankali a gare su. Kulsum ta kira Baban ta ta yi masa sallama, sabida Turaki ya ce gobe kafin su wuce Abuja za su fara zuwa 'Yalleman su yi wa Baban sallama, nan Goggo ta ke gaya mata ya kira ta dazu ya ce ba ya gari, ya je Maiduguri kan wata harka da ya samu. Tausayin Baban ta ya cika ta, mutum ne shi mai kokarin neman na kansa don rufuwar asirin iyalin sa. Ta roki Allah ya ara mata dama ko yaya ne watarana iyayen ta su huta a karkashin inuwar ta. Duk da cewa ba cikin wahala suke ba. Ta gaya wa Goggo, Turaki ya ce gobe ta Abuja za su tashi, don haka za ta biya gidan Hajiyar ta. Ba su bar gidan ba sai karfe sha daya na dare. Tunda suka koma gida suka fara hada kayan su. Washegari karfe shidda na safe suka dauki hanyar Abuja. Daga Kulsum sai Turaki a motar. Yana tuki tana gefen sa, tana so ta yi barci don barcin ta na jiya ragagge ne, ta kwana tana hada kayan su. Amma tana yaki da barcin don kada tsautsayi ya sa ta fitsare masa mota. Da ma ta yo guzurin lipton din ta, shi ta yi ta sha har da su nescape duk don su hana mata barci. Turaki na tuki ba tare da ya juyo ba ya ce, “Wai wannan shan shayin na mene ne? Ko dai…”. Ya ki karasawa yana murmushi. Kulsum da bata dago inda ya sa gaba ba ta ce, “Ko dai me? Ni don ya korar min bacci nake shan sa”. Da mamaki ya ce, “To a kan me ba za ki yi barci ba? Ana raba jikin dan Adam da barci ne?” “Uhm”. Kawai ta ce, ai it is embarrasing ta gaya masa tana tsoron jika masa mota ne. Hannun hagun sa ya mika ya kwantar mata da kujerar ta. “Please sleep baby”. Yana iya hango fargabar ta cikin kyawawan idanun ta. Ya kuma san me ta ke fargaba din. “To Ummu Kulsum, mece ce mota? Barcin ki ya fi ta muhimmanci a waje na”. Tana lumshe idanu cike da barci ta dube shi cikin shaukin so. Mutum kamar mai gani har hanji? Ya daga mata gira tare da kashe ta da wani kyakkyawan murmushi da ya ratsa har cikin ruhin ta. “Help me and sleep” (taimakeni ki yi barci). Kulsum ta lumshe idanun ta, kafin dan lokaci barci ya dauke ta. Cikin taimakon Allah ba ta yin ba har suka shiga Abuja. Yana kokarin shiga da su hotel din Rockview ta ce, “Prince, don Allah mu je in gaida Hajiya ta, ban yi mata sallama ba”. Ya ce, shi sai ya yi wanka da sallah ya huta. Kuma sai ta tabbatar saurayin ta ba ya gidan sannan za su je. Ta yi narai-narai da ido. “Ya ya za a yi in san yana gidan ko ba ya nan? Shi da gidan su?" Ya yi fuska ya ce, “Ki kira ki tambaya". Dariya ta yi ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska. “Da ma ka cire shi a ran ka, ni ban taba son sa ba, irin son da ka ke tunani. Ina son sa ne a matsayin sa na dan uwa na na jini, kuma shi ma ya sani, ya sha fada da bakin sa; “Ki taimake ni kada ki kara ambaton Turaki a gabana, zuciya ta za ta buga Kulsum”. Turaki ya yi wani lallausar murmushi yana murza sitiyarin motar sa cikin gwanin ta. “Wato har zance na ki ke masa Kulsum? Ashe kina so na duk da laifuka na gare ki?” Ya fada cikin sanyin murya. Kulsum ta kare fuska da mayafin ta, “Hatta Hajiyar mu da Goggo, sun san irin son da nake maka Prince". Turaki ya mika hannun damansa ya kama nata ya matse shi sosai a cikin hannun sa. “To say I thank you… is not enough to express the feeling….....”. Daidai lokacin da suka adana motar a parking lot. Ya mika hannu ya bude mata kofa, jakar hannun ta kawai ta dauka. Turaki ya wuce gaba ya je ya kama musu daki. Ta lifter suka bi zuwa dakin nasu. Duk abubuwan da ya lissafa sai da ya yi su; wanka, sallah, hutawa sannan suka fito don tafiya (Brains&Hammers) wato gidan Hajiya Nasara. Hajiya Nasara kadai suka samu a gidan, karshen farin ciki ta yi shi da ganin su. Ta sa Serah ta shirya musu abinci. Turaki duk ya kasa sakewa saboda surukuta, amma haka ta matsa musu kan sai sun ci abinci. A dakin ta da Kulsum ta shiga domin su gaisa sosai Hajiya Nasara ta kasa boye farin cikin ta, ta ce, “Na ji dadin yanayin da na ganki ciki Kulsum, na kuma tabbata Turaki na kula da ke yadda ya kamata. Madallah”. Nan Kulsum ta ke gaya mata sallama ta zo ta yi mata za su wuce U.K can inda Turaki ya ke zaune, ba ta san lokacin da za su dawo ba. Farin cikin Hajiya Nasara ya karu, ta ce, “Ai kuwa zama bai gan ni ba, bari in tattara miki kayan girki, don a can ba za ki samu irin su ba”. A waya Hajiya Nasara ta kira Dr. Sakeenah da Nasmah duk ta gaya musu tafiyar Kulsum. Nasma ta shiga EDD dinta, Taufeeq na Lagos, kayan amfani masu yawa Hajiya Nasara ta hada mata. Ko da wasa Kulsumu ba ta yi zancen fitsarin ta ba, ba ta so ta kara daga wa kowa hankali, wahalar da suka sha a baya Allah ne kadai zai biya su da mafificin alherin sa. Sai karfe goma suka bar gidan, domin hira ce sosai ta shiga tsakanin Turaki da Hajiya Nasara, kasancewar su duka mazauna Birnin Sarauniya. Hajiya ta ce, ta taba zuwa Reading