Downloaded From https://tknovels.com.ng ASSALAMU ALAIKUM MASOYANA INAYI MUKU BARKA DA SALLAH, ubangiji yasa Ibadan mu karbabbe ne. Alhmdlh kamar yadda nayi alkawarin kawo muku sabon littafi na kayatacce da yardar Allah to yau dai gani nadawo kamar yadda nfada muku nazo muku ne da labari mai tab 鈥檃 zuciyar mai karatu tare da soyayya mai cike da shauki, pls matured head only idan kinsan u are not matured enough karki karanta min littafi kizo kina biyoni kice zaki gayamin zancen da bazan d 鈥檃 uka ba. KAZAFI Story and written by S.borno this book is not free kibiya naira 300 kikaranta cikin salama, ga mai bukata zai tutubi wannan number 08093772168 Paid book. Free page 1&2 A cikin garin maiduguri Borno state misalin k 鈥檃 rfe hud 鈥檜 na yamma hadari ne yahad 鈥檈 sosai kasancewar lokacin damuna ne kusan kullum ruwan sama akeyi. Jiddari polo anguwa ce wacce zamu k 鈥檌 ra da anguwar manya kasancewar anguwar masu kud 鈥檌 ce, cikin anguwar ne wata mota parfection ta danno kai da gudun gaske, gaban wani katafaren k 鈥檃 ton gida motar ta shiga danna uban horn kamar zata fasa gate d 鈥檌 n gidan, da gudu wani tsoho ya taso ya bud 鈥檈 gate d 鈥檌 n. Zoya wacce tagama fusata sauk 鈥檈 glass d 鈥檌 n motar tayi tana aikawa wannan tsohon mugun kallo cikin harshen su na kanuri tace 鈥渘 yi munafuk chari ye (kai munafukin tsoho ne) taja wata uwar tsuka ta figi motar ta tashige cikin gidan, compound d 鈥檌 n gidan ya k 鈥檃 yatu sosai da flowers iri iri fad 鈥檌 n kyawun gidan kad 鈥檃 i b 鈥檃 ta lokaci ne don kana ganin gidan kasan cewa na wani k 鈥檜 san ne agarin borno. Flat kusan biyar ne agidan ko wanne yana da tazara da d 鈥檃 n uwansa sai kuma wasu biyu da ake kan ginawa suma suna opposite da juna. Rumfar Parking ta nufa tasamu gefe guda ta paker motar ta sannan ta fito, anan na samu damar k 鈥檃 re mata kallo zoya yarinya ce k 鈥檃 rama wacce bazata wuce 17 yrs ba, kyakkyawa ce ajin farko sannan acike take ta ko ina don Allah yayi mata diri gaba da baya fara ce tass tanada dogon hanci da k 鈥檃 ramin baki, duk inda ake batun kyau to tabbas za ak 鈥檌 ra zoya. Riga da skirt ce ajikinta ta atamfa green color sosai d 鈥檌 nkin ya zauna mata tayi kyau duk da cewar ba kwalliya tayi ba, bata d 鈥檃 ura d 鈥檃 n kwali ba kawai mayafi tasa mai ratsin green sai yar side bag d 鈥檌 nta hanun ta rik 鈥檈 da manyan wayoyinta guda biyu ta nufi compound d 鈥檌 n su. Tana bud 鈥檈 k 鈥檕 far palorn ta shiga ko sallama batayi ba Aunty yana ce ta juyo ta kalleta dai dai nan sukayi clash hakan yasa zoya ta shagwab 鈥檈 fuska kamar zatayi kuka tace 鈥淎 unty yana wlh nagaji gashi ma barci nakeji ko akwai abinci kad 鈥檃 n insamu inci? Murmushi Aunty yana tayi tace zoya kinaso kice min bakici abinci agidan mahaifiyar taki bane, shiyasa fa niban son kina zuwa kinsan abunka da talaka suma ba isarsu tayi ba . Tab 鈥檚 baki zoya tayi tace 鈥漬 ifa bama can naje ba Aunty wlh i don 鈥檛 know why ni inajin kunyar nunawa k 鈥檃 waye na cewar