An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels    RAYUWAR MU 🔺🔻🔺🔻🔺🔻 🔻🔺🔻🔺🔻 🔻🔺🔻 🔻🔺 🔺     *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* _Wannan shine Whatsapp group ɗin da zaku samu cigaban wannan labarin. Ku taya ni shering Please👇._ https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT Written by ✍️ SA'ADATU I FULANI (Ta Batulu) (Tafiyar ƙaddara kamar tafiyar ajali take, duk inda ka kai gurin guje mata sai ta risƙe ka. Komai na duniya yana da lokaci Kuma yana da iyaka, Rabbi ka yi daɗin salati ga shugaban kowa da komai, manzon tsira manzon Rahama Annabi Muhammad s a w.) *Bismillahir Rahamanir Rahim.* *Page 1-2*    Wata matashiyar budurwa ce tafe sanye da uniform ɗin makaranta blue black sai farin hijjabi wanda ya wuce guiwa, kana gani ka san na islamiyya ne, ba za ta wuce shekara goma sha takwas ba duk da uniform ɗin sun koɗe amman babu datti ko kaɗan ajikinshi, tana tafe tana yamutsa fuska, da dukkanin alamu akwai gajiya a jikinta, a bakin wani ƙaramin gida mai dakali guda biyu naga ta tsaya tayi kusan minti tara a zaune akan ɗaya daga cikin da kalin kafin ta shiga gidan bakin ta ɗauke da sallama. Wata mata ne zaune a kan kujera a  ƙofar wani ɗaki daga gani ɗakinta ne ta amsa sallamar tana cewa. Shukrah har andawo?" wannan matashiyar da aka kira da shukrah sai ta ce "Eh na dawo Umma sannu da gida"  Shukrah sai ta tsaya tana ƙarema ummanta kallo aƙalla  za tai 39 years Amman ya na yin rayuwa yasa ta zama Kamar mai shekara  40 da wani abu, Ɗakuna uku ne a gidan sai ban ɗaki a ƙarshen gidan,  kana shigowa akwai ɗakin  farko nanne ɗakin babansu shukrah, Daga ɓarayin dama Kuma  nanne ɗakin umman shukrah sai ta ɓangaren hagu shima ɗaki ne na amaryan ummansu shukrah , sai kitchen kusa da ɗakin babansu shukrah, Umma tana ta magana shukrah ba taji taba, umma ta tashi ta kamo shukrah ta ce. " ki rage ma kanki wannan tinanin bai da amfani." Shukrah ba ta ce komai ba ta shiga ɗakinsu two bedroom ne Parlourn yana da faɗi ba laifi Amman kujeru biyu ne kawai a parlourn mai zaman mutum biyu, sai mai zaman mutum uku masu ruwan toka duk yaji jiki Amman tsaff suke Babu datti, sai cafet Shima mai ruwan toka da ratsin baƙi, Duk ya koɗe Amman babu Datti ajikinshi.    Akan kujera shukrah ta zauna tajin gina bayanta ta rufe idanun ta kamar tana bacci, ba ta jima ba taji hayaniya na tashi a waje ta tashi ta shiga ɗaya daga cikin bedroom ɗin  tana buga tsaki.    Tana shiga sai ga wasu matasan ƴan mata sun shigo da sallama mata ne su biyu sai namiji ɗaya, sukai ma Umma sannu da gida Umma ta amsa tana cewa har kun dawo, suka amsa da eh. "Umma mun je bata nan sai da muka jira ta."     Umma ta kali ƙaramin yaron ta ce. "Mudan na ga kayi shiru hala sun gajiyar mun da kai?" sai mudan ya rausayar dakai ya ce "Ehh wallahi umma Aunty Darraini sai jana ta keyi acikin ƴan matan da suka shigo wacce tafi girma acikin su, ta taso tana cewa "Sai ta dake shi tinda sharri zai mata.    Umma ta tare ta tana faɗin ba zata dukar mata autan ta ba ai gaskiya ya faɗa, mudan ya kalli Darraini yayi mata gwalo Darraini tai ƙwafa ba ta ce komai ba. Umma ta kalli ɗayar yarinyar da tinda suka shigo ba ta ce komai ba ta ce mata. "Manaheer lafiya ki kai shiru ba kice komai ba, Wanda aka kira da manaheer sai ta zumɓuro baki tace . "Ni da nake jin yunwa Inna naga bakin surutu. Umma ta kau da kanta daga kallonta ta kalli Auta tace Mai autan maman shi ka najin yunwa sai mudan yace eh mana ummana" Ni fa jina ke kamar banda hanji yana mudan yana faɗin hakan du kansu. Suka kwashe mai da dariya Darraini Ta kalli Umma tace mata. "Umma har yanzu Yaya bata dawo daga islamiyar ba,? " Umma ta ce ta dawo tana ɗaki." suna jin hakan Suma suka shiga ciki bakinsu ɗauke da sallama .          Basu ganta a parlour ba sai suka shiga ɗaya daga cikin bedroom ɗin, suna shiga suka ganta ta kwanta rigingine fuskanta na kallon rufin ɗaki,  idonta biyu Manaheer tana ta magana amman shiru, da alama tayi nisa Domin tinda suka shigo bata motsa ba, Ganin hakan sai Darraini taje ta taɓa ta tana taɓa ta taja ajiyan zuciya, Duk sai suka hau kallon ta Shukrah ta kalli ƙanin nata guda biyu ta kau da kanta, Ganin ba tace musu komai ba sai suka sata a tsakiya suka kewayeta, ganin hakan sai shukrah ta tashi ta zauna tana ƙarema musu kallo, ba tace musu komai ba Sun san in zasu kwana a hakan shukrah ba za tace musu komai ba " Darraini tace "Aunty Shukrah mai ke damunki ko baki da lafiya ne"? Manaheer tai shiru tasa musu ido tana jiran taji abinda shukrah zatace, duk da ta san abune Mai wahala ta faɗa musu damuwarta. Babu zato taji muryar shukrah na faɗin yanzu haka zamu cigaba da Rayuwa kullum jiya iyau"?  Babu Wani cigaba a rayuwar mu,     Dukansu sun gane mai ta ke nufi Sai suka kasa bata amsa, ta kalli manaheer tace "tinda muka taso muke shan wahalar rayuwa har yanxu bamu san wani Abu wai Shi farin ciki ba,   ku duba ku gani yanda Umma take wahala akan mu kullum burinta yaya za ayi mu koma school amman hakan bai samu ba, Itace cin mu da Shan mu itace sutturan mu itace maganin mu, Komai itace Kuma kuna ganin babu wani, Sana'ar da ta keyi kullum faɗi ta shi ta keyi akan mu, tana gama faɗin hakan Kuka yaci ƙarfinta, suka haɗe kawunan su suna ta kuka sunyi 20 minutes suna kuka, Kawai ji su kayi an dafa su suna ɗagowa suka ga Umma tsaye a kansu tana ƙare musu kallo tace. Nai ta magana a fito ai sallah na ji shiru sai na shigo inga mai ya hana ku jin kiran sallah," Ashe kuna nan kuna aikin da kuka saba yi" Umma tace " Da ace kuka na maganin damuwa da tini ba ku da sauran damuwa a duniya, Ku tashi kuje ku fuskanci ubangiji shiɗin maji roƙon bawa ne, Kuma duk duniya Shi kaɗai zai yaye muku damuwarku" tana gama faɗa musu hakan ta fita ta basu guri ita kanta ƙarfin hali tayi ta rike kanta amman tin da suka fara magana take tsaye a kansu tazo tai musu magana akan suzo suyi sallah sai taji suna wannan firan, Ita kanta haƙuri take da mahaifinsu tana da gatan ta da komai amman ta zaɓi zama dashi ko dan ƴaƴanta,       Basu motsa ba har sai da auta ya shigo yace musu Umma tace suje, sannan suka tashi kowannen su jiki a san yaye suka fita parlour, suka same ta a saman darduma tana jan casbih, Da ido kawai ta kalle su kowa yayi waje ya ɗau buta Shukrah ta shiga bayi ta fito bayan ta fito sai Darraini ta shiga tana fitowa, Sai Manaheer ta tashi zata shiga har ta kai ƙofar bayin taji an bangajeta, sai da ta faɗi aka rufe ƙofar bayin da ƙarfi sai da manaheer tai saurin janye ƙafarta" Darraini na ganin hakan tai sauri taje ta faɗawa umma domin ta san halin manaheer bata yafiya Idan ka ta ɓata, tana zuwa taga umman na Sallah sai ta tsaya tana jiran ta idar da sallah, Ita kuma Shukrah taje ta ɗaga manaheer tace mata lallai Idan ki ka ƙyale wannan yarinyar keba jinin umman mu bane, tana gama faɗa mata hakan ta tashi ta shiga ɗaki tana leƙen Umma taga Mai ta keyi' tana leƙawa taga umman sallah take Darraini na gefen ta a zaune tai hamdala, Ta koma tsakar gida ta sa kujera ta zauna tana kallon manaheer da ta kasa magana kawai toilet ɗinsu take kallo idanunta sunyi jajir kamar wanda aka zuba ma yaji,         Ita dai shukrah tana ta kallon manaheer domin ta san idan ta kama na cikin bayin nan sai Allah, manaheer duk ta fisu jiki Kuma tafi su cika, ƙaran buɗe toilet ɗinne ya mayar da shukrah cikin tinanin da tafara. Allah allah take ta fito daga bayin taga abinda zai faru, Shukrah bata gama tinanin da take ba taji wani gigitaccen ƙara sai da gidan ya amsa tana kallon manaheer taga abinda tayi sai da ta zaro ido, Mimah ne a kwance a ƙasa manaheer nata du kan ta Shukrah ta ce. "Yauwa sister baki daki bakin rashin kunyar ba, ai manaheer najin hakan kamar an ƙara mata ƙarfi, ta dinga jibgan Mimah Umma jin ihun yayi yawa ne yasa ta fitowa jiki na rawa, Darraini da gyangyaɗi ya fara kama ta itama tayi waje da gudu,      Ganin a binda ke faruwa suke kamar a film duk da sun san manaheer ba tada haƙuri amman basu taɓa tinanin zatai ma Mimah wannan dukan ba, ganin Umma ta fito yasa shukrah ɗaga murya tace sister bugun ƙarshe ga Umma nan, Ai ko manaheer na jin hakan ta saɓi Mimah zata buga da ƙasa Umma ta buga mata tsawa tace mata kull kika aikata,         Manaheer ta saki Mimah ta faɗi a ƙasa kamar kayan wanki ta saki wani marayan kuka, Umma ta wai ga ta kalli shukrah ganin Hakan sai shukrah tayi huff ta faɗa ɗaki, Umma tace ma manaheer tazo ta huce, sai Darraini tace ai ba tai alwalan ba, Umma ta kaɗa kai tace yi alwalan mu huce ɗaki, manaheer ta tsallake Mimah dake yashe a ƙasa tana ta gunjin juka ta shige bayin" ta bugo ƙofa saura kaɗan ta bige ƙafar Mimah, Umma taje ta kama Mimah ta miƙar da ita tana kakkaɓe mata ka yanta da yasha ƙura ta ce mata "kiya haƙuri Mimah Dan allah Mimah ba tace Mata komai ba ta fisge jikinta ta shige ɗakin su,  Darraini ta Hau Dariya ta ɗaga murya tace amman fa Mimah sai kin gasa bakin ki da ruwan ɗumi.      