Berkshire, kuma insha Allah ba da jimawa ba in sun shigo London za su zo har Reading su gan su ita da Daddy. Ko da suka koma hotel gajiya ba ta bar su sun tsinana komai ba. Amma Kulsum ta ki yarda ta kwanta don kada ta yi fitsari. Ta hau kujera kwalli daya da ke dakin ta kishingida tana faman daddanna wayar ta. Turaki ya kwace wayar, ya kuma kashe fitila mai haske ya ce, “Malama ki kwanta please, gobe asubanci za mu yi, is good ki samu barci ko yaya ne”. Ta bi umarnin sa ne kawai don ta san ko me za ta ce ba zai kyale ta ba. Suka kwanta Kulsum kalmashe cikin jikin sa. Amma ko na sekon daya ba ta bari barci ya dauke ta ba. Ta lafe a jikin Turaki tana sauraron yadda yake sauke numfashi a hankali, ita ina ta ga wannan kwanciyar hankalin? Ta lura Turaki na jin dadin barcin sa, don haka ba ta nuna wata alama da za ta nuna idanunta biyu ba, har lokacin sallar asubahi ya yi. Karfe shidda wanda zai kai su filin jirgi ya kuma tafi da motar Turaki ya zo, wani abokin sa ne Dr. Habib mazaunin Abuja. Sun bata lokaci wajen screening da zaman jiran jirgi ya daidaita. Karfe goma sha daya na safe jirgin su ya tashi zuwa United Kingdom. *** *** *** A cikin jirgi ne Kulsum ta samu ta yi barci sosai a jikin Turaki. Tafiyar awanni takwas a cikin jirgin British Air ta sauke su a birnin London. Inda daga nan suka dauki taxi ta kai su tashar jirgin kasa, suka bi train zuwa garin Reading, Berkshire. Nisan da ke tsakanin babban birni (London) da garin Reading (37 miles) ne, wato tafiyar mintuna arba’in da biyu a cikin jirgin kasa. Reading babban gari ne mai tsohon tarihi a kan kasuwanci a yankin Berkshire (South-East England). Gidan Turaki na cikin jerin gidajen malaman jami’ar Reading. Mai taxi din da ya dauko su har kofar gidan ya sauke su. Gajiyar da ke tare da Kulsum ta sa ba ta gane komai da ke cikin gidan ba sai washegari. Gida ne a cikin Estate duka gidajen iri daya ne, masu dakuna ciki-biyu da falo, kowanne daki da toilet manne a cikin sa, sai kicin wanda kofar sa ke cikin falon, sai garden daga wajen kitchen din, mai shimfide da korran ciyayi daga sama har kasa sun yi wa gidan rumfa ruf, gidan karami ne sosai kamar sauran gidajen Estate din, sai dai ya ishi dan Adam duk wasu bukatu na rayuwar sa. Kwanan su uku ba su je ko’ina ba suna ta fama da fitsarin Kulsumu. Fitsarin da kamar jira yake su sauka a Reading ya kara ta’azzara. Hutawar da suka yi niyya duk ba su same ta ba, soyayya an jingine ta a gefe saboda Kulsumun kwata-kwata ba ta cikin hayyacin ta saboda damuwa da tashin hankali. Ita babbar damuwarta shi ne Turaki zai tsane ta. Yayin da shi kuma damuwar sa ita ce damuwar da ta ke jefa kanta a ciki, wadda yake tsananin tsoron kada ta taba brain dinta, ta jawo wata matsala wadda ta fi ta fitsarin kwance. Ya kira Dr. Ibrahim Takai kan appointment din su na ganin sa, ya ce za su hadu a asibitin nasu Turaki, wato Royal Berkshire Hospital ya zo ziyarar aiki ne daga Illinoise teaching hospital na watanni uku a asibitin koyarwa na garin Reading. Kulsum ta yi tsai da idanun ta tana kallon Dr. I.M Takai, ta dauka za ta ga mutum wanda ya manyan ta kamar likitan ta na Lagos, sai ta ga sardidin mijin na Rayhanah Baban Asma’u matashi tamkar nata mijin. Sun dade suna magana shi da Turaki, da turancin su mai accent wanda ba duka ta ke fahimta ba. Ya yi mata tambayoyi masu yawa tana ba shi amsa. Ta kuma gaya masa sunayen magungunan da ta ke sha a baya, da dukkan treatment din da ta karba daga hannun likitan ta na Lagos. Dr. Ibrahim ya dube ta sosai, sannan ya ce, “Ina tsammanin kina da karamar mafitsara ko blocked urethra (mafitsara tosasshiya), zan yi miki test har guda hudu; na farkourinalysis, inda za mu dauki sample na fitsarinki mu duba infection acikin sa ko sauran urinary tract infections. Test na biyu da za mu yi shi ne urine culture, inda za mu tura sample na fitsarin ki zuwa lab don duba ko akwai bacteria ko yeast a cikin fitsarin ki. Sai test na uku shi ne uroflowmetry, inda za ki yi fitsari a cikin special funnel da za mu ba ki, mu auna yawan fitsarin da ki ke yi and how quickly it flows out. Sai test na karshepost-void residual urine measurement; wannan test din zai nuna yawan fitsarin da yake ragewa a mafitsarar ki ba tare da ya fito ba duk lokacin da ki ka yi fitsari. Idan muka yi duk wadannan gwaje-gwaje, za mu gane what are the possible causes na nocturnal enuresis din ki. Za mu gane blocked urethra ne ko pelvic organ prolapse, ko kuma matsalar daga structure din mafitsarar ki ta ke (wanda na fi tsammani), ko enlarge prostate ne ko urinarytract stones ko infection na mafitsara. Ki ci gaba da non-pharmacological treatment irin na baya, sannan inaso ki gaya min abubuwa guda hudu. Karfe nawa ki ke bed -wetting? Yawan fitsarin da ki ke