maman jawaheer itane mom d 鈥檌 na . Murmushi Aunty yana tayi tace 鈥渮 oya kenan bari infad 鈥檃 miki mahaifiyar ki bata tab 鈥檃 k 鈥檃 unarki ba hasali ma babu wacce ta tsana sama dake a duniyar nan, tafi k 鈥檃 unar k 鈥檃 nwarki jawaheer akanki don haka ki manta cewar ma kinada wata uwa, ni nan nayi miki alk 鈥檃 warin zan zamemiki tamkar uwar data haifeki ki daukeni matsayin mahaifiyar ki ba k 鈥檃 nwar uba ba kinji koh? Tayi maganar ne tana rungume zoya ajikin ta tare da bubbuga bayanta. *wacece Aunty yana*? Aunty yana k 鈥檃 nwa ce ga Alhaji Abbas mahaifin zoya, su biyu ne wajen mahaifin su, Alhaji Abbas shine babba sai Aunty yana wacce ke bimasa, asalin su mutanen maiduguri ne kanurin usul. Aunty yana tana auren wani hamshak 鈥檌 n mai kud 鈥檌 yaranta uku ne a duniya d 鈥檃 nta babba shine Abutturab sai Wacce ke bimasa wato Batool, sai autar su mairam. Abutturab babban likita ne bai cika zama a nija ba don acan Egypt yake aikin sa kuma bawani cika zuwa nija yayiba sai idan akwai dalili mai k 鈥檃 rfi. Aunty yana da mahaifiyar ta sun kasance masu k 鈥檃 bilanci don tun bayan da Alhaji Abbas ya auri Rumanah suka d 鈥檃 uki k 鈥檌 yayyar duniya suka d 鈥檃 ura mata cewar maiyasa zai auro bafulata wacce ba yaren suba, yayya mahaifiyar Alhaji Abbas har can gidan Abbas d 鈥檌 n take zuwa tayiwa Rumanah rashin mutunci, itadai bata tab 鈥檃 d 鈥檃 ga kai koda kallon banza tayi mata ba kasancewar ta mai hak 鈥檜 ri dakuma tarbiyyah. Ahaka rayuwa taci gaba har Rumanah ta haihu inda yariya taci sunan yayya wato mahaifiyar Alhaji Abbas sai suke kiranta da zoya, ranar da aka yaye zoya aranar Yayya tazo ta k 鈥檞 ace ta sosai Rumanah tayi kuka har tagaji, shidai Alhaji Abbas halin mahaifiyar tasa yana damun sa sai dai babu yadda ya iya hakan yasa baice komai ba. Ko wata ba ayiba da faruwar hakan cikin ikon Allah Rumanah takuma samun wani cikin har lokacin haihuwar ta yayi ta haifo yarinya kyakkyawa washegarin suna yayya tazo gidan ta tsaya kan Alhaji Abbas ta matsa mishi da saiya saki Rumanah yana hawaye yana bata hak 鈥檜 ri haka ta kwashesa da mari tana ta banbami saida ya rubuta saki sannan ya samu salama. Duk da cewar saki d 鈥檃 ya yayi mata haka tabar gidan don ayanxu ita kanta tagaji da halin Aunty yana da yayya, yana fita masallaci ta bar gidan S. Borno ce 鉁嶏笍 5/4/22, 10:26 AM - AMFA €嶐煈 : 鉁煉獽 AZAFI Paid book. Free page 3&4 Alhaji Abbas yana dawowa ya tarar babu Rumanah agidan duk da cewar yabi umarnin mahaifiyar sa yasake ta hakan bai hana hankalin shi tashi ba, yana cikin wannan jimamin Yayyah takuma cewa idan yaje ya nemi inda Rumanah take bata yafe mishi ba, haka yayi hak 鈥檜 ri ya danne zuciyar sa ba don yaso ba. Rumanah kasancewar iyayen ta sun rasu kuma bata da kowa a Borno hakan yasa hankalin ta yayi k 鈥檕 loluwa wajen tashi don bata san inda zataje ba ga kuma k 鈥檃 ramar jaririya atare da ita wato Jawaheer. Tana cikin tafiya batare da ita kanta tasan ina ta nufa ba har ta iso