Downloaded From https://tknovels.com.ng [5/27, 11:32 AM] Sadiya Abdulrazak: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FTn1qlcoa83BAlCQEO7ZpH *IYA RUWA...!* (FID DA KAI) BY SADIYA ABDULRAZAƘ *First Class Writers* Page 1 Yayin da tsinken agogo ya harba ƙarfe ɗaya na dare cif a daidai lokacin Safiyya take safa da marwa a madaidaicin falonta cikin shirin kayan bacci, matashiya ce wacce auren wuri ya sa dole ka kira ta da yarinyar mace, ƙara kallon agogo ta yi a karo na babu adadi, kafin ta shiga ɗakin gado ta tofe yaranta biyu da ke sharara bacci da addu'a, hijjabi ta saka har ƙasa ta fita zuciyarta cike da fargabar yau kuma wane sabon shafin ne zai buɗe cikin littafin sauyin hali da mijinta ya siyo kullum yake biya mata shi, tsayawa ta yi a tsakar gidan tana kallon ko'ina kamar mai neman wani abu, sannan ta sauke ajiyar zuciya ta doshi ɗakin da yake mallakin mijin nata ta fara ƙwanƙwasawa tare da sallama. Kamar yana jiran zuwan nata, cikin muryar da ke nuna ya fusata ya ce"Wane kuma cikin daren nan!?". Ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, sai da ta ajiye hijjabin ta zauna sannan ta aro murmushi ta ɗora a fuskarta da sanyin murya ta ce"Abban Ni'ima wane ne zai shigo maka ɗaki da tsohon daren nan idan ba matarka ba?" Ya ɗauke kai yana haɗe gira, sannan ya ajiye wayar dake hannunsa, ya janyo babbar wayarsa ta aiki ya fara taɓe-taɓe, suka yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce"Aiki kake yi ne?" "Aiki nake mene ne?" Ya faɗa ba tare da ya kalle ta ba. Ta ce"Idan editing ne sai na taya ka ai, na ga dare ya yi, Abban Ni'ima kai ta matse kanka da aiki, ka fita tun safe kana can kana aiki, dare ma kuma ba za ka huta ba?" Kamar mai jira, sai ya rufe wayar ya ce"Safiyya ke da 'ya'yanki ba tun safe kuke cin abinci ba har dare? Ko kuna hutawa? Kin ga ba na so fa ki dinga ƙure ni, kar ki kai ni bango!". Ta ce"Allah Ya huci zuciyarka, ni ban faɗa da wata manufa ba". Sannan ta shiga banɗakin da ke cikin ɗakin ta yi alwala ta yi sallah raka'a biyu, ta hau katifa ta kwanta, sai dai sam babu bacci a idonta sai saƙa da warwara da ta yi ta yi a zuciyarta, ba ta wani jima a kwance ba ta ga ya matsar da wayar ya ɗakko ɗaya wayar wacce ita ce yake chart da sauran abubuwa, da alama chart yake yi domin ta ga yana ta rubutu da murmushi a fuskarsa. Har ya gama ya ajiye wayar, ya zo ya kwanta a gefenta bacci ya kwashe shi ita ba ta runtsa ba, tunanin sauyin da ya ƙi yarda da ya sauya ɗin take yi, daga shi sai 'ya'yan da Allah Ya ba su take jin sanyi a tare da su, idan rayuwar auren su ta ci gaba da tafiya a haka tana da tabbacin watan shiga ƙuncinta ya kama, wanda babu mai share mata hawaye sai shi amma ace yau shi yake son saka ta hawayen? Tabbas ruwa ba ya tsami banza. Washegari bayan ta yi sallar asuba ta koma ɗakinta bisa al'ada, ƙarfe bakwai da rabi ta kammala abin da za su ci, saboda Abban Ni'ima ƙarfe takwas yake fita, su na zaune a falo ita da yaran suna jiran shigowar shi, domin sun saba a tare suke cin abincin, ya ɗaga labule ya leƙo cikin shirin fita, ya musu kallo ɗaya ya fice, ba ta yi zaton gidan zai bari ba, sai da ta ji tashin babur ɗinsa, ta haɗiyi wani yawu mai ɗaci, kafin ta ɗauki waya ta kira shi, amma bai ɗauka ba, abincin suka fara ci, Ni'ima ƴar shekara huɗu ta tambaye ta "Yau ban da Abba?" Ta ce"Ya ci na shi kuna bacci". Ta gama duk aikin gidan wajen ƙarfe goma tana kwance tana duba wayarta, saƙon shi ya shigo, ta buɗe sai ta ga gargaɗi ne yake yi mata a kan kada ta sake kiran shi alhali ta san yana kan abun hawa, ko so take yi ya yi hatsari? Murmushi kawai ta yi ta ci gaba da harkokinta, da wannan tunanin sauyin na shi ta wuni, a da tare suke karin safe yana ba wa ƴaƴan shi a baki cike da nishaɗi, ya yi musu kyakkyawar sallama bayan sun tsayar da abin da za a girka daga rana zuwa dare, sai ta faɗi abin da take buƙata na cefane, shi kuma zai sa a kawo mata, dab da magriba yake dawowa daga kasuwa, idan ya yi sallah ya ci abinci daga masallaci gidan mahaifiyarsa yake wucewa, inda ƙarfe takwas da rabi ta yi ya dawo gida, wataran ma ana idar da sallar isha'i, idan yara ba su yi bacci ba sai a yi ta wasa da su, idan sun yi bacci sai su yi firar su, idan yana da editing ya ɗauko waya ya yi ta tsara hotunan atamfa, less, shadda da sauran su, kasancewar sana'arsa kenan a kasuwa, da ganin yadda yake yi kullum ita ma ta koya, wataran yana ba ta ta taya shi, daga nan kuma sai su kwanta bacci. A tsarin gidan ɗakuna ne guda huɗu wadatattu sai kitchen da banɗaki, ɗakin da take ciki ciki da falo ne, sai wani fallen ɗakin da banɗaki a cikinsa, kusa da shi akwai kitchen da banɗakin tsakar gida, sannan ɗakinsa shi ma falle ɗaya ne da banɗaki a ciki, akwai katifa da ƴan tsirarun kayansa a ɗakinsa, amma ba ya kwana a ciki a ɗakinta suke kwana tare, sai da ya fara nuna mata wannan canjin ne ya kwashe duka kayansa ya koma nashi ɗakin, sosai ta shiga damuwa saboda ba ta son barin yaranta su kwana su biyu a ɗaki, duka-duka Ni'ima ce mai shekara huɗu, Khausar biyu, amma da ya nuna dole sai dai ta zaɓi ɗaya ko shi ko ƴaƴanta sai ta zaɓe shi saboda a zauna lafiya. Da daddare haka ta yi ta zaman jiran shi, sai ƙarfe goma da rabi ya dawo, wani abu da bai taɓa yi ba sai da babban dalili kuma bayyananne, a lokacin da ya shigo tana ɗakinsa a zaune, saboda yau ɗin ta shirya tunkararsa don jin laifinta a gare shi. Sautin dariyarsa ta ji yana cewa"Kin ga yanzu dai na shigo gida, idan wannan matar ba ta shigo min ba zan kira ki, sai ki ƙarasa mini ko?" Ya ƙarashe maganar cikin wata matacciyar muryar da ya jima bai yi mata irinta ba. 'Wannan matar!' Ta jinjina kalmar a zuciyarta, lallai ba a shaidar miji, baban Ni'ima da wataran idan ta ci kwalliya har ɗaukarta yake yi ya juya yana ce mata ƴar budurwarsa ko ya ce mata Babynsa, har ce mata yake yi shekara biyar da aurensu amma gani yake kamar har yau ita budurwa ce, ta ƙi ta girma, shi ne yau yake kiran ta da kalmar matar nan? Lallai akwai matsala. "Baby ke fa na lura sam ba kya so na yi bacci, yanzu bayan auren ma haka za kina yi mini wannan dabaibayin duk ki kashe mini jiki ki hana ni aiki ko...?" Bai ƙarasa ba, wayar ta suɓuce ta faɗi, sakamakon ƙarasa shigowa ɗakin da ya yi, suka yi ido huɗu. "A'uzubillahi! Subhanallah! Haba Safiyya wannan wane irin rashin mutunci ne haka za ki firgita ni? Ko gyaran murya ai sai ki yi na san da mutum a ɗakin, wannan ai wulaƙanci ne!" Ya ƙarasa maganar yana ɗaukar wayar ya yi kicin-kicin da fuska. Ta yi jarumtar danne hawayeta, ta ƙirƙiri murmushin takaici ta ce"Ka yi haƙuri, kuma ni dai ban ga wani abun firgita ba har da yar da waya, sai dai idan dama dai a firgicen kake". Sai kuwa ya zaburo"Ni kike cewa a firgice? Kina nufin ni mahaukaci ne fa kenan! Bantan ubancan ni da gidana ki ce mini mahaukaci? A lallai Safiyya na yarda halinki ya canza". Ta ce"Duka dai magana ta ƙare, ga abincinka nan". A fusace ya ce"Ba zan ci ba! Kuma daga yau kar ki sake shigo mini ɗaki sai idan ni na neme ki" Ta ce"To in sha Allah! Amma ina so mu yi magana kafin na tafin". Ya zauna bai ce komai ba. Sai ta fara hawayen da take ta dannewa, ta ce"Abban Ni'ima me na yi maka ka canza mini? Gabaɗaya kana nema ka juya mini baya, ka daina ba ni kulawar da ka sabar mini da ita, hatta yaranka ka fara janye jikinka daga garesu, alhali ka san ni da su ɗin ba mu da wanda ya fi ka a duniyar nan, wannan sauyin naka ba ƙaramin barazana ba ne ga rayuwarmu, don Allah ka ƙaryata hasashena kar ka rabu da ni saboda wani dalili ko laifin da ban san ina aikatawa ba". Shiru ya yi kamar ba zai ce komai ba, har tsawon lokaci ita kuma tana kuka mai shassheka, sannan ya ce"Tun da kina son jin dalili to za ki ji in sha Allah, gobe idan Allah Ya kai mu su Yaya Fa'iza za su zo, su za su faɗa miki komai". Daga haka ya shige banɗaki, ita kuma ta tashi ta koma ɗakinta, ta zauna tana ta tunanin sabuwar rayuwar da take shirin tunkaro ta, daga wayar da ta ji yana yi tabbas ta san wata macen ce ta bankaɗa labulen rayuwarsu take son shigowa, ita dai ba za ta ga laifinsa ba don ya ƙara aure idan hakan ya tabbata amma wannan sauyin nashi ne babbar damuwarta, domin alama ce dake nuna idan an yi auren ba lallai a wanye lafiya ba, ita kuwa barinta gidan aurenta tamkar tonon asiri ne a gare ta, to ina za ta nufa idan ta bar gidan? Da wannan tunanin ta kwana, tana fargabar wayewar gari saboda zuwan ƴan'uwan mijin nata da ta tabbata ba ƙaunarta suke yi ba. Bayan sallar la'asar ta gama aikinta tsaf ta yi kwalliyarta mai haske, tana ɗan duba wayarta suna fira da yaranta jifa-jifa, ta ji sallamar ƴan'uwan mijin, gabanta ya faɗi har sai da ta dafe ƙirjinta, sai da ta haɗiyi wani yawu sannan ta je ta buɗe musu ƙofa, dukan su da yayyunsa da ƙannensa su shida cif, bayan sun gaisa yayarsa Fa'iza wacce ta fi kowa zafi da tsanarta ta miƙo mata ɗan ƙaramin kwalin cingam ta ce"To Safiyya Allah Ya kawo abin da muke ta jira!". Mariya ƙanwarsa ta ce"Ƙwarai kuwa lokaci ba na mutuwa ba, na tsantsar farincikin samun ƙaruwa". Ta karɓi cingam ɗin tana rarraba ido da alamar neman ƙarin bayani. Fa'iza ta ce"Cingam ɗin saka ranar auren mijinki ne, an ɗan jima fa da saka ranar ma shi ya ce kar a faɗa miki, ga shi abu har ya matso saura sati huɗu in sha Allah!". Ƙirjinta ya yi wata irin bugawa da ƙarfi, ta daure ta ce"To Allah Ya kaimu, ya kuma sanya alkhairi". Suka amsa da amin, sannan suka shiga firar budurwar, a yadda ta fahimta Anti Saude ce ta haɗa shi da ita, har hotonta suka kunno suna ta yabonta, ita dai kamar ta ce su nuna mata, sai dai ta yi shiru har suka tafi, suka barta cikin wani irin yanayi. A halittarta ba mace ba ce mai zafin kishi, tana jin ko mata nawa zai auro za su zauna lafiya matuƙar dai ba zai tauye mata haƙƙinta ba, ko a yanzun ma ba auren ne damuwarta ba, sauyin halinsa ne kaɗai ya dame ta. Da daddare bai shigo gidan da wuri ba, sai sha biyu, tana ɗakinta tana jiran shi, duk da baccin da yake neman kwantar da ita, tana jin shigowarsa ta fito tsaye ta yi a ƙofar ɗaki tana hango shi yana saka sakata. "Safiyya me ya hana ki bacci?" Ya tambaye ta yana shirin shigewa ɗaki. Sai ta bi bayansa tana faɗin"Ta ya zan yi bacci ban jira ka shigo na ga ka ci abincinka ba?" Ya yi dariya ya ce"Haba dai abinci yanzu sai ka ce dai mai yin sahur? Idan kika ga na wuce ƙarfe tara a waje idan na dawo ba ma sai kin yi mini tayin abinci ba, indai zan je gidan su yarinyar nan ba ta rasa cika min ciki da abubuwa". "Yarinya?" Ta tambaya duk da ta san abin da yake nufi. "Zancen kike so Safiyya, sai da safe". Ya faɗa zai shige ɗakin. Ta yi saurin ƙarasawa ta ce"Ai bayan wannan ma har da maganar da nake so mu yi". Ya ce"Tsakar daren nan sai ka ce wasu aljannu? Ai sai mu bar wa safiya ko?" "Yanzu nake so!" Ta faɗa a ɗan hasale. Ya ce"Da dai ba kya yi mini musu". Ya shiga ɗakin, ta mara basa baya. Bayan sun zauna ta ce"Jiya na tambaye ka dalilin canjin halayenka, sai ka ce mini yau su Yaya za su zo..." "Ba su zo ba?" Ya katse ta. Ta ce"Sun zo, amma maganar da suka zo da ita ba ta da nasaba da tambayar da na yi maka". Ya ce"Ikon Allah! Ba su faɗa miki zan yi aure ba?" Ta ce"Sun faɗa mini, amma me ya haɗa ƙarin aurenka da zamanmu? Me ya haɗa ƙarin aurenka da canzawar halinka? Idan za a ƙara auren juyawa ta gida baya ake yi, a banzatar da 'ya'ya? Idan za a yi sabo sai a jefar da tsoho tun kafin sabon ya shigo hannu a tabbatar da ingancinsa? Ka ba ni tsoro, na fara tunanin anya kuwa za ka yi adalci a tsakaninmu?" A hasale ya nuna mata ƙofa ya ce"Tashi ki fita! Na ce idan kin gama zagina ta shi ki fita, Safiyya har ni yau za ki ce ba ni da adalci dama jiya kin ce mini a rikice nake ba ni da hankali? To an barzatar da ku ɗin, sai ki ɗauki mataki!". Ta ce"Baban Ni'ima babu buƙatar tsayawa yi maka bayanin ba haka nake nufi ba, domin ka fi kowa sanin halina, ka san abin da zan yi da wanda ba zan yi ba, na gode da komai, aure kuma Allah Ya nuna mana lokaci, ya kuma ba ku zaman lafiya. Ta yi murmushin da ya fi kuka ciwo ta tashi ta bar ɗakin, tana tunanin ta inda za ta fara toshe wannan ɓarakar da ta shigo rayuwarsu babu zato. Tun daga ranar bai sake cin abincinta ba tsakaninta da shi ta gan shi da safe su gaisa, wataran ma ba ta ganin ficewarsa da daddare kuma ko ta ji dawowarsa ba ta fitowa, tu rungumi yaranta su yi bacci lafiya, har tsawon sati biyu, a lokacin bikin ya rage sati biyu kenan. Ya ɗin tana son yi masa zancen makarantar Ni'ima da yake ta cewa za a kaita, shi yasa ta jira shi har ya dawo ƙarfe goma da rabi, yana shiga ɗaki ta ƙwanƙwasa tare da sallama, ba ta jira amsawar shi ba ta tura ta shiga, tsaye ta same shi yana ta danna waya, ta zauna ta ce"Sannu". Ya juyo ya ce"Ciwo nake? Ke ma sannu!". Ta yi murmushi ta ce"Dama magana nake so mu yi, akan makarantar Ni'ima, ka ga wannan hutun za a ɗauki sababbin ɗalibai, ya kamata a kai ta". Ya ce"Wai Ni'ima nawa take da za ki matsa a kai ta makaranta? Ki bari sai wata shekarar kawai". Ta ce"Shekararta huɗu fa, ƴan shekara uku ma ana kai su, ba na son zamanta haka, don Allah a kaita". "Ni dai na ce sai wata shekarar, idan kuma kin ga za ki iya to ki kai ta, ko kin manta aure zan yi nan da sati biyu ina ta shirin hidima kuma ki kawo min zancen Ni'ima da makaranta?" Ya faɗa yana kwamciya. Ranta ya ɓaci ta ce"To shi kenan, Allah Ya kaimu wata shekarar". Tana shirin fita ya ce"Idan Allah Ya kaimu gobe za ki yi baƙi". "Baƙi?" Ta tambaya da ɗan mamaki Ya ce"E wallahi, yarinyar nan ce za ta zo za ta ga yanayin gidan, tun da a nan zan ajiye ta, sai ta duba ɗakunan a san yadda za a tsara zaman". Kai tsaye ta ce"Ɗakuna ai a tsare suke, ni dai ka san inda nake ciki da falo ne, sai naka, sai kuma idan wancen ɗayan za ka ba ta ai ko?" Ya ce"E to! Sai ta zo ɗin tukunna, za ta duba har nakin a gani!". Ta ce"Abban Ni'ima iya ƙoƙarina na kau da kai a kan lamarin aurenka, don girman Allah kada ka ƙure ni, ta ya za a ce buduruwarka ta zo har cikin ɗakina wai ta zo duba yanayin gida? To ban amince ba, kar ta sake ta zo min, ku tsaya a iya inda za ka ba ta!". "Za ta zo!" Ya faɗa ko a jikinsa. "Ba za ta zo ba!" Ta faɗa a fusace. Ya ce"To Allah Ya kai mu goben, zan ga waye mai gidan tsakanin ni da ke". Daga haka ta koma ɗaki ta kwanta, zuciyarta tana mata zafi, ta kuma ƙuduri niyyar babu wata yarinyar da za ta shigo duba mata ɗaki. [5/27, 11:32 AM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA...!* (FID DA KAI) BY SADIYA ABDULRAZAƘ *First Class Writers* Page 2 Washegari da safe suna cikin karyawa ita da yara, ya shigo ɗakin ya zauna, tuni ta daina girki da shi, saboda ko ta yi asarar shi ake yi, bayan ta gaishe shi ta tura masa plate ɗin indomin da take ci tare da kofin shayi, ya ɗauki kofin ya kurɓi shayin ya ajiye ya yi gyaran murya ya ce"Safiyya ya muke ciki?" Ta ce"Da me fa?" Ya ce"Maganar zuwan ƙanwar taki dai". Ta yi murmushi ta ce"Baban Ni'ima na ce maka babu yadda zai yiwu buduruwarka ta shigar min ɗaki". Ya ce"Amma kin san nan gidana ne ko? Don haka ina da ikon shigo da duk wanda na yi niyya!" Ba ta so a ja maganar har ta zama babbar rigima, don haka ta yi shiru, ya ce"Yawwa! Bayan sallar la'asar ƙawarta za ta rako ta, me za ki dafa a kawo cefane?" Ta ce"Duk abin da ka zaɓa shi zan dafa". Ya ce"To zan aiko, ko ke fa amma da kin tsaya kina wani cijewa ke ba tsohon babur ba? Ki saki ranki don Allah, idan ban da abunki kwana nawa ne ma za ta shigo gidan ku zama abu ɗaya? Ni gidana na zaman lafiya ne babu zancen fitina in dai kin so". Har ya gama ya fice ba ta sake cewa komai ba, ƙarfe sha ɗaya ya aiko da cefane, kayan miya mai uban yawa kamar za a yi girkin sabga, da manyan kaji har guda uku ga kuma jan nama da yawa, kwakwa ƙwallo da madarar gwangwani, ta yi murmushi bayan ta gama gani, ta hau aiki, soye kajin ta yi tsaf ta kwashi rabi ta yi jar miya ta zuba su, jan nama kuwa ta soya ta kai ɗakinta ta adana, ta dafa farar shinkafa, ta ɗibi kwakwar ta yi lemo ta zuba sauran a firji, ta haɗa komai ta kai ɗakinsa ta ajiye, sannan ta tura yaranta gidan maƙociyarta Maman Affan, ta fita ta siyo sabon kwaɗo guda biyu, ta zo ta rufe ƙofar ɗakinta ta rufe kitchen, ta zuba sauran abincin a kula ta tafi gidan Maman Affan ɗin. Sun baje suna cin abinci Maman Affan ta ce"Wai wannan uban kajin fa Maman Ni'ima?" Ta yi dariya ta ce"Albarkacin kaza ƙadangare ya sha ruwan kasko". Maman Affan ta ce"Don Allah ki min bayani, yaushe rabon da ki yi irin drink ɗin nan". Da murmushi ta ce"Baƙi za a yi a gidan, nasu kason yana can na zuba musu, sai la'asar za su ƙaraso". Ta ce"Kuma za ki yi baƙin shi ne kika fito kika baje a nan? Su waye za su zo?" Sai da ta shanye lemon ta ajiye kofin sannan ta gyara zama ta ce"Buduruwar baban Ni'ima ce za ta zo ganin inda zai ajiye ta bayan auren". Kafin ka ce kwabo Maman Affan ta ƙware da lemo, ta shiga tari babu ƙaƙƙautawa, abun ya ba wa Safiyya dariya, don ta san Maman Affan da kishin masifa, ta danƙo hannunta tana zazzare ido ta ce"Da gaske ko da wasa?" Safiyya ta yi murmushin yaƙe ta ce"Wallahi da gaske nake Maman Affan, baban Ni'ima aure zai yi zancen da nake yi miki ma saura sati biyi bikin, yau za ta zo ta ga yanayin gidan wai". Maman Affan ta buga kofin hannunta da ƙasa har ya fashe, a fusace ta ce"Da gaske ita kika yi wa girkin nan kuma?" Safiyya ta ce"Su na yi wa!". Sai ta ƙura mata ido na ƴan sakanni, ta ce"Kenan kina maraba da zuwan nata ko dai taku ne? Ko guba kika zuba a cikin abincin?" Safiyya ta yi dariya ta ce"Ke dai Allah Ya yaye miki wannan masifar kishin, ina ni ina zubawa mutum guba a abinci? Ya ce na yi girkin ya zan yi? Ta zo ta ga gida, amma na kulle ɗakina da kitchen ɗina, tun da nan ba huruminta ba ne". Maman Affan ta jijjiga kai ta ce"Kar Allah Ya kawo ranar da mijina zai yi aure, don wallahi ba ƙaramar ta'asa za a yi ba, na tsani jin kalmar kishiya, ke kam Allah Ya miki baiwar haƙuri, wallahi da ni ce da tuni na gama haɗa kayan aikina ina jiran zuwan su, don wallahi shigo-shigo babu zurfi zan yi musu, sai na tara su a ɗaki na fara hauka tuburan na bi duk na ragargaje ƙafafun shegu!" Safiyya ta yi dariya ta ce"Ke dai Allah Ya yaye miki kishi, babu ruwana da su, yadda yake rawar kan nan idan na dage komai zai iya faruwa, idan ya sake ni ina na kama? Ke kuwa kina da gatanki, wani abun mai uwa a raye ne yake yi". Maman Affan ta ce"Haba Maman Ni'ima, ke ma da gatanki muddin kin riƙe Allah, kada ma ki saka a ranki namiji ne gatanki, don za ki ga wulaƙanci kala-kala, ki dogara da Allah ki tsaya da ƙafafunki, yanzu rayuwar ta zama iya ruwa fid da kai, ita kuwa kishiya muddin kika sake mata wallahi rana za ta kai ki! Gidanki ne fa, ita ya kamata ta dinga fargabar shigowa ba ke za ki yi fargabar zuwanta ba". Safiyya ta yi ajiyar zuciya ba dan ta gamsu ba, ta ce"To Allah Ya kawo komai da sauƙi dai". Ba ta son faɗa mata canjin da suke fuskanta da mijin nata, saboda ba su saba irin firar ba, sam babu wani saɓani ma da yake haɗa su da shi ɗin sai yanzun da ya tashi auren, haka suka ci gaba da firar su har aka kira sallar la'asar. Katangarsu ɗaya da Maman Affan, shi yasa indai aka taɓa ƙofar gidanta sai ta jiyo ƙara, suna zaune a sallaya suna ƙara tattaunawa suka ji ana buga gidan Safiyyan, Maman Affan ta ce"To ko dai sun ƙaraso?" Ba ta jira amsa ba ta tashi ta je ta leƙa, ta dawo tana huci ta ce"Wallahi su ne, ga manyan mata nan su biyu da ƴan'mata biyu, ɗayar har da niƙab ɗin gulma ina ga shegiyar ce". Gaban Safiyya ya dinga bugu, da ƙyar ta haɗiyi yawu ta ɗauki mukullin gidan ta miƙawa Maman Affan ta ce"Je ki buɗe musu su shiga". Maman Affan ta tsorata da jin muryar Safiyya tana rawa kamar za ta yi kuka, ta ce"Yau ga mugun abu! Maman Ni'ima ba dai kuka za ki yi wa kishiya ba tun yanzu? A lallai zan sha kallo kenan, tashi mu je na raka ki don ba zan je ni kaɗai ba, ba kuma zan bar ki ki je ke kaɗai ba, su miki duka tun da na lura ke saiwar sala ce". Suka fito ta na ƙoƙarin saita kanta ita ta rufo gidan, saboda Mamam Affan ta yi gaba, tana ce musu"Wa alaikumus salam!" Ganin wata lukutar mata ta zage iya ƙarfinta tana ta buga gidan. Duka suka juyo suna kallon mu, ta yi gaba tana kiciniyar buɗe gidan ta ce"Ai ga ma su gidan nan, sannunku". Babu wanda ya amsa sai bin ta da kallo da suka yi, ta buɗe ta shige, Safiyya ta bi bayanta sannan su ma suka shigo, ta shiga ɗakin da zai zama na amaryar ta shimfiɗa tabarma ta ce"Ku shigo mana, Safiyya kawo musu ruwa da abinci". Ta buɗe ɗakin baban Ni'ima ta ɗakko musu, don ita da a lissafinta can za ta kai su, tun da baƙinsa ne, ta ajiye musu ta yi gefe, Maman Affan ta ce"Ku saki jikinku fa, a ɗakin amaryar kuke". Sannan ta ja hannun Safiyya da ke tsaye kamar ta haɗiyi taɓarya ta yi waje da ita, a barandar ɗakin baban Ni'ima suka zauna babu wanda ya ce da kowa komai, babu jimawa kuma baƙi suka fito. Maman Affan ta ce"To har za ku tafi? Ku gai da gida". Lukutar matat ta coge ta ce"Ina zancen mu gai da gida bayan ba mu yi abin da ya kawo mu ba? Ko ce muku aka yi yunwa muke da za ku ba mu abinci ku ce mu gai da gida?". Safiyya ta ce"Zancen yunwa kuma sai dai ku tambayi mai gidan, tun da shi ne ya yi cefane ya ce a muku girkin, kuma wannan ɗaki da kuka shiga shi ne rabon amaryar ai, shi wannan nawa ne, wancen kuma na mai gida". "Me kuke nufi da rabonta? Kenan a ɗaki ɗaya zai ajiye ta?" Wacce suke zaton ƙawarta ce ta faɗa tana wani jijjiga jiki, ita dai mai niƙab ɗin har yanzu ba ta ce komai ba. Ɗayar matar ta ce"Ai kuwa ba zai taɓa yiwu ba, wai an ba mai kaza ƙafa, yadda muka yi da shi za mu shiga duka ɗakunan gidan mu duba Ameera ta zaɓi wanda ya yi mata a bata, saboda haka ya zama dole a buɗe mana kowane ɗaki mu gani!". "An zo daidai wajen!" Cewar Maman Affan tana rataye hijjabinta a kan igiya, sannan ta ce"Ai kuwa ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, ɗakin mai gidan za ku shiga ku ga sirrin aure ko kuwa ɗakin matar gida za ku shiga ku gane mata sirrinta?" Matar ta ce"Sirrin aure kuma na nawa? Abin da za ta shigo gidan nan da sati biyu kowane sirri zai shigo hannunta? Ita kuma matar gidan har wace tsiyar ce a ɗakin nata da za a gani a faɗa? Bayan kayan ɗakin ma shi ya yi mata!". Tuni idon Safiyya ya kawo ruwa, ta fara karkarwa ta rasa abin cewa. Maman Affan ta ce"Ba kayan ɗaki ba ko shi yake ba ta ci, sha da sutura tun tana zanin goyo ba mu damu ba, domin ƙauna ce ta kawo hakan, kuma an yaba da tarbiyya ne har ƙauna ta shigo ciki, ai wallahi duk wata ƙandararriyar yarinya da Salisu zai so a bayan Safiyya take, kuma sauranta za ta a tarar, ɗaki dai ba za a buɗe ba, saboda haka idan kun gama cin abincin ku yi waje! Wataƙil ya ga yunwar ne shi yasa ya tashi baiwar Allah ta ɗora muku babbar tukunya". Nan fa zagi da gore-gore ya kaure a tsakaninsu, sai ya zama ma faɗa ya bar zancen Safiyya ya dawo kan Maman Affan, aka yi kaca-kaca, ƙarshe dai yarinya mai niƙab ɗin ce ta janye ƴan'uwanta suka bar gidan. Sannan Safiyya ta buɗe ɗakinta suka shiga, Maman Affan ta ɗauki lemo ta kwankwaɗa tana sauke numfashi ta ce"Ɗaya kenan!". Safiyya da damuwa a fuskarta ta ce"Me yasa za ki yi haka?" Ta ce"Au lakwa-lakwa za ki mata kenan ta raina ki tun kafin ta shigo?" Ta ce"Ba haka ba ne, amma yanzu kin san sai sun faɗa masa, kuma ban san matakin da zai ɗauka ba". Ta yi wani murmushi ta ce"Lallai Safiyya za ki sha wuyar zama da kishiya? Kenan gaskiya za ki faɗa masa ki ce an yi hayaniyar! Tab". Nan ta tsara mata komai ta ce kar ta sake ta ce masa an samu wata matsala, da suka duba abincin ma suka ga ko taɓawa ba su yi ba, ga shi da yawa, Safiyya ta ce"Maman Affan kwashi abincin nan kin ga ga wani a kitchen ya yi mana yawa!". Ta ce"Ai mu gaba ta kaimu, yau ba sai na yi girkin dare ba". Da haka ta mata sallama ta tafi, ita kuma ta cire kwaɗon ta ɓoye, tana ta ƙarfafa zuciyarta don kar ya gane abin da ya faru idan ya dawo. Ta idar da sallar magriba, suna zaune da yara tana koya musu karatu suka ji dawowarsa, yaran suka tafi da gudu don tarar shi, saboda ya jima bai dawo da wuri kamar yau ɗin ba, kamar yadda ta yi zato, kai tsaye ɗakinta ya shigo, kallo ɗaya ta yi masa ta san sun tsara masa komai, tana murmushi ta yi masa sannu da zuwa. Yana huci ya ce"Safiyya yau kin nuna min ban isa da gidana ba kenan!" Ta yi alamun mamaki ta ce"Baban Ni'ima mene ne ya faru?" A fusace ya ce"Ni za ki tambaya me ya faru saboda raini? Ya muka yi da ke akan baƙin nan?" Ta ce"Maganar baƙi ai mun daidaita, kuma sun zo sun ga gida sun tafi lafiya ƙalau". "Kar ki raina mini hankali!" Ya faɗa yana mata mugun kallo. Ta ce"Don Allah ka zauna, sai gumi kake dama wanka ka fara yi sai mu yi magana a tsanake". Ya ce"Ruwan kogi na zama ba gumi ba! Saboda wulaƙanci har ke za ki ɗakko hayar wata mata ku haɗu ku ci wa mutane mutunci? Kuma ki kulle ɗakuna ki ce ba za su gani ba, gidanki ne ko nawa?" Ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wannan maganar kuma daga ina?" Sai ya tsaya yana kallonta ya rasa abun cewa, don zuwa yanzu rainin hankalin nata ya fara yawa. Ta ce"Baban Ni'ima ka san halina, inda ban yarda da zuwan su ba ka san da zan tsaya a kan bakana, kuma da ba zan musu girki ba, da gidan zan bari ba za su zo su tarar da ni ba. Nan suka buga ƙofa na buɗe na tare su, suna ta ciccijewa, a ɗakina suka zauna na ba su lemo da abinci suka ci suka ƙoshi, har ma ɗayar matar ta tafi da sauran za ta kai wa yaranta, suka shiga ko'ina suka duba har banɗaki, sannan suka tafi, to ban san me yake faruwa ba kuma". Ya ce"Amma sun ce a wancen ɗakin kawai kika sauke su, kika ƙi buɗe sauran kuma kin ɗakko wata mata har kuna musu gorin abinci". Ta fara matsar ƙwalla ta ce"Shi kenan tun da abun arziƙi ya zama na sharri, amma ka ba ni mamaki da ka yarda, a zatona kai za ka bawa wani labarin abin da zan iya da wanda ba zan iya ba, sai ga shi kai za a faɗawa wani halina, ashe komai na yi da dauriyar da na yi na tare duk ba zan tsira ba, shi yasa nake tsoron kaidin kishiya". Zuwa yanzu shi ma ya yarda ba ta yi ba, fitina ce kawai ta mata, ya ce"To wata mata ce ta zo gidan?" Ta ce"Babu wacce ta zo gidan nan yau, idan ban da Maman Affan da ta leƙo da safe, ka fi kowa sanin da ita kaɗai nake mu'amula a unguwar nan". Ya jinjina kai, tabbas ya san da ita kaɗai take mu'amula, kuma ya yarda da matar ya san ba za ta taɓa aikata abin da Ameera ta faɗa ba. Suka yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta tashi ta kawo masa abinci, ya ce ya ƙoshi. Can kuma ya yi gyaran murya ya ce"Safiyya na rasa yadda zan yi, ɗazu mun yi magana da ƙanwarki ta ce ɗaki ɗaya ba zai ishe ta ba, saboda kin ga ita amarya ce ba zai yiwu kayanta su cinye ɗaki ɗaya ba". Ta ce"To me zai hana ka haɗa mata da naka ɗakin?" Ya ce"Ai yadda na riga na ji daɗin ware ɗakina gaskiya ba zan so na bar shi ba". Ta ce"To ai sai ta yi haƙuri ta haƙura da ɗayan kafin Allah Ya hore maka a samu mafita". Ya ce"Safiyya ke ce babba, kuma kin san an ce babba juji, don haka ke za ki yi haƙuri, ki bata wannan ciki da falon, ke ki koma guda ɗaya, shi kuma kitchen ki kwashe rabin kayanki, don ita ma ta saɓu damar zuba nata". Ta dinga yi masa wani kallo, ta rasa ma abin da za ta ce. Ya ce"Ki yi haƙuri mu rufawa juna asiri". [5/27, 11:32 AM] Sadiya Abdulrazak: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FTn1qlcoa83BAlCQEO7ZpH *IYA RUWA...!* (FID DA KAI) BY SADIYA ABDULRAZAƘ *First Class Writers* Page 3 Har ya fice daga ɗakin ba ta samu zarafin furta masa komai ba, saboda yadda ta ji zuciyarta tana ƙuna ta san ba magana mai daɗi ce za ta fito daga bakinta ba, shi yasa ta bari sai ta huce sai ta san ta yadda za ta masa bayanin da zai fahimta, haka ta kwana tana tunanin lamarin, ta rasa da wa za ta yi shawara, a yadda ta taso tun tana yarinya ba ta da abokin shawara sai shi, ba ta da wanda za ta kai wa kukanta ya share mata hawaye sai shi, kuma shi ɗin ne dai yake saita mata duk wata matsala da ta kutso rayuwarta, to yau ga shi shi ne yake yanko mata matsalar, ina za ta kai kukanta kenan? Washegari da safe tana kitchen ya shigo cikin shirin shi na fita, da yake ta makara yau ɗin, ta gaishe shi ba tare da ta ɗauke ido daga kan doyar da take soyawa ba, ya amsa, sannan ya ja turmi ya zauna ya ce"Safiyya ya aka yi ne, kin gama tunani?" Har yanzu ba ta kalle shi ba ta ce"Ni na ce maka ina tunani?" Ya ce"Ai da na ga jiya ba ki yi magana na, sai na ba ki lokaci ki yi tunani, zancen dai ɗakunan ne, kin ga dama kujerunki sun tsufa ina ta cewa zan canza miki Allah bai yi ba, ni a shawarata kawai ki siyar da su, sai ki zuba kayan gadon a shi ɗakin da za ki koma, idan Allah Ya hore mini na gina wannan filin nawa kin ga sai na sake miki sababbi idan za mu tare ko?" Ya tashi ya fara dudduba kitchen ɗin yana saita shi da hannu, ya ce"Kin ga nan". Ta juyo ta kalle shi daidai lokacin da ta kashe gas ɗin, ya ce"Kin ga daga nan za ki kwashe kin ga an raba daidai kenan, sai ta samu ta raɓa nata ita ma, zan sake buga muku wasu kantocin, wannan lokokin ma ki kwashe kayanki daga ciki su sai su zama store kawai". Ta zuba doya a faranti ta miƙa masa, ya karɓa ya saka ɗaya a baki ya ce"Ai hakan ya yi, ba a cuci kowa ba ko?" Ta yi guntun murmushi ta ce"Ba ka taɓa cuta ta ba ai, ka yi haƙuri baban Ni'ima, ina ga wannan ne karon farko da zan saɓa umarninka tun kafin aurenmu, gaskiya ban amince da wannan tsarin ba, ba zan bar ɗakin da nake ciki ba, kuma ban amince na raba kitchen da kowa ba". Sai ya ajiye farantin ya haɗe gira ya ce"Safiyya ai ba amincewarki na nema ba, ina yi miki bayani ne saboda kina da haƙƙi a kan abun, nan fa gidana ne sai yadda na tsara, kuma dole ki bi matuƙar ba son barin gidan kike yi ba..." "Me kake nufi?" Ta faɗa da wani irin firgici, tuni ƙirjinta ya fara lugude, ba ta taɓa zaton jin kalmar rabuwa daga bakinsa ba, duk da tana kyautata zaton ya tauna tsakuwa ne kawai don aya ta ji tsoro, don tana da yaƙinin shi ma ba zai iya rabuwa da ita ba, kamar yadda ta yardarwa kanta ba za ta iya rayuwa babu shi ba. Maganarsa ta katse mata tunani daidai inda yake cewa"Ƙwarai kuwa! Abin da kika ji shi nake nufi, ba ki san dalilina na ƙara auren nan ba, don haka duk wanda ya yi yunƙurin kawo mini cikas a sha'anin tuni zan rufe ido na tsinke igiyar alaƙarmu ko shi wane ne!". Daga haka ya fita ya bar ta a kitchen ɗin, ta zauna a kan turmi zuciyarta tana mata zafi, ga wani abu mai ciwo da ya cushe mata maƙoshi, gefe guda kuma ta cika da fargabar kalmar rabuwa da ya ambata, Salisun da ya ce ita ce mahaɗin rayuwar shi, har ma yake roƙonta ko ƙaddara ta sa ta auri wani nsa kar ta yanke alaƙa da shi saboda shi yayanta ne, kuma ƴan'uwa ba sa rabuwa yau shi ne yake nuna mata zai iya rabuwa da ita saboda zai yi aure, ita kuwa wannan yarinyar mai suna Ameera da wani laƙanin ta afko rayuwarsu, take shirin ruguza soyayyar ya da ƙanwarsa sahihiya tun ta ƙuruciya? Ta share hawaye ta tashi ta haɗa abincin ta fito don ta sallami yaranta, domin ita ta riga ta yi karinta da baƙinciki. Bayan sallar la'asar Maman Affan ta shigo, kasa jurewa ta yi har sai da ta faɗa mata halin da suke ciki na rabon gidan da za a yi, Maman Affan ta ce mata kar ta sake ta yarda, ita da yara biyu za a bata ɗaki ɗaya wacce ba ta da yara ɗaki biyu? Safiyya ta ce"Tsoro nake kar na dage daga baya na zo ina nadama". Da mamaki ta ce mata"Nadama ta me?" Ta ce"Kar ya rabu da ni, ina fargabar rabuwa da gidan aurena". Maman Affan ta ce"Allah Mai iko! To a gaskiya Safiyya za ki sha wahalar rayuwa, domin muddin kika cewa namiji sai da shi, tamkar kin ba shi sitiyarin farin cikinki ne, haka zai ta juya ki yadda ya so, ban ce kar ki yi wa mijinki biyayya ba fa, kuma ban ce kar ki ji tsoron rabuwa da shi ba, ai mutuwar aure ba ta da daɗi, kawai dai ina nuna miki ke ma kina da ƴanci ne, kuma wasu mazan idan suka ja ke ma kika ja sai ki ga saɓanin tunaninki, a maimakon su rabu da ke ɗin kamar yadda kike zato sai su dawo su nutsu suna tarairaryarki, sai ki ga an zauna lafiya". Safiyya ta ce"Kenan dai yanzu kina nufin na dage na ce ban yarda da rabon ba?" Ta ce"Ƙwarai kuwa, amma fa ba da hayaniya ba, don ba mu san yarinyar nan ta wace siga ta shigo rayuwarku ba, yanzu ki nuna masa ba zai yiwu ba, idan bai yarda ba to ki je gidansu ki faɗawa iyayensa ki ji matakinsu". Ta taɓe baki ta ce"Kin san yadda babarsa take jin haushina kuwa? Babu mamaki ma ita ta tsara komai". Ta ce"To ki tafi gidanku ki faɗawa babanki ki gani". Ta ce"Hmmm! Zan gwada". Da haka suka bar firar suka shiga wata jikinsu duk a sanyaye. Sai da aka yi kwana huɗu bai sake yi mata zancen ba, a lokacin kuma auren ya rage kwana takwas, ta faɗa masa za ta je gida ta kwana biyu ba ta je ba, kuma za ta faɗawa Baba ƙarin auren ta san bai sani ba. Ai kuwa ya ɓata rai ya ce"Au saboda zan yi aure shi ne za ki je ki kai ƙarata kenan! Idan kika yi haƙuri ma ai zan sanar masa, tun da zan kai masa katin gayyata". Ta ce"Ni ba ƙararka zan kai ba, kawai dai zan faɗa masa ne wai ko da nasihar da zai yi mini". Ya ce"Wace nasiha kike nema bayan wacce kike yi wa kanki? Tun da muke da ke ban taɓa ba ki umarni kin ƙi ba, kafin na aure ma ba ki kasa bin umarnina ba wai Safiyya sai yanzu da har muka tara yara biyu, wallahi kin ba ni mamaki! Kuma bari ki ji na faɗa miki ya zama dole ki kwashe kayanki daga nan zuwa jibi, don a satin nan za su zo jere, su ma na kitchen ɗin ki san yadda za ki yi da su, don da ƙyar ma ta yarda za ku haɗa kitchen ɗin, yanzu kayan da ta siya ma dole ta rage wasu, ke kin ci amarcinki da gida wadatacce ita za ta yi komai a ƙuntace!". Ranta ya ɓaci sosai, duk yadda ta so ta dake ta faɗa babu babu daɗi sai ta kasa, saboda ba ta saba sa'insa da shi ba, kuma faɗa ba halinta ba ne, muryarta na rawa ta ce"Ban yarda ba, kuma ba zan yarda ba, zan rage kayan kitchen, amma ba zan bar ɗakina ba". Ya ce"To mu zuba ni da ke, na ga wanda zai ci riba! Ga kuɗin mota nan, kuma kar ki kai dare". Ya faɗa yana jefo mata ɗari biyar, ya fice. Ta zauna ta fashe da kuka, yaranta da aka yi komai a gabansu suka zo suka raɓe a jikinta, sai ta haɗa su ta rungume tana kukan ta ce"Allah ne gatanmu". Ta jima a haka sannan ta tashi ta shirya yaran ita ma ta shirya, ba ta yi zaton ma zai bar ta ta je gidan ba, ƙarfe goma suka bar gidan, da ta je ta tarar Baba yana shirin fita, suka gaisa da Umma ta shiga ɗakin Baban, bayan sun gaisa ya ce"Gidan lafiya dai ko, ya Salisun?" Ta ce"Lafiya ƙalau". Ya ce"Bari na fita, ai kuna nan har yamma ko?" Ta ce"A'a ya ce kar na kai dare, dama Baba magana nake so mu yi". Ya ce"To ina ji ki Ummi" Ta ɗan yi jim sannan ta ce"Baban Ni'ima ne dama zai ƙara aure..." Ta tsagaita. Baban ya ce"To aure kuma? Allah Ya sanya alkhairi, ban ji labari ba kuwa". Ta ce"Ya ce zai kawo maka kati ai, saura sati ɗaya ma auren". Ya ce"To Allah Ya nuna mana, ai dai babu wata matsalar ko?" An zo wurin, don haka idonta ya kawo ruwa, ta ce"Baba akwai, ka ga ya ce dole na kwashe kayana daga ɗakin, na koma ɗaki ɗaya ita amaryar kuma ta zauna a ciki da falo, kuma kitchen ma wai rabawa za mu yi". Ya ce"Subhanallah!". Suka yi shiru na ɗan lokaci, can ya ce"Ki yi haƙuri, zan yi magana da shi na ji". Ta gyaɗa kai. Ya ce"Ki ƙara haƙuri kin ji, yayanki ne fa za mu yi magana in sha Allah za a daidaita komai". Ta ƙara gyaɗa kai, tana tausayin kanta da Baban, saboda a zaton shi har yanzu da yayanta take tare, bai san tuni yaya ya tashi daga wannan matsayin ba yanzu ya zama Salisu kuma mijinta, irin mijin da kuke haɗuwa da shi sama ta ka da haƙoranka cif a baki, ya aureka ba tare da kun tantance ainahin zuciyar mutum ba, ya yi zaton har yanzu yayanta ne mai tare mata rigima ya kuma rufa mata asiri. "Ni zan fita, ku gaida gida". Ya faɗa yana ajiye mata dubu ɗaya, ta yi godiya sannan ta fito. Suna fira da Umma ita ma ta faɗa mata zancen auren, babu yabo babu fallasa ta ce Allah Ya rufa asiri. Bayan azhar ta mata sallama ta tafi gidan yayanta dake ƙasan layin, da yake sun saba da matarsa sosai, suka dinga fira ita ma ta faɗa mata ƙarin auren ta dinga ba ta shawarwari, ta ce za su zo ranar tariyar, yayan nata ba ya gari saboda haka bayan ta yi sallar la'asar ta fi gida, tana jin nauyin zuciyarta ya ragu, kuma ta ji daɗi da Baba ya ce za su zauna da baban Ni'ima, ta san shi ma bai goyi bayan tsarin nashi ba kenan. Sai da ta leƙa gidan Maman Affan suka gaisa sannan ta shiga gidan dab da magriba. Tana saka ƙafa a gidan taku ɗaya biyu ta yi ta tsaya cak, kamar yadda komai na ta ma ya daina aiki na sakanni, sannan ta fara bin kayan da ta gani zube a tsakar gidan da kallo, 'kenan har an kawo kayan amaryar?' Ta tambayi kanta, sannan ta ɗauke kai daga kallonsu ta shige su Ni'ima da suke tambayarta kayan waye, sai dai tana tura ƙofar ɗakin ta ji ta a buɗe, gabanta ya faɗi ganin ɗakin kamar an yi shara babu komai a ciki, ta ƙarasa ɗakin gadon nan ma wayam, tamkar burodin da ya tsumu a cikin shayi haka ta fito jiki a sake, sai yanzu ta lura da kayan gadonta ne ashe har ma da katifarta, jagwab ta zauna a baranda hawaye suka mata sallama, tana nan zaune har aka kira sallar magriba aka idar ta kasa tashi, sai da ta ji shigowar shi sannan ta ɗago kai ta kalle shi, ƙure shi ta yi da kallo tana so ta gano wani canji a tare da shi wanda zai ba ta tabbacin ba Salisunta ba ne yau ya yi mata haka, amma ba ta ga komai ba sai mijinta yaya Salis ɗinta mai ƙaunarta da tausayinta mai goyon bayanta. Ta matso ƙwalla daidai lokacin da ya ƙaraso kusa da ita. A dake ya ce"Safiyya ni na fito da kayanki, saboda ni ne mijin ke ce matar, kuma gidana ne, don haka wannan ɗakin ɗayan shi na ba ki a shi za ki zauna, kayan sawarku suna ciki, su wannan gobe zan shigar miki da su, kujerun kuma na ga idan kika bar su a tsakar gida yanzu damuna ce za ta shigo sai su lalace, shi yass kawai na siyar da su, dubu talatin aka siya, kuma da yake ban ƙarasa shirye-shirye na ari kuɗin daga baya zan ba ki in sha Allah!". [5/27, 11:32 AM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA...!* (FID DA KAI) BY SADIYA ABDULRAZAƘ *First Class Writers* Page 4 Tun da ya fara magana kanta yana ƙasa tana hawaye har ya gama, suka yi shiru na tsawon lokaci shi yana tsaye, yaran kuma suna ta wasansu suna ɗarewa kan katifa, can dai ya sai ta ba shi tausayi ya sanyaya murya ya ce"Ki yi haƙuri don Allah! Bari na shigar miki da katifar nan". Ya faɗa yana kiciniyar janyo katifar. "Yayanaaa!" Ta kira shi cikin wata muryar da ya jima bai ji irinta ba, wannan muryar tun ta ƙuruciya wacce take ba shi matuƙar tausayi, daɗin daɗawa ta daɗe ba ta kira shi da wannan sunan ba, tun bayan aurensu ta canza masa suna take faɗa masa na soyayya duk wanda ya zo bakinta, bayan haihuwar Ni'ima kuma sai ta saka masa baban Ni'ima, tun daga nan indai ta ce masa Yaya to magana ce mai muhimmanci. Yanzun ma jikinsa ne ya yi sanyi ƙalau, bai juyo ba har sai da ta ƙara "Yaya!" A hankali ya ƙaraso ya zauna a gefenta, sai ta fara kuka ta ce"Yaya kai kaɗai nake kai wa ƙara ka bi mini haƙƙina, amma ban sani ba ko yanzu ka zubar da wannan aminci da ƙaunar da Allah Ya ƙulla". A sanyaye ya ce"Ƙanwata ce ke har abada, hakan yana nufin ba zan zubar ba". Ta ɗan ji daɗi kuma ta tabbatar da tabbas Yayan nata yana cikin hayyacinsa, ta ce"Yaya ƙara na kawo maka, ƙarar mijina, a shekarun baya muna zaune lafiya amma tun da ya fara zancen ƙara aure ya juya mini baya, ta kai yau ya fitar mini da kayana waje saboda wata za ta maye gurbin ɗakunana, kuma ya hana ni kuɗin, ya zan yi Yaya?" Lokaci ɗaya ya tuna abubuwa da dama kuma masu nauyin da ya haddasa masa cunkushewar ƙirji, sun jima a haka ya kasa cewa komai, ta saddaƙar ba shi da wata magana, don haka ta tashi ta kama hannun yaranta suka yi hanyar fita daga gidan. Ya tashi da sauri ya tare ta, ya ja hannunta ya dawo da ita ya zaunar, sannan ya ce"Ba ki da gidan da ya fi nan, don haka ba za ki je ko'ina ba, za ki zauna da yayanki har abada!". Da ƙarfi ta fizge ta ce"A'a! Wannan ba yayana ba ne, mijina ne". Ya ce"Yayanki ne kuma mijinki Safiyya, mijina bai kyauta miki ba, amma ki yi haƙuri ki bi umarninsa ke ce da riba nan gaba in sha Allah, indai kina jin maganar yayanki har yanzu to kar ki sake cewa komai, ki yi haƙuri kin ji ko?" Ta ƙure shi da kallo, yayin da shi kuma kunya ta mamaye ilahirin jiki da zuciyarsa, ya tashi don kallon waɗan nan idanun nata ji yake tamkar hukunta shi take yi, tana zaune ya shiga da katifar, ya ɗauki tsawon ɗokaci yana ta gyara ɗakin sannan ya fito ya ce"Ki yi haƙuri, bari na karɓo muku abinci ba sai kin yi girki ba". Ya fice yana jin zuciyarsa babu daɗi. Kiran sallar isha'i ne ya ankarar da ita ba ta yi magriba ba, don haka ta tashi ta yi alwala ta shiga ɗakin da yaran tuni sun riga ta shiga, ta nemo sallaya ta tada sallah, bayan ta idar ta shiga ƙarewa ɗakin kallo, har net ya ɗaura mata a katifar, ɗakin babba ne don ya so ya fi falonta girma da banɗaki a ciki, yanzu ta riga ta gane wannan yayan nata na wancen shekarun ya mutu babu shi a raye, gangar jikinsa ne kawai a na Salis, don yayanta bai taɓa yi mata irin wannan hukuncin ba, don haka ba za ta sake kiransa da Yaya ba ballanta ta kai masa kukanta, kamar yadda ya faɗa ne ba ta inda ya fi nan ɗin don haka ta saka a ranta za ta yi haƙuri za ta jure, kaza ya siyo musu da lemo, da kanshi ya juye musu a faranti, ya ɗakko kufuna ya zuba musu lemon sannan ya fita daga gidan, yau sai ya kasa zuwa wurin Ameera, a nan ƙofar gida ya zauna don yana tsoron kar ya yi nisa ta fice daga gidan, sai wajan tara da mintina ya tuna da kiran da babanta ya yi masa, nan take ya tashi ya tafi. Bayan sun gaisa Baba ya ce"Salisu ashe aure za ka yi, ai ban ji labari ba sai ɗazu da ta zo". Cike da kunya ya ce"E wallahi Baba, dayake ba a buga katin gayyatar ba, dama zan kawo maka ai". Baba ya ce"Ma sha Allah! Gidan lafiya dai babu wata fitinar ko?" Ya ce"Lafiya ƙalau Baba, babu komai wallahi". Ya ce"Ai haka ake so, to sai dai ɗazu ƙabwar taka ta zo mini da zance a kan ɗakunan gidan, wai ka ce sai ta kwashe kayanta daga ɗakuna biyu ta koma ɗaki ɗaya, su ɗaki biyun ka saka amarya a ciki, me yake faruwa ne?" Tun da ya fara magana gabansa ya fara faɗuwa, ya haɗiyi wani yawu don ba ya so ko kaɗan Baba ya san da matsala a tsakaninsa da Safiyya, don shi kansa ya san a irin halakcin da Baba ya masa idan ya ji ya cuci Safiyya ko bai yi masa magana ba shiru ma sai ya hukunta shi, ya ce"E Baba, ba dai wata matsala ba ce, wallahi ƙarin auren ne ya zo babu shiri, dayake umarni ne daga sama, e Mama ce ta ce sai na ƙara aure to kuma akwai fili da na siya kwanan baya, amma ko bulo ɗaya ban fara sakawa ba, sai na ga tun da da ɗan guri a gidan me zai hana na haɗa su lafin Allah Ya hore mini? To dayake ita ƙanwar tawa dama kwanaki ta riga ta siyar da kujerunta ta fara wani ɗan kasuwanci irin nasu na mata da kuɗin, sai na ga tun da iya kayan gado ne me zai hana ta koma ɗaki ɗaya kawai, kafin a san yadda za a yi". Baba ya yi shiru yana nazari, Salis ya ɗora da faɗin"Da farko ta ƙi yarda, amma yanzu komawata gida mun sasanta ta yarda, yanzu ma muka gama zuba kayanta a ɗakin". Baba ya ce"To ma sha Allah!". Sannan ya ɗauki waya ya kira ta, har lokacin tana zaune a sallayar nan, tana kallo yaran suka gama cakalkala kazar nan suka yi bacci ko wanke musu hannu ba ta yi ba, ta ɗakko wayar a jaka, tana ganin sunan Baba jikinta ya ba ta Salis ɗin ya je kenan, ta ɗaga da sallama, suka gaisa ya ce"Safiyya ya kuke ciki da zancen ɗakuna". Ta sauke numfashi tana ƙara kallon ɗakin da shirgin kayanta, ta ce"Baba shi kenan ai mun daidaita". Baba ya ce"Ma sha Allah! Haka ake so, ki dinga haƙuri kin ji ko? Ya ce kin siyar da kujerunki kin fara kasuwanci me kike siyarwa?" Gaban Salis ya faɗi ya ji kamar ya tashi ya zura da gudu, amma hakan daidai yake da fallasa kansa, don haka ya sunkuyar da kai yana ta salati a zuciyarsa. Mamaki ya kashe Safiyya, ta runtse ido, tana buɗewa ta sauke su a kan shirgin kayanta, idonta ya sauka a kan sabon zanin gadon da yayanta Aminu ya siya mata, kai tsaye ta ce"E Baba, zannuwan gado ne nake siyarwa". Baba ya ce"Ma sha Allah! Allah Ya sakawa abun albarka, ki ta haƙuri ibada kike yi". Suka yi sallama ta ajiye waya, ta sani shi yayi ƙaryar nan, to idan ba ta amsa ba za ta ƙaryata shi ne? Kafin ka hukunta mutum da sharrin da ya yi maka, ka tuna alkhairin da ya yi maka, Salis ya yi mata halakci ya ba ta ruwa a lokacin da take ƙishi, don haka za ta iya yafe masa komai. Sai da ta yi wanka sannan ta kwanta, da safe bayan sun gama karyawa zama ta yi tana ta tunani, har ya leƙo ɗakin, ya ce"Ni na fita, idan na dawo zan shiga da kayan". Ba ta amsa ba har ya fice. Ta ɗauki waya ta kira Maman Affan, suka gaisa sannan ta ce"Ki shigo gidana ki ga ikon Allah!" Ba ta jira cewarta ba ta kashe wayar. Babu jimawa kuwa ta shigo, a tsakar gida ta tsaya tana kallon kayan da mamaki, Safiyya ta fito sai ta fara hawaye. Maman Affan ta ce"Me yake faruwa? Kar dai ki ce min ya sake ki". Ta share hawayen ta ce"Bai sake ni ba, ya dai fito min da kayana, ga shi har na koma ɗakin". Suka shiga ta ga ɗakin ta ce"To ina kujerun?" Ta taɓe baki ta ce"Ya siyar wai ya ari kuɗin". Ta tafa hannuwa tana salati ta ce"Ya ara kuma? Wannan wane irin rainin hankali ne haka?" Safiyya ta yi murmushin takaici ta ce"Babu komai Maman Affan rayuwa ce, na haƙura yanzu komai zai yi zan zuba masa ido, idan Allah Ya yi sai mun rabu ko ba na so sai mun rabu, idan kuma addu'ata ta karɓu sai ki ga komai ya wuce kamar ba a yi ba". Maman Affan ta sauke numfashi ta ce"Wannan gaskiya ne, ki ta addu'a, wannan yarinyar idan ma sihiri ta yi masa Allah Ya sa ya tsaya a iya kan shi, ke dai ki ta addu'a zihirin safiya da na maraice, ma dai mutum ba sai dai Allah! Akwai maganin karya sihiri da yayata take haɗawa ko ba a yi maka ba idan ka yi amfani da shi rigakafi ne, dole ki dinga karɓa duk sati kina yi Maman Ni'ima kar yarinyar nan ta kasaara ki". Safiyya ta ce"To na gode, yanzu mu shirya ɗakin nan na gaji da ganin shirgin nan". Maman Affan ta yi ƙwafa ta ce"Yanzu haka za ki yi baƙi su dinga ganin gadonki? Tsakani da Allah ɗakin gadonka ai sirrinka ne!". Ta ce"To ya zan yi? Lokaci ne, indai Salis zai iya juya mini baya to tabbas babu wata mace da zai aura ta tsira". Sun haɗa gado, amma sun kasa shigar da sif ɗin, don haka ta kira shi ta faɗa masa, sun daɗe suna jira sannan ya zo, don sai da Maman Affan ta je ta gama aikin gidanta ta dawo musu da abinci suka karya su da yaran, suna zaune ya shigo shi da wani yaronsa, da murmushi ya ce"Maman Affan ce a gidan? An tashi lafiya?" Ta ce"Ni ce, ina fa aka tashi lafiya baban Ni'ima ka yanko mana aiki da sassafen nan". Yana dariya ya ce"A dai yi haƙuri maman Affan, kar ki jangwalo min ita". Suka shigar da sif ɗin, suka rago kayan kitchen ɗin ma, sai ɗaki ya cunkushe filin ɗan kaɗan ne, saboda gadonta babba ne, ga shirgi ta ko'ina. "Ɗakin nan bai yi ba!" Safiyya ta faɗa kamar za ta saka kuka. Maman Affan ta ce"Ni ma dai haka na gani, sam abun babu tsari babu kyaun gani". Safiyya ta ce"Maman Affan kawai na siyar da gadon nan, na haƙura da iya katifar ina ga ɗakin zai fi kyau". Ta ce"Rashin sif fa babu daɗi". Safiyya ta ce"Sai na sayi me biyu, wasu kuma na bar su a akwati". Haka dai suka yanke shawara, nan take kuwa maman Affan ta sa ƙaninta ya zo da dillali aka yi wa kaya kuɗi dubu sittin, suka siyar, sannan ta sa aka kawo mata sif mai biyu mai kyau ta siya dubu goma, sai suka sake sabon shirya ɗaki, maman Affan ta ba ta shawarar ta rago wasu kayan ta ajiye mata, sai ta ba ta manyan zannuwan gadonta guda uku ne, da wasu kayan kitcken ɗin kuma ta fitar da kaya da yawa ta bayar a maƙota, maman Affan tana ɗinki har na labulaye, ta je ta haɗe labule guda biyar ta ɗinke ya zama babban, ta ɗaura igiya ta saka a kusa da katifar, sai ya zama an yi wa katifar katanga ɗakin ya zama kamar ciki da falo sai ɗakin ya yi kyau, sha biyu ta wuce don haka ta tafi gidanta, ita ma ta ɗora girki. Da daddare da ya dawo ya shigo, ya ƙarewa ɗakin kallo ya buɗe labulen katifa ya ce"Mene ne nan?" Sai ya yi wata dariya ya ce"Ikon Allah! Wato mata akwai hikima wallahi". Ya zauna a kan san sallayar dake shimfiɗe ya ce"Ki yi haƙuri Safiyya, ba ga shi ɗakinki ya yi kyau ba, wannan dai ko hasidin iza hasada ba shi da ta cewa wallahi, amma Safiyya ina gadon yake?" "Na siyar" Ta ba shi amsa ba tare da ta kalle shi ba. Sai kuwa ya ɓata rai ya ce"Kin siyar fa!?" Ta ce"E". Ya ce"Dalili" Ta ce"Ra'ayi". Ya ce"Ni kike cewa ra'ayi ya sa kin siyar da gadonki? Kenan ni a banza kika ɗauke ni da ba za ki yi shawara da ni ba kafin ki siyar da abu ko?" Har yanzu ba ta kalle shi ba dai. Ya ce"Ina kuɗin kuma nawa ne?" Ta ce"Dubu hamsin ne kuma na tura account ɗin Baba ya ajiye mini". Ta yi wannan ƙaryar, don maman Affan ta gargaɗe ta sosai a kan kada ta sake ta ba shi. Ya haɗe gira ya ce"Saboda raini ko?" "Duk yadda ka ɗauka haka ne" Ta faɗa tana tashi ta fita daga ɗakin ta shiga kitchen, kafin ta fito ya fito zai bar gidan, tana riƙe da faranti ta ce"Abinci na zubo maka". Ko juyowa bai yi ba ya fice. Washegari ya zo da kafinta aka buga wasu kantocin, sannan a ka gyara mukullan lokokin da suka lalace, aka saka sababbi, maman Affan ce ta ce kar ta jera nata har sai an gama bikin tukunna, don haka gas ɗinta ne kaɗai a ciki. Ranar Lahadi ce ta kama ɗaurin aure, ranar Juma'a da safe yake faɗa mata yau za a zo yin jere, a waya ta faɗawa maman Affan, ta ce mata ta kira wasu ƴan'uwan nata kafin ta gama aiki ta shigo, amma ta samu masu zafi-zafi saboda tsaro, ta yi tsaye da waya ta rasa wa za ta kira, Salma matar yaya Aminu kullum a chart sai sun yi firar kishiyar nan tun da ta je gidan ta ba ta labari, ita ma masifaffiya ce, don duk baƙin halin yaya Aminu ba ya iya yi mata, tana kiranta kuwa ta ce ga ta nan, sannan ta kira ƙawarta Hafiza, ta yi sa'a ita ma ta ce za ta zo, kafin sha ɗaya duk sun zo, baban Ni'ima ya aiko da cefane don a musu girki, Salma ta yi tsalle ta dire ta ce ba za a yi ba, don dole Safiyya ta yarda, suka dafa iya nasu suka ci, aka dinga fira ana ba wa Safiyya shawarwarin zama da kishiya, wasu ta ɗauka wasu kuma ta san ba zai yiwu ta gwada ba. Ƙarfe biyu suka ji tsayawar motar kawo kayan, suka yi sallama wata zabiya cikinsu ta ce"Ga baƙin arziƙi idan an so". Hafiza ta turo ɗankwali gaban goshi ta ce"Mu na tsiyar ma sai dai su shafa mana lafiya!". Matar ta ce"A'a yarinya mu fa alkhairi ne ya kawo mu, alkhairin haɗa raya sunnar ma'aiki". Wata ta ce"Ƙyale ta, ai kishi halak ne, ballantana wacce za a gallowa budurwa fil a leda". Maman Affan ta ce"Allah Ya sa ita ce budurcin ma, ai duk wani amarci a bayan na Safiyya yake, ƴan matan yanzu ma da duk sanyi ya gama da su, ka ga budurwa tana susa har ina budurcin yake? Allah Ya sa ma ba a barbaɗar a titi ba!". Matar ta ce"Duk dai baƙin cikin tanda sai an ci waina, kuma zancen barbaɗa ai zama ne zai nuna hakan, Salisu zai san yanzu ya yi aure!". Haka suka dinga cacar bakin nan, suna jere suna yi har suka gama suka tafi, Hafiza ta leƙa kitchen ɗin ta ce"Ai kun ga sun cike shi tsaf!". Maman Affan ta ce"Dole su tattare ai tun da ba gidan ubansu ba ne!". Sai magriba suka tafi, tana zaune a ɗaki ya dawo ya shiga ɗakinsa, ta tashi ta bi shi ɗakin, ko sannu ba ta yi masa ba ta ce"Baban Ni'ima an yi jere, amma ka ga an cike kitchen ɗin, ni ina zan jera nawa kenan?" Ya ce"E ni na ce su jera duka, don ƙanwar babarta ce ta ƙi yarda ku haɗa kitchen ɗin, kuma da na ga ba ki jera nakin ba na za ta duka ɗakinki ya cinye har na kitchen ɗin". Ta ce"Bai cinye ba, kuma ba zan bar mata ɗakuna na bar mata kitchen ba, saboda haka a gyara!". Ya ce"Gaskiya babu wanda zai saka mini ciwon kai, yanzu ana taɓa musu kaya wata fitinar za ta iya tasowa, ki bari idan ta tare zan ce ta tattare". "Ba zan bari ba, a yau zan tattare, fitina kuma zan iya musu ba sai ka shiga ba". Ta fice daga ɗakin ta doshi kitchen ɗin. [5/27, 11:32 AM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA...!* (FID DA KAI) BY SADIYA ABDULRAZAK *First Class Writers* Page 5 "Safiyya! Ke Safiyya!" Ya kira ta a tsawace, amma hakan bai hana ta k'arasawa kitchen din ba, tsaye ya same ta tana neman ta inda za ta fara, ya b'ata rai ya ce"Na fad'a miki kada ki tab'a musu kaya!". Ta ce"Ba fa dauka zan yi ba, matsarwa zan yi". Ya ce"Ni dai na fad'a miki kar ki tab'a komai, idan ta tare za ta tattare su, shige mu tafi". Ta coge tana huci ta kuma k'i ko motsi, suka d'auki lokaci a haka sannan ta fita ta koma d'aki, babu jimawa ya shigo ya ce da ita"Ina mukullin kitchen din?" Ta dakko ta ba shi, sai da safe tana fitowa ta ga gas dinta a k'ofar d'aki ya fito mata da shi ya kulle kitchen din, ta jinjina kai ta shiga harkokinta zuciyarta cunkushe da bak'inciki. A ranar Asabar d'in wacce ta kama saura kwana d'aya d'aurin aure da yamma y'an'uwansa suka zo, kowacce fuskarta d'auke da walwala, wannan tsohuwar k'iyayyar tun ta k'uruciya ita dai tana nan daram a idanunsu, bayan sun gaisa Mariya ta ce"Ni Safiyya sai na ga duk kin k'are a tsaye". Ta yi murmushin takaici ta ce"Ko dai idonki ne? Amma ni kam ko jiya baban Ni'ima sai da ya ce mini sai k'iba kike kamar ba wacce za a yi wa kishiya ba, na ce to me zai dame ni bayan na san mijina mai adalci ne?" Duk suka yi saroro don kuwa ba su yi zaton jin haka daga bakinta ba, ita kanta da a da ne shuru za ta yi, amma yanzu dayake tana ta d'aukar darasin da ake biya mata tana da amsar ba su, Anti Fa'iza ta tab'e baki ta ce"Yo shi har ya yi wani zancen k'iba? Waye silar k'ibar tata? Mutumin da tun tana yawo da guntun kashinta yake ci da ita, ballantana yanzu da ya kawo ta gida ya rufe ake cin duniya". Mariya ta ce"K'warai kuwa, amma yanzu ai Allah Ya taro shi, tun da ya dawo hayyacinsa, sai ya yi auren nan zai gane a da goguwa ya yi ba angwanci ba, ai wani abun sai Salisu, a ce ka yi hidimarka ka yi ta amarya? Ita kuwa wannan ko cokali bai siya mata ba". Haka suka yi ta firar su, tana bin su da kallon ko a jikina, har suka gama sannan suka mik'o mata leda, wai ga kayan fad'ar kishiya. Ta fad'ad'a fara'arta ta karb'a ta bud'e, atamfa ce guda d'aya da takalmi da mayafi, ta ce"Allah Ya amfana". Fa'iza ta ce"Ga shi nan, iya abin da ya bayar kenan, ana yi da kai ya fi ba a yi da kai, wai sarki ya zama mai unguwa". Safiyya ta ce"Laa! Babu komai wallahi, ai ya yi mini bayani, ya ce ya samu matsala ne a kwanan nan, amma daga baya zai yi mini akwatina, na ce ma ya hak'ura tun da a gidan nan wane irin kaya ne ban saka ba, amna kin ga ya k'i, ya ce sai ya yi dai". Ta k'arasa maganar da murmushi kamar babu damuwar komai a zuciyarta, wannan duk cikin darasin da ta fara koya ne na kissa, kuma ta lura zai kai mata, domin kuwa tashin farko ta ga fuskokinsu sun canza. Daga k'arshe suka fad'a mata za a yi wuni gobe a gidansu idan za ta je, ta ce Allah Ya kaimu. Sai da suka tafi ta k'ara kallon kayan, atamfar ba wata babba ba ce, wai ita zai bayar a kawo mata a matsayin kayan fad'ar kishiya, ta jinjina kai ta je ta adana, don tuni ta ware kayan da za ta saka, akwai less guda biyu da ya d'inka mata ba ta tab'a sakawa ba. Da daddare yana dawowa ya shigo d'akinta, a fusace ya ce"Safiyya a kan me za ki had'a ni da uwata?" Gabanta ya fad'i, ta ce"Subhanallah! Me na yi kuma?" Ya ce"Yaushe muka yi da ke zan k'aro miki kayan fad'ar kishiya?" Shaf ta manta da an yi haka sai yanzu ta tuna, ta kauda kai gefe ta yi murmushin jin dad'i, ashe dai sosai ta cusa musu bak'iciki daurewa kawai suka yi. "Ina magana kin juya mini kai saboda raini ko!?" Maganarsa ta dawo da ita daidai, sai ta fara rawar murya ta ce"To baban Ni'ima mai zan ce maka? Indai shekarun da muka yi da kai bai sa ka gane halina ba to ko na yi maka bayani ba za ka gane ba, aure fa za ka yi, kishiya za ka yi mini, idan ba ka kwantar mini da hankali ba bai kamata ta yar ba, akan me zan yi k'aryar za ka k'ara min kaya? Na tab'a yi maka hakan? Me na yi wa y'an'uwanka ne? Meye laifina saboda kana sona?" Sai ta fashe da kukan k'arya. Jikinsa ya d'an yi sanyi domin ya san Safiyya ya san halinta, tabbas k'arya ba halinta ba ne, don haka ya yarda makircin su y'an'uwansa ne kawai tun da ya san ba sa son ta, ya jinjina kai sannan ya ce"Ke ba za ki yi taro ba ne? Na ga ba ki tambaye ni kud'in da za ki yi wani abun ba". Ta ce"To ai na ga ba sai na tambaya ba idan ka yi niyyar yi mini abu shi yasa na zuba ido". Ya ce"To zan ba ki dubu goma sai ku yi girki da bak'inki, don ba kud'i ne da ni ba, duk na kashe kud'i a auren nan wallahi, jiya da na yi lissafi abun har haushi ya ba ni". Ta ce"Ikon Allah! Kai da ka cika umarnin uwa ai riba za ka k'irga in sha Allah, kuma dama d'akko amarya ai ba a yi a araha ba". "Hmm! Ke dai a yi sha'ani kawai Safiyya". Ya fad'a yana d'an kishingid'a. Shuru na d'an lokaci sannan ta ce"baban Ni'ima ka kulle kitchen". Ya ce"Don Allah kar ki sa mini ciwon kai, zan bud'e za ta tattare kayan ke ma ki samu waje". Sai kuma ya yi tsaki ya tashi ya fice daga d'akin. Washegari da ta kama d'aurin aure tun sassafe maman Affan ta shigo, ita ma matar yaya Aminu ta yo sammako, suka yi cefane suka hau aikin abinci, k'arfe goma angon Ameera, yayan Safiyya kuma mijinta ya fito fess cikin shirin tafiya d'aurin aurensa, a lokacin tana d'akinta tana shirya su Ni'ima, ya shigo, ta d'ago ta kalle shi ya yi mata murmushinsa wanda yake matuk'ar burge ta a shekarun baya, ita ma murmushin ta yi, tana kallon yadda yi kyau sai k'amshi yake "To mu za mu tafi, kin san goma ne, mun ma yi latti". Maganarsa ta katse ta daga kallonsa, ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Allah Ya sa a gama taro lafiya, Allah Ya ba ku zaman lafiya". Ya washe baki ya ce"Amin Ya Allah! Ko ke fa, sai yanzu na tuna da Safiyyar yayanta, amma da duk kin bi kin canza kin birkice mini, kin san fa ina son ki, amma bari dai na dawo za mu tattauna". Ya fice, ta bi bayansa da kallo tana mamakin wai yau ita ce mijinta zai mata kishiya, ashe da yake ta cewa ba zai iya had'a ta da wata ba saboda gudun aikata rashin adalci duk dad'in baki ne, ta sauke ajiyar zuciya tana tunanin kalar zaman da za su yi. Babu laifi ta yi taro, mak'ota da d'aid'aikun y'an'uwan duk sun shigo, ana ta raha ana dariya, har ta ji kamar ba ta da wata damuwa, sai da magriba ta yi gari ya fara duhu aka kawo amarya, kowa ya sulalewa aka barta ita kad'ai sannan ta fara jin babu dad'i, ta yi zaton ma yau d'in sai an dambatu da su maman Affan, amma sai aka samu sauk'i, saboda habaicin y'an kawo amaryar da sauk'i, ko don sun ga idan sun yi ba a bar musu ne oho. Tana jin shigowar ango da abokansa, a lokacin tana d'aki shuru ita da yaranta, tana ta jiyo shewarsu dayake akwai sauran k'awayenta da ba su tafi ba, babu jimawa kuma suka yi sallama a k'ofar d'akinta, suka shigo da amarya lullub'e cikin mayafi suka zaunar da ita, har wata k'awar tata tana cewa"Zauna a hankali k'asa ne, babu kujera". Wata zabiya a cikinsu ta ce"To Anti Safiyya ga amanar k'anwarki mun kawo, sai a yi hak'uri Allah Ya kad'e hau". Safiyya ta yi murmushi, tana ayyana kenan yara ne ma za su kawo amanar ba iyayenta ba, duk da dai ba girmansu ta yi ba, amma ai ta ci girman uwar gida, ta ce"To Allah Ya ba mu zaman lafiya, mu dai gidanmu na aminci ne, kuma karamci gadonsa muka yi". Wata ta ce"Mu ma kam ba daga nan ba, za ku zauna lafiya da Ameera indai kin so". Ta yi murmushi ta tashi ta d'akko kayan fad'ar kishiya da aka kawo mata, dama suna nan a ledar ta ajiye a gaban amarya ta ce"Allah Ya had'a kanmu". Duk suka amsa da amin, sun fito za su tafi baban Ni'ima ya ce su bar amaryar a d'akin, ya je ya raka su ya dawo ya kulle gida, sannan ya shigo, a gefen katifa ya zauna yana wasa da hannun Kausar ya ce"Ku ba ku yi bacci ba? Ga sabuwar Anti an kawo muku". Ni'ima tana daga kwance ta ce"Abba a nan za ta kwana?" Ya ce"E kullum ma a nan za ta kwana, kin ga d'akinta can, ita ma babarku ce, za kuna shiga kuna yin wasanku". Sai ta yi shuru. Ya yi gyaran murya ya ce"To Safiyya ga Ameera nan, k'anwarki ce duk da dai ta girme ki a shekaru, don Allah ki ja girmanki, ba na son fitina kuma na san ba halinki ba ne, ku rufa mini asiri ku zauna lafiya don na samu damar gudanar da adalci a tsakaninku". Safiyya ta ce"In sha Allah!". Ya ce"Na gode, Ameera ku zauna lafiya don Allah ku had'a kanku saboda kan yaranku ma ya had'u kin ji ko?" Ta ce"To". Sun tashi za su fita Safiyya ta ce"Baban Ni'ima zancen kitchen d'in, da ta shiga ta tattare". Kamar jira yake ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Safiyya yaushe kika zama haka ne? Ameera wuce mu je". Suka fice, ita kuma ta yi murmushi dama tana sane ta yi zancen, don Ameerar ta d'an tada masa hargitsi ko banza amarcin ya rage armashi. Bayan su Ni'ima sun yi bacci shiru ta yi, tana ta tuna rayuwarsu ta baya, da irin yadda amarcinsu ya kasance cikin soyayya da sahihiyar k'aunar, cike da tausayin da ta san Allah ne ya sakawa yayan nata domin kawo mata tallafi a baud'addiyar rayuwarta ta baya. Ba ta san iya tsawon lokacin da ta d'auka tana tunani ba, ta dai ji k'arar k'ofa alamar an bud'e k'ofar d'aki, babu jimawa kuma ta ji ana yin wanka, aka dawo aka banka k'ofar d'aki da k'arfi, ta kalli agogo ta ga sha biyu da rabi, can wajan d'aya da rabi ta k'ara jin an bud'e d'akin still an sake yin wanka, wanda kamar da gayya ake shek'a ruwan, sai kuma ta ji tafiya an zo k'ofar d'akinta, ta windonta ta ji wata murya ta ce"Second round!". 