yi (kadan ne ko mai yawa)? Yawan abin da ki ke sha kafin kwanciya barci? Sauran alamomin da ke nuna za ki yi fitsari? Kulsum ta fada masa duk abin da ya tambaye ta iya sanin ta. Doctor Takai ya ce, “To yanzu za ki shiga toilet ki ba mu fitsarin ki, mu auna mu gani, sannan akai lab, gobe sai ku dawo mu ga me result ya nuna”. Washegari karfe goma na safe suna gaban Dr. Takai, nan ya gaya musu result din gwaje-gwajensu ya nuna Kulsum na da karamar mafitsara. Za ta sha magunguna masu karfi ba irin na baya ba na tsawon sati biyu, derifenacin (enablex), oxybutynin (ditropan), tolterodine (detrol) da kuma trospium chloride. Idan ba ta daina fitsari tsayin wata guda ba za su dawo. Dole sai an yi surgery. Sunan surgery din da za'a yi “Bladder augmentation”. Dr. Takai ya ce, “It’s an operation that makes your bladder larger, which raises the amount of urine it can hold (aiki ne da ake yi wanda zai kara girman mafitsarar ki, ya kara yawan fitsarin da za ta iya rikewa)”. Da wannan suka baro gaban likita Takai bayan Turaki ya sayo duka magungunan da aka rubuta musu. Haka kawai Kulsum ke jin wata irin gamsuwa wannan karon da treatment din gawurtaccen nephrologist Ibrahim Takai, domin kwata-kwata bai yi kusa da wanda ta samu a Lagos ba. Wai gaba da gabanta aljani ya taka wuta. Magungunan sun fi na baya karfi nesa ba kusa ba. Sai da ta yi sati daya ba ta yi fitsari ba ko sau daya da ta fara shan su. Murna wurin Kulsum abin ba'a cewa komai, amma Turaki kallon ta kawai yake. As a medical doctor jikin sa yana ba shi karshen ta dole sai an yi surgery din nan. Ya koma aikin sa tuni, don haka ita kadai ta ke wuni a gidan, Sajeedah da Abdul’Ahad sun bar Reading sun koma Manchester inda aka yi wa Abdul’Ahad transfer. Turaki ya mata alkawarin in hankalin su ya kwanta sun gama da asibiti za su je musu har Manchester wajen su. Ilai kuwa bayan kwana goma sai ga shi ta sake yin fitsari, wanda alama ce da ke nuna cewa, karshen ta surgery zai tabbata. Turaki bai gaza ba wajen karfafa mata gwiwa kan cewa yana tare da ita cikin kowanne hali, yana son ta a duk yadda ta ke. Sati hudu suka cika suka koma gaban likita, ko a ranar ma sai da ta yi fitsari, don haka Dr. Ibrahim Mansur Takai ya sa musu ranar surgery kwanaki biyar masu zuwa. ***** Ana i gobe surgery din Kulsumu kasa barci ta yi, gani ta ke in ta shiga dakin tiyata ba za ta fito da sauran numfashi ba. Turakin ta zai zama mallakin wata a bayan ran ta. Ta yi kuka, ta yi kuka har ta ji babu dadi. Ko da Turaki ya dawo aiki a ranar ya fahimci ta ci kuka ta gode Allah. Bai yi kasa a gwiwa ba wajen wanke damuwar ta da nau’ikan soyayyar sa masu tsayawa a zuci. Da ya fita sai ga shi ya dawo da sinkin adult diaper (pampers din manya) don su huta da wankin zanin gado, duk da yanzu ba ya taba katifar su sabida water mattress ce. Dr. Takai ne ya ba shi wannan shawarar ya ce, hakan zai fi musu sauki, after intercourse din su ta sanya diaper idan non-pharmacological treatment ya ki aiki a jikin ta. Kulsum ba ta taba jin madaukakiyar kunya a duniya irin ta yau ba. Wane embarrassment ne ya wuce miji ya sanya maka diaper? Ta jinjina wa Turaki a zuciyar ta, ta amince samun kamar sa cikin maza dubu sai an tona. She is indeed among the luckiest women on earth (tana daga cikin mata masu sa'a a duniya), amma shi din ko a jikin sa, gaya mata ma yake, “Ba shi ke nan mun huta da wankin bedsheets ba?” Ita dai kunya ba ta barta ta ce komai ba. Da idanun sa yake lalubo idon ta wanda ya cika taf da hawayen tausayin Turaki. Ta fi tausayin shi akan yadda ta ke tausayawa kanta. Ita ke fitsari, amma shi ke cin wahalar sa. Da suka hada ido ya daga mata gira, a hankali ta ce, “Na gode Prince”. Sai ta fashe da kukan tausayin kanta. Turaki ya janyo ta barin jikin sa yana fadin. “In dai diaper ce ta sa min mata kuka, sai a bar ta, babu dole”. Kulsum ta shafe hawayen ta, a hankali ta ce, "Ba kukan diaper nake ba, kuka nake don tausayin ka, ka auri wahala... Ka auri kazanta. Yet ba ka taba nuna min gazawar ka ba. Ba ka taba nuna kyama a gare ni ba. Don Allah Prince ka kara aure... Wallahi na amince, in ba haka ba sai alhakinka ya hana ni warkewa". Murmushi Turaki ya yi, ya ce, "Well, mu bari after surgery in ba ki warke din ba sai ki zabo min mata na aura. Amma ni ba ni da idon kallon mata. Mai fitsarin kwancen kawai ido na yake iya hangowa". Za ta iya cewa ba ta taba jin kalmar da ta yi mata dadi a rayuwar ta irin wannan ba. Ko da kuwa Turaki ya fada ne don ya faranta mata kadai ba don haka abin yake a zuciyar sa ba. ***** Washegari aka shiga da Kulsum dakin tiyata. Bayan sun yi wata irin sallama da mijin ta Turaki 'very emotional'. Ya sumbace ta a goshi da hanci. Ya ce, "Insha Allah lafiya za ki tashi Kulsum, kuma da yardar Allah wannan shi ne karshen wahalar ki". *** *** *** A rayuwar Dr. Ibrahim Takai, bai taba yin 'surgery' ko 'kidney transplant' an samu kuskure ba, to haka ma a wannan karon yana kyautata zaton samun nasara a aikin da ya yi wa Ummu Kulsum. Amma ba za a gane hakan ba sai nan da wata daya. Kulsum za ta ci gaba da zama a gadon asibiti. A wannan lokaci jinyar duk wata kulawa da soyayyah Kulsum ta same su daga mijin ta Turaki. 