Umma ta waigo ta kalli Darraini ganin kallon da Umma take mata yasa tai huff ta faɗa ɗaki tana ƙunshe dariya, Tana Shiga ta samu Shukrah a saman darduma ta idar da sallah tana jan casbih, Darraini ta kalli Shukrah ta kwashe da Dariya " tace mata sister a nata lazimi ne, Shukrah ba tace mata komai ba taci gaba da jan casbih, Suna cikin hakan sai ga Umma tashigo ita da manaheer Umma na gaba manaheer na baya,     Ganin Umma ta shigo yasa Darraini tayi shiru manaheer ta ɗauki hijjab ɗin Umma taje gefen Shukrah ta tayar da sallah, Darraini na ganin hakan ta tashi da sauri ta fita taje ta ɗau buta ta sake Sabon alwala, Ta shiga ɗaki ta samu Umma zaune akan kujera Darraini na ganin Umma ta duƙar da kanta Umma tai kamar bata ganta ba,                Darraini ta matsa kusa da Shukrah tace sister ɗan matsamun inyi Sallah, Shukrah ta ɗago ta watsama Darraini harara sannan ta tashi ta koma kusa da Umma ta zauna a ƙasa, Umma ta kalli manaheer data idar da sallah tace mata zoki zauna manaheer tazo ta zauna kusa da Shukrah, Umma tai shiru ba tace komai ba sai ga Auta ya shigo da sallama a bakin shi Umma ta amsa ya shigo yazo ya kwanta a jikin manaheer" Umma ta kalli auta tace daga inna kake Domin na san ba daga masallaci kake ba,"? Sai auta yace bayan an idar da sallah ne,  naga banga bashir ba shine naje gidan su naga ko lafiya sai na ganshi bai da lafiya, Umma najin hakan tai shiru ta maida dubanta gun Darraini, Tana lura da ita ta san ta idar da sallah Amman taƙi sallame wa Umma tai gyaran murya, sai duk suka ɗago suka kalleta           Umma ta kalli Darraini tace mata baki idar da sallahr bane"? sai Darraini itama tazo ta zauna a cikin su,    Umma ta kalli Shukrah tace ta kan ki zan fara saboda kece babba, Umma tace yanzu ya dace a binda ki kayi du kan su suka duƙar da kai ƙasa, Umma tace nayi tinanin ke mai tsawatarwa ne a gare su ba mai sawa suyi ba, Idan kinga suna yin a binda bai dace ba sai kitsawatar musu a matsayin ki na babba Amman abun ta kaici kece mai sawa suyi wallahi shukrah akan Hakan zan saɓa miki bazaki barni da abin surutu ba"   Yanzu a kan a binda kuka aikata kin san a binda zaije ya dawo,  Kuma kun san a kaina komai yake ƙarewa. Maiyasa idan za kuyi abu bakwa tsayawa kuyi tinanin abinda zaije ya dawo? ,      Manaheer ne tai ƙarfin halin cewa kiya haƙuri Umma in sha allah baza mu ƙara ba, Darraini ma tace Dan allah kiya haƙuri. Auta ma yace Umma sun ce kiya haƙuri ba zasu ƙara ba, Sai a lokacin Shukrah ta ɗago ta kalli Umma tace Dan allah ki yafe mana ɓata Miki ran da mukayi,  a nan Umma ta nuna ma kowa kuskurenshi Kuma sunyi mata alƙawarin ba zasu ƙaraba,  Darraini ta kalli Umma tace nifa cikina yana ciwo shukrah ta watsama Darraini harara. Umma tace kije saman gado ta gefen matashina za kiga ɗari biyar ki ɗauko kije kisiyo garin kwaki da sugar, Darraini taje ta ɗau ko tazo za ta fita Auta yace zai bita, Suka fita tare suna fita Shukrah ta tashi taje ta ɗauko bokiti taɗiba ruwa ta shiga bayi tana fitowa, taje wardrobe ɗin kayan su Wardrobe ne Mai ƙofa huɗu ta buɗe na farko ta ɗauko doguwar riga na yadi tasa, tafito parlour tazo tanzauna kusa da Umma Manaheer ma taje ta watsa ruwan ta sanja kaya,    Umma na zaune da casbih a hannunta ta naja auta ne ya shigo bakinshi ɗauke da sallama,    Yazo ya zauna kusa da Umma   Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT 🔺🔻RAYUWAR MU🔻🔺 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Written by SA'ADATU IBRAHIM FULANI (Ta Batulu) Page 3-4 Can sai ga Darraini tayi sallama ta shigo hannunta riƙe da baƙar leda, tana zuwa ta aje ta fita sai gata da kwano mai ɗan faɗi, tazo ta juye wannan garin a ciki ta fita taje ta zuba ruwa a ciki,    Ta ɗauraye ta sake wani Ruwan sannan ta shigo ta zo ta saka sugar, ta fita ta kwaso spoon ta shigo ta zo ta sa a cikin kwanon, duk a binda take Umma na zaune tana kallonta,          Auta ya sauko ya zauna a ƙasa Manaheer ta zauna kusa dashi, Darraini ta zauna kusa da Auta su kai Bismillah suka fara sha, Shukrah na hakimce a gefe tana kallon su,    Umma ta kalli Shukrah tace "Hala kin ƙoshi ne.?" Shukrah ta turo baki tace "Ni ba naci." Umma tace "Mai kikaci.?" shukrah tai shiru Umma tace "kitashi ko kuma yanzu ranki ya ɓacci."            Shukrah ta tashi tana turo baki taje kusa da Darraini ta zauna, taɗau spoon dama sauran ɗaya ne, Ta ɗiba ta kai baki tana ya mutsa Fuska ta mayar da spoon ta aje,   Manaheer ta tashi taje ta kuskure baki tazo ta zauna kusa da Umma,    sai Darraini ma ta tashi taje ta zauna kusa da Manaheer, Shukrah ta tashi ta ɗau buta tai waje, Umma tai ƙwafa ta dawo da kallon ta kan Auta, Tace "Auta meke damun Bashir ɗin naji kace bai da lafiya.?" kafin Auta yaba Umma amsa sukaji hayaniya na tashi, a tsakar gida Umma tace "Allah ya ta ƙaita wannan abun." Manaheer zata fita Umma ta hana tace su jirata taje taji, Umma ta fita Auta yabi bayanta, Amaryan ABBA ne mai suna Aisha ta keta masifa. tana zagin shukrah da ta ke zaune a tsakar gidan, tana ganin Umma ta fito tace "Yauwa ga babban munafukar nan tafito. Ta nufo Umma tana cewa "Mene yarinya na ta muku za kuyi mata taron Dangi, ku dake ta.?" Umma ba tace komai ba tai shiru tana kallon Aisha tana jiran taga mai take Shirin yi, tana zuwa gaban Umma taja ta tsaya ta gama zagin Umma tass, Sannan ta shiga ɗaki tana cewa kujira mai gidan ya dawo wallahi sai ya yi mana iyaka daku." Umma ta sauke kai ƙasa tana ajiyar zuciya, Shukrah da tinda a ka fara bata iya ɗago da kai ba, itace tazo ta kama Umma ta shiga da ita ɗaki, tana zuwa ta zaunar da ita saman kujera ta zauna kusa da ita, Ta kwantar da kan ta a jikin Umma ta fashe da Kuka, ganin Shukrah na kuka yasa sauran suka matso kusa da Umma, suka dafa shukrah su kace "kiya haƙuri sister komai zai huce Manaheer tace dan allah ki daina kuka, domin kukan ki raunine a garemu, Muma munajin abinda ki keji a ranki." Umma tasa hannu tana shafa kan shukrah tana cewa, "Babu Wani dauwamammen Abu a duniya. Kuma Duk abinda ku kaga yayi farko to yana da ƙarshe." Auta yazo ya zauna ajikin Umma Shima yasa kuka, Umma ta kalli Auta tace "Kaifa Jarumina ne ko ba kasan jarumi baya kuka ba.?" Sai Auta ya ce "To ai Umma kaɗan zanyi." Suna jin hakan dukan su suka hau Dariya Shima autan Dariya ya yi, Umma tace suzo suje su dubo Bashir da jiki, Auta ya nata murna ya na tsalle Manaheer tasa hannu ta ran kwashe shi Akai, Auta ya ɓata Fuska zaiyi kuka Umma ta ce "rabu da ita kaji haushi takeji kafita kyau." Suka shirya su uku banda Shukrah da take jin gine, Da jikin Umma ita Ko motsi ba tayi ba, Suma ganin hakan ba suce mata komai ba, Domin sun san ba za taje ba, sukai ma Umma sallama suka tafi shukrah tace a gaida mata da mai jikin, Bayan fitan su Umma ta kalli Shukrah tace mata, "inna ta tinanin sana'ar da zanyi na rasa mafita." Shukrah ta ce "koza muyi a waran sai dawa, naga a na ciniki sosai,"? umma tace a'a bana son tallah, Shukrah tace ba tallah zamuyi ba a cikin gida zamu din gayi, ana zuwa ana siya, .?"  Umma tai shiru tace "zanyi tinani akai." shukrah ba ta ƙara cewa komai ba, ta zame ta kwanta, ************************     Asalinsu Mallam Abdallahi ɗan a salin garin saminaka ne yana da mata biyu da ƴaƴa shida, Hajjiya zainab itace uwar gida mai yara huɗu sai Amarya mai yara biyu,   Ƴan ɗakin hajjiya zainab Aliyu shine babba a gidan sai Naseer, sannan Umar sai auta Fatima, Ɗakin Amarya Hajjiya Aisha Isma'eel Sai Amina Isma'eel da Fatima saanin juna ne tare a kai goyon su, Hajjiya zainab suna cema ta Mama ita kuma Hajjiya Aisha suna cema ta Inna,   Hajjiya zainab mace ce mai tsananin haƙuri ga kawaici kuma ita ce auran saurayi da budurwa, bata da wani damuwa      Hajjiya Aisha a bazawara ya aure ta mace ne Mai ta ƙama da izzah, ga rashin son zaman lafiya ga tsananin kishi suma yaran ta duk ta koya musu halinta,     Mallam Abdallahi mutum ne mai rufin siri domin Yana noma sosai, Daman saminaka garin noma ne, Kuma alhamdulellahi ya na wada ta iyalan shi, Mallam Abdullahi mutum ne mai tsananin haƙuri sosai,   Shima hak'uri yake da Hajjiya Aisha, Domin koshi bata raga mai Gidan Mallam Abdallahi  yana ɗau ke da ɗaku na biyar, a kwai ɗakin zaure inda yake a je kayan noma,    Kana shigowa ɗakin mazan gidan ne a farko  parlour ne babba mai ɗauke da ɗakuna uku sai banɗaki acikin parlour na wanka,  Ɗakin farko na Aliyu ne shi ka ɗai, sai na biyu Naseer shima Shi kaɗai sai ɗakin ƙarshe Umar da Isma'eel suke kwana,   Kowani ɗaki da ƙaton katifa a ciki da sauran kayan buƙata na maza, Amman ɗakin Aliyu duk yafi nasu kyau saboda shiɗin ya na son gayu,      Sai ɗakin Mallam a gaba da na mazan shima ciki da parlour ne da bayi, idan ka shiga ciki kuma ɗakin mama ne itama ciki da parlour ne da bayi,    Dakin Inna ya na ga ban na mama shima ciki da parlour ne,    Sai banɗakin tsakar gida guda ɗaya,        Mallam Abdallahi mutum ne Mai tsananin son ibada, kuma ya tsaya ma yaran shi suyi karatu tin daga na zamanin zuwa na Muhammadiyya, Yaran shi kaff suna karatu idan ka cire Isma'eel shi duk baya so, tin Mallam Abdallahi Yana faɗa yazo ya samai ido, Domin idan yana mai faɗa uwan cewa take duka duka guda nawa yake"?   