jiddari polo gaba da anguwar su sosai, anguwar shiru baka jin komai sai haushin karnuka, sosai tagaji sabida tasha tabiya hakan yasa ta zauna bakin wani hamshak 鈥檌 n gida don baiwa jaririyar ta nono, tana zaune wata mota ta danno cikin layin daidai bakin gidan datake zaune motar ta shiga yin horn, da sauri ta mik 鈥檈 tana k 鈥檕 k 鈥檃 rin barin wajen gate d 鈥檌 n hakan yasa wutar motan ta haskata harma wacce ke cikin motar tana iya hango ta, bud 鈥檈 motar akayi aka fito wata kyakkyawar balarabiya ce ta fito sanye take da abaya ahankali ta k 鈥檃 raso inda Rumanah take ta tsaya d 鈥檃 n nesa da ita tace 鈥淎 ssalamu-Alaiki! Da sauri Rumanah ta amsa mata nan take Balarabiyar nan tace 鈥渂 aiwar Allah mekikeyi anan wajen awannan daren? Rumanah bata b 鈥檕 ye mata komai ba ta bata labari sosai jikin matar yayi sanyi nan ta kamo hanun ta mai gadi ya bud 鈥檈 musu gate suka shiga cikin gidan, ita dai Rumanah duk tsoro yakamata tun shigan su gidan sabida tsaruwar gidan duk da cewar dare ne zaka rantse cikin gidan ranace don an k 鈥檃 wata compound d 鈥檌 n da wasu irin k 鈥檕 yayen wuta, duk irin had 鈥檜 war gidan su jitayi wannan gidan ya dokeshi sau miliyan tamkar ba a nigeria gidan yake ba. Wani palor suka shiga wanda fad 鈥檃 rshi b 鈥檃 ta lokaci ne yayi mugun had 鈥檜 wa bana wasa ba. Matar ta nunawa Rumanah kujera babu musu Rumanah ta zauna, babu b 鈥檃 ta lokaci tace 鈥渂 aiwar Allah agaskiya kin bani tausayi kuma insha Allah zan kamanta taimaka miki, ni ba yar Nigeria bace anma ina auren wani d 鈥檃 n Nigeria ne anan garin maiduguri yanxu haka bama zama anan acan saudiya muke zama, nazo ne don wani bikin dangin mijina kuma gobe zan koma insha Allah don nikad 鈥檃 i nazo, kuma agaskiya yanxu innatafi babu ranar dawowa ta wannan gidan dakika gani gidan d 鈥檃 na ne ko wata ba ayi da kammala shi ba, zaki iya zama har sanda Allah zai kawo mafita ga wannan A.t.m ne akwai wasu kud 鈥檃 d 鈥檈 zasukai 20 million kiyi anfani dasu kuma kibaiwa diyarki ilimi kinji koh? Rumanah hawaye ne ya sauk 鈥檕 mata tarasa da wani baki zatayi mata godiya nan tashiga yimata godiya murmushi matar tayi tace 鈥渂 abu komi yanxu muje innunamiki d 鈥檃 kin da zaki zauna kizab 鈥檃 kozaki zauna asama kokuma down stairs duk dai inda kike so haka takaita ta nuna mata inda zata zauna. A wannan daren matar nan tasa mai gadi ya sayo kayan abinci ya cika store. Washe gari da asuba tagama shirin ta zata tafi taje part d 鈥檌 n Rumanah tai mata sallama anan take shaida mata sunan ta Jannah anma yaranta da y 鈥檃 n uwanta suna k 鈥檌 ranta da Umaimah, Rumanah ganin matar zata girmeta ne yasa itama tayanke shawarar zata k 鈥檌 rata da Umaimah d 鈥檌 n haka sukayi sallama ta tafi, rayuwa taci gaba da tafiya har shekaru uku babu Umaimah babu lbrn ta inda Rumanah sukaci gaba da rayuwa a wannan gidan itada yarta jawaheer har jawaheer tashiga shekaru hud 鈥檜. Wannan kud 鈥檃 d 鈥檈 n da umaymah ta bata su batayi wasa dasu ba akwai wata aminiyar ta