'The one in million husband', wanda ta ke fatan har a lahira Allah ya tashe su tare matsayin abokan rayuwar juna. Bayan 'surgery' da jinyar wata guda, sun ci gaba da zuwa 'check up' a asibitin 'Royal Berkshire' hannun likitan da Dr. Ibrahim Takai ya yi 'referring' din su, wato Dr. Kennedy baturen Worcaster, shi din 'kidney and bladder specialist' ne da ake ji da shi a asibitin nasu. Yayin da Ibrahim Takai ya koma Illinoise wajen Rayhanar sa,bayan ya gama aikin da ya kawo shi Reading. A duk sanda suka zo 'check up' Dr. Kennedy na fada musu aiki ya yi kyau. Akwai ci gaba sosai, da taimakon Ubangiji wannan karon Kulsum ta rabu da lalurar 'Nocturnal Enuresis'. Ranar 'check up' din su na karshe likitan ya yi murmushi ya dube su. "Congratulations Mr. and Mrs. Abubakar Turaki Abdullahi, your wife is finally saved from bed-wetting". (Matar ka ta kubuta daga lalurar fitsarin kwance). Ya kara murmusawa ya ce yana bai wa Dr. Abubakar shawarar ya dauki hutu domin ya murmure daga jinyar nan da ya sha, su je garin Chelsea su huta. Dariya Turaki ya yi ya dubi Kulsum, wadda ta sadda kai kasa, hawayen farin ciki na zuba daga idanun ta. A haka Turaki ya kama hannunta suka bar gaban likita bayan ya yi masa godiya sosai. *** *** *** "Shi ke nan yanzu kuma sai mu fara shirin zuwan amarya tunda uwargida ta warke?" Turaki ya fada a lokacin da ya zura mukulli yana bude kofar 'apartment' dinsu. Kulsum ta yi gumm! Kamar ba ta ji shi ba. Ya sake maimaita abin da ya fada, ta dauke kai ta shige dakin ta. Wanka ta yi, ta yi kwalliya irin wadda tun zuwansu U.K ba ta taba yi ba saboda rashin kwanciyar hankali. Ta yi alkawarin ingantawa Turaki daren yau da dukkan iyawar ta, domin nuna masa godiyar ta ga dumbin lkhairin sa da soyayyarsa gare ta. Wata irin doguwar riga ta saka mai bin jiki da aka yi da yadin 'velvet', ta bi fatar jikin ta ta kwanta lambam. An tsaga ta tun daga idon sawu har zuwa gwiwa ta yadda santala-santalan kafafunta suka fito 'freely' in tana tafiya. Ta feshe jikinta da turaren nan na mata mai dadin kamshi COOL WATER (Davidoff). Gashin kanta da ba wani yawa ne da shi ba sai salki da cika irin na fulanin Gaya ta raba biyu ta tufke shi gefe-da-gefe. Ba ta taba shafa 'lip-stick' ba tun auren ta da Turaki sai yau. Ta shafa shi kalar 'light pink' samfurin avon. Ta taje gassun idon ta da girar idon ta da 'mascara' nan da nan fuskar ta ta zama 'cute' ta yi kyan da ba ta taba yi ba. A hankali Kulsum ta ke taku kamar a filin fashion-parade tana ta faman shige da fice a gaban Turaki, wanda ya baza takardu a falo yana ta aiki cikin 'macbook' din sa. A hankali ya cira kai ya dube ta za ta wuce rike da robar 'ice-cream' a hannun ta. Ya dan kara girman idanun sa yana kallonta sosai. Bai san sanda ya ce, "...Come here baby...". Ta rangwadar da kai, "Ba aiki ka ke ba Prince?" Ya ture 'macbook' din gefe, ya ce, "Na ce ki zo koh?" Ta tako a hankali tana shan 'ice-cream' din ta debo kadan ta nufo bakin sa, yayin da shi ba ta wannan yake ba, kokari yake don ganin ya zuge zib din rigarta gabadaya, yana fadin. "A duniya akwai mai hakuri iri na? Quite three months ba tare da mata ta ba...". Kulsum ta sakar masa komai, tare da inganta masa daren yadda ya kamata. Ita kanta wani abun bata san ina ta koyo shi ba. Ta dai sa wa ran ta ne za ta yi komai don ta faranta wa Turaki. Rayuwar ta kacokam fansa ce ga farin cikin sa. Daren ya kasance musu tamkar a ranar suka taba kusantar juna, ya shige cikin darare masu dumbin tarihi da suke adanawa a kundin rayuwar su. Washegari suka shirya suka tafi Chelsea, kwanan su uku a 'hotel' din 'The Chelsea Harbour Hotel' suna gwangwaje soyayyah zallah, ko wayoyin su kashewa suka yi. Sai lahadi da daddare suka bi 'train' suka koma Reading. Rayuwar auren Kulsum da Turaki kenan, rayuwa ce wadda aka gina bisa soyayyah, kauna ta fisabilillahi da yarda zallah, wadda biro ya yi kadan ya bayyanata. Sun gina rayuwar auren su ba don kyale-kyale na rayuwa ba. Babu sirrin junan su da ba su sani ba. Yo mijin da ki ke yi wa fitsarin kwance ya wanke ai zance ya kare. Turaki ba ya boye wa Kulsum komai da ya shafe shi, ko da a fannin aikin sa ne. Da hankulan su suka natsa ne ya gane Kulsum na da matsala a ido. Sai lokacin ne ya tuno zuwansu European Eye Hospital a Lagos ita da Taufeeq, ya tsare ta da tambaya kan me ya kai ta ranar? A nan