Ya rabun mata da yaro yayi abinda yake so lokacine wata rana zai Bari,      Aliyu tinda yayi candy yace ma mahaifinshi, kasuwanci yake so ya fara, shi kuma mahaifin nashi sai ya haɗa shi da abokin shi suna zuwa kasuwa tare suna saida atamfofi da shadda da sauran kayan Sawa,    Aliyu mutum ne mai zuciya, gashi da son girma,  amman baya da raini kuma yana girmama na gaba dashi, gashi yana son karatun Addini,     Idan ya dawo gida da daddare bayan sallahr isha'i yana ɗaukan karatu gun mallam ,     Yanzu haka Aliyu ya nada Shekara 26 babban burin mallam yaga Aliyu yayi Aure ya samu mace ta gari, ƴar gidan mutunci ya aura,   Naseer ya nada 23 umar kuma 19 shekarun su ɗaya da Isma'eel sai Fatima 16  sannan Auta Amina 13 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT RAYUWAR MU *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Babu Rayuwar da Babu ƙalubale acikin ta 👌 Written by ✍️ SA'ADATU IBRAHIM FULANI            ( Ta Batulu) Page 5-6 Aliyu ne ya shigo gida bakin shi dauke da sallama, Inna tana zaune a tsakar gidan ta amsa mai sallamar tana hararan Shi,   Aliyu yayi kamar bai ganta ba yace mata sannu da aiki, Inna tayi kamar bata jishi ba yana ganin hakan bai ƙara cema ta komai ba, ya leƙa ɗakin Mama ya ganta a kan darduma tana jan charbi, ya shigo ya zauna bakin shi ɗauke da sallama Fatima ta amsa,       Tace sannu da zuwa Aliyu yace yauwa Auta ya aiki tace lafiya qalau ya kasuwa, yace Alhamdulellahi daga nan taje ta kawo mai ruwa mai sanyi   Aliyu ya ƙarba yace nagode,    Daga hakan bai ƙara cewa komai ba, ya jingina da kujeran da yake zaune akai, na karema ɗakin kallo yana dauke da saitin kujeru blue black da ratsin golden a tsakiya,     Sai fridge mai ɗan girma, ɗakin yasha tayis fari ƙal yana ta ɗaukar ido, Fatima akwai tsafta bata son kazanta,   Kuma hakan ya samu ne da tarbiyan Mama, Fatima ta leƙo tace ya Aliyu in kawo maka abinci yace a'a ba zanci yanzu ba, Mama ta kalleshi bayan ta gama jan charbin, Tace mai kaci da zaka ce ka ƙoshi Aliyu yayi shiru, mama tace ma Fatima kawo mai abinci da ruwa, bayan Fatima ta fita mama tace Aliyu ban san ko sai yaushe bane zan daina Maka faɗan cin abinci ,   Aliyu ya sunkuyar da kai ƙasa yace kiya haƙuri mama, Fatima ta shigo bakinta ɗauke da Sallama hannunta riƙe da plate tazo ta aje gaban Aliyu, shinkafa ne da miya sai salat, Fatima taje ta buɗe fridge ta ɗauko mai zoɓo mai sanyi a gora tazo ta aje,   Aliyu ya sau koh ƙasa yayi bismillah yaf ara cin abincin yaci rabi yace ma Fatima ta ɗauke ya ƙoshi, mama ta kalle Shi ta kaɗa kai bata ce komai ba,   Fatima ta ɗauke plate ɗin ta fita mama ta kalli Aliyu tace, Dama inna son magana dakai, Aliyu yayi shiru Yana kallon Mama,   Fatima ta shigo ganin kamar suna magana yasa bata zauna ba tashige ciki,   Mama tace Aliyu koza kaje ka duba Yarinyar Alhaji Ibrahim ne idan tayi Maka sai ku dai dai ta,"? Aliyu yace to Mama zanyi ƙoƙarin hakan in Sha allah, ko zuwa gobe idan allah ya kaimu, Mama tace masha allah ubangiji yayi maka albarka,   Allah ya zaba maka mafi alkhairi,   Aliyu ya aje mata ledar da ya shigo dashi ya tashi ya fita, Yana fita Fatima tayi tsalle tafito dama jira take ya fita ta samu ta fito, Fatima tace mama wallahi yaya Aliyu yayi sa'ar mata, Amina bata da matsala gata da kunya allah yasa su dai dai ta, Mama tace nima yarinyar tana burgeni, Fatima tana ta murna Mama tana ta kallon ta bata ƙara ce mata komai ba, Fatima ta janyo ledar da Aliyu ya a je ta bude kayan shayi ne a ciki Mama tace ta dauka taje ta a je, Bayan fitan Aliyu dakin mahaifinsu ya shiga, ya same Shi Yana karatun ƙur'ani    Aliyu ya zauna a ƙasa kusa da mahaifinsu wanda suke cema baffa, Aliyu bai daɗe da zama ba mahaifin nasu ya rufe ƙur'anin ya kalle shi yace mai, ya a kayi gadanga daman wasu lokutan haka yake cemai, Aliyu ya gaishe da shi yace mai daman na dawo gida ne banji motsinka ba shine nace bara in duba a she kana ciki,"? Baffa yayi murmushi yace gadanga babu wani matsala koh,? Aliyu yayi murmushi yace ba komai baffa, Sai baffa yayi murmushi irin nasu na manya, yace gadanga inna son ka riƙe abubuwa guda 4 Wanda ko bayan babu raina za kai alfahari da hakan, Aliyu bai ce komai ba baffa yaci gaba da magana yace gadanga, Inna son kaji tsoran allah kaji tsoran zalunci ka guji addu'ar wanda aka zalunta, kariƙe gaskiya a dukkan lamarin ka lallai Idan kariƙe waɗan nan abubuwan guda 4 zaka zauna lafiya, Aliyu yayi murmushi yace nagode baffa allah yaƙara lafiya da nisan kwana, in sha allah kuma zan ki yaye, baffa yayi murmushi yace ubangiji yayi muku albarka, Kai da 6an uwanka allah yaƙara rufa muku Asiri duniya da lahira, Aliyu ya duƙar da kan shi yace ameen baffa,  suna cikin magana sai gashi an shigo zuruf haɗe da sallama, ko basu duba ba sun san mai wannan halin, inna ce ta shigo tazo ta zauna kusa da baffa ta ɗaure fuska Aliyu na ganin hakan ya mike, yace ma baffa a tashi lafiya yafito daga dakin, Ya shiga ɗakin su bakin shi ɗauke da sallama, Ismael yana zaune a bakin kofa, Yana ganin Aliyu ya daure fuska ya kau da kai,   Aliyu yayi kamar bai gan shi ba ya shiga ɗakin Shi yana mamakin yan da kwatakwata Ismael bai da kunya yayi murmushi, Yana tinanin irin punishment ɗin da zai bashi idan ya kama shi,   Yana shiga ya fito da bokiti yayi cikin gida ya na shiga ya ga Aminah a tsakar gidan yace mata, Kije gurin Mama ta baki ruwan zafi ki kawo mun,   Amina tazo zata karɓa tana tura baki, tana zuwa kusa dashi ya bige bakin nata, Ai ko K Kamar jira take ta fara hawaye Aliyu yace mata wallahi Idan baki shanye wannan hawayen ba sai nayi miki mugun duka, Aliyu yace baki da kunya Koh,"? ni zan aikeki kina tura mun baki koh,"? Amina tayi tsit domin ta san halin Aliyu baya son raini, ta karbi bokitin ta shiga dakin mama bakin ta ɗauke dansallama ,   Aliyu ya kada kai yana mamakin yanda, Inna take lalata tarbiyan ƴaƴanta da kanta, Kuma idan kayi musu faɗa tace ka zalunce su, Yana tsaye sai gata tafito ita da Fatima sun shiga kitchen, yana ganin hakan yace ma Fatima tazo ta huce ta bashi guri, Fatima tazo ta huce tana ƙunshe dariya, Daman tana kallon su ta window har turo Amina amsar ruwa duk ta gani da abinda ya faru, Aliyu ya maida kallon shi kan Amina dake tsaye tana kallon shi, yace mata in zo ne in zuba ruwan da kaina, Amina ba tace komai ba ta shiga ta ɗibo mai ruwan ta kawo mai ta aje, Aliyu yace mata ta ɗauka ta kai mai toilet,   Amina ba tace komai ba tazo ta ɗauka ta shiga parlour ɗin, ta samu Ismael zaune a inda yake tin dazun,  tana ganin shi ta watsa mai harara shi kuma ya hau mata dariya,    Suna cikin hakan sai ga Aliyu ya shigo Yy kalli Ismael ya daure yuska yace mai,   tashi ka wanke mun toilet yanzu, ya kalli Amina yace ke kuma shigo mun da ruwan ki share mun parlour nan, a tare Amina Da Ismael suka kalli juna kafin kowa ya kama kanshi, Domin sun san abu kaɗan za suyi ya basu punishment din da har a kwana biyu suna jinshi, Amina tabi bayan Aliyu da ya shiga ɗaki Ismael kuma ya dau bokiti yayi cikin gida, Amina ta na shiga ta samu Aliyu zaune a saman katifa ya na danna waya, tazo ta aje ruwan a bakin kofa ta fita, ta dau tsintsiya ta fara shara ta nayi tana surutai, ta na gamawa sai ga Ismael ya shigo da bokiti cike da ruwa, Yana zuwa ya shige dashi toilet ya fito ya shiga dakin su ya dauko omo da wani ruwa a gora, Ya koma bayin 10 minutes ya gama ya fito ya mai da kayan ɗkin su, Ya shiga ɗakin Aliyu da sallama ya ga Amina a tsaye, Ismael yace mai yaya na gama , Aliyu yayi kamar baiji shi ba,  Ismael ya kalli Amina ya harareta ita ma ta rama, Aliyu ya tashi ya dau kayan wankan shi da ruwan zafin ya fita yaje parlourn su ya surka, Daman su nada roban ruwa