nan tasameta tabata lbr dama aminiyar tanada shago tana business d 鈥檌 n kaya tana kawosu daga dubai nan tabaiwa Rumanah shawara cewar ta rink 鈥檃 yin turarukan wuta da humrah ta ringa kawosu shagon ta za asaya, hakan ce takasance Rumanah batayi k 鈥 檃 sa a gwiwa ba tafara turaruka cikin k 鈥檃 nk 鈥檃 nin lokaci Allah yasawa kasuwancin ta albarka matan manya ne suke sayan turarukan ta haka tacigaba da juya wannan kud 鈥檃 d 鈥檈 n dasu take biyawa jawaheer makaranta da kuma shi take ciyar dasu haka har jawaheer tafara tasowa bata san gatan mahaifi ba sai dai soyayyar uwa. Har izuwa yanxu da ta girma ta kai 16 yrs yanzu tana ss2 a capital school. Wata k 鈥檃 war Aunty yana datake zaune kusa da anguwar dasu Rumanah suke zaune ne tana yawan ganin Rumanah a anguwar hakan yasa taje tayiwa Aunty yana gulmar cewa ai taga maman zoya tana aikatau a anguwar su to wannan shine yasa zoya take k 鈥檃 ra jin tsanar uwar tata don babu abinda ta tsana kamar talaka. Aunty yana kullum bata zama agidan ta saita zo gidan yayyah don kawai ta hurewa zoya kunne wannan dalili yakesa ko yaushe tana gidan yayyah. *cigaban labari* Aunty yana saida ta gama rarrashin zoya tad 鈥檃 uki Jakarta da key d 鈥檌 n motar ta zata tafi ganin haka zoya tace 鈥淎 unty indaro lenimin? (Aunty ina zakije?) Murmushi Aunty yana tayi tace 鈥渇 atoro lenimin (zanje gida ne) daga haka zoya tace 鈥淭 oh kigaida su mairam nima zanzo gobe Aunty yana tana mik 鈥檈 wa tace 鈥漷 o sai kinzo kinsan Abutturab ma gobe zai dawo koh? da sauri zoya ta mik 鈥檈 zaune tace 鈥渄 on Allah fa Aunty, to wlh da sassafe zanzo daga haka sukayi sallama ta fito tayi tafiyar ta. Bayan sallar magrib zoya tana kwance d 鈥檃 ki tana tunanin wani irin ado zatayi gobe wanda zata burge Abutturab wayar tace tashiga ringing ganin mai k 鈥檌 ran yasa ta yatsina fuska badon taso ba ta d 鈥檃 ga. Daga d 鈥檃 ya b 鈥檃 ngaren massa yace 鈥渮 oya inda fato? (Zoya ya gida) kamar bazatayi magana ba tace 鈥渇 oto kilaiwa silai, massa kanadi alagamma wande wayanyi bangnimin wu awodiyoye ngu fuyin nbeyi (gida lafiya lau, massa don Allah na rok 鈥檈 ka kadaina k 鈥檌 ran wayana akwai abubuwa dasuka fika mahinmanci agabana) bata jira cewar sa ba ta yanke wayar sanin cewa massa zai kuma k 鈥檌 ran wayar yasa ta kashe wayar baki d 鈥檃 ya. Massa shine d 鈥檃 n gidan shehun Borno wato sarkin borno, mahaifiyar sa ya mairah yayar yayyah ce tun zoya tana y 鈥檃 r yarinya ya d 鈥檃 uki soyayyar duniya ta d 鈥檃 ura mata inda yace bazaiyi aure ba sai yajira ta har takai minzilin aure, itakuwa zoya bashi take hari ba don ita Abutturab d 鈥檃 n gidan Aunty yana shine aranta wanda baima san cewar tanayi ba kuma babban aminin massa ne, acikin wannan family babu wanda yasan zoya tana dakon soyayyar Abutturab ita kad 鈥檃 i tasan Kayan ta. Washegari da sassafe zoya ta tashi ta shiga shirye shiryen tafiya gidan Aunty yana k 鈥檃 rfe goma tagama duk wani shirin ta, sauk 鈥檕 wa tayi a palor ta tarar da yayya da