ne ya san matsalar idon Kulsum ta tun haihuwa. Mai abu da abunsa, wani ma ya yi rawa bare dan makadi? Tuni ya sa ta a gaba da bincike da gwaje-gwaje, a nan ya gano tana dauke da matsalar da suke kira amblyopia (lazy eye), wanda magunguna na digawa (eye drops) kadai zai magance shi ba sai ta saka gilashi ba. Tun daga ranar ya soma diga mataeye drops masu kyau har suka washe. ******* Ranar ta kasance juma'a, da wuri Turaki yake dawowa gida. Ya shigo a matukar gajiye, Kulsum na zaune ta bararraje tana shan 'ya 'yan 'strawberries' in zai iya tunawa yau wajen sati guda ke nan ba ta da abinci sai 'ya'yan 'strawberries'. Ta kashe shi da murmushi, ya ce, "Kulsum are you alright? Cin wannan abun naki ya yi yawa fa". Ta yi narai-narai da ido, "In ban ji shi a baki na ba sai in ji saliva (miyau) ya cika min baki". Murmushi ya yi ya aje jakar hannun sa da falmaran din 'suit' din jikin sa akan kujera. "Then, you are subject to P-t (pregnancy test)". Zaro ido ta yi abin dariya, "Haba Prince! 'yar yarinya ta da ni za ka yi min wannan fatan?" Dariya ya yi, ya iso gare ta ya mikar da ita tsaye. Ya jingina bayanta a jikin sa ya daga rigarta da hannun damansa yana shafa shafaffen cikin ta cikin shauki. "In mace ce, Batulu ce. In namiji ne Abdul'Ahad ne. Su suka taimaka min na same ki 'for the second time', a lokacin da na riga na sa a raina na rasa ki, ciwon son ki kuma shi ne zai yi ajali na. Sun ba ni 'support' din su dari bisa dari tare da tabbatar min ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare. With Almighty Allah everything is possible". Kulsum ta yi murmushi, ta ce, "Ni dai ban fada maka ina da ciki ba". Ya ce, "Amma kin iya sa miji a daki kina k......". Da sauri ta kwace jikin ta daga nasa ta yi daki, tare da sa yatsun ta biyu ta toshe kunnen ta. Turaki bai yi shiru ba sai da ya karasa mata. Ya kuma tabbata zahiri Kulsum na da karamin ciki na watanni biyu, lokacin da Turakin ya gaji da ciye-ciyen ta ya kai ta 'lab' aka auna fitsarin ta. A wannan satin suka shirya zuwa Manchester wajen su Sajeedah. A 'train' suka tafi zuwa Manchester. Sajeedah da Abdul'Ahad suka shirya musu tarba ta musamman za su yi weekend (hutun karshen mako) tare da su. Amma kasancewar gidajen U.K kanana ba 'spare room' dole sai a 'hotel' suka sauka. Da safe wanka kawai suka yi suka shirya Abdul'Ahad ya zo ya dauke su zuwa gidan su. A can suka yi 'breakfast', Kulsum da Sajeedah suka wuni hira, Sajeedah na kara wayar mata da kai a kan rayuwar duniya gabadaya. Da yamma suka debe su a motar Abdul'Ahad don su zaga da su cikin Manchester, inda suka ziyarci 'Greater Manchester, Castle Field, National Football Meseum, Man City and Man United' da suke jin labari. A karshe suka dire a 'university of Manchester' jami'a mai tsohon tarihi. Sun rabu kamar kar su rabu, a lokacin cikin Sajeedah watanni bakwai. Burin Sajeedah ya cika ta zama 'best friend' din Kulsum, abin da ba ta taba yi a rayuwar ta ba (kawa) bayan Batulu. Ba tare da shawara da ita ba Turaki ya cike mata 'application' na neman gurbin karatu. Babu jimawa 'admission' dinta ya fito, ya kawo mata har kan cinyar ta. Kulsum ta daga takardar tana karantawa a hankali. 'Admission letter' ce manne da sunan ta KULSUM ABDULHADI YALLEMAN za ta karanci digiri a fannin aikin jinya (B.Sc Nursing) na tsawon shekaru uku a jami'ar da Turaki yake wa aiki, kuma ya yi nasa karatun, wato 'university of Reading'. Da Kulsum ta buga wani tsalle sai ga ta makalkale a bayan Turaki. Da sauri ya sa hannu ya riko ta. "Kina da hankali kuwa? Wani abu ya samu cikin nan wallahi sai an fasa karatun". "Na tuba na bi Allah na bi ka, Baban Batulu, angon Kulsum. Na rasa ta hanyar da zan nuna godiya ta, ka gama cika min duk wani buri na, ka gama yi min duk wani taimako a rayuwa. A lokacin da na fi bukatar taimako. Ka ba ni dukkan kauna da kulawa ta yadda kullum nake kwana in wuni ina tunanin, ni da me zan saka maka Prince?" Tafiya ya hau yi dauke da ita a bayan sa zuwa dakin sa. Cewa yake, "Kin fi kowa sanin da me ki ke saka min UmmuKulsum. Fata na ki cika min gida da 'ya'ya shi ne kawai tukwicin da za ki yi min". Cikin sa'a cikin nata ba mai tsarabe-tsarabe ba ne. Barta dai da ciye-ciye, ci banza ci wofi don haka bai ba ta matsala sosai ba lokacin da ta fara zuwa makaranta. Da farko ta sha wahala sosai kafin ta gane kan karatun nasu, amma da ta likewa Turaki duk sanda yake gida tana gefensa rike da littafin ta, nan da nan komai ya fara zauna mata. Domin koyarwar Turaki wanda ya kasance malamin jami'a, kuma 'consultant' a kiwon lafiya ta sha bamban da ta dukkan malaman ta. Ta yarda Turaki dan baiwa ne ba a fannin soyayyah kadai ba, Ubangiji ya ba shi baiwa a ilmin kiwon lafiya. Ko da watan haihuwarta ya kama Turaki cewa ya yi ba za ta je