a cikin parlourn ya shiga wanka abin shi, Bai jima da shiga ba sai ga Fatima ta shigo da sallama ta shiga ɗakin yayan nasu, taga Amina da Ismael a tsaye tace musu dan allah ya Aliyu yana nan su kayi banza da ita, Fatima tana ganin hakan ta kwashe musu da dariya tace, Yau layi ya biyo ta kan ku, tana cikin dariyar taji motsin bude ƙofar toilet, ai ko tayi tsitt kamar wanda ruwa ya cinye, Aliyu ne ya shigo da sallama suka amsa dukan su, Duk da yaga Fatima amman yayi kamar bai ganta ba, ya huce saman mirror ya ɗauko man shafawa yazo ya aje ya nemi guri ya zauna, Ya dauko wayar shi yana dannawa, Fatima ta matsa kusa da Aliyu tace Mai, ya Aliyu dan allah zanje gidan su Nusaiba na tambayi mama tace mun babu ruwanta, Aliyu ko ɗaga kai baiyi ba ballatana tasa ran zai bata amsa, Amina ta hau murmushi tana yima Fatima gwalo Aliyu na kallonta, Shi koh Ismael tinda yaga hakan ya aro natsuwa ya yafa ma kanshi, Aliyu ya kira Nasser a waya yace mai idan zai dawo gida ya tsaya ya amso mai form guda 4 Na islamiyyar ƙasan layinsu, Fatima najin hakan ta fara tinanin zuci tace nasan wannan form din namu ne bana kowa ba, kuma nasan su Amina da Ismael sukaja mana, Aliyu yace ma Fatima ta fita ta bashi guri ba za taje ba kuma zaiyi maganin yawonta, ai kafin ma ya gama rufe baki Flfitt ta fice a ɗakin daman neman hanyar guduwa takeyi, Aliyu ya kalli Amina yace mata zamu haɗu dake, sai nayi maganin ki, Amina najin hakan ta fara kuka ta na bashi haƙuri, Aliyu yace ta fita ta bashi guri zai shigo gidan ya sameta da gudu tabar ɗakin, Aliyu ya kalli Ismael da yayi fuskan tausayi yace mai, ka sameni anjjma bayan sallahr la'asar, Ismael yace to shima yayi waje yana sauke numfashi, Yana fita yace wallahi unguwar ma zan bari gaba ɗaya, ba gidan ba kuma sai kayi bacci zan dawo,    Aliyu ya gama shafa man ya samu kaya ma rasu nauyi ya sa ya koma ya kwanta ya rufe Ido, Daga hakan bacci ya ɗauke shi,   Sai bayan la'asar ya tashi shima kiran waya ne ya tayar dashi,  Yana tashi ya duba lokaci yaga lokacin ya ƙure, Ya tashi a gurguje yaje yayi alwala yazo yayi Sallah, Koda ya idar bai tashi ba ya daukoh ƙur'ani ya fara karan tawa cike da ƙwarewa ga muryan shi mai daɗin sauraro, Aliyu matashine mai cike da haiba da kwarjini , mahaifiyar shi ba fullatana ce ta asali domin danginta duk suna ruga, Aliyu dogo ne mara ƙiba amman ba siriri bane Yana da fadin kirji, ga manyan idanu ga hanci har baka fuskan shi dai dai, Masha allah duk cikin su Aliyu yafi su haske,    Ya jima yana karatu kafin ya mike ya aje ƙur'anin ya fita ya shiga cikin gida, Yana shiga yaji hayaniya a ɗakin Mama Ta Batulu ✍️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT RAYUWAR MU *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Written by ✍️ SA'ADATU I FULANI ( Ta Batulu🥰) Haquri mai cimma rabo 🥰 Dukanin abinda haƙuri bai baka shiba rashinsa ma bazai taɓa baka, Page 7-8 Shima ɗakin ya shiga da sallama yana shiga, ya ga Nasser ne tare da umar da Fatima sun sa Mama a tsakiya a nata fira, Nasser yana ganin Aliyu yace mai bro har ka tashi,"? Nasser yace ai na shigo na samu kana bacci, Aliyu yayi murmushi yace eh na tashi, Daman gajiya ce kawai, Umar yace barka da wannan lokacin ya haydar, Aliyu yayi murmushi ya kamo shi ya rungume yace barka dai ƙanin yayan Shi , Daman wani lokacin hakan suke cema juna, Aliyu ya kalli Nasser tin kafin yayi magana Nasser yace ma umar, jeka dau koh mun jakar da na shigo da shi, Aliyu ya zauna kusa da Fatima da tayi shiru tinda taga shigowa warshi yace mata ya dai teemah,"? itama haka yake cema ta wani  lokacin, Fatima tayi murmushi bata ce komai ba, mama tace ma Aliyu ba dole tayi shiru ba zaki yazo gurin, Nasser yace ai shine dai dai dasu, a gidan nan shi dai Aliyu bai ce komai ba, sai ga umar ya shigo da sallama ya mika ma Aliyu jakan, Nasser Ya taso ya karba ya bude ya ciro baƙin leda ya miƙa ma Aliyu,  Umar yaje ya ciro ruwa mai sanyi ya ɗauko kofi ya jawo teburin dake gaban Nasser, Ya ɗaura ruwan akai ya aje a gaban Aliyu Nasser yace to sarkin iyayi, umar yayi dariya ya zauna kusa da Aliyu, Fatima ta tashi zata shiga ciki Aliyu yace ta koma ta zauna, Aliyu ya fito da form din nan duka yaba Nasser ɗaya yaba umar ɗaya itama fatiman ya bata ɗaya Slshima ya dau daya yace duk su cike mai, Ya kalli Nasser yace mai Amina zaka cike mawa, shi kuma umar yace nashi ne, tin kafin yace ma Fatima daman ta san nata ne, Aliyu yace ma Fatima ke kuma fa daga baki abu har kin fara rubutu baki tsaya kinji jawabi ba,"? Fatima tayi dariya tace ai na san nawa ne shiyasa, Aliyu baice komai ba ya mai da hankali akan form din gaban shi ya cike ma Ismael, ita dai Mama tana zaune tana kallon su cike da sha'awar yanda suke kulawa da junan su tana musu addu'ar su ɗore a hakan,   Bayan sun gama cikewa Aliyu ya kalli Fatima yace tinda naga kun kusa gama makaranta zaku fara zuwa islamiyya ranar monday, zan bawa Nasser kudi ya yanko muku uniform Sai a bada ɗinki umar yace yaya har dani,"?   Aliyu ya kalli umar yace mai ko ka girmi karatun ne,"? Nasser ya kwashe da dariya umar ya ɓata fuska yace mai a'a, Aliyu yace dukan ku zaku koma babu wanda na ware a cikin ku," Ya kalli Mama yace baki ce komai ba, mama tayi murmushi tace mai zance,"? Bayan kayi komai yanda ya dace, ubangiji yayi muku albarka, Dukan su suka amsa da ameen, Aliyu ya ɗauki ruwan da umar ya aje mai, yasha ya tashi yayi ma mama sallama ya fita, Yana fita umar yaje kusa da mama yace, Wai da girma na za a kaini makaranta kamar wani yaro, Nasser yace wato ita ka raina koh, "? Naseer yace shi wanda yayi maganar ka kasa faɗa a gabanshi, Fatima tayi dariya tace ƙyale shi ya Nasser kamar a kunnen ya Aliyu, umar yace to munafuka sai kin dawo, Nasser ya kallesu dukan su yace musu kun San menene,"? suka ce mai a'a yace musu wlh bro gata yayi muku, Nasser yace yanzu kai umar ka gama makaranta kayi candy wannan shekaran, mai ya rage Maka,"?   Umar ya hau washe baki yace saura jami'a Fatima tace ai shi mafarkin Shi kenan, Nasser ya cigaba da cewa, amman ka san ba kai tsaye bro zai barka ka tafi jami'a ba,"? Umar yayi shiru sai Nasser ya cigaba da cewa ni dai shawaran da zan baka, itace karka nuna mai baka son wannan makarantar domin kuwa, Idan kuma ka nuna mai baka so ka san abinda zai biyo baya, Nasser Ya kalli Fatima yace kefa,"? Fatima tace ni wallahi banda zaɓi Nasser yace kin huta ma kanki shima ya tashi yayi ma mama sallama ya fita,  Umar ya kalli Fatima yace mata wallahi Ismael nake tausayawa domin na san baza su kwashe ta daɗin rai ba shida ya haydar, Fatima tayi dariya ta bashi labarin abinda ya faru ɗazun, Shima dariyan yayi yace kice anjima akwai kallo,"? Fatima tace ai dukan su har yanzu basu san halin ya Aliyu ba, umar yace na tina wani mari da ya taɓa mun sai da na suma, Fatima tayi dariya Mama ita kanta sai da ta dara, Fatima tace ni dai karka ƙullar mun da ciki bari in ɗauko Assignment ɗina Dan allah,  Fatima tashiga ciki ta fito da jaka tazo ta aje a gaban shi tace mai ya koya mata ne,   Fatima tana da wani ɗabi'a guda ɗaya, ita ko abune bata iya ba bata cewa ayi mata, Sai dai tace a koya mata saboda gaba, Umar ya sau koh ƙasa ya zauna itama ta zauna a kusa dashi ta bude littafin ta suka fara, Fatima tana SS two ne going to three ita kuma Amina JSS one Ismael kuma tare suka zana jarabawa da umar, Duk da shi zana mai a kayi umar kuma yace yafi son ya zana da kanshi, Nasser kuma Degree yake ɗaurawa a cikin garin Jos, Yana karantar fannin lafiya ne sannan ya iya gyaran wayoyi, Yana zama a shagon abokin shi idan ya dawo makaranta, Shi kuma umar shagon ɗinki yasa Aliyu ya kai shi yana koyan ɗinkin keke na maza, Bayan sun gama Assignment din umar ya tashi yace ma Mama bari yaje shagon su ya dawo, Mama tace yamma yayi magariba a ke shirin kira, umar yace mata ba zama zaiyi ba yanzu zai dawo Mama tace mai a dawo lafiya, Fatima ta kwashe jakanta da kuma form ɗin da suka bari a parlourn ta shiga dasu ciki, ta zuba su a cikin jakan ta na makaranta ta shiga bayi tayi alwala tadau Qur'an ta fito parlour tazo ta zauna kusa da mama, A saman darduma irin darduman nanne mai faɗi da taushi, Mama ta tashi ta shiga ciki Fatima kuma ta fara karatu cike da natsuwa,  Fatima bata da tsawo kamar ƴan uwanta sannan kuma tana da jiki ga diri masha allah, itama tana da hanci Daman duk ƴan dakin Mama suna da hanci, kuma itama mama bata da tsawo kamar dai Fatima, Amman dukan su suna kama da juna, Bata jima da fara karatun ba aka kira sallah ta rufe Qur'anin, ta tashi sai ga Mama ta fito daga bedroom, tazo ta hau darduman suka bi jam'i, Bayan