kakanta Abuyi gaishesu tayi cikin harshen kanuri da fara 鈥檃 suka amsa mata. Yayyah ce ta juya ta kalleta tace 鈥淏 itty bazakiyi breakfast bane yau? Cikin shagwab 鈥檃 zoya tace 鈥渦 hmm yayyah ina sauri ne idan naje gidan Aunty yana zanyi tana yafa mayafinta zata fice daga palorn daidai nan . This book ix not free idan kina buk 鈥檃 tar ki tuntub 鈥檌 wannan number 08093772168 S.Borno ce 鉁嶏笍 5/4/22, 10:27 AM - AMFA €嶐煈 : 鉁煉獽 AZAFI Paid book. Free page 5&6 Zoya tun sanda taga k 鈥檃 nnen sa sune guje gujen zuwa compound don tarbo yayansu mik 鈥檈 wa tayi cikin sauri ta nufi bedroom d 鈥檌 n Aunty yana ta shiga ta ringa gyara fuskarta gaban miror tare da gyara d 鈥檃 nkwalin kanta. Aunty yana kuwa tana ta faman shirya dining batamasan wace wainar zoya ke toyawa ba. Tun kafin ya kai ga k 鈥檃 rasowa cikin palorn k 鈥檃 mshin turaren sa ya gama bada signature d 鈥檌 n sa bakin sa d 鈥檃 uke da sallama ya shigo cikin palorn da sauri Aunty yana ta amsa mishi tare da k 鈥檃 rasowa tana rungume shi Cikin farin ciki tace 鈥 滱 bu u welcome Cikin sauri ya zame k 鈥檃 sa cikin ladabi yace 鈥渘 da rubdo mummy 鈥 (inayini mummy) da murmushi ta amsa mishi tace 鈥滾 fy lau yaya hanyan haka dai suka gama gaisawa da mahaifiyar tashi suna cikin hira zoya ta fito cikin takunta ta k 鈥檃 raso cikin palorn tana wani karairaya tana kad 鈥檃 k 鈥檜 gu da manyan hips d 鈥檌 nta ta k 鈥檃 raso cikin palorn daidai nan Abutturab ya d 鈥檃 go suka had 鈥檃 ido da sauri ya d 鈥檃 uke kanshi ya cigaba da danna phone nashi zama tayi kan hanun kujera with low voice tace 鈥渋 nayini ya Abu ba tare daya d 鈥檃 go ba yace 鈥渓 fy daga haka ya mik 鈥檈 da sauri Aunty yana tace 鈥滱 liyu ndaro lenimin? (Aliyu ina zaka) cikin kulawa yace 鈥渕 ummy zan freshen up inaso naje gidan yayya da sauri ta kalleshi tace 鈥渄 aga zuwa ko abinci bakaci ba kake k 鈥檕 k 鈥檃 rin fita Aliyu? Murmushi yayi wanda yakusa haukata zoya cikin miskilinci kamar wanda maganar keyi mishi wahala yace 鈥渁 m sorry mum bafa jimawa zanyi ba I just want to see my grandma kin san nayi kewar ta sosai 鈥 murmushi Aunty yana tafi kafin tace to a gaishe da ita nima d 鈥檌 n yanxu inazuwa gidan ficewa yayi ya nufi part d 鈥檌 nshi ya rage kayan jikin sa ya fad 鈥檃 toilet ya sakarwa kanshi ruwa duk da cewar ya dad 鈥檈 baya k 鈥檃 sar amma part d 鈥檌 n nashi ko ina a tsaftace kasancewar Batool da mairam kullum sai sun gyara b 鈥檃 ngaren yayan nasu. Yana fitowa ya shirya cikin wani black t-shirt sai blue jeans yayi kyau sosai sai k 鈥檃 mshi yake zubawa iwatch d 鈥檌 nshi yasaka shima black color sumar kanshi tasha gyara daga haka ya d 鈥檃 uki p-carp d 鈥檌 nshi yasaka ya fito rik 鈥檈 da car keys d 鈥檌 nshi part d 鈥檌 n mahaifiyar sa ya wuce sai dai babu kowa yar aiki ce take shaida mishi ai sun wuce gidan yayya gabad 鈥檃 yan su, daga haka ya fito direct parking space ya wuce ya d 鈥檃 uki motar sa ya fice daga gidan. Jawaheer bata wani sha wahala wajen gane gidan su ba hakan yasa direct ta nufi gidan masu gadin