'Second round' Ta maimaita kalmar a zuciyarta, sai da ta yi tunani na sakanni sannan ta gane abin da ake nufi, sai kuma ta ji an sake bud'e k'ofa an rufo, ta sauke ajiyar zuciya ko za ta ji sauk'in abin da ya tokare mata k'irji, yanzu ita ake fad'awa second round? Ita da suka shekara biyar da mijin, to kuma wane dare ne jemage bai gani ba? 08028966015 [5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA* (FID DA KAI) BY SADIYA ABDULRAZAK FIRST CLASS WRITERS Page 6 Sai ta fara tunanin to me ya hana ta wanka a d'akin nashi, sai ta zo band'akin tsakar gida? Kuma ma k'ofar d'akinta ta ji ana bud'ewa da rufewa ba ta mai gidan ba, kenan dai shi ya biyo ta d'akinta ya kwana. Ta sauke numfashi a ranta ta ce'ku yi ku gama'. Washegari sassafe ta fito, ta k'wank'wasa k'ofar d'akin shi "Baby ce? Shigo mana". Ta ce"A'a ba ita ba ce, wannan uwar Baby ce". Sai kuwa ya fito ya hade rai ya ce"Safiyya rainin naki har ya kai haka? Ni kike zagi?" Ta yi murmushi ta ce"Ni fa ba da wata manufar na fad'a ba, tun da ni na tsufa na wuce Baby, Khausar ai Baby ce, ita babynka ni kuwa guzuma uwar baby". Ta k'arashe da y'ar dariya. Ya had'e gira ya ce"Mene ne?" Ta ce"Mukullin kitchen". Ya ce"Safiyya don Allah me ya sa ba kya so mu dinga rufawa juna asiri?" Ta ce"Na dinga rufa maka dai, ni nawa a rufe yake in sha Allah! Kawai ka ba ni mukullin kitchen". "Ameera!" Ya k'wala mata kira. Ta fito tana wani yauk'i cikin kayan bacci ta ce"Honey". Ya tsaya yana kallonta kamar ba tare suka kwana ba jiya, Safiyya ta kalle ta ta ce"Mun tashi lafiya?" "Lafiya k'alau" Ta amsa da gadara. Safiyya ta ce"Ma sha Allah! Ya kwanan bak'unta?" Sai ta yi dariya mai kama da ta rainin hankali ta ce"Ni da gidana ina zancen bak'unta?" Ta yi murmushi ta ce"Haka ne fa". Ameera ta k'araso ta ce"Me ake yi ne Honey?" Safiyya ta karb'e zancen ta ce"Wai mukullin kitchen zai ba ni, na gyara kayanki na samu wurin zuba nawa, ke ma ko d'an ruwan zafi kin ga na dafa miki". Ameera ta yi wa baban Ni'ima kallon tuhuma. Ya ce"Ki yi hak'uri Ameera ku biyu za ku had'a kitchen d'in, dama cewa na yi idan kin tare sai ki gyara ta zuba nata". Ta tab'e baki ta ce"Illar auren mijin wata kenan, kuma sai da na ce maka ka kama mini gidan haya ka ce ba haka ba, ga shi daga zuwana jiya zan fara shak'ar takaici!". Ta shige d'akinta a fusace, shi kuma ya bi ta. Safiyya ta shiga d'akin nasa don rainin hankalin ya ishe ta haka, ta bud'e loka inda yake ajiye mukullai ta d'auki na kitchen d'in, ta je ta bud'e, ta hau kwasar kaya tana jibge su a gefe wasu kan wasu, ta juyo za ta fito don kwaso nata ta ga Ameerar tsaye ta rik'e k'ugu tana kallonta, ta rab'e ta ta wuce ta kwaso nata kayan, ta kusa shigowa ta ji k'arar fashewar abu, dinner ne guda biyu Ameerar ta fasa su, sai dai ba ta sani ba tana sane ko tsautsayi ne, ta ga dai ta fice fuu kamar kububuwa, ita kuwa ta shiga jera kayanta, babu jimawa sai ga ta nan ita da shi, a fusace ya ce"Wannan wane irin bak'in hali kika koya ne Safiyya, ta ya za ki d'aki farantanta kina sane ki sake su a tsaye? Kuma sai da na ce miki ki bari za ta kwashe da kanta, amma saboda kin taki mugunta kika fasa mata!" "Wallahi sai an biya ni!" Cewar Amerar tana kumbura. Ya ce"Ai ya zama dole, kuma ita ce za ta biya wallahi, a cikin kud'inki zan zari na wannan farantan". Safiyya ta yi murmushi ta ce"Babu damuwa, na gode". Suka fita ita kuma ta k'arasa gyaranta, ta dafa abun karyawa ta fice. Suna zaune da yara ya shigo ya ce"Ina abincinmu?" Ta ce"Abincinku?" Ya ce"Shi". Ta ce"Ban dafa da ku ba, tun da ba ni da wannan hurumin, ka kawo ta ne na dinga yi mata girki? Kai ma sai ranar kwanana zan ba ka abinci ai ko?" Ya ce"Amma da na ga ita amarya ce ga gajiyar biki tun da kina nan bai kamata ta fara shiga kitchen yau ba ai". Ta ce"E to! Da wannan ma, ga wahalar daren amarci watak'il ma ten raound". Ya yi murmushi ya ce"Kash! Safiyya wane irin ten round sai ka ce wani taure, ita jiya ma tana d'akinta ina nawa, dayake ba ta da lafiya, kuma kin san..." "Ni ban ce ka fad'a mini sirrin aurenku ba" Ta katse shi. Ya sosa kai ya ce"Daure don Allah ko indomi da k'wai ki sama mana, ki dafa wannan shayin naki mai kayan k'amshin nan". Ta yi murmushi ta ce"Baban Ni'ima kenan, na ga nan ka daina karyawa a gida kake tsallake shayin ka tafi teburin mai shayi". Ya ce"Assha! Wallahi ban je wajen mai shayi ba, ita Ameera ce fa kullum sai ta aika mini abun karyawa a kasuwa". Safiyya ta had'iyi wani yawun takaici ta ce"Ai ka ga ta kwana gidan sauk'i, tun da ga ta a gida dad'in ciyar da kai kenan, sai ta fito ta dafa". Ya ce"Haba Safiyya, tsakaninki da Allah ke washegarinki a gidana kin yi girki?" Ta ce"Ban yi ba, amma babu wacce ta yi mini, fita ka yi ka siyo". Ya ce"Ita ma na siyo mata kenan!". Ta yi shiru, ya gama tsayuwarsa ya fice, da kan shi ya shiga kitchen d'in ya had'a musu abun karyawa, Safiyya ta ce"Kad'an ma ka gani!". Bayan ya fita, ta fito k'ofar d'aki ta zauna, tana kallo Ameera ta fito ta shiga wanka, ita kuma ta tashi ta shiga kitchen, da hanzari ta d'akko flask d'in shayi guda biyu ne babba da k'arami, a k'aramin suka sha shayi, babban a kwali ta ciro shi, ta had'a shi da bango ta gwara ya ce tushhh! Ta d'auki k'aramin ma ta fasa, sannan ta mai da babban kwalinsa ta fito a ranta ta ce, 'dama farantai biyu kika fasa, bari na bar ki haka'. Sha biyu ta gama girkinta, lokacin gidan cike yake da bak'in amarya, ta zuba a madaidaiciyar kula ta aiki Ni'ima ta kai wa Ameera, babu jimawa Ni'ima ta dawo mata da abincin, ta karb'a ta ajiye, tana idar da sallar azhar kiran Salis d'in ya shigo wayarta, sai da ta shafa addu'a sannan ta d'auka da sallama, ya amsa ya ce"Safiyya me yasa kike haka ne?" Ta ce"Me kuma na yi?" Ya ce"Ameera ta ce kin zuba mata abinci d'an kad'an ita da bak'inta". Ta sauke numfashi ta ce"Ikon Allah! Ni fa na zuba mata ne saboda hakkin mak'obtaka, ni zan yi wa bak'inta girki?" Ya ce"Ai sai ki duba ki gani tana ta fama da bak'i yaushe za ta fita d'ora girki? Kuma ma na manta ban zuba mata gas d'in ba, yi hak'uri ko taliya ce ki dafa musu ko leda uku ce". Ta ce"Ni ma gas d'in nawa ya k'are k'araf, don a gidan maman Affan ma na k'arasa girkin, kuma na bar shi a can, idan mai babur d'inta ya zo zai zubo min". "Subhanallah! To bari na aiko a zuba natan sai ki dafa don Allah!". Ta ce"Ka yi hak'uri baban Ni'ima, kaina tun safe yake ciwo, nawa ma da k'yar na yi". Ba ta jira cewarsa ba ta kashe wayar duka, ta kwanta. K'arshe y'an'uwan Ameera ne suka yi girkin, shi kuma da ya dawo duk fad'an da ya yi ba ta ce komai ba. Ya dawo da kayan abinci da yawa, don haka ya kira su d'akinsa, ya fara bayani "Ga kayan abinci nan za a bar su a nan ku kwashi wanda zai kwana biyu ku kai kitchen, tun da babu fili a kitchen d'in, sannan duk wacce take da kwana ita za ta yi girki, a dafa wadatacce kowa ya d'ibi Wanda zai ishe shi, amma na safe kowa ya yi nashi". Duk suka amince. Daga nan bai sake cewa ta yi mata girki ba gar suka gama satin amarci ya dawo d'akin Safiyya, a satin nan kullum sai Safiyya ta ji wannan k'arar wankan, yanzu dariya ma abun yake ba ta. A ranar da ta karb'i girki da rana Ameera ta yi bak'i su biyar, ita kuma ba ta dafa da su ba, ta kira shi ta sa ya ce wa Safiyya idan wata ta yi bak'i a ranar girkinka dole ka yi musu girki, dama tana da yaji ai kuwa ta dafa musu farar taliya, tana ji suna mitar sun ci mai da yaji a gidan amarya, abun ya b'atawa Ameera rai ta fad'a masa da ya dawo ya yi wa Safiyya fad'a sosai, ta yi shiru, amma ta saka a ranta babu bak'in da za ta b'ata lokaci wajen yi musu girki. Yadda ta lura duk ranar girkin Ameera cefane ya fi yawa da kyau, da ta yi masa magana sai ya ce ai ita kullum cikin yin bak'i take shi yasa, haka ta yi shiru ta k'yale. Sai kuma ta lura duk ranar girkinta shi yake zab'ar abin da za a dafa, kullum da rana shinkafa da wake mai da yaji, da daddare tuwo, sai dai ta dinga canza miya, saboda haka babu wani cefane da ake kawo mata, sab'anin Ameera da ba ta tab'a yin tuwo ba ko mai da yaji. Yau ma kaji take dafawa tana kallon sanda aka kawo mata ta fara aikinsu, indai ta dafa kaza ko k'afa ba ta ba Safiyya tata ce ita da Ango, abun yana damun Safiyya, don haka Ameera tana fitowa daga kitchen d'in Safiyya ta yi wuf ta shiga, a zaninta ta fito da abu a leda ta bud'e tukunyar ta zazzage shi duka ta juya ta yi sauri ta fice, tana cewa"Yau sai dai ki ci ke kad'ai, shi ma sai idan ke mayya ce!". 08028966015 [5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA* (FID DA KAI) BY SADIYA ABDULRAZAK FIRST CLASS WRITERS Page 7 Safiyya tana zaune a k'ofar d'aki ta fara jiyo k'auri da yaji, ta yi murmushin jin dad'i, sai ga Ameera ta fito da gudu ta shiga kitchen d'in, tana shiga ta fara tari kitchen d'in ya turnuk'e da yaji ta yi sauri ta kashe gas d'in, tana ta mamaki don ta ga ba ta cika attaruhu a kazar ba, sanda ta d'and'ana romon gabanta ya fad'i da ta ji wani uban yaji ya kaure mata baki, ta ci gaba da tari tana mamaki, haka dai ta juye kaza a flask ta ajiye. Da daddare baban Ni'ima yana dawowa ta kwaso abinci ta kai masa, ana ta fira cikin nishad'i da zumudin amarya, ta zuba masa jollof d'in shinkafa, ta zuba kaza a palate, kazar ya fara ci, ya yaga ya kai baki, nan take fara'ar fuskarsa ta d'auke ya ce"Baby wannan wane irin yaji ne haka?" Ta ce"Wallahi na rasa yadda aka yi na cika yajin nan". "Gaskiya ba zan iya ci ba" Ya fad'a yana tashi zai fita. Ta b'ata rai sosai ta ce"Amma inda wannan matar ce ta yi ko me ka ji haka za ka ci, shi kenan!" Ta tashi ta shige d'aki. Ya san ta yi fushi sosai, shi kuwa sam ba ya k'aunar fushinta, tsakani da Allah har jiran ranar kwananta yake yi, saboda haka ba zai so abin da zai shiga tsakaninsa da samun nutsuwarsa ba, don sosai yake jin dad'in y'ar Babyn tasa, da sauri ya bi ta, ya rik'o hannunta ya dawo da ita ya zaunar, ya ce"Haba Love! Idan kika yi fushi da ni ina zan kama? Kaza ce ko?" Ta d'aga masa kai alamar e. Ya ce"To sakko mu ci". Ta sakko, ya ja plate ya fara ci, sai da ya daure sosai sannan ya had'iye, wani azababben yaji yake ji a mak'oshinsa, harshensa kamar zai tsage saboda zugi, ji yake yajin kamar har cikin idonsa, amma haka ya daure yake ta ci saboda farincikinta, yana zuk'ar iska ya ce"Babyyy ke ba za ki ci ba ne?" "Na ci tun d'azu" Ta yi masa k'arya. Ya ce"Don Allah ki k'ara, ni ko y'ar k'ibar nan ban ga kin fara ba, kin san fa kaza ce mai saka mutum k'iba, shi yasa nake siyo miki". Ta ce"Haba Honey ni me zan yi da wata k'iba?" Ya ja yaji ya ce"Kaii! Ashe ma ba ki san mijinki ba kenan, ai ni wallahi ina son mace mai k'iba sosai, kin ga ita dai Safiyya jikin ne a haka a bushe shi yasa ma na daina asarar siya mata kaza". Ta ce"Ba fa zan iya cin kazar nan ba, ina da olser". "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ya fad'a jin cikinsa kamar an kunna wuta Ta ce"Mene ne?" "Yaji mana!" Ya fad'a kamar an tsikare shi. Ta yi murmushi ta ce"Haka dai za ka hak'ura ka cinye". Sai da ya ci rabin kazar nan a wahalce sannan ya mik'e ya ce"Ke yasin ba zai yiwu ba, na k'oshi haka". Bai ma jira cewarta ba ya fice daga d'akin, kitchen ya shiga ya d'auki madarar ruwa ya kwankwad'e, amma duk da haka bai ji daidai ba, ya fad'a d'akin Safiyya a zabure yana ta shan yaji, Ni'ima ta ce"Abba sannu da zuwa". Ya ce"Yauwa Ni'ima ba ni biskit ko alawa". Ta ce"Abba babu". Ya ce"Safiyya akwai biskit ko wani d'an abun tab'awa?" Tun da ya shigo take danne dariyarta, duk da ta tausaya masa don kuwa muddin mutum ya ci kaza da wannan uban barkonon da ta zuba dole rayuwarsa ta shiga yanayi. "Safiyya ya ina magana kin juya kai? Wannan ai raini ne, biskit na ce ki ban". Ta ce"Ikon Allah! Biskit sai ka ce wani d'an yaye? Ai ka zauna mu gaisa ko? Ya kasuwar". Cikin jin haushi ya ce"Subhanallah! Idan ba za ki ban ba na yi gaba". Ta ce"Yaushe rabon da ka siyowa yara alawa da biskit, inda akwai ai a kitchen za ka gani..." Bai ma jira ta gama ba ya fice daga gidan, shago ya je ya siyo alawowi ya yi ta taunawa, kafin ya zo gida ya d'an ji sauk'in abun, haka ya shiga d'akinsa ya kwanta yana tsotsar alawa, ya so cin shinkafar nan k'warai amma yaji ya riga ya rud'a cikin, ya tuna da Safiyya ce ta yi wannan girkin yau da sai ya kusa kwana yana mita, amma wannan sabuwa ce babu dama, amma tabbas sai ya yi mata kyakkyawan gargad'i akan saka yaji a abinci, sai ka ce makauniya? Murd'awar da cikinsa ya yi ne ya katse masa tunanin, ciki ya k'ulle yana rugugi tamkar ana yak'i a ciki, ya rik'e cikin yana cije baki, da gudu-gudu ya afka band'aki nan take ya b'arke da gudawa, a daren sai da ya yi sau uku sannan ya ji sauk'i, haka ya kwana ciki babu dad'i, ko ta kan Baby bai bi ba, don juya mata baya ma ya yi. Bayan an kwana biyu Safiyya ta gaji da rainin hankalin da ake yi mata na zab'ar girki, yau ma kamar kullum ya ce mata shinkafa da wake da rana tuwo miyar kub'ewa da daddare. Ai kuwa da ta tashi ta dafa taliya da miya da daddare ta yi sunasir da miyar agushi don ta san yana so sosai, da kud'inta ma ta siyi kifi ta saka a miyar, da ta gama ta zuba masa nashi ta saka kifin ta tsame sauran, don kar Ameera ta zo zubawa ta saka kifin. Abin da Safiyya ba ta sani ba, Ameera ce ta tsarawa mai gidan wannan dafa shinkafa da wake da tuwon, saboda ta cusawa Safiyyar takaici, ita ta yi ta canza girki miji yana jin dad'i ita kuma ta yi ta tuwo ta san dole zai fi marmarin ranar girkinta, amma ita ma ba gwanar cin tuwo ba ce daurewa kawai take ta ci, wataran ma ba ta ci, don haka yau ta cika da mamakin dalilin da yasa Safiyya ta canza girki. Yana dawowa ya shiga d'akin Safiyya, ta kawo masa abinci, yana bud'ewa ya ga sunasir ya ji dad'in, don ya dad'e bai ci ba "Yau sunasir kika yi? Ma sha Allah!". Kafin ta yi magana wayarsa ta yi k'ara, a tare suka kalli wayar da sunan my Sugar ya bayyana a screen, Safiyya ta kau da kai tana zuba masa a plate, ya d'auki wayar ya ce"Baby". Ameera ta ce"Ina kiranka yanzu". Ya tashi ya ce da Safiyya"Ina zuwa". Yana shiga ya ga Ameera ta had'e fuska, ga kular sunasir a gabanta, ya zauna ya ce"Babyna ya dai?" Ta ce"Me yasa ba a yi tuwo ba yau?" Ya ce"Shi ne abun b'acin rai? Wallahi ni kaina shiru na yi saboda farin cikinki, amma na gaji da cin tuwon nan". Ta ce"Gaskiya ni indai ban ci tuwo sau uku ko hud'u ba a sati ba na jin dad'i". Ya ce"To Baby ki dinga yi ranar girkinki mana". Ta ce"Aikinsa wahala yake ba ni, ita tun da ta saba ai sai ta dinga yi". Ya ce"To ki yi hak'uri zan yi mata magana". Ta ce"Yanzu me zan ci kenan? Ni ba cin sunasir nake ba". Ya ce"To me zan siyo miki?" Ta ce"Siyan abinci kuma? Ta dai dafa min wani abun". Ya ce"To ina zuwa". Ya fice. Ameera ta bi bayansa da harara, tana son sunasir, don sai da ta ci guda biyu, kawai so take ta nunawa Safiyya ta fi ta fada a wajen miji shi yasa ta yi hakan. Ya shiga d'akin Safiyya ya ce"Safiyya me yasa yau ba ki yi tuwo ba?" Ta ce"Baban Ni'ima na gaji da cin tuwon wallahi, kuma tuwon nan sai ranar girkina ake yin shi, na kasa ganewa". Ya ce"Ni kaina na gaji! Ameera ce take so shi yasa, ga shi yanzu ma ta kasa cin sunasir ashe ba ta ci, sai ki yi hak'uri ko taliya ce ki dafa mata". Safiyya ta ji takaici ya rufe ta, ta ce"Yanzu dama umarninta nake bi nake yin tuwo da garau-garau kullum? Ai kuwa wallahi ta ci na k'arshe! Kuma ba ta isa na tashi na mata sabon girki ba, wannan ai rainin hankali ne!". Ya ce"A'a Safiyya rufe ni za ki yi da duka kawai, to yaushe za ki tsaya kina zagina, ai dukan sai ya fi". Ta ce"Ni ban zage ka ba!" Ya ce"Umarnina kika bi ba nata ba, don haka ni za ki fad'awa na ci tuwon k'arshe, kuma ki zab'i d'aya ko ki wuce ki sama mata abin da za ta ci, ko ni na shiga na dafa mata". Ba ta ce komai ba ta fice, akwai sauran taliyar rana y'ar kad'an, da wacce su Ni'ima suka jagalgala suka barta, sai ta had'e su, ta d'auraye da ruwan d'umi ta tace, ta saka miya, ta nemi waje ta zauna a kitchen d'in, babu zato ta ji k'walla ta zubo mata, tana zaune k'alau da mijinta cikin nishad'i rana d'aya wata ta wargaza mata gidan da ba a san da yadda ta tsara shi ba, ko mai zai faru sai dai ya faru, amma ta saka a ranta ba za ta yi saken da za a raba ta da gidan da take jinsa kamar kabarinta ba. Tashi tayi ta fito, a tsaye ta tadda shi yana safa da marwa, ta ajiye farantin ta ce"Na dafa mata taliya baban Ni'ima saura me zan yi mata?" Sai ta ba shi tausayi, ya dake bai ce komai ba, ya d'auka ya fice, ya kai mata tana kwance a kujera tana danna waya, ya d'an yi murmushi ya ce"Ga taliya ta dafa miki tashi ki ci". Ta tashi a tsiwace ta ce"Taliya kuma? To wallahi ta rana ce, ita fa muka ci da rana!". Ya ce"Wallahi a gabana ta dafa, kuma idan ma laifi ne ni na yi saboda ni na ce ta dafa taliyar". Ta ce"To gaskiya ba zan ci ba". Ransa ya b'aci, ya ce"Amma kin san ba zan kuma saka ta aiki ba ko?" Ta ce"Ko siyo mini ne ka yi". Sai ya ji kunyar mai da taliyar nan Safiyya ta ga ba a ci ba, don haka ya zauna ya cinye ta ya sha ruwa, sannan ya koma d'akin Safiyya, ya so ya ci sunasir din da yawa, amma saboda ya ci taliya sai kad'an ya ci ya fita siyo mata wani abun. Washegari wajan goma na safe Ameera ta yi sallama a d'akin Safiyya, ta amsa sai ta shigo ta d'auki sallaya ta shimfid'a ta zauna ta mik'e k'afa tana danna waya, Safiyya ta yi mamaki, saboda ko gaisuwa ba ta had'a su, kuma tun ranar da aka kawo ta gidan ba ta sake shigowa d'akinta ba, ta kwashi mintuna ba ta ce komai ba kanta a kan waya. Safiyya ta ce"Ameera lafiya dai ko?" Ba ta kalle ta ba ta ce"K'alau". Safiyya ta d'auke kai, suna fira da yaranta, sha biyu ta yi Ameera ba ta da niyyar fita, ita kuwa Safiyya ba za ta iya barinta a d'aki ta tafi kitchen ba, don ba ta yarda da ita ba, don haka ta ce"Ameera zan shiga kitchen". Ta ce"To a fito lafiya". Ta ce"Dayake turare zan kunna sai na rufo k'ofar d'akin". "Ok!" Ta fad'a, sannan ta tashi ta fita. Safiyya ta bi ta da kallon ni ma a shirye nake, sannan suka fito da yaran sai da ta saka mukulli ta kulle d'akin sannan ta shiga kitchen. 08028966015 [5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA* (FID DA KAI) BY SADIYA ABDULRAZAK FIRST CLASS WRITERS Page 8 Tana shiga ta nemi kayan miya ta rasa, duk da jiya ta ga da saura da yawa, da za ta siya da kud'inta sai kuma ta fasa ta d'auki waya ta kira shi ta ce ya aiko kayan miya. Ya ce"Safiyya yau ma ba shinkafa da waken za ki yi ba?" Ta ce"E". Ya ce"To shi kenan, zan aiko". Ya aiko har da nama ta yi girkinta had'add'e, da daddare ma haka. Bayan ya gama cin abinci suna tab'a fira kamar gaske, ya ce bari ya shiga ya ga Ameera yau da wuri zai kwanta, yana shiga ya tarar da ita a falo tana kallo a TV, ta yi masa sannu ya amsa yana cewa"Y'an mata ya garin ne?" Ta ce"Ni dai gaskiya ana yi mini abin da aka ga dama a gidan nan". Cikin k'osawa ya ce"Me kuma ya faru?" Ta ce"Ka ce ta daina yin tuwo, yanzu shinkafa da waken ma ta daina? Bayan kasan shi ne favorite food dina". Ya ce"Ikon Allah! To gaskiya zan samar da maslaha a kan maganar girkin nan". Ya d'auki waya ya kira Safiyya, tana d'agawa ya ce"Ki shigo d'akin Ameera". Ta ce"Da dai ku d'in kun shigo nan". Ba ta jira cewarsa ba ta katse wayar, saboda ba za ta shiga ba d'in. Ya ce"Ameera taho d'akina". Sannan ya lek'a d'akin Safiyya ya ce ta shigo nashi d'akin. Suka zauna, ya ce"To Assalamu alaikum". Kafin su amsa ya d'ora"Wato Safiyya na fara gajiya da yadda kike neman kawo mini fitina saboda girki, idan na ce ga abin da za ki dafa sai ki k'i, saboda dama kin riga kin raina ni, to don haka na raba girkin nan, kowa ya dinga yin girkinsa, kowa ya dafa son ransa idan kashi mutum yake so ya dafa idan yaso in mutum ya dafa abin da ba na ci sai na siyo wani a waje, ko idan mutum ya yi kwab'a a girkin sai na yi ta kaina don ba za a kashe ni kwanana bai k'are ba". Safiyya ta ji dad'in hakan sosai, ta ce"Hakan ya yi, mun gode. Ya ce"Ameera ke fa?" Ta k'ara had'e fuska tana d'auke kai. Safiyya ta tashi ta fice, sannan Ameera ma ta tashi za ta fita, sai ya rik'o hannunta, ta ce"Malam sake ni! Ka gama ci mini mutunci a gabanta me kuma za ka ce mini?" Ya ce"Subhanallah! Mene ne na cin mutunci a nan? A ganina hakan zai fi ai, ke ki dafa abin da kike son ci ita ma haka". Ta ce"Amma ai da ka ce za a kasheka da ranka da ni kake, saboda rana d'aya an samu matsala da dafa kaza". Ya ce"Ba haka nake nufi ba, ita Safiyya ai ta san da ita nake, ko ba ki ji yanayin girkinta ba, duk ba ta iya ba? Wallahi ba da ke nake ba". Ta ji dad'i har sai da ta murmusa sannan ta bar d'akin. Da haka aka samu maslaha kowa yake yin girkinsa kuma yana mata cefane daidai gwargwado, bayan an kwana biyu watarana Safiyya ta je unguwa ba ta dawo da wuri ba, sai bayan isha'i, ba ta wani damu ba saboda ba ranar girkinta ba ce, tana shiga d'akinta ta gan shi a hargitse, kamar an yi mata bincike, ta kasa hak'uri har sai da ta tambayi mai gidan ko ya nemi wani abu a d'akinta ya ce bai shiga ba, ta nutsu ta duba tsaf ba ta ga alamar an d'auki komai ba, amma duk ta kamu da tsoron d'akin. Wata rana da safe tana had'a abun karyawa, ta kad'a k'wai tana jira doya ta dahu sai ta tafi yi wa Khausar tsarki, Ameera ta yi wuf ta fad'a kitchen ta dumbuzo gishiri ta zuba a cikin k'wan ta fice, Safiyya sauri take ta gama ta sallami mai gida shi yasa ba ta lura da tsinkewar k'wan ba, ballantana ta gane magi yayi yawa, sai da ta gama ta zuba masa, yana ci ya ji bakinsa fau! Da k'yar ya had'iye, ya tashi ya fice bai ce komai ba saboda takaici, sai da ta ci ta ji sannan ta fahimcesa, ta girgiza kai don ta san Ameera ce, saboda ita ba ta cika amfani da gishiri ba ma. Da rana Ameera ta karbi girki, tana ta iyayi tana girki, sai da ya kusa tsotsewa Safiyya ita ma da take kitchen d'in tana nata girkin ta d'akko ruwan kanwa da ta jik'a shi tun safe mai yawa ta juye a girkin Ameera, ta juya ta rufe mata, ta ci gaba da nata girkin, tana kallo ta gama ta juye a kula ta fice. Sai da daddare Mai gida ya dawo ta zuba musu za su ci don ko d'and'anawa ba ta yi ba, yana yin cokali d'aya, ya guntse baki yana rarraba ido, ya tashi ya fita waje ya tofar ya dawo ya sha ruwa ransa a b'ace, Ameera da ba ta fahimci komai ba, ta kai cokali d'aya bakinta, gabanta fa yad'i, ta kalle shi tana sosa kai, da k'yar ta daure ta cinye cokali d'ayan, ta ture palate d'in. Ya ce"Ya kika matsar da shi, ki ci mana!". Ta ce"Ban san yadda aka yi ya yi haka ba wallahi". Ya ce"Ni kuma k'addarata a girki za ta k'are kenan, ita da safe ta cika gishiri kamar makauniya, ke kuma yanzu na rasa ma me kika cika, abun dai ba a cewa komai". Ta b'ata rai ta juya kai gefe, a zuciyarsa ya ce'Wallahi ko fashewa za ki yi ba zan ci ba, haka kawai wancen karon na you gudawa wannan watak'il na mutu ma' Ya tashi ya fice, kai tsaye gidansu ya tafi, a can ya ci abinci, Hajiyarsa ta ce"Wai kai Salisu ya aka yi da matanka biyu ka zo nan ka zage kana cin abinci?" Ya ce"Babu komai Hajiya, wulak'anci kawai suke ji, yau idan wannan ta cika yaji gobe sai wannan ta cika gishiri to ba sai na hak'ura na bar musu ba, idan kuma na gaji wallahi wacce ta k'ware a girki zan auro". Hajiya ta had'e rai ta ce"Yau d'in Safiyya ce ta yi girkin?" Ya ce"Ina fa! Ameera ce wallahi, wani abinci babu fasali na rasa ma mene ne ya yi yawa". Hajiya ta tsuke fuska ta ce"To makircin Safiyya ne wallahi, ita ce take saka mata wani abun". Ya ce"Ai ita ma Safiyyar d'azu gishiri rangad'ad'au a doya". Hajiya ta ce"A haf! Ai kissa ce, saboda kar a zarge ta, mu wata irin kissa ce ba mu sani ba? To zan je da kaina na taka mata burki, Allah Ya sa dai ba ka bari ta raina Ameerar ba, don yadda kake son wannan busasshiyar kamar ita kad'ai ce mace". Ya ce"A'a Hajiya, babu wanu fad'a da suke yi, kuma Safiyya yanzu ai ta san matsayinta, saboda ni ta ba ni mamaki wallahi, a yadda na tallafi yarinyar nan ko wuta na ce ta shiga ai za ta shiga, amma sai ki ga akan abu k'alilan ta kafe kamar tsohon babur tana musu da ni". Hajiya ta ce"Ai abin da ake kokarin nuna maka kenan ka kasa ganewa, sai yanzu da ka fara dawowa hayyacinka!". Washegari Hajiya da kanta ta je gidan, wai ta zo gargad'in Safiyya, idan ta sake ji ta b'atawa Ameera girki sai ta yi ta igiyar aurenta, Safiyya ta ba ta hak'uri tana hawaye. Da ya dawo ta dinga kuka ta ce"Baban Ni'ima me na yi maka za ka had'a ni da Hajiya? Ameera ce ta ce maka ni nake b'ata mata girki? Mene ne ribata a cikin hakan? Ina ruwana da rayuwarku?" Jikinsa ya yi sanyi, ya ce"Ni fa ban ce kin b'ata mata girki ba, amma daga yau na saka doka duk wacce ta sake cewa an mata wani abu a girki ko ta yi girkin da na kasa ci gaskiya komai zai iya faruwa, ita ma zan fad'a mata, ya za ku saka kayan abinci a gaba ku dinga b'arnarsa?" Ya fice ita ma Ameera ya je ya yi mata gargad'i. Tun daga ranar Safiyya ba ta sake sakawa Ameera komai a girki ba, amma ita Ameera ta k'ara mata gishiri sau uku, sai dai ta zubar ta sake dafa wani, daga nan sai take zama a kitchen d'in har sai ta kammala girkinta, sai ta zuba a kula ta kai d'akinta. Daga nan kuma Ameera ta ci gaba da shigo mata d'aki haka kawai ta zauna kuma ba za ta yi mata magana ba, sau biyu Maman Affan tana tarar da ita a d'akin, idan ta shigo sai ta fita, har ta nunawa Safiyya ta hana ta, ta ce ta k'yale ta, da ta samu sake ma sai ta ga Maman Affan din ta shigo, ita ma sai ta zo d'akin ta zauna, ba za dai ta saka baki a firarsu ba, amma za ta zauna tana danna waya, watarana suna zaune a hakan Maman Affan ta b'ata rai ta ce"Safiyya za mu yi magana". Safiyya ta kalli Ameera ta ce"Ko za ki ba mu wuri?" "Ok!" Ta fad'a ta tashi ta fita, sai da ta koma d'aki abun ya dame ta sosai, tana so ta san abin da za su tattauna, saboda ta tsani wannan matar ba ta yarda da ita, kuma ta ga ko kallon kirki ba ta yi mata, kasa jurewa ta yi ta je k'ofar d'akin ta lab'e, amma ba ta jiyo komai ba, don haka ta d'an bud'a labulen kad'an ta lek'a ko za ta hango abin da ake yi, maman Affan da ta hango ta ta yi kamar ba ta ganta ba, ta d'auki gorubar da Khausar suka gama kokowa da ita, cikin shammata ta wurga ta jikin labulen, aikuwa ta samu Ameera amma ba ta samu idonta ba, da gudu ta shige d'akinta, ita ma maman Affan ta fito da gudun ta ce"Ni'ima ban hana ki lek'e ba?" Ni'ima da suke ta wasan su ba su san ma wainar da ake toyawa ba ta ce"Ba mu ba ne, ba mu lek'o ba". Ta d'aga murya ta ce"Duk munafukin da yake lek'e wataran sai na yi masa balaraben ido kuwa!". Safiyya ta yi dariya ta ce"Wallahi da kin k'yale ta, idan ta lek'o ma me za ta gani? Zargi ne kawai". A ranar da daddare baban Ni'ima ya kira Safiyya kamar abun arzik'i, ya ce"Safiyya daga yau na kafa dokar da karyata zai iya jawo miki babbar matsala!". Ta ce"Ina ji". Ya ce"Daga yau kar Maman Affan ta sake shigo mini gida, domin duk wata fitina na gano ita ce take haddasawa a gidana, wato bayan koya miki raina ni da taurin kai yanzu har tsubbace-tsubbace za ta koya miki?" K'irjin Safiyya ya yi wani irin bugu ta ce"Me kake nufi da tsubbace-tsubbace?" Ya ce"Me kuka binne ke da ita d'azu da ta zo?" A tsorace ta ce"A ina? Ni ce na binne wani abu?" Ya ce"Tashi mu je" Ya kunna fitilar wayarsa, ta bi bayansa saitin kanta duk ya kunce, gindin fanfo ya nufa wajen da suke da y'an shuke-sheke dama nan ne babu siminti, suna zuwa ita ma kallo d'aya ta yi wa wajen ta ga alamar an yi tono, ya ce"Tona ki ciro abinda kika binne da kanki!". Jikinta ya fara karkarwa saboda tsananin bak'in ciki, ta ce"Wallahi baban Ni'ima..." "Ki tona!" Ya daka mata tsawar da ta saka ta fashewa da kuka. Tana tonawa ba ta yi nisa ba ta ciro wani abu k'ulle a cikin tsumma, gabanta ya tsananta fad'uwa ta jefar da abun cikin furgici ta ce"Wallahi ba ni na binne ba, kuma ban san komai a kai ba". Ameera ta saki murmushin samun nasara daga windo da take lek'ensu ta ce"Kad'an ma kika fara gani". Rai a matuk'ar b'ace ya ce"Kin ba ni mamaki Safiyya! Ina kika kai tarbiyyarki? Tun da na k'ara auren nan da me na rage ki ke da yaranki da har sai kin kai ni wajen bokaye saboda ki raba ni da matata ko? To wallahi wannan ya zama na k'arshe don ban sani ba ko ba shi ne na farko ba, duk ranar da haka ta sake faruwa zan d'auki mataki". Ya wuce ya barta a wajen, ta fashe da kuka sosai, tana sake kallon k'ullin abun, sai da ta ci kuka ta more sannan ta tashi ta shiga d'aki, har lokacin jikinta rawa yake yi. Ameera kuwa farin ciki ya lullub'e ta, indai wannan k'aramin abun zai fusata Salis to kuwa tabbas watan barin Safiyya gidan nan ya tsaya cak, don a dabarun korarta da ta shirya wannan k'aramin abu ne, kukar nera hamsin ce fa ta siyo ta tsinto tsumma a hanya ta yaga ta juye ta ta k'ulle, duk a zaton ta ma abun ba wani tasiri zai yi ba, sai yau ta gwada saboda ta ji haushin abin da maman Affan ta yi mata, ta ce masa ya kula da maman Affan saboda tana lura da take-takenta, kuma yau ta ga suna binne abu a gindin fanfo. 08028966015 [5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA* (FID DA KAI) BY SADIYA ABDULRAZAK FIRST CLASS WRITERS Page 9 Da bak'in ciki sosai ta kwana, a ganinta ya kamata a ce ya tsaya ya saurare ta, tun da a tsawon zamansu bai tab'a kama ta da makamancin haka ba. Da sassafe ta jiyo shi yana k'wala mata kira daga tsakar gida, ta fito tana kallon shi yadda yake had'e rai, kallon sakanni ya yi mata ya kau da kai, daga ganin idonta ta yi kuka, har yanzu k'asan ransa yana son ta ba ya son ganinta cikin damuwa, haka indai ta yi masa laifi ta bi shi da wannan marayan kallon nata sai ya ji mugun tausayinta, don haka indai yana son hukuntata ba ya tsayawa kallon idonta. "Ga ni". Ta katse shurun Ya ce"Ki d'auki wannan k'ullin naki ki san yadda za ki yi da shi". Hawaye ya kawo idonta ta ce"Wallahi ban san komai ba a kan wannan abun, Allah ne shaidata". "Ki d'auke!" Ya daka mata tsawa. Sai ta d'auka ta je za ta saka a dustbin, ya ce"Ki fitar da shi daga gidan nan". Ta sako hijjabi ta d'auka ta fita ta jefar a waje, ta dawo ta ce"Na jefar". Ya juya ya shige d'aki, daidai lokacin da Ameera fito daga d'aki ta juya mata ido ta ce"Sai ki kiyaye". Safiyya ba ta ce komai ba ta shige d'aki, ko abun karyawa ba ta ba su ba, ta koma ta kwanta tana hawaye. MENE NE ALAK'AR SAFIYYA DA MIJINTA? Briged Nasarawa local government Kano state. Alhaji Muhammad d'an kasuwa ne da yake gudanar da kasuwancinsa a k'ofar Wambai, suna cikin rufin asiri da matarsa Maryam y'a'yansu biyu, Aminu shi ne babba, kuma daga kansa Allah bai kawo wata haihuwar ba sai da ya shekara goma sannan ta haifi Safiyya, kasancewar tana koyawa Aminu aikin gida yana taya ta, sosai yake taimakonta da rainon k'anwarsa idan aka tashi daga makaranta haka za su zo tare da d'an mak'otansu Salisu wanda Allah Ya d'ora masa son yarinyar, kusan ma ya fi Aminu iya rainon don haka Mama take yawan cewa ta ba shi ita, shi kuma sai ya yi dariya, akwai lokacin da Salisu ya had'o kud'insa 'yan canji da yawa ya kawowa Mama ya ce a siyawa Safiyya kayan sallah, abun ya ba ta mamaki da ya fad'a mata kud'in break dinsa ne yake tarawa, ta saka hijjabi ta je gidansu bayan sun gaisa da Hajiya ta ba ta wannan kud'in ta ba ta labari, Hajiya ta yi dariya ta ce"Haba ai ni ce ma nake yi masa bankin, tun da dai kun ba shi ita ai gara ya fara sauke nauyi tun yanzu, ana abu kamar wasa inda rabo sai ki ga ya tabbata, girman d'an mutum babu wuya". Mama ta yi godiya ta tafi. Tun daga nan fa Salisu komai ya samu na Safiyya ne, Safiyya tana shekara biyar a duniya Mama ta sake samun ciki, sai dai wannan karon ya zo mata da laulayi mai zafi, tana ta rashin lafiya, k'arshe dai abokin tafiya ne ta kusa haihuwa Allah Ya yi mata rasuwa, a lokacin Safiyya ba ta san ciwon kanta ba, ballantana ta san zafin rashin uwa, sosai Salis ya shiga damuwa da ya ji cewar Safiyya za ta koma can Ungogo gidan kakarta, ya dinga rok'on mahaifiyarsa don Allah ta karb'i Safiyya ta zauna a wajenta, har ta amince, sai dai Baban Safiyya da sauran y'an'uwa ba su amince ba, haka ya hak'ura aka kai ta can d'in, duk sanda Safiyya ta zo sosai yake shiga farin ciki, haka ita ma tana son Yaya Salis don yana kyautata mata fiye da Yaya Aminu, shi ma kuma duk sanda Aminu zai je tare suke zuwa, don shi Aminu a gidan yayan baban nasu aka bar shi bai je Ungogo ba, sai bayan shekara uku Allah Ya yi wa kakar Safiyya rasuwa, sai a lokacin ne kuma Baba ya ga dacewar ya yi aure, sai ya samu wata bazawara ya aure ta, ya d'akko Safiyya ya ba ta amanarta a lokacin shekararta takwas. Bayan shekara biyu. Yarinya ce y'ar kimanin shekaru goma, tsugunne a bakin wuta tana ta fifitawa, sai hayak'i take yi saboda yanayin damuna icen ba ya ci, da k'yar ta samu ta kama sannan ta tashi ta koma ta ci gaba da wanke-wanken da take yi, sai dai hayak'in ya taso mata da larurar idonta ta amosani, don haka k'aik'ayi ya addabe ta ta dinga murza idon babu k'akkautawa. Salis dake tsaye yana kallonta tun da take fifita wutar ya k'araso inda take ya yi tafi ya ce"Ya isa haka". Ta daina susar ta saki murmushi ta ce"Yaya". Ya ce"Na'am k'anwar Yaya ki daina sosa idonki, kin ga sai k'ara k'ank'ancewa yake, ya yi ja sosai". Ta ce"To zan daina, amma damuna yake da k'aik'ayi shi yasa". Ya ce"Yi hak'uri, ina fasa bankina zan kai ki asibiti, bari na taya ki". "To!" Ta fad'a tana matsawa gefe, don dama ta gaji, ya ci gaba da wanke-wanken suna fira. Umma ta lek'o daga d'aki tana ganin shi ta had'e rai cikin k'unk'uni ta ce"Ana ji ana gani an d'aurewa yarinya k'ara gindi tana karuwanci a cikin gida, ka yi magana a ce an ba shi ita, ai da an sani an d'aura auren tun yanzu. *A yi hak'uri na san ya yi kad'an, Allah Ya kaimu gobe*🙏🏻 [5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA* (FID DA KAI) BY SADIYA ABDULRAZAK FIRST CLASS WRITERS Page 10 "Tun da kin ba shi wanken-wanken ai sai ki yi shara" Suka ji muryarta. Safiyya ta tashi ta share gidan, ya fifita wutar sannan ya ba ta ɗari da hamsin kud'in littafin da ta ce za ta siya, sai uku Baba yana ba ta kuɗin Umma tana karɓewa, don haka jiya ta tambayi Salis shi yasa yanzun yana ba ta ta ɓoye. Baban Safiyya irin mazan nan ne da ba sa lura da gidansu sosai, ya yarda da matarsa saboda haka bai taɓa bibiya ya tabbatar da Safiyya tana rayuwar ƴanci a gidan ko akasin haka ba, ya wadata gidansa da komai amma Safiyya ba ta da ƴancin da za a kai mata wanki kuma ba ta da damar ɗaukar omo ta yi da kanta sai lokacin da ta ga damar bata, sam ba ta iya wankin ba jiƙa-jiƙa kawai take yi, sai kayanta duk suka dafe, Salis ya yi zaton omo ne ba a samu saboda haka yake siyo mata, sai Umma ta dake ta ta ce tana roƙo tana kai gulma a waje tana cewa ba a ba ta omo, kuma ta karɓe omon haka za ta yi ta saka kaya da datti, ba ta faɗawa kowa shi kuma Yaya Aminu sam ba ya janta a jiki ballantana ya san damuwarta, sai da abun ya dame ta ta faɗawa Salis, sai yake karɓar kayan nata ya tafi da su gidansu ya wanke ya goge ya kawo mata a ɓoye, don Umma ba ta taɓa sani ba. A lokacin shi yana da shekara ashirin, kuma yana aiki a gidan biredi, kullum da safe sai ya jira ta a ƙofar gida shi yake raka ta makaranta, ya ba ta kuɗin makaranta ya ba ta biredi tare da shayin da yake siyowa, Umma ba ta taɓa sanin haka ba, sai da wata maƙociyarsu ƙawarta ta kai mata gulma, a ranar ta ritsa Safiyya ta dinga dukanta don ce mata aka yi nama ne kullum yake ba ta, ta ce daga yau ta daina cin abincin safe a gidan tun da saurayi yana ba ta, ta raina wanda ubanta ya bayar, washegari sai ta hana ta zuwa makarantar ma, da safe ta gama wanke-wanke da shara tana ɗaki ta ji sallamar shi, saboda ya daɗe a ƙofar gidan yana jiranta, ya gaida Umma ya na tambayar Safiyya. Ta ce"Tana ciki ai, jiya da zazzaɓi ta kwana". Ya ce"Bari na ganta, ta sha magani?" Ta ce"Ai kuwa yanzu na leƙa na ga tana bacci". Jiki a sanyaye ya miƙa mata ledar ya ce"Ga wannan a ba ta idan ta tashi". Ta ce"Yawwa Salisu dama baban Safiyya ya ce a faɗa maka ka daina ba wa Safiyya abinci tana tafiya da shi makaranta, saboda ba ta rasa komai a gidan ba!". Ya ce"To na daina". Ya fice Umma ta bi bayansa da harara, sosai yaron yake ba ta haushi saboda a ganinta zaƙewarsa ta yi yawa, ta buɗe ledar ta ga shayi da biredi da naira hamsin, ta ce"Munafuka! Ashe har kuɗ'i yake ba ta". Safiyya tana leƙen komai ta windo, sai da Umma ta cinye tas sannan ta ƙwala mata kira, ta fito tana sosa ido, ta ce"Shirya ki tafi makaranta!". Ta shiga ta shirya ta fito ta ce"Ban karya ba". A fusace ta ce"Kuma ba za ki karya ɗin ba! Ba dai ke kin raina abin da ubanki ya kawo ba? Ai kuwa kin yi biyu babu, babu na gidan ba na kwaɗayin". Safiyya ta tafi ko kuɗin makarantar ba ta bata ba, kuma sai da aka yi mata dukan latti. Da yamma Salis ya zo duba ta da lemo da kankana, sai ya ji ta tafi islamiyya, Umma ta ce"Jikin ne na ji da sauƙi, ta ce ba ta so ta yi fashin islamiyya". Ya ba ta kayan dubiyar ya tashi, a ƙofar gida ya zauna har ta dawo, tana ganin shi ta ji sanyi a ranta tana murmushi ta ce"Yaya!" Ya ce"Ƙanwar Yaya, ya jikin?" Ta ce"Na ji sauƙi". Ya ce"Me ya kawo zazzaɓin? Ko wanka kika yi da tuwan sanyi?" Ta ce"A'a haka kawai ne". Ya ce"Na siyo miki kankana da lemo, sai kuma me za ki ci?" Ta ce"Ba komai". Daidai lokacin Yaya Aminu ya zo shiga gidan, ya sakar mata ranƙwashi a kanta ya ce"A nan za ki juye ladan makarantar ko?" Salisu ya ranƙwashe shi ya ce"Aminu wallahi ka kiyaye ni". Safiyya ta shige tana ɓata rai, idan da sabo ta saba, Yaya Aminu ba ya son ganinta da abokin nasa. Ita dai har lokacin bacci ya yi ta kwanta ba a ce mata ga abin da Salis ya kawo mata ba, washegari ya zo ya raka ta makaranta, amma bai ba ta komai ba, haka a gida Umma ba ta ba ta abinci ba kuma ba ta bata kuɗin makaranta ba, sai da aka yi sati ɗaya a haka, sannan watarana suna tafiya ta faɗa masa duk yadda aka yi, kuma ta faɗa masa ba a ba ta abun karyawa, tun daga ranar sai ya daina zuwa rakata makarantar sai dai ya jira ta a hanya, sai ya ba ta abun karyawa da kuɗin makarantar. Da haka suke gudanar da rayuwarsu cikin ƙauna da tausayi, har Salis ya samu wanda ya ɗauke shi yaron kasuwa kuma yana samu daidai gwargwado, duk wani banki da zai yi idan ya buɗe na Safiyya ne, ita yake yiwa hidima yayarsa ya sa ta tsaya a kan ciwon idonta tana kai ta asibiti har sai da ta warke, Baba ya yi iya ƙoƙarinsa a kan idon Safiyya, ya sha ba da kuɗin kai ta asibiti Umma ba ta kai ta sai ta cinye kuɗin, don haka rana ɗaya ya ga ƴar tasa ta warke duk a zatonsa da kuɗinsa ne. Duk sallah ɗinki kala biyu yake yi mata takalmi, mayafi da kuɗin barka da sallah, haka duk sati sai ya ba ta kuɗin kitso, duk wata kuma shi yake siyo mata pad, sannan haka kawai yana ba ta kuɗi ya ce ko za ta sayi wani abu, abin da Yaya Aminu bai taɓa yi mata ba, kuma shi ma yana samun kuɗin don Baba ya ja shi kasuwa. Lokacin da Safiyya ta kai shekara goma sha bakwai ta girma ta yi kyau sosai ƴar farar burwa mai matsakaicin kyau, doguwa mara ƙiba, a kaf unguwar babu mai cewa yana sonta don babu wanda bai san cewar matar Salis ba ce, a lokacin ta san wace ce ita, ta san so kuma abu ɗaya da ta sani Salis shi ne mai sonta da shi ta saba da shi kuma take burin gudanar da rayuwar aurenta har abada, sun yi wani mugun sabo da shaƙuwa ta yadda take jin kusancin su kamar ya fi na Yaya Aminu, ba ta shakkar tambayarsa duk abin da take buƙata, shi ma kuma ba ya ƙasa a gwiwa wurin faranta masa, ankon ƴan'uwa da na ƴan unguwa duk aikinsa ne, haka har lokacin bai daina yi mata wanki da guga ba. To babban ƙalubalen da suka fara fuskanta shi ne da ɗan'uwan Umma ya ga Safiyya rana tsaka ya ce yana son ta, Umma kuwa ta ce gida bai ƙoshi ba ba a kai wa dawa, yayinda Safiyya ta yi tsalle da dire ta ce ba ta da miji sai Salis, suka kai ta kai ruwa rana kafin Baba ya takawa abun burki ya ce tabbas Safiyya ba ta da miji sai yayanta, haka aka haƙura sai dai Umma ta ƙara tsanar Safiyya da zangwamarta, wani lokacin abinci ma ba ta bata sai dai idan tana jin yunwa sosai ta faɗawa Yayanta ya kawo mata abin da za ta ci. Ba a daɗe da saka aurensu ba Baba ya kwanta jinya, nan kuma wani abokin kasuwancin su ya zo dubiya shi ma ya ga Safiyya ya ce yana so, Aminu kuma ya yi masa alƙawarin zai same ta, yake ta karɓe ƴan kuɗaɗe a wajen mutumi, nan ya fara kushe Salis yana faɗa mata dama fa ya yi shiru ne amma Salis yana shaye-shaye, kuma yana taɓa neman mata, Safiyya ta yi tsalle ta dire ta ce ko me yake yi ta ji ta gani, akwai ranar da Aminu har dukanta ya yi, shi a ganinsa tun da ga babban mutum mai kuɗi ya zo me zai sa ta auri wani Salis, bai san cewa zuciya tana karkata bisa son wanda yake kyautata mata ba, a yadda take son Salis a lokacin har gara Aminu ya mutu Salis ya rayu. Shi Baba yana jinya bai san abin da suke toyawa ba, Aminu ya zagaye ya ja wannan Alhaji mai son Safiyya ya kai shi Ungogo ya dinga yi musu ɓarin kuɗi, nan ƴan'uwa duk suka amince, aka ce ba za a biye ta Safiyya ba ita har yanzu ba ta mallaki hankalin kanta ba, shi kuma Baba yana kwance kar a saka da shi ya zo ya shiga damuwa, su suka kitsa komai dama kuɗin auren da Salis ya kawo yana wurin yayan Baban, don haka suka ɗauka rana tsaka suka mayar gidan su Salis da sunan an fasa auren, saboda sun ji labarin yaro ba shi da tarbiyya. Sai da ran kowa ya ɓaci a dangin Salis, zance ya karaɗe unguwa ana cewa Safiyya da iyayenta butulu ne sun ci amana, sosai hankalin Salis ya tashi, lokaci ɗaya ya fita daga hayyacinsa, sassauci ɗaya da ya samu na ganin Safiyya har yanzu tana son shi shi ya tsayar da shi a kan ƙafafunsa, don da tuni shi ya kwanta jinyar, wani irin yanayi Safiyya da Salis suka shiga mara misali, kullum cikin damuwa suke, kaca-kaca aka yi tsakanin Salis da Aminu, akan kuɗi aka yi fatali da abota tun ta ƙuruciya. Kamar yadda Aminu da sauran dangin Safiyya suka tsani Salis ɗin da yake neman yi musu katanga da haɗa jini da mai hannu da shuni haka su ma dangin Salis suka tsani Safiyya, saboda zargin butulce wa wanda ya yi mata hidima tun tana yarinya. Ƙarshe dai da ruguntsumin ya yi yawa a dole Baba da ke kwance ya ji komai, sosai ya shiga baƙin ciki, jikinsa ya rikice ya ba da umarnin ko bayan ransa Salis ne mijin Safiyya muddin shi ne ya haife ta, ba da son rai ba haka limamin unguwar ya tara su don yin sulhu, aka ce Salis ya dawo da kuɗin aure, inda dangin Salis suka ce sun fasa ba zai aure ta ba, shi kuwa ya yi tsalle ta dire ya ce ba shi da mata sai ita. Ƙarshe dai da ƙyar aka sasanta, a ka tsai da ranar auren wata ɗaya a maimakon wata biyar da ya yi saura, Baba ya ba da umarnin a ɗauki kuɗi a yi wa Safiyya komai na aure, amma saboda baƙin cikin ta yi musu taurin kai suka ƙi yi mata komai, dangin babarta dai sun haɗo mata kayan kitchen, don sai a na gobe ɗaurin auren aka san ma ba a yi mata kayan ɗakin ba, ga shi rabin kayan lefenta Umma ta kwashe ta siyar kuma suma dangin nasa sun rage kaya sosai kafin su kawo. Dangin babarta sun nemi idan an ɗaura auren a ɗaga tarewar zuwa sati biyu, su harhaɗa su mata kayan ɗaki, Aminu ya yi rantsuwar ana ɗaurawa ba za ta sake kwana a gidan ba, haka ta faɗawa Salis tana ta kuka, shi ma ya ce ba za a ɗaga ba, ya kwantar mata da hankali sosai, a ranar ɗaurin auren kuma ya siyo mata kujeru da kayan gado, ai kuwa sosai ya sha faɗa a wajen Hajiyarsa ta ƙara tsanar Safiyya sosai. Haka aka kai ta gidan miji ƴan'uwanta suna fushi da ita, Aminu ko cokali mai siya mata ba, ta tare rai babu daɗi. Amma dayake suna ƙaunar juna sai komai ya wuce cikin ƙanƙanin lokaci, suka fara shimfiɗa rayuwa cike da nishaɗi, har ta kusa haihuwar Ni'ima Aminu ba ya ɗaukar wayarta, haka sun yanke alaƙa da Salis, sai da ya fara son ƙawarta Salma sannan ya nemi taimakonta ta kuma shige masa gaba har aka yi auren dalilin shiryawar su kenan, Baba kuma ya samu lafiya ya ci gaba da harkokinsa yana sakawa auren su albarka. [5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA* (FID DA KAI) BY SADIYA ABDULRAZAK FIRST CLASS WRITERS Page 11 Da daɗi da babu daɗi aka shafe wata uku da ƙarin auren Salis, ashe Ameera ta samu ciki watansa biyu Safiyya ta yi tunanin hakan a lokacin da take laulayi, amma Salis yake ta maimaita mata maleria ce take damunta, haka ta taɓa ji daga bakin yayarta da ta zo dubiya tana cewa"Oh! Wannan malaria ta sako ki a gaba, Allah dai Ya yaye". Su ma ƴan'uwan shi da suka zo dubiya ta ji suna zancen malaria, ita dai ba ta ce komai ba, tana dai yi mata sannu, don amai take yi sosai, ga yawan zazzaɓi da take yi, ko girki ba ta iya yi, dama sharar tsakar gida gyara kitchen da wankin banɗaki tun da ta zo ba ta taɓa yi ba Safiyya ce take yi, da ta ga yadda take jin jiki sai ta yanke shawarar ta dinga yin girki da ita, amma Salis ya ce Hajiya ta ce za ta dinga aiko mata abinci, haka kuwa aka yi kullum sai ta aiko mata abincin rana da na dare, da safe kuma shi da kansa yake haɗa mata shayi, ita dai ta ɗauki ido ta zuba musu. Watarana ta dama kunu da safe Ameera ta kira Ni'ima ta ce ta je ta ce a sammata kunu, Safiyya ta zuba mata ta kai mata da kanta, Salis ma ya sha ya tafi kasuwa, babu jimawa ta ji sallamar Yaya Fa'iza, lokacin tana tsakar gida tana wanke-wanke, ta ɗan saki fuska ta ce"Yaya ce? Sannu da zuwa". Ta haɗe rai ta ce"Yawwa!" Ta wuce ta shiga ɗakin Ameera, can sai ga Salis ya shigo, ya shiga ɗakinta, da mamaki ta ce"Mantuwa ka yi ne?" Ya ce"Ban sani ba! Safiyya me kika saka mata a cikin kunu?" Da firgici ta ce"Wa kenan?" Ya ce"Ameera mana! Daga ba ta kunu ta sha, ta fara ciwon ciki, to wallahi idan wani abu ya samu cikin nan ba zan bar ki ba!". Kafin ta dawo daga mamaki ta ji Yaya Fa'iza tana faɗin"Ka fito mu tafi asibitin kafin burinku ya cika, ai laifinka ne, sai da a ka gargaɗe ka kar ta ji zancen cikin nan, amma ka zagaye ka faɗa mata, ga shi yanzu za ta zubar da shi". Tuni ƙwalla ta kawo a idonta, ta fito tana rarraba ido ta ce"Wai me kuke nufi ne? Me ya samu Ameerar?" Yaya ta zaburo ta ce"Ke dalla rufe mana baki! Makircinki a kanki zai ƙare in sha Allah!". Ta wuce ɗakin Ameera Salis ya bi ta, tana nan tsaye sai ga shi Yaya ta ruƙo Ameera take ta ciccijewa tana sunkuyawa riƙe da ciki, a gabanta suka fice daga gidan, ta zauna a nan ƙofar ɗaki ta yi shiru tana tunanin mafita, a yanzu ta karaya da makircin Ameera kuma ta lura muddin ba ta ɗauki mataki ba, sai ta raba ta da igiyoyin aurenta, amma ta wace hanya za ta samu mafita? Salis bai san kissa ba, duk abin da ya gani ko ya ji ba ya bincike yake yanke hukunci, ya yarda da matarsa sosai ta yadda har ya manta wace ce ita, ya manta abin da za ta yi da wanda ba za ta yi ba, amma babu komai tun da ita makirci ta riƙe ita kuma za ta riƙe Allah ta ga tsakaninsu wanda zai yi kyakkyawan ƙarshe. Sai bayan azhar suka dawo daga asibitin, lokacin ta gama girki tana ɗaki a zaune, har da ƴan'uwan Ameera aka zo, tana jiyo su suna ta zage-zage, daga zantukan nasu ta gane cikin bai zube ba, ita dai ta yi shiru a ɗaki, har suka gama suka tafi. Bayan la'asar ta fito za ta shiga kitchen ta ga Ameera za ta shiga banɗaki, Safiyya ta tsarkake zuciyarta ta ce mata"Ya jikin?" Ta juya ido tana murmushi ta ce"Jiki Alhamdulillah". Safiyya ta shige ta barta, da wuri ta gama girki ta shiga gidan maman Affan, tun sanda ya ce kar maman Affan ta sake shigowa ba ta sake shigowar ba kuma ba fushi ta yi ba, ta fahimci Safiyya sosai don haka ta daina shigowa saboda sama mata maslaha, amma ita Safiyya tana shiga, kuma kullum suna chart, abin da ya faru ya yi mata ciwo sosai kuma ita ce abokiyar shawararta soboda haka duk ta ba ta labari, maman Affan ta ce"Tabɗijan! Lallai kin gamu da makira, ga ki ke kamar ruwa ba ki da wani zafi, idan an ba ki dabara kuma ba kya iyawa". Ta yi huci ta ce"Ko na yi ni nake kwana a ciki daga ƙarshe, saboda baban Ni'ima yanzu babu ni a zuciyarsa, yana zaune da ni ne kawai don ba shi da dalilin da zai faɗa idan ya sake ni". Maman Affan ta ce"Haka dai za ki dage ke ma ki dinga yi mata kissar nan fa, wani wajen idan an faɗi a wani riba za a ci". Da wuri ya dawo saboda yanayin jikin nata, tana zaune tana danna waya, da ta ji shigowarsa ta ajiye ta kwanta, ya ga ɗakin Safiyya a kulle, ya shiga nata ɗakin, ya ƙarasa yana taɓa goshinta ya ce"Sannu ya jikin?" Ta ce"Da sauƙi, cikin dai har yanzu bai daina ba, ni tsoro nake kar cikin nan ya zube". Ya ce"Sun ce zai daina, kuma ba zai zube ba in sha Allah!". Ya ce"Safiyya fita ta yi?" Ta ce"E tun kafin la'asar Maman Affan ta zo suka fita, ni fa na yi shiru ne ma don a zauna lafiya amma..." Ya tattara nutsuwarsa ya ce"Mene ne". Ta ce"Shi kenan dai an ce zato zunubi". Ya ce"Baby ki faɗa min mana, me kike zato?" Ta ce"To ni dai jiya Maman Affan ɗin nan ta zo sun fita unguwa da Safiyya, to da suka dawo ni na leƙo ina neman ɗan aike, su kuma sun dawo suna ƙofar gidanta, sai na ji tana cewa Safiyya, wannan a kunu za ki saka mata, amma ni na za ta ko yaranta ta karɓowa magani". Ƙirjinsa ya fara bugu, ransa ya yi matuƙar ɓaci, ya tashi a fusace ya ce"Wato da gaske Safiyya so take ta ga bayan cikin nan!". Cikin muryar marasa lafiya Ameera ta ce"A'a fa zato zunubi, ni ma abin da ya sa na yi zargin saboda na ga haka kawai ta kawo mini kunu". Rai a ɓace ya ce"To ke ma ban da kwaɗayi kin ji su suna zancen amma yau ta ba ki abu ki sha?" Ta marairai ce ta ce"Tsautsayi dai". Ya ɗauki waya ya kira Safiyya. Suna cikin fira wayarta ta yi ƙara, ta duba ta ga shi ne mai kira, ta ɗaga da sallama, ya ce"Kina ina?" Ta ce"Ina maƙota". Ya kashe, ta tashi ta ce"Bari na je ina ga ya dawo". Tana yin sallama ya fito ya tare ta a tsakar gida. Ameera ta bi bayansa da gwalo ta tashi tana leƙo su ta windo. A fusace ya ce"Da izinin wa ki fita?" Ta ce"Nan maƙota ne fa, na ga ina shiga kuma kai ka ce ba sai na tambaya ba". Ya ce"Ban raba ki da maman Affan ba!?" Ta ce"Ka ce dai ta daina shigowa, amma ba ka raba mu ba". Ya ce"Tun da ke yarinya ce sai na yi miki dalla-dalla kenan! To ina nufin babu ke babu ita har abada, tun da ba mutuniyar kirki ba ce, so take ta hargitsa mini gida ta hana ni zaman lafiya, da hankalinki da wayonki ta koya miki bin bokaye?" "Bokaye!?" Ta tambaye shi ranta a ɓace. Ya ce"E mana, idan ba haka ba ina kuka je jiya kuka karɓo abin da kuka sakawa matata a cikin kunu!?" Safiyya ta ce"Baban Ni'ima ba ni da bayanin da zan yi maka, saboda ko na yi ba za ka fahimta ba, amma a nan gaba za ka gane matuƙar muna tare, ban taɓa zuwa wurin boka ba, kuma miji ko kishiya sun yi kaɗan su saka ni na yi shirka!". Ya ce"Ni dai daga yau babu ke babu matar nan, kuma zan samu mijinta na faɗa masa, idan na sake ganinta a gidana kotu ce za ta raba mu! Ke kuma kin yi na farko kin yi na ƙarshe wallahi ko mene ne ya samu cikin matata ke ce, kuma ba zan yafe ba! Ban da kin shirya makirci akan me za ki ba ta kunu?" Safiyya ta haɗiyi yawu mai ɗaci, ta shige ɗakinta, ya biyo ta ya ce"Ina yi miki magana kin bar ni saboda kin mai da ni wawa ko?" Har ya yi rashin mutuncin da zai iya ya gama ba ta ɗaga kai ta kalle shi ba, haka ta kwana zuciyarta cunkushe da baƙin ciki, da tunanin mafita. Bayan sati ɗaya Safiyya ta yi mopping ɗin kitchen, ta fito tana share tsakar gida, ta jiyo Ameera da ta shiga kitchen ɗin ta ƙwalla ƙara, gaban Safiyya ya faɗi, Ameera ta ƙara ƙwalla ƙara, sannan ta nemi waje ta kwanta a kitchen ɗin, Safiyya ta ci gaba da shararta tana karanto addu'ar neman tsari daga musifa, yayin da Salis ya fito da gudu-gudu daga ɗakinsa yana faɗin"Ameera mene ne!?" Sai da ta yi ƙara na uku sannan ya gano inda take, a guje ya shiga kitchen ɗin, yana shiga ya yi wata wawuyar sufa suuuu ya tiƙu da ƙasa, a ɗaga kai ya kalli Ameera da take wanwar tana riƙe da ciki. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!". Ya furta ya na tashi zaune, ya riƙo ta ya ce"Me yake faruwa ne?" Ameera ta ce"Wayyo bayana da marata, ina shigowa na ji santsi ya kwashe ni". Yana tashi tsaye don ɗaga ta, santsi ya ƙara kwashe shi, sai a lokacin kuma ya ga abu kamar miyar kuka a ƙasa, har kayansa sun ɓaci". Ya ƙwallawa Safiyya kira, ta shigo ganin yanayin da suke ta ce"Subhanallah! Me ya faru?" Salis ya ce"Wane irin wulaƙanci ne za ki zubar da miya mu taka mu faɗi?" Ameera ta fashe da kuka ta ce"Karkashi ne wallahi, na ji ƙamshinsa, maman Ni'ima me na yi miki za ki jiƙa karkashi ki zuba min? Me cikin jikina ya miki? Ko mene ne ai da ni za ki yi shi babu ruwansa". Ta fashe da kukan ƙarya. Don a jiƙe ta taho da karkashinta, ta zuba shi a ciki ita sam ba shi ne ya kada ta ba. Safiyya ta ce"Duk abin da kika yi mini Allah Ya yi miki! Aniyarki ta bi ki! Kuma Allah ya yi mini sakayya, ke da ƙaunar miji da ɗaurin gindinsa kike neman ganin bayana, ni kuma da Allah na dogara". Ta fara kuka ta ce"Baban Ni'ima ka nutsu kafin ka yarda da maganarta, ka san tun ina yarinya ba na cin miyar karkashi, haka ba ka taɓa ganin karkashi a gidan na ba, me ka yi mini da zan so ganin bayan cikin matarka? Ka yi mini adalci!". Ya ruƙo Ameera suka dab da fita daga kitchen ɗin ta kalli Safiyya ta yi mata siririn gwalo, ba tare da ta yarda Salis ya gani ba, ya kai ta ɗaki ya kwantar da ita ya ɗakko waya ya ce"Bari na kira Yaya mu tafi asibiti". Ta riƙe hannunsa ta ce"A'a, na ji ma cikin ya lafa, bari zuwa anjima idan na ji wani abun sai mu tafi, kuma ma ba na so ka kira wani sai su ga laifin matarka, irin wannan babu daɗi a yi ta cewa tana yi mini abu". Ya ce"Ai ta yi na ƙarshe, don yau ba za ta kwana a gidan nan ba!". Ya fice, ya shiga ɗakin Safiyya zaune ya tarar da ita tana sharar ƙwalla. Ya ce"Safiyya me Ameera da cikinta suka tsare miki a gidan nan?" Ta ce"Babu komai". Ya ce"To me yasa kike son ganin bayansu?" Ta ce"Ban yi mata komai ba, Allah ne shaidata, amma ban ce dole ka yarda da ni ba, idan ba ka yarda ba duk hukuncin da ka yanke zan karɓa". Ya ce"Gaskiya Safiyya halinki ya canza tun da na ƙara auren nan, Ameera tana zaune da ke da zuciya ɗaya, wallahi wancen na kunu ma sai ce mini take zato ne, kuma zato zunubi ne, a wannan karon ma yanzu ita ta hana ni kiran kowa saboda ba ta so a ga laifinki, to a gaskiya wannan shi ne na ƙarshe, duk ranar da haka ya sake faruwa ba za ki kwana a gidan nan ba!". Ta ce"Na gode, amma zan tafi tun yau kafin ya sake faruwa". Ta tashi ta ɗakko jaka ta fara zuba kaya. Ya ce"Ni ban ce ki tafi ba tukunna". Ta ce"Gara na tafi saboda na san sai ya ƙara faruwa, na haƙura da aurenka, zan gwada rayuwar da babu kai na gani duk da na san ba abu ba ne mai sauƙi rabuwa da wanda ka saba da shi, na gode da komai". Lokaci ɗaya jikinsa ya yi sanyi, yana son Safiyya halayen da take tsiro da su ne kawai yake jawo musu matsala, a hankali ya ce"Kar ki tafi". Ta ce"Ta ya zan zauna ina cutar matarka da ɗan cikinta? Ai gara na tafi ɗin". Ya ce"Ya wuce, amma don Allah ki dinga tunani kafin ki yi wani abun, kishi fa ba hauka ba ne!". Ya fice jiki a sanyaye. Ta matsar da jakar ta fashe da kuka tana kallom ƴaƴanta da suke rakuɓe a gefe suna kallon ta, ta gama kuka ta share hawaye, ta haƙura da tafiyar, tun da idan ta je ma ba ta san me za ta ce ba, kuma ya yi mata umarnin kar ta tafi. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE A KAN NAIRA 300 KACAL! SAURA SHAFI ƊAYA FREE PAGES SU ƘARE, ZA KI IYA TURA KUƊINKI A ACCOUNT ƊIN NAN 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank Ki tura shaidar biya ta 08028966015 Ko katin mtn na 300 [5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA* (FID DA KAI) BY SADIYA ABDULRAZAK FIRST CLASS WRITERS Page 12 Ya shiga ɗakin Ameera ya zauna, jikinsa duk ya yi sanyi, Ameera ta ce"Ta tafi?" Ya ce"A'a, na ɗaga mata ƙafa dai". Ta ji baƙin ciki ya rufe ta, amma ba ta nuna ba ta ce"Yawwa har na ji daɗi, wallahi ba na so a ce ka kori matarka ta sanadina, mutane ba za su duba abin da ta yi mini ba, sai dai su ce laifina ne na shigo zan raba ku". Ya ce"Ya wuce, amma don Allah ki dinga kiyayewa, irin wannan mutum ya na harin abin da yake cikinki dole ki kiyaye shi, kin ga yanzu ko dambe ne ya tashi ba za ki yi da ita ba, ki bar mata kitchen ɗin tun da ba girki kike yi ba". A zabure ta ce"Kana nufin na kwashe kayana na bar mata kitchen!?" Sai da ya yi mamaki, ganin ƴan mintinan da suka wuce muryarta kamar ta dashe tana marairaicewa amma lokaci ɗaya ta saki muryarta ta zaburo, saboda ta ji maganar barin kitchen. Ya ce"Ba haka nake nufi ba, nufina tun da yanzu ba girkin kike yi ba sai kin ji sauƙi, idan ma abu za ki ɗauka a kitchen ɗin sai ki kira ƴarta ki aike ta, ai kema ƴaƴanki ne, kin ga ai ba za ta sakawa yaranta karkashi ba". Ta ce"Hmm! Allah dai Ya sa ta gane gaskiya, ni na fi so mu zauna lafiya kamar ƴan'uwa, mu dinga gasar kwantar maka da hankali ba tada maka ba". Ya ce"Ba komai kishi ne amma Safiyya da ba haka take ba ita ma". Da yamma Safiyya suna zaune tana koyawa yaranta karatu, Ameera ta kira Ni'ima ta shiga ɗakin, ta miƙa mata mafici tana zazzare ido ta ce"Riƙe ki yi mini fifita, ai ubanku ne ya min cikin!". Ni'ima ta tsorata da zare mata idon nan, ta karɓa ta fara yi mata, har bacci ya fara ɗaukarta Ni'ima tana ta yi, ta haɗa gumi ta gaji sai ta ajiye maficin tana so ta fara kuka. Ameera ta ce"Ba za ki yi min ba? Ubanku ya haɗa ni da wahala na sha wahalar ni kaɗai?" Ni'ima ta ci gaba da yi mata, tana ɗan matso ƙwalla, sai da bacci ya fara ɗaukar Ameera ta ajiye maficin ta fice da gudu, Ameera ta biyo ta ita ma a guje, Safiyya da tun shigar Ni'ima ɗakin hankalinta ya ƙi kwanciya kasancewa ba su saba shiga ba, don Ameera ba ta shiga harkarsu, tana ganin fitowar Ni'ima a guje ta miƙe tsaye ta faɗa jikinta tana fashewa da kuka, Ameera ta kai hannu za ta fizgo ta, Safiyya ta riƙe hannun ram ta ce"Baiwar Allah ƙalau kuwa?" Tana huci ta ce"Ni zan saka yarinyar nan fifita ta gudu?" Ta kai mata duka. Safiyya ta ce"Haifarta kika yi da za ta miki fifita? To wallahi ko da wasa kar ki yi zaton za ki dakar mini ƴaƴa na ƙyale ki!". Ameera ta ce"Me za ki yi?" Ta tura Ni'ima gabanta ta ce"Dake ta sai ki ga yadda zan yi!". Ameera ta yi ƙwafa ta ce"Zai dawo gidan na ji idan shi ya ɗaure gindin kar na mori ƴaƴan shi!". Safiyya ta ce"Allah Ya dawo da shi! Saboda rainin hankali ko ni da na haifi ƴar ban saka ta fifita ba sai ke? Ki jira ki haifi naki sannan ki yi iko!". Ameera ta ce"Kwana nawa ne maye ya yi amarya? Ni da zan haifo magajin mai gida ma! Kuma a yau idan na yi niyya wallahi sai kin bar gidan nan, kuma na sa ya karɓi yara ya ba ni na ga ƙarshen taƙamarki!". Safiyya ta ce"Don Allah kar ki fasa!". Ta haɗa kan ƴaƴanta suka shiga ɗaki. A shirye take da jiran dawowar tasa ta ji ta inda zai ɓullo, sai ta ji shiru har washegari bai ce komai ba. Da rana Salma matar Yaya Aminu ta zo ta kawo mata kayan baccci kala uku da Aminun ya siyawa Safiyya, Salma tana ƙaunar Safiyya sam babu ruwanta da kalmar dangin miji, ita ta koyawa Aminu kyautatawa ƙanwarsa, don indai ya siyo mata abu sai ta ce ina na Safiyya? Idan abu ta gani ya burge ta kuwa haka za ta nuna masa ta ce ya ba ta kuɗi ta siyo musu ita da Safiyya, shi kuma Allah Ya ɗora masa ƙaunar matarsa, irin mazan nan ne ma su bautawa mata, sam ba ya mata musu, yanzun ma haka ya siyo kayan baccin guda uku, ta ce saura uku, shi ne sai jiya ya kawo yau ta kawowa Safiyya, bayan sun gama gaisawa Salma ta yi mata raɗa sannan suka fita tsakar gida suka shimfiɗa tabarma, Ameera tana zaune daga ƙofar ɗakinta tana chart, Safiyya ta shiga ɗaki ta fito da ledar da Salma ta shigo da ita, Salma ta ce"To me muka samu?" Safiyya ta ce"Me na samu dai, abun arziƙi ne jiya baban Ni'ima ya siyo mini". Ƙirjin Ameera ya yi wani sauti dum! Ta ƙyallo gefen ido, daidai lokacin da Salma take ɗaga kayan bacci, ta yi wata guɗa ta ce"A lallai baban Ni'ima ashe har yanzu bai daina siyo miki wannan kayan harka ba". Safiyya ta ce"Ai shi indai muka ɗan samu matsala ya min faɗa ina fara fushi duk sai ya rasa nutsuwa, sai ya yi ta min siyayya yana ba ni haƙuri ko kuma haka kawai na ga alert". Salma ta ce"Ashe bai manta ba, da tsohuwar zuma ake magani, kuma ya ga babu ciki babu goyo ya ce bari na dawo nan na buɗe sabon amarci". Suka tafa suna ta shewa. Ameera ta kumbura, sai dai tana shakkar anya da gaske ne kuwa? Ba ta gama sarewa ba sai da Safiyya ta shiga ɗaki ta ɗakko kuɗi ta miƙawa Salma ta ce"Ga kuɗin ankon Fati, sai jiya ya ba ni". Salma ta ƙirga kuɗi ta ce"Yo ya na ga dubu ashirin? Ai atamfar dubu takwas ce". Safiyya ta ce"Ai da yake na ce har da mayafi za mu yi anko, ki sai min atamfar sauran ki bawa Yaya Aminu ko yashi a siya a ƙara wani abun a ginin gidana". Sauran ƙiris Ameera ta ƙware da yawun bakinta, ganin baƙin ciki zai daskarar da ita a zaune sai ta tashi fuuu ta shige ɗaki, Salma ta bi bayanta da gwalo, suma suka shige ɗaki, kafin ta tafi sai da ta kwantarwa Safiyya da hankali sosai, ta kuma kawo mata wasu kayan aiki ta ce ta gwada, ta yi alƙawarin za ta gwada duk da a tsorace take, gani take kamar za a gane. Da daddare yana dawowa ya yi ɗakin Ameera kasancewar ranar kwananta ne, tana zaune ta kasa saita zuciyarta ballantana ta kalle shi, ya na ajiye ledar hannunsa ya ce"Baby!". Ta ce"Salis don Allah kar ka sake ce mini Baby! Ga Baby can a ɗakinta!". Ya ce"Subhanallah! Me ya faru kuma?" Ta ce"Ashe dama duk bambamin da kake yi idan matarka ta taɓa ni na ƙarya ne? Ashe a bayan idona ta fi ni daraja? Wato kawai kana yi ne don kar su Hajiya su gane ba ka karɓe ni hannu biyu-biyu ba!" Salis ya tsani faɗan rashin dalili, don haka a ɗan hasale ya ce"Ya kike ƙoƙarin zagina ne!? Me ya faru, me na miki!?" Kamar za ta yi kuka ta ce"Wancen satin na tambaye ka kuɗin ankon babbar ƙawata ka ce mini na yi haƙuri akwai kuɗin da kake tattarawa tukunna, ashe Safiyya kake tattarawa kuɗin, ka siyo mata kayan bacci, sai ka saka ni a ɗaki ka dinga ce mini yanzu ka san ka yi aure, ashe doluwa ka mayar da ni!". Salis ya rasa ta inda zai fara, saboda sam bai fahimci komai a maganarta ba, ta tashi za ta shige ɗakin gado, ya riƙo hannunta, ta fizge ta ce"Malam sake ni! Ba ka da abin da za ka faɗa mini". Ta shige ɗaki, ya bi ta ta kwanta a gado ta fara kuka, ransa ya fara ɓaci amma ba ya son ganinta a damuwa ko dan ƙaramin cikin da yake jikinta, ya ce"Haba Baby, don Allah ki mini bayani". Ta ce"Ashe matarka har fili ka siya mata take ginawa ko?" Dariya ya ɗan yi ya ce"Safiyyan ce me gina fili?" Ta ga raina mata hankali yake son yi, don haka ta ce"Shi kenan yanzu na san matsayina, don Allah je ka!". Ya ɗaga kafaɗa alamar babu damuwa, ya fita saboda ya ga kamar ba ta cikin nutsuwarta daga baya ta yi masa bayani idan ta shirya. Haka aka bar zancen ba ta sake yi masa ba, shi ma bai yi mata ba, abun ya mata ciwo sosai don haka ta faɗawa babarta, ita ma sosai ta ƙara tsorata Ameera ta ce"Gini kuma? To ashe ma ta gama yashe shi tsaf, tana ta tatsar shi tana gini saboda ke wawuya ce kina ƙafafar kin karɓe gida ke ce mace? Ashe bariki suke yi miki ita da shi ɗin? To wallahi ki tashi tsaye, ki matse lamba dole ke ma ki samu naki filin kafin ki haihu, idan ya so wanda za mu yaga idan kin haihu sai a fara ginin da shi!". Ameera ta gamsu sosai, kuma ta saka a ranta tun daga yanzu za ta fara yi masa bani-bani ko da cikin jikinta ta fake ai za ta tara. Bayan kwana biyu Salis ya wayi gari da wani abin al'ajabi, ya nemi gajerun wandunansa kaf ya rasa ko ɗaya, abun ya ba shi mamaki har sai da ya tambayi matan nasa, duk suka ce ba su gani ba, haka ya siyo wasu ya saka a zuciyarsa babu abin da zai faru aikin jinnu ne. Kwana uku da faruwar haka da safe zai kai Ameera asibiti don ta ce kwana biyu ba ta jin motsin cikinta, so ta yi ko dubu goma ce ya ba ta ta fara tarun da ita sai ya ce su je ya kai ta asibitin a gani, ta ji haushi sosai, tana tunanin me za ta ce idan aka yi scanning aka ga lafiya lau? Kuma dama cikin bai fara motsi ba ma, so take ta ɓata masa lokaci ya gaji ya ce ya yi lattin tafiya kasuwa sai ya ba ta kuɗin ya ce ta tafi, don haka take ta jan jiki tana nuƙu-nuƙu, ya gama shiryawa yana tsaye a tsakar gida sannan ta fito ta shiga wanka, Safiyya ta fito ta ce"Baban Ni'ima don Allah dubo min takardar haihuwar yaran nan, Baba ne ya ce zai turo a karɓa ban san me zai yi ba". Bai ce komai ba ya shiga ɗakin nasa yana tsaki. Har karkarwa take ta yi sauri ta shiga ɗakinta ta buɗe sif ta ɗakko wata babbar ƙwarya ta fito ta yi wuf ta faɗa ɗakin Ameera, ta ajiye a kan kujera, ta ɗauki doguwar rigar da ta cire kafin ta shiga wanka ta lulluɓe ƙwaryar ta fito da sauri ta koma ɗakinta, tana sauke ajiyar zuciya. Har ya ɗakko takardun Ameera ba ta fito ba, don haka tana fitowa ya bi ta ɗakin yana cewa"Don Allah ki yi da jiki!". Ameera tana tura baki gaba ta janyo rigarta don ta shigar da ita ta saka a kwandon kayan wanki, nan ƙwarya ta bayyana rufe da faifai kamar za a ga nono a ciki. Daga ita har shi mamaki suka yi, wanda Salis ya ɗauka nata mamakin tsoro ne, ya ce"Wannan fa?" A tsorace ta ce"Wallahi ban san daga inda ta fito ba!". Ya kai hannu ya buɗe ƙwarya nan gajerun wandunansa suka bayyana, a linke tsaf, tare da ƙananun kwalaben turare da wata laya ƙarama, sai takarda an rubuta Salis, Safiyya, Ni'ima, Kausar, daga ƙasa aka rubuta farraƙu, duk cikin rubutun ajami kuma da tawada. Salis kansa ya fara juyawa da ƙyar ya kalli Ameera da take muzurai ya ce"Ameera mene ne wannan?". *LAST FREE PAGES!* IYA RUWA NA KUƊI NE A KAN NAIRA ƊARI UKU KACAL! YANZU AKA FARA LITTAFIN, AKWAI TIRKA-TIRKA KALA-KALA A GABA. KI SIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI KI TURA KUƊINKI TA NAN 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 IDAN KATI NE KI TURO HOTONSA. ƳAN NIGER KU SAKA 300 AIRTEL [6/1, 11:49 AM] Sadiya Abdulrazak: *PAID PAGE* 13 Wata irin bugawa ƙirjinta ya yi, sai da ta ji tsikar jikinta ta tashi, lokaci ɗaya ta fara karkarwa, Salis ya daka mata tsawa ya ce"Mene ne wannan!". Da rawar murya ta ce"Wallahi ban sani ba, ba nawa ba ne, tare muka gani ai ko?" A mugun fusace ya ce"Zan wanka miki mari idan kika ce za ki yi musu! Dama bin bokaye kike yi? Wace masifar aka yi da gajerun wandunana? Ko sawa kika yi aka mai da ni mace saboda kishi? Kuma raba mu za ki yi da matata da ƴaƴana? Ki mallake ni ke kaɗai ki zauna da ni ki tara naki ƴaƴan!?" Tun da ya fara magana take ta girgiza kai alamar a'a, kan ya ƙi tsayawa kamar wacce wani noti ya kunce a kan, hawaye sai ambaliya suke. Wata irin tafasa zuciyarsa take yi, yana jin kamar ya saki Ameera a take a wurin nan, bai taɓa zaton abun nata ya kai haka ba, amma wata zuciyar tana tausar shi da cewar ya mata uzuri har da ƙuruciya da kuma guguwar kushi, wanda shi kishi so ne yake kawo shi, gefe guda kuma tunanin mahaifiyarsa yake yi da me za ta fassara abun? Amma dole a yi wa tufkar hanci don ba zai zauna da mushrika ba. Waya ya ɗaga ya kara a kunne, bayan sakanni ya ce"Hello Yaya Fa'iza don Allah ki zo gidana yanzu!". Ya kashe ya zauna ya riƙe baki. Mugun tashin hankali ya kama Ameera ta ce"Wallahi wannan makircin Safiyya ne, ita nake zargi, na rantse da Allah ban san komai ba ban san hanyar gidan Malami ba ballantana boka, ka tuhume ta!". Ya ce"Wallahi idan kika sake ambatar Safiyya sai kin sha mamaki! Nata ne me yasa aka same shi a ɗakinki? Kuma ita ba ta da hankali haka kawai za ta yi wa kanta farraƙu da ni? Za ta raba ƴaƴanta da babansu? Yanzu idan Yaya ta zo duk abin da ta yanke shi zai faru!". Hankalin Ameera ya ƙara tashi, ta fi kowa sanin halin Yayar, saboda ita ƴar ɗakinta ce, ba ta da kirki sam idan abu ya haɗo ku, ballantana a kan wannan ƙanin nata da suke jinsa kamar tsoka ɗaya cikin miya, saboda shi kaɗai ne namiji, don haka ta zo gabansa ta tsugunna tana fashewa da kuka ta ce"Don Allah ka yafe min ba dan halina ba, tabbas wannan kayan nawa ne, kuma na yi komai saboda sonka amma wallahi na maka alƙawarin ba zai sake faruwa ba, har abada!". Ya ce"Mene ne ribarki idan kin raba ni da ƴaƴana?" Cikin kuka ta ce"Babu riba mugunta ce kawai, amma wallahi ban riga na kai ba, dama na tattara ne idan zan je asibiti zan wuce na kai". Ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Kenan dai gidan boka kike zuwa ko?" Ta ce"Wallahi ban san gidan boka ba, ƙawata ce zan kai wa ta kai". Nan take ya fara jin shakkar son da yake yi mata, ya ce"Ni ma asiri kika min nake son ki ko?" Ta ce"E wallahi, amma ba zan ƙara ba don Allah ka yafe min kar Yaya ta ji don Allah! Idan na ƙara komai ma ka yi min". Salis ya sauke numfashi mai nauyi, yana son Ameera sosai, bai taɓa zaton son ba na Allah da annabi ba ne sai yau da ta faɗada bakinta, mamaki ya daskarar da shi, ya ce"Ameera idan kin cuce ni Allah Ya saka min, na ƙyale ki ko don umarnin uwa, ina zaune ƙalau da matata ta sa na aure ki, ashe nakasa ni za ki yi ki mai da ni mace, wato za ki kai wandona da sunan Safiyya kin ga sai na zama mace ranar kwananta ko? Shi kenan idan kin nakasa ni ai su Hajiya ne suka rasa Safiyya wani auren za ta yi, ke ma haka, ni kuma na yi da wandon jikina". Ameera tana ta kuka tana girgiza kai alamar a'a, ba ta taɓa zaton wannan ƙaddarar za ta rufto mata da safen nan ba. Salis ya ciro dubu biyar a aljihunsa ya ajiye mata ya ce"Ni na tafi kasuwa, idan Yaya ta zo ki ce dama raka ki asibiti za ta yi, kowa ya yi na gari kansa". Ya fice ya tafi. Kuka sosai take yi, tana kuma kyautata zarginta akan Safiyya, ta saka a ranta ya zama dole ta sake sabon ɗauri maganin bajewar kaya, don ita da gidan Salis mutu ka raba!". Ban ɗaki ta koma ta wanke fuskarta, ta shirya, babu jimawa Yaya ta zo, a zaune ta same ta duk ta yi fiƙi-fiƙi, ta gaishe ta ta amsa tana kallon yanayinta ta ce"Ameera lafiya kuwa? Salisu ya kira ni". Ta ce"E lafiya ƙalau, dama asibiti ya ce ki raka ni, saboda cikin har yanzu bai fara motsi ba". Yaya ta ce"Ikon Allah! Ameera cikin naki har wata nawa ne?" Ta ce"Wata uku ne". Ta yi dariya ta ce"Idan ban da abunki ai zai yi, wani ma sai wata biyar yake farawa, duk kin rame ko laulayin ne?" Ta ce"Shi ne, kuma Yaya zaman ma fa sai haƙuri wallahi". Yaya ta tattara hankalinta wurinta tana ɓata rai ta ce"Kenan Salis bai nutsu ba har yanzu ta wannan busasshiyar yake?" Ta ce"To da farko dai kamar gaske, amma yanzu abun ya motsa wallahi, don jiya akan ƴarta ta fasa min faranti na mata faɗa Safiyya ta ƙare min zagi tass, shi ma da ya dawo ya dinga yi min har yana cewa shi yana jin a jikinsa wataran sai na bar gidan nan, wai na zo zan raba shi da matarsa". Ganin fuskar Yaya ta canza sosai alamar ranta ya ɓaci Ameera ta kwantar da kai ta ce"Yaya don Allah ina neman alfarma, ina son Salis ba na so na bar gidan nan, saboda ni cetonaa nake son yi idan kin ga wulaƙancin da Safiyya take masa wallahi kare ba zai ci ba, amma shi sam ba ya gani, wataran abinci ma hana shi take sai dai na zuba a leda na lallaɓa na kai masa zaure, sai ya ɗauka ya tafi, to don Allah kar ki faɗa masa mun yi wannan maganar, saboda ni ce a ruwa don yadda na lura ba zai taɓa ganin laifinta ba, don Allah kar ki nuna na faɗa miki, ni komai ina yi ne don Allah, indai ba zai sake ni ba zan jure komai wallahi, amma ina tsoron ranar da za ta zuga shi ya sake ni, ga rabo mun fara samu". Yaya ta ji tausayin Ameera tare da tsanar Safiyya, ta ce"Ke da gidan nan Ameera ai mutu ka raba, kuma in sha Allah ba zan ma faɗa masa ba, zan sa Hajiya dai ta gargaɗe sa kan indai ya sake ki babu ita babu shi, mun gode don Allah ki ci gaba da kula da shi". Nana ta ce mata ba sai ta je asibiti ba babu abin da zai samu cikin za ma ta aiko mata da rubutun tsari, Ameera ta ji daɗi sosai, ta ɗauki waya ta kira shi ta faɗa masa yadda suka yi da Yaya ta ce ba sai an je ba. Ya ce"To ki ajiye min kuɗina, kuma kar ki sake na dawo na tarar da wannan abubuwan a gidana!". Ameera ta ce"To zan fita da su". Ƙaninta ta kira a waya ta ce ya zo, da ya zo ta ba shi wandunan ta ce ya wanke ya saka Salis ne ya canza sababbi, ƙwaryar kuma ta ce idan ya fita ya fasa ta, haka layar ma da ƙwalaben turare ta ce ya zubar, haka ta wuni a ɗaki cikin damuwa, ranar kwananta ne amma da daddare da ta shiga ɗakinsa sai ya ce ta koma nata ɗakin sai ya neme ta. Safiyya ba ta san yadda wasan ya kwashe ba, amma ta tabbata tarkonta ya ɗanu, don da daddare Salis ya zo ɗakinta ya zauna ya yi shiru, ta kalle shi ta ce"Baban Ni'ima ba ka da lafiya ne?" Ya sauke numfashi ya ce"Kusan hakan, Safiyya ki dage da addu'a don Allah, su ma yara ki dinga shafa musu". Ta ce"To ai dama muna yi". Ya ce"Ku dai ƙara ninkawa saboda shi maƙiyinka yana tare da kai, kuma mugu ba shi da kama". Ta ce"Allah Ya tsare mu bakiɗaya". Ya tashi ya fice jiki a sanyaye. Washegari da safe Ameera tana kitchen Safiyya kuma tana sharar tsakar gida, yayin da Salis ya shiga wanka, Safiyya wuf ta faɗa ɗakinsa, ta san al'adarsa ce zaɓen kayan da zai saka tun kafin ya shiga wanka, tana shiga kuwa taga wani farin yadi da hula a kan katifa, ta yi sauri ta zaro wandon ta shige ɗakin Ameera zuciyarta na bugu don kar a kamata, ta wurga shi ƙarƙashin kujera amma ana ɗan hango shi, ta yi sauri ta koma ɗakinta. Ameera ta gama da kitchen ta shiga ɗaki, tana sharewa, yayinda Salis ya zo saka kaya ya ga sai riga babu wando, ya sake duba sif ko bai fito da shi bane sai kuma ya tuna ai har ATM ɗinsa da mukulli ya saka a wandon sanda ya fito da shi, don haka ya fito cike da mamaki kai tsaye ɗakin Ameera ya yi. Ameera tana cikin shara ta hango tazuge a ƙarƙashin kujera, da mamaki ta janyo shi, sai ga wandon Salil ya bayyana, daidai lokacin da ya banko ɗakin rai a ɓace ya ganta tsaye da wandonsa a hannu, Ameera ta rasa abun yi sai kawai ta rungume wando ta fashe da kuka sosai, Salils ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Yau ga mugun abu, Ameera me zan gani haka? Me na miki ne? Me kike nema a wandona?" Ta kasa magana sai kukanta da ya tsananta sosai, nan take ya ce"To sako hijjabinki ki saka wando a jaka ki fito!". Ta ce"Ina za mu je?" Don ita ma yanzu ta fara zargin ko aljanu ne suke son raba ta da mijinta. Ya ce"Gidanku za mu je". Babu musu ta saka hijjabi ya saka wasu kayan ya saka wandon a jakarta ya bata ta riƙe ya buga babur suka tafi gidansu. LITTAFIN IYA RUWA PAID BOOK NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank SHAIDAR BIYA TA 08028966015 KO KATIN MTN. ƳAN NIJER MA ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/1, 11:49 AM] Sadiya Abdulrazak: PAID PAGE 14 A ƙofar gida ya tsaya ita ta shiga, Ummanta tana ganin Ameera ta shigo tana hawaye hankalinta ya tashi, ya ture kwanon wainar da take ci ta ce"Ke lafiya da sassafen nan?" Ta ce"Tare da shi muke Umma, yana ƙofar gida". Umma ta ce"To lafiya dai ko?" Ameera ta shige ɗaki Umma ta bi ta gabanta yana faɗuwa, Ameera ta ce"Umma kome Salis ya ce kawai ki ce masa aljanu ne da ni don Allah!" Umma ta ce"Kamar ya aljanu?" A taƙaice Ameera ta ba ta labarin duk abin da ya faru, Umma ta ce"A lallai na haifi lusara! Tafi ki shigo da shi". Bayan Salis ya shigo sun gaisa da Umma a mutunce kamar ba ta san komai ba ta ce"Salisu lafiya kuwa? Ta shigo tana ta kuka da safe haka me yake faruwa". Ya sosa kai ya ce"Wato dama Umma wani abun al'ajabi ne yake faruwa tsakanina da Ameera, kwanan baya na nemi kayana na rasa, sai jiya na gansu a ɗakinta ta zuba su cikin ƙwarya tare da wasu abubuwa masu kama da shirka, da na matsa da tambaya ta faɗa min ƙawarta ce take rakata gidan boka, saboda ta raba ni da matata, muka yi alƙawari jiyan ta ce ba za ta ƙara ba, kuma kwatsam yau ma na fito da kayan da zan sa na shiga wanka na fito na ga ba wando, ina shiga ɗakinta na same shi a hannunta, to abin da ya tsorata ni kuka take yi riƙe da wandon, shi ne na ce to bari mu zo gidan a yi bincike". Umma ta ɗauki dogon salati ta dire ta ce"Ita Ameerar ce take wannan lamuran?" Ya ce"Yanzu haka wandon yana jakarta". Umma ta tashi ta ce"Bari na kira ta". Tana shiga ɗakin ta cewa Ameera"Don ubanki duk abin da ya ce ki musa, ki ce ba ki san zancen ba, ba ki san an yi ba!". Ta ce"Umma ki ba shi haƙuri kawai kar ya sake ni, amma me faruwa ai ta faru". Umma ta ce"Kin ci ubanki! Ki yi yadda na ce!" Suka fito, Umma ta ce"Ameera me yake faruwa ne?" Ta ce"Babu komai". Umma ta ce"Ga mijinki ya ce kina ɗaukar masa wanduna kuma ya ga kayan shirka a ɗakinki?" Ameera ta fara rarraba ido ta ce"Ni fa ban gane ba, wane irin wando kuma?" Salis ya ce"Ya muka yi da ke jiya, kuma yanzu me ya kawo mu?" Ta ce"Ni jiya ba mu yi komai ba, yanzu kuma cewa ka yi na tashi mu je gida". Ransa ya ɓaci sosai da rainin hankalinta, amma ba zai iya yi mata tsawa a gaban babarta ba, ya ce"Ɗakko jakarki". Ta je ta ɗakkota ta miƙa masa, ya zuge jaka sai ga wando ya bayyana ya fito da shi ya ce"Mene ne wannan?" Ta zaro ido a tsorace ta ce"Wannan ai wando ne, me ya kawo shi jakata?" Sai kuma ta dafe kanta tana lumshe ido, ta ƙwalla wani uban ƙarar da ya tsorata duk wanda yake cikin gidan, sannan ta faɗa kan Umma yaraf. Salisu ya miƙe tsaye yana salati, Umma ma salatin take yi, ya ce"Umma bari na samo adaidaita sahu mu tafi asibiti". Umma ta ce"A'a! Wannan yanayin nata ba na asibiti ba ne, dama tun da ka faɗa min abin da ta yi na san akwai matsala, ka tafi kasuwarka akwai malamin da zan kira ya duba ta, duk yadda aka yi idan ka dawo da daddare sai ka zo ka ji". Da damuwa ya ce"Ai da na samo malamin..." Ta katse shi da faɗin"Babu komai ka tafi kawai". Ya ce"To Allah Ya ba ta lafiya, ga wannan". Ya zaro dubu biyar ɗin jiya da ta dawo masa da ita ta tafiya asibiti ya ajiyewa Umma ya tafi, a zuciyarsa yana yarda lallai akwai ƙamshin gaskiya a lamarin Ameera tana da aljanu, gida ya dawo ya ajiye wandonsa sai ya kasa cin abinci ma, kuma bai faɗawa Safiyya komai ba, ita ma ba ta tambaye shi ba, haka ya yi wunin kasuwa cikin zulumi da fargaba. Da daddare yana dawowa daga kasuwa can ya wuce, lokacin Ameera tana ɗaki, ya gaisa da Umma, ta fara ba shi bayani, ta ce"Salisu ashe lamarin ba na wasa ba ne muka raina shi? To Ameera dai yau Allah ne ya tseratar da cikin jikinta, don wallahi inda ka ga yadda ta dinga buge-buge tana zubar da mutane a gidan nan sai ka yi mata kuka..." Sai ta fara kukan ƙarya ta ce"Ameera dai aljanu ne arna suka shige ta, ba ka ga wuyar da ta sha ba kafin su faɗi ture aka yi mata, amma an ce mu yi shiru ba sai mun faɗi wacce ta yi turen ba". Salis da tsoro ya kama shi, jikinsa duk ya yi sanyi, a hankali ya furta"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah Ya taƙaita haka". Umma ta ce"An dai samu sun lafa, amma sun ce ba za su fita ba fa sai wacce ta turo su ta ce a ruguje aikin nan, don su umarni suke bi wai" Ta ƙarasa tana share ƙwalla. Salisu da ya zama kamar an zare masa laka ya ce"Don Allah an san wacce suka ce ɗin? Me Ameera ta yi mata?" Umma ta ce"Kai dai a bar kaza cikin gashinta, wani sirrin rufewarsa ta fi bankaɗe shi". Ya ce"Umma ni fa ba zai yiwu na zuba ido a saka mata ciwo ba, ko wace ce dole zan ɗauki matakin shari'a da ita!" Don shi har ya fara hasashen cikin danginta ne suka samu matsala da wata. Umma ta ce"Yanzu dai a zuba ido a ga yanayin jikinta, idan ta haihu lafiya a yi komai, kar mu matsa su zubar da cikin". Ya ce"Tana ina Ameerar?" Umma ta ce"Ameera ai ba za ta ganu ba! Wuyar da ta sha yau sai dai Allah Ya mata sakayya, bacci take yi". Ya ce"To shi kenan gobe na zo na ɗauke ta". Ta ce"A'a, da dai ka bar ta ta huta, saboda ka ga magunguna fal leda wanda za a na yi mata turare da na sha da na shafawa, sai gobe ma na ce ya zo ya karɓi kuɗin kafin nan na sa yayanta ya turo min". Salis ya ce"A'a ba za a yi haka ba, ai haƙƙina ne, nawa ne?" Ta ce"Dubu talatin ne, don ya san ni ne ma, amma a dubu hamsin yake yi". Ya ɗan yi jim, sannan ya ce"To yaro ya biyo ni sai ya karɓi kuɗin, Allah Ya ba ta lafiya". Umma ta amsa da amin, sannan ta ce ƙanin Ameera ya bi shi su je. Dubu arba'in Salis ya cira, ya sayi kayan shayi da biredi babba, har da tsire ya ba shi ya ce ya kai gidan. Gidan Hajiya ya wuce, ya faɗa mata duk halin da ake ciki, Hajiya ta zabura ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Kar fa kishi ya sa Safiyya ta kashe ƴar mutane!". Da mamaki ya ce"Safiyya kuma?" Hajiya ta ce"Ƙwarai kuwa! To idan ba ita ba wace?" Ransa ya ɓaci ya ce"Haba Hajiya! Wai me yasa duk wani laifi na Safiyya ne? Me ta yi muku wai? Akan wane dalili za ta turawa Ameera aljanu? Haba don Allah" Hajiya ta ce"Au tambaya kake? To dalilin ta aurar mata miji, mijin da take ji kamar don ita kaɗai na haife shi, kuma ta ga kana son ta, kana na ta kulawa kamar yadda kake yi mata, shi yasa take son yi mata illah, kuma wallahi ba ta isa ba!". Salis ya ce"Hajiya su fa ba su faɗi sunan kowa ba, ni dai ba zan taɓa yarda Safiyya za ta je wajen boka ba". Hajiya ta matso kusa da shi har da rage murya ta ce"Ba ka ce a jikin takardar sunan Safiyya ba ne da yaranta?" Ya ce"Har da nawa". Ta ce"To ai duk ita ta sa aljanun suka yi hakan saboda kar ma a zarge ta, ta aiko aljanu suka ajiye abu a ɗakin baiwar Allah saboda ka gani ka sake ta, to wallahi Salis ko bayan raina idan ka saki Ameera ba na tare da kai! Ita kuma Safiyya gobe zan je na same ta". Ya ce"A'a Hajiya don Allah ki yi zamanki, zan bincika idan ma ita ɗin ce". Da ƙyar Hajiya ta yarda ba sai ta je ba, ta ce gobe za su je duba Ameerar. Ya koma gida jiki a sake kamar burodi a cikin shayi, Safiyya har ta kwanta don tara ta yi kuma ba ranar kwananta ba ne, ya tura ƙofar ɗakinta da sallama, ta amsa tana tashi zaune ta ce"Sannu da zuwa". Bai amsa ba ya nemi waje ya zauna ya yi shiru. Safiyya ta ce"Baban Ni'ima lafiya?" Ya ce"Ina fa lafiya! Ameera ce ba ta da lafiya wai aljanu ne suka shiga jikinta, tana can abun babu daɗi". Safiyya ta ji babu daɗi, ta ce"To Allah Ya sawaƙe, tare kuka shigo?" Ya ce"Tana gidansu fa, aljanu da suka so haukatata, tana ta kwasar mini wanduna tana ɓoyewa, kuma har tana ba ni labarin asiri ta min nake sonta, ashe baiwar Allah duk ba ta san me take yi ba, ba ta cikin hayyacinta". Dariya ta so ƙwacewa Safiyya, ta danne ta ta ce"Subhanallah! Wane irin wando kuma Baban Ni'ima?" Ya ce"Hmm! Kun rage abinci ne?" Ta ce"A'a, bari na dafa maka wani abun dai". Ya ce"Bar shi haɗa min shayi ma kawai, jikina duk ya yi sanyi wallahi, har tunanin dawowarta nake, wallahi tsoron me aljanu nake sosai Safiyya". Safiyya ta yi murmushi ta ce"Babu abin da zai faru in sha Allah! Za ta samu lafiya". "Allah Ya sa!" Ya faɗa yana sake yarda Safiyya ba za ta iya yiwa wani turen komai ba, ita kuma ta tafi kitchen don kawo masa shayin. Washegari da safe kafin ya tafi kasuwa sai da ya je ya duba Ameera, yau ya ganta duk ta yi sanyi kamar ba ita ba, ya mata sannu ya tafi kasuwa. Da yamma Hajiya dan ƴaƴanta suka je dubiya, da suka tambayi ba'asi nan babar Ameera ta faɗa musu aljanun sun ce kishiyarta ce, sannan ta ce musu don Allah kar su bari Salis ya ji, idan ta haihu sai a san abun yi, suka dinga zagin Safiyya babar Ameera tana ba su haƙuri, ita dai Hajiya suka ce ta tafi gida su kuwa suka tafi gidan Salis kai tsaye. Safiyya ta gama girkin dare kenan ta shiga wanka, ta ji ana buga gidan, dayake ta hana Ni'ima buɗe mata ƙofa sai da ta fito daga wankan ta zo ta buɗe, ta ɗan saki fuska tana musu sannu da zuwa, duk da ba wai daɗin ganin su ta ji ba saboda yanayin zaman nasu, a tsakar gidan suka yi cirko-cirko fuskar kowa babu annuri, Safiyya ta ce"Yaya ku shiga mana!". A fusace ta ce"Ba za mu shiga ba! Sai ka ce wata uwar ce a ɗakin! Wajenki muka zo". Gabanta ya fara faɗuwa ta dake ta ce"To Allah Ya sa lafiya". Yayar ta ce"Lafiya ai tana wajenki tun da kin illata maƙiyiyarki! Wallahi Safiyya mun ba ki sati ɗaya ko ki koma wajen bokanki ki sa ya raba Ameera da aljanun da kika turo mata ko mu sa a mayar da su kanku ke da ƴaƴanki!". Ta ji ƙirjinta ya yi wani irin bugu, ta ce"Ni fa ban gane ba, kuna nufin ni kuke zargi da yiwa Ameera ture?" Ta ce"Aljanu sun faɗa da bakinsu, don haka ba za su miki sharri ba, to wallahi ki warware komai ko zaman gidan nan ya gagare ki! Ai dama matsiyaci bai san arziƙi ba, duk abin da Salis ya miki ko matarsa ya sa tana taka ki ai kya yi haƙuri saboda halakcinsa a gare ki, ballantana ma me matarsa ta tsare miki da za ki mata bi ta da ƙulli?" Tuni hawaye suka wanke mata fuska ta ce"Wallahi ƙarya ake yi mini, ban san komai ba, ban yi mata komai ba". Haka suka mata kaca-kaca suka tafi suka bar ta tana kuka sosai, tana kan sallah ya shigo bayan isha'i, a sanyaye yake saboda ya ji komai na zuwan ƴan'uwan nasa, ya nuna musu ɓacin ransa sosai ya ce kar su sake zuwar masa gida da sunan cin zarafin matarsa, amma da Yaya ta zauna ta tsara masa komai kamar a gabanta aka yi ruƙiyyar sai ya yarda amma abun da sarƙaƙiya don haka bai kamata a tunkari Safiyya da cin zarafi ba, tun da su ma aljanun an ce suna ƙarya. Ta amsa sallamar da ya yi, ya zauna yana kallon idonta da ya nuna ta yi kuka ya ce"Safiyya kuka kika yi?" Ta ce"Baban Ni'ima ba zan yi ba? Ni ake zargi da cutar matarka". A sanyaye ya ce"To ai da ya kasance su aljanun ne suka faɗa kin ga dole a zarge ki ɗin, amma na faɗa musu kar su sake yi miki haka". Ta ɗago ta kalle shi da sauri tana sarewa da lamarin, ashe shi ma ya yarda ita ɗin ce. Ya katse mata tunani da cewa"Safiyya ni mijinki ne kuma ɗan'uwanki, zan nemi wata alfarma a wajenki ba don ni ba sai don girman Allah, don Allah idan kin san ke ce ki dubi halin da yarinyar nan za ta shiga ga cikin fari a jikinta ki yi haƙuri ki janye ki raba ta da aljanun nan kar su yi mata illa". Da ido kawai take kallonsa jikinta ya fara karkarwa cikin muryar kuka ta ce"Kai ma ka yarda ni ce?" Ya ce"To babu tabbas roƙonki dai kawai na yi, don na ji suna zancen za a yi ƙaiƙayi koma kan masheƙiya, Safiyya ba zan so ki cutu ba..." Ta katse shi cikin kuka ta ce"Don Allah kar ka hana su, su yi komai daga nan za a ga mai gaskiya". Ya tashi ya fita ransa babu daɗi, gabaɗaya an ɗaure shi ya rasa mai gaskiya, shi dai fatansa kawai Ameera ta samu lafiya a bar kaza cikin gashinta. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL. [6/1, 11:49 AM] Sadiya Abdulrazak: PAID PAGE 15 Washegari da safe ya shigo ɗakinta ya ci abinci bai tada zancen ba, ita ma sai ta yi shiru, ya gama ya fita, haka ta yi wunin ranar cikin damuwa kamar ta faɗawa Salma sai kuma dai ta yi shiru, da ya dawo ya wuce ya ga Ameera. Haka suka cigaba da yi kullum zai je duba Ameera kafin ya tafi aiki da daddare ma zai riƙe leda ya je ya sake ganinta, kuma kullum sai ya bawa Umma dubu biyu, tsakaninsa da Safiyya kuma babu yabo babu fallasa, yana cin abincinta ita kuma tana ta lissafi duk ranar girkin Ameera ba ta zuwa ɗakinsa tun da bai tsara mata ga yadda za a yi da kwana ba kafin ta dawo, cikin kwanakin ta lura yana yawan jan ƴaƴansa a jiki, har ma yana shigo musu da biskit su zauna su yi fira wanda da kwata-kwata ya daina, sati biyu suka yi a haka sannan Ameera ta dawo. Ranar da kanta ta cewa babarta zaman nan fa ya ishe ta, gara ta koma su ci gaba da fafatawa, Umma ta ce"Gaskiya kam ni ma na yi tunanin hakan, tana can kin bar mata miji tana kalallame shi da kissa, wannan makirar yarinya ce fa dole sai kin dage dantse rayuwar aure ta zama iya ruwa fid da kai, idan ba ki iya ba kina ji kina gani za ta watso ki waje ta ɗaiɗaita miki ƴaƴa". Ameera ta ce"Umma ya aka yi da dubu talatin ɗin nan?" Ta ce"Tana nan na adana, har dubu biyun da yake kawowa kullum kuɗinki suna nan dubu hamsin cif, kin ga yanzu sai ki ƙara ƙaimi ki ta yagowa mu samu kafin Allah Ya sauke ki a sayi filin, don wallahi idan ta gama ginin nan ke ba ki da ko taku kin shiga uku, kuma kin tabbata borar gida, idan ma kuɗin cefane ne ki ɗan dinga ragewa duk a ganganɗa a fito da ke". Ta taɓe baki ta ce"Shi fa ba wani sakin kuɗi yake ba, kuma cefane aikowa yake yi". Ta ce"To ba yana ajiye kayan abinci da yawa ba? Ai sai ki dinga yafitowa kina aikowa ana kai shi shago ana siyarwa". Ameera ta ce"Zan gwada na ga idan zai yiwu". Haka ta yi ta mata huɗuba tana ɗora ta a gadar kwali kuma ita tsakaninta da Allah so ne irin na ba ka so ka ga an fi ɗanka a komai. Da daddare Salis ya zo za su tafi, Umma ta ce"To ga ta nan sai a lallaɓa Allah Ya ba ta lafiya, don Allah sai a guji ɓacin ranta saboda kasan masu matsalarta da ransu ya ɓaci sai su taso, mun gode Allah Ya haɗa kanku". Salis ya ce"In sha Allah za a kiyaye Umma Allah dai Ya yaye mata". Ta amsa da amin sannan suka tafi. Suna hanya, cikin yanayin nuna ta yi kewarsa ta kwantar da kanta a bayansa, ƙirjinsa ya yi wata irin bugawa, saura kaɗan su faɗi, ya ce"Ameera lafiya?" Ita ma da ta tsorata saboda gargadar da babur ɗin ya yi ta ce"Mene ne?" Ya ce"Ai na ji kin kwanta a jikina, na ce to ko jikin ne?" Ta ce"A'a fa ka san fa na yi kewarka sosai". Ya ɗan sauke ajiyar zuciya, saboda har ga Allah tsoronta ya fara yi, shi tunani ma yake yadda za su kwana waje ɗaya, yadda ya ji an ce tana buge-buge tana zubar da mutane, idan suka motsa yanzu ya zai yi da ita? Da wannan zulumin suka ƙarasa gidan. Safiyya ba ta san yau za ta dawo ba, tana kwance a ɗakinta tana chart ta ji shigowarsu, dariyar Ameerar ce ankarar da ita tare suka dawo gabanta ya faɗi ta yi addu'ar neman tsari daga masifa, tsakani da Allah sati biyun nan da ba ta nan ta fi ji daɗin rayuwar gidanta, haka su ma yaran ta lura sun fi sakewa su yi wasansu a tsakar gida, shi yasa idan ta tuna za ta dawo sai ranta ya ɓaci. Ɗakinta suka wuce ya buɗe mata, ta shiga ta fara gyara shi daga ƙurar da ya yi, shi kuma ya shiga ɗakin Safiyya, bai zauna ba ya ce"Kin ga yau Ameera ta dawo, ta ji sauƙi". Safiyya ta ce"An yi ƙaiƙayin kenan?" Ya ce"Ba a yi ba, tun da sun lafa kuma ai shikenan". Ta ce"Ko tsoro na ji to na sa suka lafa?" Ya ce"Kayya Safiyya a bar zancen haka don Allah! Allah dai Ya rufa asiri, akwai abinci?" Ta ce"Akwai mana". Ya ce"Da ɗan yawa?" Sarai ta san inda ya dosa, ta ce"Akwai mana daidai yadda kake ci". Ya ce"Ai wai da na ga yau ga Ameera ban sani ba ko ba ta tsaya ta ci a gidan ba". Ta ce"Ikon Allah! Ba ga kitchen ma, ai ina ga na rage kayan miya, kuma ma akwai barkono". Ya ce"Haba Safiyya ta ya za ta yi girki daga dawowarta?" Sai ta tashi ta shiga kitchen ta fito masa da abincinsa ta kawo ba ta sake bi ta kansa ba, ya gama tsayuwarsa ya ɗauki abincin ya shiga ɗakinta, daidai ta gama sharar tana kunna turaren tsinke ya ce"Sannu daga zuwa kin hau aiki, ga abinci". Ta ce"Kai mana ɗakinka kawai, gani nan zuwa". Ya je ya kai ya zauna yana jiranta, sai da ta sake yin wanka ta shirya cikin kayan bacci sannan ta shiga ɗakin, yana kallonta ya ji ta burge shi, amma da ya tuna mutanen kanta sai tsoro ya kama shi, ya haɗiyi wani yawun fargaba, ya buɗe kular, jollop ɗin shinkafa ce da ta ji kayan lambu, ya zuba ya matsa kusa da ita ya ɗiba ya kai mata baki, tana ci ta yamutse fuska, ya ce"Lafiya?" Ta ce"Ba na son ƙamshin, kamar zan yi amai". Ya ce"Subhanallah! Ya za a yi kenan?" Ta ce"Da zan samu doya da miya ita nake sha'awa". Ya ɗan ji fargaba don ya san ba lallai Safiyya ta dafa ba, amma ya dake ya ce"To bari sai a dafa miki, ina zuwa". Ya fita Ta janyo farantin ta yi cokali biyar ƙwarara ta sha ruwa ta ture shi yadda yake, don dama kawai so take Safiyya ta san ta dawo. Yana shiga ɗakin Safiyya ya ce"Maman Ni'ima ba a yi bacci ba?" Ta ce"Tukunna dai". Ya ce"Dama kin ga wallahi Ameera ce wai ta kasa cin abincin, ta ce doya take sha'awa da ƴar miya, shi ne na ce don Allah ko za ki dafa mata?" Daga ganin yadda yake maganar ta san dole ce ta kawo shi, ya ba ta tausayi amma hakan ba zai sa ta yi wa matarsa girki ba, ta ce"Doya da miya da daren nan? To ai da ka siyo mata, ba akwai a bakin titi ba?" Ya ce"Ai dayake kin san mai ciki ita ta fi so a miyar a ɗan saka alayyahu haka don inganta lafiya". Bai san maganar cikin haushi ta ba ta ba, ta ce"Ai kuwa ka ga babu alayyahu a gidan". Sai yanzu ya ga ashe ya kwafsa ya ce"Dama fa alayyahun cewata ne, dafa mata haka ɗin ma". Ta ce"Baban Ni'ima yanzu kai za ka yarda Ameera ta ci abun hannuna? Ni da nake son illata ta, ai kamata ya yi ta kiyaye ni". Ya ce"Haba Safiyya magana ba ta wuce ba kuma?" Ta ce"Ba ta wuce ba, babu yadda za a yi na sake bawa matarka abuna, ya muka ƙarke akan kunu?" Ya sani tun da ta kafe ba za ta dafa ba, don haka ya fice daga gidan, ya je ya siyo doyar dama yana da niyyar siyo mata kaza sai ya taho da ita da lemuka masu sanyi, da ya kawo ya juye mata a plate ta ce"Wai siyowa ka yi?" Ya ce"Ai Baby tunani na yi kar a sake maimaita yadda aka yi a kunu shi yasa, har ta tashi za ta dafa na tuna na ce ta bar shi". Ba ta ce komai ba ta fara cin doya, shi kuma yana cinkafa, suka gama suna cikin cin kaza Safiyya ta yi sallama, Salis ya amsa ba ta jira izini ba ta shiga, zaune a cinyarsa ta tad da ita yana ba ta kazar a baki, Safiyya ta tsallake su ta nemi waje a katifa ta yi kwanciyarta. Salis mamaki ya kashe shi ya ce"Safiyya lafiya dai ko?" Ta ce"Me ka gani?" Ya ce"Wane irin wulaƙanci ne haka kin zo kin haye katifa ranar kwananta?" Ta ce"Lissafa dai, yau ai ranar kwanana ne". Ameera cikin fusata ta ce"Kin yi sati biyu da mijin kuma yanzu ki ce wai ranar kwananki!?" Safiyya ta ce"Ke bar ni na yi da shi, ke ba ki kai na yi da ke ba tukunna". Ta ce da shi"Da ta tafi ka ce min ga yadda za a yi da kwana? Ba ka ga ina fashi ba? To ranar kwananta ce nake tsallakewa, ka lissafa ka gani yau ranar kwanana ce gobe zan fita daga girki". Ya yi shiru, can dai ya ce"Ameera haka ne, ƙyale ta gobe sai ki zo". Ameera ta kumbura tana huci, ya tashi ya ja ta ɗaki ya ba ta haƙuri don ba ya son ɓacin ranta musamman a yanzu da ta zama a lallaɓa auren zamani, a can suka ƙarasa cin kazar sai da ta kwanta sanna ya fito ya rufo mata ƙofa, ya koma ɗakinsa. "Safiyya kar ki sake yi mini haka! Wannan ai raini ne, me yasa tun ɗazu ba ki min bayani ba?" Ya faɗa a fusace Ta yi kamar ba ta ji sa ba, ya fice daga ɗakin, har bacci ya ɗauke ta bai dawo ba, sai wajan ƙarfe biyu ta farka ta kura har yanzu bai dawo ba, baƙin ciki ya turnuƙe ta don ta san Ameera ya bi ɗakinta suka kwana kenan ita ya barta da katifa, tashi ta yi ta koma ɗakinta, tana zuwa ta same shi kwance a kusa da ƴaƴan shi yana baccinsa hankali kwance, ta yi murmushi ta yi shimfiɗa a ƙasa ta kwanta, sannan bacci mai cike da nutsuwa ya ɗauke ta. Bayan sati ɗaya da dawowar Ameera, watarana da sade Safiyya ta shiga kitchen za ta ɗora girki Ameerar ta shigo tana wani zazzare ido ta ce da Safiyya"Baiwar Allah fita za mu yi girki!". Safiyya ta yi mamaki ta ce"Ƴar aiki ta fita saboda matar gida za ta yi girki ko?" Ta ƙaraso dab da Safiyya ta daka mata wata tsawa cikin ƙarajin da har Salis sai da ya jiyo ta ta ce"Ki fita muka ce!!!". Safiyya ta ce"Ba zan fita ba don kutumar ubanku!". Tass! Ameera ta wanka mata mari, daidai shigowar Salis ita ma Safiyya ta zage ta fesawa Ameera mari, Salis ya ce"Innalillahi! Haba Safiyya ba ki..." Kafin ya ƙarasa Ameera ta yi kukan kura ta faɗa kan Safiyya ta rufe ta da duka, Safiyya da ranta ya gama ɓaci, zuciya ta ciyo ta ta rufe ido ita ma tana kai wa Ameera duka ta ko'ina, nan da nan kayan kitchen suka fara fareti komai yana ta kansa, don ma ba ta kunna gas ba. Salis ganin Safiyya ta fi jibgar Ameera a ruɗe ya ce"Safiyya ciki ne da ita fa, kuma ba ita ba ce aljanu ne, kin san fa aikin mai aljanu!". Safiyya cikin ƙaraji ta ce"Ni ma ai ina da su, ni masarauta ce a kaina don kaza- kazar uban na kan nata!". Ta ja ta ƙiii ta kai ta jikin bango ta maƙure ta, shi kuma Salis tsoron aljanu ya hana shi ƙarasawa ya raba su, har sai da Ameera ta sulale ƙasa tana wani farfar da ido, ya ɗora hannu biyu aka ya ce"Shiken Safiyya kin kashe ta, kin kashe mai ciki!". Safiyya a haukace ta wawuro taɓarya ta yo kanta idonta ya rufe, Ameera tana ganin halaka ta tashi ta yi kan Salis da gudu, amma ina kafin ta ƙaraso ya kwasa a guje ya yi ɗakinsa ya danna sakata, sau ta afka ɗakinta ta kullo ƙofa. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/1, 11:49 AM] Sadiya Abdulrazak: PAID PAGE 16 Safiyya ya yi jifa da taɓaryar tana huci, duk iskancin Ameera ba ta taɓa zaton za ta iya saka hannu ta dake ta ba, wato za ta fake da aljanu ta dinga dukanta tana cin bulus, ta saka a ranta ko aljanun gasken ne ba za ta zuba ido ba sai dai idan ta ga abun ya fi ƙarfinta. Ta koma kitchen ɗin ta gyara kayanta da suka zubo wasu har sun fashe ta ɗora girkinta har lokacin jikinta bai daina tsuma ba. Shi kuwa Salis zaune ya yi a ɗaki yana tunanin dama ita ma Safiyya tana da aljanu ashe, kuma da alama ma har sun fi na Ameera, shi yanzu ya zai yi da su kenan, don muddin aka ce za su dinga wannan damben shi kam zai ma iya bar musu gidan su cinye kansu, babu wacce za ta illata shi don ya san tunkarar mai aljanu sai wanda ya shirya, ta windo yake leƙe har Safiyya ta gama girkinta ta fito daga kitchen ɗin. Ita kuwa Ameera tana ɗakinta kwance girjinta sai bugu yake, ta daku duk da dai ita ma babu laifi ta jibgi Safiyyar, ta yi mamaki ƙwarai don ba ta yi zaton Safiyya tana da ƙarfi ba, ita ta yi zaton za ta ji tsoronta ne sai ta dinga fakewa da aljanun tana ɗan saita mata hanya ko da mari ne, ashe ba zai yiwu ba, wannan plan ɗin bai yi ba dole a haƙura da shi ko wataran reshe ya juye da mujiya, tana nan kwance tsawon lokaci ta ji ƙarar wayarta ta ɗakko tana dubawa ta ga Salis ne, ta ɗaga, ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Yawwa, Baby ya jiki?" Cikin takaici ta ce"Kai ɗin kana ina?" Ya ce"Ina kasuwa!". Ta ce"Amma kana kallon halin da nake ciki shi ne ka fita ko ka duba ni?" Ya ce"Ba haka ba ne, na ƙwanƙwasa a hankali saboda ban sani ba ko bacci kike yi kar na tashe ki". Ta ce"Jikina duk ciwo yake yi, yanzu me zan ci?" Ya ce"A ki dafa wani abun mana". Ta ce"Na ce maka ban da lafiya!" Ya ce"To bari na aiko miki, don Allah kar ki sake kula ta, idan babu dama ki tafi gidan Hajiya ki wuni". Ta yi harara kamar yana kallonta ta ce"Babu inda zan je!". Ya aiko mata da abinci, ta ci tana so ta fito ta yi wanka ta kasa saboda har kunyar Safiyya take ji. Shi kuwa Salis kiran Safiyya ya yi ya ce"Safiyya ya jikin?" Ta ce"To! Dama ba ni da lafiya ban sani ba?" Ya ce"To Safiyya ina lafiya ta ishe ku? Allah dai Ya yaye kawai, don Allah ki tafi gida ki ɗan wuni mana". Ta ce"Me kake nufi?" Ya ce"Babu komai kawai saboda na ga kin kwana biyu ba ki je ba shi yasa". Ta ce"To, zan biya har gidan Yaya Aminu ma". Ya ce"A dawo lafiya". Suka yi sallama ta yi murmushi da ta lura Salis ɗin da gaske tsoron mai aljanu yake yi, ta shirya suka tafi, ba ta samu Baba a gida ba don haka ba ta daɗe ba ta da suka gaisa da Umma ta tafi gidan Yaya Aminu, kaf ta kwashe labari ta bawa Salma suka ci dariya sosai, Safiyya ta ji daɗin firar su ta yaye mata damuwa, sai dab da magriba ta koma gidansu suka gaisa da Baba, saboda Salis ne zai zo ya ɗauke ta. A ɓangaren Ameera ta ji daɗin fitar Safiyya, don haka ta tashi ta shiga kitcen duk rabin kayan abinci ta kwashe hatta mai da magi ba ta bar su ba, ta yi wa Umma waya ta aiko ƙanwarta ta tafi da su, kuma ta bawa Umma labarin badaƙalar da suka karya da ita yau ɗin, Umma ta ce to kar ta sake gwadawa tun da dai abun bai karɓe ta ba. Safiyya tana dawowa ta ga kamar an mata bincike a ɗaki, sai kuma ta ga wayam babu firjinta, gabanta ya faɗi ta tafi ɗakinsa yana shirin shiga wanka ta ce"Baban Ni'ima ko dai yau an shigo mana gida?" Ya ce"Kin ga babu firjinki ko?" Cike da mamakin yadda aka yi ya sani ta ce"Ƙwarai kuwa ashe ka sani ma". Ya ce"Ki yi haƙuri wallahi Ameera ce tun da ta gamu da wannan larura take yawan shan ruwan sanyi, shi ne na ce to tunda dama ɗakin naki a matse yake kawai bari na ba ta firjin idan ya so daga baya na siyo miki ƙarami". Ta ji baƙin ciki ya rufe ta, ta ce"Kenan dama saboda ka ɗauki firjin ka ce na tafi gida!" Ya haɗe rai ya ce"Ba fa na son raini! Idan na yi niyyar ɗauka ban isa na ɗauka a gabanki ba ne?" Ta ce"Ka isa, tun da kai ne ka siya dama don ka ƙwace me zai dame ni?" Ta fice daga ɗakin ranta a ɓace. Daga ranar tana ji tana gani Ameera ta mallake firjinta, sai kuma ta tsiri sarar jone wutar ɗakin Safiyya, ga shi ana tsananin zafi, haka kawai tsakar dare sai ta fito ta cire wata waya, wutar ɗakin Safiyya ta ɗauke, haka za ta kwana cikin zafi, sai washegari a nemo mai gyara kuma babu wanda ya gane, ƙarshe Salis da ya gaji ya ce shi ya daina gyaran nan ta yi haƙuri idan ya samu kuɗi zai canza waryar wajen kawai, haka tana ji tana gani ta rasa wutar nefa. Daga nan Ameera ta shiga kwasar kayan abinci babu kama hannun yaro, da ta faki idon Safiyya wuf sai ta kwaso wani abun ta kawo ɗaki, ƙanwarta ta zo ta saka a hijjabi ta fice, har Safiyya ta fara zargi don ta ga nan da nan kayan abinci sun ƙare sai an ƙaro wanda suke ɗakinsa, wataran Safiyya za ta kwaso na ɗakinsa, da mamaki ya ce"Safiyya ba shekaran jiya aka ɗibi kayan abinci ba?" Ta ce"Wallahi ni ma ina ta mamaki, ka ga babu komai a kitchen ɗin". Ya ce"To wane irin girki kuke yi haka?" Ta ce"Ni dai yadda nake yi da haka nake yi har yanzu, ban sani ba ko ita". Daga nan ya fae faɗa akan saurin ƙarewar kayan abinci, kuma iya Safiyya kawai yake yiwa, bai taɓa yi wa Ameera faɗa ba, da Safiyya ta gaji ta ce masa a raba kayan abincin ya dinga bawa kowa tana, sai a gane ta inda abun yake, shi ma ya gamsu da wannan shawarar don haka ya yi wa Ameera bayani, aka fara raba kayan abinci, kowa da lokar da yake zuba nasa, sai Ameera ta ce idan kun san wata ba ku san wata ba, ba ta yin girki sai ta ga Safiyya ta gama, idan ta shiga sai ta kwashe kayan abincin Safiyya ta dafa, nata kuma ta aika gida, bayan kwana biyu aka gane kayan abincin Safiyya ne yake saurin ƙarewa don haka Salis ya dinga yi mata faɗa, abun ya dame ta ta rasa gane me yake faruwa. Watarana ta zo yin girki, ta san ta bar taliya ɗaya loka amma ta ga wayam babu, ta buɗe lokar Ameera don ta ɗauki wacce za ta dafa, kasancewar shi ya daina barin mukulli a gida, tana buɗewa ta ga babbar leda a ƙulle, ta kunce kawai ta ga taliya, macaroni, shinkafa, har da mai wajen kwalba biyu, ta shika da mamakin me yasa Ameera ta ƙulle su da ban, ai kuwa ta mayar mata ta ƙulle, ta ɗauki taliya ta dafa. Ta saka ido sosai a shige da ficen Ameera don haka ta ga lokacin da ta ɗakko ledar ta dawo da ita ɗakinta Safiyya tana ta mamaki, da yamma ta ga ƙanwarta ta zo wacce take yawan zuwa don har ta fara mamakin zuwan nata, ba ta daɗe ba ta fito za ta tafi hannunta da abu a hijjabi, Ameera ta rako ta. Safiyya ta yi wuf ta tashi ta ƙarasa wajensu ta kira sunan yarinyar kamar yadda ta ji Ameerar tana faɗa ta ce"Nabila ɗan tsaya". Duk suka juyo suna kallonta, Ameera ta haɗe rai ta ce"Lafiya dai ko?" Safiyya ta ce"Ita ta kawo hakan". Ta ce da Nabila"Fito da abun hijjabinki zan ɗan gani". Ita da Ameera duk gabansu ya faɗi, Ameera ta ce"Ban gane ba fa!" Safiyya ta ce"Ai so nake ki gane ɗin". Ta fincuko hijjabin yarinyar ta warci leda, leda ta fashe sai ga kayan da ta gani ɗazu sun tarwatse a ƙasa har da ƙullin madara,milo da suga, ta ce"Ikon Allah ke kuma yunwa ake yi a gidan naku? Kina ji Salis yana cigiyar inda ake kai masa abinci kika ƙi yi masa bayani! Ni'ima maza miƙo min wayata". Jikin Ameera ya yi wani irin sanyi, amma saboda ƙarfin hali ba ta nuna ba ta ce"Babu ruwanki da duk abin da zan yi, yadda yake mijinki haka ni ma mijina ne kuma gidana ne, ta kai hannu za ta tattare Safiyya ta doke hannun ta ce"Don gidan mijinji ne sai ki dinga yi masa sata kina ci da gidanku?" Daidai lokacin da ta karɓi wayar da Ni'ima ta miƙo mata, ta yiwa kayan vedio har ma ta hasko Ameera dake tsaye cikin borin kunya da rashin abun yi, ta kuma hasko Nabila, ta wuce ta bar wajen ta shige ɗaki, ta kunna data ta turawa Salis tare da rubutu ta ce ka zo fa ana fati a gidanka. Babu jimawa Ameera ta shigo ɗakin Safiyya a sanyaye ta zauna, Safiyya ta ce"Lafiya? Me ya kawo ki ɗakina?" Ameera ta ce"Babu komai". Safiyya ta nuna mata hanya ta ce"To tashi ki fita!". Ta ce"Maman Ni'ima, na mayar da kayan don Allah ki yi haƙuri kar ki faɗa masa". Safiyya ta da wayarta ke hannunta ta kunna recording sannan ta ce"Me kika ce?" Ameera ta ce"Kayan abincin na ce na mayar da su don Allah kar ki faɗa, ba don halina ba". Safiyya ta ce"Amma ke tsakaninki da Allah tun yaushe kike fitar masa da kayan abinci? Yunwa ake a gidanku?" Ameera ta shaƙa sosai na wulaƙancin da Safiyya take son yi mata, ita za ta cewa ana yunwa a gidansu? Amma tun da rufin asiri take nema dole ta jure, ta ce"A'a kawai dai kyautatawa ce". Ta ce"Kyautatawa da abin da ba naki ba? A ina ake yin haka? Kuma tun yaushe kike ɗiba?" Ta ce"Yau ne na farko". Safiyya ta ce"Wallahi ƙarya kike, dama duk ƙoarafin kayan abinci da ake yi yana saurin ƙarewa ashe ke ce kike kwashewa, ke yanzu da ɗan rufin asirin mijinki za ki na ci da gidanku? Irin wannan ai farantawa miji za ki yi sai ya farantawa iyayenki, ke ma ya dinga yi miki kyautar kuɗi". Ameera dai ta yi shiru zuciyarta na ƙuna, amma ta saka a ranta sai ta rama Safiyya ta ce"Tashi ki fice min, ni na riga na faɗa masa fa!". Ameera ta miƙe tsaye ta ce"Bura'uba! Kin faɗa masa!?" Safiyya ta ce"Ƙwarai kuwa!". Ta ce"Ai kin yi a banza, don kuwa yau za ki san ke ɗaliba ce a fagen kissa, sai kin yi nadamar shiga gonata!" Ta fice fuuu tana huci, ta ɗakko kayan abincin ta kai ƙofar ɗakin Salis ta ajiye. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/1, 11:49 AM] Sadiya Abdulrazak: 17 Ko da Salis ya ga saƙon Safiyya ya dai yi mamaki da ya ga kayan abinci ga kuma ƙanwar Ameera, amma ya share bai ce komai ba, kuma bai sa a ransa zai zo ɗin ba, haka kawai ba zai bar kasuwa ba yanzu haka dambe suke yi shi kuwa ba zai iya raba su ba, don yanzu duk sun fara ba shi tsoro har gara ma Safiyya. Sai dare ya dawo a ɗakin Ameera yake, don haka can ya fara shiga, sai ya ga ta kasa sakewa kamar tana cikin damuwa. Ya ce"Baby lafiya? Na ga ba ki da walwala,ko kun ui faɗan ne?". Ta ce"Idan faɗa ne ai da sauƙi akan makircin da Safiyya take son ƙulla mini, kuma na san dole ma ka yarda". Ya ce"Me ya faru?" Ta ce"Ba ta ce maka na yi komai ba?" Ya ce"Tabbas ta tura min video kuma har da ƙanwarki a ciki da kuma kayan abinci". Ameera kamar za ta yi kuka ta ce"Na zo raka Nabila za ta tafi gida na tarar da su ita da Maman Affan ta miƙa mata leda tana cewa ta kai wa Idi mai kanti sun gama magana da shi, shi ne na ce wallahi sai na faɗa maka, sai Maman Affan ta ce ai kuwa sai dai reshe ya juye da mujiya, ta sa Safiyya ta yi wannan videon wai a ce ni ce na ɗebo kayan zan ba Nabila ta kai gida..." Ta fashe da kuka Hankalinsa ya tashi da kukanta, tsoronsa kar mutanenta su tashi, ya ce"Kin ga ya isa haka, bari na je na ji". Ya tashi ya fita daga ɗakin. Ya shiga ɗakin Safiyya, ya haɗe rai sosai ya ce"Safiyya ashe ba ki rabu da matar nan ba ko? Wai Maman Affan ce take aurenki?" Da mamaki sosai ta ce"Haba Baban Ni'ima, me kuma ya dawo da abin da ya wuce? Tun da ka raba mu ba magana ta ƙare ba?" Ya ce"Me ya kawo ta gidan nan yau da har kika ba ta kayan abincina ta kaiwa Idi mai kanti?" Ta yi murmushi ta ce"Au abin da ta tsara maka kenan? To bari ka ga shaidata". A fusace ya ce"Me ta tsara min!? Babu wani abu da zan gani, na faɗa miki ki fita daga harkar matar nan, wannan shi ne karo na ƙarshe da zan sake jin an ganki da ita!" Ta ce"Ameera ce fa take kwashe duk kayan abincin gidan na da kake zancen tana ƙarewa da wuri, ashe gidansu take..." Ya ce"Don Allah Safiyya ya isa haka! Ni zancen da nake da ban, shi kuma abinci na san yadda zan yi! Wannan wane irin abu ne haka ba za ku bar ni hankalina ya kwanta ba? Na yi aure saboda na ƙara samun hutu da nutsuwa amma sai akasin haka ne yake ta faruwa, kai Allah Ya raba bawa da wahala!". Ya yi ficewarsa ya shiga ɗaki ya yi shiru yana ta tuna rayuwar gidansa ta baya nutsattsiya mai cike da farinciki, amma yanzu komai ya jagule idan yana kasuwa suka kira shi har fargabar ɗagawa yake yi. Waya ya ɗaga ya kira kowaccen su, suka nemi wuri suka zauna, ya ce"Safiyya, Ameera na gaji da abubuwan da suke faruwa, don Allah tun da ba za ku iya haɗa kanku ba to kowa ya fita daga harkar kowa, kowa ya yi rayuwarsa, akan kayan abinci kuma gobe zan kawo in sha Allah, zan raba Safiyya ke da ƴaƴanki ki saka naki a ɗaki ki adana, ke ma Ameera ki adana naki a ɗakinki, ya kasance tukwane da gas ne kawai a kitchen ɗin, daga nan a ga wacce nata zai ƙare da wuri". Ameera da wannan tsarin ya ƙona mata rai sosai, a tsiwace ta ce"To ka ce Safiyya da ƴaƴanta, kenan nata zai fi yawa?" Ya ce"Idan ma nata ya fi yawa ai ban ɓata ba, tun da ga yara biyu". Ameera ta ce"Ni ma ai ga ciki, kuma ka san mai ciki da cin abinci, sannan na fi ta yin baƙi, ƴan'uwanka ma idan suka zo a nan suke sauka". Ya ce"To babu damuwa, zan ware miki na ɗan cikinki, zan ware na baƙi a ɗakina, duk wacce za ta yi baƙi sai ta faɗa". Da wannan aka samu maslaha akan satar abincin da Ameera take yi, daga nan kuma sai hanyar samu ta toshe mata, ɗan abin da take samu duk ranar da taje asibiti ba yawa ne da shi ba, shi kuma haka kawai ba ya baka kuɗi, idan ƙaryar biki ko sunan ƴan'uwa ta yi masa abin da yake ba ta a ya yi wuta dubu biyu, ko kuɗin anko ba ya bata, ga Umma ta matsa mata da zancen ta kawo a harhaɗa, har ma kuma ta ce ta fara haɗa na kayan barka da gara saboda a fita kunya, gidan ya yi mata zafi don haka ta sake sabuwar dabara, idan Salis ya dawo daga kasuwa yana shiga wanka za ta yi wuf ta shiga ɗakinsa ta zari kuɗi a aljihunsa dubu uku kullum, ranar da ta ga da aukinsu kuma ta zari shida wataran har goma. Da abun ya yi mata daɗi sai ta ƙaro dabara da safe duk ranar girkin Safiyya idan ya shiga wankan tafiya kasuwa sai ta yi wuf ta zari dubu ɗaya ko biyu a aljihunsa, saboda kafin ya shiga wanka yake fito da kayan da zai saka ya zuba duk abin da zai buƙata a ciki, bayan ya ware wanda zai saka a account. Kuɗin ba wani mai yawa yake sakawa a aljihun ba, don haka cikin ƙanƙanin lokaci ya fara ganewa, da ya saka ido don ya gane sai ya gano duk ranar kwanan Safiyya ne ake masa sata, kuma ya san sata ba halinta ba ne, to amma an ce yau da gobe ba ta bar komai ba, don haka wataran ya tsara zai tunkare ta. Safiyya tana zaune a ɗaki ranar za su fara karyawa ya kira ta ɗakinsa, don akwai ranar da ta ce masa ko me zai mata ya daina yi a gaban ƴaƴanta, ta shiga da sallama ya gama shiri yana zaune ranshi a ɓace, don ranar dubu uku ya saka a aljihunsa ya zo ya ga babu ɗaya, Safiyya ta ce"Gani baban Ni'ima". Ya ce"Safiyya tun da na ƙara auren nan na hana ki abincin da nake ba ki ko kuma na daina yin wani abu da nake yi miki wanda haƙƙina ne na yi?" Ta ce"Ba ka daina komai ba, amma me ya kawo zancen?" Ya ce"Safiyya na lura duk ranar girkinki sai kin ɗaukar min kuɗi a aljihuna idan na shiga wanka, kuma ba wani kayan cefane na ga kina ƙarawa ba, kuɗin me kike tarawa?" Tun da ya zo kan tana zarar kuɗi a aljihunaa ta ji ƙirjinta ya yi wata irin bugawa, zuciyarta ta zo har wuya, ta ce"Yanzu ni kake zargi da sata? Ni kake tunanin ina duba aljihunka na ɗauki kuɗi!?" Ta fara kukan baƙin ciki Ya ɗaga mata hannu ya ce"Ni dai ba kuka na ce ki yi ba, kawai dai na faɗa miki ne, don ki san na gane, kuma ki kiyaye, tun da na yi auren nan shi kenan kin canza hali ki ta tsiro sabbin halaye idan an ɗinke nan ki barka can, to gaskiya na gaji!". A dake ta ce"Tun da har ka gane lokacin da nake ɗauka me ya hana kana shiga ka fito ka kama ni? Duk shekarun da muka yi da kai ban yi maka sata ba sai da ka yi aure? Me kake tunanin aurenka ya tare mini? Kai ne ka canza hali ba ni ba! Tsawon shekaru idan sata halina ce dole na nuna, ga wacce ta zo sama ta ka ba ka zarge ta ba sai ni, haka akan kayan abinci ka ƙi tsayawa ma ba ka shaida..." Ya ɗaga mata hannu ya ce"Don Allah tashi ki je, ni dai gargaɗi ne na yi miki". Safiyya ta tashi ta ce"Baban Ni'ima mene ne amfanin na dinga cutar da mijin da yake ciyar da ni da ƴaƴana? Zan tafi gida kawai ko hakan zai sa ka samu nutsuwa da matarka". Ya ce"Ni ban ce ki tafi gida ba!". Ta ce"Babu amfanin zama da ɓarawo, don haka zan tafi". Ya ce"Kar ki tafi, idan kuma kika tafi to kar ki sake ki dawo, kuma kar ki tafi da ƴaƴana". Ta ce"Zan tafi kuma da su zan tafi, don ban ga wurin barin su a cikin gidan nan ba!". Ya ce"Indai akwai wurin zamansu a gidanku to akwai wurin barinsu a gidan nan". Ta yi masa kallon sakanni ta ce"Me kake nufi?" Ya ce"Dawo ki zauna". Ta ce"Yi maganarka". Ya sassauta murya ya ce"Safiyya kina yawan cewa za ki tafi gida, ban sani ba ko zuga ki ake yi, amma ki fara tuna irin rayuwar da kika yi a gidan nan da kuma wacce za ki yi idan kika koma kafin ki tafi, ki dinga abu da lissafi don Allah! A kan me za ki na zarar mini kuɗi? Na ga da idan kina da buƙata tambayata kike yi, wannan ya wuce amma kar ya sake faruwa don Allah". Ta share hawayen da suka zubo mata ta ce"Tun da dai mi kaɗai kake yi wa kallon ɓarauniya to kuwa dole zai sake faruwa!" Ta fice daga ɗakin, haka ta wuni cikin baƙin ciki, ko tantama ba ta yi Ameera ce take masa sata, amma so ya rufe masa ido ya ɗora mata, saboda ita ce juji. Bayan kwanaki da ya lura ba a daina satar nan ba fa, sai yake ƙirga kuɗinsa tun a kasuwa, ya kai wanda zai saka a account, sauran kuma idan ya zo sai ya ɗauka duka ya bawa Safiyya ajiya sai gobe ya karɓa, ai haka ake wa ɓarawo tun da ya san ita take ɗauka gara ya ba ta ajiya ya ga ta yadda za ta ɗauka, daga nan sai wannan hanyar sata ta Ameera ita ma ta toshe. Aka ci gaba da zama har tsawon watanni babu wani abun kuma, dab da haihuwar Ameera Ummanta ta ce mata ga wani fili nan ƙawarta za ta siyar, har ta faɗa mata Ameera za ta siya don Allah ta san yadda za a yi ta ciko kuɗi kar ta ba ta kunya. Ameera ta buga ta ga babu wani space ɗin samun kuɗi, cikin satin ne za a yi sunan ƙanwar shi da ta haihu, saura kwana biyu sunan ya daina fita da babur ɗinsa, don ya ce birkinsa ne ya fara samun matsala yau zai zo da mai gyara, ranar sunan ya ba su kuɗin adaidaita sahu, amma saboda rashin haɗin kai kowa tafiyaraa da ban, Ameera ce ta fara tafiya, Safiyya sai la'asar ta tafi, Ameera tana can ta yi wa Hajiya waya ta ce ta samo wanda zai zo ya ɗauki babur, Hajiya babu kwaɓa saboda tsabar son zuciya da buri, ta samo wani ɗan unguwar ta kwatanta masa nesa da gidan sunan, ya zo ta fita ta ba shi mukullin gidan ta ce yana shiga zai gan shi ya ɗakko, ya kula da birkin sosai. Bayan ya ɗakko ya kawo mata mukullin ya tafi kaiwa gidan Hajiyarta, ta bi bayan babur ɗin da kallo tana jin rashin daɗi a zuciyarta amma ya za ta yi? Ƙaddara ce. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/1, 11:49 AM] Sadiya Abdulrazak: 18 Dab da magriba Safiyya ta koma gida don ita ce da girki, ta idar da sallah tana kitchen tana ƙarasa girki Salis ya dawo gidan, sai da ya fito daga wanka sannan ya lura babu babur ɗinsa, da mamaki ya ce"Safiyya ina kuka matsar min da babur ɗin kuma?" Ita ma da mamakin ta ce"Ba ka gan shi ba ne?" Don ita sam ba ta lura babu shi ba. Ya ce"Nuna min tun da ke kin gan shi". Ta ce"Ikon Allah! To ina babur zai tafi shi kaɗai?" Ya ce"Abun da mamaki, amma wannan ai ku zan tambaya, tun da ku na bari da shi a gidan ko?" Safiyya ta ce"To sai dai ko mun gamu da fatake yau ɗin, don kuwa har na bar gidan nan babur ɗin yana nan". Ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!". Ya fice daga gidan. Sai bayan sallar isha'i ya dawo, babu jimawa kuma Ameera ma ta dawo, ya ce"Ke kuma sai yanzu?" Ta yi murmushi ta ce"Wallahi kuwa ana ta fira da ƴan'uwa, kuma da na ga ba ni ce da girki ba". Ya ce"To sai ki bincika ɗakinki ko an ɗauki wani abun don yau mun gamu da fatake, shi kenan na rasa ɗan babur ɗin nawa". Ta yi alamun tsoro har da fe ƙirji ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Kuma wallahi sanda na tafi babur ɗin yana nan, dayake ni sammako na yi, Safiyya ce sai yamma ta tafi, kuma ka ga ta riga ni dawowa". Ya ce"Babu komai ƙaddara ce, Allah Ya tsayar a kai". Ta buɗe ɗakinta, ta ce"Honey ɗan zo mana". Ya bi ta jiki a mace, ta ce"Ni fa ba dan kar a ce na yi zargi ba da na faɗa maka wani abu". Ya tattara hankalinsa ya ce"To mene ne?" Ta ce"To dai kafin na fita na ji Safiyya tana waya kuma kamar da namiji, tana cewa amma sai ka kula da birkin babur ɗin, ni na yi zaton ma ko wani ne zai zo ya kai ta gidan sunan". Salis ya yi shiru yana nazari. Ameera ta ce"Amma fa wannan hasashe ne kawai, ina ga dai an yi a makari ne, tun da me za ta yi da babur? Duk da dai tana ginin gidanta amma wannan ai ita ta san hanyoyin samunta". Salis ya ce"Kamar ya ginin gida?" Ta ce"Kar ka ce min ba ka san tana gini ba, har ya yi nisa?" Ya yi guntuwar dariya ta takaici ya ce"Zance ne, ina ta gaɗin gini?" Ameera ta ce"Tambayi yayanta a hannunsa komai yake". Cikin ko'inkula ya ce"To sai dai ko na gadon da babarsu ta bari ne". Ta ce"Amma ba za ka tuntuɓe ta ba ko ita ta ɗauki babur ɗin ta kai maka wajen gyara?" Ya ce"Haba Ameera, Safiyya ba za ta ɗau babur ba, don ba ta da wata alaƙa da maza bayan danginta". Ta ce"Ai shi kenan, Allah Ya rufa asiri". Ya amsa da amin ya tashi ya fice. Ɗakinsa ya je ya zauna ya yi shiru yana ta nazari, ya ga alamar Ameera tana son ankarar da shi Safiyya na da masaniya akan satar babur ɗinsa, amma kuma ba zai yarda Safiyya za ta iya ba, to ta yi me da shi? Yana nan zaune ta shigo ta kawo masa abinci, ta ajiye ta ce"Baban Ni'ima ka yi haƙuri ka bar wa Allah komai, in sha Allah asirin ɓarawon zai tonu". Ya ce"To Allah Ya tabbatar!" Ta ce"Ga abincinka". Sai da ta ga ya fara ci sannan ta ɗan ji sanyi a ranta, yana cikin ci ya ɗauki waya ya kira Hajiyarsa, bayan sun gaisa yake ba ta labarin abin da ya zo ya tarar, Ameera da ke laɓe a ƙofar ɗakin, tun shigar Safiyya, da ta ji yana waya da Hajiya, ta daddage iya ƙarfinta ta ƙwalla wani uban ƙaran da sai da Hajiyar ta ji, sannan ta nemi waje ta kwanta a tsakar gidan tana shure-shure. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Shi kenan musiba ta shigo gidan!" Salis ya faɗa shi ya manta ma waya yake yi, sai da ya ce Hajiyar ita ma cikin firgici ta ce"Me ya faru? Waye yake kuka haka?" Da rawar murya ya ce"Ameera, wallahi Ameera ce ta faɗi innalillahi wa inna ilaihi raji'un!". Hajiya ta katse wayar tana faɗawa ƴaƴanta dake zagaye da ita. Maman Sadiq maƙociyar Yaya Fa'iza da ita ma ta je gidan sunan tana zaune suna shirin tafiya, Fa'izan ta ce"Maman Sadiq mu je don Allah ki mata tofin ruwan addu'a" Kasancewarta Malama, indai aka tada aljanu takan je ta yi wa mutum addu'a a ruwa, saboda haka ta tashi za su tafi, Hajiya da duk hankalinta ya tashi ita ma ta saka hijjabi ta ce"Mu je na gani da idona, yarinya da tsohon ciki ta dinga faɗuwa? Ai lakwa-lakwa kuka mata wallahi shi yasa ba ta raba ta da aljanun nan ba!". Suka ɗumguma suka tafi dukansu. A can gidan Salis kuwa Safiyya murmushi ta yi ta tashi za ta fita daga ɗakin, Salis da sauri ya ce"Safiyya ke ce?" Ta ce"Kamar ya? Daina gani ka yi?" Ya ɗan ji daɗi don ya gane nata ba su ƙaraso ba, ya ruƙo hannunta ya ce"Ina za ki je? Don Allah kar ki fita, kar ta miki wani abun". Safiyya ta ce"To ta gwada ta gani" Ta fizge hannunta ta fice, kallo ɗaya ta yi mata ta shige ɗakinta. Salis ya rufe ƙofa ya dinga safa da marwa yana karanta duk addu'o'in da ya tuna, gefe guda kuma yana neman mafita, ana cikin haka sai ga sallamar su Hajiya, ya ce"To Alhamdulillah!". Tana jin shigowarsu ta ci gaba da shure-shure tana faɗar wasu maganganun da ba a gane me take cewa kamar yara masu koyon magana, duka suka ɗau salati, Hajiya ta ƙaraso ta ce"Bismillahir rahmanir rahim! Ku ya ku, mu ya mu, ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba, wa innahu Sulaimanu wa inna bismillahir rahmanir rahim!" Ta ɗago ta tana cijewa, duk da a tsorace take. Ameera ta yi wata miƙa har sai da mararta ta yi ƙara, ta buge Hajiya, Hajiya ta yi baya da sauri ƙirjinta yana bugu ta ɗaga murya ta ce"Subhanallah Salisu! Salisu ba ka gidan ne?" Salis da ke leƙe ta window ya ce"Hajiya kin ganni daga nan, sannunku na gode". Fa'iza ta ce"Ubanka da godiyar! Kana kallo za ta make mana uwa ba za ka fito ka riƙe ta ba?" Ya ce"Tab! Ai Yaya idan kin ga na buɗe ƙofa to yasin na ga ƙurar nan ta lafa ne". Maman Sadiq a nutse ta buɗe robar ruwa ta ɗauki kofi ta ɗebo ruwa ta yi addu'o'i tana tofawa a ciki, sanna ta ƙarasa wajen Ameera da bisimillah ta yarfa mata a fuska, Ameera ta yi miƙa da ƙaton cikinta ta fara wani gurnani, ta ƙara watsa mata, sai ta fara shure-shure tana cewa "Kar ki ƙona mu, za mu yi magana, mu da ban muke ba wanda Safiyya ta turo ba ne, mu masu tonon asiri ne!". Ta ƙwalla wani uban ƙaran da har maƙota suna ji, maƙocinsu ya tashi gulma tana cinsa ya ce"Maman Haidar bari dai na je na gani, na ga dai Salisu kamar ba ya dukan matansa, amma yau da gobe ta fi ƙarfin wasa, bari na je kar ta ɓaci!". Ita ma ji ta yi kamar ta bi shi, amma babu dama, yana zuwa ya ga ƙofar a buɗe ya yi sallama ya shiga, Hajiya ta ce"Yawwa bawan Allah taimaka ka kamata mu kai ta ɗaki". Ya ce"To me yake faruwa?" Salis da kishi ya turnuƙe ya ce"Ku yi ku gama a nan, idan ta farka ta shiga ɗakin". Hajiya ta ce"Rufe mana baki! Ragon banza kawai". Hajiya ta taso ta dawo kusa da Ameera ta ce"Gafaranku dai bayin Allah! Me ya faru wane asiri za ku tona?" Ameera ta ce"Kishiyar goɗiyarmu ce ta sa aka ɗauke babur ɗin mai gidan nan, don ta siyar, ku hanzarta ba ta siyar ba tukunna!" Ta saki wata atishawa, tana sauke numfashi. Kowa ya ɗauki salati, ban da Safiyya da ta tsaya cak tashin hankali ya rufto mata lokaci ɗaya, take ƙirjinta ya fara bugawa da sauri. A ɓangaren Salis kuwa jikinsa ne ya yi sanyi, har ma ya ji yana shakkar abin da aljanun nan suka faɗa, gaskiya ba ya zargin Safiyya. Maƙocinsu ya ce"Wai Salisu babur aka sace maka ne?" Daga ɗakin ya ce"E wallahi, ɗazu abun ya faru". Ya ce"Dalla ka fito, sai ka ce wani babban abu, yau ka fara ganin iska?" Ya fito gabansa yana faɗuwa. Maƙocinsa ya ce"To a gaskiya ɗazu ina zaune a ƙofar gida na ga wani matashi ya zo da mukulli ya buɗe gidan nan ya fito da babur, abin da ya sa ban kula shi ba, na ga da mukulli sai na yi zaton aiko shi aka yi". Salis ya ce"Innalillahi! To tabbas akwai ayar tambaya a nan!" Hajiya ta ce"Rufe mana baki dalla! Ga shi aljan ya tona asiri saboda kai dai ba ka ganin laifin matarka!". Ta yi ɗakin Safiyya a fusace Salis ya ce"A'a Hajiya kar mu yi saurin yarda da zancen jinnu, an ce suna ƙarya". Hajiya ta ɗage labulen Safiyya da ke zaune hawaye na zuba, ta ce"Safiyya salun alun ki fito ki wuce ku je ki karɓo masa babur ɗinsa! Wannan ai wulaƙanci ne, wanda yake ba ki ci da sha shi za ki tozarta ki nemi kaiwa ƙasa?" Safiyya cikin kuka ta ce"Wallahi Hajiya ban san komai ba akan babur ɗinsa, me zan yi da shi?" Fa'iza ta ƙaraso ta ce"Malama fito, babu wanda zai yi miki ƙarya wallahi sai kin fito da babur ɗin nan!". Safiyya ta tashi ta fito, daidai lokacin kuma Ameera ta fara motsawa ta ce"Wayyo bayana!". Sai duk hankali ya koma kanta, ta tashi zaune tana dafe kai, suka bi ta da sannu kafin a ɗago ta aka kai ta ɗaki ta kwanta, tana jin ranta fess. Hajiya ta ce"Salis kai nake jira na tafi, idan ni uwar mijinta ce ta raina ni, kai dai ni uwarka ce". Cikin rashin sanin abun yi ya ce"Safiyya tsakani da Allah kin ɗauka?" Sai ta girgiza masa kai alamar a'a, tana ci gaba da kuka. Hajiya ta ce"Yo ita ta san Allah ne? Ku je ta karɓo shi tun da an ce ba ta siyar ba tukunna!". Ya kalli Safiyya ya ce"Sako hijjabinki". Ta shiga ɗaki ta ɗauki jaka ta haɗa kayanta kala uku dana yaran, ta fito. Sai a lokacin maƙocinsu ya juya zai fita, Fa'iza ta ce"Idan ka ga yaron za ka gane shi ko?" Ya ce"In sha Allah! Zan gane shi tsaf". Ta ce"Salisu ku je ta kai ka, Safiyya a canza hali dai ka rasa wa za ka cuta sai miji? Allah Ya kyauta. Shigewa ta yi gaba, yaranta na bin bayanta, tana kuka, shi ma ya bi bayanta jiki a mace. Su kuma suka shiga ɗakin Ameera. Suna ta tafiya babu wanda ya ce ƙala, ganin sun yi nisa ya ce"Safiyya tsaya". Ta yi kamar ba ta ji ba, sai ma sauri da ta ƙara. Ya ce"Tsaya mu hau adaidaita saboda yaran" Nan ma ba ta kula shi ba, sai da tafiya ta yi nisa ya gane gidansu za ta je, jikinsa ya ƙara sanyi ya sha gabanta ya ce"Safiyya na san ba ki ɗauka ba, gida za ki ki yi yaji ko?" Ta kauce shi ta wuce, ta ci gaba da tafiya yana binta da ƴaƴan. Sai da suka zo ƙofar gida ta juyo ta ce"Baban Ni'ima ban ɗaukar maka komai ba, kuma ka sani, amma tun da an ce ni ce babu komai, zan zauna a gida na fara sana'a har na tara kuɗin babur na biya ka, idan da rabon za mu ci gaba da zama sai na dawo". Ya riƙo jakar hannunta ya ce"Ni ban ce kin ɗauka ba, kina kallo umarnin uwa na bi, kuma ban ce ki biya ni ba". Ta shige gidan, yana ta kiranta ba ta dawo ba, shi ma ya yi saurin barin ƙofar gidan don idan Baba ya fito bai san me zai ce masa ba. 08028966015 [6/1, 11:49 AM] Sadiya Abdulrazak: 19 Sai da ta daidaita muryarta sannan ta yi sallama, Baba ya zaune yana cin abinci, suna fira da Umma, suka amsa sallamar, Umma ta ce"Safiyya ce da daren nan? Lale". Safiyya ta nemi waje ta zauna tana gaishe su, Baba ya amsa ya ja yaran suna cin abinci tare, ita kuma ta fara share hawaye a ɓoye, sai da Baba ya gama ya ce"Ummi lafiya dai ko?" Kamar tana jira ta fara kuka, ta ba su labarin duk abin da ya faru, Umma ta rafka salati ta ce"Yanzu shi Salisun ne ya iya yi miki haka?" Baba ya ce"Safiyya tsakaninki da Allah ba ki san komai a kan babur ɗinsa ba?" Ta ce"Baba me zan yi da shi? Wallahi sharri kawai ta yi mini". Baba ya ce"Shi kenan, ku kwanta idan ya zo a san yadda za a yi, Allah Ya rufa asiri". Ɗakinta na da shi ta shiga, fess yake saboda Umma tana amfani da shi, ta sake gyarawa, sai ta fara waigen neman abin shinfiɗa ba ta samu ba, ta fito ta ce"Umma akwai abin shinfiɗa?" Umma ta taɓe baki ta ce"Yo ke irin wannan zaman idan ya kama ai har abun shinfiɗar ake naɗowa a taho da shi" Sannan ta tashi ta ɗakko mata wani tsohon zanin gado, shi ma na yadi ne, ba su saba kwana babu net ba ga sauro a ɗakin don haka ta leƙa ta aiki yaro ya siyo mata maganin sauro, ta kunna ta yi shimfiɗar suka kwanta, haka suka kwana cikin rashin jin daɗi, don wajen kwanciyar bai yi wa yaran daidai ba. A can gidan Salis kuwa, ko da ya dawo daga raka Safiyya bai wuce gida ba, kuma ya kashe wayarsa don kar su kira shi, haka suka gaji da zama har goma da rabi sannan suka tafi suna ta zagin Safiyya. Sai sha ɗaya da rabi ya dawo, sai a lokacin ya ga Safiyya ba ta ma kulle ƙofar ɗakinta ba, ya shiga ya ɗakko mukullin ya kulle mata, yana jin babu daɗi a ransa, wannan shi ne karo na farko da ta yi yaji, ba don Ameera tana da aljanu ba gaskiya yau da sai ya nuna mata ɓacin ransa sosai, kamar ya share ta sai kuma ya shiga ɗakin nata, tana kwance, ya ce"Ameera" Yana ɓata rai. Ta ce"Na'am! Ka dawo?" Ya ce"E, ya jikin naki?" Ta ce"Da sauƙi, su Hajiya har suka gaji da jiranka, ashe an gano wacce ta ɗauki babur?" "Sai da safe" Ya faɗa yana ficewa daga ɗakin. Sai da ya ƙarasa cin abincinsa ya yi wanka sannan ya kwanta, bai jima da kwanciya ba, Ameera ta ƙwanƙwasa ƙofar, ya harari ƙofar ya ce"Waye?" Ta ce"Ni ce mana". Ya tashi ya buɗe ya koma ya zauna bai ce mata komai ba, tana ƙoƙarin hawa katifa ya ce"Amma yau fa ranar kwanan Safiyya ne". Ta ce"To tun da ta tafi wa ya san ranar dawowarta? Ai kawai kwana ya sauka a kanta ko?" Ya kalli ƙaton cikinta cike da takaici, shi da yake tunanin ma ta haƙura da rabon kwana har sai ta haihu amma saboda zalama har da neman ƙarin na Safiyya, ya ce"Lokacin da ba ki da lafiya ba haka muka yi da Safiyya ba, don haka ki je ɗakinki, kuma Safiyya ko gobe za ta iya dawowa". Ameera ranta ya ɓaci ta tashi ta fice, ya bi bayanta da harata, haushinta yake ji saboda ita ce silar komai, yanzu ko ya ƴaƴansa za su kwana? Ko wace irin tarba Safiyya ta samu daga wajen Umma, ya yi tsaki ya kwanta yana ta tunanin mafita. Washegari da duku-duku Safiyya ta fito ta yi wanke-wanke ta yi shara ta wanke banɗaki, sannan ta koma ta kwanta, bacci ya ɗauke ta don jiyan baccinta ƙalilan ne, kwana ta yi yiwa yaranta fifita, kasancewar babu fanka a ɗakin ga sauro, har suka tashi tana bacci, don haka suka fita tsakar gida suna wasansu, tare da Umma suka fita siyan waina maƙota, ta zuba musu kunu da waina suka ci, sannan ta ajiye na Safiyya a gefe, har Baba ya shirya fita Safiyya bacci take, suka gaisa da yaran ya fita, sai ƙarfe tara ta tashi, ta fito fa gaishe da Umma, ta nemi gefe ta zauna, Umma ta tura mata abincinta, ta ɗauka ta yi godiya ta shiga ɗaki, waina ce ƙwaya huɗu kunun ma ba wani mai yawa ba ne, haka ta ci ta fito ta yiwa yara wanka, ita ma ta yi, suka zauna a ƙofar ɗaki tana chart, Umma ta fito da faranti mai ɗauke da shinkafa ta ce"Safiyya kina zaune ɗan gyara min kasuwa zan je, idan ban dawo da wuri ba ki ɗora, akwai ice ki duba ɗaki da wake da barkono da komai". Ta ce"To a dawo lafiya" Ta janyo tana gyarawa. Da safe Salis yana fita gidan Hajiya ya wuce, bayan sun gaisa ta ce"Ai jiya ka nuna min iyakata, shi ne ka tafi ka ƙi dawowa ko?" Ya ce"Hajiya ba haka ba ne wallahi, mun tafi da niyyar ta kai ni wajen, sai kuma na ga ashe ita gidansu ta yi, yanzu jiya a gida ta kwana". Hajiya ta taɓe baki ta ce"To sai me? Ai gara hakan mene ne amfanin zama da ɓarawo?" Ya ce"Hajiya wallahi ni na san Safiyya ba ta ɗauka ba..." Ta daka masa tsawa ta ce"Dalla rufe min baki! Kuma kar ka sake ka ce za ka je bikonta na dai faɗa maka!". Ya tashi ya fita rai babu daɗi, yana kasuwa ya kira ta a waya, ya yi zaton ma ba za ta ɗaga ba, sai kuma ya ga ta ɗaga, suka gaisa kowa a sanyaye, shiru na ɗan lokaci kafin ya ce"Safiyya na san ba ki ɗauka ba". Ta ce"To na gode". Ya ce"Anjima ki dawo gidanki don Allah, na san ba wani jin daɗin zaman gidanku za ki yi ba". Ta ce"A'a zaman gidanmu da daɗi, don ko mene ne a gidanmu gara na zauna a ciki da dai na koma inda za a dinga bi na da sharri". Ya ce"Ba haka ba ne, ni ma ba ni da yadda zan yi ne, kin san uwa kuma ta ce kar na je gidanku, shi yasa yanzu ma ban zo ba". Suka yi shiru na ɗan lokaci ya ce"Ina yaran? Kun karya? Yanzu me kuke yi?" Ta ce"Ga su nan suna wasa". "Kun karya ko na aiko muku wani abun?" Ya sake tambayarta. Ta ce"Mun karya, kuma ba na buƙatar komai". Jin ya yi shiru ta katse kiran, tana share hawaye, babu jimawa kuma ta ga alert daga gare shi na dubu biyar. Sai da ta gama girki tsaf bayan azhar sannan Umma ta dawo, lokacin yaran sai yunwa suke ji, Umma ta buɗe tukunya ta ce"Safiyya ba ku ci ba? Ko sai yanzu kika gama?" Ta ce"A'a na jira ki dawo ne dama, sannu da zuwa". Ta ce"Daɗina da ke akwai sokanci Safiyya, sai ki bar yara da yunwa? Sai kace ba gidan ubanki ba har sai an ci ki ci? Allah Ya kyauta, ki zuba muku". Ta yi alwala ta shiga ɗaki sannan Safiyya ta tashi ta zuba musu suka shiga ɗaki. Haka da yamma Umma tana kishingiɗe ta ce"Safiyya ko za ki tuwo? Ni ma yau ɗaya na huta na ci albarkacinki" Ta ƙarashe da murmushi, ita ma Safiyya murmushin ta yi ta ce"Umma me zai hana?" Umma ta ce"Yawwa tashi ki ɗora, ku kuna cin tuwo kuwa? Don uwarku yau sai kun ci tuwo" Ta faɗa tana jan rigar Ni'ima cikin wasa. Safiyya ta ce"Ai suna son tuwo sosai". Washegari ita aka aika siyan ƙosai, daga nan kuma Umma ta daina fita cefane ta daina aikin gida komai sai Safiyya, ga shi da daddare ba ta wani samun isasshen bacci saboda zafi da sauro. Sai da ta yi kwana uku Baba ya kira Salis a waya, ya ji kamar kar ya ɗaga, ya daure ya ɗaga, suka gaisa sannan Baba ya ce"Salisu ƙanwarka ta zo gida yau kwana uku". Ya ce"A e ta zo Baba wallahi ni ma ba da son raina ba". Baba ya ce"Mene ne ya faru?" Salis ya ba shi labari irin wanda Safiyya ta ba shi, sannan ya ɗora da faɗin"Na san ba ita ba ce, wallahi ba na zarginta, sha'anin iyaye ne ka san idan girma ya zo sai an bi su a hankali, amma zan zo mu tafi a yi haƙuri Baba". Baba ya ce"Shi kenan Allah Ya rufa asiri". Satinta ɗaya a gida watarana da yamma yana kasuwa abokinsa ya yi masa waya ya ce ga wani tallan babur an kawo wa abokinsa kuma ya ga irin nasa ne ya zo ya duba ya gani, ai kuwa babu ɓata lokaci ya yi masa kwatance ya tafi wurin, shi kuma abokin ya ce musu zai siya ya riƙe su da magana har Salia ɗin ya ƙaraso, tun daga nesa ya gane babur ɗinsa, ai kuwa ya yi ta hamdala a zuciyarsa, ya ƙaraso suka gaisa ya ce"Ina mai babur ɗin?" Wani saurayi ya ce"Ga ni". Ya ce"Nawa ne?" Ya ce"Gaskiyarsa dubu ɗari uku, amma babu takardunsa, dayake mun yi gobara kwanan baya, amma ba shi da wata matsala!". Salis ya ce"Mu ga mukullin". Yana miƙa masa ya yi wani murmushin farin ciki ganin har keywalder nasa ne, ya zura mukulli ya tashi babur ɗin ya hau ya buga ya ce"Ku biyo ni a baya". Bai ma jira cewarsa ba ya yi tafiyarsa. Saurayin yana ta kiransa bai saurare shi ba, kai tsaye ya yi police staiton. Abokin Salis ɗin ya kira shi a waya, ya ɗaga ya ce"Ka riƙe shi zan dawo da ɗan sanda". Ya sauke wayar ya kalli saurayin yana dariya ya ce"Kar ka damu zai yi gwaji ne, dama yana ta nema zai siya". Suna zaune suna ɗan taɓa fira sai ga shi ya dawo da ƴan sanda biyu cikin fararen kaya, suna sauka Salis ya nuna shi, nan take suka kama ƙugunsa, suka ɗunguma zuwa staion ɗin yana ta tambayar me ya yi cikin ƙarfin hali, saboda ya san babur ɗin sata ne dama. Ba a wani sha wahala ba ya faɗi sunan Maman Ameera a matsayin wacce ta ba da babur ya siyar mata, sannan ya faɗi yadda aka yi ya je ya ɗakko shi a gida, baƙin ciki, kunya, danasani suka rufe Salis, da ya san haka ne ai ba zai kai abun staion ba a tozarta surukarsa, gefe ya ja ɗan sandan ya ce masa a kashe case ɗin, abun ya zo a bazata na gida ne, ɗan sanda ya ƙi yarda ya ce dole sai sun hukunta wannan saurayi kuma sai an zo da Ameera da babarta, da ƙyar ya yarda ya ba shi cin hanci aka sallami saurayin, wanda yana tafiya bai zarce ko'ina ba sai gidan Babar Ameera, ya zayyane mata komai, hankalinta ya tashi sosai, har sai da ta zaga banɗaki, ta kira Ameera ta faɗa mata asiri ya tono. Ameera ta hau salati tuni ta fara hawaye ta ce"Kin ga abin da nake gudu ko Umma? Ga shi kin sa duniya za ta yi min kallon ɓarauniya, yanzu ya zan yi?" Umma ta ce"Ya kuwa za ki yi? Mazewa za ki yi, idan ya yi magana ki saka masa kuka kawai, ki ba shi haƙuri, abun kunya dai an yi shi". Ameera ta katse wayar tana nazari cike da nadama, yayinda Salis ya buga babur ɗinsa ya tafi gidan Hajiya. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/1, 11:49 AM] Sadiya Abdulrazak: 20 Da fara'arsa ya shiga gidan bayan sun gaisa da Hajiya ya ce"Hajiya kin ga dai asirin ɓarawon babur ya tonu, Allah Ya bayyana gaskiya, ga babur a ƙofar gida". Hajiya ta ce"Alhamdulillah! Addu'a ta karɓu kenan, ita Safiyyan ce ta fito da shi?" Salis ya ce"Hajiya kenan, ai na faɗa miki ba ita ba ce, to ƙarshen magana dai ƴarki Ameera ce ta ɗauki babur ta aikawa babarta za su siyar". Nan ya kwashe labari daki- daki ya bata. Hajiya ta ɗauki dogon salati ta dire tana tafa hannuwa, ta ce"Ikon Allah! Wannan fa shi ne ana zaton wuta a maƙera sai ga ta a masaƙa, ashe mun ɗauki alhakin Safiyya". Cikin jin daɗi ya ce"Ai dama ni ban yarda ita ba ce, ko da aljanu suka faɗa ai dama an ce suna ƙarya suna haɗa faɗa kuma". Hajiya ta riƙe haɓa ta ce"Lallai wannan yarinya ta yi mana bazata, ita kuwa me ya yi mata zafi haka? Sai kace azal, ko dai aljanun ne suka far sakata sata?" Ya ce"Hajiya kuma idan su ne ai ba za su tona asiri da kansu ba". Hajiya ta ce"Yo na ga kashi-kashi ne a kan nata, ga wanda Safiyya ta aika mata ga masu tonon asiri, gobe kuma ba mu san waɗanda za su bayyana ba, wallahi satar ma sai su saka ta, na ga har haukata mutum suke yi". Salis ya ce"Wannan dai babu wani hauka, sata ce kawai, kuma ni dai ban hana ta abinci ba, Allah dai ya kyauta!". Hajiya ta ce"Ba ta kyauta wa kanta ba, amma don Allah kar ka faɗawa ƴan'uwanka ni zan je da kaina na mata nasiha, kuma kar ka yi mata hayagaga ka ga tsohon ciki ne da ita, kar wata matsalar ta faru". Ya ce"Hajiya ni dai tun da ga babur ɗina ai magana ta wuce, yanzu na je na dawo da Safiyya?" Hajiya ta taɓe baki ta ce"Wannan kuma ruwanka ne!". A gidan ya ci abincin dare sannan ya fito kai tsaye ya tafi gidan su Safiyya. Kiranta ya yi a waya ya ce yana ƙofar gida, ta fito ya shigo zaure suka gaisa babu yabo babu fallasa, ya ce"Don Allah Safiyya ki yi haƙuri, ɗan leƙo ki ga". Ya yi waje ta bi shi ta leƙa ta yi mamakin ganin babur,amma ta ɓoye mamakinta ta ce"Me zan gani?" Ya ce"Babur ɗina mana, kin ga dai Allah Ya bayyana gaskiya, ashe Ameera da babarta ne suka ɗauka za su siyar". Safiyya ba ta wani yi mamaki ba don dama ta yi zargin hakan, ta ce"To Allah Ya tsare gaba". Ya ce"Amin, daga gidan Hajiya nake ai, ta ce na ba ki haƙuri na je na taho da ke ki koma ɗakinki". Safiyya ta ce"Da ba ka zo tafiya da ni ba sai da ta tabbata ba ni na ɗauka ba ki, ka ga alamar ni kake zargi sai yau da gaskiya ta fito, to ni babu inda zan koma, gara na ba ku iska kai da matar so ƴar lelenka da danginka". Ya yi murmushi ya ce"Haba Safiyya, ke ma dai kin san ba a canzawa tuwo suna, ai ba ni da ƴar lelen da ta fi ki, duk wacce za ta zo daga baya saura ta tarar, ni wallahi da muke tsayen na sai na tuna shekarun baya, kamar zance na zo". Ta taɓe baki ta ce"Allah Ya kyauta, ni zan shiga gida sai da safe". Ya ce"A haba Safiyya, don Allah fito da yaran mu tafi komai ya wuce ai, me kuma za mu jira? Na ba ki haƙuri su ma sun ce a ba ki haƙuri". Safiyya ta yi murmushi ta ce"Baban Ni'ima na gaji da dmuwarku daga wannan sai wannan, ɗan kwana biyun da na yi a gida har hankalina ya kwanta, ba ni da wata matsala, yanzu ina komawa za a ɗora daga inda aka tsaya, ka bar ni na huta nan da sati biyu ko uku zan koma in sha Allah". Ya yi wani murmushi ya ce"Safiyya kenan, ashe za ki iya sati uku ba a gidana ba? Ni yanzun ma ban yarda hankalinki a kwance yake ba, sai na ga ma kamar kin ɗan rame, shiga ki fito don Allah! Na fi so kawai ta ga mun shigo a tare ga kuma babur, sai ta fi jin kunya". Safiyya ta ce"Babu ruwana da jin kunyarta, ni dai na ce ka bari sai na ƙara hutawa tukunna". Ya ce"Don Allah, kin ga yau ma ranar kwananki ne kuwa, na san kin yi kewata". Ta ce"Babu wata kewa, da nake can ɗin ma kana yi da ni ne? Kai da kake da amarya babynka?" Ya ce"Wace baby da ƙaton ciki, yanzu ai ke ce babyn kin gan ji ƴar caras babu ciki babu goyo, wallahi kwanan baya na zata ma za ki ce min ciki ne da ke, da na ga sai ƙara kyau kike yi abunki". Ta taɓe baki ta ce"Baban Ni'ima sai da safe". Ba ta ma jira cewarsa ba ta shige gida, tana ji yana kiranta ba ta juyo ba, tsaye ya yi a ƙofar gidan yana shirin tafiya sai ga Baba ya dawo, suka gaisa ya faɗa masa an samu ɓarawon babur, amma bai faɗa masa matarsa ce ta ɗauka ba, Baba ya ce"Ma sha Allah! Allah Ya tsare gaba". Ya ce"Amin, zuwa na yi mu tafi gida amma ta ce ba yau ba". Baba ya yi murmushi ya ce"Ko ba ta huce ba ne, to ka yi haƙuri gobe sai ta koma". Ba dan ya so ba ya ce"To Baba na gode sai da safe". Baba ya ce"Allah Ya tashe mu lafiya". Ya shige gida Salis ma ya tafi. Cike da jin haushin Ameera ya shiga gidan, shi bai ma san ta ina zai fara ba, yanzu me zai yi mata ya huce? Ita ba abun ya dake ta ba, sosai ya ji nadama da ya bari Safiyya ta tafi saboda sharrin da ta mata, shi yanzu ya fara zargin babu wasu aljanu ma wallahi, ba don kar ya ƙaryata su tashi su masa hauka ba da yau sai ya fito mata a mutum wallahi. Da ya shigo da babur ɗin cikin gida sai da ya wani wina shi kamar zai yi kwabo, sannan ya fara danna horn babu ƙaƙƙautawa, Ameera da ke ɗaki cikin nadama gabanta ya ci gaba da faɗuwa jin shigowarsa da babur, "Magana ta tabbata" Ta faɗa tana ɗauke ƙwallar da ta zubo mata, tana jin shiru alamun ya kashe babur ɗin ta nemi ƙasan kafet ta kwanta ta fara wani numfarfashi tana dafe ciki. Shi kuwa wanka ya yi, ya yi shirin bacci sannan ya shigo ɗakin nata, turus ya yi ganinta kwance a ƙasa tana wani sauke numfashi, "Wayyo marata, na shiga uku!" Ta faɗa tana kukan ƙarya. Ya ƙaraso yana mata kallo a ɗage ya ce"Lafiya?" Ta ce"Tun safe nake mawuyacin hali, ciwon mara ina ga haihuwar ce, wayyo Allah na". Salis ya ɗan ruɗe ya ce"To ai sai ki tashi mu tafi asibiti". Ta tashi tana cije baki, ta sako hijjabi suka fito, ba ta ɗauko komai na haihuwa ba don ta san ƙalau take, tana tafiya da ƙyar har suka ƙarasa titi, suka hau adaidaita sahu suka tafi asibiti, suna zuwa aka duba ta aka ce ba haihuwa ba ce, nan likitocin suka ce dama akan ji hakan idan an kusa haihuwa, don da Salis ya matsa ce musu ta yi ciwon ba sosai ba ne, don kar ma su jagwalgwalata sosai, aka sallame su, a daidaita sahun suka yi shiru sai ita da take share hawaye lokaci-lokaci. "Sannu!" Ya faɗa ciki-ciki. Ta ce"Yawwa na gode". Suna ƙarasawa gida ta kwanta, ta fara baccin ƙarya, ƙyale ta ya yi sai da safe sa yi maganar. Washegari kuwa da safe ya gama shirin fita ya haɗa shayi ya sha, don duk ranar kwanan Safiyya Ameera ba ta girki da shi saboda ba ya bari ta kwana a ɗakin, ya kammala komai ya shiga ɗakinta ya tarar tana bacci, ya bubbuga fulon da take kwance, ta ƙi motsawa, ya kai hannu ya bubbuga ƙafarta, sai kuwa ta tashi zaune a firgice tana zazzare ido ta ce"Su waye akanmu? Waye ya katse mana mafarkin da muke yi na ƙoramar ajali?" Sai ta saki wani ƙara mai ƙarfi ta duro daga gadon tana wata haniniya, Salis da ya saka a ransa dole ya rage jin tsoronta, tsayawa ya yi daga inda yake yana yin bismillah yana tofa mata, sai dai ganin ta yo kansa gadan-gadan ya fasa jarumtar, ya fita da gudu bai bi ta kan babur ba ma ya fice daga gidan yana kullo ƙofa, a ƙofar gida ya zauna ya yi tagumi yana tunanin mafita. Ita kuwa Ameera murmushi ta yi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, ba dan cikinta ya yi nauyi ba da yau ƙaramar mahaukaciya za ta zama, don ya kiyaye ta sosai, saboda idan ya zo mata da zancen babur wallahi ba ta san me za ta ce masa ba, ta yi nadamar aikata son zuciya, kuma ta ɗora laifi akan Ummanta don ita ce ta azalzale ta da zancen kuɗi ai, ga shi ta bar ta da borin kunya. Salis ya jima a ƙofar gida, sannan ya dawo, ya leƙa ɗakin nata, ya ganta kwance, sai ya yi zaton ta yi bacci ne, ya fice ya tafi kasuwarsa. Da daddare da ya dawo gidan su Safiyya ya wuce, ya kira ta a waya, ta fito suka gaisa, yana murmushi ya ce"To Allah Ya nuna mana yau ɗin, sai ki zo mu tafi ko?" Ta ce"Ni dai sati uku na ce maka, ba mu yi da kai ka dawo yau ba". Ya ce"Ni ai mun yi da Baba, ya ce yau idan na zo ki bi ni". Ta ce"Ikon Allah! Amma Baba bai faɗa mini ba, ga shi kuma yau ba ya gari". Salis ya ce"Haba Safiyya yanzu har sai ya faɗa miki? Don Allah ki bar yi mini haka, ki fito da yara mu tafi". Ta ce"Ba fa zan koma yau ba baban Ni'ima, sai na gama hutawa, kafin na ka ƙara samun space da babynka". Ya shafa kai ya ce"Ikon Allah! Wato duk kowa sarki ne idan ka zo neman alfarmarsa, hmm Safiyya kenan". Ya ciro waya ya kira Baba, sai dai har kira uku Baban bai ɗauka ba, ta kuwa ji daɗin hakan ƙwarai, haka dai ya gama surutunsa ya tafi, ransa babu daɗi. Yana zuwa ya tarar da takalmin baƙi a ƙofar Ameera, yayyunta ne Umma ta turo su duk dai akan babur ɗin ne, suka tafi bayan sun gaisa da Salis a kunyace. Ya shiga ɗakin, tana zaune ta sunkuyar da kai, ya ce"Ameera ke ce?" Sai ta fara hawaye ta sakko ƙasa ta saka gwiwowinta tana kuka, don yayyunta faɗa sosai suka mata suka ce ta ba shi haƙuri, ta ce"Don Allah ka yi haƙuri da abin da ya faru, kuskure ne da sharrin shaiɗan, in sha Allah ba zai sake faruwa ba". Ya nemi waje ya zauna ya ce"To me ya faru?" Ta ce"Babur ɗinka da na ɗauka..." Sai ta ci gaba da kuka, har ta ɗan ba shi tausayi, duba da yanayinta na mai tsohon ciki. Ya ce"Tashi ki zauna Ameera". Ta gyara zama a ƙasa, kanta a sunkuye. Ya ce"Ameera na hana ki ci da sha? Ko na tauye miki haƙƙi?" Ta yi saurin girgiza kai ta ce"Ka yi haƙuri". Ya ce"Ban ji daɗi ba sam! Wannan dai na yafe miki, amma ya zama na ƙarshe, gaskiya idan haka ta sake faruwa dole za mu samu matsala babba, don ba zan iya zama da ɓarawo ba". Ta ce"Na gode". Ya ce"Ya jikin naki?" "Da sauƙi" Ta amsa cike da kunyarsa. Ya ce"Shi kenan ya wuce, ita ma Safiyya gobe in sha Allah za ta dawo sai ki ba ta haƙuri, tun da kin sa an ɗauki alhakinta". Baƙin ciki ya rufe ta, ita ta so ma a ce ya yanke hukunci da wuri ya sake ta tun lokacin, kuma wai ta ba ta haƙuri saboda neman raini? Ai kuwa ba zai yiwu ba. Ya ce"Hajiya ta zo?" Ta ce"A'a". Ya ce"Ta ce za ta zo, ita ma sai ki ba ta haƙuri, tun da ba ki kyauta ba, kowa ransa ya ɓaci". Ta ce"To, ka yi haƙuri don Allah". Ya ce"Wannan ya wuce, sai ki kiyaye!". Ya tashi ya tafi ɗakinsa, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/2, 6:12 PM] Sadiya Abdulrazak: 21 Har ya kwanta Baba ya kira shi, suka gaisa ya ce masa ya ga miss call, Salis cike da kunya ya ce"E wallahi dama ɗazun ina gidan ne, da na ji jiya ka ce yau na zo mu tafi da Safiyya, to kuma sai ta ce ba ku yi haka da ita ba, shi na na kira na ji, amma yanzu na dawo gida ma". Ya ce"E na manta ban faɗa mata ba, yanzu dare ya yi, amma gobe in Allah Ya kaimu ka je ka ɗakko ta". Salis ya yi masa godiya ya ajiye wayar, haka kawai ya ji ya yi kewarta, da ba ta nan sai ya ji gidan duk babu daɗi wallahi, har so yake gari ya waye, yana jin ma tun safe zai ɗakko ta kafin ya tafi kasuwa. Da safe Baba ya kira ta suka gaisa ya ce"Safiyya akwai sauran matsala tsakaninki da yayanki ne?" Ta ce"A'a" Ya ce"To me ya hana ki bin shi ki koma ɗakinki?" Ta ce"Babu komai". Ya ce"Zaman gidan ne ya miki daɗi? To lallai lallai gobe idan ya zo ki bi shi ku koma, kar na dawo na same ki a gida". Ta ce"To Baba". Suka ajiye waya. Washegari da sassafe ya kira ta ya ce idan zai tafi kasuwa zai zo ya ɗauke ta. Ta ce"Da ni za ka kasuwar?" Ya ce"A haba dai, ki koma gida mana, wai saboda ki ɗan kaɗe ƙura". Ta ce"A'a ka bari sai ka dawo, ni gidan kitso ma zan je". Ya ce"To na gode Safiyya, yanzu zan turo kuɗin kitson don Allah ki yi har da lalle ma kin ji?" Ta manta rabon da ta yi lalle ya yaba, saɓanin shekarun baya da idan ya ga hannunta babu lalle har gori yake yi mata ya ce ba su da maraba da shi, ta yi murmushi ta ce"Lalle ai sai amarya, ni nawa tuni ya daina burge ka". Ya ce"Haba Safiyya ki daina gwasale ni don Allah! Idan na yi kuskure a baya na zo gyara ai sai ƙarfafa mini gwiwa, nawa zan turo miki?" Ta katse kiran, ya kira ba ta ɗaga ba, sai ya tura mata dubu biyar, ta tura masa saƙon godiya, bayan sun karya ta shirya yara suka tafi gidan Yaya Aminu, Salma ce ta kira mai yi mata kitso da ƙunshi ta yi musu har yaran, kuma ta biya kuɗin, tana ta tsokanarta amarya bayan ta ji komai da ya faru, ta kuma ba wa Safiyya wasu shawarwarin, Salma ta ce"Yau za ki koma ki ga idon mai gajeren wando" Suka saka dariya. Salma ta ce"Ko za ki yi wani, yanzu na aika a samo kayan aiki?" Safiyya ta yi ƴar dariya ta ce"Ƙyale ta ta kusa haihuwa fa, ta kanta take". Salma ta ce"Hmma Safiyya kenan, wallahi da tana ta kanta da ba ta yi miki sharri ba, wai ma me ya hana tun kafin su Hajiyan su zo ki ce ke ma naki sun tashi ki ci mata uwa? Kai da ni ce da tuni ta nutsu". Safiyya ta ce"Kar ki damu, ai akwai ƙanwarta zan yi wa Yaya magana na haɗa su". Ta kwashe da dariya ta ce"Wallahi ina jiranta". Sai da yamma ta koma gida bayan Salma ta haɗo mata kayan mata, saboda ta ce mata yanzu ita ce amaryar Baby ta zama rugwagwa, ta koma gida tana jin zuciyarta wasai, Yaya Aminu ya yi dacen mace ta gari, ba dan ita ba da wataƙil har yanzu ba zai dinga tuna alaƙarsu ba ballanta ya ja ta a jiki, amma yanzu ko anko ne na ƴan'uwa dole sai ta yi, don kuwa sai ya cakewa Salma kuɗinta da na Safiyya cass. Ana idar da sallar magriba Salis ya zo gidan, yau har cikin gida ya shiga suka gaisa da Umma, ya ba ta dubu biyu, sannan ya tafi waje yana jiranta, su Ni'ima sun yi gaba da kayanta, suna ta yi masa fira, ita kuma kawai ta samu waje ta zauna a ɗaki, tana jin daɗi har ranta yau za ta koma ɗakinta, sai dai tana fargabar ta inda wata matsalar za ta sake kunno kai, a haka dai ga Salis kamar gaske, amma dayake shi sam bai san kissa da kaidin kishiya ba, da wuri ake juye masa kai, sai da ya kira ta a waya sannan ta taso ta fito, ta yi wa Umma sallama da godiya ta fita. "Bismillah!" Ya faɗa yana tada babur ɗin, don har ya ɗora yaran. Ta ce"Ni ba zan sake hawa babur ɗinka ba fa, ka samo min adaidaita sahu". Ya ce"Haba Safiyya, kenan dai da sauran rina a kaba". Ta juyar da kai gefe, ya ce"Don Allah hau mu tafi Safiyya". Ta ce"Ba fa zan hau ba". Ya jinjina kai ya ce"To bari na turo mai adaidaitan". Ya tafi titi ya turo mata wani mai adaidaita, ta shiga suka tafi, ya riga su ƙarasawa yana ƙofar gida yana jiranta, ya biya mai adaidaita suka shiga gidan a tare, a lokacin an fara kiraye- kirayen sallar isha'i. Ameera da ke tsakar gida tana alwala ta ɗago ta yi musu kallo ɗaya ta ci gaba da alwalarta, shi ya buɗe mata ɗakin ta shiga, ta hau gyarawa, shi kuma ya ce"Bari na je na samo muku wani abun, me za a siyo". Ta ce"Mun ci abinci ai". Ya ce"To bari na karɓo muku kaza, amarya ai sai da kaza" Ya ƙarasa yana dariya, Ameera ta ji kalmar amarya sai da kaza ta shaƙa kuwa, farin cikinta ma yau ɗin ranar kwananta ne, ta ga ta ƙaryar amarcin. Da ya dawo ta gama gyara ɗakin ta saka turare, ta idar da sallah kenan tana zaune suna fira da yaran, ya shiga ɗakin ya zauna yana ajiye mata ledojin, ta je kitchen ta ɗakko palate ta juye suna ci tare da yaran cikin nishaɗi abun sha'awa. Ameera tana fitowa daga wanka ta fito ta ɗage labulen Safiyya cike da gadara ta ce"Sannunku!". Safiyya ta ce"Yawwa sannu". Ta tsaya tana bin shi da kallo ranta a ɓace. Safiyya ta ce"Baiwar Allah lafiya dai ko". Ameera ta ce"Ita ta kawo hakan". Safiyya ta ce"Ina fa lafiya kin tsaya a kanmu da ƙaton ciki durum kamar elagement ɗin jaka? Ai gara ki shigo ki zauna, bisimillah!" Safiyya ta yi maganar tana murmushi ta tura mata palate ɗin. Ameera ta ce"Ke ba sa'ar yi na ba ce. Kasan dai yau ranar kwanana ce ko?" Ya ce"To da na sani kin ga na kwana a nan ne, ai zan koma ɗakin nawa sai ki jira ni a can". Ta ce"To ai gani na yi babu niyya wai ango ya kwana da wando". Safiyya ta ce"Don Allah je ka, sai da safe kai ne yau Baby take binka? Lallai ga muguwar shekara inji kwaɗo da ya faɗa ruwan zafi". Ameera ta saki labulen ta shiga ɗakinsa ta kwanta cike da takaici. Shi kuma har ƙarfe goma suna fira sannan ya je ya kwanta, yana ji a ransa Ameera ba za ta canza ba, ya ce idan ta dawo ta ba ta haƙuri ba ta ba ta ba sai ma neman rigima da take. Bayan sati biyu da dawowar Safiyya, gidan da sauƙi, don Ameera ta yi nauyi ba ta wani neman rigima, kowa harkar gabansa yake yi, babu wata matsala da ta sake shiga tsakanin su. A cikin sati na ukun ne kuma rana ɗaya Ameera ta fara naƙuda, lokacin bayan azhar ne, ta fara jin ciwon, tana ta daurewa sai da aka yi la'asar sannan ta kira shi ta faɗa masa, ya baro kasuwa ya zo gidan, Safiyya ba ta san me yake faruwa ba, ta dai ga ya shigo ya shige ɗakin Ameera, babu jimawa kuma ya fito ya shiga nata ɗakin ya ce"Safiyya Ameera ce ba ta da lafiya ina jin haihuwar ce, ko za ki zo mu tafi asibitin?" Ta ce"Abun ya zo kenan, Allah Ya raba su lafiya, amma na zo mu tafi yaran fa ina zan kai su?" Ya ce"Ko maƙota ai sai ki miƙa su". Safiyya ta ce"Ba ta kama ni ba gaskiya, yanzu ban da wata maƙociya". Ameera ta ƙaraso ta ce"Wai ce maka na yi ba ni da dangi da sai kishiya ta raka ni haihuwa, haihuwar da dama don dai babu yadda za a yi da ni ne!". Da mamaki ya ce"Ke da kike fama da kanki Ameera meye na wannan zantukan? Ke da za ki shiga tsakanin rayuwa da mutuwa, to Allah Ya kyauta!". Suna tsaye ta ɗaga waya ta kira yayarta ta faɗa mata ta ce mata su yi gaba ga ta nan zuwa, suka fice tana wani hura hanci, abu biyu ya haɗar mata ga jin haushin Safiyya har ma da Salis ɗin ga zafin ciwo. Bayan sallar isha'i Ameera ta haihu lafiya, ta haifo ƙaton ɗanta namiji kamar Salis, a kai ta yi mata barka ana farin ciki, shi ma cikin farin ciki yake ta kiran ƴan'uwa yana faɗa musu Ameera ta sauka lafiya. Hajiya kuwa kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha don farin ciki sai waya take tana sanarwa kamar ba ta taɓa yin jika ba. Safiyya har ta fara bacci wajen sha ɗaya na dare Salis ɗin ya dawo, ta ji shigowarsa amma ta bar shi sai da safe ta ji halin da ake ciki, bayan mintuna sai ga shi yana buga mata ƙofa, ta taso ta ce"Baban Ni'ima". Ya ce"Ki buɗe". Ta buɗe, ta ce"Sannu ya mai jikin?" Ya ce"To kin damu da jikinta ne? Ai Safiyya kin ba ni mamaki wallahi, yarinya tana naƙuda na ce mu tafi asibiti ki nuna ko'inkula, kuma tun da muka tafi ko ki yi min waya ki ji halin da take ciki, yanzu da na shigo na zata ma zan tarar ba ki kwanta ba kina jira ki ji yadda ake ciki, ashe ke har kin fara bacci, to Ameera ta haihu lafiya, ɗanta namiji yana nan gobe da safe za a sallame ta" Bai jira cewarta ba ya koma ɗakinsa a fusace. Safiyya mamaki ya daskarar da ita tana tsaye riƙe da ƙofa, ita sam ba ta san ta yi laifi ba wallahi, a fili ta ce"Allah Ya kyauta!" Ta koma ta kwanta. Washegari da asuba bayan ya dawo daga masallaci ya shigo ɗakinta, ta gaishe shi ta ce"An samu ƙaruwa Allah Ya raya mana". Ya ce"Amin, sai ki haɗa musu abun karyawa ita da yayarta ce suka kwana, da safen nan ma dai za a sallame ta". Ta ce"To, Allah Ya ƙara lafiya". Ta haɗa abinci da yawa, ta je ta faɗa masa ta shirya, shi ma a shiryen ya fito ya ce"La ba ki ga wata leda a hanyar banɗaki ba?" Ta ga ledar kuma ta fahimci mene ne a ciki, ta ce"Na ga leda". Ya ce "Kayan Ameera ne suka ce na kawo gida, ko za ki ɗauraye su idan muka dawo?" Ta ce"A'a gaskiya ba zan iya ba, gara dai idan sun dawo a samu mai wankewa, kayan jini ai sai naka!". Ta yi gaba, ya yi ƙwafa cike da jin haushi, ya fita da babur ya ɗora yaran ta ja ta tsaya, ya ce"Ke nake jira!". Ta ce"Ku yi gaba zan nemi adaidaita". A fusace ya ce"Ba na son wulaƙanci Safiyya kar ki kai ni bango, wato ke yanzu kin wuce ki hau babur ki keta unguwa ko? Kin raina arziƙina! To ki koma ba sai kin je ba". Ta ce"Ni dai ba haka nake nufi ba". Sannan ta ƙarasa ta hau babur ɗin suka tafi. Kusan a tare suka ƙarasa da Hajiya, fuskarta kamar gonar auduga, a tare suka shiga Safiyya ta duƙa ta gaishe ta, ta amsa tana cewa Ni'ima"Kun yi ƙani, ko ma na ce Yaya tun da shi namiji ne". Safiyya ta ce"Ai kuwa dai". Suka shiga, sai da suka fara gaisawa da Hajiya sannan Safiyya ta ce"Sannu Ameera, Allah Ya raya mana". Ta amsa da amin. Hajiya ra karɓi ɗan sai farin ciki take yi ta ce"Oh! Da farko Salisu ya yi ƙin auren nan ashe dai ke za ki haifa masa magajin gidansa, kai ma sha Allah! Laya ta yi kyaun rufi". Safiyya sai da ta tsargu, ta yi murmushi dai kamar yadda kowa ya yi, sannan ta matsar mata da kwandon da ta zubo abinci ta ce"Ameera ga abinci, ga shayi ma". Ameera kamar ba ta ji ba ta ce"Hajiya me na samu ne?" Ta ce"Kunu ne na dama miki na sayi ƙosai da waina a hanya maza zuba mata" Ta ƙarasa tana kallon yayar Ameerar, ta zuba mata sannan ta ce"A haɗa miki shayin?" Ta girgiza kai amar a'a, suka ci gaba da fira har da Salis ɗin, ita sai ta zama ƴar kallo, ga shi ta gaji da tsayuwa ita da yaran, ta kalli Salis ta ce"Zan koma sai kun taho". Ya ciro kuɗin adaidaita ya ba ta ya ce"Anjima zan aiko yo aike sai ki dafa mata kafin su dawo". Ta ce"To Allah Ya raya". Ta haɗa kan ƴaƴanta suka fice, Hajiya ta bi ta kallo tana taɓe baki, Ameera ta bi ta da harara ƙasa-ƙasa. LITTAFIN IYA RUWA... NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/2, 6:12 PM] Sadiya Abdulrazak: 22 Wajan ƙarfe goma ya aiko mata naman kai, da icen wanka, ta ɗora sannan ta ɗora girki a gas ɗin Ameerar, ta fito ta gyare gidan tsaf, ba ta gama girkin ba ma suka dawo, ta ƙara yi musu sannu da barka, suka wuce ɗakin Ameera, ashe tare da Hajiya suke ta shigo lokacin Safiyya tana kitchen, tana jiyo ta tana faɗin"Wai ba a ɗora ruwan wankan ba dama?" Har kitchen ɗin ta bi Safiyya, ba da hayaniya ba ta ce"Haba Safiyya yau ko zaman yanke-yanke kuke yi da yarinyar nan ta haihu ai kya ɗora mata ruwan wanka, mene ne amfanin kishiyar idan babu taimakon juna?" Ta ce"Hajiya ba a ce na ɗora ba, kuma tun da na dawo kin ga girki nake yi mata ban zauna ba". Ta ce"Au to ashe ita kike yi wa girkin, don Allah ku haɗa kanku ki taimaka mata, ke ma idan kika haihu za ta yi miki". Ta ce"To Hajiya". Ƙin fitowa ta yi daga kitchen ɗin har sai da ta fara gano hayaƙi alamar an ɗora ruwan, sannan ta zubo abincin da naman ta kai ɗakin Ameera, ta ajiye, yayarta tana banɗaki tana wanke kayan, ta koma ta zubowa Hajiya a kula ta kawo mata, ta koma ɗakinta ta kwanta, sai wajan azhar Hajiya ta bar gidan, da yamma kuma ƴan'uwan shi da nata suka dinga zuwa barka ita dai tana ɗaki tana jiyo su suna jefo mata habaici lokaci-lokaci, ku ƴan'uwan shi har suka tafi ba su leƙo ɗakinta ba, ita ma ba ta je ta gaishe su ba, ashe hakan ta yi laifi, da daddare da ya dawo ya zo ya dinga faɗa wai ta raina ƴan'uwansa sun zo ba ta je ta gaishe su ba, ta ba shi haƙiri ta ce bacci take yi shi yasa. Da daddare yayarta ta tafi, sai washegari ta dawo da sassafe ta ɗora ruwan wankan, tana ɗaki Salis ya shigo suka gaisa ya ce"Yanzu Safiyya ko ruwa ba za ki na ɗora mata ba kafin yayar tata ta zo?" Ta ce"Baban Ni'ima ka ga fa kwana biyun nan ciwom idona kamar zai dawo, ballantana na shiga hayaƙi". Ya ce"A lallai na ɗaure miki gindi da nake zuba miki gas, har ni za ki cewa hayaƙi?" Ta yi shiru tana ɓata rai, don gaskiya ba ta jin za ta yi wa Ameera wahala, tun da ba ta san mutunci ba ita ma. Haka aka ci gaba da yi kullum yayarta ta zo ta dafa ruwa ta yi musu girki idan sun yi wankan yamma ta tafi, saura kwana uku suna Salis ya zo ya ba ta atamfa turmi biyu ita da yara da dubu uku kuɗin ɗinki, ta karɓa ta yi godiya. Washegari ta faɗawa Salma yadda aka yi, sannan ta tura mata dubu goma ta ce ta siyowa yaran ƴan kanti, ba za ta saka musu atamfa ba, Salam kuwa a ranar ta tafi kasuwa ta siyo musu kaya masu kyau, ta siyo kayan jariri kala uku masu kyau, ta siyowa Safiyya leshi rantsattse, saboda faɗawa Yaya Aminu ta yi kishiyar Safiyya ta haihu kuma ba ta da kuɗin gudunmawa ba ta da sabon kayan da za ta saka idan ba ta yi ba zai zama abun magana, ya turo mata dubu arba'in, ta ɗora dubu goma a kai kuɗin ya zama dubu sittin har na wajen Safiyyar, a ranar ta kai mata ɗinki, ana gobe suna ta kawo mata Safiyya ta yi farin ciki sosai ta faɗa mata Baba ma ya turo mata dubu biyar ya ce ta bayar gudunmawa, Salma tana gidan har yamma sai da su Yaya Fa'iza suka zo suna tsara girkin da za a yi goben sannan Salma ta ce ta kai mata kayan barkar, Safiyya ta ɗakko atamfa ɗaya cikin wanda Salis ya ba su su ɗinka ta ɗora a kai, kayan yaro kala uku da dubu biyar ɗin wajan Baba, ta shiga ta gaishe su ta miƙa mata ta ce"Ameera ga shi Allah Ya raya". Ta yi mata godiya ciki-ciki, sai da ta fita suka buɗe kayan, Ameera ta taɓe baki ta ce"Ai dama na ga shekaan jiya ya shiga ɗakinta da leda, su ne dai ya ba ta ta bayar, wataƙil ma sai da ta rage, sauran suka ce za ta aikata, har da masu rantsuwar sun san dole sai da ta rage. Da daddare da ya shiga ɗakin Ameera ta ɗakko kayan ta nuna masa ta ce Safiyya ta kawo kayan barka, so take ya ga iya wanda ta kawo don ya san wanda ta rage ɗin, da mamaki Salis ya ce"Ikon Allah! Ita kuwa Safiyya ina ta samu kuɗi haka? Kaya sun yi, an gode". Ameera ta bi shi da kallon sheƙeƙe ta ce"Haba Honey sai ka ce ban san kai ne ka ba ta ta kawo ba?" Ya ce"Wallahi ban ba ta komai ba bayan atamfa da na basu ita da yaran, don su ma su saka sabo, ni ban san za ta yi wa jariri kayan barka ba sam". Ameera ba don ta yarda ba ta ce"To ga shi dai ta yi da kuɗinta, kenan har ɗinkuna ka yi musu su ma?" Ya ce"A! To ba zan yi musu ba Ameera? Idan ba ta saka sabon ba ai sai a zage ni, ke mai haihuwa na miki leshi da atamfa ita kuma na mata atamfa bai yi ba?" "Hmm! Ya yi" Ta faɗa ranta babu daɗi, ita so ta yi a ce an ga Safiyya da tsohon kaya a cikin tsumma ita da yaranta, kuma kar ta yi wa jariri komai yadda za a yarda baƙinciki take yi, kowa ya zage ta, sai ta ga akasin hakan, ga shi ban da yajin daddawa da rigunan yaro kala uku sai atamfa babu abin da Ummanta ta yi, ta ce ba za a kashe kuɗin nan dole sai an sayi filin nan, shi yasa ranta duk a jagule yake. Ranar suna tun safe ake ta aikin abinci kala-kala, Safiyya ta shiga cikinsu ta taya su, wajan azhar ta zame ta yi wa yaranta wanka ta saka musu kayansu masu kyau, ita ma ta saka wanda ba ta taɓa sakawa ba, Ameera da kalle ta ta taɓe baki, don ta yi zaton ita ce atamfar da Salis ɗin ya ba ta, sai da yamma da Ameera ta saka leshi, ita ma Safiyya ta saka nata wanda ya fi na Ameera kyau nesa ba kusa ba, ta yi kwalliya ta yi kyau sosai ta ci ɗauri ta fito tana gaisawa da baƙi, Ameera da ƴan'uwan Salis baƙin ciki kamar ya kashe su, Ameera gani tayi ma kamar tata kwalliyar ta dusashe Safiyya kawai ake kallo, ta koma ɗaki ta ƙule a gado tana jin lallai Salis ya raina mata hankali, wato ita ma har da leshin ya mata ya ce iya atamfa ce, ita da shan wuyar haihuwar amma an musu komai kai ɗaya har ma leshin Safiyya ya fi kyau, ga ƴaƴanta ma ashe ƴan kanti ya siya musu masu kyau an shirya su kamar ƴaƴan mai kuɗi, a ranta har ta fara jin anya ma kuwa za ta tafi gida wanka ta bar su tare a gidan? Allah ne kaɗai ya san yadda za a yi kafin ta yi arba'in ta dawo. Haka aka yi taro aka watse, Safiyya tana alwalar sallar isha'i ta ji Ameera tana waya da Salis tana ta masifa wai babu kayan miyan da za a dafa naman kai, ba ta san me Salis ɗin ya ce mata ba Safiyya ta ji tana cewa"Ai kuwa sai dai a bar shi ya lalace, indai ba za ka nemo kayan miya ba!". Safiyya ta yi murmushi, ta idar da sallah ta fito za ta shiga kitchen ta ga naman kan a buɗe a wajen murhun da ake dafa ruwan wankan, lokacin ƴan'uwan Ameera duk sun tafi, ita kuma ta shiga wanka kasancewar ba ta yi na yamma ba yau ɗin, Safiyya koma ɗakinta ta ɗakko mukullin ɗakinsa, don kafin ya fita ya ba ta ya ce idan za a ƙara wani abun na kayan abinci ta bayar, ta je da sauri ta buɗe ɗakin ta ɗakko naman kan nan ba ta dire shi a ko'ina ba sai tsakiyar katifar Salis ɗin, ta taka kujera ta ciro ƙaton ragon dake saƙale don jansa ma ta yi a ƙasa shi ma ta kai shi ta ajiye, ta janyo ƙofar, sannan ta kai mukullin ɗakin Ameera ta ajiye a kan kujera, ta koma ta zubo abincinta tana ci hankali kwance. Salis yana dawowa ya shiga ɗakinsa kawai ya ci karo da wannan lamarin, ransa ya yi matuƙar ɓaci, ya fito a fusace ya shiga ɗakinta, sai cika take tana batsewa, ya ce"Ameera kenan wulaƙancin naki har ya kai haka?" Ranta ya ƙara ɗugunzuma, dama a ƙule take da shi ya ce"Ni ce ma nake wulaƙanci ba kai ba ko?" Ya ce"Ameera ni kike faɗawa haka? Saboda raini don na ce ban san inda zan samu kayan miya da daddare ba shi ne za ki kai nama ki ajiye a wajen kwanciyata?" Ta ji gabanta ya faɗi ta ce"Ban gane ba!". Ya ce"Za ki gane!". Ya fice, ta bi bayansa, tsaye ta gansa a tsakar gidan ya ma rasa me zai yi. Ta duba inda naman kai yake ba ta gansa ba, ba ta damu ba ta yi zaton wata tashigar da shi kitchen, tana shirin ce masa ya shigo mata da ragon ɗaki sai ta ga ba ta gan shi ba, da mamaki ta ce"Ni ina suka saka ragon ne?" Salis a matuƙar fusace ya ce"Wallahi Ameera ki shiga hankalinki, ki yi takatsantsan da ni, don wulaƙanci ki rasa inda za ki kai rago sai ɗakina kuma yanzu kina son raina mini hankali?" Ta zaro ido da mamaki ta ce"Ɗakinka kuma?" Tun kafin ta ƙarasa shiga ɗakin ta ga robar naman kai da da rago kwance a katifa, gabanta ya faɗi ta ce"Wallahi ba ni ba ce, kuma ƴan'uwana ma babu mai yin wannan aikin wallahi, sai dai ko haɗin faɗa" Ta ƙarasa tana kallon ɗakin Safiyya. "Safiyya!" Ya ƙwala mata kira. Ta fito ta ce"Ka dawo ashe sannu". Ya ce"Waye ya ajiye nama a ɗakina?" Ta ce"Ni kuwa meye hurumina da nama da zan sani?" Ya ce"Amma dai ke na barwa mukulli". Ta ce"Ka bar min mukulli amma da suka karɓa suka ƙara shinkafa ba su dawo min da shi ba". Ameera ba ta sani ba ko an ƙara shinkafar don haka ta yi shiru, ta shiga ɗakin ta fito da su ta kai ragon ɗakinta naman kai ta kai kitchen. Ya ce"Ku fito min da mukullina!" Safiyya ta ce"Ni kam ba ya ɗakina". Ameera tana shiga ɗaki ta gan shi a kan kujera ta ɗakko ta ba shi, sannan kunna gas ta ɗora naman kan. Safiyya tana shiga ɗaki ya bi ta, ya ce"Safiyya wa ya ba ki kuɗi kika sayi leshi kika siyawa yaranki kaya?" Ta ce"Yaya Aminu ne". Ya ce"To ki faɗa masa daga yau kar ya sake yi min haka, babu ruwansa da harkar gidana, abin da Allah Ya hore min na kawo miki dole shi za ki saka, idan kin fi ƙarfin gidan nan Safiyya ki fita ki yi rayuwar da kike so, Aminu ya ci gaba da ciyar da ke yana yi miki suturar da na kasa miki". Da mamaki ta ce"Kenan kana nufin ɗan'uwana ba shi da ƴancin kyautata min saboda mijina ba ya so? Za ka raba hanta da jini ne?" Ya ce"Ni ban isa na raba ku ba, amma sutura ban amince ya ƙara miki ba, wacce na kawo ita za ki saka, ashe atamfar da na ba ki mayar min da ita kika yi tun da kin kai wa matata a matsayin kayan barka, to ɗakko ɗayar ki ma ki ba ni abata!". Tsam ta tashi ta ɗakko ta ajiye masa ya juya zai fita ta ce"Mu ɗan dawo baya mana, da ka ce na fita daga gidan na je Aminu ya ci da ni me kake nufi? Don wannan magana ce mai harshen damo". Ya ce"Ni babu abin da nake nufi, na dai faɗa miki ne kawai ki kiyaye, su Hajiya sai faɗa suke min na fifita ki akan me jego da ta sha wuyar haihuwa, sun kasa ba ni na miki ba, to gaskiya ba zan lamunta ba ai shi ma da biyu ya miki, yana ganin yanzu ya fi ni arziƙi, to idan babu dama sai ki koma gidan nasa ai dama can mai arziƙi ya so ki aura, kuma shi ma zan masa gargaɗi!". Ta ce"To zan tafi tun yau, ina ga zai fi ko?" Ya ce"Ba za ki kiyaye ɗin ba kenan?" Ta ce"Zan dai tafi saboda gudun sake faruwar hakan". Ya ce"Ai ban ce ki tafi ba! Ki kula dai". Ya fice daga gidan. Sam ba ta shakkar ya tunkari Yaya Aminu don Aminu babansa ne a rashin mutunci idan ya kawo masa raini tsaf za su dambace, ballantana dama har yanzu ba son Salis ɗin yake ba, ta jima tana shawarar ta tafi ko ta zauna, kafin ta yanke gara ta tafin kawai, a wannan karon ta je ta daɗe ko zai gane tana da amfani, haɗa akwati ta yi, yara har sun fara bacci ta tashe su, suka fito, ashe yana ƙofar gida tana fitowa ya zo ya tare ƙofa ya ce"Ina za ki je?" Ta ce"Inda ka ce na je mana!". Ya ɓata rai ya ce"Koma!" Ta ce"Zan tafi ɗin zai fi". Ya ce"Ki koma!" Ta ce"Wallahi sai na tafi!". Ya ce"To ba ni ƴaƴana!" Ta saki hannun Kausar dake cikin nata ta ce"Ga su dama ban zo da su ba". Ni'ima ta fara kuka ta ruƙo ta tana "Umma zan biki" Safiyya ta buge hannunta ta yi tafiyarta, shi kuma ya daka wa yaran tsawa ya haɗa kansu suka shige ciki. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/2, 6:12 PM] Sadiya Abdulrazak: 23 Tsawar da ya yi musu ce ta maida kukan nasu ciki, a tsakar gida suka tsaya, baƙin cikin abin da Safiyya ta yi masa ya ji shi sosai, Safiyya ta canza gabaɗaya ta koyi wani taurin kai da kafiya cikin ruwan sanyi babu hargowa, ko me ya ce mata tun da ya ce kar ta tafi ai bai kamata ta tafi ɗin ba. Ameera da ba ta san me yake faruwa ba, ta fito daga kitchen ta shiga ɗaki ta ga ya biyo ta da yara, ya ce"Ku zazzauna mana". Suka zauna a ɗarare saboda ba su saba shiga ɗakin nata ba, Ameera a ƙule take da shi don haka ta yi banza da su tana jira ya faɗi dalilin kawo mata su ya jera, shi ma ya san fushi take da shi ga kuma neman alfarma ya taso babu zato, ya ɗan sassauta murya ya ce"Ina Sauban ɗin?" Ta ce"Bacci ya ke". Ya ce"Amma na ce ki daina barin shi shi kaɗai ki dinga goya shi". Da faɗa ta ce"Kenan a bayana zai dawwama!? Da me zan ji? Ko yanzu ba daga kitchen nake ba, ga gajiyar zirga-zirgar da na yi ta suna, ga gajiyar haihuwa ka ce wani kar na kwantar da shi?" Ta juya kai tana ɓata rai sosai. Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Wannan ke ta shafa, ni dai ki daina barin shi shi kaɗai". Ta harari yaran ta ce"Waɗan nan kuma fa?" Ya ce"Ni'ima ce fa da Khausar, ba ki gane su ba?". Ta ce"Na san su ne ai, ina nufin me suka shigo yi?" Ya ce"Ke ma ai uwarsu ce, don sun shigo ɗakinki har kya tambaya?" Ba ta kula shi ba, ya ce"Ajiyar su na kawo miki...". "Kamar ya ajiya, sai kace wasu kaya? Ina uwar tasu?" Ta katse masa maganar da ya kwaso Duk da ransa ya ɓaci amma ya daure ya ci gaba"Ta je gida ne, na ce kar ta tafi da su, to za su zauna a wajenki ne kafin ta dawo". "Tabɗijan!" Ta faɗa ba tare da ta shirya ba, to ita ko sakin Safiyya ya yi za ta yi farin ciki ne kawai saboda ta bar mata gida za su baje ita da yaran da za ta haifa, amma ba zai taɓa yiwuwa ta riƙe mata ƴaƴa ba. Ya ce"Me kike nufi da tabɗijan?" Ta ce"To na ga dai ka san gobe zan tafi gida wanka, kuma ka zo min da zancen yara". Ya sani tun kafin ta haihu take zancen zuwa gida wanka, don Umma ce ta kafe akan hakan, saboda su samu ko dubu hamsin a haɗa kafin ta yi arba'in, amma shi ne zai kawo mata yaran kishiya? Salis ya ce"Ni wallahi ba son zuwa gidan nan nake ba, tun da kin ga ita yanzu ta tafi, ni kuwa ba biko zan je ba, don wulaƙancin nata ya fara yawa gara ta zauna a gidan ta ɗanɗana tukunna da ƙafarta za ta dawo". Ameera ta taɓe baki, ita ma za ta so hakan, amma sai idan ba ita za ta riƙe masa yara ba, ta ce"To ai kuwa ba zai yiwu ace haihuwar fari ban samu hutu ba, ita fa mai zuwa wankan nan daga gobe za ta daina, to ya zan yi ga aikin gida ga ɗawainiyar jariri ga kuma waɗan nan abubuwan da ka kawo min? Sai dai ko za ka nemo wacce za ta dinga yi mana hidima, ka ga ko a ɗakin babarsu sai ta zauna tun da ita ba a san ranar dawowarta ba ko?" Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Ni kam idan ba ƙyauye zan tafi ba a ina zan samo miki mai zama? Ga su nan dai kafin gobe na yi shawara". Ta ce"To ka kai su gidan Hajiya mana". Ya ce"Ai kar ta ce ke kin gaza shi yasa" Ya faɗi hakan don ba ya tunanin Hajiyar ma za ta riƙe ta daɗin rai, kuma ba lallai su samu kulawar da yake buƙata ba, ga Hajiya ba ta zaman gida wuni take ta yi nan ta yi can, sai dare ta kwanta ta ce ciwon ƙafa. Ya ce"Allah Ya kai mu goben za mu yi shawara da ita". Ya kalli yaran sun takure a gefe suna rabon ido, suka ba shi tausayi, amma ya za su yi uwarsu ce ta ja, ya ce"Kun ci abinci?" Suka ɗaga masa kai. Ya ce"Za ku ƙara?" A tare suka girgiza masa kai alamar a'a, ya ce"To za ku kwana a nan kun ji ko?" Nan ma suka gyaɗa kai. Ameera ta ce"To ai da ka yi musu shimfiɗa a ɗakinsu, tun da dama ta saba barin su su kaɗai ta kwana a ɗakin miji". Ransa ya ɓaci ya ce"A'a ki musu shimfiɗa a nan! Ta ya za a bar su su kaɗai, idan wani abu ya faru cikin daren fa?". Ta ce"To ka ɗakko musu abun shimfiɗa, don nawa duk a wanke suke kar su yi min fitsari". "Hmmm!" Kawai ya ce, ya buɗe ɗakin nasu ya ɗakko musu abun shimfiɗar ya kawo mata, a falo ta musu shimfiɗa, ta sa suka fita suka yi fitsari suka kwanta sannan ya fita, ya zauna a ƙofar gida ransa babu daɗi. Ita kuwa ganin su a falon ma wani baƙin ciki take ji mara misali, ta ja tsaki ya fi cikin carbi, can Kausar ta ce"Yaya ruwa" Don Yaya take cewa Ni'ima. Ni'ima ta tashi zaune ta ce"Anti ruwa za mu sha". Ameera ta ce"Ubanki ke da ruwan, munafuka har da wani Anti, sai yau kuka san Anti da kullum ana yi muku huɗubar zagina, ko gaishe ni ba ku san ku yi ba!". Kausar da ba hankalin sanin abin da ke faruwa ta yi ba ta ƙara cewa"Yaya ruwa zan sha". Ameera ta ce"Ke buhun ubanki! Yau ga ƴan iskan yara marasa mutunci salon ku sha ruwa ku saka ni wanke kayan fitsari, Ni'ima da ita ma take jin ƙishiruwan sosai ta ce"Wallahi ba ma fitsari a kwance". Ta ce"Kuka ƙara magana sai na murɗe bakin gadon nan, gadon rashin kunya, shegu indai ya ce sai na riƙe ku uwarku za ku ci da mai da yaji, gayyar tsiya kawai". Ta saka sakata ta shige ɗaki. Babu daɗewa bacci ya ɗauke su, wani wahalallen bacci suka yi, saboda sauro, babu net babu maganin sauro ga ƙishiruwa da suke ji, don dama suna da shan ruwa har tsakar dare farkawa suke yi su sha. A ɓangaren Safiyya tana tafe kafin ta ƙarasa titi tana ta tunanin yadda rayuwar aurenta ta yi juyin waina lokaci ɗaya, indai haka kishiya take ba ta fatan ko ƴaƴanta su zauna da ita, gefe guda kuma tana ganin kishiyar ma hali ta tarar, don abin da ya faru yau ai bai shafi kishiya ba laifin shi ne, ƴan'uwan shi ba sa son ta sam, sun fi so su ganta cikin tozarci da ci baya a rayuwarta, kuma Allah bai amince ba, ban da wulaƙanci ta ya zai ce kar ɗan'uwanta ɗaya tilo ya yi mata kyauta? Bayan ta shiga adaidaita sahu gidansu ta ce ya kai ta kai tsaye, cikin jin kunya ta shiga gidan, ita da tun da ta yi aure tsawon shekarun nan ba ta taɓa yaji ba, amma ga shi canjin yanayi ya sa ta yi yaji sau biyu a wata ɗaya, duk saboda ya ƙara aure. Ta yi sallama, tsakar gidan babu kowa, daga ɗaki Umma ta amsa sannan ta fito, turus ta yi ta ce"Safiyya ce da daren nan?" A sanyaye ta ce"Ni ce Umma ina wuni?" Umma ta ce"Kuma dai? A bun bai ƙare ba kenan?" Daidai nan Baba ya fito, don tun da ya yi sallar isha'i ya kwanta saboda zazzaɓi da yake yi, ta ce"Baba ina wuni?" Ya ce"Safiyya lafiya? Ina yaran?" Ta fara hawaye ta ce"Suna gida". Umma ta ɗakko tabarma ta shimfiɗa suka zazzauna Baba ya ce"Me ya faru kuma Safiyya?" Ta share hawaye ta faɗa masa duk yadda aka yi. Baba ya ji babu daɗi ya ce"Yau ga zancen banza! To shi kuwa Salisu ko dai ya manta tsakaninku da Aminu ne? Hauka ake yi da za a ce ya daina hidimta miki? Idan bai yi miki ba waye zai yi miki, wa ya san gobe? A yau idan na kwanta dama shi kuma zaman naku ba a samu daidaito ba kina da inda ya fi gidan Aminu ne?" Umma ta ce"Wallahi babu! Gaskiya Salisu ya yi mana bazata, ni fa shi yasa dama can ban so auren nan ba, duk inda dangin miji suka ce babu kai to kar ka shiga, amma kuka dage, yanzu ga irinta nan, wancen zuwan naki ɗan aiken da nake yi miki nan wani ya aiko babarsa ya ce idan kin gama idda, na ce ai da aurenki!" Cikin fushi Baba ya ce"To ke kuma akan me za ki aike ta? Kar a sake aikenta". Safiyya ta tashi za ta shiga ɗaki, Baba ya ce"Zauna ai ba mu gama ba". Ta dawo ta zauna Ya ce"Salisu ba shi da dalilin da zai ce Aminu ya daina miki hidima, amma ke kuma ba komai idan aka yi za ki kwaso ki taho gida ba". Ta ce"Baba shi ne ya ce na tafi gidan Yaya Aminun na zauna, kuma na bar masa yaranshi". Ya ce"To shi kenan gobe dai na ji ƙarin bayani daga bakinsa, je ki kwanta". Ta je ta gyara ɗakin ta kwanta, wannan karon har da net ta ɗakko, sai kuma ta tuna su yaran ko yau a ina za su kwana? Ko za a saka musu net ɗin? Ta sauke ajiyar zuciya, tana son Salis har yau kuma har yanzu, amma yanzu ta fara sarewa ta fara tunanin dole sai ta yi nesa da shi zai gane shi ma bai daina sonta ba, bai daina tsoron rabuwa da ita ba kamar yadda ita ma har yau tana jin rabuwa da shi ba mai yiwuwa ba ne. Idan ta rabu da shi anya za ta iya rabuwa da yaanta mata har biyu? Wa zai ba ta riƙe? Ameera za ta iya kuwa? Idan ta riƙe wace tarbiyya za ta ba su? Dole za ta koma ko dan ƴaƴanta, amma akwai buƙatar ta daure na wani lokaci ta ba su iska, da wannan tunanin bacci ya ɗauke ta cike da kewar ƴaƴanta. Shi ma Salis a nashi ɓangaren tunanin ya dinga yi mai zurfi ma kuwa, har yau yana son Safiyya amma halayen da ta tsiro da su ne suke ɓata masa rai, tun da ya ƙara auren nan gabaɗaya ta raina shi, ya ga da babu abin da Aminun yake yi mata, sai yanzu zai ce wai har sutura zai yi mata saboda ya haɗa shi da matarsa a ce shi ne yake yi mata? Kuma saboda raini ya ce kar ta tafi amma ta kafe sai ta tafi, shi ya yi zaton ma idan ta ji ya ce ta bar yaran za ta fasa tafiya saboda tausayin su, ashe zuciyarta ta bushe, yanzu shi ya zai yi da yaran nan? Ya yi alƙawarin ko shekara za ta yi ba ta dawo ba, ba zai neme ta ba kuma ba zai ba ta yara ba, sannan ba zai sake ta ba, ita kuma Ameera idan ba ta kiyaye shi ba akan yaran nan sai sun samu matsala don ya ga kamar ma kallon wulaƙanci take yi musu. Washegari da sassafe Ni'ima ta fito ta kwankwaɗi ruwa, ta taso Kausar ma ta sha, sannan ta zuba musu ruwa a buta suna alwala Ameera ta fito ta daka musu tsawa"Don ubanku ku tashi daga nan!". Salis da yake kallon su ta windo cikin tausayawa tun lokacin da suke shan ruwan, ya fito ya ce"Kamar ya su tashi?" Don ya lura alwala suke yi, kuma daidai babu kuskure abun sha'awa ya ba shi. Ameera ta ce"To akan me za su tarki wasan ruwa da sassafe sai ka ce ƴaƴan agwagi?" Ya ce"E ni da uwarsu ai agwagi ne dama, ni suka gado, kai ku yi alwalarku" Ya faɗa yana kallon yadda suka bar butocin duk sun firgice. Ta shiga kitchen fuuu tana huci. Da suka gama ya ce su shiga ɗakinsa, a nan suka yi sallah, Ni'ima ta ce"Abba yau za ta dawo?" Ya ce"A'a, ba yanzu ba sai an daɗe, ba ga ni ba za mu yi zamanmu?" Suka gyaɗa kai ransu babu daɗi. Da ta gama haɗa abun karyawa ta shige ɗakinta, ya ji shiru ba ta kawo musu ba, ya je ɗakin ya ce"Ameera ina abun karyawarmu?" Ta ce"Ikon Allah! Ka manta yau kwanan Safiyya ne?" Shi ma da mamakin ya ce"Kar fa ki raina min hankali, ai kin san ba ta nan, kuma na ce miki ban san ranar dawowarta ba ko? Kuma idan ni ba za ki ban ba su yaran fa?" Tana ɓata rai ta ce"Bari na gama abin da nake yi tukunna!". Ya ce"Kar ki gama, ki dawwama kina yi". Ya fice, ta bi shi da harara, wanka ya yi musu ya buɗe ɗakin ya saka musu kaya, sannan shi ma ya yi, ya leƙa ɗakin nata ya ce"Kayan miya da me za a kawo muku?" Ta ce"Shi ne kawai, fita za ka yi ne?" Ya ce"E, akwai matsala ne?" Ta ce"To ni fa ana gama soya naman nan zan tafi gida". Ya ce"Kar ki tafi, sai na yi shawara tukunna". Ta ce"Kamar ya shawara?" Bai kula ta ba, ya haɗa kansu suka tafi gidan Hajiya. A hanya ya tsaya ya sayi biredi da ƙosai ya tafi da shi, bayan sun gaisa ya miƙa mata ya ce Hajiya "Akwai shayi kuwa?" Ta ce"Akwai shayi, lafiya na ganka da yara kana neman shayi?" Ya ce"Hajiya ai jiya saboda na mata magana akan kayan da ta saka ta ce yayanta ne ya mata, na ce ta faɗa masa kar ya sake yi min haka, shi ne ta yi fushi ta tafi ta bar yaran". Hajiya ta ce"Oh! Wannan yarinya da kiciyi take, ai sai ta yi ta tafiya, yo wata uwar za ta samu a gidan nasu?" Ta ɗakko flaks da kayan shayi ta miƙo masa tana cewa"Ita ina Ameerar? Ko ruwan shayin ba za ta iya dafawa ba?" Salis ya ce"Hmm ƙyale ta Hajiya, cewa ta yi ba ranar kwananta ba ne yau". Hajiya ta riƙe haɓa ta ce"Shi yasa ba za ta baku shayi ba?" Bai ce komai ba suka fara karyawa, da suka gama ya ce"Hajiya ga yaran nan, anjima zan kwaso kayansu". Ta ce"Kai dawo baya" Ya dawo Ta ce"Yanzu ni za ka bari da wahalar yara ina fama da ciwon ƙafa?" Ya ce"To ina zan kai su? Ita yau za ta tafi gida wanka, ni kuma ina kasuwa ya zan yi?" Ta ce"Haka ne, to shi kenan idan ta gama wankan sai ka mai da su can ta riƙe ƴaƴan mijinka ai naka ne". Ya ce"Ai na san ma za ta dawo kafin Ameerar ta dawo, don na san ba iya zaman gidan za ta yi ba". Ya tafi kasuwa bayan ya aika mata kayan miyan. Wajan azhar Aneera ta kira shi, don lokacin an gama rabon nama, kuma ta shirya tsaf sai tafiya gida. Ya dawo gidan ya ba ta dubu biyar da kayan shayi, ya ce zai aiko da kayan abinci gidan, ta ba shi na shi kason har da na Safiyya, ana sallar la'asar ta tafi gida. Shi kuma ya aika wani yaro da naman Safiyya da dubu biyar ya ce ya kai mata, Baba yana gida aka kawo aiken, ya kira Salis a waya bayan sun gaisa ya ce"Mene ne ya haɗa ku da ƙanwar taka?" Ya ce"Wallahi Baba yanzu Safiyya duk ta canza hali, kullum da abin da take tsiro da shi, kuma jiyan sai da na hana ta tafiya amma ta kafe sai da ta tafi". Baba ya ce"Salisu ba zai yiwu ka ce Aminu kar ya yi wa ƴar'uwarsa hidima ba, don bayan ni ba ta da wanda ya fi shi ɗin". Ya ce"Haka ne Baba, a yi haƙuri". Baba ya ce"Don Allah ku haɗa kanku, ku dinga mutunta juna, zan yi mata nasiha itama kuma yau za ta dawo in sha Allah!". Salis ya ce"To na gode Baba". LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/2, 6:12 PM] Sadiya Abdulrazak: 24 Salis ya ajiye wayar yana sauke ajiyar zuciya, kuma ya saka a ransa ba zai je gidan ba, sai dai ta dawo da ƙafarta kamar yadda ba shi ne ya kaita ba, don wancen karon saboda ya nuna son dawowar tata har wani jan aji ta dinga yi masa. Baba ya kira Safiyya ɗakinsa, ya ce"Na yi waya da shi yanzu, ashe sai da ya hana ki tahowa ma ko?" Ta ce"Ai Baba sai da fa ya gama rashin mutuncin nasa sannan ya dawo ya ce kar na tafi, kuma shi gani yake kamar nan a gidan kun gaza min sai a gidansa nake jin daɗi". Da mamaki Baba ya ce"Shi ɗin ne ya ce miki hakan?" Ta ce"To Baba ya ce ba ni da inda ya fi gidansa". Baba ya yi murmushi ya ce"To ai so ne ya sa ya ce miki hakan, kuma da gaskiyarsa ba ki da inda ya fi ɗakin mijinki, idan ka wuce zaman gida ai ka wuce shi sai dai ko ƙaddara, ke kuwa yanzu babu ta inda zaman gida ya kama ki, saboda haka ki shirya ki koma ɗakinki yau ba sai gobe ba". Ta ji wani abu ya tokare mata maƙoshi, tuni idanunta suka kawo ruwa da rawar murya ta ce"Amma Baba shi kenan fa idan na koma zai tabbatar da ba zan iya zaman gidan namu ba, ba ni da gata sai nashi". Baba ya yi murmushi ya ce"Ummi kenan! Har yanzu akwai ƙuruciya, ba a gidan naku ya gani ya yi sha'awa ya aura ba? To me zai sa ya ce ba za ki iya zama a yanzu ba? Ɓacin rai ne kawai shaiɗan ya gifta a tsakani, ki koma ki tsarkake zuciyarki zaman aure sai ka daure ba a samun lada daga kwance, ba wahalar za ki duba ba, ki dinga tuna ibada kike yi, kuma ma duniyar nawa take? Kana tafe ba ka san kwanakinka sun kusa ƙarewa ba". Safiyya dai hawaye kawai take yi, ya ce"Ki uo haƙuri ki shirya ko da magriba ne na san zai zo ya ɗauke ki, ki dinga tuna naki yaran, ke kin taso da rashin uwa kin rayu babu ɗuminta, amma kin ga ke Alhamdulillah Allah Ya ba ki wata uwar ta gari ba ki san wuyar uwar ruƙo ba, su naki yaran kin san ya za su ƙare? Ke ƙaddara ce tun da mutuwa ita ce ajin ƙarshe, su kuwa idan kika bar su kin ga duk abin da ya faru da saka hannunki". Ta tashi za ta fita, ya ce"Dawo ki zauna". Ta dawo, ya kalle ta cikin tausayawa ya ce"Kin yarda za ki koma ba dole aka yi miki ba? Ba na so ki koma kina ɓacin rai". Ta ce"Ba ka yi min dole ba Baba". Ya ce"Na gode, Allah Ya yi miki albarka, Allah Ya ba ku zaman lafiya". Ta amsa da amin, sannan ta koma ɗakinta ta zauna tana ta tunanin yadda za ta ɓullowa zaman nasu, yanzu ta fahimci zama da Salis kamar dole ya zame mata, idan kuwa haka ne to ya zama wajibi ta ci ɗamarar ƙwatarwa kanta ƴanci, ta daina ɗaukar duk wani raini da yake yi mata a kan matarsa, haka ita ma Ameera duk ranar da ta sake kawo mata raini sai sun hau sama sun faɗo idan ya so ko me zai faru ya faru, bayan ta yi sallar magriba ta yi wanka tana jiran zuwan nashi wannan karon ba ta ma faɗawa Salma komai ba, saboda tana fargabar ta daina saka Yaya Aminu yi mata abu, burin Salis da danginsa ya cika don haka ta ja bakinta ta tsuke. Shiru har tara na dare tana zuba idon zuwan shi, ƙarfe goma tana yi ta yi shimfiɗa ta kwanta. Shi kuma a nashi ɓangaren jira yake yi ya ga dawowarta, da ya ga goma ta yi ya san ba za ta dawo ba ɗin, ya yi ƙwafa ya kwashi kayan sakawar yara ya kai gidan Hajiya, sai da ya faɗa mata duk yadda suka yi da Baban Safiyya, Hajiya ta yi wata dariya ta ce"A haf! Ai dama dole za ta dawo, ko wancen karon ma da ta tafi kafin a ga babur don ka matsu ta dawo ne, da ka yi banza da ita da kanta za ta dawo, yo tana da inda ya fi gidan naka ne?" A nan ya ci abinci, sannan ya tafi gida ya kwanta yau damuwarsa da sauƙi tun da ya ji matsayar zance, kuma ya ga Hajiya ta saka su a katifa ta saka musu net, bayan sun ci sun ƙoshi shiyasa hankalinsa ya kwanta. Washegari da Safiyya ta gaishe da Baba ya ce"Me ya hana ki komawa jiya?" Ta ce"Bai zo ba". Ya jinjina kai, ya ce"To babu damuwa". Yau da yamma ya dawo ya kai kayan abinci gidan su Ameera, suka gaisa Sauban na hannunsa ta ce"Ya su Ni'ima?" Ya ce"Suna nan ƙalau". Ta ce"Uwar tasu fa yaushe za ta dawo?" Ya ce"Yau za ta dawo, ina ga ma ta dawo". Ta ji wani baƙin ciki ya rufe ta ta ce"Yau kuma? Kai da ka ce ba a san ranar dawowarta ba? Kenan ka je bikon?" Ya ce"Ban je ba, an dai sasanta ta waya". Ta yi huci mai zafi ta ce"Ai na bar muku gidan kwa fi sakewa ma kafin na dawo". Da mamakin yadda duk ta sauya cikin ƙanƙanin lokaci ya ce"Kamar ya? Ke ɗin me kika tare mana?" Ta ce"Na tare muku mana, tun da na ga wani abun sai ka faki idona kake yi mata, nan ka ce min atamfa ka musu ita da yara ashe leshi ka siya mata har ya fi nawa kyau, kuma da atamfar, yaran ma ka siya musu ƴan kanti masu tsada, hmm ai ni da Sauban za mu ga rayuwa, musamman shi da yake yaro, wataƙil suturar ma ta gagare shi...". Kafin ta ƙarasa ya ɗaga mata hannu cikin ɓacin rai ya ce"Don Allah ya isa haka Ameera, wannan wane irin rashin tunani ne haka? Kina nufin ni ba na adalci a tsakaninku kenan kuma wannan yaron da ko sati biyu bai yi a duniya ba shi ma za ki fara zargin ba zan yi masa adalci ba? Kar ki sake yi min irin haka!". Ya ajiye mata ɗan a cinyarta ya fice daga gidan zuciyarsa babu daɗi, ita ba ta san akan kayan fitar sunan Safiyya take gida ba ne da za ta ƙara masa wani bayani? Ya gama gane halinta tana da ƙorafi sosai da zargi, dole zai taka mata burki. Da ya koma gida bai ga Safiyya ba, ya yi zaton sai dare za ta dawo, dare ya yi ya ji shiru, ya yi baccinsa hankali kwance. A haka aka shafe sati biyu, bai je ya ɗakko ta ba, ita kuma ba ta koma ba, Baba bai sake cewa komai ba, zuwa lokacin Salis ya fara kewarta, kusan kullum a cikin damuwa yake, yau ma kamar kullum dawowarsa daga kasuwa kenan ya sauka a gidan Hajiya kamar yadda ya saba, a ƙofar gida ya tarar da yaransa cikin yaran unguwa suna wasan ƙasa sun yi futu-futu kamar an tono daga rami, dab da magriba ne amma babu mai ɗankwali a kanta, ya ji babu daɗi sosai, ya haɗa kansu suka shiga gidan, a ɗaki ya tarar da Hajiya tare da yayarsa Saude suna fira, bayan sun gaisa ya ce"Haba Hajiya, yaran nan bai kamata suna shiga cikin kowasu kalar yara suna wasan ƙasa ba, anan yara suke koyon wasu ɗabi'un, kuma kansu babu ɗankwali ga magriba ta yi, kamar ba a musu wanka ba". A tsawace ta ce"Ba a musu ba kama su ka yi musu! Ni za ka yi wa maganar banza? Uban wa ya ce ka kori uwar tasu? Saka su zan yi a gaba muna fira tun da sa'annina ne? To idan ba ka kiyaye ni ba wallahi za ka kwashe yau ka tafi da su". Saude ta taɓe baki ta ce"Idan ba ka gamsu da zamansu a nan ba ai sai ka dawo da uwarsu, ta gama rainon nata ƴaƴan ka dawo da ita baya tsohuwar Allah tana fama da kanta ko tausayinta ba ka ji ba?" Ya ji babu daɗi sosai amma ya yi shiru, tun da ko ma me aka faɗa masa shi ya ja, da bai kawo su ba da haka ba ta faruwa ba, bayan ya ci abincin dare zama ya yi suna taɓa fira, da suka zo cin abincin ma sai shi ya saka su wanke hannu da a haka za su ci Hajiya kuma ba ta damu ba, suna shirin kwanciya ya ce"Hajiya ta ya za su kwanta a haka jiki duk ƙasa, ai ƙaiƙayi sai ya dame su na zata za a musu wanka". Hajiya ta tsuke fuska ta ce"Salisu don Allah haɗa kan ƴaƴanka ku tafi! Da daren nan zan hau yi wa yara wanka? Ai da sai ka haɗo su da ƴar aiki tun da dai ni ba baiwarku ba ce kai da su ɗin!". Ta kunna radionta tana ɓata rai. Ya tashi ya yi musu wanka ya nunawa Ni'ima ƙananan kaya marasa nauyi ya ce su za su dinga sakawa idan za su kwanta, sai da suka kwanta sannan ya bar gidan, sai ranar ya fara nadamar tafiyar Safiyya, sam ba ya jin daɗin yanayin da yake ganin yaran, sai ya ji dama bai karɓe su ba ya bari ta tafi da su, ya san su ma za su fi son hakan, ba ya so ya zubar da aji ya ce mata ta dawo, Baba kuma bai sake kiransa ba, shi kenan kullum cikin zuwa gidan Hajiya cin abinci, ga yanayin buƙatuwa da yake damunsa, ban da ƙaddara kamar shi me mata biyu ace yana gwauronci? Abun duniya duk ya ishe shi, a haka ya ci gaba da lallaɓa Hajiya sai dai kullum sai ya yi musu wanka kafin ya bar gidan. Cikin haka ne kuma Kausar ta fara ƙyanda, sosai ta kwantar da ita yarinyar abun tausayi, idan ciwo ya dame ta sai ta yi ta kuka tana kiran Umma ita a kai ta wajen Ummanta, Ni'ima ma duk sai jikinta ya yi sanyi, ta daina fita wasa ita ma kamar mar lafiya babu walwala saboda ganin halin da ƴar'uwarta take ciki, sosai Salis ya damu yake tausayin ƴaƴan nasa, watarana ya yanke shawarar faɗawa Safiyya ko hakan zai sa ta dawo, da daddare ne ya kira ta a waya, ta ɗauka suka gaisa sama-sama ta ce"Lafiya?" Ya ce"Lafiya ƙalau, dama faɗa miki zan yi Kausar tana kwance ba ta da lafiya sosai". Ta ji gabanta ya faɗi, ta daure ba ta bari muryarta ta yi rauni ba ta ce"To Allah Ya ba ta lafiya". Ya amsa da amin, sannan suka ajiye waya, sai da ta share ƙwalla, tana tunanin ko me ya same ta? Ko a wane hali take ciki? Ko ana kula da ita? Bai ma faɗa mata abin da yake damunta ba, kada fa kewa ta kashe mata ƴaƴa, ta fara tunanin kenan ƴaƴanta ba su kai ta sadaukar musu da farin cikinta ba, idan ta ƙi komawa sun mutu tana da tabbacin ba za ta koma gidan Salis ba? Idan ta koma bayan mutuwarsu ko kuma wani naƙasu ya same su me ta yi kenan? Da wannan tunanin ta kwana, amma ta daure saboda ba ta jin za ta koma muddin bai sauke zafin kai ya zo bikonta ba. Tun daga ranar ba ta da walwala, tana so ta ji ya jikin nata amma kuma ba ta jin za ta iya kiransa a waya, gara ta nuna masa ba ta damu ba, kwana uku da faɗa mata ya ji shiru ba ta ma kira shi ba ballantana ta yi zancen zuwa dubiya ko ma dawowa bakiɗaya, don haka rana ta huɗu ya daure ya kira ta, suka gaisa ta ce"Ya mai jikin?" Ya ce"Alhamdulillah za a ce, amma Khausar kam tana kwance, ita ma Ni'ima duk ta zama wata iri, da sai dai su yi ta wasansu amma yanzu ta gaji da rashin ganinki ina jin, saboda sai ta zauna ta yi shiru, sai dai kawai ki ga hawaye ɗaya na bin ɗaya". Sosai ta ji rauni da nadama a muryarsa, ta yi murmushin takaici ta ce"Allah Ya ba su lafiya, Ya kawo mafita". Kamar ya ajiye waya ya daure ya ce"Safiyya". Ta ce"Na'am!" Ya ce"Kin san fa ke ce mafitar". Ta ce"A'a ban sani ba saboda ban ga alama ba, ni kuwa ta ina zan zama mafita?" Ya sauke numfashi ya ce"Na san kina fushi har yanzu, kuma ya kamata ki yi, ni ma na bar ki ne ki ɗan huce, amma yanzu ai komai ya wuce ya kamata ki dawo ko don ƴaƴanki". Ta yi murmushi mai sauti ta ce"Ƴaƴana fa ka ce? Indai don su ne zan zaɓi zamana a nan, tun da na san tun da ka karɓe su daga hannuna kana da inda za ka kai su su samu kulawa fiye da tawa, so kar rashin lafiyar Khausar ya sa ka sare, za ta yi jinya ko ina na nan tun da Allah Ya rubuta, kuma za ta samu lafiya ko ba na nan". Salis ya rasa yadda zai yi, ya daure zuciyarsa ya ce"Ki yi haƙuri Safiyya ki dawo ɗin zai fi, kin ga ni ma zaman gidan duk babu daɗi sai ni kaɗai, na san ana miki kuskure amma za a gyara in sha Allah". Ta ce"A'a ni babu wanda yake min ba daidai ba, don haka Ameera ta gama wanka ta koma ku zauna, sai kun fi samun farin ciki". Ya ce"Haba Safiyya ki manta da komai don Allah! Zan zo yau mu tafi". Ta ce"Kar ka zo, don ba zan koma ba". Ta katse wayar ta ajiye, a yadda take ji ba ta ƙi ta koma a yau ɗin ba, amma tana so ta ƙara lokaci saboda ya ƙara nutsuwa, ta yi sa'a kuwa bai zo ba. Washegari ƙarfe tara na safe ya yi mata waya ba ta ɗaga ba, ya yi mata tex ya ce mata ta ɗauki wayarsa Ni'ima ake nema tun sassafe da ta fita siyan waina ko ta zo wajenta? Sosai ta tsorata da ganin saƙon, don haka da ya kira ta ɗauka, ya ce"Safiyya ta zo?" Ta ce"Ba ta zo ba, Ni'ima ba lallai ta gane gidanmu ba daga gidan Hajiya, tun da ka ga ba sosai muke zuwa ba". Ya katse wayar ya bar ta da tashin hankali. Wajan azhar ta kira shi, yana ɗagawa ya ce"Safiyya don Allah idan kin san ta zo ki faɗa mana, ni ban ce zan karɓe ta ba amma hankalinmu zai kwanta, kin ga ƴar'uwarta jikinta ya birkice yanzu ma suka tafi asibiti da Mariya mu kuma muna ta yawon staitons". Sosai hankalinta ya ƙara tashi, ta katse kiran ta fara hawaye. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/2, 6:12 PM] Sadiya Abdulrazak: 25 Ya sake kiranta ta ƙi ɗauka, Umma ta leƙo ta ce mata za ta fita ta ganta riƙe da waya tana kuka, Umma ta yi murmushi a zuciyarta ta ce'Abun ya zo kenan' don ita a yadda take lura da Safiyya tuni ta fara marmarin komawa gidanta, ta yi musu shiru ne ita da Baban don kar a ce korarta take yi, ta ƙaraso cikin ɗakin ta zauna ta ce"Safiyya me ya faru kike kuka?" Safiyya tana shasaheka ta ce"Ni'ima ce ta ɓata, kuma dama Kausar ba ta da lafiya, yanzu an ce jikin ya matsa sosai saboda ɓatan Ni'ima". Umma ta ɗakko salati ta dire ta ce"Ni'ima ta ɓata? Garin ya, kuma tun yaushe?" Ta ce"Yau da safe yake faɗa min, tun sassafe da ta tafi siyan waina, an zagaye ko'ina har yanzu babu ita". Ta ce"Innalillahi! Yau ga ƙaddara, to ai sai ki tasho mu je, ke ki tafi kan ita Kausar ɗin kar ta haɗiyi zuciya ta mutu, yarinya an raba ta da uwarta ƴar'uwarta da take gani ta ji daɗi ita ma yau babu ga shi ba sabo suka yi da dangin nasa ba ai sai a samu matsala, kin ga shi yaro bai san babu ba, tashi ni ma da fita zan yi, amma ki yi gaba bari na ƙarasa girkin sai je gidan Hajiyar". Safiyya da ta fi tunanin Ni'ima amma da ta ji haka sai ta ga tabbas gara ta fara zuwa wajen Kausar ɗin, ita da take hannu, don Hausawa sun ce ƙwai a baka ya fi kaza a akurki. Hijjabi kawai ta zura ta ɗauki wayarta, sai kuma ta tuna ba ta san ma a wane asibitin suke ba, ta kira shi ya ɗaga ta ce"Zan je ganin Kausar ɗin, suna wane asibiti?" Ya ce"Ni ma kin gan ni a gidan Hajiyar na zagayo na ji ko da wani labari, bari na zo sai mu je". Ya ɗan jima kafin ya ƙaraso, har ta ƙagauta, ta kira Baba ta yi masa bayani shi ma hankalinsa ya tashi ya ce zai kira Salisun, tana ganin kiransa ta san ya ƙaraso ta fita da sauri, ta hau babur ɗin suka tafi, a kallo ɗaya shi ma ya ba ta tausayi, duk ya firgice, tsoro ta ji ma kar ya faɗi a babur ɗin, ba ta ce masa komai ba, sai da suka fara nisa ya ce"Yanzu ma Yaya ta kira ni wai sai an kai takardar haihiwar Kausar, kwanaki kin karɓa ko?" Safiyya ta ce"E suna ɗakina". Ya ce"To mu biya ta gidan mu ɗauka sai mu wuce". Ba ta ce komai ba suka ci gaba s zuga gudu. Tare suka shiga gidan bayan ya buɗe, yana kiciniyar shigar da babur ya ce"Kin san yanzu ɓarayin babur sun ƙara ƙaimi da sun faki ido sai dai ki ji tiii har sun kai ƙaraye". Ita dai ba ta kula shi ba, ya buɗe ɗakin nata, tare suka shiga, ta doshi inda ta san ta ajiye kai tsaye ta fara dubawa, cak ta tsaya ganin ya cire riga ya ajiye yana zare dogon wando, ta yi zaton kaya zai canza ta ce"Ha'a! Dama da kayanka a ɗakin nan?" Ya ce"Ga ki kuwa, ai ke ce manyan kayana, wannan da nake sawa sunansu tsumma" Yana murmushi ya nemi katifa ya kwanta, ranta ya fara ɓaci da abin da yake yi, ta ce"Haba don Allah! Wai me kake nufi ne?" Ya lumshe ido ya ce"Zo ki ji mana ƴar ƙanwata". Safiyya mamaki ya daskarar da ita, lokaci ɗaya takaici ya rufe ta, kenan buƙatarsa ta fi zuwa asibiti duba ƴarsu, kuma a tunaninsa za ta dawo yau ne da har zai wane tuɓe shi ga mai gida, ranta a ɓace ta ce"Wai me kake nufi!?" Ya buɗe idanunsa masu cike da kewarta da kuma buƙatuwa ya ce"Ai kin gane". Ta juya za ta fita, ya tashi da sauri ya ruƙota ya rungume ta ta baya yana ajiye numfashi, a hankali ya ce"Ban yi tunanin zuwan ranar da ƙanwa za ta gaji da Yayanta ba, Safiyya ina son ki, na yi kewarki, don Allah kar ki sake tafiya ki bar ni, ashe ƙarya nake da na ce zan jure". Jikinta ya yi sanyi lokaci ɗaya, ita ma ajiyar zuciyar ta sauke tana jin ashe matuƙar kewarsa da kewar furucin da yake yi mata rungume da ita, hakan ya tuna mata rayuwarsu ta baya, saukar hawayeta ya ji a hannunsa, ya juyo da ita suka kallon juna, sai ta kauda kai tana ƙoƙarin dakatar da hawayen ta ce"Mu tafi asibitin kar su jira ka". Ya ce"Safiyya ke ce lafiyar Kausar, ke ce lafiyar Ni'ima haka ke ce lafiyar Salis ɗinki, don haka Kausar ta samu lafiya, Ni'ima kuma an ganta cikin aminci, saura ni ki saita ni". Sai yanzu ta gane ainahin kan game ɗin, ta rasa taƙamaimai abin da take ji a zuciyarta, ta zare hannunta daga na shi ta nufi hanyar barin ɗakin, ya dawo da ita ta fizge da faɗa ta ce"Kar ka sake yi mini haka! Da bugar min da zuciya za ka samawa kanka mafita? Duk wasan kwaikwayon da za ka yi kada ka sake saka ƴaƴana a ciki, saboda bayan iyayena ba ni da wanda ya fi su, kar ka sake yi min haka, ka ɗorawa ƴarka cutar ƙarya ka janyowa ƴarka musiba ka yi mata fatan ta ɓata? Saboda ko me zai same su ba ka da asara ko?" Ta yi murmushin takaici ta ce"To dama me zai dame ka tun da kana da magajinka? To su matan ni ban raina su ba, saboda haka sun fi mini kowa, kar ka sake haɗa plan da su, gidanka kuma ba zan dawo ba!". Ta juya za ta fita ya ruƙota, yana murmushi sam bai ji haushin maganarta ba, yau wani burge shi take yi sosai, idan ya cire sabon halinta na faɗa sai ya ganta kamar Safiyyarsa ta wancen shekarun ƴar ƙanwarsa, ya ce"Yaya bai kyauta ba, ƙanwar Yaya ta yi haƙuri ko kuma ta yi masa hukunci amma kar ta sake barin shi, ta tuna alƙawarin nan" Ya ƙarasa maganar kamar ƙaramin yaro, wanda hakan ba komai ya ƙara mata ba sai jin haushin abin da ya yi da kuma wanda yake yi a gabanta. Ta ƙara yunƙurin fita, ya saka sakata, ya janyo ta har katifar ya ce"Babu fa inda za ki je Safiyya, kin dawo ɗakinki". Tana hawaye ta ce"Yau da ka buƙace ni ko? Matarka ba ta yi tsarki ba har yanzu ko?" Ya ce"Haba Safiyya me kike cewa ne? Kin san dai duk wacce zan so a bayanki take, ke ɗin ce dai kuma wallahi ke ce gidan nan, ni na kasa ganewa kanki ne, tun da na yi aure Safiyya kamar kin manta da yadda matsayinki yake a wajena, wallahi babu abin da ya ragu, ko abin da kika ga ina yi miki wasu lokatan ni ma ba na jin daɗi a raina, ni ina ga ma asiri aka yi mini wallahi, idan ba haka ba ta ya mace kamar ke namijin da kansa babu wani motsi zai ce tafi gidanku? Ki yi tunani fa, wallahi akwai ayar tambaya a lamarina, haka kwanaki fa na yi ta mafarkin wasu tsuntsye wai ga su nan suna shawagi a kanki, idan na zo zan ɗauke ki sai su kawo min caki, ke kuma kina kuka kina kiran Yayana, mafarkin nan ya firgita ni, shi yasa na ce gara ki dawo don ban san halin da kike ciki a can ɗin ba..." Ranta a ɓace ta ɗaga masa hannu, ta ce"Don Allah Ya isa haka, ai ni ina da fassarar mafarkinka". Ya nutsu ya ji me za ta ce, don shi babu wani mafarki da ya yi, kawai gyaran hanya ne yake yi don ta zauna, ya ce"To ina sauraronki" Ta ce"Zan faro maka ta ƙarshe, da ka ce ba ka san a wane hali nake ciki ba, to zaman gidanmu ya fi mini daɗi a akan zaman gidan nan, saboda a can babu mai takura mini, ƙalau nake rayuwata ban rasa komai ba, ba kamar yadda ka sani a baya ba, yanzu komai ya canza, don haka kar ma ka sake tunanin ba zan ji daɗi a gidanmu ba". Yana ta gyaɗa kai kamar ƙadangare, ta ce"Farkon mafarkinka kuma, su waɗan nan tsuntsayen a zahiri maza ne, don kuwa ɗan zamana a gida suna ta inkiya suna kawo hari saboda sun zata sakina ka yi, kai kuma da kake son ɗaukata suna cakinka to inaga nan gaba idan ka rabu da ni za ka gane muhimmancina, sau ka dawo kana son gyara kuskure lokaci ya ƙure tun da wasu sun yi min ƙawanya, kuma da ka tuna mafarkin da kyau da ka ce ina kiranka gaskiya ba zai zama haka ba, sai dai idan ƴaƴana nake kira". Tun da ta ambaci maza fara'ar fuskarsa ta ɗauke, ya ji kamar ya buge bakinta har sai ya yi jini, amma ya daure don ya ga gudun ruwanta, a fusace ya ce"Kenan Safiyya maza kika je kike kulawa da aurena ko?" Ta ce"Allah ne shaidata ban kula kowa ba, na dai fassara maka mafarkinka ne". Ya tashi ya saka kayansa, ya fice daga ɗakin rai a ɓace, da mukulli ya rufe gidan ya tafi gidan Hajiya zuciyarsa babu daɗi, lallai Safiyya ta gama canzawa, bai taɓa zaton idan ya lallashe ta za ta cije ba, sai ga shi neman ƙure dauriyarsa ma take yi, koma mene ne ba zai bari ta koma gida ba, haka kuma ba zai sake lallashinta ba, su zauna a duk yadda ta zaɓa. Ta ji sanda ya rufe gidan da mukulli, kuma da bai rufe ba ita ma ba ta da niyyar komawa gidan, abin da bai gane ba yanzu ta gane matsayinta a wajen shi, ba zai ƙara yi mata daɗin baki ta yarda ba, duk da ba wai ta daina jin ƙaunarsa ba ne, amma wannan abun da ya yi mata yau rainin hankali ne mai zaman kansa, za ta zauna ko don ƴaƴanta, amma sabon zama saboda ta miƙe ita ma babu wanda zai sake mayar da ita karkatacciyar kuka. Tana zaunen Baba ya kira ta, ta ɗaga ya ce"Ina ta kiran Salisu a kashe". Ta haɗiyi yawun baƙin ciki ta ce"E ai yanzu ya fita daga gidan ma". Ya ce"Nan gidan ya zo?" Ta ce"Baba babu wanda ya ɓata fa, kawai saboda na dawo ya yi hakan". Baba ya yi murmushi ya ce"Yanzu kina gidan nashi?" Ta ce"E". Ya ce"Ina yaran?" Ta ce"Ina jin ɗakko su ya tafi". Ya ce"To Allah Ya rufa asiri, ki yi haƙuri kin ji ko? Ku yafi juna". Ta ce"To". Suka ajiye waya. Yana zuwa gidan Hajiya ya tarar ba ta nan, ya yi sallama a maƙota inda take kai ajiyar yaran, aka fito da su ya ɗora su a babur suka taho gida, yana ƙarasowa tun kafin ya ajiye babur suka shige ɗakinsu cikin jin daɗi, Kausar ce ta yi kan Safiyya ta zaunar da ita a cinya tana jin yadda ta yi kewar su, sannan ta kalli Ni'ima da ta tsaya daga gefe kamar baƙuwa tana ɗan murmushi, ta miƙo mata hannu, ta zo ita ma ta zauna, sai hawaye ya zubo mata tausayin yaran ya ƙara kama ta, ta ce"Na dawo, ba zan sake tafiya na bar ku ba kun ji? Ko kun fi so na bar ku?" Suka girgiza kai alamar a'a. Ta tashi ta shimfiɗa musu tabarma a waje, ta hau gyaran ɗaki, kafin ta gama ya fita ya yo cefane ya dawo ya zauna a gidan, da alama yau ba zai je kasuwar ba, tana gamawa ta yi musu wanka ta canza musu kaya, sannan ta shiga ta gyara kitchen ɗin, don shi ma ya yi ƙura, sai yamma sosai ta gama girkinta mai rai da lafiya, don kaji biyu ya haɗo da su a cefanen, ita ma ta yi kewar dafa kalar abincin da take so, gidan iyayenka ba gidanka ba ne, a gidanka ne kake da ƴancin dafa son ranka, gidan iyaye kuma su ke da zaɓi tun da gidansu ne ba naka ba, a tare suka ci abinci da yaran bayan ta kai masa nasa, babu wanda ya jira sai dare saboda dukansu ba su samu nutsuwar cin abincin rana ba, har gara yaran sun sha garin kwaki a gidan da Hajiya ta ajiye su. Cikin yaranta ta kwanta suka yi bacci mai daɗi da sakewa sosai, ba ta je ɗakinsa ba, shi ma bai neme ta ba. Washegari ta gaishe shi ta haɗa masa abun karyawa, ya ci ya ƙoshi don ya yi kewar abincin gida, kullum sai dai ya ci wainar siyarwa ko shayi a gidan Hajiya indai ba teburin mai shayi ya je ya ci indomi ba, bayan ta gyara gida ta tsife musu kansu ta wanke tas ta tufke musu da niyyar gobe za ta tambaye shi su je kitso. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/2, 6:12 PM] Sadiya Abdulrazak: 26 Washegari da safe sun gama karyawa ta ce masa za ta je kitso ya ce ba za ta je ba, saboda fargaba yake yi har yanzu bai gama sakewa ba, gani yake kawai za ta iya komawa gidan, ta ce"Haba don Allah, yaran nan kalli yadda kansu ya zama, ni ina ga ma tun da na tafi ba a sake yi musu kitso ba. Ba ƙarya ta yi ba babu wanda ya musu kitso har ta dawo, amma duk da haka sai da ya ji ransa ya ɓaci, saboda ta nuna kamar Hajiyarsa ta gaza kenan ko kuma ba ta yi wa yaranta ruƙon da ya dace ba, ya ce"E ba a yi musu kitso ba tun da kika tafi, ai har wanka da wanki ma babu wanda ya yi musu, a haka su ka yi ta rayuwa, kin ga gobe ma kya sake barin su". Ta yi murmushi ta ce"A lokacin ma ai kai ka ce na bar su, ba don haka ba babu abin da zai sa na bar su". Ya ce"Ƙwarai kuwa ni na ce ki bar su, kuma ko gobe idan za ki ƙara tafiya ƙofa a buɗe take, amma babu inda za ki je da su, yara suna hannuna duk inda za ki je". Suka yi shiru na ɗan lokaci sannan ta ce"Baban Ni'ima kana ta ba ni mamaki wallahi, lokaci ɗaya duk ka canza, kalli kalaman da kake yi min kamar ba kai ba". Ya ce"Safiyya ke ba ku lura kin canza ba? Ko ba ki kula da irin rainin da kike yi mini ba?" Ta ce"Ni ban raina ka ba, idan ka ga raini ya shiga tsakani to namiji ne yake rashin adalci, wani abun ina kafewa ne saboda na ga ka yi adalci, so ne ya kawo hakan, duk mai son ka ba zai so ranar ƙiyama ka tashi rabin jikinka a shanye ba". Ya yi shiru yana kallon hotuna a wayarsa. Ta ce"Ni na fi so idan na yi maka laifi ka zaunar da ni ka ce Safiyya kin yi abu kaza me yasa kika yi? Idan na yi sai na faɗa maka dalili, idan rashin fahimta ne na fahimtar da kai, idan kuma ba ni da hujja sai na ba ka haƙuri na kiyayi gaba, idan ban yi ba na yi maka bayani, kai kuma ka yi adalci ka saurare ni sai ka yi bincike kafin zartar da hukunci, amma kai fa ba ka yin haka, duk abin da aka ce na yi kawai sai ka yarda". Hankalinsa yana kan waya har lokacin, amma duk nutsuwarsa tana wajenta, ya ce"Ba yarda nake yi ba wallahi wani abun na san ba ki yi ba, ina yarda kin yi ne saboda a zauna lafiya, ko kuma umarnin uwa". Ta ce"Kuma a ganinka kana yi min adalci kenan?" Ya ce"To ai ya wuce". Ta karɓi wayar hannunsa ta ajiye ta ce"Ni fa na fi so ka faɗa min mene ne sabbin halayen da kake cewa na tsira? Ka ga sai na daina, ina so mu dawo kamar da mu zauna lafiya". Ya ce"To ni dai da ba ki da taurin kai, amma tun da na yi aure kika koya, yanzu ko larurorin da su ka yi ta samun Ameera idan na ce ki mata girki ki duba ki ga yadda kike yi mini, sai ki nuna ban isa ba, kuma dole a tafi a hakan, da idan muna zaune kin ta ba ni labarai kala-kala wataran har na gaji, amma yanzu sai ki yi mini jugum tun da na ƙara auren nan, da da wuri kike shiga ɗakina da daddare, amma yanzu wataran sai na fara bacci ma zan farka na gan ki, kalli jiya abin da kika yi mini, sai haka na kwana kamar mara gata, ɗan oyoyon nan kin daina, su ma yaran da suna ganina za su taho a guje yanzu sun daina, to me na yi muku? Ɗan ƙunshin nan akai- akai kina yi, yanzu Safiyya kin daina, da ke kike wanke min ƴan ƙananan kaya yanzu kin daina, duk saboda na ƙara aure, kuma wannan abubuwan da na jero miki ita ma ba yi min take ba, an ce mai mata biyu ɗan gata ni kuwa ɗan wahala ne, ana gasar kyautatawa miji ku gasar wahalar da ni kuke yi da firgita ni, duk na rame a maimakon ƙiba". Safiyya ta yi murmushi ta ce"Baban Ni'ima kenan! Ai kai da kanka ka rikita gidanka, waɗan nan abubuwan da ka jero duk kai ka ja na daina, tun kafin ka yi auren nan kake nuna mini wacce za ka aura ta fi ni, duk ka canza nan har yajin cin abinci ka yi, ka ke zuwa kana ci a gidan su buduruwa, wannan ba zubar da mutunci ba ne? A ce ba na ba ka abinci shi yasa za ka yi aure, ƙarshe ma cewa ka yi kar na sake shiga ɗakinka sai ka neme ni, haka ɗin kuwa a ka yi, saboda za ka yi sabuwar amarya ka gaji da tsohuwa, yanzu a ganinka zan manta abin da ka yi min na cire ni daga ɗakina ka ba ta ka saka ni a ɗaki ɗaya? Ka ɗauki firji ka ba ta saboda kai ka siya, wannan bai isa ya sa na janye jikina daga gareka ba na kama kaina?" Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"To na ji, za a gyara in sha Allah!". Ta ce"To ni ma zan gyara, in sha Allah". Ya yi dariya ya ce"Oh! Ƙanwata ta zama ƴar rigima, wai har guduna take yi ma ina ji ina gani, kuma Allah da gaske za ki iya rayuwar da babu ni a ciki?" Ta miƙa masa wayarsa tana murmushi, ya riƙe hannunta ya ce"Ki faɗa min mana, yanzu sai ki rabu da ni?" Ta ce"Ai yanayi ne zai zo da hakan, kai ne ka fara furta zan bar gidan nan, komai yana hannunka idan ka ce na zauna zan zauna, idan ka ce na tafi zan tafi". Ya ce"Za mu zauna in sha Allah! Safiyya ai ke ce gidan nan idan na rabu da ke ban yi muku adalci ba ke da ƴaƴanki, ƴan kwanakin nan da ba kya nan yaran sun zama abun tausayi, ni ma fa na ɗan sha wahala ko ta ɓangaren abinci, ke ma ba za ki rasa wani ƙalubalen ba, kin ga mu gyara mu zauna sai ya fi ko?" Ta ce"Haka ne, ai dama kowa yana da ranarsa, ballantana zama ba yau ba ba jiya ba". Ya ce"Yawwa bari na fita, ga shi sai ki yi har ƙunshi ko?" Ya faɗa yana miƙa mata dubu biyu, ta karɓa ta yi godiya, shi kuma ya fita. Daga ranar dai suka fara sabuwar rayuwa a nutse, ita da shi ɗin duk hankalinsu ya kwanta, ya tabbatar Safiyya ita ce gidansa kuma nutsuwarsu shi da ƴaƴansa, suna yin rayuwar farin ciki sosai a lokacin. Bai faɗa mata Ameera za ta dawo ba, sai ganinta ta yi da safe ita da ƙanwarta, lokacin Safiyya tana ƙofar ɗaki a zaune ita da yara, ta ɗan saki fuska ta ce"Maraba da Sauban! Ashe yau za ku dawo". Ameera ba ta san Safiyya ta dawo ba, don bai faɗa mata ba, ita kuma ba ta tambaye shi ta sakankance ba ta nan kuma tana tunanin ba ma lallai ta dawo ba, sosai ta ji haushin ganinta, ita dai a duniya ta tsani ta buɗe ido ta ga Safiyya da ƴaƴanta suna shawagi a gidan nan, har ce masa ta yi ya canza mata gida ya kama mata haya amma ya ce ba zai raba matansa ba. Tana hura hanci ta ce"E Allah Ya dawo da mu". Safiyya ta ce"Ma sha Allah! Wanka ya yi kyau, Allah Ya raya mana Sauban". Ta ce"Amin". Safiyya ta shige ɗaki, su kuma suka shiga gyara ɗakin Ameera, can Ameera ta shigo ɗakin Safiyya ta miƙa mata Sauban ta ce"Don Allah ga shi nan, ya hana mu aiki". Safiyya ta karɓe shi da bismillah tana yi masa wasa, Ameera ta koma ɗaki, babu jimawa ma ya yi baccinsa, wajan sha biyu Safiyya ta fita ɗora girki bayan ta fito da su Ni'ima saboda kar su taɓa shi, tana cikin girki ta ji kukansa, ta taho da sauri sai dai kafin ta ƙarasa ta ja burki ganin Ameera riƙe da kunnen Ni'ima ta murɗe shi tana faɗin"Don ubanki kashe shi za ki yi?" Ta hankaɗe ta da ƙarfi sai da ta faɗi, ta fincikota ta dawo da ita, Safiyya ta ce"Ameera ya isa haka, me ya faru ne?" Ta ce"Kashe min ɗa taso yi, ina kawo kai na tarar tana toshe masa hanci, dama baƙin ciki ake yi don Allah Ya ba ni namiji, idan ban da sun yi gadon baƙin hali Sauban shi da yake namiji nan gaba ba shi ne gatansu ba? Ƴar iskar yarinya!". Tass! Safiyya ta wanke Ameera da mari da iya ƙarfinta, zuciyarta tana tafasa ta ce"Ba ki isa ba! Ke ba ki ma kai ba ballantana ki isa, kin yi ƙarya ki saka ƴaƴana a cikin haukan kishinki na ƙyale ki, wannan yaran ba na ki ba ne nawa ne, saboda haka ba ki da ƴancin ɗaga hannu ki dake su wallahi, yaran da ba ki taɓa yi musu tsarki ba ta ina kika san wahalarsu da har za ki samu damar nuna iko akan su? To wallahi wannan ya zama na ƙarshe, kar ki sake dukar mini ƴa!". Ameera da ke dafe da kunci ta ce"Safiyya ni kika mara? Ni kika mara saboda na daki ƴarki?" Ta ce"Ƙwarai kuwa, zan ma iya yi miki fin hakan!". Ameera ta ce"Wallahi ba ki mari banza ba, yau sai kin yi nadama!". Safiyya ta ce"Ke ce za ki yi nadama, ke ba ki isa ki saka ni nadama ba, shi wanda ya auro ki za ki saka nadama dama ya ce ya yi tun tuni". Ameera ta shige ɗaki kamar kububuwa, ta ɗauki waya ta kira shi, yana ɗaukar waya ta fashe da kuka, ya ce"Ameera lafiya, me ya faru?" Ta ci gaba da kukan ba ta yi magana ba hankalinsa ya tashi ya ce"Ameera wai mene ne ki min bayani, ina Sauban ɗin?" Sai ta miƙawa ƙanwarta wayar ta karɓa ta ce"Baban Sauban Safiyya ce wallahi ta yi mata duka ta tattakata, ta gwara kan Sauban da jikin ƙofa". Salis ya miƙe tsaye cike da mamaki ya ce"Wace ce Safiyya kuma?" Don shi ma bai san yau Ameera za ta dawo ba, ta dai ce masa a cikin satin nan, kuma da yake ba wani marmarin dawowar tata yake ba sam bai saka abun a ransa ba, shi yasa ya yi mamakin jin sunan Safiyya. Nabila ta ce"Safiyya dai matarka!". Ya ce"To a ina kuka haɗu?" Ta ce"Ai mun dawo ɗazu, ina taya ta aiki..." Ameera ta warce wayar ta kashe, don an zo inda ya kamata Nabila ta tsaya sauran bayani nata ne. Salis ya sake kira ba ta ɗaga ba, ya yi tagumi zuciyarsa babu daɗi yana shin Ameera ce musiba a gidansa ko kuwa kishin Safiyya ne? Daga dawowarta yau har an fara? Shi kenan ƴar ƙibar nan dai sun rantse ba zai yi ta ba, watan fargabarsa kuma ya tsaya, ya yi tsaki yana ajiye wayar, shi kam ba zai bar kasuwa akan wannan halin nasu ba, idan ya koma ya ji komai, don idan ya biye musu kasuwar ma sai ya rasa ta duka. Safiyya ta ƙarasa girkinta, tana ta harkokinta a tsakar gida, jira kawai take Ameera ta kawo mata raini wallahi babu abin da zai sa su dambatu a gaban ƴaƴansu. Da daddare da ya dawo ɗakin Safiyya ya fara shiga, ta tsara masa duk yadda aka yi amma ba ta ce ta mare ta ba, ta ce dai ta yi mata gargaɗin kar ta sake dukar mata ƴa. Da ya shiga ɗakin Ameera ya tarar da ita ta cika ta batse, ya ce"Ameera ashe kin dawo, sannu da zuwa". Ta ɓata rai sosai ba ta ko kalle shi ba. Ya ce"Ameera me ya faru ne? Safiyya ta ce ba ta dake ki ba..." "Bura'uban can! Ba ta dake ni ba? Kuma ka yarda ko?" Ta faɗa bayan ta miƙe tsaye. Ya ce"Zauna Malama yanzu gidan nan ya gyaru an daina hayaniya, ki yi min bayani kawai magana ce ta fatar baki". Ya faɗa yana haɗe gira amma cikin zuciyarsa a mugun tsorace yake da ita. Ta ce"Ba zan zauna ba! Ai dole ka ce haka tun da matarka ce ba ta da gaskiya, har nan ta shigo ta karɓar min ɗa ta ce saboda na fi sakewa na yi aiki, ashe sun shirya kashe shi ne, kawai na ji kukansa ina leƙawa na ga ƴarta tana toshe masa hanci, don na ja kunnen yarinyar shi ne Safiyya ta dinga marina, ta hankaɗe ni har kan Sauban ɗin sai da ya bugu, ta yi min duka ta tattakanni!". Ya yi shiru yana kallonta, har ta dire sannan ya ce"Ita Safiyyar?" A fusace ta ce"Ba ita ba uwarta!". Ya ji maganar ta daki zuciyarsa don ji ya yi kamar ta ce uwarka, ya tashi a mugun fusace ya ce"Ameera ni kike zagi? Ni kika zaga?" Ta ce"Ni dai ban zage ka ba!". Ya yi hanyar fita daga ɗakin, a fusace ta riƙo rigarsa ta ce"Kana nufin ta daki banza kenan!?" Ya fizge ya ce"Ta daki banza ta daki jaka!". Ya fice Lokaci ɗaya Ameera ta yi wani tsalle ta dire ta ƙwalla ƙara ta fito a guje ta yi kitchen tana wani ihu tana cewa wallahi ba ta daki banza ba, kan me uwa da wabi yau, ko ni ko ku a cikin gidan nan!". Salis yana jin haka ya yi ƙofar gida da gudu, sai kuma ya dawo da gudu ya shiga ɗakinsa ya saka sakata yana leƙe ta windo. Ita kuwa Safiyya tun da ta ji ta ƙwalla ƙara ta miƙe ta zira dogon wando, ta finciko wayar jikin TV dake saman sif, ta naɗe ta a hannunta ta yi ready. Ai kuwa sai ga Ameera kamar an jeho ta riƙe da muciya da taɓarya, tana zuwa ta shigo tana cewa"Ku fito, Safiyya ki fito ba ki daki banza ba don uwar ubanki, funakukar ƙarya!" Ta wurgo muciyar ta sauka a kan Kausar, Safiyya da zuciya take cinta, ta yi kanta a miliyan ta dinga dukanta ta ko'ina kamar mahaukaciya, ita ma Ameera idonta ya rufe sai dukanta take yi, har dai Safiyya ta hankaɗo ta suka fito tsakar gida, ta dinga tsula mata wayar, idan ta yo kanta sai ta kauce, zane ta kawai take yi, Salis yana windo yana kallon yadda suke ta artabu kamar ƙosassun karnuka, tsoro ya dabaibaye shi, a sanyaye ya ce"Allah ga ni gare ka, Allah ba zan iya ba kai kaɗai za ka iya, Allah ka dube ni ka kawo maslaha a gidana, Allah ka yi min mafita cikin gaggawa!". "La haula wa ka ƙuwwata illa billah!" Ya faɗa a tsorace da ya ga Ameera ta ruga kitchen a guje, sai ga ta fito da tukunya, ta jefowa Safiyya, Safiyya ta ɗauki tukunyar ta ƙwala wa Ameera a kai, Salisu ya ce"La ha ila ha illallahu!". Ya ce"Safiyya da Ameera kowacce ta shige ɗaki, ta sako hijjabi ta tafi gidansu!" Babu wacce ta bi ta kansa Ya ɗaga murya ya ce"Safiyya, Ameera idan na ƙirga uku duk wacce ta ƙara dukan wata a bakin aurenta! Ɗaya, biyu, uku!". Duk suka tsaya suna huci kamar zakuna. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/2, 6:12 PM] Sadiya Abdulrazak: 27 Safiyya ta shiga ɗakinta, sai a lokacin ne ta fara jin kukan Kausar, tana shiga ta ga goshin yarinyar ya kumbura, ashe muciyar ta ji mata ciwo, ita ma Ni'ima kukan take yi ganin ana dambe da babarta duk ta rikice, Safiyya ta janyo Kausar ta fara mulmule mata wajen, amma ihun da take yi ya sa ta sake ta, ta fito riƙe da ita, ba ta ga Ameera a tsakar gidan ba, shi kuma bai fito daga ɗaki ba, ta windo ta yi masa magana ta ce"Baban Ni'ima ka ga ta ji wa Kausar ciwo da muciya". Ya buɗe da sauri, ya kalli yarinyar ya ce"Iyyi! Ba sai ku yi ta yi ba, wataran ma kashe ƴaƴan za ku yi, tun da ba ku da cikakken hankali, yarinya ba ta ji ba, ba ta gani ba za ku nakasa ta". Ya jango hannunta, ya kwantar da ita, ya ce Safiyya ta riƙe ta, ya mulmule mata tana ta kuka, bayan ya gama ya ce"Ku ma da kuke yara ba ku tsira ba, irin wannan idan kun ga idon su ya rufe suna yi, ku dinga shiga ɗaki kuna saka sakata, kun ga dai ko ni ba zama nake ba, don babu wacce za ta nakasa ni". Safiyya ta ce"To ku tashi mu tafi kar mu yi dare". Ya ce"Ina za ku je?" Ta ce"Ta ce ba ka ce kowa ya tafi gida ba?" Ya ce"Haba Safiyya, ai don na kawo maslaha ne, yi zamanki kawai, amma gaskiya ku kula ku san ciwon kanku!". Safiyya ta ce"Kana kallo dai ita ta fara, ni za ta daka? Ai wallahi mai dukana sai ruwan sama, ni dole ma tanadi bulalar zane ta". Ya jinjina kai ya ce"A gidana? A wallahi ba zai yiwu ba, tabɗijan!". Safiyya ta je ta kwantar da Kausar da har lokacin ba ta daina kuka ba, shi kuma ya fita ya samo mata magani, don ya san za ta ji ciwon kai, ya ce Safiyya miƙawa Ameera maganin nan, don na ga lokacin da kika ƙwala mata tukunya a kai". Ta yi ƴar dariya ta ce"Wa ya aike ni? Ka kai mata dai ka lallashe ta". Ya ce"Oh! Gida ya zama na ƴan dambe, daga dawowata ko abinci ban ci ba". Safiyya ta ce"Ai dama irin wannan bari ake sai an ci abinci an nutsu sai a ɗakko zancen a baje". Ta je ta kawo masa abinci, ya gama ci, sannan ya leƙa ɗakin Ameera, a zaune ya tarar da ita da Sauban a hannunta ya ajiye mata magani ya fice bai ce komai ba, saboda ya ji haushin zagin da ta yi masa, haka ya kwana shi kaɗai, ranar kwanan Safiyya ne, amma ta yi zaton Ameera yau za ta karɓi girki, ita kuwa Ameera baƙin ciki ne ya hana ta zuwa ga ciwon kai mai tsanani da ta kwana da shi. Washegari ƴan'uwan shi suka zo yi mata sannu da zuwa, nan take ba su labarin abin da ya faru jiya, amma cewa ta yi Safiyya ta zane ta, ba ta ce dambe suka yi ba, ransu ya ɓaci sosai, suka zo suka samu Safiyya suna ta bala'i da faɗin baƙin ciki take yi da haihuwar namiji, babu kalar cin mutuncin da ba su yi mata ba, ita dai ko kallonsu ba ta yi ba, tana ta kallo a wayarta har suka gama suka tafi, sannan ta ajiye wayar zuciyarta tana zafi. Daga ranar dai abu ya lafa, shiru babu abin da ya sake tasowa kuma, kowa harkar gabansa yake yi, idan Sauban zai wuni yana kuka babu ruwan Safiyya, haka Ameera ba ta sake kula ƴaƴan Safiyya ba, hakan ya yi wa Salis daɗi don yanzu har ya ya fara samun nutsuwa. Bayan wata biyar ya saka su a makarantar boko, sannan ya saka su a islamiyya har Khausar ɗin, suka fara karatunsu cikin nutsuwa. Salis da Safiyya duk sun yi zaton shi kenan Ameera ta miƙa wuya za a zauna lafiya, ashe wasa farin girki, watarana da daddare kawai Ameera ta fito tsakar gida ta yi shimfiɗa duk da yanayin sanyi da ake ciki, ta kwantar da Sauban, ita kuma ta zauna, ta jima a zaune tana so ya fito ya ganta haƙanta bai cimma ruwa ba, saboda haka ta kwanta, sai da asuba ta tashi zaune ta miƙe ƙafa, Salis ya yi turus ganin an ɗaura net a tsakar gida, ya haska wajen ya ce"Ameera!" Don ya san Safiyya a ɗakinsa ta kwana. Ameera ta fashe da kuka ba ta ce komai ba, da mamaki ya ƙaraso ya ce"Ameera lafiya kuwa? Me yasa kika kwana a waje?" Tana kukan ta ce"Babu komai, kawai na gaji da ɗakin ne". Ya yi shiru yana kallonta, kafin ya ce"To kamar ya kin gaji da ɗaki? A sanyin nan ki fito da yaro ku kwana a waje? Ai kuwa babu lafiya". Ta sunkuyar da kai ba ta ce komai ba, ya ce,Tashi ki koma ɗaki! Gaskiya kar ki sake saka min yaro cikin sanyi". Kamar mai jiran umarni sai ta tashi ta koma ɗakin ta kwanta, baccin da ba ta samu damar yi ba ya ɗauke ta. Washegari ma sai ta yi hakan, nan ma bai san a waje ta kwana ba sai da asuba, kamar dai jiya yau ma haka suka yi, kuka kawai take tana cewa ta gaji da ɗaki, wani washegarin ranar girkinta ne tun da wuri ta shiga ɗakinsa, sai dai tsakar dare ta tashi zaune tana kuka, a tsorace ya ce"Ameera lafiya kuwa? Me yake faruwa ne?" Tana kukan ta ce"Babu komai! Ji nake gara na kwana a waje, idan na shiga ɗaki kaina ciwo yake, na fi son waje". Salis abun ya ba shi mamaki sosai, daga ranar dai sai da ta yi sati tana yin haka, da ya ga abun ba mai ƙarewa ba ne sai ya je ya faɗawa Hajiya, Hajiya ta sa ya taho da ita gidanta, da fara'arta ta shiga suka gaisa lafiya ƙalau, Hajiya ta ce"Ke Ameera me yake faruwa ne? Ya ce kin daina kwana a ɗaki sai a waje, kuma wai idan kin shiga ɗaki kanki yana ciwo". Dama tun da ya ce su je gidan ta san zancen kenan, sai ta fara kukan tana cewa babu komai. Hajiya ta ce"Tafi kasuwarka Salisu, da daddare ka zo ku tafi". Ya tafi jikinsa duk a sanyaye, Ameera ta ba shi tausayi, don yanzu duk wannan tsiwar ma ta daina yi. Bayan ya tafi, kwanciya ta yi, tun tana baccin ƙarya har na gaske ya ɗauke ta, kafin ta yi baccin gasken tana ji Hajiya tana yi wa ƴaƴanta waya, tana ba su labarin abin da yake faruwa, ba ta ji me suke cewa ta wayar ba, ta na ji dai Hajiya tana cewa"Ni ma haka nake tunani, jifa ne, Safiyya ce take son ta fita daga gidan, kin ganta baiwar Allah sai bacci take, a can ba ta samu ta yi, duk ta rame". Sai da Sauban ya fara kuka sannan ta tashi tana mai da fuskarta kalar tausayi ta ɗauke shi, Hajiya ta ce"Sannu Ameera, ga shi ya tashe ki, ai da kin samu bacci mai daɗi". Ta ce"Ba komai Hajiya, hakan ma ai na rage, rabon da na yi bacci me daɗi wallahi na fi sati biyu, ina farawa sai na fara mugun mafarki, na tashi a firgice, ko kuma na ji kamar ana ta kira na ana cewa"Ameera tashi, tashi, tashi, har sai na fita zan daina ji, kuma amma sai na ji kamar a mafarki, idan kuma a ɗakinsa na kwana ina kwanciya sai ciwon kai mai tsanani ya dirar min, na rasa abin da yake damuna". Hajiya ta dinga jinjina lamarin ta ce"Wannan ai jifa ne, bari dai yaran nan su zo na ce su zo dukansu a samu mafita". Ameera ta ce"Ai Hajiya da kin bar su, komai zai wuce in sha Allah!". Ta ce"Ko kuma ya ƙara gaba ba! Wannan dai jifa ne aka yi miki, so take ta kore ki daga gidan!". Ameera ta ce"Hajiya wa kenan?" Ta ce"Da wa kuke zaune? Wa kika ragewa jin daɗi idan ba Safiyya ba?" Ameera ta ce"Gaskiya ba na jin Safiyya tana bin malamai, amma kwanaki fa na ji tana waya tana cewa a cikin fulon zan saka ko a ƙarƙashin fulo? To ni kuma ban kawo komai ba, kuma sai da kika yi maganar nan na tuna sai fa na ɗora kaina a fulon ɗakin Salis nake fara jin ciwon kai". Hajiya ta ce"A haf! Ita ta san abin da ta ƙulla miki, to wallahi ba ta isa ba! Sai dai ita ta bar gidan ba dai ke ba! Don gida naki ne ba nata ba, ke da kika ajiye magajin gida? Ai dama na san dole ta yi yunƙurin hakan!". Ameera ta ce"A'a Hajiya zato ne...". Hajiya ta katse ta da faɗin"Kayya Ameera! Ke yarinya ce, ba ki san komai ba tukunna, ba ki san kaidin kishiya ba". Da rana ta yi sai ga ƴaƴan Hajiya suna zuwa ɗaya bayan ɗaya, Fa'iza, Saude sai ƙanwaraa Mariya, da kuma ƙanwar Hajiyar da suke ce mata Mama Asabe, sai da suka hallara duka bayan sun ci abincin rana sannan Hajiya ta mai da zance kamar yadda Ameera ta faɗa mata, kowa ya dinga salati ana mamaki, Hajiya ta ce"Wannan fa ba abun mamaki ba ne ba, indai kishiya ce za ta yi fiye da hakan". Daga ƙarshe suka yi shawarar su tafi gidan a duba fulon ɗakin Salis ɗin, suka ɗunguma suka tafi ban da ita, suka ce ta basu mukullin ɗakin nashi ta ce babu a hannunta, suka kira shi a waya, Hajiya da kanta ta ce"Salisu ka dawo ka ba mu mukullin ɗakinka za a yi bincike". Da mamaki ya ce"Wane irin bincike kuma?" Ta ce"Idan ba za ka ba ni ba ka faɗa kai tsaye". Ya ce"Akwai mukulli a hannun Safiyya". Suka ƙara shaƙar baƙin ciki da jin hakan, kenan ita da mukulli a hannunta, bora ce ba a ba ta ba. Da ƙarfi suka dinga buga gidan, don bayan yaran sun tafj makaranta Safiyya ta rufe ta kwanta bacci ya ɗauke ta, ta yi zaton ma Ameera ce, ta taso ta buɗe, ta ga ƴan'uwan nasa, sai ta yi zaton wajen Ameera suka zo tun da wajenta suke zuwa, don a zatonta Ameera gidansu ta tafi, ta saki fuska ta ce"Sannunku da zuwa, ku shigo". Suka shigo, Saude ta ce"Safiyya ba mu mukullin ɗakin Salisu". Babu musu ta ɗakko ta ba su, suka buɗe suka shiga, ita kuwa ta shige ɗakinta, tana tunanin abin da ya kawo su. Cak suka ɗage katifar suka jingine ta, suka ɗauki fulo suka cire rigad fulo ba su ga komai ba, Mariya ta shiga kitchen ta ɗakko wuƙa ta farke fulo, sai ga ƙananun laya sun faɗo guda biyu, dukansu suka ɗauki salati, Fa'iza ce ta saka layar a jaka tana ce musu su yi shiru, Mama ta ce"Allah sarki Ameera ashe dai abun na gaske ne, so ake a raba ta da gidan". Saude ta ce"Ai bari ya zo, kawai ya kama mata haya ta bar mata gidan, sai ta ci kanta". Fa'iza ta yi murmushi ta ce"A cika mata burinta kenan? Idan Ameera ta bar gidan nan ai burinta ya cika, babu inda za ra je nan gidanta ne wallahi, sai dai ita Safiyyar ta bar gidan". Mama ta ce"Ba ni layar nan za ku yi, ina zuwa wajen malamina zai yi ƙaiƙayi, reshe ya juye da mujiya, ta yadda dole sai Safiyya ta bar gidan nan da ƙafarta!". Fa'iza ta miƙa mata laya ta ce"Wannan harkar ku ce, ni ba ni da wani malami, amma na yarda ki yi duk abin da za ki yi Safiyya ta bar gidan nan!". Daga haka suka fice, bayan sun gyara ɗakin, suna komawa suka faɗi duk yadda aka yi, Hajiya ranta ya yi matuƙar ɓaci ta tashi ta ɗakko hijjabi, Mama ta zaunar da ita ta ce"Ina za ki je?" Ta ce"To zan zuba ido ne ta kori yarinya daga gidan? Za ta yi abun ne a zuba mata ido?" Mama ta ce"Yanzu idan ta ji mun gane kina tunanin ba za ta canza wani abun ba? Ai gara kar ta gane, mu kuma mu biyo mata ta inda ta biyo" Nan suka faɗa mata hukuncin da suka yanke, kuma nan take ta amince. Ameera ta yi farin ciki sosai, don ba ta yi zaton plan ɗinta zai yi tasiri da sauri haka ba, wani shago ta je haɗo magunguna da ta yi arba'in, a nan ta ga wani magani a roba da laya guda biyu a ciki, ta tambaya aka ce mata na mallaka ne, wai a ƙarƙashin fulo ake saka shi bayan an shanye garin maganin, shi ne ta siya da niyyar ta mallake Salis, daga baya kuma sai dabarar hakan ta ɓullo mata. Da daddare da ya dawo suka nuna masa, suka yi masa bayanin komai, amma sam bai yarda ba, rai a ɓace ya ce"Yanzu nufinku Safiyya ce ta saka laya a cikin fulona?" Suka ce"Ga zahiri ka gani". Ya ce"Gaskiya ni ban yarda ba, Safiyya ba ba haka take ba, kun kasa fahimtarta ne kawai!". Hajiya da ta ji kamar ta dake shi ta ce"Yo kai ana saka ka a lissafi ne? Kai ai ta gama mallake ka, tun da kai ka zaɓi hakan ka je ka yi ta yi, amma ba za mu zuba ido a cuci ƴar mutane ba". Ransa a ɓace ya ɗauki Ameera a babur suka tafi, da yana tausayin halin da take ciki, yanzu kuwa wani mugun haushinta yake ji, kamar yadda suka ce mata tana zuwa ta ɗinke fulon da zare da allura, Salis da takaici duk ya ishe shi ya ce"Ki fitar min da filon, ke daga yau ma kar wacce ta sake shigo min ɗaki, duk ranar da na yi niyya zan dinga binku ɗakunanku, wannan ma ai wulaƙanci ne, ita ma zan faɗa mata". Ba ta ce komai ba ta tashi ta fice ranta fess, ita dai burinta su yi komai da wuri. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/2, 6:12 PM] Sadiya Abdulrazak: 28 Safiyya ba ta san wainar da ake toyawa ba, tana zaune ya shigo ya zauna ya ce"Safiyya za mu yi magana". Ta ce"To ina jinka". Ya ce"Na yanke shawarar daga yau kar wacce ta sake shigar mini ɗaki, duk wacce take da girki zan shigo ɗakinta na kwana wannan shi ne magana kawai". Ta ce"Ikon Allah! Wani abun ne ya faru kuma?" Ya ce"To mene ne ma ba ya faruwa? Ni dai ga abin da na ce kawai". Safiyya ta ce"To wannan tsarin ni kuma ai ka ga ba zai yi min daɗi ba, ita ɗakunanta biyu ne, ni kuwa ka ga ɗaya ne, haka za mu dinga cakuɗa da yaran?" Ya yi shiru shi ma yana tunani, ta ce"Idan satar ce aka dawo da yi maka ni na yarda duk ranar da na kwana a ɗakinka kafin na fito ka caje ni ka gani". Ya ce"Ba sata ba ce, kawai dai doka ce na kafa". Ta ce"To tun da haka ne, ni ina ganin zan yafe maka kwanana kawai, saboda a samu maslaha". Ya ce"Me kike nufi da kin yafe kwana?" Ta ce"Ina nufin duk ranar kwanana sai ka kwana a ɗakinka, tun da ka ga ai ba za mu kwana a waje ba ko? Ko kuma yaran zan dinga yi wa shimfiɗa a wajen?" Ya yi shiru, ta ce"Idan kuma kana ganin mu koma kitchen da kwana to duka dai shawara ce". Ya ce"Safiyya ba na son irin rainin nan da kika yi mini fa, a kan me zan kwana a kitchen? Su yaran ba sa yin bacci ne? Ki dinga yi musu shimfiɗa a ƙasa, ni dai babu mai shigo min ɗaki ehe!". Safiyya ta ce"To na ce ni na yafe kwanan..." "Shi kenan Safiyya Allah Ya gani ai ban shiga haƙƙinki ba, ke kika ce kin yafe," Ya faɗa ya tashi ya fice daga ɗakin. Daga ranar bai sake shiga ɗakinta ba, sai dai ya shiga ɗakin Ameera, ta zuba musu ido ta ga ƙarshen abun. Sati biyu da faruwar haka kuma ta fara fuskantar matsala, indai tana ɗaki sai ta dinga jin wani irin zafi kamar gidan biredi, dole sai ta fito ƙofar ɗaki ta zauna take ɗan jin sassauci, don ba za a kira shi da sauƙi ba, saboda gabaɗaya ji take kamar ta bar gidan ta tafi ko ma ina ne, sam ta nemi nutsuwarta ta rasa tun tana daurewa da daddare ta kwana a zaune abun ya kai sai dai ta kwana a waje, gani take su ma yaran hakan suke ji don haka ba ta bari su ma su kwana, duk sanyin da ake yi a kansu yake ƙarewa, Salis ya yi har ya gaji, tambayar duniyar nan sai dai ta ce haka kawai, don ita ma ba za ta ce ga taƙamaiman dalili ba, Ameera kuwa farin ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, cikin farin ciki take jinta, ta yi ta juyi tana yi mata habaici. Watarana Salis da kan shi ya je ta je gida ta yi kwana biyu, ko ta ɗan samu ta huta, saboda tausayinta yake ji, ganin duk ta zama wata iri, ƙarshe cewa ya yi ta koma ɗakinsa ta dinga kwana, amma da ta gwada nan ɗin ma dai duk kanwar ja ce, tana ji tana gani miji ya zama na Ameera ita kaɗai, ta ji daɗin barin ta ta kwana a gida, ta je ta yi kwana ɗaya ta je gidan Yaya Aminu ma ta yi kwana ɗaya, babu laifi ta ji daɗi, ta yi bacci mai daɗi wanda ta daɗe ba ta yi ba, sai dai ta kasa faɗawa kowa matsalar da take fuskanta. Da yamma ta dawo gidan gabanta yana ta faɗuwa, ƙunci ya mamaye mata zuciya, ta saka mukulli ta buɗe ɗakinta, jaka kawai za ta ajiye ta fito da tabarma, sai da ta shiga tsakiyar ɗakin kamar an ce ta kalli gadonta, kawai ta ga wasu narka-narkan ƙadangaru guda uku a baje, ba ƙaramin tsoron ƙadangare take yi ba, don haka ta ƙwalla wani ƙara ta fito daga ɗakin a guje, a tsakar gida ta tsaya dafe da ƙirji tana sauke numfashi, sai kuma ta zauna ta fara hawaye ƴaƴanta suna tambayarta mene ne? Ta kasa faɗa musu. Ameera da ke ƙofar ɗakinta a zaune murmushi kawai ta yi, a ranta ta ce"Ba ke kin nace ba kamar gidan ubanki! Kaɗan ma kika gani". Ga shi tsoro ya sa ta saki wayar a ɗakin, kuma ba za ta iya shiga ba ballantana ta ɗakko ta kira shi a waya, haka suka zauna har sai dare da ya dawo, ta yi masa sannu da zuwa, ya amsa jiki a mace, indai zai ganta a ƙofar ɗakin nan sai ranshi ya ɓaci, ta ce"Baban Ni'ima ƙadangaru ne a ɗakina". "Ƙadangaru kuma? Garin ya suka shiga?" Ya faɗa a tsorace, don ba zai iya fito mata da su ba. Ta ce"Wallahi ina dawowa na buɗe ƙofa kawai na gansu, har uku kuma akan katifa". Ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ina zuwa". Ya fita, ya dawo da wasu matasa su biyu ya ce su shiga su fito da su. Suna shiga suka fito da su, ɗaya yana cewa "Wannan ai matattu ne ma". Salis ya ce"To ina ga tun shekaran jiya suka shiga suka mutu a ciki, dayake ba ta gidan". Ɗayan ya ce"Wannan daga gani kashe su aka yi, kuma mutuwar yau ce ma, gaskiya sai dai idan zuwa aka yi aka ajiye muku". Salis ya ce"Ai shi kenan" Ya yi musu godiya suka tafi. A sanyaye ya ce"Ki shiga Safiyya sun cire ai". Ta ce"Bar ni a nan kawai". Ta shiga kitchen, shi kuma ya shiga ɗakinsa. Suna zaune har aka yi isha'i, ta tashi don kwaso kayan shimfiɗa, a tsorace ta shiga, tana buɗe sif ɗin ta ga wani narkeken ƙadangaren a kan kayan shimfiɗar da za ta ɗauka, take ta saki wayar da take haskawa ta tarwatse ta ƙwalla ƙara mai ƙarfi, tana innalillahi, ta zo fita ta ji ta taka abu mai laushi, wanda duhu bai sa ta gane jakarta ba ce, saboda waya kawai ta ɗauka ta bar ta a wajen, ta yi tsalle ta fito duka jikinta rawa yake yi. Salis ba ya nan, haka ta tsaya a tsakar gida tana ta kuka, yaran suna taya ta. Sai ƙarfe goma ya dawo, lokacin ta gaji ta zauna a wajen bakin ƙofar gidan, yaran har sun yi bacci akan sallaya ga sanyi sai ta lulluɓe su da hijjabinta, Salis ya haskata wani sabon kuka ya zo mata ta shiga yi kamar za ta shiɗe, ya ce"Safiyya mene ne?" Ta ce"Wani ƙadangaren na gani a cikin sif". A firgice ya ce"Cikin sif kuma? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ba dan ɗazu ya ga an fito da su ba da sai ya ce Safiyya gamo ta yi, to me zai kai ƙadangare cikin sif? Ya fice hankalinsa duk ya tashi, ya kira wani yaro, ya zo ya ciro su ashe har biyu ne a sif ɗin, su ma duk matattun ne har jini ya taɓa kayan shimfiɗar, Salis ya ce ya bincike ɗakin ko zai ga wani, nan ya ƙara ganin wasu guda biyu, ya fito da su su huɗu duk matattu, Safiyya ta dinga karkarwa tana kuka, shi ma sosai ya tsorata da wannan lamarin. Bayan yaron ya tafi, Safiyya ta ce"Baban Ni'ima don Allah ka yi haƙuri, zan bar gidan nan, gara na koma gida kawai kafin komai ya yi sauƙi". Ya ce"Gaskiya ni ma abun ya ba ni tsoro sosau, Safiyya ban hana ki tafiya ba, amma da kin yi haƙuri dama gobe zan samo Malami a yi sauka a yi addu'a a ɗakin naki". Ta girgiza kai ta ce"Gaskiya ba zan ƙas kwana a ɗakin nan ba, ba zan iya ba, ni taimakon da za ka yi min don Allah yanzu ka kai mu gida, don Allah!". Ya ce"Dare ya yi, ki yi haƙuri gobe sai mu je". Ba ta sake cewa komai ba, don ta lura ba zai fahimci halin da take ciki ba, ya shiga wanka ta tashi yaran ta wanke musu ido, ta zare sakata a hankali ta fice daga gidan, tana ayyanawa a ranta ta tafi kenan har abada, idan har Salis ba zai sake ta ba to sai dai ya sama mata gidan haya. Adaidaita sahu suka hau ta kai su har ƙofar gida, ta shiga da sallama, Baba da Umma suna tsakar gida, suka amsa da mamakin ganinta, a wajensa ta karɓi kuɗi ta sallami mai babur ɗin, don ba ta fito da komai ma, hatta wayarta tana inda ta tarwatse, ta dawo ta zauna tana gaishe su, Baba ya ce"Safiyya da daren nan?" Kamar tana jira kawai ta fashe da kuka, sosai ta dinga kuka sannan duk ta faɗa musu abin da yake faruwa, Baba ma ya tsorata kuma ya tausaya mata, ya ce su je su kwanta gobe zai kira Salis ɗin a san yadda za a yi, ta yi shimfiɗa suka kwanta sai dai har lokacin a tsorace take don haka ba ta samu baccin kirki ba. Shi kuwa Salis yana fitowa ya ga basa wurin, ya leƙa ɗakin ya ga babu kowa, ya san ta tafi ne, don haka ya ja ƙofar ɗakin, yana jin tausayinta na kama shi. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/2, 6:12 PM] Sadiya Abdulrazak: 29 Washegari Safiyya har baccin safe ta yi mai tsayi cikin kwanciyar hankali, sanda ta tashi ma Umma har ta gama gyara gidanta, sun karya, wanka ta yi wa yaran ita ma ta yi sannan ta karya, wasai take jin zuciyarta irin yanayin da ta daɗe ba ta ji ba, gidan Salis ya zamar mata kamar gidan bala'i. Da damuwa sosai Salis ya kwanta, wajan sha biyu na dare Ameera ta shigo ɗakinsa, yana kwance idonsa biyu, amma bai kalle ta ba, ta kwantar da Sauban tana shirin kwanciya ya ce"Ameera yau kwanan Safiyya ne". Ta ajiye numfashi tana murmushi ta ce"Kai kam na kasa gane maka, to yaushe rabonka da Safiyya? Ko yanzu ba na ga ta fice ba? Yanzu ita ta ɗorawa kanta tafiya gida, abu ƙalilan sai ta yi yaji ta barka kana garari a gari, yanzu ni gani amma sai ka ce za ka tsaya raba kwana da ita? Ni wallahi ban ma taɓa jin wannan tsarin ba, wai mutum ko ba ya nan ma sai an lissafa kwana da shi, gaskiya ka canza tsari!". Ya ce"Haba Ameera, ke ba ki ga halin da take ciki ba ne? Kin san abin da ya sa ta bar gidan yau? To ba yaji ta yi ba, maganar rabon kwana kuma idan ta dawo sai mu zauna mu tsara shi, yanzu dai koma ɗakinki!". Ta tashi ta ɗauki ɗanta ta fice ranta a ɓace, wato shi har yana tunanin za ta dawo gidan? Kodayake sai ya yi tunanin hakan tun da bai san kan lamarin ba, ita ma Safiyya tana da nacin masifa, idan ba haka ba an yi mata farraƙu da gidan ma amma ta ƙi ta barsa? Shi yasa da ta tafi gida ta ji Salis ya ce kwana za ta yi, ta bawa ƙaninta dubu biyu ta sa ya kawo ƙadangarun nan, dama ta saci mukullin ɗakinta da yake ɗakin Salis ya saka mata su a ɗaki, kuma sosai ta ji daɗi da ta ga hakan ya yi tasiri, ita don dai ma kawai su Fa'iza sun kasa ganewa, amma da sun bar ta ma da kissa za ta kore ta, ita dai tun da ba ita ta je wajen Malami ba ta san ba ta yi shirka ba to Alhamdulillah. Tana zaune wajan ƙarfe goma yaro ya zo ya ce Salis yana sallama, dama Baba shi yake jira, don sun yi waya ya ce masa zai zo, don haka ya ce ya shigo, bayan sun gaisa Baba ya nemi jin ƙarin bayani, Salis duk ya faɗa masa abin da yake faruwa kamar yadda Safiyya ta faɗa masa, sannan ya ɗora da faɗin akwai Malamin da ya faɗawa zai zo gidan yau ɗin. Baba ya sauke ajiyar zuciya ya ce"To Allah Ya yi mana magani, dama Malaman ya kamata a nema a gani, abun dai babu daɗi sam!". Ɗakin da take Baba ya nuna masa ya ce ya shiga, ya shiga da sallama, yana cewa Ni'ima"Yau ba ku je makaranta ba ko? Anjima zan ɗakko muku kayan makarantar". Suka gaisa ya ce"Ina ta kiranki a kashe". Ta ce"Wayar ai tana ɗakin". Ya ce"Ikon Allah! Wallahi Safiyya lamarin nan sosai yake ba ni tsoro! Amma ki yi haƙuri, haka Allah Ya ƙaddara, yanzu yau Malamin zai je ya yi addu'a a ɗakin, ke ma kuma ki dinga yi don Allah, idan an yi ko kwana biyu sai ki yi ki huta kafin ki koma ko?" Safiyya ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Baban Ni'ima ba fa zan koma gidan nan ba". Ya ce"To! Kamar ya kenan?" Ta ce"Kawai na haƙura da zaman gidan, ka kama mini haya ina ga zai fi". Ya ce"Haba Safiyya, ina da gidana kuma sai na tafi kama haya? Kuma gidan da kike ciki aka zo aka same ki a ciki wajen shekara nawa yanzu Safiyya ki ce kin fita ki koma na haya?". Ta yi murmushi ta ce"Baban Ni'ima wannan har wani abun mamaki ne? Tun da har aka fitar da ni daga ɗakunana aka ba ni ɗaya ai ka ga ba abun mamaki ba ne don na bar gidan ma, yanzu Ameera ai ita ce mai gida, don haka ni dai ba zan koma ba". Salis ya ce"Gaskiya ni dai ba ni da ra'ayin raba wa matana gida, kuma wannan gidan idan kin ga kin bar shi yo a gaskiya sai dai sabon gini na yi za mu koma tare". Ta ce"To ai babu matsala zan zauna a nan har ka yi sabon ginin". Ya ce"Haba dai! Gidan da ko bulo ɗaya ban saka ba ki ce za ki zauna a gidanku har na gama? Ai ke ma kin san ba zai yiwu ba ko?" Ta ce"Zai yiwu mana idan ta kama". Ya ce"Kuma da aurena a kanki za a yi hakan?" Ta ce"Wannan kuma ra'ayinka ne baban Ni'ima idan ka ga ba za a yi hakan da aurenka ba, sai ka sallama mini haka Allah Ya ƙaddara". Ya yi wani murmushi ya ce"Ke ma dai bai kai zuciyarki ba na sani. Yanzu zan je ne na ɗakko Malamin, idan aka gama abin da za a yi ai za ki koma, tun da daga nan dai matsalar za ta kau in sha Allah!". Ta ce"Ni dai ba zan koma gidan nan ba". Ya ce"To sai yanda ta yiwu dai, anjima zan dawo na kawo miki wayar da kayan sakawarku ko kala biyu ne". Ya ba ta dubu uku ya tafi. Daga nan gidan Malam Ibrahim ya tafi, shi ma Malam ɗin ya shirya shi yake jira, saboda bai san gidan nasa ba, a kasuwa wani abokin Salis ɗin ya haɗa shi da shi ya kwatanta masa gidan, Malam ya karɓi Salis hannu biyu-biyu, bayan sun gaisa ya yi masa bayanin irin matsalar, Malam ya ce"Subhanallah! Abun kamar akwai jifa a ciki, mu je dai mu gani". Ameera tana tsakar gida tana wanki Salis ya shigo ya ce ta ɗan shiga ɗaki baƙo zai shigo, ta shiga ɗaki ta dawo windo tana leƙe, ta ga sun dawo tare da Malamin, sai da gabanta ya faɗi da ta ji sun buɗe ɗakin Safiyya, a zuciyarta ta ce'Kar fa su karya sihirin tun yanzu'. Ba ta gama sarewa ba sai da Salis ya zo ya ce mata za ta sama musu garwashi, ta haɗe gira ta ce"To ni a ina zan ga wani garwashi? Sai dai ka shiga maƙota ka samo". A wajen mai ƙosai ya samo, aka yi wa ɗakin turaren magani, wanda ya karaɗe gidan duka, sannan ya yi addu'o'i, ya kuma ba shi addu'o'in da za su dinga yi duka ƴan gidan musamman ita Safiyya, Salis ya maida shi gida ya ba shi sadaka, sannan ya zo da samari ya sa duk a ka fito da kayan ɗakin nata, aka bincike su tsaf, aka share ɗakin, ya yarfe shi da ruwan addu'ar da ya ba shi, ya ɗauki kayan da zai kai mata, ya kai mata ya faɗa mata an yi addu'a Malam ya ce ko yau za ta iya dawowa, amma dai yana ganin ta bari sai zuwa jibi kafin nan ta huta. Safiyya ta ce"To Allah Ya rufa asiri". Ta karɓi kayan ya faɗa mata wayar ya ga ta ƙi kawowa sai ya kai mata wajen gyara, ita ma ta duba wayar ta ga ta ƙi kawowa, ya ba ta keypad ɗinsa ya ce ta saka layukanta a ciki. Daga nan gidan Hajiya ya wuce, suka gaisa ta ce"Yau ba ka je kasuwar ba ashe". Ya ce"E wallahi, Safiyya ce ba ta jin daɗi, amma yanzu ma zan tafi kasuwar". Ta taɓe baki ta ce"Mene ne ya same ta?" Ya ɗan yi jimm, saboda ba ya so ya faɗa mata gaskiyar, tun da ya san Hajiya ba wani damuwa ta yi da lamarinta ba, kuma ma za ta iya cewa Safiyya ƙarya take yi, yana cikin tunanin ya ji ta ce"Ai yanzu muka yi waya da Ameera, ta faɗa min komai, kuma har nawa ka ba wa Malamin?" Ya yi mamaki da ya ji Ameera ta faɗa mata, ya ce"Hajiya sadaka ce kawai ba wani abu ba". Ta ce"Dama ai dole ka va hakan, tun da an riga an shanye ka, shi kenan yarinya ta maida kai sususu, ta haɗa karyarta ta haɗa baki da Malamin ƙarya an zo an ci kuɗinka ko?" Ya ce"Haba Hajiya, akan me za ki yi wannan tunanin? Ni fa da kaina na nemo Malamin ma, kuma Safiyya ai ba za ta yi ƙaryar ciwo ba, yanzu ma halin da muke ciki cewa take ba za ta koma ba sai dai na kama mata gidan haya, saboda yadda ta tsorata da ɗakin nata". Hajiya ta ce"Iyye! Lallai yarinyar nan ta samu waje, yanzu daga yawon neman hayar kake ko har ka samu?" Ya ce"A'a na faɗa mata ba zan kama haya ba, na dai bar ta ta kwana biyu a gidan ta huta tukunna". Hajiya ta ce"To kuwa muddin ba ta koma ba sai dai ta bar auren duka, babu wata haya da za ka kama mata, Allah Ya rufa maka asiri da muhallinka ace wai ka kama haya ita ga hamshaƙiya!?" Salis ya ce"Sai yadda ta yiwu dai Hajiya, bari na je kasuwar". Gidan ya koma, ransa a ɓace ya ce"Ameera ina ruwanki da abin da ya shafi Safiyya?" Ta ɓata rai ta ce"Me kuma na yi?" Ya ce"Nan Safiyya ta kasa kwana a ɗakinta kina kallo, amma ko damuwa ba ki yi ba, nan aka ciro ƙadangaru a ɗakinta kina kallo, nan ta tafi gida duk kina kallo, sai yanzu na kawo Malami ya yi maganin matsalar shi ne wai har kin kira Hajiya kin faɗa mata? To wallahi ki kiyaye ni! Babu ruwanki da abin da ya shafi matata ki yi rayuwarki mu yi tamu!". Daga haka ya fice bai ma tsaya sauraronta ba. Da daddare da ya dawo daga kasuwa ya je ya faɗawa Baba an yi addu'a, Safiyya kuma sai jibi zai zo su koma, Baba ya ji daɗin hakan ya ce Allah Ya sa ƙarshen abun kenan. Sai ranar da ya shirya za ta koma ɗin, ya mayar da kayan ɗakin nata, ya share ya gyara komai har da kunna turaren maganin da aka ce sai an yi sati ana kunnawa, ya haɗa mata net ya shirya komai sannan ya tafi gidan. Da yamma ne, suna tsakar gida tana taya Umma aikin abincin dare suna fira jefi-jefi, ya kira ta a waya ya ce yana ƙofad gida, ta tashi ta fita, suka gaisa ya ce"Safiyya na zo mu tafi ne fa". Ta yi murmushi ta ce"Baban Ni'ima kenan! Haka za mu yi ta maimaita magana kamar yara?" Ya ce"Me kike nufi ne?" Ta ce"Ai na faɗa maka ba zan koma ba fa, sai dai ka sama mini gidan haya". Ya ce"Safiyya gaskiya ba ni da kuɗin da zan kama miki haya". Ta ce"Babu damuwa, ko Yayana zai iya kama mini". Ya yi mata wani kallo ya ce"Yayanki ne yake aure ki da zai kama miki haya?" Ta ce"Ai a neman maslaha ne, tun da ni dai na ce ba zan koma ba, ka ga mai son zaman lafiya ai zai iya kama mini haya, tun da kuɗin ne ba ka da shi". Ya ce"Gaskiya Safiyya kin koyi taurin kai, amma har na saka a yi addu'ar ai ya kamata ki koma ki gani, idan da sauran matsalar sai a san yadda za a yi ko?" Ta ce"Ai na bar gidan nan in sha Allah! Idan ba za ka sama min hayar ba a bi wata hanyar". Ya ce"Kina nufin za ki iya haƙura da auren akan wannan matsalar?" Ta ce"Indai hakan ka zaɓa ni ma zan karɓa". Ya ce"Yanzu Safiyya ni kike faɗawa za ki iya rabuwa da ni? To ni dai ba zan kama miki haya ba, ɗakinki za ki koma, ko kuma ki ta zama a gidanku". Ta ce"To tun da ka yarda na zauna a nan ɗin ai ba matsala, na gode". Ya hau babur ɗinsa ya tafi ransa a ɓace, ita kuma ta shiga gida, tana ji a ranta ta bar gidan na har abada. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/2, 6:12 PM] Sadiya Abdulrazak: 30 Da daddare sun gama cin abinci suna zaune Baba ya dawo, bayan ta yi masa sannu ya ce"Safiyya bai ƙaraso ba ne?" Ta sunkuyar da kai ta ce"Ya zo ya tafi". Ya ce"To me yasa ba ku tafi ba, ko kun ɗaga tafitar?" Ta yi shiru, wani baƙin ciki ya taso mata har maƙoshi. Baba bai sake yi mata magana ba, da ta ga ya fara cin abinci sai ta sulale ta je ta kwanta. A ɓangaren Salis da baƙin ciki ya kwana, duk ya saka ran yau ɗin za ta dawo, ya rasa yadda aka yi Safiyya ta raina shi, da sam ba ta yi masa musu, idan ya ce ta yi tana yi ko ba ta so, amma tun da ya ƙara auren nan shi kenan raini ya shiga tsakaninsu, ya rasa da wa zai raba wannan takaicin, ya san Hajiya da Ameera sai dai su ƙara masa, ga shi su ne dai makusantan nasa. Washegari bai je gidan ba, bai kuma kira ta a waya ba, amma yana kunna turaren maganin a ɗakin nata, da daddare Baba ya dawo ya sake ganin ba ta tafi ba, da mamaki ya kira Salis a waya, bayan sun gaisa ya ce"Salisu akwai sauran matsala ne?" Ya ce"To ai Baba sai ta dawo za a gani tukunna, amma komai ya daidaita ma in sha Allah!". Baba ya ce"To sai yaushe za ta koma?" Ya ce"Baba ai sai yadda ta zaɓa, na zo mu tafi ta ƙi yarda, shi yasa na barta ta huta". Baba ya ce"To ka yi haƙuri, ka ga yanzu dare ya yi, amma gobe in sha Allah za ta dawo tun da safe ma kuwa". Salis ya yi masa godiya suka ajiye waya. Baba ya kira ta, gabanta sai faɗuwa yake har ta fara hawaye saboda ta san kwanan zancen, Baba ya ce"Kukan me kike yi?" "Babu komai" Ta faɗa tana share hawayen. Ya ce"Me yasa ba kya son komawa ɗakinki?" Ta ce"Baba tsoro nake ji, idan na shiga ɗakin nan zuciyata kamar za ta buga, zafi nake ji ba zai taɓa yiwuwa na yi minti talatin a ciki ba, har ɗakin nasa ma kuma, Baba ƙadangaru ba a san ta inda suka shiga ba, wallahi ba zan iya ba, kawai ya kama mini haya". Baba ya yi shiru yana tausayin ƴar tasa, ya sauke numfashi ya ce"Ai duk na ji wannan, yanzu kuma an yi maganinsa, komai ya wuce, ki koma ki gani, indai kika sake ji ko ganin wani abu bayan kin koma na yi miki alƙawarin da kaina zan sa ya kama miki gidan haya, idan ba zai kama ba ni zan kama, idan bai yarda ba kuma za ki zauna a nan ba zan bari ki koma ba". Ta yarda Baba zai yi hakan, amma wane bayani za ta yi masa ya gane cewar sam ita ba za ta iya ƙara rayuwar gidan ba? Da ɗayansu zai tsinci kansa a halin da take ciki ta san za su fahimce ta, kuka ta dinga yi sosai, sai da ta yi shiru Baban ya ce"Ki yi haƙuri, aljannarki kike nema kuma za ki samu matuƙar kin yi biyayya ga mijinki, ki daure ki koma ɗin ki gani kin ji?" Ta gyaɗa masa kai, har lokacin tana hawaye, sannan ya ɗakko leda mai ɗauke da magungunan karya sihiri ya ba ta ya nuna mata yadda za ta yi amfani da su, ya kuma yi mata nasiha akan kula da ibada da addu'o'i, ta karɓa ta koma ɗaki ta kwanta, tana jin ƙirjinta a cunkushe, ta saka a ranta za ta koma tun da ga bayanin da Baba ya yi mata, don haka da fargabar komawar tata ta kwana, ta nemi farin ciki ta rasa, ji take a duniya babu wani abu da ta tsana sama da gidan mijinta, amma za ta koma idan ajalinta a can yake shi kenan za ta mutu kowa ya huta. Washegari wajan ƙarfe tara Baba ya ce ta shirya ta fito su tafi ya raka ta, Umma ta ce"Da dai ka tafi, sai na raka ta anjima". Baba ya ce"To a tabbata a gidanta ta yi sallar azhar" Ya tafi yana son danne zuciyarsa daga raunin da ta yi na tausayin marainiyar ƴar tasa, Ni'ima ta tafi makaranta, Umma ce ta yi wa Kausar wanka ta shirya ta, Safiyya tana shiryawa tana share hawaye, hango waɗan nan ƙadangarun kawai take, da kuma tuna irin yanayin da take ji idan ta doshi ɗakinta ko na Salis ɗin, a haka ta tattara komatsanta suka fito da Umma, ganin har sun kusa ƙarasawa ba ta daina hawaye ba Umma ta ce"Yanzu Safiyya haka za a maida ke kina hawaye? Ba dole kishiya ta raina ki ba?" Ta share hawayen, tana ƙarfafa zuciyarta. Da sallama suka shiga gidan, Ameera ta amsa tana fitowa daga ɗaki, turus ta yi ganin Safiyya, nan take baƙin ciki ya mamaye ta, har ta kasa dannewa sai da ya bayyana a fuskarta, ta juya ta shige ɗakinta, Umma ta ce"Ina mukullin?" Safiyya ta ce"Babu a wajena, sai dai na kira shi". Yana kasuwa ya ga kiranta, ya ɗaga ko amsa sallamarsa ba ta yi ba ta ce"Na dawo babu mukulli". Ya ce"Kin dawo? Yanzu kina gidan?" Ta ce"E mana". Ya ce"Gani nan zuwa, ai ban san za ki dawo ba, me za a taho muku da shi?" Ba ta ce komai ba, ta katse wayar, ta kalli Umma ta ce"Umma ki je kawai, wai ba ya kusa kar mu ɓata miki lokaci". To dama ita ma tana son zuwa kasuwa ƴan siye-siyenta don haka ta ce"To shi kenan, Allah Ya rufa asiri, ya ƙara karewa, ai ta haƙuri dai". Safiyya ta amsa da amin, Umma ta tafi, sai ta shiga kitchen ta ɗakko turminta ta nemi waje ta zauna tana jiransa, ba a jima ba ya shigo gidan, da ƴar fara'arsa ya ce"Ashe kin dawo, sannu, bari na buɗe in sha Allah komai ya wuce, kullum sai na shiga na sake dubawa, babu komai a ciki". Ko kallon inda yake ba ta yi ba, shi kaɗai yake yi, ya je ya buɗe ya shige yana cewa"Bisimillah Safiyya shigo mana". Ta shiga ranta a ɓace, ta ce"Ina kayan shimfiɗar?" Ya ce"Suna nan, na sa an wanke, yanzu kuma ai kin daina amfani da su ko?" Ta ɗauki tabarma da sallaya bayan ta ajiye kayan da ta shigo da su, ta fice daga ɗakin, ya fito ya tsaya a ƙofar ɗakin yana kallonta tana shimfiɗa tabarmar a tsakar gida ya ce"Safiyya ya ina ta magana kin ƙyale ni?" "Me kake cewa?" Ta tambaye shi fuskarta babu yabo babu fallasa. Ya ce"Ya za ki zo ki zauna a waje ko gaisawa ba mu yi ba, ballantana na yi miki bayani?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba, ya zo ya tsugunna a gefenta ta kau da kai tana danne zuciyarta daga jin haushin shi, ya ce"Safiyya! Mene ne? Ko ba ki so kika dawo ba? Baba ne ya ce sai kin dawo?" Har yanzu ba ta kalle shi ba, ya tashi zai fita ya ce"Za kiyi girki ko? Me da me za a kawo?" Nan ma dai babu amsa, ya fita yana jin babu daɗi a ransa. Tana nan zaune ya dawo da cefane ya ajiye mata, sannan ya je ya buɗe ɗakinsa ya fito mata da kayan abinci, ya ce"Ki duba ko akwai abin da kike buƙata sai a kawo". Ta yi banza da shi, ya ce"Na fi so na ga kin shiga ɗakinki Safiyya". Ta ce"Idan da rabon shigar nan gaba zan shiga". Ya ce"Me kike nufi ne?" Ta tashi ta shiga kitchen ba ta ce komai ba, shi kuma ya koma kasuwa. Da ta gama girki ta dawo ta zauna a tsakar gidan, ga shi ba ta da babbar waya ballantana ta samu abun ɗebe kewa, sai ta dinga saƙa da warwara, Ameera ta fito ita ma tana zirga-zirgarta tana waƙa cike da nishaɗi, babu wanda ya kula wani, tana nan har aka yi sallar la'asar, yaran sun tafi islamiyya sai ita kaɗai, ta tashi ta yi girkin dare, ta yi wanka, a tsorace ta shiga ɗakin ta saka kaya, ta ɗakko kayan shimfiɗa har da net ta fito da su, tana idar da sallah ta yi musu shimfiɗa a wajen, suna cikin cin abinci Salis ya dawo, ransa ya yi matuƙar ɓaci, ya ce"Safiyya mene ne haka?" Kamar ba ta gane nufinsa ba ta ce"Me aka yi?" Ya ce"Wannan ai raini ne, ya za ki maida ni yaro? Kin cee ga matsala na kawo maganinta kuma ki shiga ɗakin ki gwada ki gani don wulaƙanci ba za ki shiga ba?" Ta ce"Ai na faɗa maka na gama kwana a ɗakin nan, tun da ka ce dole a gidan nan zan mutu ga ni nan, zan ta zaune a tsakar gida har zuwan ranar da baƙin ciki zai yi ajalina, Baban Ni'ima na tsani gidanka!". Sosai ya ji haushi, ya ce"Ba gidana kika tsana ba Safiyya ni kika tsana! Kuma duk tsanar da kika yi mini haka za ki zauna da ni, ba zan kama miki haya ba, kuma aurena da ke babu saki, sai dai ki yi ta rayuwa a tsakar gidan!". Ya shige ɗakinsa, ita kuwa hankalinta kwance ta gama cin abincin, sannan ta ɗauki nashi ta kai masa ɗaki ta fito, da ya fita sai goma na dare ya dawo, lokacin yaran har sun yi bacci, yana zuwa ya ɗauki Ni'ima ya kai ta ɗakinsa ya kwantar, ya dawo ya ɗauki Kausar ma, tana kallo ya banko ƙofa, sai ita kaɗai a tsakar gidan, haka ta kwana a tsorace, gani take kamar za ta ga waɗannan ƙadangarun. Haka Safiyya ta dinga wannan rayuwar har tsawon wata uku, idan ta shiga ɗaki to abu za ta ɗauka, don a tsawon lokacin nan ko share ɗakin ba ta taɓa yi ba, rayuwarta ta koma tsakar gida ana ji ana gani, Salis tun yana fushi har ya saba, ya kai ƙararta ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, Baba ya yi mata duk faɗa da nasihar duniyar nan, amma wanda ya yi nisa ba ya jin kira, ita kaɗai take kwana a waje, yaran sun koma ɗakinsa da kwana, ranar kwananta Salis ya kwana tare da yaran ranar kwanan Ameera ya kwana a ɗakin Ameera, a tsawon wata ukun babu wata mu'amula da ta haɗa su. Ameera kuwa ranta fess, har gayyato ƙawayenta take yi don su ga kishiyarta a tsakar gida, sai ta ba su labari, haka dangin Salis idan suka zo wajen Ameera sai dai su bi ta da kallo a ɗage suna ganin ai abin da ta yi ne aka yi mata, Salma ma babu yadda ba ta yi da Safiyya ba, amma ta ƙi shiga ɗakinta, idan ƙawayenta suka ce za su zo ba ta ma bari su zo sai ta ce ba ta garin, ba wani abu take ji game da gidan ba yanzu, don Alhamdulillah tun kafin ta gama amfani da magungunan ta ji salama a zuciyarta, kawai dai ta saka a ranta ba za ta shiga ɗakin nata ba ne. Rana ɗaya babu zato Salis ya ce ta shirya za su fita, ta saka hijjabinta ya ɗauke ta a babur, tafiya mai nisa ta kai su wata unguwa, suka sauka ya buɗe ƙofar gidan da mukulli, tana kallonsa da mamaki ya ce"Bismillah!" Ta bi bayansa, gida ne ƙarami mai ɗakuna biyu, kitchen da banɗaki, ta kalle shi da son jin ƙarin bayani, ya ɗage kafaɗa ya ce"Gidanki ne, gidan hayar da kike ta so a kama miki". A sanyaye ta ce"To na gode". Ya ce"Ki shiga ki dudduba". Ta ce"Ai ba sai na duba ba ma, na gode". Ya ce"Gobe sai ki dawo ko?" Ta gyaɗa masa kai alamar e, ya ce"Hmm! Safiyya kenan yanzu kuma za ki iya kwana ke kaɗai ba ki ji tsoro ba? Unguwa ba ki san kowa ba?" Ta ce"Na yarda". Ya ce"Ai shi kenan! Allah Ya rufa asiri, gobe sai ki kira masu taya ki tarewa ko? Na sa an yi sauka tun shekaran jiya, da safe zan kawo mota a kwashe kayan". Ta ce"To na gode". Haka kuwa aka yi, washegari Safiyya ta tare a gidanta, Ameera ba ta san da zancen ba sai da safe yake faɗa mata ya ce ta shirya ta je, ta ce ba ta jin daɗin jikinta, saboda sosai ta ji baƙin ciki, ita so take Safiyya ta gaji da zaman tsakar gida ta ce sai ya sake ta, ta ƙara gaba ta huta da ganin kishiya, ashe shi zama daram tun da har biye mata yake ya kama mata gidan haya, ai kuwa yana fita ta kira Hajiya, bayan sun gaisa ta ce"Hajiya su Yaya za su je tariyar Safiyya? Ni ba ni da lafiya ne". Hajiya ta ce"Tariya kuma? Wace Safiyya?" Ameera ta ce"Ai ya kama mata gidan haya, yau za ta tare". Hajiya ta ce"Gidan haya? A lallai Salisu wuyansa ya isa yanka, yanzu har ya kai ya yi abu ba tare da sanina ba?" Ameera ta ce"Ai ban san ma ba ki sani ba, da ban kira ki ba, sai anjima" Ta kashe, ta zauna tana ta kumbura. [5/31, 5:51 AM] Sadiya Abdulrazak: 31 Nan take Hajiya ta kira shi a waya, bai zo ba sai da yamma da ya dawo daga kasuwa, saboda ya san kwanan zancen, yana shiga ya ga fuskar Hajiyar kamar hadari, jikinsa ya yi sanyi, ya zauna yana gaishe ta, ba ta amsa ba ta far magana"Da gaske ka kamawa yarinyar nan gidan haya?" Ya ce"Hajiya ai gani na yi abun ya yi yawa, wata nawa tana rayuwa a tsakar gida, wannan ko mara gata ai ƙarshe kenan". Hajiya ta ce"To ba ita ta ɗorawa kanta ba? Ko wani ne ya hana ta shiga ɗakin? Sannan ya muka yi da kai akan zancen haya? Ba na ce maka idan ta dage sai ka kama mata gida ba ta tafi gidansu?" Ya ce"Ki yi haƙuri Hajiya, tun da na riga na kama, so nake ma na fara ginin wancen filin, idan na gama sai mu koma bakiɗaya". Ta taɓe baki ta ce"To ban dai yi maka baki ba, amma wannan figigiyar indai kana tare da ita ban ga ranar da za ka yi gini ba! Banda samun wuri yarinya duk yadda ta ce haka za ka yi? Ga gidanka amma ta saka kashe kuɗi ka kama haya? Lallai!". Ya ce"Yi haƙuri Hajiya, bari na tafi, sai da safe". Ya tashi ya fita, yana jin ransa babu daɗi, yanzu haka zai zuba ido Safiyya tana rayuwar ƙunci a gidansa? Tun da ta kafe ai gara ya kama hayar ya ga gudun ruwanta. Dama bari ya yi sai ranar girkinta a yi tariyar, saboda haka kai tsaye gidanta ya nufa, ko sallama bai je ya yi da Ameera ba, ya shiga da sallama, suna ɗaki a zaune da yaran, ya ce"Ku dinga kulle gidan nan fa, kin ga sabuwar unguwa ce, ga mu baƙi a unguwar". Ta ce"To in sha Allah! Sannu da zuwa". Ya amsa yana kallonta cike da ƙauna, ya daɗe bai ga kwalliyarta ba, ga daɗe bai ganta cikin sakewar fuska da walwala ba sai yau ɗin da ya yi mata abin da take so, ta kawo masa abinci, sai ga su suna firar da suka daɗe ba su yi ba, ya gama cin abinci suka ci gaba da firar su, ya ce"Yau dai za ki yi bacci mai daɗi ko? Buri ya cika". Ta yi murmushi ta ce"Ai kuwa dai, sai yanzu hankalina ya kwanta". Ya ce"Ni ma yau nawa zai kwanta, wallahi kin ba ni mamaki Safiyya, ƙiri-ƙiri fa kika zaɓi nesa da ni yaushe rabona da ke? Ko kewata ba kya yi, babu ruwanki sai dai mu kalli juna ko?" Tana shirin yin magana kiran Ameera ya shigo wayarsa, ya ɗaga, ko sallama babu ta ce"Ba ka dawo daga kasuwar ba?" Ya ce"Na dawo, na wuce gidan Safiyya ne, kuna lafiya dai ko?" Ta ce"Ina fa lafiya? Tun rana cikina yake ciwo wallahi, ga Sauban ma jikinaa da zazzaɓi, ni dare nake tsoro". Ya ce"Subhanallah! Tun yaushe yake zazzaɓin?" Ta ce"Tun safe fa". Ya ce"To bari na sa a kawo muku magani". Ta ce"Kenan ba za ka zo ba!" Ya ce"Ai da nisa fa unguwar..." Ta katse wayar tun kafin ya ƙarasa magana, ta kira Hajiya ta marairaice tana faɗa mata ba su da lafiya sosai kuma yau kwanan Safiyya, tana tsoron dare ita kaɗai a gida don haka za ta tafi ta kwana a gida, Hajiya ta ce ba zai yiwu ba kar ta je ko'ina. Ya gama waya da wanda zai kai mata maganin sai ga kiran Hajiya, yana ɗagawa ta ce"Salisu ka je ka kwana a gidanka ka kula da jikin matarka da ɗanka". Ya ce"Hajiya na sa a kai musu magani". Ta ce"To ai dare ake gudu, bai kamata su kwana su kaɗai a gida ba". Ya ce"Ai Hajiya da naga Safiyya yau ta tare, bai kamata a ce ita kaɗai ta kwana a gidan ba..." A fusace ta ce"To ba illar rabawa mata gida ba kenan! Na faɗa maka dai ka tafi wajensu!". Ya ce"To Hajiya" Ya kashe wayar ya kalli Safiyya, ya ce"Ameera ba su da lafiya, Hajiya ta ce na tafi". Duk da ba ta ji daɗi ba ta daure ta ce"To babu damuwa ka je ɗin sai da safe". Ya ce"To, idan na ga da sauƙi ba sai na kwana ba, ku kulle ko'ina ku yi addu'a sosai". Ta amsa da to, sannan ya tafi, ta kullo gidan, suka yi addu'a suka kwanta, don ba ta saka ran Ameera za ta bari ya dawo ba. Washegari da safe ya zo suka gaisa sannan ya tafi kasuwa, da daddare da ya dawo ya shiga wanka Ameera ta kira shi, Safiyya tana kallon wayar ta ga ita ce, ta yi sauri ta ɗauka ta kashe, kamar yadda ta san shi haka yake har yanzu ba ya sakawa waya key, ta yi sauri ta saka lambarta a black list, ta goge miss call ta ajiye, sai da safe ta faki idonsa ta yi unblock. Washegari ne kuma ƴan'uwansa suka zo ganin ƙwaƙwaf don Hajiya ce ta ce su je su ga gida, wajen sha biyu ne tana shirin ɗora girki, ta tare su babu yabo babu fallasa, suna ta bin gida da kallo, ko da suka zauna ita kam kitchen ta shiga, farar shinkafa ce ta dafa da miya, kuma ya aiko har da kaji guda biyu, don haka komai daidai, tana ajiye musu abinci ta lura suna kallon-kallo, ita dai ta fice ta yi alwala ta koma ɗayan ɗakin, suna zaune ta yi wanka ta yi kwalliyarta sannan ta dawo inda suke, kamar suna jiranta suka ce za su tafi, ta ɗakko dubu biyu ta ba su, su hau adaidaita sahu, don sun yi waya da Salis ya ce ta ba su idan za su tafi, idan ya zo zai bata, ta yi musu godiya suka tafi. Tass suka je suka bawa Hajiya labari, domin su dai a yadda suka ga Safiyya babu wani alamar damuwa a tare da ita, don har kaji suka ci albarkacin amarya, Hajiya ta ce"Lallai Salisu, ni bai siya min ba, bai siyawa matarsa ba sai ita isasshiya ko?" Fa'iza ta ce"Ai dama tun da suka yi nesa da kowa ai sai abin da aka gani kuma, yanzu za ta ƙarasa lalube shi tsaf, kasuwar ma sai ta lashe jarin idan muka yi wasa". Haka sai suka yi ta tattaunawa. Watan Safiyya ɗaya a sabon gidanta, Salis ya yi mata kujeru masu sauƙin kuɗi, ya saita mata kayan kallonta, ta tambayi Yaya Aminu firgi, ya siya mata babba amma ba sabo ba ne, falo ya yi kyau, suna zaune lafiya da shi babu wata matsala. Yanzu ta riƙe addu'a sosai, tana zikirin safe da yamma suma yara ta yi musu, har mp ta siya kullum cikin kunna suratul Baƙara take, Baba kuma ya zo ya ga gidan, duk sati kuma sai ya aiko mata da magani, shi yasa yanzu hankalinta a kwance. Ta shisshiga maƙotanta sun gaisa, dayake ma sabuwar unguwa ce ba a cike take ba, sai dai duk yaran mata ne irinta da wanda ba su kaita ba, a yadda ta fahimta irin unguwar nan ce ta marasa kamun kai, don matan unguwar kusan a titi suke rayuwar aurensu, zaman majalisa suke babu safiya babu yamma, tana daga gida tana jin shewarsu, har girki suke yi a ƙofar gida, tsarinsu sam bai yi mata ba, saboda haka ba ta sake shiga gidan kowa ba, kuma dama Salis ma ya gargaɗe ta a kan hakan, don sai daga baya ya gane yanayin unguwar, su kuma suna shigowa jifa-jifa, don Salma ta kawo mata humra tana siyarwa kuma suna shigowa su siya, har ma su yi fira baya-baya dai amma. Tun da Safiyya ta tafi sai Ameera ta kasa nutsuwa, kullum tunaninta Salis fa yana can yana nuna rashin adalci, yana can yana yi wa Safiyya da ƴaƴanta hidima, ita ya mai da ita ƴar iska, abun duk ya dame ta, idan ya zo sai dai ta yi ta ɓacin rai ya rasa dalili, wataran ta ce masa za ta je gidan Safiyya, ai kuwa ya ji daɗin hakan saboda yana son haɗin kan matan nasa don dai abun ya fi ƙarfinsa ne, watarana ya dawo da wuri daga kasuwa, ya ɗauke ta suka tafi, faran-faran Safiyya ta karɓe ta, ta ɗauki Sauban tana ta yi masa wasa, ita kuwa Ameera kasa ɓoye baƙin cikinta ta yi, na ganin ashe har ya yi mata kujeru da firji, wa ma ya san abubuwan da yake yi mata? Sai ta ga ma kamar har ƙiba ta yi, don haka duk ranta ya yi baƙi, ta ji dama ba ta yi sanadin barin Safiyya gidan ba, kuma nan take ta fara tunanin yadda za a yi ta dawo, gara ma su ci gaba da zama a waje ɗaya tana kallon komai, don haka suna da zama da Hajiya na musamman dole a sake lale. Aka rasa wanda zai gaida wani, sai Safiyya ce ta ce"Ina ta zuba ido ba ku zo ba sai yau". Ameera ta ce"E wallahi, ban samu dama ba". Safiyya ta ce"Haka ne, Allah Ya rufa mana asiri". Ta kawo mata abinci ba ta ci ba, ko ruwa ba ta sha ba, ta ce masa za ta tafi. Safiyya ta ba ta humra, ta ba ta garin kunu ta ce a damawa Sauban. Abin da ya ƙara ba ta haushi ma bai wuce yadda suka shiga ɗaki wai zai yi mata sallama ba, suka bar ta a tsaye a tsakar gida tsabar wulaƙanci, don haka ta yi ficewarta, tana fita ta ga wata ƴar layinsu, suka gaisa take ce mata "Hajara dama unguwar nan aka kawo ki?" Ta ce"E wallahi, ai har Zainab me awara duk a nan muke". Ameera ta ce"Ni kuma kin ga kishiyata ce ta dawo nan ɗin". Hajara ta ce"Ikon Allah! Dama maman Ni'ima kishiyarki ce? Matar babu ruwanta wallahi, kin yi sa'a". Daidai lokacin da ya fito, Ameera ta ce"Hmm! Ke dai ba ni lambarki" Ta miƙa mata waya ta saka mata lambar, ta tafi, ita ma ta hau babur suka tafi. [6/1, 6:48 AM] Sadiya Abdulrazak: 32 Bayan an kwana biyu Ameera da ta je gidan Hajiya, bayan sun gaisa tana tambayarta ya gidan, Ameera ta marairaice ta ce"To gida ga shi nan sai addu'a, amma ana ta haƙuri dai". Hajiya ta ce"Kamar yaya? Me yake faruwa?" Ameera ta ce"Wallahi ni dai tun da ya canzawa Safiyya gida na kasa gane kansa, sai ya yi ta fito min da wasu halaye wanda da ban san shi da su ba, ga shi cefanen ma yanzu sai a hankali, haka rannan wani yaro ya zo da cefane mai yawa na karɓa na buɗa na ga har da kaji manya, ina ga sun kai guda uku ma, ina ta murna yau zan ci nama tun da na manta rabon da na ci, Nabila tana zaune har nake ce mata ba za ta tafi ba sai na gama soya kajin nan ta kai miki, kawai sai ga yaron ya dawo ya ce ina cefanen nan? Na ce mene ne? Ya ce ai na Safiyya ne bai san ta tashi daga gidan nan ba, haka na tattara na ba shi, Nabila tana cewa na ɗauki ko kai da ƙafa ne, na ce babu komai lokaci ne". Ta karasa tana langaɓar da kai kamar marainiya. Hajiya ta riƙe haɓa tana jinjina kai, ta ce"Kenan Salisu da gaske ba zai iya adalci ba? Shi yasa ta kafe ai sai ya kama mata hayar, saboda su bar idon kowa ta dinga lalube tattalin arziƙinsa, to ai shikenan ya je ya yi duk yadda ya tsara, ke kuma ki ƙara haƙuri za mu ga ƙarshen abun in sha Allah!". Ameera ta ce"In sha Allah! Amma don Allah ba sai an yi masa faɗa ba, ni lallaɓawa nake don kar ta yi sanadin haɗa mu faɗa". Hajiya ta ce"To abin da idan ma an yi faɗan ba ji zai yi ba? Ki ta haƙuri ke dai, amma ni yanzu gaskiya na daina wahalar da kaina akan Salisu, abun nasa ya girmama!". Haka Ameera ta bar gidan ba ta wani ji daɗin yanda Hajiyar ta sare ba, kenan babu wani mataki da za ta ɗauka? Sosai take jin nadamar sanadin barin Safiyya gidan, yanzu hankalinta ya ƙi kwanciya duk ranar girkin Safiyya bacci ma rabi da rabi take yi. Ba a daɗe da haka ba watarana Hajiya ta je gidan ƙanwarta Asabe take ba ta labarin halin da gidan Salisu yake ciki, Asabe ta ce"Ita ma fa wannan Ameerar ta cika kawo ƙorafi, ya kamata ki rage sakar mata fuska tana kawo miki magana kina ɗauka nan gaba sai ta fara haɗawa da ƙarya ai". Hajiya ta ce"Haba dai! Ameera ai yarinyar kirki ce ba za ta yi haka ba, ga irin albarka a tare da ita daga zuwa ta haifi namiji". Asabe ta ce"Haka ne, kenan dai har yanzu shi Salisu yana liƙe da yarinyar nan kamar cingam". Hajiya ta ce"Ke dai bari, ai wallahi uwar da ta haifi Safiyya ma ba zan yafe mata ba, yarinya ta shiga rayuwar ɗana ta yi kane-kane! Sai juya shi take yi kamar waina". Asabe ta ce"To me zai hana na koma wajen Malamin nan na sa a yi musu farraƙu, ya daina son ta gabaɗaya ya sallame ta kowa ya huta?" Hajiya ta ce"Asabe na rasa inda kika koyi bin Malamai kedai, yanzu nan ba kin je wajen Malamin ba, amma ƙarshe me yake faruwa yanzu? Ba gaba ta kaita ba?" Asabe ta ce"A'a babu laifin aikin Malam, cewa aka yi fa ya raba ta da ɗakinta, kuma ba ga shi ba sai da ɗaki ya gagare ta? Yanzu shi Salisu za a yi wa, ya tsane ta ya sake ta kowa sai ya huta". Hajiya ta ji abun banbarakwai wai ƙanwarta ce mai cewa za ta yi wa ɗanta asiri, ta yi shiru tana nazari kafin ta ce"Gaskiya kar a yi a kansa, ita za a yi wa wanda za ta ji ta ma tsane shi, kin ga daga nan sai ta sa ya sake ta". Asabe ta ce"Shi kuma yana sonta ya za a yi ya sake ta ɗin? Shi kuwa ana yi masa zai sake ta, ai ba cutar shi aka yi b, taimako ne". Hajiya ta ce"A'a Asabe ni dai idan sai shi za a yi wa a bar aikin ma kawai, kar abu ya ɓaci a sabauta mini yaro, shi kaɗai gare ni namiji, shi ne cina, shi ne shana da suturata". Asabe ta ce"To shi kenan Hajiya a bar shi ɗin kawai". Daga haka suka shiga wata firar. Bayan Hajiya ta tafi Suwaiba ƴar Asabe ta dawo gidan, Asabe ta ce"Yanzu Hajiya ta tafi, ina ta so ki dawo na ji ki shiru". Suwaiba ta yi murmushi ta ce"To ya ake ciki Umma?" Asabe ta taɓe baki ta ce"Ki kwantar da hankalinki fa, gidan Salisu kamar kin ma shiga ne, yo gida bai ƙoshi ba za a kaiwa dawa ne? Ya tara mata biyu duk marasa amfani! Ita ma Hajiyar tana kallo kina zawarci ai ya dace ta yi tunanin bari ta haɗa ku aure ko dan ƙarfafa zumunci, amma ta yi mirsisi kamar ba ta san rasa mijin auren kika yi ba". Suwaiba ta ce"Ni fa Umma indai ba zai saki matan nasa ba, ba aurensa zan yi ba ma". Asabe ta ce"Ke dalla can! Ko da su ɗin ma ke ina ruwanki? Ko yanzu ba fafutukar da nake ta yi ba kenan? Indai an samu ya rabu da wannan Safiyya ita wannan makirar mai sauƙi ce don ya fi son Safiyya". Daga haka suka dinga tattauna yadda za su tsara komai, idan abubuwa suka zo musu a yadda suke so. Ameera jin shiru babu ta inda Hajiya take shirin ɗaukar mataki akan Safiyya, watarana suna zaune da shi take ce masa"Baban Sauban ni fa kwana biyu na rasa me yake damuna". Ya ce"Too! Kamar ya kenan?" Ta ce"Ka ga gabaɗaya tsoron gidan nan nake yi, idan kana gidan Safiyya ba na iya bacci, kuma shi ma Sauban na lura yana yawan firgita, sannan tsakar dare sai na dinga jin kamar ana tafiya, wataran na ji kamar ana wanka a banɗaki, rannan ma ji na yi ana ta aiki a kitchen". Salisu ya yi shiru yana tunani, wani tsoro ne ya shige sa, a bayaninta ya fahimci aljanu ne kenan suke tsorata ta, to shi dai tun da ta gina gidan nan ko tsuntsu bai taɓa tsorata shi ba, saboda haka sai dai idan aljanun kanta ne suke bayyanar mata. Ta ce"Ka yi shiru". Ya ce"To Ameera me zan ce? Ki dinga addu'a kawai, idan ba ki daina gani ba sai na kawo Malami a yi addu'a ko?" Ta ce"Ni fa ina ga har da zaman kaɗaici ma, tun da sanda Safiyya tana nan ai ba na jin hakan, kuma ka ga ɗakinta an bar shi babu kowa a ciki, su fa aljanu suna zama a wajen da ya daɗe babu kowa a ciki, yanzu kar ka yi mamakin jin ɗakinta ya zama gidan wasu ahalin aljanun". A tsorace ya ce"Subhanallah! Don Allah daina yi mana wannan fatan". Ta ce"Ai na faɗa maka ne don ka nemi mafita". Ya ce"To ki saka wasu kayan naki a ciki mana, ko idan kin yi baƙi ku ɗan dinga zama a ciki?" Ta ce"Yanzu ita Safiyya haka za ka bar ta a wannan unguwar? Matan unguwar fa zaman majalisa suke yi mazan mutane duk wanda ya wuce ana yin sharhi a kansa, a haka ma har wata sai ta fara son mijin wata ka ga ƙarshe ana neman kauce hanya". Salis ya yi tsaki ya ce"Kayya! Ni dai na yarda da matata, kuma zaman majalisa ba ta yi, kullum tana gida da yaranta, ni islamiyya ma ta ce za ta shiga, ga bussines ma tana so ta fara, za ta dinga tallata min kayan shagona tana samun ribarta, ko ke ma za ki yi?" Ameera ta shaƙa sosai, tana ga yaƙi shi yana ga ƙura, ta taɓe baki ta ce"A'a ba sai na yi ba". Ya ce"To shi kenan! Ita ma ba ta fara ba, dayake ƙaramar waya ce a hannunta, amma ƙarshen satin nan zan siya mata babbar saboda ta fara, ga humra ma ta ce ana ta siya wallahi abun sha'awa, wancen satin ma da kanta ta je kasuwar ta haɗo kayan, kin ga da matar Aminu ce take haɗa mata". Ameera ta taɓe baki, ba ta ce komai ba, can kuma ta ce"Kenan waya za ka canza mana?" Ya ce"A waya zan siya mata dai na ce, ke me wayarki ta yi?" Ta ce"Tun da na zo gidan nan fa ba ka taɓa canza min waya ba, duk ta tsufa". Ya ce"Haba Ameera ana ta kai wa ke ta kaya? Babu abin da wayarki ta yi ai, ita kin san daɗewar wacce ta lalace ɗin a hannunta? Ba ki sani ba, komai ai da lissafi ake yi, saboda a taru dai a rufawa kai asiri ko?" Ta yi banza da shi, daga haka aka bar firar, haƙanta bai cim ma ruwa ba. Kamar yadda ya faɗa wani satin ya siya mata wayarta mai kyau, Safiyya ta yi ta farin ciki, yanzu hankalinta a kwance yake don suna zaune ƙalau da mijinta, ita da ta san zaman waje ɗaya da kishiya ne zai tarwatsa mata rayuwar aure ai da tun farko ba za ta yarda ya haɗa su ba, duk kaiwa ruwa rana da za a yi kuwa. Bayan kwana biyu ta fara bussines ɗin kayan shi na kasuwa, atamfofi da leses manya da ƙanana har ma da kayan kitchen wanda ya haɗa ta da masu siyarwa, kuma Allah Ya saka mata albarka, harkar ta buɗe mata, ƴan'uwa ma wanda suka sani sukan sayi kayan. To dama ita rayuwa an ce kana taka Allah na tashi, ta Allah kuma ita ce gaskiya, a yayin da hankalin Salis da Safiyya yake a kwance, suke gudanar da rayuwa cikin farin ciki, tare da gudana laulayin ƙaramin cikinta na wata biyu wanda ba wani rashin lafiya yake saka mata sai kasala, da canzawar test, gefe guda kuma Asabe ƙanwar mahaifiyar Salis wacce suke uba ɗaya da ita, ta matse lamba sosai wajen ganin ta raba kan ma'auratan biyu, Hausawa sun ce tsafi gaskiyar mai shi, tun bayan da komai ya faru Safiyya ta daina wasa da azkar, ta ƙasa kusancinta da Allah sosai, shi kuma Salis fa? Shi irin mutanen nan ne wanda kamsus salawati kaɗai suke yi, babu ruwansa da wasu azkar kasuwa kawai ya saka a gaba, saboda haka surkullen Asabe ya fara tasiri a kansa cikin ƙanƙanin lokaci, ba su tashi gane an samu canji a tare da shi ba, sai da abun ya yi girman da ya mamaye su duka. Haka kawai ya fara jin rashin jin daɗi idan ranar kwananta ya zo, duk sai ya wuni da damuwa, idan ya je gidanta da ya kalle ta sai ya ji ɓacin rai, bai ankara ba ya nemi son da yake yi mata ya rasa, ya tsani ta raɓe shi, shi yasa ma ba ya zuwa gidan da wuri sai dare ya yi sosai, kuma yana cin abinci a nan falon yake kwanciya, komai ta yi ba ta burge shi, sai dai ya ji mugun haushinta, wani lokacin har tunani yake yi shi me ma ya gani a jikinta yake sonta ne? Yana jin kamar ya rabu da ita, wani ɓangare na zuciyarsa kuma yana hana hakan. Sosai Safiyya ta shiga damuwa saboda wannan sabon sauyin da ya tsiro da shi, duk sanda ta tambaye shi dalili sai ya ce mata babu komai, kuskure kaɗan za ta yi ko ƴaƴanta su yi ya hau ta da masifa kamar zai kai mata duka, ko kaya za a siya wani lokacin sai ta yi masa magana ta whatsApp ya duba ya yi banza da ita, kuma duk ranar girkin Ameera ba ya ɗaukar wayarta, ba ya aiko mata cefane, ƙarshe sai yake ajiye mata ɗari biyu a matsayin kuɗin cefanen shi ma sai ranar da ya kwana a gidanta, watarana tana cikin girki gas ya ƙare, ta kira shi ta faɗa masa, ya dinga bala'i ya ce daga yau ma an daina amfani da gas ɗin, a ranar ya jibgo mata itace, ta zauna ta ci kuka ƙarshe ta cire kuɗinta aka zubo mata gas, ko da aka kwana biyu ya ga ice bai ƙare ba sai ya tambaye ta da me take yin girki? Ta ce"Baban Ni'ima ni zan dinga zuba gas ɗin in sha Allah!". A fusace ya ce"Ai ni ma ba gagara ta ya yi ba! Shi itacen na zaɓa miki, saboda haka da shi zaki yi". Ranta ya ɓaci ta ce"Wai me yasa kake son sai ka ƙure ni!? Na ce zan yi da kuɗina, ko cefanen ba da kuɗina nake yi ba?" Ya ce"Au haka ma za ki ce? To daga yau ma ki dinga ci da kanki kawai!" Ta ce"Ai kuma wannan ba zai taɓa yiwuwa ba! Sai dai idan sallama ta ka yi". Salis ya ce"Ban sallame ki ba, kuma ba zan sallame ki ba! Amma babu yadda za a yi kina ƙarƙashina ki dinga raina ƙoƙarina!". Ya tashi ya shiga kitchen ya ɗakko gas ɗin ya fice da shi. Safiyyata zauna ta fara kukan rashin sanin makama. [6/3, 5:18 PM] Sadiya Abdulrazak: 33 Ta rasa me za ta yi, ta kira Salma a waya take faɗa mata halin da ake ciki, Salma ta taya ta jimami sosai, Safiyya ta ɗora da faɗin "Kin ga saboda shi ya siya shi yasa ya ɗauke, don haka ni yanzu zan sayi nawa na dinga amfani da shi, kuma a hankali zan biya shi duk abin da ya siya min". Salma ta ce"A'a Safiyya kar ki yi hakan, ki ƙyale shi da zobe ladansa da yake yi ma kaɗai ya ishe shi, kuma kar ki sayi gas ɗin nan, ki siyo mangal ki dinga yi da gawayi, komai zai wuce in sha Allah, ki ƙara haƙuri wani abun idan kina kau da kai shi da kansa zai fara jin kunyarki". Safiyya ta ɗauki shawararta, ta siyo mangal da gawayi rabin buhu ta koma yin girki da shi. Da kayan abincinta ya ƙare sai ya kawo zallan abinci babu mai da magi, babu abin da za su dinga karyawa da shi, ta yi masa magana bai ce komai ba, bai kuma kawo ba, haka take ta cefane da kuɗinta da safe kuma su dafa taliya su ci, duk ranar girkinta ba ta siyan kayan miya don ta nuna masa tun da bai kawo ba ba zai ci ba, sai dai ta dafa fara da mai ta barbaɗa masa magi, idan ya buɗe ya gani sai ya rufe ya tashi ya tafi, daga ƙarshe ma ya ce kar ta sake yin girki da shi, sannan bussines ɗin ya daina yi da ita, ya ce ya hana ta harka da kowane ɗan kasuwa kuma, sannan bai amince ta je kasuwa ba, haka ta tattara sana'ar ta daina yin komai take ta cin kuɗin da ya rage mata, lokacin da biyan kuɗin makarantar Ni'ima ya yi nan ma ya ƙi biya, abun ya dame ta, ta je ta faɗawa Baba duk halin da ake ciki. Baba bai ji daɗin wannan abu ba, ya ce"Amma kin je kin sanarwa mahaifiyarsa?" Safiyya ta ce"Baba wannan matar fa ba so na take ba, ko na fala mata babu wani mataki da za ta ɗauka wallahi". Baba ya ce"A'a kul na sake jin haka daga bakinki, Hajiya duk irin zaman da kuke yi uwa ce a gare ki, saboda haka kar ki sake cewa ba ta sonki, kuma ki tafi ki faɗa mata idan ba ta ɗauki mataki ba sai ki faɗa min na san abun yi". Safiyya ta amsa da to, ba dan tana ji a ranta za ta yi hakan ba, ta san wace ce Hajiya, ta san daɗi ma za ta ji a maimakon ta sama musu sasanci saboda haka ta ƙi faɗa mata, shi yasa ba ta dawo wajen Baban ba, ta ci gaba da gwagwarmayarta kawai, Yaya Aminu ta kira ta tambaye shi kuɗin makarantar, da mamaki ya ce"Ke Safiyya wai wace irin rayuwa kike yi ne? Shi yanzu kuɗin makarantar ma ba zai biyawa yara ba?" Safiyya ta ce"Wallahi da yana yi, yanayi ne kawai ya canza". Ya ce"To a gaskiya zan zo na same shi na ji dalili, don fa ba zai yiwu ya dinga cutarki ba, ace kuɗin makaranta ma ya gagara? Ko babu yake yi?" Ta ce"Ban sani ba, amma ina ga kasuwar ce ta ɗan tsaya, don Allah Yaya ba sai ka same shi ba, ka ƙyale shi kawai". Aminu ya ce"To shi kenan, ki turo account number" Ta tura masa ya saka mata kuɗin, tana ta godiya. Washegari ta ciro kuɗin da Salis ya zo gidanta, ta yi musu cefane mai kyau suka yi girki har da nama, da ya zo ya tarar suna cin abinci ya bi abincin da kallo don ya ga yau ta canza, dama ta daina yi masa tayi tun da ya ce ya daina ci, sai da ta gama, ta tashi ta ɗakko kuɗin ta ba shi, ya bi su da kallon neman ƙarin bayani, ta ce"Ka kai kuɗin makarantar Ni'ima, ita ma Kausar dama ka ce a watan nan za a kai ta ko?" Ya ce"To daga ina kuɗin suka fito?" Ta ce"Yaya Aminu ne ya turo min". A fusace ya ce"Kenan dai Safiyya ba ki daina roƙon Aminu kina yi masa ƙaryar ba na yi miki komai ba ko?" Da mamaki ta ce"Ƙarya kuma? A kan me zan yi masa ƙarya? Kuma ni dai ban cewa kowa ba ka yi mini komai ba, ko igiyoyin aurenka da suke kaina da kuma yadda ka ba ni wajen zama ai komai ne, kuɗin makaranta ne da ka ce ba ka da shi, shi ne na tambaye shi, tun da na san ai babun ce sanda kake da shi ai ba ka ƙi yi ba". Ya ce"Ƴaƴan nan ni na haife su ko shi ne?" Ta ce"Kai ne". Ya ce"To Safiyya daga yau zan yi miki gargaɗi, babu ruwan yayanki da harkar gidana, idan yaran nan za su yi ta garari a titi babu ruwan shi! Ba zan biya kuɗin makarantar ba! Kuma ban amince kowa ya biya musu ba, indai an yarda ƴaƴana ne, idan kuma kin canza musu uba to ki kwashe su ki kai ya riƙe su, saboda haka ga kuɗin sa nan ki mayar masa!". Ya tashi ya fice daga gidan. Safiyya ta share hawayen da ya zubo mata, tana tunanin mafita, washegari ta bawa mai babur ɗin da yake Ni'ima makaranta kuɗin ta ce ya kai, duk da tana fargabar abin da zai iya biyo baya, amma ba za ta iya barin karatun yarinyar ya salwanta ba. To daga ranar ma bai sake zuwa gidanta ba, tana kallo ranakun kwananta za su zo su wuce ko leƙowa ba zai yi ba, a haka har aka yi sati biyu, da kayan abincinta suka ƙare ta kira shi a waya don ta faɗa masa bai ɗauki wayar ba, ta yi masa tex sai ga shi ya aiko da shinkafa tsurarta, ranar ta tafi gida ta faɗawa Baba duk halin da ake ciki, zancen Baba ɗaya ne dai me yasa ba za ta faɗawa babarsa ba? Ya dai ba ta dubu uku ya ce ta yi cefane, don haka daga gidan nasu gidan Hajiya ta wuce, ta manta rabon ma da ta je, don inda ake sonka nan kake zuwa, babu yabo babu fallasa suka gaisa da Hajiya, ta zayyana mata duk irin zaman da suke yi da shi, Hajiya ta ce"To idan ya zo za mu yi magana na ji gaskiyar lamarin". Safiyya ta ce ta gode ta tashi ta tafi, da sauran kuɗin da Yaya Aminu ya tura mata ta haɗa ta yi siyayyar abincin, tana ta jira ta ji Hajiya ta kira ta ko Salis ya zo ta ji shiru har sati ɗaya, cikin satin ne kuma ƙanwarsa Mariya aka tashe su daga gidan da suke haya, suka samu gida a nan cikin unguwar da Safiyya take, ba ta ji labari ba ma sai bayan sun tare, Mariyar ta zo take faɗa mata ta dawo nan da zama, ta wuni a gidan duk da ba wai fira suke yi ba, duk da akwai kayan miya amma mai da yaji ta yi, saboda Mariyar ta gani ta san ba yadda suke zato ba ne, to haka fa Mariya ta sarƙi gidan Safiyya kullum da safe mijinta yana fita za ta taho ta tare a nan, sha biyu idan yaranta suka taso daga makaranta su ma su sauka a nan har su huɗu ita ta biyar, ba ta tafiya sai bayan la'asar, saboda haka kullum a nan suke cin abincin rana, kafin Safiyya ta ankara shinkafa ta kusa ƙarewa, saboda haka ta rufe ta, ta auno garin kwaki kwano ɗaya, ranar Mariya tana zaune ta ga Safiyya shiru ba ta ɗora girki ba, sai da yaranta suka dawo ta ga ta haɗa musu garin kwaki, da mamaki Mariya ta ce"Safiyya yau ba za ki yi girkin ba ne?" Safiyya ta ce"E, shinkafar ta ƙare kuma kina kallo tun da kike zuwa gidan nan kin taɓa gani Salisu ya zo? Kin taɓa gani ya aiko mini cefane?" Mariya da sai da ta faɗa ta lura da hakan ta ce"Tabbas ban gan shi ba, shi dama bai sai dare ba? Kuma kuɗin cefane ji nake ba ki kuɗi yake?" Safiyya ta ce"Hmm! Na fi wata ɗaya ban saka shi a idona ba, kuma tun da ya aiko wannan shinkafar ita kaɗai babu ko nera biyar babu abin da ya sake aiko mini wallahi, da kuɗina nake cefane da kuɗina nake siyan abin da muke ci da safe, yanzu da shinkafar nan ta ƙare ko kiransa na yi a waya ba zai ɗaga ba ballantana na faɗa masa, shi yasa ma na siyo garin kwakin, kin gan shi na ɗari ne, ni yau ma ban san me zan ci ba". Mariya jikinta ya yi sanyi, tun da ta fara zuwa gidan ta ga Safiyya kullum shinkafa ce dai take dafawa mai da yaji, amma duk a zatonta da daddare tana yin girki mai kyau, ga shi ta lura dama duk ta ƙara ramewa kamar tana cikin damuwa, ta ce"Amma da gaske shi Salisun ne yake yi miki haka?" Safiyya ta yi murmushi ta ɗakko wayarta ta kira shi, Mariya tana ji har ta gama ringing bai ɗauka ba, sai da ta yi masa kira uku bai ɗauka ba, sannan ta ce da Mariyar"Kawo wayarki mu gani". Mariya da kamar an zare mata laka ta miƙa mata wayarta, Safiyya ta saka lambar ta kira shi, tana fara ringing ya ɗauka, jin muryar Safiyya ya ce"Safiyya lafiya?" Ta ce"Lafiya ƙalau, dama na kira ka ba ka ɗauka ba, faɗa maka zan yi shinkafarmu ta ƙare, yau ma ba mu da abin da za mu ci". A fusace ya ce"To ai sai ku zauna da yunwa! Har yaushe na aiko shinkafar da za ta ƙare? Kawai dai almubazzaranci kike yi min da abinci, to ku zauna haka!" Ya katse wayar. Ta miƙa mata wayarta, ta ce"To kin dai ji da kunnenki, shinkafar ce dama kawai take raba mu, ita ma yanzu ya ce ba zai siya ba, ƴan'uwana ne suke taimaka mini su ba ni abin da nake ci saboda na zauna dai a gidan aurena, ni ce omo ni ce sabulu, ni ce biyan kuɗin makaranta duk ya daina, ranar kwanana ma ya ɗaukewa kansa, ya kaiwa Ameera, amma babu komai zan ta haƙuri na ga abin da hali zai yi". Mariya ta jinjina kai ta ce"Ikon Allah! Shi kuwa me ya same shi? Tabɗijan, ki yi haƙuri Safiyya komai zai daidaita in sha Allah!". Safiyya ta ce"Allah Ya yarda". Mariya ta haɗa kan ƴaƴanta suka tafi, ta je ta ɗora girki tun da yau babu na banza, ta ji daɗin samun garaɓasar nan kullum ta ci a gidan Safiyya tana taƙamar ai yayanta ne yake kawowa, har ma tana ƙullatar Safiyya saboda ba ta canza girki, su cika cikinsu da yamma sai ta koma gida ta yi musu girkin dare mai ɗan daɗi, tun da ta samu ƙarin kuɗin cefanen rana da ba ta yi ba, ashe wani nauyi take ƙarawa Safiyya, sosai ta ji tausayinta, don ba ta yi zaton tana da kyakkyawar zuciya kamar haka ba, tana zuwa ta ɗora girki da ta gama ta bawa ɗanta ya kawowa Safiyya. Daga ranar sai ta daina zuwa, Safiyya kuma ta ci gaba da dafa sauran shinkafar tana cefanen kayan miya, sai bayan sati ɗaya sannan shinkafar ta ƙare tass, ta sake yi masa tex sai ga shi ya aiko da zallar shinkafar, abun duniya ya ishi Safiyya, ta rasa ma yadda za ta yi alƙawari ta yi ba za ta sake kai wa Baba ƙarar Salis ba, don ta lura ba zai fahimce ta ba, shi kuma Yaya Aminu yana da zafi ba za su kwashe ƙalau ba, ita kuwa Hajiya ba ta ga alamar za ta ɗauki mataki ba, don haka bussines ɗin da ya hana ta shi ta koma tana yi ba tare da saninsa ba, ta tafi kasuwa ta yi siyayyarta duk babu izininsa, jifa-jifa Mariya tana zuwa yanzu har fira suke yi, sosai take tausayin Safiyya amma da ta faɗawa su Hajiya babu wanda ya yarda, ƙarshe ma cewa suka yi ta barbaɗa mata wani abun a abinci ita ma ta mallake ta, don haka Mariyar ba ta sake faɗa musu ba, ita ma Safiyya takan je gidan nata su gaisa, idan ta canza girki tana aika mata, kamar yadda ita ma take aiko mata, duk ranar da babu makaranta yaran Mariyar haka suke zuwa su tafi da nata yaran su yi ta wasa. Mariya ita ma dayake mijin nata ba wani samu yake ba, rayuwar ta fara basu wahala sai ta fara yin abincin siyarwa tana bawa almajiri ya kai mata kasuwa, watarana suna fira da Safiyya take ce mata"Safiyya ba dan kin yi nauyi ba ai da sai ki dinga yin zobo ko kunun aya muna haɗawa almajirin nan, kya dinga rage wani abun". Safiyya da dama ta daɗe tana neman ƴar sanar cikin gida wacce za ta dinga yi don shi bussines ɗin nata ba wani tafiya yake yi ba, ta ce"Ai kuwa zan iya, ai haihuwar da saura fa kin ga a wata na biyar nake, kuma me nake yi a gidan? Zan yi wallahi". Mariya ta ce"Yawwa kin ga kullum za ki samu ƴan canji ya fi zaman haka, ki tambaye shi ko zai ba ki jari". Duk da ta san ba bata zai yi ba, amma haka ta ɗaga waya ta kira shi ta ƙaro ƙarar wayar saboda ta ji komai, amma bai ɗauka ba har ta gama ringing, da ta kira da wayar Mariyar sai ya ɗaga, yana jin muryarta ya ce"Safiyya wai a ina kuke haɗuwa da Mariya?" Ta ce"Gidan take zuwa". Ya ce"To ya aka yi?" Ta ce"Dama sana'a nake so na fara haka ta cikin gida, shi ne na ce ko za ka ba ni jari?" Ya ce"Kamar ya jari? Ni yanzu ba kuɗi ne da ni ba, ga shi za a yi bikin ƙanwar Ameera kuma gudunmawar dubu hamsin aka ce ta bada, ina ta ga dubu hamsin? Kin ga dole ni zan bayar, ga anko zan yi mata saboda haka ba za ku nakasa ni ba sai dai idan na samu na baki!". Ta ce"Amma ka san shinkafa ce kawai a gidana, ko tunanin da me muke karyawa ba ka yi, babu kuɗin cefane ba omo ba sabulu nefa ma duk wata fa ni nake biya, amma za ka bawa Ameera dubu hamsin ta kai gudunmawa?" Ya ce"Ni fa ban ce zan ba ta ba! Idan ban haɗa ba kafin bikin ai ba zan ba ta ya kai hamsin ba, kuma ita shinkafar ba abinci ba ce? To idan kin raina ki tafi gidanku ki ci kalar wanda kike so mana!" Ta ce"Shi kuma kwana da ka daina yi a ɗakina mene ne ma'anarsa? Ka san kuwa idan namiji ya yi wata huɗu da ƙauracewa matarsa za a tambaye shi dalili, idan bai dawo ba za a raba auren?" Ƙitt ya kashe wayar. Ta miƙa mata wayarta tana share hawayen da ya zubo mata. Mariya da jikinta ya mutu, saboda tsananin mamakin halin yayanta wanda ba ta taɓa sanin haka yake wa Safiyya ba a sanyaye ta karɓi wayar ta ce"Ki yi haƙuri Safiyya, watarana sai labari, zan aika a siyo miki duk kayan haɗin zoɓon gobe sai ki fara". Ta ce"Na gode". Mariya ta ce"Don Allah Safiyya ki yafe mana, wallahi da wani ne ya ce mini wannan rayuwar kike yi ba zan yarda ba, duk a zaton mu kin mallake mijinki yana yi miki komai, kuma Ameera ma kullum cewa take ke yake yiwa ita cefane ma ba ya yi mata, ashe ba haka ba ne, lallai zato zunubi". Safiyya ta ce"Babu komai na yafe miki, yanzu dai da muke zaune waje ɗaya ai kinga zahiri ko?" Ta ce"Na ga zahiri kam, har zai iya bata dubu hamsin ta kai gidansu ke kuma ya hana ki jarin da bai taka kara ya karya ba, ga shi babu cefane, babu kwananki? Tabɗijan! Ai ko ni ba zan iya wannan rayuwar ba, Safiyya kina da haƙuri". Suna zaune ta aika duk aka yo cefanen zoɓo har da robobi, aka wanke su tass washegari Safiyya ta fara yin zoɓo, kuma Allah Ya ba ta kasuwa tass ake siyewa kuma tana samun ribar dubu ɗaya ko da ɗari biyar, sai ta biya almajiri ta kuma zuba masa abinci, haka take ta gudanar da rayuwarta, idan ta je gida Baba yana ba ta kuɗi, haka Salma ma tana bata, Yaya Aminu ma yana yawan turo mata, da haka take rufawa kanta asiri. Idan ta kalli rayuwarta ta yau ta tuna rayuwarta ta baya sai ta ci kuka ta godewa Allah, daga baya ta yi wa kanta faɗa fa fara tashi tsakar dare tana kai wa Allah kukanta, idan ta tashi biyu da rabi sai ta yi sallar asuba take hutawa, idan ta sallami ƴan makaranta sai ta kwanta ta runtsa kafin sha ɗaya ta tashi ta fara aikin zoɓo, don ma almajirin nata yana taya ta da wanke robobin, kuma kullum shi yake yi mata shara, wanke-wanke, da aike kasuwa, ya kuma kawo mata kuɗinta cass, tana jin daɗin yaron sosai. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/4, 4:15 PM] Sadiya Abdulrazak: 35 Watarana Safiyya ta gama zoɓonta tana zuzzubawa a robobi almajirinta yana daga zaune a gefe Ni'ima ta dage ita a dole karatu take koya masa, Safiyya tana kallon su tana murmushi kwatsam suka ga Salis ya shigo kamar an jefo shi, yaran suka tare shi suna murna, ya ɗan sakar musu fuska, kallo ɗaya ya yi mata ya shige falon ya zauna, shi ma bai san abin davya kawo shi ba, kawai ya ji a jikinsa yana son zuwa gidan, daga kasuwa ma yake ya taso ya taho, yaran da suka ga babu fuska sai suka koma tsakar gidan, tana dab da gamawa ya fito tsakar gidan, ya haɗe gira yana kallon almajirin ya ce"Waye wannan kuma?" Ni'ima ta ce"Yaya Sadi ne" Don haka Safiyya ta ce suna kiransa. Salis ya haɗr rai ya ce"Safiyya waye wannan?" Ba ta kalle shi ba, sai da ta ɗorawa Sadi bokitin a kansa ya tafi sannan ta ce"Sannu da zuwa, ka shiga mana". A tsawace ya ce"Ina tambayarki wane yaro ne wannan kin yi banza da ni saboda raini..." Ta katse shi da faɗin"Almajiri ne". Ya ce"To uban me ya kawo almajiri gidana!?" Ta ce"Talla yake yi mini, zoɓo ne yake kai mini kasuwa". Ya ce"Da izinin wa kike yi? To daga yau na hana, kar wani almajiri ya sake shigo mini gida!". A fusace ta ce"Ba na buƙatar jiran izininka! Ko akuya ka ajiye ai tana da ƴancin ka dinga duba ta kana kula da ita, amma ka ajiye ni da yara da ciki shinkafa ce kaɗai take raba bi da kai, sannan ka ce kar na nemi sana'a!? Wallahi sana'a yanzu ma na fara yinta, kuma ban ga ranar bari ba har sai ka dawo cikin hayyacinka ka fara sauke nauyinmu da yake kanka!". A fusace ya ce"Au haka ma za ki ce? To tun da haka ne ki tafi gidanku, tun da kin ce ba na yi muku komai, ki tafi gidanku kawai zai fi!". Ta ce"Ni ban ce ba ka yi min komai ba, amma kai ma ka san ba ka yi min adalci ba". Ya ce"Na dai ce ki tafi". Ta ce"Zan tafi ai, Allah Ya sa hakan shi ya fi alkhairi". Ya shiga falo ya zauna, ita kuma ta yiwa yara wanka, ta ƙarasa girkinta suka ci ta zuba sauran a kula, sannan ta yi wanka fa shirya akwatuna maƙil da kaya saboda ko za ta dawo tana ji a jikinta ba dai nan kusa ba, yana zaune ta fita ta samo mai adaidaita sahu, ta loda kaya ta haɗa kan ƴaƴanta suka tafi, a ƙofar gidan Mariya ta tsaya ta miƙa mata kular ta ce ta bawa Sadi idan ya dawo, sannan ta faɗa mata duk abin da ya faru, ta ce Allah Ya sa hakan shi ya fi alkairi. Tana zuwa gida, Umma ta fara salati ta ce"Safiyya ya na ganki da uban kaya, ko babu auren?" Ta ce"A'a, ya ce dai na tafi gida". Umma ta ce"Ikon Allah! Abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa?" Ta shiga da kayanta tsaf, ta zauna tana ji a ranta gara zaman gidan da wannan rayuwar da take yi ɗin. Shiru Salis ya yi yana ta tunani, shi kansa ya san yana yi mata ba daidai ba, amma ya rasa dalilin da yasa yake yi mata, kuma idan ya yi yunƙurin gyara zaman nasu sai ya ji haushinta ya kama shi, sai wata zuciyar ta dinga faɗa masa ba shi da laifi ita ce mai laifi, damuwa sai cin zuciyarsa take yi, duk ya rame sam ba shi da nutsuwa, ga Ameera ta takura masa da ba ni ba ni, kuma yanzu ya riga ya fahimci ita take yi masa sata a aljihu, babu dama ya ajiye kaya sai ta lalube masa ya rasa yadda zai yi. Yana gidan Safiyya a zaune har aka kira sallar magriba, ya tashi ya yi alwala a ɗakin ma ya yi sallah, ya idar da sallah kenan sai ga kiran baban Safiyya ya shigo, gabansa ya faɗi saboda bai san da me zai kare kansa ba ma, ya daure ya ɗaga wayar suka gaisa Baba ya ce"Salis me ya haɗa ku ka ce ta taho gida?" Ya ce"Wallahi Baba Safiyya ce gabaɗaya ta canza mini, abin da ta ga dama shi take yi, ban hana ta ci da sha ba, amma sai ta dinga faɗawa ƴan'uwana ba na ba ta abinci, haka kawai ta tsiri fita babu izinina, kaf kasuwannin garin nan babu inda ba ta zuwa fa, wai kasuwanci take yi na hana ta ta ƙi dainawa, yanzu kuma ta samo wani matashin yaro wai almajiri ne ba ta san asalinsa ba kullum a nan gidan nata yake wuni, wai tana ɗora masa talla, ga mu da ƴaƴa mata yadda yaran nan ba mutunci gare su ba idan wani abun ya faru ya kenan? To shi ne na ce kar ya sake shigo min gida, ta ce ita yanzu ma ya fara shigowa, shi yasa kawai na ce to ta tafi gidan, na san za ka nemi jin dalili sai na yi maka bayani". Baba da ransa ya gama ɓaci da irin abubuwan da ya ji tana yi jinjina kai kawai yake yi, ya ce"To shi kenan Salisu zan yi mata faɗa in sha Allah! Amma irin wannan ai zuwa za ka yi ka kawo ƙararta ba wai ka koro ta gida ba". Salis ya ce"To a yo haƙuri Baba, ni dama gani na yi abun nata ya yi yawa, amma babu damuwa ko anjima zan zo mu tafi". Baba ya ce"A'a ka bari zuwa gobe da safe, zan yi mata nasiha yau ɗin, gobe idan Allah Ya kai mu sai ka zo ku tafi ɗin". Suka ajiye waya. Baba ya kira Safiyya ya ce"Da gaske kina kasuwanci?" Ta ce"Ina yi, amma yanzu kasuwar ta tsaya ma". Ya ce"Ke da kanki kike zuwa kasuwar?" Ta ce"E Baba". Ya ce"Da gaske ne kin samu almajiri kina ɗora masa talla?" Ta ce"E zoɓo ne nake yi masa, saboda na dinga samun na cefane, tun da yanzu..." Ba ta ƙarasa ba ya katse ta da faɗin"Ya isa, ba na son jin komai daga bakinki, amma Ummi kin ba ni mamaki, ina hankalinki da iliminki da har kika koyi halayen banza? Ki dinga fita babu izininsa har kasuwa, kuma kin san yadda tarbiyya ta zama a zamanin nan amma kin ɗakko yaro babu dangin iya babu na Baba kin ajiye a gida? To bari ki ji na faɗa miki, kar ki ga idan kin yo yaji ina bari ki zauna ki yi zaton ko ke ce ba ki da gaskiya zan bar ki ki zauna! Ba zai taɓa yiwuwa ba, ni ba na bayan ƙarya, saboda haka yau kawai zan iya ɗaga miki ƙafa ki kwana gobe mijinki zai zo ku tafi, kuma ki ba shi haƙuri, sannan idan na sake jin wani abun gaskiya ba za mu shirya da ke ba!". Tun da ya fara magana take ta kuka, har ya gama ta tashi ta koma ɗaki, don ba ta da abun faɗa kuma, tun da ya yarda da maganar Salis a tafi a hakan ba za ta ce masa ƙarya yake yi ba, za ta koma amma ta yi alƙawarin duk ranar da ya sake korarta ba za ta tafi ba, sai dai idan sakinta ya yi, ta kira Yaya Aminu tana kuka duk ta faɗa masa halin da ake ciki, Aminu ya ce"Ai ke Safiyya wannan auren kamata ya yi duka a bar shi kawai, na samo miki wanda ya kamata ki aura tun farko!" Ta ce"Ba haka ba ne Yaya Aminu, ba ka ga yaran da Allah Ya ƙaddara za mu haifa ba? Kuma yanzu idan na bar su wace irin rayuwa za su yi?" Ya ce"Ai shi kenan, amma kina buƙatar ki huta fa, ni a shawarata kar ki koma, ni na san inda zan kai ki kawai a neme ki a rasa ma har Baban, ki je ji huta sannan ki dawo, idan ma ya gaji ya sake ki shi kenan, amma wannan wace irin rayuwa ce?" Ta yi dariya ta ce"Ina za ka kai ni?" Ya ce"A, indai za ki je ɗin kawai ki yi min magana". Ta ce"Babu komai Yaya zan koma, na yi haƙurin komai ya yi farko zai yi ƙarshe". Suka yi sallama, haka ta zaɓi raba dare tana sallah da addu'ar neman sauƙi a lamarin sai ta samu salama a zuciyarta. Washegari sai da magriba ya zo da mai adaidaita sahu suka tafi, bayan Baba ya sake yi mata faɗa sosai, har suka ƙarasa gidan babu wanda ya yi wa wani magana, sai da suka shiga yana buɗe ɗakin yake cewa"Ki yi haƙuri Safiyya". Ta yi kamar ba ta ji ba, a falo ta ga kayan abinci ya siyo komai da komai, ta yi musu kallo ɗaya ta ɗauke kai, ya ce"Ki duba abin da babu sai na siyo". Ta ce"Ba sai na duba ba, lokacin da ka daina ba mu mun mutu?" Yaran suka fara tattaɓa kayan, Ni'ima ta yi tsallen murna ta ce"Umma har da doya, gobe za a soya mana". Don ta manta rabon da su ci doyar wacce da ba ta yanke musu. Ya fice daga gidan, tana kallo suna ta birkita kayan har suka gama suka yi bacci, ta kai su ɗaki, ta je ta kulle gidan ta kwanta, wajen ƙarfe goma ta ji ana ƙwanƙwasa gidan, da fargaba ta fito tana tambayar wane ne? Ta ji muryar Salis ya ce shi ne, ta zo ta buɗe, ya saka sakata ya wuce ya kwanta a falo, washegari da ya tafi sallar asuba bai dawo ba, da daddare ya dawo ya kwana a ɗakinta, kuma daga ranar ya ci gaba da rabon kwana amma babu wata firar arziƙi da take haɗa shi da Safiyya. Bayan sati biyu watarana da yamma ta shirya don zuwa gidan kitso kansu ya tsufa, ta kira shi a waya bai ɗauka ba, don haka ta yi tafiyarta, gidan da ta saba zuwa kitso ta shiga da sallama, sun saba da Halima sosai don ita ma takan zo gidanta su yi fira, da ta shiga tana zaune tana wanke-wanke, a firgice ta amsa sallamar da Safiyya ta yi, kamar wacce ta ga abun tsoro haka ta tashi, ta ɗauki yaronta da yake rarrafe ta kai shi ɗaki, ta dawo tana zarewa manyan ido tana cewa su shiga ɗaki, Safiyya ta saki fuska ta ce"Ina wuni?" Fuskarta a murtuke ta ce"Lafiya, ya aka yi?" Da mamaki Safiyya ta ce"To sai ka ce ni ɗin baƙuwarki ce? Kitso muka zo". Halima ta ce"A'a ni kam ba zan so ma ki zama baƙuwata ba, duk da dai mu nan daidai muke da kowa, mun sha la haula mun sha li'ilafi!". Safiyya ta ce"To! Halima me kuma ya kawo maganar nan?" Halima ta ce"Ni dai na daina yi miki kitso don Allah je ki kawai". Safiyya ta ce"To na gode" Ta fita ranta babu daɗi tana ta mamakin abin da ya haɗa ta da Halima. Gidan maman Aiman ta wuce, wacce ita ma ta san tana yin kitson duk da ba ta taɓa zuwa kitson ba, ta ƙwanƙwasa maman Aiman ta na buɗewa Safiyya ta saki fuska ta ce"Maman Aiman". Maman Aiman ta tare ƙofa tana leƙen yaranta dake tsakar gida ta ce"Safiyya lafiya kuwa?" Safiyya ta ce"Lafiya lau, kitso muka zo ko za mu samu". Da sauri ta ce"A'a ba za ku samu ba!" Ta banko ƙofarta ta bar Safiyya tsaye da ɗumbin mamaki. Ta ƙasara gidan Mariya, suka gaisa take faɗa mata kitso ta fito kuma duk ba ta samu ba ma, a nan gidan ta yi sallar magriba saboda ba girkin dare za ta yi ba, suka ci tuwo a gidan sannan suka koma gida. Washegari ta tambaye shi zuwa gidan Salma ya barta, ta san sai dare za ta dawo saboda haka ta ɗauko hijjabin Ni'ima da ya yage yau ɗin ta ba ta ta kai ɗinki a maƙota, babu jimawa Ni'ima ta dawo da hijjabin ta ce wai an ce ba za a ɗinke ba, Safiyya ta ɗauka shirme ta je ta yi kawai, saboda haka da suka shirya za su tafi ta saka hijjabin a jaka suka fito, a ƙofar gida tana yaran mai ɗinkin suna wasa yara biyu suka shige gida da gudu, Safiyya ta ciro hijjabin ta miƙawa ɗayan yaron da yake zaune ta ce"Kai shiga ka bayar a ɗinke min wannan". Har ya karɓa wani yaro da ya zo wucewa da almar tsoro ya ce"Kai Sadik ba an ce mu daina kula wannan matar da ƴaƴanta ba, shi ne za ka je aikenta?" Ya tafi da sauri. Yaron da sai yanzu ya tuna, ya saki hijjabin a ƙasa da mamaki Safiyya ta ce"Kai ba za ka je ba ne!?" Daidai lokacin da babarsu ta fito, fuska kicin-kicin ta ce"Safiyya me ya haɗa ki da ƴaƴana? Me kike yi musu?" Safiyya ta ce"Ikon Allah! Me zan yi musu? Ɗinkin hijjabin nan na ce ya miƙa miki fa". Matar ta ce"Ba zan ɗinke ba, kuma babu ruwanki da ƴaƴana, don duk abin da ya same su ke ce!". Ta shige gida ta bar ta tsaye da mamaki. Ta saka hijjabin a jaka suka tafi, har ta baro gidan Salma mamaki ya ƙi barinta jikinta duk ya yi sanyi. Washegari da safe ta sallami yara sun tafi makaranta ta ji ana buga mata ƙofar gida da mugun ƙarfi, a tsorace ta tambayi waye? Daga wajen ta ji muryar mata sun ce su ne, ta sako hijjabi ta buɗe, tun kafin ta ce wani abu ta ga mai ɗinkin jiya ce, da wata wacce ba ta santa ba. Ɗayar matar ta ce"Wannan ce Safiyyar?" Mai ɗinki ta ce"Ita ce". Matar ta kalli Safiyya ta ce"Kin gan ni nan? Duk duniya babu shege ko shegiyar da nake tsoro, wallahi ba maita ba ko tsafi sai dai ya gan ni ya ƙyale, saboda haka salun alun shige mu je ki tsallake ɗan mutane ki sakar masa kurwa!". Wata irin bugawa ƙirjin Safiyya ya yi, ta ce"Me kuke nufi?" Ba ta ankara ba matar ta wanka mata mari, ta ce"Yaron da kika bawa hijjabi da ƙaryar ya miƙa miki ɗinki, kika kame kurwarsa ga shi nan yau da zazzaɓi ya kwana! Don haka dole sai kin tsallake shi, idan kuwa kika kashe shi babu abin da zai hana mu kashe ki!". Lokaci ɗaya Safiyya ta fara karkarwa muryarta tana rawa ta ce"Wai ni kuke zargi da maita? Ni?" Mai ɗinki ta ce"To a unguwar nan uban waye bai san ke mayya ba ce!? Ashe shi yasa aka koro ki daga inda kika taso shi ne kika zo nan za ki lashe mu ɗaya bayan ɗaya! To wallahi ki ci kowa ki kwana lafiya ban da kurwar ahalinmu!". Hayaniyar da suke yi ce ta fito da matan maƙota daga gidajensu, kafin wani lokaci an fara cika kowa yana tofa albarkacin bakinsa, babban abin da ya ba ta mamaki babu mai goyon bayanta kowa ya yarda wai ita mayya ce. Ana cikin haka sai ga Mariya wacce labari ya je mata, ta daɗe tana jin ƴan unguwar suna raɗe-raɗin Safiyya mayya ce, sai dai ta faɗa musu ba haka ba ne, ba ta so ta zaƙe a ce don matar yayanta ce, sai yau da maƙociyarta ta shigo take ce mata ta fito kallo ga shi can Safiyya ta kame kurwar yaro daga ba shi hijjabi jiya ya taɓa ya kwana da zazzaɓi, Mariya ta sako hijjabi ta fito a kiɗime, tana zuwa ta tarar har an cika maƙil Safiyya sai kuka take, har da wanda suka fara janyota tana fizgewa ga ciki abun ya bawa Mariya tausayi, nan ta fara tijara tana ƙaryata mutane da cewar sai an shiga koto kowa sai ya bada shaidar inda aka ga ta yi maitar, sannan ta ɗaga waya ta kira Salis, yana kallon kiran ya ƙi ɗagawa don ya yi zaton Safiyya ce mai kiransa. Ƙarshe dai mazan unguwar da ba su kai ga fita ba su suka kwantar da tarzomar, ta hanyar cewa Safiyya ta kira babanta da mijinta su zo za a yi sulhu, Safiyya kai tsaye lambar Yaya Aminu ta bayar, ta yi sa'a yana garin kuma yana gida a kwance, tana kuka ta yi masa bayani, da mugun ɓacin rai ya duro daga kwancen da yake a gado, ko bayani bai yi wa Salma ba ya fice zuciyarsa tana tafasa. Tun kafin ya ƙaraso ya hango dandazon mutane a ƙofar gidan, hakan ya sa ya gane kwatancen da ta yi masa, sosai ransa ya ƙara ɓaci, ya yi tsalle ya ɗare bishiyar darbejiya ya karyo reshi ya tattare hannun riga ya taho a fusace, yana ƙarasowa ya ce"Kowace shegiya ta bar wajen nan!" Ido ya koma kanshi, bai tsaya wata-wata ba ya fara ɗaga ice yana zugawa duk wanda hannunsa ya kai kansa, kafin ka ce kabo ihu ya kaure unguwar matan kowa ya yi nesa, mazan ne suka riƙe shi suna zaginsa yana ramawa duk da wasu ma sun haife shi, amma idonsa ya rufe. Da ƙyar ya nutsu aka tafi gidan mai unguwa tare da mai ɗinkin har da yaron da ba shi da lafiyar, nan aka ce sai mijinta da babanta sun zo, Safiyya ta dinga kiran Salis bai ɗauka ba Aminu ya ce"Ni nan ni ne a matsayin ubanta, shi kuma mijinta ɗan iska ne shi da babu duk ɗaya, saboda haka a yi duk abin da za a yi kawai!". Nan matar ta mai da magana, mai unguwa ya ce a ina ta ji cewar Safiyya mayya ce? Ta ce a unguwa ta ji, sai da ta faɗi sunan matar da ta faɗa mata baki da baki aka zo da ita, ita ma ta ce a gari ta ji, aka ce sai ta faɗi wacce ta faɗa mata, ita ma ta faɗa, aka zo da matar, ƙarshe dai aka gano a bakin Hajara maganar ta samo toshe, saboda haka aka tiso Hajara a gaba wacce mijinta ya biyo bayanta, aka ritsa ta aka ce ta faɗi a inda ta ji, ta yi tsuru-tsuru tana ta kame-kame, sai da mijinta ya ce idan ba ta faɗi gaskiya ba daga nan gidansu za ta wuce sannan tana kuka ta ce kishiyarta Ameera ce ƙawarta, kuma ita ta ba ta dubu ashirin don ta ƙirƙiri maganar, kowa ya yi mamaki, nan aka tisa ƙeyar Hajara aka tafi har gidan Ameera, ashe Salis yana gidan ma bai fita ba zazzaɓi yake yi, aka yi sallama ya fito, ya bi mutane da kallon mamaki, har da Aminu da bai taɓa zuwa gidansa ba, ga Safiyya kana kallonta za ka san ta sha kuka, daga ciki suka shiga aka kira Ameera aka mai da zance, dama Ameera tun da ta ga Hajara gabanta ya yanke ya faɗi, don ta san aiki ya lalace, Salis ya kalli Ameera ya ce"Haka ne maganar da aka faɗa?" Ta gyaɗa masa kai tana sharar hawaye. Salis ya ji ɓacin rai sosai ya ce da mutanen da mai unguwa"Don Allah ku yi haƙuri, wannan maganar ta gida ce, za mu yi wa tufkar hanci, a yi haƙuri don Allah!". Nan aka yi wa Hajara faɗa sosai, da kuma cewa za ta bi duk gidan unguwar nan ta faɗa musu buyanta aka yi ta yi mata sharri, ita ma Ameera aka yi mata nasiha, aka bawa Safiyya haƙuri, sannan suka tafi suka bar Safiyya da Aminu. Salis ya kalli Safiyya ya ce"Don Allah ki yi haƙuri, zauna a nan, bari na yi wanka na raka ki gidan". Ya juya zai tafi, Aminu ya janyo jallabiyarsa ya maido shi baya, Salis ya kalle shi da mamaki, Aminu ya ce"Kai wa ka mayar ɗan iska tsakanin ni da Safiyya?" Salis ya haɗe rai ya ce"Aminu ka san dai ina da ƴancin korarka daga gidana ko? Saboda haka ka fi ce mini!". Aminu ya ce"Kai ban da ƙaddara ta haɗa ƙanwata da kai ka isa ma na kalle ka ballantana kejin gidanka? Safiyya tashi mu tafi!". Ya yi maganar yana kallonta. Safiyya ta tashi, Salis ya ce"A matsayina na mijinki ban yi miki izinin fita ba!". Aminu ya ce"Da gaske kake?" Safiyya tana shirin fita Salis ya ce"Idan kika fita daga gidan nan kar ki sake ki dawo!". Ta ce"Me hakan yake nufi?" Ya ce"Kawai dai na faɗa miki ne, sai dai ki bi shi ya ajiye ki a gidansa!". Aminu ya ce"Za ta bi ni, kuma wallahi ba za ta dawo ba sai ranar da ka saka gwiwarka a ƙasa ka ba ni haƙuri ka ce na dawo maka da ita". Salis ya ce"Ko da hakan zai katse igiyar aurenta?" Aminu ya ce"Wannan shi zai fi komai sauƙi ma". Daga haka ya yi hanyar ficewa daga gidan, Safiyya ta bi bayansa, ko waiwaye babu, suka fice suka bar Salis tsaye kamar an shuka shi. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/6, 9:15 AM] Sadiya Abdulrazak: *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan Kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *Nationwide delivery* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 36 Safiyya ta ce"Tsoro nake fa kar Baba ya yi faɗa". Aminu ya ce"To faɗan me zai yi indai da adalci? Sai ki zauna mijinki da matarsa suna juyi da rayuwarki, har ki zauna ana yi miki ƙazafin maita saboda tsabar raini, yana cewa a yi sulhu a gida, yana kare matarsa kuma ki dinga tunanin za ki ci gaba da rayuwa da shi? To mu tsaya tun daga hanya mu samu matsaya, ni na gaji da rayuwar rashin ƴanci da kike yi, zan sama miki mafita ne, idan kina so yau zan tafi da ke inda za ki huta ki zama mutum, idan kuma ba kya so to ki nunawa Salisu duniya ba ki da wanda ya fi shi, ki juya ki koma ki zauna a inda ya ajiye ki, amma wallahi duk ranar da kika sake kawo min ƙara ke ko ƙafarki na gani a gidana ko Salma ta ce na ba ki wani abu Allah sai kin ga rashin mutunci!". Safiyya kamar za ta yi kuka ta ce"Yaya Aminu ni fa ban ce ba na son ƴanci ba, Baba nake gudun..." "Dalla kyale shi! Shi ma daga baya zai san haƙurin da kika yi, yanzu dai za ki bi ni?" Ya tambaye ta babu wasa a fuskarsa. Ta ce"Yaya idan na je gidanka na tare ba zan takurawa Salma ba?" Ya yi dogon tsaki ya ce"Allah wadaran naka ya lalace! To idan ba waɗɗamsul basiratu ba Safiyya ina yi miki maganar ki yi nesa ki huta kina zancen gidana? Kina gidana ai kamar kina gidan Salisu ne, mu je ki kwaso kayanki tukunna dai". Suka hau adaidaita sahu, suka je gidan Safiyya ta haɗa akwati da duk abubuwanta masu muhimmanci, sai da ta fito za su tafi ta fara kuka, da mamaki ya ce"Safiyya idan fa kina son mijinki ki yi zamanki". Ta ce"Yarana fa? Suna makaranta". Aminu ya yi tsaki ya ce"Idan kin tafi da yara ta ya za a san muhimmancinki? Sai ya kai wa matar tashi ko uwarsa!". A sanyaye ta wuce suka tafi, gidansa suka je ta yi wanka ta ci abinci sannan Aminu ya faɗawa Salma abin da ya faru, ya kalli Safiyya ya ce"Safiyya Baba bai nuna mana muhimmancin dangin babarmu ba, su kuma duk maza ne kin ga ita kaɗai ce mace, ku mata kun fi zumunci shi yasa duk su ma ba sa nemanmu, to kin ga ni daga baya na neme su duk da sau ɗaya na taɓa zuwa, amma muna waya sosai da su, ina Baba Garba da na ba ki lambarsa?" Safiyya ta ce"Ina ga mun yi waya kamar sau uku". Ya ce"To kin ga ina ta so dama na samu dama mu je tare, to tunani nake kar wannan ɗan iskan mijin naki ya hana, shi yasa na ƙyale ki, ranar da na je gaskiya matarsa tana da kirki sosai, don haka ina tunanin can gidan zan kai ki a Gombe ki yi zamanki ki huta na wani lokaci, har sai kin dawo mutum, shi kuma idan ya yi hankali ya neme ki sai na kora masa warning idan ma kuma mun samu abin da muke fata ya sake ki shi kenan, ko ni zan samo miki wanda ya fi shi in sha Allah". Safiyya ta yi na'am da wannan shawarar, don ita ma ta gaji tana so ta yi nesa da gidan Salis ɗin, amma tunanin ƴaƴanta duk ya sanyaya mata jiki. Salma da ita ma abun ya dame ta ta ce"Amma Love ba ka ganin Baba zai shiga damuwa? Kuma idan ya san kai ne ka ɗauki Safiyya anya ba zai yi fushi da kai ba?" A fusace ya ce"To Salma tashi ki je ki faɗa masa tun kafin mu tafi! Je ki faɗa masa ya biya ki abin da kike nema a duniya, me ma ya zaunar da ke a nan wai muna sirrinmu?" Ta tashi tsam ta ce"Ku yi haƙuri rabon ayi ne ya zaunar da ni". Ta fice daga ɗakin, sai ya bi ta da kallo ya yi murmushi, halinsa ne faɗa shi yasa har ita yake yi mata, sai dai idan ta yi fushi ya san yadda zai yi ya gyarota, don sosai yake son Salma da farin cikinta, musamman da ba ta taɓa haihuwa ba, sai yake ganinta kullum kamar yarinya take ƙara zama. Sai da suka yi sallar azhar sannan suka fito suka ɗauki hanyar tafiya Gombe, bayan ta faɗawa mai babur ɗin su Ni'ima ya kai yaran gidan Hajiya, a mota ana fara nisa da tafiya Safiyya ta ji iska tana shigarta har zuciyarta, wanda hakan ya ƙara mata sanyin jiki, fata take a ranta Allah Ya zama gatan ƴaƴanta, kuma Ya sa wannan tafiyar ta zame mata alkhairi. A gidan Salis kuwa Aminu yana tafiya da Safiyya ya shiga ɗakin Ameera da take zaune dirshan a ƙasa abun duniya da kunya sun yi mata yawa, a fusace ya shigo yana huci ya ce"Ameera burinki dai ki tozarta Safiyya ko? Burinki na sake ta ki zauna da ni ke kaɗai ko, yanzu har ke za ki je ki biya kuɗi a ɓata mata suna? Inda ba a yi sulhu ba an shiga koto ya za ki yi? Ko kina tunanin ni zan fito da ke ne? To wallahi ba ki isa ba dai a nan gidan ba, wallahi wannan ƙarin auren bai yi mini rana ba, tun da na aure ki ban huta ba, matata ba ta huta ba, duk na birkice sai ƙarewa nake a tsaye kamar kuɗin guzuri, to ki shiga hankalinki wannan ya zama na ƙarshe da za ki shiga harkar Safiyya, kuma burinki ba zai cika ba! Ba zan saki Safiyya ba, ba zan sake ta ba, wallahi ba zan sake ta ba!". Ameera ta yi kukan kura ta miƙe tsaye ta yi tsalle ta dire a gabanshi kamar za ta shige jikinsa, cikin ƙaraji ta ce"Kar ka sake ta ɗin! Na ce Salisu kar ka sake ta! Kuma wallahi yau sai mun yi takife a gidan nan!" Ta fita da gudu ta yi kitchen, sai ga ta ta fito da taɓarya, cikin dakiya ya tsaya yana muzurai saboda abokinsa da ya ba shi shawarar ya daina tsoron matansa don sun tada aljanu, duk da zuciyarsa bugu take yi amma ya dake ya ce"Bisimillah Ameera ƙwala min, ina jiranki!" Sai ta yi mamaki, kuma ta kasa ƙwala masa ta tsaya tana ta huci kamar zakanya, hakan ya ƙarfafawa Salisu gwiwa ya shiga ɗakinsa da gudu, ita kuwa da ta ga hakan ta mara basa baya tana faɗin"Ka tsaya mana! Ka tsaya mu ga ƙarshen ƙaryarka, mu za ka rainawa hankali?" Salisu da dama abun duka ya shiga nema da bai samu ba ya fito ya shiga ɗakinta, wayar TV ya fizgo, ita ma da take ta binsa tana shigowa ya shiga zumbuɗa mata yana faɗin"A'uzubillahi minash shaiɗanirrajim!" Idan ya faɗa sai ya zabga mata wayar ya tofa mata yawu, da ta yi yunƙurin tashi ya taɗe ƙafarta ta koma, kuma shi tsakaninsa da Allah duk aljanu yake duka, don haka abokinsa ya faɗa masa irin wannan ba mutum kake duka ba, indai kana ta maimaita a'uzubillahi ba su isa su yi maka komai ba, don haka ya ƙara zage damtse yake ta zane ta yana a'uziyya. Ameera da ta jigata a wahale ta ce"Ka yi haƙuri don Allah, za mu tafi, mun tafi ba za mu sake ba!". Salisu da yau yake jinsa kamar wani jan wuya kuma ya cika jarumin jarumai ƙara shauɗa mata wayar ya yi yana cewa"Da uban me yasa kuka shiga jikin matata? Me ya kawo ku kuka hargitsa min gida?" Ya ɗaga bulala zai ƙara mata ta ce"Don Allah Salisu ka yi haƙuri, wallahi Safiyya ce ta turo mu, kuma ita take hargitsa maka gida". Ya ƙara shimfiɗa mata bulala ya ce"Kenan ba za ku daina sharri ba!". Sai kuwa ya cire jaɗɗabiya ya ajiye a gefe, ya ɗauki waya yana gyara ta zai shiga sabon zagon, Ameera ganin da gaske kasheta yake son yi da sauri ta fara jero atishawar ƙarya tana cewa"Mun fita, wallahi mun fita, attishawa! Ga matarka ta dawo mun bar ta har abada!". Salisu ya ce"Ni za ku rainawa hankali? Kun fita kuma kuke magana daga jikinta? Lallai ba ku daku ba ashe" Ya ɗaga ya sake zabga mata. Ta fara kuka sosai ta ce"Ameera ce ba aljanu ba Honey don Allah ka yi haƙuri, wallahi ni ce, kashe ni za ka yi? Dama ƙarya nake, ba ni da aljanu, Safiyya ba ta yi min turen komai ba na ƙarya ne wallahi!". Salisu ya ce"Ameera". Ta ce"Na'am!" Ya ce"Ameera ke ce?" A wahale ta ce"E wallahi ni ce, maman Sauban ce Babynka ce". Ya sauke ajiyar zuciya ya zauna yana haki, ashe ga magani a gonar yaro sai rashin sani, ai bai san da gaske ana zane aljanu a zauna lafiya ba sai yau ɗin, ya ce"To tun da sun tafi mu dawo maganarmu! Me ya sa kika yiwa Safiyya sharrin maita?" Tana kuka ta ce"Wallahi babu komai, tsautsayi ne kawai da sharrin shaiɗan". Ya ce"To ba zan lamunta ba, don haka yanzun nan ki haɗa kayanki ki tafi gidanku sai na neme ki". Ta ce"To!" Ta tashi da sauri, don wani mugun tsoronsa take ji, kar ta yi maganar da zai yi zaton aljanun ba su tafi ba, ta haɗa akwati, ta goya Sauban da take ta bacci, ta saka hijjabi ta tafi, tana jin ilahirin jikinta yanda yake mata zugi, sai karkarwa take yi, ko karyawa ba ta yi ba, ta karya da masifa. Tana tafiya ya yi wanka ya tafi kasuwa, ya san zai samu kira daga Hajiya, amma wannan karon ba ya jin zai iya sauraron kowa akan abin da Ameera take yi masa, haka sai ya ga ta gaji da zaman gidan zai neme ta. Shi kuma Aminu idan bai fita daga hanyarsa ba zai shayar da shi giyar mamaki, domin a yanzu ya fishi iko da Safiyya tun da matarsa shi, ya san Aminu bai ƙi ya saki Safiyya, to kuwa sai dai ya mutu don auren shi da Safiyya babu saki ko da kuwa ƙiyayyar da yake ji akanta za ta yi ajalinsa, ita ma alƙwari ya yi ba zai neme ta ba, sai dai ta dawo da ƙafarta, don ya san Baba ma ba zai bar ta ta zauna ba ai, da haka ya shiga harkokin shi na kasuwa. Sai sha biyu Hajiya ta kira shi, ya ɗaga suka gaisa ta ce"Salisu me ya faru ne na ga yaranka an kawo su da unifom wai babarsu ce ta ce a kawo su ba ta nan?" Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Hajiya su zauna a nan ɗin, idan na dawo zan yi miki bayani". Ta ce"To gaskiya ni dai ba za ka min na wancen karon ba, ka ajiye min yara na yi ta fama ni ba lafiya ba, kuma ka dinga iyayin ba na kula da su, don haka ka zo ka kwashe su, ka kaiwa Ameerar, meye amfanin matan biyun? Ai ana ƙara aure ne don idan dama ta ƙiya a koma hagu!". Ya ce"Yi haƙuri Hajiya sai na zo ɗin". Suka ajiye waya, ta zuba musu abinci suka ci, haka suka wuni da unifom a jikinsu tun da babu kayan da za su saka. Ameera tana shiga gida ba ta bi ta kan Ummanta da ke bin ta da kallo ba, ganin yadda ta shigo a birkice ga idonta kana kallo ka san ta sha kuka, ta shige ɗaki, ta sauke Sauban, ta cire hijjabi ta cire riga ta yi ɗaurin ƙirji ta kwanta ta saki wani marayan kuka, Umma da ta biyo ta burki ta ja tana kallon jikin ƴar tata da ya yi ruɗu-ruɗu da shatin bulala, ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah Ya raba mu da mugun ji da gani, Ameera me zan gani haka, wane shegen ne ya yi miki wannan ɗanyen aikin? Waye ya yi miki dukan da ko ni ban taɓa yi miki irinsa ba?" Ganin Ameera ta ƙi ko motsi sai ma sautin kukan da ta ƙara, ta ce"Ke tashi don ubanki ki yi min bayani, wane isasshen ne ya dake ki haka?" Ameera ta ce"Shi ne fa, Salisu ne". Sai jikin Umma ya ɗan yi sanyi ta zauna ta ce"Kama ki ya yi kin ɗauki kuɗi?" Ta girgiza mata alamar a'a. Ta ce"To uban me kika yi masa?" Ameera duk ta yi mata bayani tun daga farko har ƙarshe, Umma ta yi tagumi ta cire ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Ke me ya kai ki yiwa mutum sharrin maita? Kin san kuwa shari'ar maita ba ta mutuwa? Yau idan suka kai mu kotu ya za mu yi? To bari ki ji ko gidan nan da muke ciki za mu siyar sai kuɗin sun ƙare a kotu, gaskiya ba ki da tunani, ni dai na haifi raguwa lusara, ashe ke ba ki san rayuwar nan ta zama iya ruwa fid da kai ba? Ke har yau ba ki san kissa ba? Tun farko me ya hana ki tsalle ki ce ita Hajara sharri ta yi miki? Me yasa kika amsa kin aikata? Allah na tuba ko kisan kai na yi indai daga ni sai gawar zan amsa ne? Ke kam an yi shashasha! Shi kuma zai zo ya same ni, wallahi sai ya san ya yi miki wannan dukan, na rantse da Allah har Hajiyar yau sai ta san ba a taɓa min ƴa a taɓa banza, idan ma ta kama a raba auren sai ya sake ki, ki zo ki yi idda ki samu wani, ai ba kwantai kika yi ba, na ɗauka na ba shi!". Ameera ta ce"Umma ni fa ban ce ina so ya sake ni ba, kuma da kike cewa na zo na zauna a nan, na ga omon wanki ma daga gidana nake tara miki, haka kawai na zo na zauna nama ma sai na shekara tab!". Umma ta ce"To mayya don ubanki ki koma, ki koma ki ci nama, idan ba ki ci ba ai shi ya cinye ki, wannan ai wulaƙanci ne har ya saka bulala ya dake ki wai ruƙiyya? Kuma ma ban ce kar ki sake yin aljanun nan ba dama?" Ta ce"Tsautsayi ne, kuma don na ga da yana tsoro ne, abun yana kai min idan na yi, amma ba zan sake yi ba". Umma ta ce"To tashi ki yi wanka ga ruwan zafi nan a wuta, kawo kuɗi idan akwai sai a siyo miki madara ki sha shayi, a samo miki magani ki shafa a jikinki". Ta ɗakko jakarta ta miƙa mata dubu ɗaya, Umma ta karɓa ta ce"Wanke ƙafata zan yi na je gidan Hajiyar ta zo ta ga halin da kike ciki". Ameera ta ce"A'a Umma ki ƙyale su, za su zo da ƙafarsu, don wallahi ba zan koma ba sai sun ɗanɗana rashina sosai, sai ya sha wuya kafin na koma". Umma ta fita ta haɗa mata ruwan wanka, kafin ta gama ta siyo madara da maganin shafawa, tana shan shayi tana shafa mata, tana ta zagin Salisu har danginsa. Dab da magriba Safiyya da Aminu suka sauka a Gombe, jikinta a sanyaye Aminu riƙe da akwati suka ƙwanƙwasa ƙofar gidan, duk da ya ga a buɗe yake ma, yarinya ta fito tana kallon su ta ce su shigo, suka shiga matar gidan ta tare su da fara'arta, don ta gane Aminu, ta rungume Safiyya tana cewa"Lallai Aminu ka cika alƙawari, sannunku da zuwa". Suka shiga madaidaicin falon ta kawo musu ruwa da abinci tana ta yi musu sannu, a masallaci Aminu ya haɗu da Baba Garba, wanda ya yi farin ciki sosai da ya ji da Safiyya suka zo, sanda suka shigo gidan Safiyya ta idar da sallah tana zaune suna taɓa fira da yarinyar da ta ce jikar gidan ce ita, ita kuma matar gidan ta shiga kitchen don ta ƙara yiwa baƙi girki. Baba Garba ya ce"Lale maraba da ƴata, sannu da zuwa, Aminu ya kyauta!" Ya zauna suka fara fira yana ta tambayar rayuwarsu da ƴaƴanta, ta ce ba ta zo da su ba, a ɗakin Samira ta kwana Aminu kuma ya kwana a wani ɗakin, ɗakuna biyar ne a gidan, sai babban filin tsakar gida, bacci mai daɗi Safiyya ta yi, don ma tunanin yaranta yana tsaye a zuciyarta, amma tana ta ƙoƙarin mai da komai ba komai ba. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/7, 5:07 PM] Sadiya Abdulrazak: *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan Kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *Nationwide delivery* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 37 A gidan Hajiya dab da magriba Salisu ya dawo daga kasuwa, kai tsaye gidan nata ya wuce, yana shiga ya ga yaran duk a takure saboda ba su saba da zuwa gidan nata ba, haka ma sam ba ta da halayyar jan jikokinta a jiki, ya zauna yana kallon su sai ya ji tausayin su, bayan sun gaisa da Hajiya ya ce"Yanzu da unifom suka wuni?" Hajiya ta tsuke fuska ta ce"To ka kawo musu wasu kayan ne? Ko nawa zan ara musu?" Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Bari na je na kwaso musu kaya, sai na nemo mukullin gidan Safiyyan ma, don ya yi nisa". Hajiya ta ce"Ba ka yi min bayani ba fa, me yasa ta tafi ta bar yaran, kuma akan me ba ka bawa Ameera ba?" Ya ce"Hajiya ita ma fa Ameerar tana gidansu..." Nan ya kwashe komai ya faɗa mata, ta ɗauki salati ta dire sannan ta ce"To wai ko dai abin da Mariya take faɗa a kan Ameera gaskiya ne? Ni na ga Mariya lokaci ta ɗaya ta rikiɗe ta koma ganin gaskiyar Safiyya, tana cewa Ameera ba mutum ba ce". Salisu ya ce"Hmm! Hajiya dukan su dai ban yi dace ba, kowacce da nata halin, ni dai da na san haka ƙarin aure yake da ban ƙara ba wallahi, tun da Safiyya ai da ba ta fito da wasu halayen nata ba sai da ta ga na yi aure, da muna zaune lafiya abun sha'awa, kowa ya tuna bara bai ji daɗin bana ba!". Hajiya ta ce"Amma kuwa indai da gaske Ameera ta aikata wannan sharri da tuggun Allah na dawo daga rakiyarta, ni dama tun da aka ce wai ka bata gudunmawar bikin ƙanwarta har dubu hamsin amma ka ƙi bawa Safiyya jarin da za ta yi zoɓo na ce to lallai Safiyya ta gamu da wacce ta fi ta iya dafe miji..." Salis ya ce"Hajiya kenan, ai wannan zuwa a faɗa miki ƙananun maganganu shi ya kawo kika tsani Safiyya, yanzu daga zancen zan bata gudunmawa ban kai ga bata ba, an zo an ce miki na bata?" Hajiya ta ce"Yo idan ma ka ba ta mene ne? Salisu ni ai dama matanka na haifawa kai, ka je ka yi ta musu hidima wallahi babu komai, nima ai mijina ya yi min, ka dai dinga tuna inda aljannarka take kawai". Bai ce komai ba, ya tashi saboda sallar magriba da aka fara kira, har zai fita ya ce da yaran"Kun ci abinci?" Suka gyaɗa masa kai alamar sun ci, ya ce"Za ku ci wani abun?" Suka girgiza masa kai. Sai da ya yi sallah sannan ya tafi gidansa, wanka ya yi ya nemo mukullan gidan Safiyya da ya ajiye a nashi ɗakin, ya fito yana kallon ɗakin Ameera ya fice daga gidan, gidan Safiyya ya je ya kwaso musu kayan sakawarsu ya duba kichen ya kwaso abubuwan da za su iya lalacewa kafin ta dawo, sannan ya koma gidan Hajiya, ya kai mata kayan, ya yi wa yaran wanka ya saka musu kaya marasa nauyi, ya wanke unifom ɗin don kala ɗaya ne da su kuma gobe ma akwai makarantar, Hajiya ta zuba musu tuwon dare suna ci, shi ma ta saka masa, tana ta surutunta shi dai bai sake tofa komai ba, ya gama ya tashi ya yi mata sallama ya tafi. Duk yadda Ameera ta hana Umma zuwa gidan su Salisu ba ta yarda ba, don cewa ma ta yi dole tare za su je da ita a ga yadda ya yiwa fatar jikinta wal mukalafatu, amma Ameera ta ƙi zuwa don gani take gara su zo da ƙafarsu sannan a yi musu duk wacce za a yi. Wajan tara na dare ta yi sallama a gidan su Salis, Hajiya dake tsakar gida tana jin radio, ta amsa tana tantance muryar, Umman Ameera ta shigo fuska babu walwala, Hajiya ta ɗauki fitila ta haska ta ganin ta yi tsaye ta ƙi zama, ta ce"Au ashe ke ce! To ki zauna mana Dije ya za ki yi min tsaye a ka, kamar kin zo dambe?" Umman Ameera ta ce"Ai dayake ba zaman ne ya kawo ni ba". Hajiya da take ciki da Ameera na gane ita ma tatike mata ɗa take yi, ta haɗe gira ta ce"To mene ne ya kawo ki?" Ta ce"Tashi za ki yi mu je gidana ki ga yadda ɗanki ya yiwa ƴata, ya yi mata dukan mutuwa kamar ya samu ɓarawo, ya faffasa mata jiki!". Hajiya ta ce"Ai kuwa indai ba uwata Saude ce za ta taso daga ƙabari ba ban ga uban da ya isa ya sa na fita a daren nan ba, sai ka ce wata ƴar iska da daren nan ki ce na tashi na je na ga wata Ameera? Kuma da kike cewa ya dake ta kamar ɓarauniya yo meye ɓarabar dambe da faɗa, ke Dije inda kina da kunya ma har kya zo ki tsaya min a ka saboda an daki ƴarki? Na ga nan ta sace babur ɗin ɗana ta kai miki har kin saka shi a kasuwa asirinku ya tono, amma saboda ni ƴar halak ce na yi shiru na rufe maganar ko ƴan'uwansa ban faɗawa ba, nan Salisu ya ɗauki gudunmawar dubu hamsin ya ku wa ya sani ma ko ya fi haka? Tun kafin Ameera ta haihu maƙotanku suke ta kawo mini gulmar yanzu Salisu shi yake ci da gidanki, ƴar sana'ar da kike yi ma kin daina, kayan abinci kullum sai ƙanwarta ta je ta karɓo, omo da sabulu duk shi ne, amma saboda yadda nake kallon ƴarki da idon so ba na ganin laifinta, sai na ce musu babu komai ai kyautatawa ce, shi ne don ya dake ta har ni za ki kwaso ƙafafuwa duk kaushi ki ce za ki ci min mutunci? To ba sai a dawo miki da ƴar taki ba ki kwaɗa ki ci!". Umman Ameera da jikinta ya yi sanyi, ajiyar zuciya ta sauke ta ce"Ai abun bai kai haka ba Hajiya, kuma ba ki fahimce ni ba wallahi..." "To fahimtar da ni!" Hajiyar ta katse ta. Umma ta ja kujera ta zauna ta ce"Ki yi haƙuri, wallahi yadda ya iya saka bulala ya zane ta ne abun ya ɓata mini rai, Ameera ai ta wuce duka yarinya da ɗanta ya zane ta sai ka ce a makaranta?" Hajiya ta ce"Ai ke ce ba ki zo da fuskar fahimtar juna ba, kin ga yanzu ya bar gidan, duk ya faɗa mini duk abin da ya faru, Ameera ta yiwa matarsa sharrin maita, amma wallahi bai ce min ya daki Ameera ba, bai faɗa min ba kuma duka da ya yi mata ai ko kotu aka je sai an yi mata shi, saboda ƙazafin da ta yi". Umma ta ce"To a yi haƙuri dai, amma gaskiya Ameera ba za ta koma nan kusa ba, dole sai ya gane laifinsa". Hajiya ta ce"To ai babu damuwa Allah Ya ganar da shi ɗin". Umma ta fice, jikinta duk ya yi sanyi da zancen satar babur da aka tada, kuma ba ta taɓa zaton duniya ta san ana kawo mata ƙulli daga gidan ƴarta ba, sai yanzu da ta faɗa mata, ashe kallon hotiho ake yi musu ita da ƴar tata, lallai yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba. Bayan fitar ta Hajiya ta taɓe baki ta ce"Yo ba sai ya gane laifinsa ba mu gani, Allah na tuba wani abun arziƙin za ki na yi mata a gidan wanda ɗana ba ya yi mata? Yarinyar da take garari a gidajen unguwa ta yi aiki, ta yi aike kasuwa, ta yi raino don ta samu wani ihsanin shi ne za a mana fankamar ba za ta dawo ba? Kar ta dawo ɗin, shi dai Salisu bai yi dace ba, ba abun na saka shi ya ƙaro ta uku ba". Ta ɗauki wayarta, ta fito ta samu matasan da suke zaune a ƙofar gidan ta miƙawa wani ta ce"Yaro kira min Fa'iza a wayar nan" Ya kira ya miƙa mata, ta shiga gida tana yi mata bayanin komai har da ƙari ta ce babu kalar zagin da babar Ameera ba ta yi mata ba, don Hajiya kam sharri ya zame mata jiki, Fa'iza ta kumbura, da so ta yi ma ta bari da safe ta je gidan amma ta kasa jurewa, jira take mijinta ya gama cin abinci ta tashi ta tafi, don ba wanda zai taɓa mata uwa ya kwana lafiya. Da ta koma gida ta faɗawa Ameera duk yadda suka yi, Ameera shiru ta yi saboda takaici, Umma ta ce"Ameera! Ko kin fara bacci ne?" Ta ɗan bankaɗa labule ta duba jin kamar an yi sallama. Ta sake cewa"Ameera!" Ameera ta ce"Idona biyu, ai duk na ji ki". Ta ce"Kenan shashasha kika mayar da ni". Cike da baƙin ciki ta ce"Haba Umma, akan me za ki je ki yi abin da za ta raina miki hankali, wannan ai wulaƙanci ne ta ce miki wai ƙafarki duk kaushi, to wallahi da tare muka je sai na wanke ta tass, ai ba tsoronta ake ji ba da ɗanta zai dake ni, kuma ta ce miki da kaushi a ƙafarki kuma wai har ki bata haƙuri daga ƙarshe". Umma ta ce"Duk abin da aka yi min ai ke kika siya min, ni tana min zancen satar babur wallahi sai na ji kamar an zare mini laka, jikina ya yi sanyi ƙalau, ga kuma ashe duk ta san kina kwashe kayan abinci kina kawo mini, ashe duk mutane suna hankalce da mu, ke har gudunmawar da zai ba ki, har an faɗawa matar nan wai ya riga ma ya ba ki, to na dai faɗa mata wallahi ba za ki koma nan kusa ba!". Ameera ta ce"To duk ba ke kika ja mana ba? Inda ba ji ce dole sai na gina gida ba ai da ban yi satar babur ba, kuma ni duk kayan abincin ma na rasa da gaske siyarwar ake ko ci kuke? Gini dai har yau babu labari, kuma ni kima daina cewa zan zauna a gidan nan, idan ya zo ya ba da haƙuri kawai zan bi shi, ni babu ruwana da abin da wannan tsohuwar ta yi miki!". Umma da ta zaburo kamar za ta kai mata duka, cak ta tsaya ganin mace ta faɗo kamar an jefo ta, Umma ta ce"Subhanallah! Wace haka?" Ameera ta yi juyi don ba ta son ƴan unguwa su san ta yo yaji, don a tunaninta maƙota ne ƙawayen Umma. Fa'iza ta ce"Ameera tashi ki maimaita abin da kika gama faɗa!". Ameera ta juyo da sauri jin muryar Fa'izar, zaune ta tashi tana basarwa tana haɗe gira ta ce"Yaya ce?" Ta ce"A'a ba ni ba ce! Ai ni kam matsayin Yaya an sauke shi, abin da uwata ma kina ganin damarta har kina cewa za ki wanke ta tass to ni kuwa yaushe zan tsira? Yanzu ke Ameera duk halaccin da na yi miki da wannan za ki saka mini?" Umma da ta fusata da laɓen da Fa'izar ta yi musu a zuciye ta ce"Halakcin uwar me kika yi mata?" Ameera ta ce"Umma don Allah ki yi shiru". Fa'iza ta ce"To gara dai ki faɗa mata, tun da ba ki manta sanda kike gudun koriyar miya ki zo gidana neman ceto da jar miya, kwananki kullum a gidana, ko nama na ci sai na ajiye miki, idan na aike ki kasuwa na ba ki kasonki, ƙarshe ban bar ki haka ba sai da na ɗauke ki na bawa ƙanina mai rufin asiri, kika yi bulunbuƙui a gidansa kalli yadda kika yi ƙiba, kin ji jar miya da ƙashin miya, madara borodi da tsire, ga suturar arziƙi, wane wulaƙanci da ƙasƙanci ne ba mu yi wa Safiyya ba duk saboda ke, ashe kya ce ku gama niƙa na kwashe garin, shi ne za ki saka mana da wannan, ashe da gaske har kayan abinci kike kwashewa? To kuwa yau ba sai gobe ba, take a nan sai Salisu ya sake ki, sai kin dawo kejin gidanku, ƴar iska wacce ba ta gaji arziƙi ba". Ameera da tuni take hawaye, kasa cewa komai ta yi, idan Umma ta zaburo za ta yi magana sai ta damƙe hannunta, da ta gaji da fizge ta miƙe tsaye tana gyara ɗaurin zani ta ce"Idan ba ki fasa ba ba ki haifu ba! Fa'iza idan ba ki karɓo takarda kin kawowa Ameera ba a titi Hajiya ta yi naƙudarki...". Ameera ta katse ta da faɗin"Haba Umma don Allah! Na ce ki yi haƙuri ki ƙyale ta". Umma ta ce"Ba zan yi shirun ba don buhun ubanki! Ko an faɗa miki za ki rasa miji ne idan ya sake ki ɗin?" Suka yi shiru jin Fa'izar ta ɗaga waya tana kira. Salisu da yake kwance ya yi nisa a tunani, ƙarar wayarsa ne ya dawo da shi, ya yi tsaki yana duba mai kiran, ganin Fa'iza ce ya ɗauka murya a sanyaye ya yi sallama, ko amsawa ba ta yi ba ta ce"Salisu idan kai ɗan halak ne, haihuwar Hajiya don Allah yanzu a nan ka ba ni saƙon saki na faɗawa Ameera!". Salisu ya tashi zaune yana murtsika ido ya ce"Yaya me kika ce?" Ta ce"Na ce ka saki Ameera yanzun nan, saboda ba macen zama ba ce! Yau dai Ameera da uwarta babu kalar zagin da ba su yiwa mahaifiyarka ba, uwarta har gida ta je ta ƙare mata zagi kamar za ta dake ta, yanzu na zo gidan na ji dalili na tarar suna ƙara maimaita zance, wai Salisu she har babur ɗin nan ita ta sata, kuma kake zaune da ƙasurgumar ɓarauniya?" Salisu ya yi wani shegen murmushi a zuciyarsa ya ce'An zo wurin kenan' a fili kuwa ya ce"Wai ko ɓata kika yi ne Yaya? Ameera ko Safiyya?" Fa'iza ta ce"Ubanka kai da Safiyyar..." Ya katse ta da faɗin"To ai gani na yi Ameera zaɓinki ce, ke kika yiwa Hajiya ta yi, har ta amince kuka tursasa ni, ni kuwa tun da ina so na gama da duniya lafiya ni da Ameera ai mutu-ka-raba". Daga haka ya katse wayar, ya kashe ta duka ya ajiye. Fa'iza ta yi huci mai zafi ta ce"Wallahi Ameera idan ma sihiri kike yi masa sai mun warware shi, ai kin ga dai yadda aka yiwa Safiyya ƙaiƙayi aka hana ta zaman gidan ko? To ki saurari naki!" Daga haka ta fice kamar za ta kife don baƙin ciki. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/8, 4:42 PM] Sadiya Abdulrazak: *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan Kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *Nationwide delivery* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 38 Ameera ta fashe da kukan tashin hankali, don kuwa yadda take jin son zama a gidan Salisu gani take idan ta bari ya sake ta kamar ba za ta samu wani ba, don shi ɗin ma da ƙyar ta same shi, samarin ta yi su kala-kala amma duk ba da niyyar auren suke zuwa ba, kuma yadda take jin rayuwar wasu gidajen auren wasu ko abinci da ƙyar ake ci, ai kuwa gidan Salisu da rufin asiri, ji take ita indai ba zai sake ta ba za ta ma iya zub da makaman yaƙinta su zauna da Safiyya lafiya, don haka ita za ta ma iya faɗa masa asiri su Hajiya suka yi wa Safiyya ta tsani ɗakinta, saboda ya dawo da ita gidan, yanzu ta gane gara ma ace suna kusa tana ganin wainar da suke toyawa. Cikin takaici Umma ta wawuri mafici ta jefe ta a fusace, ta ce"Tashi ki koma ɗakin naki, yau ga mara kirkin yarinya ana ƙoƙarin kankaro miki daraja kina cijewa!". Ameera ta ce"Ai Umma duk ke ce kika ja min komai, ga shi yanzu ai ta faru ta ƙare, shi kenan sun tsane ni, kuma ina kallon yadda suke yi wa Safiyya, wataƙil ni ma su yi min asirin na tsani Salisun ma gabaɗaya..." Ta ɗauki wayarta ta kira shi, ta ji a kashe, ta rushe da kuka ta ce"Shi kenan ya saka ni a black list, saura gobe na ga saƙo". Ta ƙara fashewa da kuka.Umma da takaici ya ishe ta ta fita ta bar mata ɗakin tana cewa"Allah wadaran naka ya lalace!". A ɓangaren su Safiyya kuwa da asuba bayan sun idar da sallah Aminu ya zayyanawa Baba Garba duk labarin halin da Safiyya take ciki, ya kuma ɗora da faɗa masa toƙonsu na son Safiyya ta zauna a nan ɗin kafin wani lokaci. Baba ya kira matarsa ya ce su zo tare da Safiyya, a gabanta ya nemi jin ƙarin bayani daga bakin Safiyya, ta kuwa zayyana musu har wanda Aminu ma bai san an yi ba, duk suka ji tausayinta kuma suka yi na'am da zamanta a nan ɗin Mama ta ce za ta riƙe Safiyya ko da kuwa har abada ne, Baba ya ƙara da faɗin ya zama wajibi Safiyya ta zauna a nan ɗin, don nesa da juna ne kawai ke sa wasu mazan su san muhimmancin mace, idan kuma ya sawaƙe mata shi kenan, shi yana roƙon ma ta yi zamanta a nan ɗin har ta samu wani mijin, don sun ɗaura ɗamarar yin zumuncin da ba su raya shi ba a baya, Baba ya shiga damuwar yadda bai ja ƴaƴan ƙanwarsa a jika ba ballantana ya san damuwarsu, don haka yanzu ne ya kamata ya nuna musu gata ta hanyar kyautata Safiyya, a mayar da ita mace mai dogaro da kanta, wanda hakan ne zai sama mata ƴanci a duk inda ta shiga. Aminu a ranar ya yi niyyar komawa, amma Baba ya ce ya ƙara kwana, don ya zaga dangi a gaisa, ita Safiyya tun da ta zama ƴar gida idan ta huta sai ta fara zagayen a hankali, sai washegari Aminun ya tafi ya bar Safiyya wacce ta fara sakewa da Mama suna fira. Kwananta uku wata ƴar gidan ta zo, wacce ita ce babbar ƴar Baban, bai fi ta girmi Safiyya da shekaru biyar ba, ta birge Safiyya, ganinta fess da ganin suturar jikinta da kalar fatarta ka san rayuwa take yi ta jin daɗi, ga shi ta ji har Baba Hajiya Ramla yake ce mata, suna ta wasa da dariya cike da nishaɗi, ita ma Ramla ta yi farin cikin ganin Safiyya kuma ta sake sosai suna ta fira cike da tausayin rayuwar da ta ji Safiyyan tana yi a gidan aure, nan take tambayarta wace sana'ar take yi? Safiyya ta faɗa mata da ta fara bussines ɗin kayan sakawa da na kitchen sai ta daina, ta dawo zoɓo shi kuma ba wata riba ce da shi ba. Ramla ta yi murmushi ta ce"Haba ƙanwata wane irin zoɓo ana zaune ƙalau?" Safiyya ta ce"To tun da ya hana ni kasuwancin ai sai na yi na cikin gida, ko na kayan miya zan dinga samu". Ramla ta ce"To da wannan ma, amma yanzu shi kasuwanci ai ba sai kin fita ba, kin gan ni nan ni ma farkon aurena na fuskanci ƙalubale, ni ba ni da kishiya shi ne dai mai gidan ba mai alheri ba, idan ya ajiye min abinci shi kenan, sutura sai sallah ta zo, na yi ta ganin ƙawayena suna fantamawar su, na dinga ganin ni ban yi dacen miji ba, na yi ta raina kaina ina raɓewa a cikinsu, da da yake ni mai yawan karance-karance littafan hausa ce, har muke gaisawa da wata marubuciya, ban sani ba ko kina karatu?" Safiyya ta ce"Ina ɗan taɓawa amma ba sosai ba". Ramla ta ce"Kin san wata marubuciya sunanta Surayya Dee, wacce ta yi littafin Halin yau, baƙar ta'ada, sabo da kaza da sauran su?" Safiyya ta ce"Tabbas na karanta halin yau, labarin ya yi ma'ana sosai". Ramla ta ce"To marubuciyar ce da muke gaisawa, ina ganin status ɗinta tana siyar da magunguna, ban taɓa bi ta kansu ba saboda tsoron maganin mata nake yi har ga Allah da kwata-kwata ba na amfani da shi, saboda yadda na ji ana cewa yana da illa, lokacin da na haifi ɗana na biyu, kamar da wasa na ce bari na gwada, muka yi magana ta haɗa min haɗin mai jego cikin farashi mai rahusa, na duƙufa ina ta amfani da su, kin san Allah Safiyya na sha mamakin yadda na ji sauyi a jikina sosai, na taƙaice miki labari kayan matar nan ne suka kankaro min darajata a wajen miji, don ni dai kamar tsafi daga lokacin da na yi amfani da su shi kenan sai ka ce wacce na sha karya tambaya, tun kafin na faɗi buƙata yake ba ni, da na ji daɗi sai na sa ta haɗa min maganin sanyi, ni da cewa nake ba ni da sanyi, ta ce na daure na sha na rigakafi, sai da na sha na san ashe sanyi dai yana danƙare a marata, wallahi kafin na gama amfani da shi wasai na ji marata babu nauyin komai, na sanwa maƙotana biyu da muke mutunci, suka rikice suka ce na siyo musu daga nan duk wacce na sanwa sai ta dawo, sai kawai na fara sarar magungunan nan ina ta talla cikin ƴan'uwa, unguwa da status kafin shekara ta zagayo Safiyya Allah ne kaɗai ya san alkhairin da na tara, kullum handala nake yi kasuwanci yana ƙara haɓɓaka, da shi na tara jarin da na fara kasuwanci kala-kala, ni ce atamfofi kayan kitchen takalma, ke duk dai wani abu da kika san akwai shi a kasuwa ina siyarwa, kuma ina daga gida a zaune da wannan waya dai nake yin komai, ga shi yanzu Allah Ya dafa mini har aikin hajji na je da kuɗina, zan saka suturar da nake ra'ayi babu abin da nake jira miji ya yi mini, ni lafiya ƴaƴana lafiya". Safiyya ta jinjina kai ta ce"Allah mai yadda ya so, muma Allah Ya saka mu a danshinku!". Ta ce"Amin Ya Allah! Ai Safiyya yanzu ya zama dole na haɗa ki da Hajiya Surayya, don kuwa dila nake so ki zama kema bayan kin fara gyara naki jikin, kina da kishiya Safiyya ki zauna babu saiwowi? Kin san ita kalar wanda take yi? Saiwa ce ba ta da wata illa, ki fara gwadawa ki ji na san da kanki za ki sake nemanta, Allah dai ya sauke ki lafiya, in sha Allah ba za mu yarda ki koma ba sai kin zama babbar ƴar kasuwa". Safiyya ta yi dariya ta ce"To Allah Ya amince, ki ba ni lambarta sai na ga irin kayan tun yanzu". Ta faɗa tana ɗaukar wayarta. Ramla ta ce"Ki saka 08032773332 in sha Allah mijin nan naki sai ya dawo ya fuskanci alƙibla". Safiyya ta yi mata godiya sosai, ta shiga nuna mata kayan da take siyarwa a waya, kuma ta ce mata gobe za ta aiko mai adaidaitanta ya zo ya kai ta gidanta. Washegari sai Mama ta ce a'a gidan Anti Hajara za ta je, facalarta kenan ita ma matar yayan Umman Safiyya ce, haka kuwa aka yi aka kira ta a waya aka ce Safiyya za ta zo yau, Samira ce ta raka ta, tun daga ƙofa ta san shi Baba Safiyanu ya fi Baba Garba hali, don gida ne babba mai kyau, suna shiga matar ta tare su da murnarta, suka wuni tana jan Safiyya da fira, ƙarshe ta ce dole ta kwana tun da Baban nata sai dare zai dawo, da Baba ya dawo suka gaisa suka kuma sake jajanta maganar aurenta, don Baba Garba duk ya yi masa bayani, sosai ya ji tausayinta shi ma, don da har cewa ya yi sai ya kulle Salisu da matarsa, Baba Garba ya ce a bari sai lokacin da ya zo ƙafarsa sai a yi wacce za a yi ɗin, yanzu a bar ta ta haihu ta huta tukunna. Ita ma matarsa da ta ji ɓurɓushin maganar a bakin matar Baba Garba ƙaunar Safiyya da tausayinta ne suka kamata, ganin ashe ma ƙaramar yarinya ce ake wannan watangaririyar da ita, roƙon mijinta ta dinga yi a kan ya karɓi Safiyya ita za ta riƙe ta, to shi ma ya so hakan ya dai ce mata ta bar ta a inda ta sauka ɗin tun da Garban shi ne babba, amma zai tuntuɓe shi idan babu matsala sai ta dawo nan ɗin, washegari sai ga dogayen riguna kala uku ta ba wa Safiyya, ta kuma ba da atamfofi uku less biyu a yi mata ɗinki, duk a cikin kuɗinta ne, don ita hamshaƙiyar ƴar kasuwa ce daga gidanta, kuma iyayenta masu hali ne, ga ta da son mutane, ƴaƴanta biyu ne mata duka suna makaranta, daga ita sai mai taya ta aiki, shi yasa take son Safiyya ta zauna a nan ɗin, girke-girken kayan ƙwalama kala-kala ta dinga sakawa ana yi wa Safiyya don tana sha'awar ta ga mace da ciki, saboda tana ƙaunar haihuwar yara da yawa. Da yamma suka fita kasuwa da Safiyya ta ce ta ɗauki abubuwan da take buƙata, Safiyya ta kasa ɗaukar komai, sai ita ta tsaɓar mata duk abubuwan da take ganin za ta buƙata, ta siya mata irin saitin mayuka da sabulun da take shafawa masu kyau da fito da ainahin kalar fatar mutum, ta siya mata turaruka ta ce sauran kayan gyaran a bari sai ta haihu lafiya tukunna, suka dawo da kaya rigijib Safiyya tana ta godiya. Ko da ta yi mata zancen sana'a ta faɗa mata ba ta yin komai, amma ga yadda suka yi da Hajiya Ramla za ta fara da magungunan Hajiya Surayya ta gani, nan take ta karɓi lambar account ɗinta ta saka mata dubu ɗari kyauta don gani take a yadda mijinta yake sakar mata don ta yi wa ƴarsa hidima ba komai ba ne, ta ce mata ai bai kamata ta yi sanya ba, ta fara siyan kayan tun yanzu ta gani, kuma za ta tambayar mata jari a wajen babanta kafin nan ta sama mata sana'ar da za ta fara yi. Safiyya ta yi ta godiya, kuma a daren ta yi wa Hajiya Surayya magana, cikin wayewar kasuwanci suka yi ciniki ta sari kayan dubu ɗari, washegari aka aiko da kaya, a ranar ta turawa Salma hoton kaya ta yi mata bayani, sannan ta saka a status Salma ma ta saka, Anti Hajara ma ta tura a group ɗinta ta kuma tutturawa ƙawayenta, a ka fara siyan kaya babu ɓata lokaci. A ɓangaren Salisu bayan sun gama waya da Yaya Fa'iza mamaki ya yi sosai da jin maganganunta, a zuciyarsa yake ayyana ko zai saki Ameera ba dai yanzu ba, sai sun fara gano kalarta tukunna tun da su suka haɗa shi da ita, duk ta hargitsa masa gida. Washegari da sassafe ya tafi gidan Hajiya don da tunanin yaransa ya kwana, yana zuwa ya tarar ko buɗe gida ba su yi ba, ya bubbuga suka buɗe, ya tare su yana yi musu murmushi yana tambayar Hajiya, suka ce bacci take yi, ya kalli agogo ya ga bakwai saura minti biyar, ya shiga da sallama ya tarar Hajiya baccinta take ta shararawa, ba ya son tashinta saboda haka ya ce da yaran"Kun ci abinci?" Suka girgiza masa kai alamar a'a. Sai ya yi musu wanka ya shirya su, ya fita ya siyo musu shayi, biredi da ƙwai, da ya dawo ya tarar Hajiya ra farka tana ta fama da hura ice, ta saki baki ta ce"Kai ne da sassafen nan?" Ya ce"Yanzu Hajiya har na zo na yi musu wanka na shirya su kenan duk ba ki ji ba? Inda ɓarawon yara ne ma haka zai haɗa kansu ya tafi da su kenan". Hajiya ta ce"Oho! Ni na gansu da unifom zaune kamar an jera su na zata ma su da kansu suka shirya wallahi, biredi ka siyo? Ba ga tuwo ba zan yi ɗumame?" Ya ce"Hajiya yanzu kafin wutar nan ta maka ai sun yi latti, kuma kin ga fa suna tafiya da abinci yanzu yau sai dai su haƙura, ke kin ƙi a siyo miki gas". Ta ce"Allah Ya yi mini tsare, haka kawai ka siyo min ajalina ga abin da muka gada tun kaka da kakanni? Duk abin da gas ya yi ice ma zai yi". Ya wuce, ya ɗauki kofuna ya zuba musu shayin, kafin su gama karyawa har mai babur ɗinsu ya zo, haka suka tafi duk babu nutsuwa, sai daga baya ya sayi biskit da lemo ya kai musu, yana ta mita. Hajiya da ta yi ta zuba idon dawowar shi don ta faɗa masa yadda suka yi da sirikarsa ta ji shiru bai dawo ba, sai dare ya dawo ya siyowa yaran kwalin biskit da katan ɗin lemo wanda ya manta rabon da ya siyo musu, Hajiya ta tsare shi da zancen Ameera don yau mitin aka yi akan Ameera har da Mama Asabe wacce farin ciki ya lulluɓe ta da jin Salisu ya kaɗa duka matan nasa, Mariya ce ta dinga yi musu bayanin wulaƙancin da yake yi wa Safiyya wanda a da suka ƙi sauraronta sai yanzu da tauraruwar Ameera ta yi duhu, Fa'iza kuwa ta fi kowa hasala sai rantsuwa take kan sai ya sake ta ko ba ya so, don da shi aka so a yi zaman amma ya kashe wayoyinsa duka. Salis bayan ya gama sauraron Hajiyar ya ce"Hajiya haƙuri za ku yi, ni ma wallahi haƙuri nake yi da ita, ai ban ce zan je bikonta ba, sai ta sha zaman gida tukunna, amma mutuwar aure ai ba ta taso ba". Hajiya ta ce"O'o! Ni dama ban ce ka sake ta ba ai, ko dan irin ƴaƴa maza da ta zo da shi ai a bar ta ta zauna, amma ni kam na bar rakiyarta har abada, babu ni babu ita kowa ya yi ta kansa kawai, yadda ban ce ka saki Safiyya ba ba zan ce ka sake ta ba ita ma, idan jikinka ya faɗa maka za ka san mafita". Bayan ya wanke wa yara unifom ya tafi gida yana ta tunani, har bacci ya fara ɗaukarsa ya ji ƙarar wayarsa ya ga baƙuwar lamba ce, ya ɗauka ya ji mace ce suka gaisa duk ya za ta abokan kasuwanci ne. Suwaiba da take ƙara kashe murya ta ce"Ya yarana suke?" Ya ce"Suna lafiya da wa nake magana?" Ta ce"Ƴar'uwarka ce, kuma mai tausayinka, na san yanzu haka kana kwance cike da kewa shi yasa na ce bari na taya ka fira". Salisu da mamaki ya ce"Baiwar Allah tafi kanki tsaye dai, daga ina? Me kuma kike so?" Don haushi ma ya fara ji saboda shi yanzu ba wata buduruwa da za ta ruɗe shi. Suwaiba ta ce"So nake ka ba ni dama na shigo cikin rayuwarka, ta yadda zan samu damar ba ka farin cikin da yake neman zame maka kallo daga nesa, so nake na fahimtar da kai matan biyu da kake aure ba mata ba ne, so nake na rungumi ƴaƴanka na ba su tarbiyya da gata irin wanda ya dace, so nake na sharewa mahaifiyarka hawaye na rashin dacen surukai, so nake na zama fitilar da za ta haske duhun da gidanka yake ciki!". Ta yi shiru tana sauraron amsar shi, shi kuwa kashe wayar ya yi yana ta jujjuya maganganunta, ita ma ba ta sake kira ba ta bar shi ya yi nazari tukunna. _I love you darling brother_. Ta tura masa saƙo, ta kwanta tana faɗin"Allah ya kai damo ga harawa. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/9, 3:58 PM] Sadiya Abdulrazak: *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan Kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *Nationwide delivery* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 Washegari Salis yana kunna wayarsa da saƙon Suwaiba ya fara cin karo, yau ma da wuri ya tashi ya tafi gidan Hajiya, yau ma shi ya shirya su Hajiya ta yi musu girkin da za su tafi da shi, tana ta mitar an kawo mata aiki da tuni koko za ta siyo ta sha, don haka Salisu ya yi cefane kullum da sassafe yake tashi ya dafa musu abinci ya zuba musu a kula ya kuma zuba musu wanda za su karya da shi, a dole ya ƙara ɗinka musu unifom saboda ya gaji da wankin dare kullum, ga tausayin yaran da yake yi, saboda sun ƙi sakewa kullum a takure yake ganinsu. Ameera ta sha kiransa ba ya ɗauka, ƙarshe ma ya saka ta a black list don ba yanzu zai waiwaye ta ba, kamar yadda yake jin Safiyya ma ba ta isa ya neme ta ba, sai kuma yarinyar da take neman takura masa da kira a waya, idan bai ɗauka ba ta dame shi da tex, watarana yana kasuwa sai ga yaro ya kawo masa abinci a kula wai inji Sweet sister kamar yadda ta sakawa kanta suna, abokan shi ne suka hana ya mayar da abincin sai dai shi ko cokali ɗaya bai yi ba, su ne suka cinye, tun daga ranar kullum sai Suwaiba ta aiko masa abincin da take gwamutsa shi da barbaɗe da ƙulle- ƙulle kashi-kashi, wanda har sun fara mamakin yadda lamarin soyayyar tasu babu canji, don ta yarda da aikin Malaminta, kuma ya yi mata aiki akan Salisun dai ya kama shi amma yanzu abun ya ƙi har ta fara shawarar ko a canza na abincin, dama don dai Malamin ya ce na abincin ne sharp-sharp. Wani abokin Salisu me shegen son banza ganin irin garar da kullum buduruwa take aikowa kuma babu alamun Salis ɗin ya damu da ita, sai ya ce don Allah idan ba ya sonta shi ya yi masa hanya, zai je ba tare da nuna ya san Salis ɗin ba su daidaita da ita, sai a lokacin Salisun ya nemi ganin Suwaibar, wacce babu wata kwana-kwana ta ce kwatanta masa gidan maƙotansu, don kar ya yi saurin gano ta, niyyarsa ya je su fahimci juna ya faɗa mata shi babu wata soyayya a gabansa ballantana ƙarin aure ta yi haƙuri ta nemi wani, amma yana zuwa babu zato kawai sai ya ga ƙanwarsa Suwaiba, shi har yana cewa idan sun gama da Sweet sister ɗin zai shiga gidan Mama Asaben to ashe ma ƴarta ce Sweet ɗin, Suwaiba irin yaran nan ne masu shegen rawar kai, sam ba ta da nutsuwar da zai ma kalle ta, shi yasa ransa ya ɓaci sosai da ya ga ashe ita ce take yi masa wasa da hankali har ta saka shi tasowa takanas ya zo wajenta, masifa sosai ya yi ta zazzaga mata kamar zai kai mata duka, sannan ya ƙarasa gidan Maman don ya kai ƙararta, Mama shiru ta yi bayan Salisu ya gama baloƙoƙonsa na cewar Suwaiba ta raina shi, a yi mata gargaɗi, kuma a kula da tarbiyyarta. Mama ta ce"Kai yanzu Salisu kenan ba za ka iya son jininka ba? Ka auri bare ma har biyu ballantana ƴar'uwarka? Mene ne aibu don ka auri Suwaiba? Ai ita hankali ta yi ta ga matan naka duk ba ka yi dace ba, ga ƴaƴanka a tagayyare, shi ne fa ta tausaya". Salis ya ɓata rai ya ce"Mama ni fa ƴaƴana ba a tagayyare suke ba, suna cikin aminci, kuma taimakonta ta riƙe ba na so, ni ban ƙi ta ba, amma babu wani aure da zan yi yanzu". Bai ma jira cewarta ba ya fice daga gidan ransa a ɓace. Da ya zo gidan Hajiya yana ta fushi, ta tambaye shi dalili ya ƙi faɗa mata, daga ranar ya saka lambar Suwaiba a black list, sannan ya haɗa ta da abokin nasa. Kuma a cikin satin zance ya famtsama har ya iso kunnen Hajiya wai ƙanwarta Asabe ta ce ko za ta yi yawo da zani ɗaya sai Suwaiba ta shiga gidan Salisu matsayin matarsa, sosai hankalin Hajiya ya tashi, saboda ta san wace Asabe, kuma ƴarta sam ba ta da halin da za ta so ɗanta ya aure ta, saboda ta lalata mata tarbiyya da gata tun tana yarinya, dalilin mutuwar aurenta kenan ma. Wanke ƙafa Hajiya ta yi ta tafi har gidan ta same ta, sosai ta nuna ɓacin ranta da jin wannan maganar, kuma ta yi mata kyakkyawan gargaɗi a kan ko me ya samu ɗanta ita ce, sannan ta faɗa mata ko sama da ƙasa za ta haɗe Salis ba zai auri Suwaiba ba, haka ta bar gidan ranta babu daɗi. Da daddare da ya zo ta faɗa masa yadda aka yi, ya nuna kamar bai sani ba, ya ce Allah Ya kyauta, duk da haka Hajiya ba ta samu nutsuwa ba dai, sai da ta je islamiyyar layinsu suka gaisa da Malamin ta faɗa masa ɗanta take nemawa maganin karya sihiri, Malam ya nemi ganin Salisun, wanda da ƙyar ya je saboda ya dage a kan shi babu wani boka da ya isa ya yi masa wani sihirin da zai kama shi, a cewarsa sihiri ba ya zama a jikinsa. A dole ya je ya bada kuɗi saboda kar Hajiya ta ƙullace shi, aka haɗa masa magungunan masu kyau da tsarki, tare da ba shi addu'o'in da zai dinga yi safe da yamma, da kuma ba shi shawara a kan sallar dare, a gidan Hajiya aka ajiye maganin, kullum a gabanta yake sha, ya kuma riƙe addu'o'in yana yi, haka ma yakan yanke lokaci cikin dare ko raka'a biyu ce ya yi, ya yi addu'a. Satin Safiyya ɗaya a gidan ta koma gidan Baba Garba, bayan baban nata ya ba ta jarin kuɗi har miliyan ɗaya, ta huta na kwana biyu sannan ta ci gaba da zaga dangi cike da jin daɗi, a gidan wata ƙanwarta da ta je ta nuna mata ita kuma sana'ar da take yi, na harhaɗa sabulai, dulka, da kayan gyaran jiki masu kyau sosai, don kalar fatarta ce ma ta sanar da Safiyya lallai kayan masu kyau ne, a ranar a gabanta ta haɗa komai abun ya ba wa Safiyya sha'awa ta ce za ta gwada ita ma, ta ba da kuɗi aka siyo mata kayan haɗi, bayan an kwana biyu ta je gidan ta koya mata, aka yi package ɗin abun da steaker mai haɗe da sunanta, ta tutturawa Salma har ta nunawa Yaya Aminu suna ta taya Safiyya murna, maganin da ta sara a wajen Hajiya Surayya cikin sati ɗaya ya ƙare ana ta nema, nan ta saro wani mai yawa, ta haɗa da kayan gyaran jiki tana ta tallatawa abokan arziƙi suna taya ta, a cikin wata ɗaya sai ga Safiyya ta samu alkairi mai yawa, don kuwa kayanta duk wanda ya siya sai ya dawo, kuma sai ya ba wa wasu labari, Mama da ta ba ta shawarar ta ci gaba da bussines ɗin atamfofin ma, har Mama Hajara ta ce za ta haɗa ta da wani a nan Kanon kantin kwari, ta ce ta bar shi ai tana da wasu ƴan kasuwar, sabon layi ta siya ta saita whatsApp da shi, ta yi wa Salis magana a kan za ta dinga sarin kaya, suka daidaita kuwa babu wani jira ta fara siyan kaya yana aiko mata har Gombe, ba tare da sanin matarsa ba ce, gani ta yi da ta yi wa wani ciniki gara ta yi masa, tun da ko da rabuwa suka yi ai shi uban ƴaƴanta ne, idan ya ƙaru kamar ƴaƴanta ne suka ƙaru, sauran kayayyakin da take siyarwar ma ta ci gaba da yi, Allah Ya buɗe mata kasuwa sai ciniki take yi tana ƙirga ribarta, a yanzu ta rage damuwa sosai saboda yadda ta fara shiga busy na yawan tattaunawa da ma su siyan kaya, ga kuma aikin haɗa kayan gyaran jiki da take yi, ita kanta ta ga kyaun sabulun a jikinta, ta murje sai ƙara haske take yi. Suna waya da Baba wanda har yau bai san ƴar tasa ta yi nisa da gari ba, ballantana ya san duniyar da take da yadda ta samu sauyin rayuwa. Bayan wata biyu. Tun da Salis ya fara amfani da magungunan nan ya ji salama tana sauka a zuciya da gangar jikinsa, shi kansa ya san nutsuwarsa ta dawo duk da ba duka ba, saboda zamansa shi kaɗai a gida babu matansa, ga kuma hidimar yaransa, wanda shi ne girkinsu shi ne wankin kayansu, kitso ma sai ya ce a kai su ake kai su, yana jin tausayin su sosai, don haka ma ya fara tunanin ya kamata ya sama musu farin ciki ta hanyar dawo musu da mahaifiyar su, shi sai yanzu da ya nutsu ma sannan yake ta tuna irin abubuwan da ya dinga yi wa Safiyyar daga kan wanda ba yin kansa ba ne, har wanda yana sane yake yi da kuma wanda ya yi ta sanadin Ameera, ya ji a ransa dole shi zai haƙura ya neme ta kamar yadda Aminu ya ce, sai dai fa Aminu bai isa ya je ya ba shi haƙuri ya roƙi Safiyya ta dawo ba. Da daddare ya je gidan Hajiya ya ja yaransa gefe suna yin home work, Hajiya tana gefe kwance tana jin radio, bayan sun gama ya ɗauki waya ya nemo lambar Safiyya ya kira ta, lokacin tana kwance tana hutawa kiransa ya shigo wayar, ta yi mamakin ganin shi ne mai kiran, ta sauke ajiyar zuciya ta ɗauki wayar don tana son jin dalilin kiran. Da muryarta mara hayaniya ta yi sallama, shi ma ajiyar zuciyar ya sauke, yana jin ya yi kewar muryarta, ya yi kewar ganin Safiyya da taurin kanta sosai, ya amsa yana cewa"Safiyya ya kike, ya gari?" Safiyya ta ce"Ya gari sai kace wata ma'aikaciyar duba-gari? Ya gida dai ko Malam?" Salis ya ce"Hmm! Safiyya kenan, to ai gida a wajenki indai ya wuce nawa to kamar kin shiga gari ne". Ta ce"Ikon Allah! Wai da wa nake magana ne, kai kuwa daga ina haka har kake zancen zan shiga gidanka?" Salisu ya yi dariya ya ce"Haba Safiyya, ai ko mutuwa kika yi kika dawo ba za ki manta lambata ba, ballantana kuma muryata, kin tafi kin bar mu da kewarki ko? Kin ga yaranki nan home work muka gama". Safiyya ta ce"Bawan Allah ina ga fa ka yi wrong number ne". Ta katse wayar, ta ajiye tana murmushi da ta tuna ƴaƴanta, ya sake kira ta ƙi ɗauka sai ta kashe wayar ma duka, ya kalli yaran ya ce"Mamanku ce fa, kun ji wai ba ta san ni ba ma" Ya faɗa yana murmushi. Ni'ima ta ce"Don Allah gobe ka kai mu". Ya ce"Ku bari sai ranar Juma'a, zan kai ku sai ku kwana biyu ma ranar Lahadi na zo na ɗauke ku, kafin ta gama ja min aji ra dawo ko?" Suka gyaɗa masa kai suna ta murna, sannan ya kira Baban Safiyya suka gaisa lafiya lau, yana tambayarsa ya yaran? Don a ranar ma sun yi waya da Safiyya shi yasa bai tambaye ta ba, Salisu jikinsa ya ƙara sanyi da ya ga Baba ko zancen Safiyya bai yi masa ba, hakan ya tabbatar masa wannan karon ma Baba ya yi fushi, idan kuwa haka ne Allah ne kawai zai fitar da shi, shi ne fatansa kada Allah Ya nuna masa ranar da zai roƙi alfarmar Aminun. "Ameera!" Umma ce tsaye a tsakar gida tana shirin fita ta ke ƙwallawa Ameera kira, ta yi juyi tana tsaki, don baccin sam bai ishe ta ba, ta tashi ta fito tana amsawa, Umma ta ce"Wannan wane irin bacci ne kike yi, ga wanke-wanke ƙuda har ya fara bi, ni ina ga sai azhar ma zan dawo idan kin gama gyara gidan ki ɗora abincin da wuri don Allah". Har za ta fice Ameera ta ce"Ina abin karinmu?" Ta ce"Koko ne na siyo ɗanki ya kusa shanye nakin, ga nera hamsin nan ita ta rage min kya je ki siyo". Ta jefo mata hamsin ta fice tana ta sauri. Zama Ameera ta yi a dokin ƙofa sai zumɓura baki take yi tana haɗe gida, sosai ta gaji da zaman gidan don dai ba ta da yadda za ta yi ne, Umma ta tatike kuɗin hannunta tass, yanzu ko omo ita take siya musu bayan ta gama yi mata mita, tun da aka yi auren Nabila ita ce take wanke-wanke da duk aikin gidan, ga aikin abincin siyarwa wanda suke yin kwano huɗu a siyar da rabi a gida, almajiri ya fita da rabin, da Umma cewa ma ta yi ita ta dinga fita da shi, saboda ganin Ameera take kamar ma mara aure, don ita kam ba ta son ta koma ta fi son ya sake ta, ko wajen tallan abincin ma ai tsaf za ta samu wanda ya fi shi, tun da ga shi dai wanda Nabila ta aura da rufin asirinsa kuma wajen tallan suka haɗu. Ameera ta yi kiran Salis har ta gaji ta bari, don da ya saka ta a black list aron waya ta koma tana kiransa, da ya ji muryarta sai ya katse, a ganinta ko don ɗansa ai ya kamata a ce ya zo ganinta, haka aka ci bikin ƙanwarta aka cinye bai zo ko ɗaurin aure ba, ballantana ta saka ran zai ba ta gudunmawar, ga shi gari ya ɗauka ya basu dubu hansin gudunmawa, wasu masharrantan ma cewa suke har kayan ɗakin ma shi ne ya yi, haka dai Ameera take ta wannan rayuwar cike da ƙunci da kewar gidanta da mijinta. Ranar Juma'a da yamma ya shirya yaran tsaf, da kayansu kala biyu, tare da yi wa Safiyya siyayyar kayan ƙwalamar da ya san tana so, zuciyarsa cike da farin ciki saboda yau zai farantawa yaran, kuma shi ma zai ganta, idan ya yi sa'a ma Baba ya ce ta wuce su tafi. A ƙofar gidan ya tsaya ya tura su ciki da ledoji ya ce su ce ta zo idan sun shiga, Umma da ke yin tuwon dare ta tari yaran da fara'a, tana jiran shigowar Safiyya, yayinda su kuma suke rarraba idon ta inda za su ga uwar tasu. Umma ta ce"Ku zo ku zauna mana, ina Safiyyan ta tsaya?" Sai suka kalli juna, Khausar ta tashi ta nufi ɗaki don ta yi zaton tana ciki, Ni'ima ta bi ta, sai suka yi turus ganin dai babu alamarta a gidan, Umma ta ce"Ku ina Safiyyar ko shi ya kawo ku?" Suka gyaɗa mata kai. Sai ta saka hijjabi ta leƙa wajen, ta hango shi tsaye yana waya, ya kashe wayar ya ƙaraso ya gaishe ta, ta amsa tana cewa"Ashe kai ne ka kawo su". Ya sosa kai ya ce"Ni ne wallahi Umma, dama na ce wai su zo su ɗan kwana biyu". Umma ta ce"Madallah! Ai kuwa ka kyauta na samu ƴan tayin fira, to sai anjima ka gaida Safiyyar". Salis ya ji kalmar ka gaida Safiyya ta yi masa amsa kuwwa a kunnensa, kafin ya gama tantance abin da take nufi ya ga za ta shige gidan. Da sauri ya ce"Umma, Umma Safiyya ba ta ciki ne?" Umma ta ce"Ikon Allah! Ta ce maka ta taho nan ne?" Ƙirjinsa na bugu ya ce"Ai Safiyya wata biyu kenan ba ta gidana, to kenan tana gidan Aminu". Umma da mamaki ya kama ta, don ba ta taɓa jin wannan labari ba ta ce"Safiyya ba ta gidanka? Kuma har wata biyu? Anya kuwa tana gidan Aminu? Gaskiya ban san an yi ba, sai dai na tambayi Babanta wataƙil an ɓoye mini ne, ka shigo ciki mu ji". Salis ya shigo jiki a mace, yana ayyana kenan Aminu gidansa ya kaita kuma har wannan lokacin babu wanda ya sani. A gabansa Umma ta ɗaga waya ta kira Baba, wanda shi ma nan take ya shiga matuƙar mamaki, bai wani ji tsoro ba tun da suna waya yana jinta lafiya ƙalau, sai dai ransa ya ɓaci da jin wai watanta biyu ba ta ɗakin mijinta, don haka nan take ya baro kasuwa yana hanya ya saka kiran lambar Aminu. Aminu shi ba ya garin ma a lokacin, Baba ya kira shi bayan sun gaisa yake tambayarsa ina Safiyya? Aminu a zuciyarsa ya ce 'an zo wurin kenan'. Aminu ya ce"Safiyya tana nan mana Baba ba kwa yin waya ne? Ni kuwa ɗazu ma ta kira ni". Baba ya ce"Mijinta ya zo yanzu haka yana gida, ya zo da zancen wai ba ta gidansa har tsawon wata biyu, kuma ga yara suna wajenshi". Aminu ya ɗauki salati ya dire sannan a fusace ya ce"Baba wannan ai rainawa mutane hankali zai yi, ga shi ni ba na garin, ta ya zai ce Safiyya ba ta gidansa alhalin muna waya da ita? Ko dai zuƙe-zuƙe ya fara yi?" Baba ya ce"Ni ma dai shi na gani, amma bari na je gidan na ji". Suka ajiye waya. Baba yana zuwa gida Salis ya yi masa bayanin duk yadda aka yi har Safiyya ta bar gidan, da kuma yadda yake zargin tana gidan Aminu, Baba ya ce"Tabbas Aminu shaƙiyyin yaro ne zai aikata" Nan take ya yi wa Umma umarnin su tafi da Salis gidan Aminu a taho da Safiyya yanzun nan. Suka tafi, inda suka ga wayam babu alamarta, Salma ta faɗa musu rabon Safiyya da zuwa gidanta wata biyu kenan, tun a gidan Salis ya kira layinta ya ji a kashe, wanda Aminu ne suna gama waya da Baba ya kira ta ya faɗa mata ya ce ta kashe wayarta, kamar yadda shi ma ya kashe tasa wayar. Haka Baba ya ce da Salis ya tafi zuwa gobe su samu layin Safiyyar a san yadda za a yi, haka ya bar gidan jikinsa duka a mace. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/11, 9:15 PM] Sadiya Abdulrazak: *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan Kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *Nationwide delivery* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 Salis har dare yana kiran layin Safiyya a kashe, haka ya kwana da tunani barkatai, to Baba ma bai samu Aminun ba ballantana ita, har sai ranar Lahadi da Aminun ya yiwa iyayen nasu na Gombe bayani, suka kira Baba a waya duk suka yi masa bayani, Baba ya ce ai dama zaman aure ɗan haƙuri ne, suka nuna masa sam ba za su yarda Safiyya ta koma ba tare da mijinta ya shiga taitayinsa ba, da Salis ɗin ya zo ɗaukar yaran Baba yake yi masa bayanin duk yadda aka yi, shi ma kuma ya nuna masa ɓacin ransa sosai na yadda yake abubuwan da suke nuna bai fi ƙarfin gidansa ba, ya yi masa nasiha sosai sannan ya faɗa masa shi ba zai ce zai karɓo Safiyya daga dangin babarta ba, saboda haka wannan yaƙin nashi ne, idan suka daidaita da Safiyya babu mai hana ta dawowa. Shiru ya yi yana jin damuwa sosai da kuma haushin Ameera, kafin ya yi wa Baban bayanin ai ya ɗauki mataki, ita ma Ameerar tana gidansu ko waiwayenta bai yi ba, saboda yadda ya ji zafin abin da ta aikata, a maimakon ya ga Baban ya ji daɗi saboda ya yi hukunci don ƴarsa, sai ya ga saɓanin hakan, Baba ya ce masa ba ta haka ya kamata ya yi hukunci ba, ya ce masa yana roƙonsa alfarma ya je ya dawo da matarsa ɗakinta ko da sakinta ya yi ma ya haƙura ya dawo da ita ko don ɗan dake tsakaninsu, Salis ya ce in sha Allah za a yi hakan, ya karɓi lambar ƴan Gomben ya haɗa kan ƴaƴansa wanda ba ma daɗin zaman kwana biyun suka ji ba, suka tafi, tausayin yaran yake yi jikinsu duk ya yi sanyi, ba su da kazar-kazar. Da ya yi wa Hajiya bayanin yadda aka yi, taɓe baki kawai ta yi ta ce"Wannan kai ta shafa, sai ka tafi Gomben ai ka ajiye kasuwa a gefe, idan ka ɓalɓalta jarin babu shegiyar da za ta zauna da kai ai, duk ta kansu za su yi". Salis ya ce"Haba Hajiya don Allah! Wai ni me yasa sam ba kya son Safiyya? Ke yanzu kin fi so ki ta ganina ina rayuwa a haka babu mata? Kuma idan ta dawo ta ɗauki yaranta ke ma ai kin ga an rage miki aiki". Hajiya ta ce"O'o! Ni fa ban ce kar ta dawo ba, ka dawo da matanka jiki magayi!". Da daddare ya kira layin Safiyya ta shiga amma ba ta ɗagawa, sai ya kira layin da ya karɓa na Baba Garba suka gaisa, ya yi masa bayani mijin Safiyya ne, Baba ya ce"To ma sha Allah! Ya yaran suke?" Salis ya ce"Suna lafiya Baba, dama haƙuri na kira na ba ku, don Allah a yi haƙuri wallahi duk tsautsayi ne, tun da na ƙara auren nan dai shi kenan zaman namu ya canza, amma yanzu komai ya wuce zan gyara". Baba ya ce"Malam Salisu maza nawa ne suke ƙara auren kuma a ji gida shiru? Kawai dai ba ka da tsari tun farko, inda ka tsara gidanka to za ka fi ƙarfin gidanka, ba ka da ilimin zama da mace fiye da ɗaya shi yasa duk ka samu wannan matsalar". Salis ya ce"E wallahi Baba duk laifi nane, amma in sha Allah ba zai sake faruwa ba". Baba ya ce"To Allah Ya rufa asiri sai anjima". Da sauri Salis ya ce"A Baba dama ina ta kiranta ba ta ɗagawa, so nake na ji yaushe zan zo mu tafi?" Baba ya ce"Wannan tsakaninku ne, amma zancen tafiya ma ai bai taso ba tukuna, ya ga dai ta yi nauyi, sai mu bari ta sauka lafiya tukunna, sannan muhallin da za ta zauna ma ka ga sai ka san yadda za ka yi, tun da matarka ta ɓata mata suna a wancen gidan da take zaune, shi kuma nakan ta ce ƙadangaru take gani, ka ga duk ba wajen zama ba ne". Salis ya yi ajiyar zuciya ya ce"To Baba zan nema in sha Allah na gode". Suka yi sallama Shiru Salis ya yi yana tunanin mafita, ta ma ƙi ɗaukar wayarsa ballantana ya san ta inda zai fara, bayan kwana biyu kawai sai ya yanke shawarar tafiya Gomben, ya faɗa wa Baba ya yi masa kwatance, sai a ranar da zai zo ɗin Baba ya faɗawa Safiyya, sai ta ji duk ta shiga damuwa, don gani take za a ce ta bi shi su tafi, ita kuwa sam ba ta shirya ba, don sosai take jin daɗin zaman gidan babu mai yi mata hayaniya ballantana hankalinta ya tashi, har sai da Mama ta lura da yadda yanayinta ya canza, ta faɗa mata ta kwantar da hankalinta Babanta ya ce sai ta haihu za ta koma, sannan ta ji daɗi ta ɗan saki jikinta, har ta fito ta taya ta aikin abinci. Ana sallar azhar Salis ya shiga Gombe, saboda haka a masallacin unguwar ya tsaya ya yi sallah, sannan ya kira Baba ya faɗa masa ya ƙaraso unguwar, Baba ya da yake kasuwa ya kira Mama ya faɗi inda Salis ya tsaya ya ce a je a taho da shi gidan. Fitowar Safiyya daga wanka kenan tana shafa mai Mama ta shigo ta faɗa mata ta je ta taho da shi, kamar za ta yi kuka ta ce"Kin ga Mama kaya zan saka, kuma har na yi alwala ban yi sallah ba, Samira ta je". Mama ta yi murmushi, ta sa Samira ta shigo da shi, Mama ce ta sauke shi a ɗakin baƙi ta kawo masa kayan ruwa da abinci suka gaisa ta fita, shi dai yana ta raba idon ta inda zai ga ta taho ya ji shiru, ta idar da sallar tana zaune a sallayar tana kallon wayarta da take a silent sai kiranta yake yi babu ƙaƙƙautawa, ta ƙi ɗauka, har sai da ta ji shigowar Baba gidan sannan ta ga ya daina kiran. A tsanake suka gaisa da Baban, wanda ya yi masa bayanin duk matsalolin da Safiyya ta faɗa, bai musa ba saboda ba ƙarya ta yi masa ba, shi ko ta yi ƙaryar ma zai amsa indai za ta dawo ɗin su huta shi da ƴaƴansa da wannan jula-jular, shi bai san ma watannin cikin nata ba, sai yanzu ake faɗa masa a watan haihuwarta take, baƙinciki ya cika zuciyarsa, ya rasa me ya same shi ya yi wa Safiyya ruƙon sakainar kashi, shi kansa daga baya idan ya tuna wani abun da ya yi mata har haushin kansa yake ji, kuma duk Ameera yake ɗorawa laifi, saboda aurenta ne ya ja musu duk wata matsalar da suke fuskanta da Safiyya. Sai da Baba ya ce ta je ta gaishe shi sannan ta tashi, ta yafa ɗankwalin doguwar rigar dake jikinta mai faɗi, waɗanda su ne suke yi mata daɗin sakawa a yanzun, ƙamshin kayan gyaran jikin da take mulke jikinta kullum wanda ya riga ya gama ratsa ta ya haɗu da ƙamshin humrar da take amfani da ita mai sanyi da daɗi, sun ba da wani irin yanayi mai daɗin shaƙa, fuskarta wasai babu kwalliyar komai, don ko hoda ba ta shafa ba, amma kyaun da fatarta ta yi da hasken da ta ƙara tana wani yellow ya fito da kyaunta sosai, ta kuma yi ƙiba daidai misali kamar ba ita ba, fuskarta babu yabo babu fallasa ta yi sallama ta shiga ɗakin, wanda tun kafin ta shigo ƙamshinta ya kiɗima shi saboda ta yi sakanni a bakin ƙofar tana ƙoƙarin saita kanta, ba ta so ta nuna masa tana fushi da shi, haka ba ta so ya ga fuskarta babu walwala ya yi zaton cikin ƙunci take. Da sauri ya amsa sallamar, yana bin ta da kallo, musamman ƙaton cikinta da ya ba shi mamaki, ya kuma ƙara jin bai yi mata adalci ba tare da jin tausayinta, tana cikin halin da take buƙatar kulawarsa, amma ga shi suna mabanbamtan muhalli, ta nemi waje ta zauna a gefe ta miƙe ƙafarta da suka fara kumbura duk da tana tattakawa a tsakar gida, tana kallonsa ta ga ya ƙure ta da kallo, ta juyar da kai gefe tana gaishe shi. Ya sauke ajiyar zuciya, yana jin wata nutsuwa a zuciyarsa, ƙaunarta tun ta asalin nan ta Yaya da Ƙanwarsa yake ji a yau ɗin, ita ce dai Safiyyarsa, matarsa uwar ƴaƴansa, ƴar ƙanwarsa, amma cikin wata biyu da bai ganta ba ya ga ta ƙara kyau da nutsuwa sosai. "Lafiya ƙalau, ya jiki-jiki?" Ya faɗa har lokacin yana kallonta. Ita kuma ba ta juyo ba, ta ce"Ni ƙalau nake". Ya yi murmushi ya ce"A da sauƙi dai ko?" Suka yi shiru na ɗan lokaci, ita tana ta kallon screen ɗin wayarta, mai ɗauke da hoton fuskarta ne, shi kuma yana ta kallonta ya rasa ta ina zai fara, ya so a ce sun gama daidaitawa tun a waya, yanzu ɗaukarta kawai ya zo yi su tafi. Can dai ya ce"Ki yi haƙuri Safiyya, ashe cikinki har ya tsufa haka". Ta ce"Ya ƴaƴana, suke?" Ya ce"Ƴaƴanki suna nan lafiya ƙalau, sai dai kewarki tana neman nakasa su, saboda sam ba su da walwala, har yau sun kasa sakewa da gidan Hajiya, sun kasa sabawa da rashinki, ko ma dai na ce mun kasa jurewa ni da su ɗin". Ta ce"Su ɗin dai! Amma ni wace da za ka kasa jurewa don na yi nesa da kai?" Ya marairaice ya ce"Wallahi kuwa Safiyya ba ki ji yadda duk na damu ba, don Allah ki haƙura mu tafi yau ɗin, ba na so na koma hannu Rabbana". Safiyya ta ce"Ni ce fa, ni ce fa wacce kake ɗauke kwanana ka kai wa matarka matar so wacce ta fi ni, ka manta lokacin da ka ƙaurace mini? Tsawon wata nawa ka yi babu ni, alhalin muna kusa da juna, don yanzu ka yi wata biyu babu ni ka ce ka yi kewata na yarda?" Ta yi wani murmushi. Ya ce"Wallahi Safiyya da kin san yadda nake ji idan na tuna irin waɗan nan abubuwan da na yi miki da ba za ki sake tada zancen ba, na yi kuskure kuma ya kamata ki yi min adalci, tun da na aure ki na taɓa yi miki makamancin hakan...?" Ta katse shi da faɗin"A'a ba ka taɓa ba wallahi, sai da ka auro wacce ta fi ni". Ya ce"Babu wacce ta fi ki har gobe, kuma in sha Allah ba zan samu wacce ta fi ki ba Safiyya, komai da ya faru mu ɗauka jarabawa ce, saboda haka ki daure mu cinye wannan jarabawar, yanzu na dawo cikin hayyacina tun da na kama ibada, ki gwada ni ki gani Safiyya za mu zauna lafiya in sha Allah, kuma ma duk yadda kika tsara hakan zan dinga yi". Ta yi guntun murmushi ta ce"Kuma a hakan kake cewa za ka gyara? Ni ce zan tsara maka gidanka? Idan na ce da ni kaɗai za ka zauna ba na son kishiya ya za ka yi? Za ka bi tsarina?" Ya ce"Wallahi zan bi, matuƙar dai za ki riƙe mini Sauban, me zai hana na rabu da Ameera? Dama rabo ne ya sa ni na aure ta, yanzu haka ma tana gidansu fa tun ranar da kika tafi, kuma saboda wannan ƙazafi da ta yi miki ne fa na kore ta, har yau ban waiwaye ta ba, yanzu hakan bai nuna miki na san zafinki ba?" Ta taɓe baki ta ce"Wannan tsakaninku ne, ƙazafin da ta yi min kuma ni na bar ta da Allah, shi zai yi mini sakayya, ban ce ka rabu da ita ba, idan ma ka rabu da ita ba zan riƙe wannan yaron ba, ni na kai matsayin da zan riƙe Magajin gida? A dai bar ni da bororin gidan". Salis ya ce"Safiyya kenan, to mu dawo dai zancenmu ko? Yanzu kin yarda sai kin haihu a garin nan sannan ki koma? Ga ƴaƴanki abun tausayi, kullum kuka suke suna Ummansu". Ta ce"Idan mutuwa na yi ai haka za su yi kukan su bari, ai ko na haihu ba lallai na koma nan kusa ba". Ya ce"Haba dai, faɗa kike, yanzu faɗa min mene ne matsalarki da ni, me kike so na daina yi me zan gyara a halina?" Safiyya ta ce"To saurin me kake yi ne? Bari na sauka lafiya sai a yi komai a tsanake ai". Ya ce"A gaskiya sauri nake yi, haba Safiyya kin san dole na yi sauri ai, yanzu cikin watan nan za ki haihu? Wataƙil ma ko awo ba kya yi". Ta ce"Ina zuwa awo mana, EDD ɗina kuma ƙarshen wata ya nuna". Ya ce"To Allah Ya sauke ki lafiya, za dai a haifo min ɗan Gombe ko ƴar Gombe kenan, ikon Allah wato ita rayuwa kana taka Allah na tasa, ban ma taɓa zaton bayan na aure ki za mu yi rabuwar wata ɗaya ba, sai ga shi wai yau wata biyu ban ganki ba, kuma har sai kin ƙara wani wata ɗayan kin haihu sannan za ki dawo". Safiyya ta ce"Ka ma daina cewa wani wata ɗayan, saboda ni fa ba lallai na koma kwana kusa ba, ina ga ma sai ka yi ginin wannan filin, ka ware mini ɗakina da na ƴaƴana sai na koma a tsanake, tun da yanzu ba ni da wurin zama, don ba zan sake zuwa gidan haya ba, gidanka kuma na matarka ne". Ta faɗi hakan ne don Mama ta ce mata duk runtsi kar ta koma gidan haya, gidanta dai shi za ta haƙura ta koma ta zauna, kuma ta yi alƙawarin za ta bi maganarta. Salis ya ce"Haba Safiyya, gidan nan ai naki ne, ke ce kika yi niyyar barinsa, amma ko yau za ki koma ai babu matsaka gyara kawai za a sake yi miki". Safiyya ta ce"Ni kar ka sake cewa gidana ne, gidan da ka cire ni a ɗakunana, ka cusa mu a ɗaki ɗaya ni da yara biyu? Gidan da ka hana ni shiga ɗakinka saboda zargin ina yi maka sata?" Da damuwa a fuskarsa ya ce"Haba Safiyya ki daina dawo da bara bana don Allah, wannan duk ya wuce, ina roƙon ki yafe mini ba don halina ba, sai don ƙaunar dake tsakaninmu da kuma rausayin ƴaƴanki, kuma indai ɗakinki kike so sai ki koma, sai ta kwashe kayanta ki koma". Safiyya ta ce"Ni ban ce ba, ɗaki ɗayan da ka ba ni zan ci gaba da rayuwa a cikinsa duk wuya zan jure in sha Allah! Ba dan halinka ba sai dan ƴaƴanka". Ya washe baki ya ce"Na gode, kuma dama ai sai dai ki yi don yaran, zan gyara gidan in sha Allah, kuma zan yi ƙoƙari na fara wancen ginin ma, ki yi haƙuri kin ji". Haka ya dinga ba ta haƙuri da alƙawarin samun canji idan ta dawo, har ta haƙura, suka shiga firar yaushe gamo cike da kewar juna, ya kira Hajiya a waya ya haɗa ta da yaranta suka gaisa, wanda hakan ba komai ya ƙara musu ba sai damuwa saboda an fama musu ciwon rashinta, bai tafi ba sai da ya ga duk ya sauke fushin da take yi da shi, ya kuma ba ta kuɗi don zuwa awo da ƙananun abubuwa, sannan ta nuna masa kayan da take so ba Baby wanda za a buƙata kafin haihuwar, ya ce zai siya ya aiko mata, har yake faɗa mata akwai wata mata kuwa da yake aiko mata da kaya a Gomben, Safiyya ta yi murmushi kawai ba ta faɗa masa ita ce ba. Mama ta haɗawa su Ni'ima kayan ciye-ciye ta ba shi ya kai musu, haka ya tafi yana jin farin ciki, a zuciyarsa kuma yana taƙama da ayyana Aminu ya zo yau ya nuna masa Safiyya ta waye a tsakaninsu? LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/12, 3:19 PM] Sadiya Abdulrazak: *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan Kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *Nationwide delivery* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 Da farin ciki ya sauka gidan Hajiya, ya yi wa yaran albishir ɗin idan Umman su ta haihu za su je suna, kuma ita ma za ta dawo, nan yake faɗawa Hajiya a watan Safiyya za ta haihu, ta ce Allah Ya raba lafiya, babban abin da ya ƙara masa farin ciki da daddare yana shirin bacci sai ga tex ɗin Safiyyan tana yi masa ban gajiya, akuyar ɗaure fa ta samu saki nan take ya kira ta suka daɗe suna waya kafin ta ce bacci take ji, duk ta faɗa masa kasuwancin da ta fara yi, ya kuma yi addu'ar Allah Ya saka mata albarka, ranar sai duk suka yi bacci mai daɗi, don ba ta taɓa yarda ta yi kewarsa ba sai a yau ɗin da ya zo ta gan shi, ganinsa da kalamansa masu daɗi ya tuna mata rayuwarsu ta baya, kuma ya wanke laifukansa ta yafe masa duk abin da ya yi mata, dama ita ba ta daina son shi ba, sababbin halayensa ne na saurin fushi, rashin fahimta da rashin bincike su ne suke haɗa ta da shi, amma a yanzu ta ɗaura niyyar ƙwatar mijinta a wajen Ameera ta hanyoyi tsarkakakku wanda ba za ta ɗauki alhakin kowa ba, sharri da ta yi wa Ameera a baya kuma tana roƙon Allah Ya yafe mata, yanzu rayuwa ta nuna mata kissa kala-kala ce, kuma wacce ta yi da farko ta haramun ce, amma yanzu za fa fara ta halal, fatanta dai Allah Ya sauke ta lafiya. Tun daga ranar kullum sai sun sha waya da Salis haka ma sai ya haɗa ta da yaranta sun gaisa, wataran sukan gaisa da Hajiyar ma, wataran kuma idan ya ce ga Safiyya sai ta ce kar su dame ta, ta san tana son mijin da ƴaƴan ta tafi ta bar su za a wani dame su da waya? Cikin fira yake faɗa mata zai kamawa Ameera gidan haya, ita sai ta zaunaa gidantaita kaɗai, Safiyya ta ce ba ta yarda da haka ba, gara su zauna tare, ita ta tsara masa yadda za a yi, ɗakinta ne zai zama na Ameera, wanda dama can shi ya kamata a bata, ita kuma za ta koma beedroom ɗin Ameera wanda yake nata tun asali, sai ya fitar da ƙofa ta waje ya toshe ta cikin ya zama ɗakuna uku kenan a maimakon ciki da falo, shi wannan falon sai ya zama na kowa da kowa, ya yarda da wannan shawarar babu jira ya fara shirin gyara, sai ana gobe za a fara gyaran ya cire Ameera a black list ya kira ta, a lokacin tana zaune a tsakar gida, tana kallon Umma da ta matse Sauban tana yi masa ɗurar kunu sakamakon ƙin cin abinci da yake yi, saboda zazzaɓin da yake ta yi, Umman ta ƙi ba da kuɗi a kai shi asibiti sai maganin da ake siyo masa, zazzaɓin kuma sai gaba yake yi babu sauƙi, baran-baran suka yi da Umman akan kuɗin tarun ginin gidanta, don ƙarshe cewa ta yi ta fasa ginin a ba ta kuɗinta, Umma ta dinga bala'i kamar za ta ari baki, ta ce da shi aka haɗa aka fita kunyar auren ƙanwarta, kuma sannan zamanta a gidan ita da ɗanta ma nawa ta kashe musu? Har take cewa za ta nemi kuɗinta ta ba ta, ita kuma ta san inda dare ya yi mata, hakan ne ya sa ta nutsu ta kama kanta, ta kuma koma ga Allah tana ta addu'ar Allah Ya karkato mata da hankalin mijinta, don ta gane gidansa shi ne rufin asirinta. Kamar almara haka ta ga kiran, hannunta na karkarwa ƙirjinta yana bugawa ta ɗauki wayar ta tashi tsam ta shige ɗaki, ta ɗaga da sallama da ya amsa ta gaishe shi wanda rabon da ta gaishe shi tun farko-farkon da ya fara neman aurenta, kafin ya saki jiki ya mato a kan ƙaunarta, daga nan sai dai ya gaishe ta ita ga Baby shalelen miji, ya amsa gaisuwar babu yabo babu fallasa ya ce"Ya Sauban?" Kamar za ta yi kuka ta ce"Ga shi can ba shi da lafiya, ya daɗe yana zazzaɓi kuma ba a kai shi asibiti ba ma". Sai ya ji tausayi da kewar yaron sun kama shi lokaci ɗaya, ya ce"To me yasa ba ki faɗa min ba, ya za ki yi wasa da lafiyarsa?" A zuciyarta ta ce"Da uban me zan kai shi asibitin, ka damu da shi ne?" A yanzu sasanci take nema don haka ta ce"Kuɗin ne babu". Ya yi tsaki ya katse kiran ya tashi ya tafi gidan nasu, kiranta ya yi a waya ya faɗa mata yana ƙofar gida, sai ga ta ta fito da sauri tana kiciniyar saka hijjabi, Umma ta kalle ta sheƙeƙe ta ce"Ke kuma ina zuwa har da tuntuɓe?" Ta ce"Salis ne ya zo". Umma ta girgiza kai cike da takaici ta ce"Saboda haka kika bazamo har kina tuntuɓe? To ai kin manto akwatin". Ameera ta sunkuyar da kai ta ce"Ɗansa fa ya zo dubawa". Umma ta ce"E lallai yaron nan ya cika tantiri, wato ya zo duba ɗansa, ɗan da ya banzatar bai ko yi waiwayensa bai san cinsa ba bai san shansa ba, ballantana lafiyarsa, to ki ce masa ya shigo!". Ameera ta marairai ce ta ce"Umma don girman Allah ki yi haƙuri a bar zancen nan, don Allah ni na riga na yafe duk abin da ya yi mini wallahi". Umma ta ce"Amma wannan yarinya an yi sakarya! Lallai ɗan yau sai a bar shi kawai, to don ubanki ni ban yafe ciyar da ɗansa da na yi ba". Da sauri ta ce"To Umma ki yi haƙuri na koma ɗin, zan biya ki ko ma nawa ne". Ba ta jira cewarta ba ta fice. Yana tsaye yana waya, ta sunkuyar da kai har ya gama, sannan ya matso fuskarsa babu yabo babu fallasa suka gaisa, ya ce"Ina Sauban ɗin?" Ta ce"Yana ciki, ka shigo mana". Ya yamutse fuska ya ce"A'a fito da shi mu tafi asibitin kawai". Ta ce"To" Saboda ba ta son yi masa musu ta kwaɓe mata. Tana shiga ta ga Umma ta shiga banɗaki, sai Sauban dake kwance yana marayan kuka, ta ɗauke shi da sauri ta goge masa jikinsa da tsumma ta fito da shi da sauri, Salis yana kallon yanayin yaron ransa ya ɓaci, ya buga babur ya ce ta hau su tafi, a hanya yana ta yi mata faɗan me yasa ko aikowa ba ta yi an faɗa masa ba? Kuma kalli yadda ta bar shi haka ko wanka ba ta yi masa ba, ita dai ba ta da ta cewa, ita ba ta ƙi ma daga nan ɗin ya ce su wuce gida ba. Gado aka ba shi a asibitin saboda sai an saka masa ruwa don ya galabaita, ya biya kuɗin komai, ya ce zai je ya dawo, waje ya fita ya kira layin Hajiya, tun kafin ma ya faɗi dalilin kiran ta fara masifa "Kai kuma yau me ya hana ka zuwa ka shirya ƴaƴanka? Bacci ya yi min nauyi sai tashi na yi na ga rana ta yi, suke ce min mai babur ɗinsu ma ya zo har ya tafi, ga shi nan ai yau ka yi musu asarar karatun, suna zaune a gida!". Ransa ya ƙara ɓaci, ya ce"Haba Hajiya don Allah, ba ki ji uzurina ba kina ta faɗa..." Ta katse shi da faɗin"Yo wane uzuri naka na banza, kawai ka zo ka haɗa ni da aikin yara, na gama rainonku na yi na ƴaƴanku, gaskiya Salisu na gaji ka san yadda za ka yi ka dawo da matarka, yo wane wulaƙanci ne za su riƙe ta su ce sai ta haihu a can? Mu za a faɗawa gata, gatan banza da wofi wanda tana ƙuruciya da kashinta a ɗuwawu ba a nuna mata ba sai yanzu da ta zama mutum, gata ai kai ka yi mata, idan ma raba ku suke son yi sun yi na banza, tun da dai babu abin da wani shege zai faɗa maka a kan Safiyya!". Shiru ya yi sai da ta gama tsaf, sannan ya ce"To ki yi haƙuri Hajiya, kuma ma ai kamar yau ne za ta haihun, duk ba wannan ba ma, Sauban ne ba shi da lafiya muna asibiti duk ya galabaita". Ta yi gyatsine ta ce"Sauban ɗin ɗan waye?" Ya ce"Haba Hajiya, ɗana Sauban mana". Ta ce"Ni uwarsa nake tambaya". Ya daure ya ce"Ɗan Ameerarki ne mana". Hajiya ta ce"O'o! Allah Ya raba bawa da wahala, ni dai kar ka sake jona ni da ahalin ɓeraye, wallahi ban san wata Ameera take ko Nafisa, can ta matse maka". Ta kashe wayarta ta ajiye tana cewa"Ni me zai sake haɗa ni da yarinya mara tarbiyya kuma? Ta yi yamma na yi gabas". Sannan ta zubawa Kausar duka a baya da take wasan ruwa da buta ashe har ta jiƙe Hajiyar ba ta ji ba saboda tana masifa. Kausar ta matsa gefe ta fasa kuka, Hajiya ta ɗauki mafici ta jefa mata ta ce"Duk za ku ci ubanku, daga ku har uban naku, sai ka ce Salisu ne kaɗai ɗana shi da matansa da ƴaƴansa sun hana ni sakat!". Ɗakin ya koma ya ja kujera ya zauna, yana kallon yaron da yake bacci, ya kalli Ameera ta sunkuyar da kai, ya ce"Wai ɗana ne haka ko wanka ba ya samu!". Mitar ta fara isarta, ta kauda kai ta ce"Ta ya za a ƙi yi masa wanka? Kunu aka gama ba shi fa ka zo". Ya taɓe baki ya ce"Yanzu wannan rayuwar kika zaɓar muku ke da shi ɗin?" Murya a tausashe ta ce"Ai kai ne ka zaɓar mana, ka ce mu tafi sai ka neme ni, kuma ba ka neme ni ba tukunna ko?" Ya ce"Ai Ameera abin da kika yi ne idan na tuna har yau sai raina ya ɓaci, ta ya za ki ƙalawa matata sharrin maita? Ki zo ki same ta a gidanta da mijinta da ƴaƴanta amma kullum burinki ki muzguna mata! Tun ina biye miki har na gane ba ki da niyyar alkhairi akan Safiyya". Hawaye ya zubo mata ta ce"Ka yi haƙuri don Allah, in sha Allah ba zai sake faruwa ba, kuma ma zan je har gidan na ba ta haƙuri". Ya taɓe baki ya ce"Ita tana Gombe, sai ta haihu za ta dawo ma". Ta ce"Allah Ya sauke ta lafiya". Ya amsa da amin. Sannan ya ce"Akwai gyara da zan yi a gidan, ɗakunan da kike ciki za ki bar su ki koma ɗakin Safiyya, za a toshe ƙofar ciki a yi wata ta waje, falonki ya zama naku ku biyu". Ta ji maganar ta dake ta sosai, amma babu damar tijara, ta ce"Amma ta ya za mu haɗa falo mu biyu?" Ya haɗe gira ya ce"Ta yadda kuka haɗa miji ɗaya ku biyu! Ameera na ɗaura ɗamarar gyara gidana fa, saboda haka ke ko ita duk wanda ya kawo mini wargi gidansu zai koma da zama gabaɗaya, ban ga dalilin da zai sa ku yi ta gara ni ba, ni da gidana ban isa da ku ba, daga na ɗinke nan ku farke can, idan na yinƙura zan ɗauki mataki kuma ku fara tada aljanu, kodayake aljanu yanzu na san maganinsu!". Ya girgiza kai. Ameera ta ce"Shi kenan, ni dai ban ce komai ba, Allah Ya b mu zaman lafiya, amma kenan kujeruna su kowa zai ta dirza?" Ya ce"Babu wanda zai kashe miki kujeru, kiran da na yi miki ɗazu dama faɗa miki zan yi ki aiko a kwashe su, saboda yau na so fara aikin, sai kuma kika kawo min zancen rashin lafiya, ni zan sayi kujeru na zuba zan sayi kayan kallo da firji kowa ya mora". Ameera ta ce"To shi kenan, yaushe zan dawo kenan?" Ya ce"Da bari zan yi sai Safiyya za ta dawo, sai ku dawo tare, amma idan kin ga kin matsu idan na gama gyaran sai ki dawo". Ta ce"To zan dawo ɗin idan ka gama, ai bai kamata a tsaya jiranta, ita da za ta haihu ta shiga jego kuma, wataƙil ma sai ta yi arba'in za ta dawo, kana ta zaune babu mace a gidan, wai ya kake yi da abinci ma?" Ya ce"Wannan ai ke zan tambaya, kalli yadda ɗana ya rame, ke ma duk kin wane motse, wani irin kunu kike ba shi ma?" Ta ce"Na tsamiya ne ake siyo masa a maƙota". Ya yi tsaki ya ce"Allah Ya kyauta!". Kwanansa ɗaya aka sallame su, a hanya ya tsaya ya siyo musu kayan shayi, sannan ya ba ta dubu ashirin ya ce ta haɗa masa kunun gyaɗa ko na alkama, kar ta sake ba shi tsamiya a lalata masa cikin yaro, ita dai kawai binsa take yi da to, a zaure ta tsaya ta zare dubu goma ta maƙe a jikinta sannan ta yi sallama ta shiga, ƙaninta kawai ta tarar a gidan Umma ba ta nan, ta ji daɗin hakan sai ta juya ta shiga maƙota ta aiki wata yarinya kasuwa ta siyo mata kayan haɗin garin kunu, sannan ta dawo gidan, sai azhar Umma ta dawo, tun da ta hango ɗakinta a buɗe ta fara mamaki, ta yi zaton baƙi ta yi, ta shigo da sallama, Ameera ta amsa tana mazewa daga tsoron da take ji. Umma riƙe da labule ta ce"Wannan kuma fa? Me ya dawo dake, ko har ya ƙara koro ki? Yanzu ke Ameera har ni za uwarki za ki watsa wa ƙasa a ido ki rungume miji? Ai kuwa kar ki manta duk wacce ta ɗauki miji uba ta mutu marainiya, ni fa ban ce kar ki bi mijinki ba amma duk wani faɗi tashi da nake yi akan lamarin aurenki wallahi saboda na sama miki ƴanci ne, tun da ba kya so ai shi kenan!". Ta saki labulen ta baje a tsakar gida, tana cewa"Me kika dafa?" Ameera ta fito ta ce"Ban yi girki ba ai, a asibiti fa muka kwana Umma, ga wannan ya ce na yi wa Sauban kunu, har ma na yo cefanen" Ta miƙa mata sauran kuɗin da kayan shayin. Umma ta karɓi kuɗin tana rogon da ta siyo a hanya ta ce"Allah Ya amfana". Sannan Ameera ta faɗa mata duk yadda suka yi da shi, da gyaran gidan da za a yi. Umma ta ce"Ai idan zaure ma zai kai ki babu komai tun da kin ji kin gani, ni dai tun da ya raina ni ban kai ya shigo ya gaishe ni ba babu komai, ko ma mene ne ke ce kika ja min". Ameera ta ce"Umma ba haka ba ne, cewa ya yi fa kunyarki yake ji". Ta ce"Dalla rufe min baki!". Da yamma aka aika aka kwaso kujerunta, sauran kayan kuma aka shigar da su ɗakin gado, tun daga ranar kuma suke waya da Salis wataran ma yana zuwa ya gan su, shi kansa sai a yanzu ya ƙara samun nutsuwa da suka shirya da matan nasa, cikin satin Ameerar ta koma da rakiyar ƴan'uwanta wanda suka taya ta kwashe kaya ta mayar ɗakin Safiyya, falo kuma wayam yake babu komai don kulle shi ma ya yi, ya ce sai ya gama hidimar gabansa zai zuba kaya, zaman su lafiya lau don tana takatsantsan da ɓata masa rai. LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [6/13, 6:13 PM] Sadiya Abdulrazak: *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan Kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *Nationwide delivery* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 Satin Ameera uku da komawa Allah Ya sauki Safiyya lafiya, ta haifo ƴarta mace, washegari Salis ya je Gombe, can ya gano Safiyya da ƴarsa waɗanda suke cikin kulawa da gata ta ko'ina, ya yi mata huɗuba da sunan Mama wato Maryam, suna ce mata Ihsan, duk wani kuɗin da za a buƙata a asibiti dama ya riga ya bayar tun kafin haihuwar, da ya tambaye ta abin da suke buƙata ma ta ce komai akwai, saboda haka kuɗi kawai ya bata don ƙaro wa ƴar kaya da kuma nata ɗinkunan, ya tafi cike da kewarsu. Da ya faɗa wa Hajiya babu yabo babu fallasa ta yi masa barka, ya kira Safiyya a waya ta yi mata barka, Ameera ma ta karɓi lambar Safiyya a wajensa ta kira ta sun gaisa ta yi mata barka, ana gobe suna ya zauna da ƴan'uwan don ya ji su waye za su je suna? Duk suka ce ba za su je ba, sai Mariya ce ta ce za ta je, sai da Hajiya ta nusar da su muhimmancin zuwan nasu, saboda a gano yanayin da Safiyya take ciki sannan yayarsa Saude ta ce za ta je, sai suka tafi Saude, Mariya, su Ni'ima, Salma sai kuma Ameera wacce Salis ɗin ya ɓata rai ya ce ta shirya su tafi. Kuɗin ragon suna ma tura musu ya yi aka siya, sannan Baba ma ya yanka mata wani aka haɗa biyu, bayan ƙaurin da suka yi mata tun washegarin haihuwar. A can gidan Mama Hajara aka yi taron sunan, saboda ya fi girma, don haka su ma a nan suka sauka, tun daga ganin yanayin irin gidan da Safiyya take Saude ta sha jinin jikinta, Ameera kuwa kafin a gama taron sunan nan bindiga ce kawai ba ta yi ba, ganin yadda Safiyya ta yi mugun kyau tun kafin ma a zo kan suturar da dinga canzawa, ita kuwa Safiyya ganin ƴaƴanta ne ya dawwamar da farin ciki a fuskarta, don haka ta kasance a cikin fara'a da walwala har suka tafi, babu ƙarya an yi taro na kece raini, wanda ita kanta Safiyya ta yi mamakin yadda suka nuna mata ƙauna, haka ta samu alkhairi sosai, a nan gidan ta yi zamanta Mama Hajara ta ci gaba da kulawa da su ita da ƴarta. Safiyya ma ba ta jira komai ba, ta yi wa Hajiya Surayya magana, inda ta fara da yi mata dahuwar kazar mai jego mai masifar kyau, ta haɗa mata da garin daka, da tsumi wanda da su ta yi zaman kwana arba'in ɗin suka bi jikinta a tsanake, kafin a haɗo mata parckage ɗin mai jego wanda ya haɗar da komai har da ingantattun magungunan matsi wanda ba sa cutarwa, ita kanta ta san ta gama haɗuwa ta wannan fannin, saboda haka ta bar shi haka, ta koma gyara fatarta, cikin sati biyu ta yi wani sihirtaccen kyau, haskenta ya ƙara fitowa, ga wani ƙamshi mai kama duk inda ta zauna da suturarta, hutu ya sa ta yi ɓulɓul da ita. Sai da ta yi wata biyu da haihuwa sannan ta fara shirin komawa, wata uku ma ta so yi, amma yadda Salis ya matse lamba ya sa suka ce ta haƙura ta koma kawai, shi ta sa ya siyar mata da duka kayan ɗakinta, ta turo masa kuɗi ya siyo mata kayan gadonta masu kyau, kujeru kuma da ya nuna mata kalar wanda zai siya ta ce ba su yi mata ba, ta ƙara masa kuɗi a ka sayi kalar wanda take so, haka kayan adon falo ma duk ita ce ta siya, firji ne ya sayi sabo babba da kayan kallo, Ameera kawai sai gani ta yi ana shigo da kayan ɗaki, aka jere na falo, tana kallo aka shigar da na Safiyya ɗakinta, ba ta gama sarewa ba ma sai da ta ga Salis ɗin ya zo da kayan kichen sababbi ya ce ta matsar da kayanta kamar yadda suka yi a da, haka aka jere kayan Safiyya har da Gas ɗinta babba mai oven, ɗaki ta shige ta share hawayen baƙin ciki, haka ta wuni tana kumbura, yana ankare da ita ya ba wa banza ajiyarta. Da daddare kasa jurewa ta yi, bayan ya gama cin abinci kamar za ta yi kuka ta ce"Amma baban Sauban ba ka yi min adalci a wasu abubuwan". Da mamaki ya ce"To kamar me kenan?" Ta ce"Ka san bai kamata ka canza mata kayan ɗaki ni ba ka canza min ba, kuma ka ƙi saka komai a falon nan sai yanzu da za ta dawo, sannan yanzun ma ka rufe shi kana jira sai ta dawo tukunna, kenan komai nata ne, kuma kalli gas ɗin da ka siya mata ba irin nawa ba, ka canza mata komai ni ko cokali ba ka siya min ba, wannan adalci ne?" Salis ya yi murmushi ya ce"Dama don haka kike ta ɓata rai? To ni ban yi mata komai ba, duka da kuɗinta ta yi, nera biyar ɗita babu a kayan gadonta da na kitchen, kuma zancen falo da kike yi, kuɗi muka haɗa ta bada rabi na bada rabi aka sayi kujerun nan, sannan da kuɗinta aka sayi kayan adon ɗakin da aka saka, firji da kayan kallo ne kaɗai ni ne na siya, abin da ya sa na rufe kuwa saboda ya kamata a ce ta zo ta gani tukunna kafin a fara amfani da kayan, ko da za ta ce ba su yi ba kin ga dole a canzo, wannan shi ne dalili". Ta ce"Ko da kuɗinta ne, ai dai a aljihunka ta tatso kuɗin! Don haka naka ne". Ya ce"Haram! Wallahi Safiyya ba ta taɓa min satar kuɗi a aljihuna ba, yo ina take gidan ma ballantana ta ɗauka?" Ta yi huci mai zafi, ganin bai gane hausarta ba, kawai ta bar zancen. Ya ce"Ameera ita fa Safiyya sana'a take yi take ta ƙirga ribarta, saboda haka duk wani abu da za ki ga ta siya ko ƴaƴanta kar ki zarge ni da rashin adalci, guminta ne, ni kuwa ba zan hana ta yi wa kanta abu ba saboda tsoron kar ki ce ni ne na yi mata, idan kin so ke ma ki tashi ki nemi naki, ban hana ki ba!". Ya fice ya barta da zafin zuciya. Ashe wannan ma duk sharar fage ce, sai da Safiyya ta dawo sannan ta gane lallai ruwa ba sa'an kwando ba ne, don kuwa wani kyau, aji, nutsuwa da wayewa da ta ga Safiyyar ta ƙaro, abun har razana Ameera ya yi, Safiyya sai wani ɗaukar ido take yi, tana ƙamshi ga sababbin sutura kullum da kalar da za ta saka, babban abin da yake ƙara mata takaici bai wuce yadda duk ranar girkin Ameerar Salis yake rawar jiki ba, don shi kaɗai ya san romon demokraɗiyyar da suke sharɓa na sabon salon soyayyar da Safiyya take tsiro da shi kashi-kashi, ya rasa tsakanin satin amarcinsu da kuma yadda ta koma a yanzu wanne ya fi ba shi nutsuwa? Saboda Safiyya ta riƙe saiwowin Hajiya Surayya ba ta wasa da su, ga kasuwar magungunan sai ƙara haɓɓaka take yi, saboda duk wanda ya siya sai ya dawo, Maman Affan ma tuni ta zama dila a harkar maganin, saboda ingancinsa, Salma ma da infection ne ya hana ta haihuwa, sai da ta rungumi saiwowin nan na ingantaccen maganin sanyi sai ga shi mararta ta samu lafiya, cikin ƙanƙanin lokaci Allah Ya ba ta rabon samun ciki, haka kayan gyaran jiki kullum cikin aikin yinsu take, amma da ta yi ba sa taɓa kwana biyu an wawashe ta adana ribarta cass, Salis ganin Safiyyar kamar hidimar haɗa kayan ta fara yi mata yawa ga rainon Ihsan sai ya bawa Ameera shawarar ta dinga taya ta, shi da kansa zai dinga biyanta, Ameera ta ce Allah Ya kiyaye, ita ma Safiyya ta maze ko ƴar hodar gumin hammata ba ta taɓa sammata ba. Gidan Salis ya fuskanci alƙibla, falo ya zama kamar na Safiyya ita kaɗai, don Ameera idan ta zo ta zauna Safiyya tana shigowa cikin suturarta da ƙamshinta ta hakimce a kujera tana ta waya da abokan kasuwanci tana ambatar kuɗaɗe sai baƙin ciki ya turnuƙe Ameera, haka a gabanta Safiyya take bada kuɗi a siyo kayan ruwa masu daɗi a zuba a firji, don haka Ameera ta yi zuciya ta daina kula firjin, tsohon nata da yake cikin ɗakin gadonta a shi take zuba ruwa ta sha, tana ji tana gani Safiyya ta sayi sola mai fankoki uku ta saka ɗaya a ɗakinta ɗaya a ɗakin Salis ɗaya a falonta, don tuni Ameerar ta bar mata, ta koma rayuwar ɗaki ko ƙofar ɗaki, to bangaren abinci ma haka duk ranar girkin Safiyya sai ta ƙara cefane akan wanda Salis yake aikowa, saboda haka kullum haɗaɗɗen girki take yi duk ranar girkinta haka za su bajekolinsu tana kallo, sai dai Safiyya ta zubawa Sauban, wanda idan Ameera ta hana shi ci ya yi ta zunduma ihu, har Salis ya gane ya tsawar mata, ya ce babu mai raba masa kan ƴaƴansa. Safiyya ta karɓe mijinta kamar yadda ta karɓe gidanta, don shi kansa bai san lokacin da ya fara bin umarninta ba, tun da babu shirme a cikin shawarwarinta, haka ta koyi yi masa kyautar kayan sakawa, takalma, hula, da ƙananun kaya, haka kawai sai ta canza masa gajerun wanduna da singlet, ta kuma cusa kanta a wajen Hajiya da kyautata, duk yadda take gwasale ta ba ta damuwa yanzu kullum da kular abincin Hajiya, ga yawan kyautar atamfa da take yi mata, haka duk ranar Juma'a sai ta sayi goro mai kyau ta yi wa Hajiyar miya haɗaɗɗiya ta haɗa kan ƴaƴanta su je su gaishe ta, wanda hakan ya sanyaya gwiwar Hajiyar tun tana cijewa har ta saki jiki da ita, don duk yadda ta kao ga haɗe ranta babu ruwan Safiyya wuni take a gidan, don haka yanzu sun gyara komai tsakaninsu, ganin hakan ne su ma sauran ƴan'uwan kowa ya sakko, Safiyya ta sa kowa ya fuskanci alƙibla. Haka da Ramadan ta saka shi raba musu kayan abinci wanda da ba ya yi, ita kuma da sallah ta bi su da atamfofi su da ƴaƴansu, haɗaɗɗiyar shadda ta siya suka yi ɗinki dukansu ita da yaran da shi uban gayyar, ta ɗora masa hula mai kyau da ta sa aka saƙa masa, ta siya masa takalmi da agogo da turare, ana gobe idi ta ba shi, har da na Sauban da ɗinkinsu iri ɗaya, Salis ya yi ta farin ciki yana ƙara jin ƙaunarta a zuciyarsa. Ranar Idi da safe Ameera ta ga Safiyya da ƴaƴanta sun fito tsaf cikin kalar shaddar da Salis ya kawowa Sauban jiya, wani malolo ya zo ya tsaya mata a wuya, ta yi zaton sauran ɗinkin nashi ne ya yi wa Sauban ɗin, don haka yau da taƙamarta ta saka masa, don su gani su san ita ke da magaji ga shi za su yi ango da babansa, sai ta ga saɓanin hakan, kenan ita Salisu zai wulaƙanta ya ɗinkawa Safiyya da yaranta shadda ita bai yi mata ba sai Sauban kaɗai? Ba ta gama tsinkewa ba sai da gogan nasu ya fito yana baza babbar riga cikin irin ƙamshin turaren Safiyyar, sai washe baki yake yi, Safiyya ta ce"Wow! Ka ganka kuwa? Anya yau ba za ka ƙaro mana ta uku ba?" Yana dariya ya ce"Ai ke kika fito da ni, Allah dai ya shi albarka, ku wuce mu tafi". Dukansu suka wuce, shi har ga Allah Ya manta da Ameera wacce ke tsaye cikin sabuwar atamfar da ya siya mata da hijjabinta, riƙe da ɗanta da sallaya, sai da suka fito ya ga bai ganta ba, sannan ya koma, a ɗakinta ya same ta ta kifa kai a gado tana ta kukan baƙin ciki, da mamaki ya ce"Suhanallah! Ameera me ya faru? Ba za ki masallacin ba?" "Ba za ni ba!" Ta faɗa a fusace kamar za ta dake shi. Ya ɗauki Sauban da yake ta kukan ganin an dawo da shi ɗaki sauran ƴan'uwansa sun tafi, ya fice da shi, suka tafi idi. Tun a hanyar dawowa Safiyya ta yi status ɗin hotunan da suka yi a masallaci, wanda Ameera tana gani gudun hawayenta ya ƙaru, haka aka gama bikin sallar nan tana kallon kayan da ya ɗinka mata kamar tsumma akan wanda Safiyya take shiga ita da ƴaƴanta, idan ta yi magana ya ce sana'a take da kuɗinta take yi. To da babbar sallah ma, saniya ya yanka aka raba gida uku kowa ɗaya har Hajiya, Safiyya ta yanka rago da kuɗinta, nan ma Ameera ta shaƙi takaici. Haka rayuwar take ta tafiya Ameera girman kai ya hana ta sakko ta haɗa kai da Safiyya ko ta samu alkhairi, kuma ta ƙi sana'ar komai don kar ace ta kwaikwayi kishiya. BAYAN WASU SHEKARU Salis kasuwar shi ta ƙara albarka, ya zama babban ɗan kasuwa, magidanci mai kula da lamarin gidansa da iyalansa, ya sayi babban fili ya gida daidai da tsarinsa, babban falo ne na kowa da kowa da dining, sai ɗakinsa da bandaƙi a ciki, ɗakin Safiyya ciki da falo, kitchen da banɗaki, na Ameera ma haka, sai ɗakin yara ciki da falo, ɗakin Sauban magajin gida ɗaki ɗaya, ɗakin Hajiya da ta dawo gidan ita ma ciki da falo da banɗaki, Safiyya ta ƙara haifar wasu har huɗu duka matan, Ameera ma huɗun ta ƙara duka mata, ƴaƴan gidan yanzu su goma sha biyu ne, Kausar da Ni'ima sun yi aure, kuma kowaccensu tana sana'a a ɗakin mijinta, Ihsan ce ta yi karatu sosai yanzu haka Nurse ce, tana kula da lafiyar Hajiya sosai wacce ta tsufa ta gaji da duniya in ji Sauban, wanda shi ne ɗan ɗakinta, don a falonta yake kwana, shi kasuwa Salis ya saka shi amma asha ruwan tsuntsaye yake yi, don duk gidan shi ya fita zakka ba ya jin magana sosai. Yau Ihsan dawowarta daga aiki kenan ta zarce ɓangaren Hajiya, kusan cin karo suka yi da Sauban wanda Hajiya ta biyo shi da mafici cike da ƙarfin hali take faɗin"Wallahi yau sai Salisu ya zo ya raba ni da kai, fitinannen yaro ko goro ba ka siya min amma idan ka ga kuɗina sai ka gwada min ƙuruciyar matashin ɓera!". Ihsan ta girgiza kai don babu wanda bai saba da diramarsu ba, ta ciro dubu ɗaya a jakarta ta miƙa masa ta ce"Don Allah ka mayar mata da kuɗinta, wuni za ta yi tana mana mita". Ya karɓa ya fice yana yi wa Hajiyar gwalo, ta koma ɗaki ta zauna tana cewa"Oh! Ni dai an cuce ni a ce wai wannan yaron ne jikana, ku matan duka kun fi shi hankali, ni dama ku Salisu ya kai kasuwar da ya fi ganin daidai. Zaman Ameera da Safiyya lafiya lau, yanzu komai ya zama tarihi don da Ameera ta ga wankin hula zai kai ta dare, ga shi babarta ta rasu, ba ta da wani sauran mai ɗaure mata gindi, sai ta yi ladab, ta haɗa kai da Safiyya tana tallata mata kasuwarta tana biyanta, Safiyya ta ba wa Salis kuɗi yana juya mata, duk wata haka zai ƙirgo ribarta ya bata Ameera tana ji tana gani, sai idan ya ji tausayinta ya yi mata ihsani. ALHAMDULILLAH! A NAN LABARIN IYA RUWA FID DA KAI YA ƘARE, DON GYARA, SHAWARA, SUKA KO KUMA JINJINA ZA KU IYA TUNTUƁATA KAI TSAYE 08028966015 Downloaded From https://tknovels.com.ng