an idar Fatima ta kwaso littafan ta na addini tazo Mama tana mata bita, Sun jima a hakan kafin Fatima ta mayar da littafan tazo ta fara azkar,   Bayan ta idar ta ɗauko chasbi ta naja har aka kira sallahr Isha'i, Bayan sun idar da sallah sukayi nafila sannan Fatima ta tashi taje kitchen, Tana zuwa ta samu Amina zata shiga ɗauko abincin baffa, Fatima tana ganin Amina ta bata guri ta huce, itama ta shiga ta ɗauko abincin su ta koma ɗaki, tana shiga umar na shigowa shida Nasser, suka gaida Mama suka zauna Fatima ta koma kitchen ta kwaso plate da spoon takoma, Bayan ta kai sai ta shiga bedroom tana shiga umar ya mike yana cewa daɗin abun dai muna da hannu, Mama da take gefe tayi murmushi Nasser kuma yace to acici mala'ikun tauna, Fatima dake fitowa tayi dariya tace wallahi kuma sunan ya dace dashi,  umar bai tanka musu ba ya bude kular abincin, shinkafa ne jallop na manja da wake, ya zuba a plate ya koma ya zauna Fatima na ganin hakan ta bude fridge ta ɗauko zobo da ruwa tazo ta aje musu, Umar yace kinyi taimako domin bana gane baƙin karatun shiyasa ban tsaya nai man ruwa ba, Fatima ta kalli Nasser tace in zuba maka abincin,"? Nasser yace a'a bari bro ya shigo daman tayi tinanin hakan, indai suna gida basu cika cin abinci ba tare ba, tazo ta ɗiba ta koma kusa da mama ta zauna ta faraci bayan tayi bismillahi bata ci da yawa ba ta tashi ta shiga ciki sai gata da roban yaji, umar na ganin hakan yace daman tin ɗazun nake tinanin inda zan samu yaji, Dukan su suka mai dariya saboda tinda ya fara cin abinci baiyi magana ba, Fatima ta ɗiba ta aje Mai roban yajin a gaban shi, mama tace ma Fatima idan kin gama ki ɗaura mun Lipton, Fatima tace ai muna dashi a cikin plask, mama tace to gama ki ɗauko mun, suna cikin hakan Aliyu yayi sallama ya shigo hannun shi riƙe da baƙar leda, Yana zuwa ya miƙa ma Fatima Ya gaida mama ya zauna kusa da Nasser suka gaisa, umar kam sai da ya gama cin abinci, Sannan yace sannu da dawowa, Aliyu yayi murmushi yace an gaishe da acicin gidan mu, Umar yace kuma banci da yawa ba, Domin nasan zaka dawo mana da tsaraba, Fatima da take shigowa ɗakin tace wallahi kaji tsoran allah ya umar duk irin abincin da kaci,"? Umar ya kalleta yace to inna ruwanki dani, Nasser yace haba Fatima ya zaki tona mai asiri, Mama tayi dariya tace karku tasa mun ƴa a gaba, Fatima ta zauna bayan ta shigo da babban plate ta juye abinda Aliyu ya shigo dashi, Nama ne mai yawa sai ƙamshi yake tashi, Mama tace ma Fatima ta diban ma Inna takai mata, Fatima ta ɗau plate guda ɗaya a cikin wanda  ta kwaso domin suci abinci ta ɗibo naman aciki ta fito, ta shiga ɗakin Inna bakin ta ɗauke da sallama , Inna ta amsa sallamar ta ɗauke kai Fatima tace barka da dare Inna gashi inji mama tsaraban ya Aliyu, Inna tace to aje kice angode Fatima ta fita daga ɗakin, tana fita Amina ta sauko da sauri tazo ta bude plate ɗin taga nama ne, aciki Inna tace Mai kike shirin yi,"?   Amina tasa hannu ta faraci tai banza da  Inna,   tana cikin cin namar saiga Ismael ya shigo babu sallama baice musu Komai ba, ya zauna kusa da Amina shima ya fara cin namar, Ta Batulu ce🥰✍️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6o 💖💖RAYUWAR MU💖💖 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Written by ✍️ SA'ADATU I FULANI     (Ta Batulu🥰) Page 9-10 Inna ta kalle su tace amman baku da zuciya, Babu wanda ya kalle ta acikin su, bayan sun gama cin namar, Ismael yace Amina ta zuba mai abinci, Amina ta ɓata fuska, Inna ta kalli Amina tace bakiji ana magana ba,"? Amina ta tashi ta fita tana turo baki, Ismael ya kalli Inna, yace mata wallahi wata rana sai na karya wannan yarinyar gaba ɗaya ta raina mutane, Inna tace ma Ismael ka dinga haƙuri dan allah koba ka ganin ita yarinya ne,"? Inna taci gaba da cewa, Ismael kaine babba dan allah kaja girmanka, Amina ta shigo tana tura baki, ta aje mai abincin gabanshi tashige Bedroom ɗin su,   Shima ɗakin irin na Mama ne komai da komai sai dai ya nayin kayan ɗakin, wannan ɗakin duk yayi ƙura kamar babu masu rayuwa aciki , Domin Inna akwai ƙazanta kuma ta koya ma ƴarta, Tarbiyya ana koya ne daga uwa ba daga uba ba Domin na uba da ban naki da ban, Duk yanda kike yi a gidan mijinki itama ƴarki haka za tayi a gidan nata mijin, ubangiji ka datar damu, allah ka haɗamu da iyaye na gari,🙏    Inna ta kalli Ismael da yake cin abinci, tace mai ya maganar makaranta, nifa nagaji da ganinka hakan, bokon baka mayar da hankali ba islamiyyar ma hakan, gashi kowa yana zuwa gurin sana'a amman banda kai, Ismael yace mata nifa bana son wahala ne shiyasa, kuma ni nagama makaranta sana'a kuma inna tinanin wanda zai dace dani ne, Inna ki daina damun kanki a kaina,   Yana gama fada mata hakan yayi waje Inna tace zaka dawo ka same ni, Ɗakin Mama bayan sun gama cin abinci mama ta kalli Aliyu tace karka manta da maganar mu ta ɗazun Aliyu yace mata ban manta ba,   Suka taɓa fira da ƴan uwan shi yana jadadda musu maganar tafiyansu islamiyya babu fashi su zauna cikin shiri,   Yayi musu sallama ya fita yana fita Naseer shima yayi musu sallama ya fita , Aliyu ɗaki ya shiga yaje ya ƙara shirya wa ya fita, Mama tace ma umar ya duba mata ɗakin baffan su idan yana nan, Umar na fita yaga Inna tana tsaye a bayan windows din ɗakin su,   Tana ganin umar ya ganta sai ta hau borin kunya tana ta zagin shi , Umar baice mata komai ba ya huce,     Mama tana jinsu tai shiru tana ma Inna fatan shirya, Umar ya shigo da sallama yace ma Fatima baffa yace ta kai mai Lipton, mama tace ma Fatima ta kai mai wanda ta zuba mata idan ta dawo sai ta zuba mata wani,   Umar yace bari in zuba miki ita kuma Fatima ta dauki na baffa ta fita, Fatima tai sallama ɗakin baffa ya amsa yace mata ta shigo, tana shiga sai ga Inna ta shigo babu ko sallama Fatima tai kamar bata ganta ba, Fatima ta matsa gaban baffa tace mai barka da dare ta aje kofin ta tashi ta fita, Inna ta kalli baffa tace mai wannan zalunci ne ba adalci ba, kuma allah yana gani wallahi sai yayi mun sakayya, baffa bai ce mata komai ba har ta gama maganar ta, sai ma tashi da yayi ya shiga daga ciki hannun shi ɗauke da kofin da fatima ta kawo,   Inna tayi kwafa tace wallahi zaka dawo ka same ni,     Fatima tashiga ɗakin su bakinta ɗauke da sallama ta samu umar suna fira da Mama, itama ta zauna suka cigaba da firan da ita, tara da rabi baffa ya shigo ya zauna suka ɗan taɓa fira kafin yayi musu sai da safe, Yana fita umar  yayi musu sallama ya tafi ɗakin su, Mama tayi alwala ta hau darduma Fatima tayi alwala ta kwanta, Agurguje anyi auran Amina da Aliyu baffa ya basu gidan zama amman ba unguwa ɗaya suke ba,   Umar ya tafi jami'a Fatima juma ansa mata rana da saurayin da baffa ya zaɓan mata,   Duk da Aliyu baya gidan suna zuwa islamiyyar da ya sa su, ita, kuma Amina rashin kunya ya ƙaru tinda mai tsawatar wan yabar gidan, Ismael kuma baffa ya kaishi garin zaria karatu bayan ansha fama da Inna,   Yanzu gidan daga Fatima sai Amina sai Nasser sannan umar,   Fatima tayi candy  baffa yace idan taje ɗakin mijinta taci gaba a can yanzu Amina ka ɗai ke zuwa boko itama ba kullum ba, Gidan Aliyu zama suke cike da Farin ciki da jin daɗi Amina tana girmama shi, suna son junansu sosai, gashi allah ya fara dafa mai, mai gidan shi ya bashi shago ya zuba mai kaya, yace ya mayar mai da kuɗin kayan, ya riƙe ribar shima ya kula da kanshi tinda yanzu ya aje iyali, Bayan shekara uku anyi auren Nasser da budurwan Shi maryam har ma ta nada ƙaramin ciki, Nasser ya gama makaranta ya kama sana'ar saida wayoyi a shagon da Aliyu ya buɗe mai, Shima baffa ya bashi gida kusa da Aliyu daman gidan ya siyane domin su zauna aciki Idan sun tashi aure, Fatima tayi aure da mijinta Abubakar yana saida motoci suna zaman lafiya da mijinta, Domin Fatima halin mahaifiyarta ne da ita, Abubakar yana sonta sosai kuma yana kulawa da ita yanda ya dace, Umar yana cigaba da karatu  Ismael kuma yana Zaria, Mama ta ɗauko Yar kanwarta mai suna Rabi'a tana taya ta zama, Amina kuma anata tara samari a kofar gida tin baffa na fada, Inna tana kareta ya gaji ya sama ta ido, Acewar Inna gwanda ta zaɓa ta darje ta samo wanda yafi na Fatima kuɗi, Gidan Aliyu suna rayuwa cike da farin ciki ƴar su ɗaya mai sunan mama suna cemata Shukrah, Yarinya mai kama da babanta sakk, Duk da itama uwan ba baya ba gurin kyau, Amman idan kaga shukrah kana ganinta kasan waye Aliyu ne babanta, Shekarun shukrah 2 a duniya Fatima tana son shukrah sosai, haka shima baffa yana sonta, itace jika na farko a gurin baffa kuma ta fito daga gurin ɗa mafi soyuwa a zuciyar shi, Ta Batulu 🥰 ce✍️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT 💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Written by ✍️ Sa'adatu I Fulani    (Ta Batulu🥰) Page 11-12 Bayan wani lokaci abubuwa da yawa sun faru, Dawowar Ismael gida auren Amina umar ya kammala karatu ya samu aikin banki, Fatima ta haihu na miji sunansa Aliyu suna kiransa da Sajjad, matan Nasser ma ta haihu na mace sunan yarinyar Khadija, Yaran Aliyu biyu bayan shukrah sun ƙara samun Sa'adatu suna ce mata Darraini, Tsufa ya ƙara kama baffa sosai domin yanzu yaran suke riƙe da gidan, Amina tayi aure bayan ta gama ruwan ido ta zaɓo wani mai suna sager, suna zaune a cikin garin Jos yana sana'ar sai da takalma, Shima Naseer kudi sun fara zama, Matan Aliyu da matan Nasser kan su a haɗe yake, Duk da ka san cewar ba gida ɗaya suke zaune ba, Amman suna zaman lafiya babu mai jin ƙan su, Aliyu ya gina gidan shi mai kyau sun tare plat biyu, Sai nasa plat ɗin daban, kowani plat two bedroom ne kowanne da toilet a ciki sai kitchen a parlourn, Gidan yasha tayis ga famfo harda gate, Yanzu haka shagunan Aliyu biyu ɗaya a garin su ɗayan kuma a Jos, Yana ta tinanin ya ɗaura Ismael a shago ɗaya tinda duk cikin su kowa yana da abin yi amman banda shi, Saboda shi yaƙi karatu ko yanzu da ya dawo gida babu abinda yake yi face zaman majalissa, Aliyu ya tara ƴan uwan shi ya fada musu abinda ke cikin zuciyar shi game da Ismael, Naseer ya ce shi a nashi shawaran ya fara jaraba shi ya bashi jari ko treda ya buɗe mai ya ga kamun kan shi kar yaje ya ɗaura shi a kan dukiyar shi a samu matsala," Shima umar haka ya ce," Aliyu ya ce musu zai je gida anjima gurin baffa, Daga haka ya sallame su kowa ya kama gabansa, Da daddare Aliyu ya shirya tsaff zai je gida sai Amina tace mai, ita ma zata je domin ta kwana biyu bata je ta gaida baffa ba, Aliyu yace mata tai sauri ta shirya yana jiranta," Amina tace to bata jima sosai ba ta fito hannunta riƙe da Darraini ɗayan kuma leda ne mai ɗan girma tana tafe shukrah ƴar shekara 8 na binta a baya, Tsakanin Shukrah da kuma Darraini shekara 4 Aliyu ya ɗau shukrah ya fita ya ce ta same shi a waje, Daman lokacin auren Amina ya sai mashin," Amina tana fitowa ta hau mashin ɗin shukrah na gaban mashin Darraini na tsakiyya suka tafi, Bayan sun isa gida ya aje mashin ɗin ya riƙe shukrah suka shiga cikin gidan bakin su ɗauke da sallama, babu kowa a tsakar gidan sai Ismael shima yana ganin su ya fara zare ido kana ganin shi kaga mara gaskiya, Aliyu yayi kamar bai ganshi ba shukrah ta ƙwace hannunta ta shige ɗakin baffa tana kiran sunan shi, Amina kuma ta nufi ɗakin mama hannunta riƙe da Darraini," Aliyu ya kalli Ismael yace mai ka keyi a nan,"? Ismael yayi ƙasa da kai yace mai babu komai," Aliyu ya kalle shi yace mai kaji rani ina neman ka tinda kai baka zumunci da kowa," Ismael yace to Aliyu ya huce ɗakin baffa yayi sallama ya shiga ya samu shukrah ta haye mai jiki tana ta surutu, Aliyu yana mamakin yanda shukrah take sakewa da baffa take mai surutu, Shukrah bata da yawan magana duk da ka san cewar Aliyu muskili ne, Amman shukrah tafi shi, domin ita ko magana kayi mata idan bai mata ba ko kallon ka baza tayi ba, Amman idan kaji zancen ta tazo gurin baffa ne idan kaji dariyar ta mai yawa tana tare da baffa ne, Aliyu ya kalli baffa yana zaune yana jan charbi duk ya tsufa domin wani lokacin ko fita ba yayi," Aliyu ya gaishe shi ya mai ya jiki baffa yace jiki Alhamdulellahi," Aliya yace ma baffa daman wata magana ne ke tafe dani baffa ya gyara zama yace Inajin ka," Aliyu ya faɗa mai shawaran da suka yanke da ƴan uwan shi," baffa yayi farin ciki sosai yayi murna daman abin yana damun baffa zaman shi hakan babu sana'a tinda shi yaƙi yin karatun gaba ɗaya, Sauƙin ta ɗaya ma daya kai shi zaria babu laifi yayi karatun domin har sauka yayi," Baffa yasa musu albarka dukan su sannan ya ƙara mai da nasiha kamar yanda ya saba," Baffa yana yawan gaya ma Aliyu yaji tsoran allah ya kula da hakkin iyalin shi karya zalunce su, domin suɗin amana ne a gurin shi kuma za a tambaye shi yanda ya tafiyar da wannan amanar da aka bashi," Aliyu yayi ƙasa da kai yace in sha allah zan kiyaye na gode baffa allah yaƙara nisan kwana, baffa ya ce mai yaje ya gaisa da mutanan gidan yazo su tafi gida kar dare yayi musu a hanya, Aliyu ya fita daga ɗakin baffa jiki a sanyaye" Saboda har yanxu ya kasa saba wa da wannan nasihar na baffa, Gani yake kamar wasiyya yake barin mai, Aliyu ɗakin Inna ya shiga bayan yayi sallama an amsa ya shiga ya zauna a ƙasa ya gaishe ta," Ita fa har yanxu Inna bata sanja halin ta ba domin duk cikin yaran baffa tafi kishi da Aliyu, Inna ta amsa tana washe baki tace Inna rigimammiyar take haka take cema shukrah, Saboda Inna shukrah bata son zuwa gidan, Domin jinin su bai haɗu ba, Bayan sun gama gaisawa ya tashi ya fita Inna ta bishi da harara, Aliyu yayi sallama ɗakin mama ya shiga ya same ta a zaune Amina tana shafa mata man zafi a ƙafafun ta" Amina tana ganin ya shigo tace bari taje ta gaida baffa," mama tayi murmushi tace daga nan kya tawo da sarkin rigima, Amina tana murmushi tafita, Ɗakin baffa ta shiga bayan tayi sallama yanda Aliyu ya barsu shida shukrah itama haka ta same su, Amina ta duƙa har ƙasa ta gaida baffa tayi mishi sannu da jiki baffa yace jiki ai ya warware," Baffa ya kalli Amina yace mata daman ina nemanki," Amina tayi ƙasa da kai tace to baffa allah yasa ba ƙarana shukrah ta kawo ba," Baffa ya ce a'a Wani amana nake son baki," Amina tai shiru tana sauraron baffa,"   Baffa yayi ƙasa da kai yace Amina dan allah ina son ko bayan raina kiyi mun alƙawarin zaki zauna da Aliyu," Amina tayi tsit kanta a ƙasa baffa yaci gaba da magana yace Amina akwai tarin ƙalubale a gabanki," baffa yace kinga Aliyu duk cikin ƴaƴana yana da wata ɗabi'a wanda ba kowa ya san da ita ba, amman nasan ke kinsan da wannan ɗabi'ar tashi," Baffa yace Amina ki rage bacci domin akwai aiki mai tarin yawa a gabanki, Sannan kuma ki kula da yaranki duk rintsi karki bari tarbiyan yaranki ya lalace, Baffa ya shiga daga ciki sai gashi ya fito hannun shi riƙe da wani babban gora yazo ya zauna inda ya tashi,   Yace ma Amina tazo ta karɓa," Amina taje ta karba jikinta yana ta rawa, Baffa yace mata rubutu ne a ciki ina so kiba yaranki su sha kema kisha sannan shima Aliyu kiba shi yasha," Amina tayi godiya ta tashi taje ta ɗau shukrah da ta fara bacci a jikin shi tayi mai sai da safe tata shi zata fita," baffa ya kirata, Amina ta dawo ta zauna baffa yace mata ki ƙara hakuri akan wanda kike dashi," Sannan kuma ki ƙara riƙe sirrinki da kyau duk abinda zaki gani ki ya haƙuri komai zai huce, Amina ta kasa magana baffa yace mata zaki iya tafiya," Bayan fitan Amina baffa yayi murmushi yace tabbas ubangiji baya zalunci kuma baya barin azzalumi, Ta Batulu 🥰 ce ✍️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT 💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Written by ✍️ Sa'adatu I Fulani   (Ta Batulu🥰) Page 13-14 Bayan Amina ta fito daga ɗakin baffa sai ta ɓoye jarkan da ya bata a cikin hijjab ta nufi ɗakin Inna, Ta yi sallama ta shiga ɗakin ta samu Inna zaune a kan kujera suna fira da Ismael,   Amina ta samu guri ta zauna ta gaishe da Inna Ismael ya gaishe ta Amina ta ce," Ba zan amsa ba saboda tun da ka dawo ban ganka a gidana ba, Ismael ya ce," In Sha Allah zan zo gobe idan Allah ya kaimu Amina tayi murmushi ta ce," Allah ya kawo ka lafiya Inna ta kalli shukrah dake kafaɗar Amina tana barci  tace rigimamiyar tayi bacci, Amina ta ce," eh ta yi barci a ɗakin baffa Idon Inna yana kan hannun Amina tana son ganin a binda ke ɓoye a hannunta domin ta san daga ɗakin baffa ta shigo, Amina tayi kamar bata ganta ba hassalima da taga kallon yana yawa ta tashi tayi ma Inna sai da safe  ta fita, Ɗakin mama Amina ta shiga ta samu Aliyu da umar suna zaune suna fira, Aliyu yana ganin Amina ya ce," daman ke nake jira mu wuce, Umar yace Aunty na ni ka dai barka da dare Amina tayi dariya ta ce," Allah ya shirya mana kai umar yayi dariya, Aliyu ya ce," karki biye ma wannan sarkin surutun kinga dare yayi ga shukrah ma tayi barci zo mu wuce gida, Mama ta fito daga bedroom hannunta riƙe da leda taba Amina taba takwaran ta, Amina ta duƙa har ƙasa ta karɓa  tana godiya Aliyu ya karɓi shukrah, Umar kuma ya ɗau Darraini itama tayi barci suka fita, Suna fita su kaci karo da Inna a bakin window tana tsaye, Dukan su sun ganta amman sai suka nuna kamar basu ganta ba domin idan da sabo sun saba da halinta har Amina tasan halin Inna, Bayan sun fita Aliyu ya kalli Umar ya ce," Ismael ya same ni a gida gobe idan Allah ya kaimu, sannan ya karbi shukrah Amina