gidan basu hanata shiga ba don sunga kamanninta da zoya hakan yasa har suka barta ta shiga gidan. Jawaheer compound d 鈥檌 n datake jiyo kamar akwai d 鈥檃 n hayaniya can ta nufa bakinta d 鈥檃 uke da da sallama ta shiga palorn yayyah cikin mutanen dake palorn babu wanda ya amsa sallamar tata saima mugun kallo dasuke wurga mata da shi, zoya kuwa tsaki taja bata sake kallon inda take ba, jawaheer bataji haushin abunda sukai matan ba don ta tsanmaci fiye da haka awajen nasu, cikin ladabi ta duk 鈥檃 tana gishe su a maimakon su amsa mata ne yayyah tayi saurin cewa 鈥渒 e bamu buk 鈥檃 tar gaisuwarki tunda Allah yasa kinzo kwad 鈥檃 yi to maza tashi kije kitchen akwai wanke wanke kiyi, itama yar aikin yau hutawa zatayi don komi kezakiyi batayi musu ba tace 鈥渋 nane kitchen d 鈥檌 n? Cikin tsawa Aunty yana tace 鈥渄 on uwarki wa kikewa wannan tambayar hala acikinmu kinga sa 鈥檃 rki ne oya b 鈥檃 cemin dagani Shegiya mai kama da aljanu mai halin uwarta Jawaheer jike a sanyaye ta mik 鈥檈 ta fito a compound ta had 鈥檜 da d 鈥檃 ya daga cikin ma 鈥檃 ikan gidan sunata safgar su nan ta tambaye shi inane kitchen ya nuna mata, bata wani b 鈥檃 ta lokaci ba ta isa zuwa kitchen d 鈥檌 n ta cire hijab nata ta hauyin uban wanke wanken nan. A can palorn kuwa zoya ce ta kalli Aunty yana tace 鈥滱 unty nifa abinda ke bani haushi wai ace maman jawaheer tana aikatau anma dubi wai har irin atamfar 20k danake sakawa itace jikinta, ita wacece da har zan d 鈥檃 ura super itama ta d 鈥檃 ura wlh daga ita har mamanta na tsanesu da sauri yayyah tace 鈥渉 mm Allah natuba to ina yar mai aikatau ina batun d 鈥檃 ura super aiduk wacce kikaga ance tana aikatau tofa wlh kika bincika sace sace suke agidan mutane balle Rumanah datake yar fulani baduk suke kidnapping mutane ba sallamar Abutturab ce ta katse musu hirar tasu. Yayyah tafa hanu tayi tana wani irin jin farin cikin ganin jikan nata wanda take matuk 鈥檃 r k 鈥檃 unar sa cikin harshen kanuri tace 鈥滼 iwonyi tada bara yiwa layyi? (Jikana d 鈥檃 n albarka kaine atafe) Abutturab gaishe da yayyah yayi yana tambayar ina kakan sa da hanu tayi mishi nuni da yana can b 鈥檃 ngaren sa. Zoya ce tayi saurin cewa 鈥漼 a Abutturab muje innuna maka part d 鈥檌 n Abuyi d 鈥檌 n banza yayi da ita don ko kallon inda take baiyi ba ita kuwa zoya duk atunanin ta baiji bane hakan yasa ta mik 鈥檈 tana wani karairaya tace 鈥漨 uje wani mugun kallo da yayi mata yasa tasha jinin jikin ta babu shiri ta koma ta zauna. Aunty yana ce ta wurga mishi harara da sauri ya mik 鈥檈 yana sosa kai ya fice dai dai nan jawaheer tafito daga kitchen hanunta rik 鈥檈 da hijabi tana k 鈥檕 k 鈥檃 rin sakawa ga dukkan alamu ta kammala wanke wanken da yayyah ta sakata .. This book is not free 08083772168 S.Borno ce 鉁嶏笍 5/4/22, 10:28 AM - AMFA €嶐煈 : 鉁煉獽 AZAFI Hot romantic nd pure luv Story and written by S.Borno. This book is not free idan kina bukata ki tuntubeni kai tsaye 08093772168. Downloaded From https://tknovels.com.ng