gida ba, kasancewar suna tsakiyar karatu. Ta haifi kyakkyawar 'yar ta mace a asibitin 'Royal Berkshire' ranar litinin. Turaki ya rungumi 'yar shi ta farko a duniya yana tsaye a kan mahaifiyar ta da ake gyarawa. Tare da shi aka karbi haihuwar. A wurin ya yi mata khutbah da sunan da ya tanadar mata tuntuni, wato Fatima- Batulu. Lokacin da Kulsum ta samu kanta, Turaki ya dauko babyn ya ajiye mata a kan kirjin ta. Murmushi ta ke yi tana kallon yarinyar. Komi na Turaki ta kwashe, har zara-zaran yatsun hannun sa. Ta karanta addu'ar kariya daga zina ta tofa mata a al'aurarta, wato aya ta 11 cikin 'suratul Tahrim'. (Wa Maryam ibnat Imranal-laty ahsanat farjaha fanafakhna fiihi min ruhina wa sadaqat bikalimati rabbiha wa kutubihi wa kanat minal qaniteen) kafa 41, sannan ta mika wa Turaki ita, wanda ya zauna a kusa da ita yana rada mata kalaman da suka zamo sirri ne a tsakanin su. Lokacin da Kulsum ta yi wa Batulu albishir da sunan da Turaki ya saka wa baby, Batulu kuka ta saki don farin ciki. Tun ba su bar gadon asibitin ba kowa nasu da ke Gaya ya samu labarin haihuwar, Turaki ya kira Hajiya Nasara ya gaya mata, ta ce da man cikin satin nan za su shigo U.K ita da Daddy za su shigo Reading su ga baby. Hakan kuwa aka yi, washegarin komawar su gida su Hajiya Nasara suka zo, Sajeedah ma da danta Naufal duk sun zo. Duk da Turaki ya dauki nurse wadda za ta kula da su a gida, Hajiya Nasara ita ta ke wa maijego wanka da tawul, ta kuma wanke baby safe da yamma. Dole Turaki ya debi kayansa ya bar musu gidan don ya yi musu kadan, daki ya je ya kama a 'hotel' na tsawon sati biyu da Hajiya Nasara za ta yi. Umma ta yi fadan lallai ya dauko Kulsum da baby ya dawo mata da su, amma da ta ji Hajiya Nasara na tare da su sai ta hakura, ta tabbatar za ta ba su kulawa yadda ya kamata. Jego na sosai Hajiya Nasara ta yi wa Kulsum, Sajeedah ce mai musu girki. Cikin kwana bakwai sun murmure sun yi kyau. Turaki da Abdul'Ahad sai dai su zo su ci abinci su tafi, don Abdul'Ahad din tare da Sajeedah da dan su Naufal suka zo. Ya yi 'weekend' tare da su ya koma Manchester ya bar su Sajeedah ita da Hajiya Nasara suka ci gaba da kula da mai jegon da baby har tsayin sati biyu, inda Hajiya Nasara ta soma shirin koma wa London inda ta baro Daddy, za su kara sati daya sannan su wuce gida. A bakin Hajiya Kulsumu ta ji labarin Taufeeq ya samu mata, diyar abokin Daddy ce, nan da watanni uku za a yi bikin. Ta nuna wa Mum farin cikin ta sosai tare da yin fatan alheri. A ranta ta ce, da a ce tana da wata sana'a ko tana da kudi, da ta yi wa Taufeeq gudunmuwar lefe. Kamar Turaki ya san abin da ke ranta, lokacin da Mum za ta koma ya dunkulo kudi masu dama ya ba ta, ya ce ta hada wa kowa da ya dace tsaraba. Don haka ta rubuta wa Sajeedah duk abin da ta ke so ta sayo da kudin. Goggo da Umma atamfofi Sharaton turmi uku kowannen su, Baffa da Malam Hadi bandirin shadda excelcior, Maimartaba turare mai daraja, hatta yaya Hadiza da Batulu ta aika musu 'laces' masu kyau, sannan ta sa Sajeedah ta saya mata takalma da jakunkuna set (24) bayan ta sa Nasmah ta tambayo mata 'size' din kafar Fahima matar Taufeeq, ta shirga su cikin akwati ta bai wa Mum ta ce a bai wa Taufeeq gudunmuwar ta. Aka ce naka-naka ne, sai dai ka yi kara da kawaici. Hajiya Nasara ta yi farin ciki sosai ba don ba ta da shi ba. Sai don alheri wa naka ko ya ya yake dadi ne da shi. Washegari ta koma wajen mijin ta suka fara shirin dawowa gida. Taufeeq ya yi mamakin sakon da Kulsum ta aiko masa. Ya dauka ta yanke alaka da shi kenan tunda ta samu dan Sarkin ta. Ko ba komai hakan ya rage kullacin da ya yi mata. Har da Hajiya ta kira ta ya karbi wayar ya yi mata barka, wannan ya faranta ran Hajiya Nasara sosai. Su ma su Sajeedah washegarin tafiyar Hajiya Nasara suka koma Manchester. A daren Turaki ya dawo daga balaguron 'hotel' dinsa, ya tadda iyalinsa cikin koshin lafiya. Aka dora soyayya daga inda aka tsaya, musamman da ya kyalla ido ya ga Kulsum na sallah. Kulsum har da kukanta kan cewa za'a sa ta yin kazamin jego, da gwarne (rurrutsa). Duk sai ta bai wa Turaki dariya, ya ce yana mai tallafo kanta cikin tafukansa, "Rurrutsa na taso na ga ana yi a gidanmu, kuma ban ga kowa ya mutu ba. Mun rayu bi-da-bi cikin koshin lafiya. Ni in za ki haifa min yara duk karshen wata ina so Kulsum, tunda Allah bai hana min yadda zan yi da su ba". A yanayin da ya yi maganar ya karya zuciyar Kulsum. Ta ji cewa, ba gwarne/rurrutsa ba, ko haihuwar kullum yake so za ta yi masa muddin hakan yake so. Ta shige cikin jikin Turaki a hankali tana mai sallamawa dukkan bukatun sa. Idan ta tsaya tana lissafo gudunmuwar Turaki cikin rayuwar ta, sai ta ga cewa ita ba ta taba yi masa komai a duniya ba. Don haka kamar yadda ya ce din ne, da haihuwar kawai za ta biya shi. Burin sa ya bude ido kullum ya ga 'ya'yan ta sun cika masa gida. Wannan ne kadai martanin soyayyar da yake so daga gare ta. Kafin Kulsum ta kammala B.Sc din ta 'ya'yan su biyu; Batulu da Iftihal. Zuwa wannan lokacin Turaki ya yi murabus daga aiki a 'United Kingdom' ya tattaro tarin kwalayen sa da experience din sa da iyalin sa sun soma shirin dawowa gida gabadaya. Kulsum Abdulhadi, a matsayin cikakkiyar ma'aikaciyar jinya mai shaidar HND da B.Sc. ***** MURFI GAYA Suka dawo mahaifar su kamar yadda suka barta shekaru uku a baya. Cikin iyayen su, kakannin su da 'yan uwan su. Ba jimawa Turaki ya soma ginin asibitin sa a Gaya, wanda ba ido kawai za a dinga dubawa ba. Don haka ya debo kwararru daga fannonin da Kulsum ke so su bada taimakon su, musamman 'obstetrics and gynaecologists'. Da taimakon Maimartaba Sarkin Gaya III tangamemen asibitin ya kammala cikin dan lokaci kalilan. Wanda Turaki ya sanya wa suna GAYA SPECIALISTS HOSPITAL. Asibiti ne na lalurorin mata da haihuwa da cututtukan kananan yara, sannan da matsalolin da suka shafi ido, wanda ya samu lasisi daga hukumar lafiya ta kasa. A kyauta ake duba marassa lafiya, magunguna kadai za su saya, domin akwai hannun gwamnati a cikin sa. Kulsum ta hada kudaden ta da ta dade tana tarawa da dan aikin 'part-time' da ta yi a U.K ta biya wa Baban ta Malam Hadi hajji shi da Baffa, sai Turaki ya biya wa Goggo da Umma da yayar sa Hadiza, suka tashi gabadaya zuwa kasa mai tsarki. A wannan tafiya Kulsum ta sha addu'a daga mahaifin ta da kakannin ta, wadanda dukkan burinsu a duniya bai wuce ingantuwar rayuwar ta ba, da dorewar ta cikin zaman lafiya a gidan auren ta. Ta yi burin dora 'course' a kan 'perioperative' bayan dawowar su Gaya, amma laulayin ciki na uku ya hana ta. Sannan ba za ta iya tafiya Yola shekara guda ta bar Turaki ba shi ya sa ta tsaya haikan a kan asibitin su a matsayin 'Chief of Nurses'. Sun tarar da rasuwar Fulani kakar su Turaki watanni kadan kafin dawowar su. Gudunmuwar Dr. Abubakar Turaki Gaya ga kiwon lafiya bai tsaya a garin su Gaya kadai ba, ana daukar sa hayar aiki a fannin sa na 'Ophthalmology' a manyan asibitocin idon nan na 'European Union' da ke Lagos, asibitoci masu zaman kansu da manyan Asibitocin gwamnati. Duk inda Turaki ya je ya yi aiki garin su Gaya yake dawowa cikin iyalinsa bai yi gida a kowanne gari cikin maraya ba. Kulsum ta zauna ta yi tunanin ya kamata ta fito duniya ta yi 'creating awareness' ga mata 'yan uwan ta masu fama da lalurar fitsarin kwance, domin da yawan wadannan mata, wadanda mostly suna gidajen aure, ko gaban iyayen su sabida zaman aure ya gagare su, a kan su fito su nemi 'medical help' a kan lalurar 'ENURESIS'. Yanzu zamani ya zo da sauyi na ci gaba da babu irin lalurar da ba a magancewa a asibiti, maimakon su zauna cikin bakin cikin rayuwa. Ta kuma yi kira ga maza kan su taimaka su kuma tausaya wa matan su masu lalurar fitsarin kwance. Nuna kyama da wulakanci a gare su ko rabuwa da su babban kalubale ne ga rayuwar su. Hakan zai jefa rayuwarsu cikin 'risk' na kamuwa da depression, self-hatred da inferiority complex, wani lokacin har ya jawo tunanin kashe kai, wato (suicidal thought) ga masu raunin imani. Ta tattauna da mijin ta uban 'ya'yan ta Dr. Abubakar Turaki kan kudirin ta. Shi kuma ya ba ta goyon baya dari bisa dari. Ta soma gabatar da makalar a media (talabijin da radiyo) a manyan tasoshi da taimakon Turaki. Lakcoci ne ta ke gabatarwa masu taken 'Enuresis in Adults; A way out in the medical profession'(fitsarin kwance ga manya; mafitar sa a fannin kiwon lafiya). A wata makalar kuma ta ce 'Psychological Trauma of Noctural Enuresis; ta kawo bayanin yadda mata da yawa ke fama da shi a gidan aure. Yadda maza ke 'treating' dinsu da kyama, hantara, wulakanci da raini, ta yi kira ga masu fama da wannan lalura kan cewa lokaci ya yi da ya kamata su san cewa fitsarin kwance ba shi ne karshen rayuwar su ba. Su mike su nemi magani, don tsira da martabar su a gidan aure. Tun daga lokacin da aka fara sakin lakcocin Kulsum a 'social media' ta fara karbar kira daga mata daban-daban inda suke tabbatar mata halin da suke ciki kenan, da yanayin zaman su da mazajen su. Kulsum in ta ji wani abun, ta tuno Turaki da nasa kalar 'treatment' din a gare ta, sai kuka ya kwace mata. Ta kara godewa Ubangijin ta, ta amince Turaki daya ne cikin dubu, kuma Ubangiji ya so ta da rahma ne da ya nufe ta da dawowa hannun sa. ***** Baffa ne ba ya jin dadi, ta yi masa girki na musamman ta zuba yaran a mota suka tafi don su duba shi. Goggo da Baffa wadanda tsufa ya dada kama su, amma shar suke cike da koshin lafiya sabida kulawar da suke samu daga Kulsumu da Turaki, suka shiga ina suka saka-ina-suka-aje da tattaba kunnensu masu kiriniya. Iftihal ta yi tsalle ta haye wuyan Baffa tana fadin, "Baffan Goggo ka yi min doki irin wanda Baba na yake mana". Kulsum ta mako ta a fusace tana fadin, "Sai kin karya min Baffa na? Ki je Baban naki ya yi miki amma wannan Kakana ne". Iftihal ta bare bakin shagwabar ta tana kuka, Baffa ya jawo ta jikin sa yana rarrashin ta. "Kyale Mama, ni ma ba Baban ta ba ne, Baban ta yana 'Yalleman". Goggo kuwa ta hau yi wa Kulsumu fadan saurin duka irin nata, fada ta ke, "Ke wa ya doke ki? Akwai wanda ya kai ki hawa jikin mutane?" Kulsum murmushi ta ke tana zubo wa Baffa dafuwar hanta da ganyen alayyahu da ta kawo masa a faranti ta mika masa, ta zuba wa Goggo tana fadin, "Ku ci sosai ku murmure, umarah za ku koma sati mai zuwa, a can za ku yi azumi gabadaya". Baffa sai ya kasa cin abincin don farin ciki, a rayuwar sa ba abinda ya ke so irin zuwa Makkah, ya dinga sanyawa Kulsum albarka, ba ya taba gajiya da ganin sa gaban dakin Ka'abah mai alfarma. Washegari kuma 'Yalleman suka tafi, boot din motar su shake da buhunhunan kayan abinci da kayan masarufi. Direban Turaki ne ke jan su kasancewar Turaki ba ya gari, ya je wani aiki a AKTH. Malam Hadi ya tarbi 'yan jikokin sa cike da farin cikin ganin su, Lami sai hidima ta ke da su don yanzu tsakanin ta da Kulsum biyayya ce irin ta ubangida da yaron sa, ta yarda Allah ya gama daukakata a kan 'ya'yan ta, kuma ita ce marufar asirin su. Ta gaya wa Malam Hadi sakon Turaki cewa, su samu wani gidan aro su koma sati mai zuwa za a zo a rushe gidan a yi musu ginin zamani. Malam Hadi ya ce, "Kulsumu kina dora wa mijin ki hidimar mu, wadda na tabbatar ta fi karfin aljihun sa, a kan me? Gini fa Kulsumu! Ni ai gidan nan ya ishe ni a hakan da yake in ganganda in karashe ‘yar ragowar rayuwa ta, hidimar da ku ke mana kuwa Allah ne zai saka muku. Addu'o'in mu gare ku ba za su taba yankewa ba". Kulsum ta yi murmushi, ta ce, "Baba, duk abin da ka ji ya ce zai yi, to zai iya ne. Burin mu shi ne ku kasance cikin farin ciki ku yi ta sanya mana albarka". Lokacin da suka dawo Gaya yamma ta yi sosai. Tun a harabar gidan ta ga motar Turaki a ma'adanar adana motocin sa, tabbacin ya dawo kenan daga Kano. Wani sanyi ya ratsa zuciyar ta. Kwanaki biyun da ba su sanya juna a idanun su ba, tamkar shekaru biyu suke ganin su. Batulu da Iftihal suka bude motar suka fice da gudu suna fadin. "Our Daddy is back..." (Baban mu ya dawo). A falon suka tadda shi, yana tsaye yana waya sanye cikin kaftan na danyar farar shadda ga sajen nan nasa ya kwanta luf a saman fuskar sa ma'abociyar zati da kamala. "Kullum girma ya ke, shekarun sa turawa suke, amma kamar kullum kara masa kuruciya ake!" Kulsum ta fada a zuciyar ta. Ya suri yaran su duka biyu a hannayen sa hagu da dama yana fadin, "Ina Mummy ta kwashe min ku ta kai ku na dawo babu kowa a gidan?" Batulu sarkin magana ta ce, "Ai 'Yalleman muka je, Grandpa yana gaishe ka". Dariya ya yi ya ce, "To in ce kun kawo min tsarabar 'Yalleman?" Iftihal ta mika masa katuwar gorubar da ke dunkule a hannun ta. Ya sumbaci goshin yarinyar ya ce, "Dadi na da Ifty babu rowa, Batulu ke ina taki?" Ta shagwabe fuska ta ce, "Daddy na cinye, na yada kwallon". Ita ma ya sumbace ta a kumatu ya ce yana kokarin sauke su kasa, "Maza ku je Baba Laraba ta yi muku wanka ku huta, a bar ni in gaisa da Mummy sosai". "I missed you Prince...". Ta fada tana sakalo hannayen ta ta saman wuyan sa. Kallon ta yake kamar yau ya soma ganin ta. Kullum Kulsum (sweet 16) ta ke kara komawa a idanun sa. Kulsumun da ta dusar da hasken sauran mata daga idanun sa, ta cike masa gurbin da mata hudu da kwarkwarori goma, ba za su iya cike masa ba. Kulsumun da ta dauke kuruciyar sa ta ci gaba da gwagwarmaya da shi a shekarun girman sa. Kulsumun da ba zai iya hadawa da kowacce mace ya yi adalci ba... Kulsumun da yake fata har a aljanna Allah ya tashe su tare, matsayin shugabar duka hurul-eenin'sa!. Daukanta ya yi gabadaya yana tafiya da ita a hannunsa zuwa katafaren dakin barcin su. A lokaci guda yana gaya mata kalaman da suka fi karfin biro na ya rubuta. Wannan shi ne labarin KULSUM,....UMMUKULSUM ABDULHADI 'YALLEMAN. Karshensa kenan ba shi da littafi na hudu. Masha Allah laquwwata illa billah!!! Kuskuren da ke ciki, ku taya ni rokon Allah ya yafe min. Alkhairin da ke ciki, Allah ya raba mana ladan ni da ku bakidaya. Sai mun hadu a sabon littafina. YI WA KAI HISABI!!! Tuna sunan; YI WA KAI HISABI!!! YI WA KAI HISABI!!! Shima zai zo muku complete insha Allah nan ba da jimawa ba. And I promised you a thrilled reading ! SUMAYYA ABDULKADIR TAKORI ke cewa. "Da fatan watarana Allah ya hada mu cikin ALHERInSa, amin". Ga masu bukatar tsofaffin littatafaina softcopies ko hardcopies ku tuntubeni a 07030137870 (whtsp only). Downloaded From https://tknovels.com.ng