ta karɓi Darraini suka tafi, Bayan sun isa gida Amina ta kwantar da shukrah a ɗaya ɗakin inda suke kwana ita da ƙanwarta, taje tai wanka tazo tasa kayan bacci  ta tsaya tana ma shukrah addu'a, Aliyu kuma ya kai Darraini ɗakin su ya kwantar da ita shima yaje yayi wanka yazo yasa kayan bacci yayi addu'a ya kwanta, Amina ta shiga ɗakin bakinta ɗauke da sallama ta samu Aliyu har yayi bacci ta zuba mai ido tana kallon shi, tana ta nazarin maganar baffa tabbas akwai abinda yake shirin faruwa, Ita da kanta tasan Aliyu yana da ɗaukan zuga, kuma wani lokacin yana da yawan ɗaukar maganar mutane koda kuwa ba gaskiya suka fada mai ba sannan akwai shi da yarda da abinda yaran shi suka faɗa mai, Amina ta daɗe a zaune tana ta tunanin maganar baffa tabbas ta san gidan su Aliyu akwai abinda ke faruwa, A ƙarshe dai ta yanke shawaran zata tsananta  addu'a koma mene ne yazo mata da sauƙi, Darraini ta tashi tana kuka Amina ta ɗauke ta ta kaita toilet tasa ta tayi fitsari, tazo tasa mata pampas ta haɗa mata tea ta bata tasha sannan ta kaita ɗakin su ta samu  kaya marasu nauyi tasa mata ta kwantar da ita a gefen shukrah, Har ta fita ta dawo ta ɗau shukrah ta kaita toilet ta sata tayi fitsari itama ta sanja mata kaya ta kwantar da ita ta ƙara musu addu'o'i ta jamusu kofar ta fita, Kitchen ta shiga ta haɗo Lipton ta fito ta zauna a parlour tana sha tana tinani parlourn yasha saitin kujeru pink da fari ga ƙaton kafet a tsakiya shima pink da fari, Lokacin da zasu tare Aliyu ya sanja mata kayan ɗaki komai na parlourn pink da fari ne, kayan kallo ga ƙaton fridge show glass masha Allah komai yaji a parlourn, Gaba ɗaya jikin Amina  yayi sanyi gashi baffa yace ta ƙara riƙe sirrinta, Babu wanda zata iya shawara dashi bata da ƙanwa ko ɗaya kuma mahaifiyarta ta  rasu tin bayan haihuwar shukrah bada jimawa ba, Sunan Darraini sunan mahaifiyar ta ne shiyasa suke kiranta da suna Darraini Saadatul Darraini, Amina takai wajen ɗaya da wani abu a zaune, kafin ta tashi ta shiga ɗaki tayi alwala ta shimfiɗa darduma ta fara sallah, Bayan ta idar ta ɗauki Qur'ani bata tashi a gurin ba sai da aka kira assalatu, Amina ta tashi ta shiga kitchen tana shiga suka kawo huta ta jona buta domin ya ta fasa mata ruwan zafi ta ɗau plas ɗin ruwan zafi ta fita, Ɗaki ta shiga ta aje plas ɗin ta shiga toilet ta ɗauko bokiti ta juye ruwan plas ɗin ta shiga wanka bata jima sosai ba ta fito tazo ta zauna a gaban mirror tana shafa lotion, Tayi simple make-up ta samu doguwar riga tasa ta fesa turare tayi ɗaurin ɗankwali mai kyau, Ta tashi taje gaban gado tana tashin Aliyu tace mai lokacin sallah yayi Aliyu ya kafa mata ido ya kasa magana, Aliyu ya ce ma Amina zokiji wata magana Amina tayi dariya tayi hanyar barin ɗakin tana ce mai zai rasa jam'i fa ya tashi, Tafita ɗakin ta leƙa ɗakin su shukrah taga sunata barci taja musu ƙofar ta fita kitchen ta shiga taga  ruwan da ta ɗaura yana ta tausa, Ta koma ɗaki  ta samu Aliyu har yayi alwala zai fita massalaci tace mishi a dawo lafiya ta ɗau plas ɗin ta koma kitchen ta  juye ruwan ta ƙara jona wani ruwan ta fita ta koma ɗaki daman bata ɗauke darduman da tayi sallah a kai ba tana shiga aka tayar da sallah , Daga masallacin Zuwa gidan su babu nisa gida uku ya raba bayan Amina ta idar da sallah tayi addu'o'i sama sama tayi azkar ɗin safe, bayan ta idar ta fita ta koma kitchen tana zuwa ta samu ruwan ya tausa, Ta kashe jikin socket ɗin ta fita ta koma ɗaki ta shiga toilet ta ɗauko bokiti ta koma kitchen ta juye duka ruwan a ciki ta ƙara jona wani ruwan ta ɗau bokitin ta fita, Ɗakin su shukrah ta shiga ta kamo shukrah ta shiga da ita toilet ta wanke mata baki tayi mata wanka tasa ta tayi alwala ta ɗaura mata ɗaya daga cikin towel ɗin dake rataye a toilet ɗin, Amina ta fito shukrah na biye da ita a baya shukrah ta zauna saman ƙaramin kujeran dake gaban mirror Amina ta buɗe man shafawa taba shukrah, Sannan ta ɗauki Darraini ta shiga da ita toilet, Ta cire mata pampas ɗin jikinta tayi mata wanka ta wanke mata baki ta samu ƙaramin towel wanda bai kai na shukrah girma ba ta ɗaura mata ta kamo hannunta suka fito, Amina tana fitowa ta samu shukrah tasa uniform ɗin school tana sallah da  hijjab ɗinta har ƙasa, Amina ta aje Darraini ta fita ta koma kitchen tana zuwa taga ruwan ya tausa ya kashe kanshi, taje toilet ta ɗauko bokiti ta juye ruwan zafin ta fita dashi, Ɗakin yaran ta leƙa ta samu shukrah tana shafama Darraini man shafawa, ganin hakan sai Amina ta tafi ɗakin ta, Tana shiga ta samu Aliyu yana zaune a saman darduma yana karatu, Amina ta shiga bayan tayi sallama toilet ta nufa ta shiga bakinta ɗauke da addu'a, Ta shiga toilet ɗin ta ƙara ɗaurayewa saboda lokacin da za tayi wanka sai da ta wanke ta ɗauko wani ruwa a gora ta yayyafa ta ɗauko bokitin da ruwan zafin yake ciki ta shiga dashi toilet ɗin ta janyo ƙofar ta fito, Tana fitowa ta samu Aliyu zaune yana kallon ƙofar toilet ɗin, Amina taje kusa dashi ta duƙa ta gaishe shi Aliyu yasa hannu ya jawota jikin shi, yace mata sannu da ƙoƙari matar aljanna Amina tace baka amsa gaisuwata ba," Aliyu ya ce nayi kewarki ne da yawa Amina za tai magana taji sallamar shukrah a bakin ƙofa Aliyu ya amsa sallamar, Ta Batulu 🥰 ✍️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT 💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Written by ✍️ Sa'adatu I Fulani    (Ta Batulu 🥰) Page 15-16 Amina ta tashi a jikin Aliyu sannan ya basu izinin shigowa ɗakin. Shukrah ta shigo hannunta riƙe da Darraini ita ma sanye da uniform ɗin school Aliyu ya kalli Amina ya ce. "Madam kin manta yau monday baki bamu breakfast ba" Amina ta ce ruwan wankan shi yana toilet Shukrah ta duƙa har ƙasa ta gaida Aliyu sannan ta gaida Amina Darraini itama tayi yanda shukrah tayi, Amina ta ce Shukrah ta zo suje kitchen. Darraini ta zauna ta jira su Aliyu ya ce." A'a karki ƙona mun yarinya. Amina tayi dariya ta kamo Shukrah suka fita Aliyu kuma ya aje Darraini a saman gado ya shiga toilet. Amina tasa Shukrah ta gyara mata kayan miya. Ita kuma ta haɗa tea a ƙaramin cup ta fita ta koma ɗaki ta samu Aliyu yana wanka. Ta ɗau Darraini da ta fara bacci ta fara bata shayin saboda ita bazata iya jiran a gama breakfast ba. Bayan ta gama bata shayin ta kwantar da ita ta fita ta koma kitchen Ta samu Shukrah har ta niƙa mata kayan miyan a greater. Amina ta kunna gas saboda sun kashe wuta ta kwaso kayan ƙamshi ta zuba a tukunya tasa sugar tasa ruwa ta ɗaura a wuta. Shukrah ta fita daga kitchen ta yi sallama ta shiga ɗakin Amina. Bayan shukrah ta fita daga kitchen Amina ta cigaba da aikin ta. Bayan  ta sauke ruwan shayin ta  ɗauko wani flas ɗin ta juye wannan ruwan zafin a ciki. Ta ɗaura tukunya a wuta ta zuba mai ta soya kayan miya tayi sanwa tasa spices ta rufe tukunyar. Sannan ta koma parlour ta hau gyarawa ka san cewar babu datti sosai yasa ba a ɗau dogon lokaci ba ta gama gyarawa. Tasa turare ta koma kitchen ta samu ruwan ya tausa. Ta kwaso indomie ta zuba ta rufe tukunyar ta kwaso albasa tana yan kawa bayan ta gama yan kawa ta zuba a ciki ta rufe tayi ƙasa da wutan ta fita. Dakin yara ta shiga ta gyara tasa turare ta kwaso musu jakan makaranta ta ɗauko darduman da suke shimfiɗawa idan zasu ci abinci ta rufe ɗakin ta fito. Parlour tazo ta aje kayan hannunta ta kira Shukrah tazo ta fara kwaso cups a kitchen. Ita kuma ta shimfiɗa darduman ta shiga ɗaki ta samu Aliyu zaune Darraini tana jikin shi yana mata wasa Amina ta ce "Abban Shukrah komai yayi ready Aliyu ya ɗauko  Darraini ya fito Amina kuma ta ɗau flas ɗin data aje ta fita. Amina kitchen ta shiga ta aje flas ɗin ta sauke girkin ta ɗauko kulan Darraini na makaranta ta zuba mata indomie sauran ta juye a plate guda biyu. Shukrah ta shigo kitchen din Amina ta bata kayan tea tace taje ta aje gata nan zuwa   Amina ta fita da plates ɗin data zuba indomie, Ta samu Aliyu zaune a saman darduman da suke cin abinci yana haɗa ma Shukrah tea Amina ta aje plate ɗin ta ɗau cup tana haɗa ma Aliyu nashi. Shukrah abinci bai dame ta ba domin ko school bata zuwa da abinci sai dai drinks da biscuits, Bayan sun gama breakfast Aliyu ya tafi kai su shukrah school Amina kuma ta ƙara gyara gurin tayi wanke wanke. Ta shiga toilet ɗin yara ta wanke ta fita ta koma ɗakinta, Ta zauna zaman make-up tayi kyau sosai ta samu kaya riga da wando tasa Amina akwai diri ga idanu dara dara masha Allah, Bayan ta gama ta ƙara gyara bedroom ɗin har toilet sai da ta ƙara gyarawa ta ɗau rigan da Aliyu ya cire ta haɗa da nata ta fita. Ɗakin su  Shukrah ta shiga tasa musu turare ta shiga toilet ta ɗauko bokiti ta kwaso kayan da suka cire ta haɗa da na hannunta ta fita dasu, Ta za gaya ta baya inda igiyar shanya yake ta aje wankin ta fita ta koma toilet ɗin ɗakin su Shukrah ta ɗauko sabulun wanki da omo ta fito, Ta zo ta fara wankin bata dade ba ta gama saboda kayan babu datti a jiki ta shanya ta wanke bokitan da tai wanki ta koma ciki, Taje ta aje su a inda ta ɗauko su ta ɗau wayarta ta koma parlour ta zauna. Tana chart sai ga sallamar Aliyu kallo ɗaƴa tayi mai ta ɗauke idon ta bayan ta amsa sallamar, Aliyu da sauri ya ƙariko ya zauna kusa da ita ya ce " Haba madam irin wannan kwalliyar haka. Kin manta yau monday ina da ayyuka da yawa Amina ta juya ido ta ce. Allah ya kiyaye hanya ranka ya ɗaɗe mijin Amina Aliyu ya ce "Ai yau babu inda zani madam, Amina tayi dariya ta ce " dan Allah rufa mun asiri Aliyu ya ce" Daman shekarun Darraini 4 tana buƙatar ƙani, Amina ta ce" ai ni na gama haihuwa yanzu domin Darraini itace auta na Aliyu ya ce " Zakiga auta. Suna cikin hakan sai ga sallamar almajirin su mai suna Sani. Amina ta sa hijjab ɗin dake kusa da ita Aliyu ya ce "Ya shigo, Sani ya shigo ya tsaya daga bakin ƙofa ya duƙa ya gaida Aliyu sannan ya gaida Amina ya tashi ya fita. Amina ta tashi ta shiga kitchen ɗauke ma Sani Abinci tana tashi Aliyu ya bi bayan ta. Ta shiga kitchen ta ɗauko kulan da take zuba mai abinci. Ta haɗa mai tea a cup ɗin shi tazo fitowa taci karo da Aliyu tsaye a bakin ƙofa yana kallon ta, Amina ta ɓata fuska ta ce " Abban Shukrah zan wuce. Aliyu bai ce komai ba ya bata hanya tazo wuce wa ya riƙo ta ya ce" Haba madam laifin me nayi ake share ni Amina ta ɓata fuska Aliyu ya ce" Na tina abin da ya faru ya karɓi kayan hannunta ya fita dashi. Ya samu Sani yana shara ya bashi abincin ya ce" Idan ya gama aikin shi yaje ya dawo bai jira Amsar Sani ba ya koma ciki. Yana shiga parlour yaga Amina zaune a saman kujera ya je ya zauna kusa da ita yana cewa tazo suje ya nuna mata wani abu, Amina tayi shiru taƙi magana Aliyu bai ƙara cewa komai ba ya ɗauke ta yana dariya ya nufi bedroom ɗin su, Bari mu leƙa gidan Baffa mu dawo Ta Batulu 🥰 ✍️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT 💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Written by ✍️ Sa'adatu I Fulani    (Ta Batulu 🥰) Page 17-18 Ismael ne zaune a ƙofar ɗakin Inna suna fira da ita, Rabi'a kuma tana wanke wanke a ƙofar ɗakin mama Amina ce ta shigo idonta jajir fuska ta kumbura babu sallama bata ce musu komai ba ta shiga ɗakin Inna Ismael ya ce zanga lokacin da yarinyar nan za tai hankali wallahi ana girma ana ƙara hankali amman ke ƙara hau kacewa kikeyi, Inna ta kalli Ismael ta ce  "dan Allah ka rufa mun baki ban san dogon zance ko baka ga yanda ta shigo a furgice bane Ismael yaci gaba da cewa Allah yasa ba wani haukan tayi ma mijin ba ya kileta, Inna tai banza dashi ta tashi ta shiga ɗakin ta samu Amina kwance a saman kujera tana kuka Inna ta kamo Amina ta ce "dan Allah ki natsu ki faɗa mun abinda yake faruwa, Amina tayi banza da Inna taci gaba da kukan ta Inna tayi tayi ta faɗa mata abinda yake faruwa amman taƙi magana, Inna ta tashi ta fita kai tsaye ɗakin Baffa ta shiga ko sallama ba tayi ba ta bankaɗe ƙofar ta faɗa, Baffa yana zaune a saman darduma yana jan carbih Inna ta shigo ta fara bashi labarin abinda ke faruwa har tayi ta gama Baffa bai ɗaga kai ya kalleta ba, Inna tasa mai kuka ta na cewa saboda ita ba yarinyar so bane shiyasa yayi banza da ita amman da Fatima ne da tini ya fusata yayi waje. Inna taci gaba da magana tana cemai wallahi yaji tsoron Allah ya daina nuna bam bamci a kan iyalan shi har tayi ta gama bai kalleta ba Inna tasa kai ta fita, Bayan fitan ta Baffa ya tashi yaje ya tsaya a bakin ƙofa ya hango Rabi'a tana kwashe wanke wanke Ismael kuma yana zaune a inda yake tin ɗazun bai motsa ba, Baffa ya kira Rabi'a ya ce "ta kira mishi Mama sannan ta kira mishi Amina a ɗakin Inna, Baffa ya kalli Ismael ya ce "zoka kira mun gadanga ko Nasser a waya Ismael ya tashi yabi bayan Baffa da ya shiga ɗaki, Baffa ya bashi ƙaramar wayar da Aliyu ya siya mai ya ce  maza kira mun su kabani wayar, Ismael ya kira Aliyu ta shiga tana ringing bai ɗauka ba sai ya kira Nasser ringing ɗaya Nasser ya ɗauka Baffa ya karɓi wayar bai tsaya amsa gaisuwar da Nasser yake ba ya ce  kazo gida ka sameni yanzu, Nasser ya ce gayi nan zuwa Baffa yaba Ismael wayar Ismael ya amsa ya kashe wayar Mama tayi sallama ta shiga ɗakin. Baffa ya samu guri ya zauna Mama ta zauna kusa dashi Baffa ya kalli Ismael ya ce "ka gaya ma tsohuwarka ita nake jira. Ismael ya fita yana ƙunshe dariya ɗakin Inna ya shiga ya same su zaune ta tasa Amina a gaba tana kallo ita kuma Amina ta nata kuka, Ismael ya kalli Inna ya ce  "Baffa yana jiranku keda wannan mara kunyar yana faɗin hakan yayi waje da sauri, Inna tace daka sani ka tsaya kaga a binda zanyi maka ƙaramun mara kunya kawai Inna ta hau lalaɓa Amina akan ta tashi suje kiran da Baffa yake musu. Daman tin ɗazun take lalaɓa ta amman taki motsawa suna cikin hakan Nasser yayi sallama ya shigo ya tsaya bakin ƙofa. Inna ta amsa sallamar ya duƙa har ƙasa ya gaishe ta Inna ta amsa ta tambaye shi iyali ya ce Alhamdulellahi Nasser ya kalli Amina ya ce waye sa'an wasanki a gidan nan da zaki shanya mutane zaman jiranki Amina ta duƙar da kai ƙasa. Inna tai karaf ta ce  "bacci ne ya ɗauke ta yanzu ta tashi Nasser bai kara magana ba ya fita Amina ta tashi tana tura baki tabi bayan shi Inna tabi ta a baya. Amina tayi sallama ta shiga ɗakin ta gaishe da Baffa ta gaida Mama ta samu guri ta zauna Baffa ya kalli Amina ya ce "lafiya kika zo kina kuka kuma kinƙi magana Amina ta duƙar da kai tana hawaye ta ce "Daman shi ya ce in zo gida sai ya nemeni Baffa ya kalli Nasser ya ce "kira mun mijinta muji gaskiyar zance, Nasser ya miƙama Amina wayarshi ya ce "tasa mai number shi Amina taƙi karɓan wayar Baffa ya daka mata tsawa ya ce idan tai wasa yanzu nan zata ji a jikinta, Hannu yana rawa ta karɓi wayar tasa number Nasser ya karɓa ya baɗe kiran gaba ɗaya sannan ya kira ringing ɗaya a ka ɗauka haɗe da sallama, Suka gaisa da Nasser tin kafin Naseer yayi magana ya riga shi Ya ce "Amina ta zo gida Nasser yayi banza dashi ya cigaba da cewa. Wallahi Amina bata da mutunci ga rashin kunya ga rainuwa idan yayi mata abu sannan kuma ta raina mahaifiyar shi bai isa yasa ta ko ya hanata ba. Duk abinda yayi mata bai iya ba ga hangen rayuwar wasu. Ga faɗar baƙar magana hatta mahaifiyar shi gaya mata ta keyi dan Allah su barta a gida ta kwana biyu ko zata sanja hali amman shi gaskiya ya gaji da ita. Nasser zaiyi magana Baffa ya hana sai da suka gama jin abinda ya faɗa sannan Baffa ya karɓi wayar ya ce " idan babu damuwa yana son ganinshi ko zuwa anjima Sager ya ce " in sha Allah zaiyi ƙoƙirin zuwa. Bayan sun gama magana ya kalli Inna da ke tsaye a bakin ƙofa ya ce "ta shigo ya kalli Nasser da Amina tin kafin yayi magana suka fita. Baffa ya kalli Inna ya ce " hanakalin ki ya kwanta kin ɓata mun tarbiyan yarinya Inna ta ce "tayaya daga faɗan magana zai hau kai ya zauna babu bincike ita yarinyar mana a tambayeta aji ta bakin ta. Baffa ya kalli Inna ya ce "duk abinda ya faɗa bakiji ba Baffa ya cigaba da cewa wallahi kinji na rantse duk abinda ya faɗa ta aikata shi. Baffa ya cigaba da cewa cikin yarana nasan halin kowa nasan abinda in a kace sun aikata zan yarda amman saboda ƙin gaskiya irin naki kince sharri a kai mata. Inna ta fara hawaye Baffa ya ce "ta adana hawayenta domin lokacin zuban su baiyi ba ya ƙara da cewa ta fitan mishi a ɗaki zai zo ya sameta Inna ta fita tana kuka. Mama ta kalli Baffa za tayi magana ya da katar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu ganin hakan Mama tayi shiru tana kallon shi. Baffa ya ce " tasa Rabi'a ta kawo mishi tea idan ta fita. Mama ta najin hakan ta miƙe tana cewa dan Allah yayi haƙuri kar yasa wannan damuwar a zuciyar shi tinda baida isashen lafiya. Bayan fitan Mama daga ɗakin Baffa ɗakinta ta nufa ta samu Rabi'a tana guga Mama ta ce " ta haɗa ma Baffa Lipton ta kai mishi bata jira amsar da Rabi'a ke bata ba ta shige bedroom domin ta kwanta. Rabi'a ta kashe socket ta fita kitchen ta shiga ta haɗa kamar yanda ta san yana so ta shiga ɗakin bayan tayi sallama ta samu Baffa zaune a inda Mama ta barshi. Rabi'a ta duƙa tayi mishi sannu da jiki ta miƙa mishi tean Baffa ya karɓa yana samata albarka. Rabi'a tana son Baffa saboda duk idan suka haɗu sai ya sa mata albarka ko gaishe shi taje yi da safe zaita mata addu'o'i. Rabi'a ta koma ɗaki ta cigaba da aikin ta. Bari mu koma gidan Aliyu Ta Batulu ✍️ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels